Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga raɗaɗin da nake ji a zuciyata..."

"Ya isa dalla." Ya daka mata tsawa yana dakatar da ita da hannu, yayinda ya sauke mata wani banzan kallo daga sama zuwa ƙasa, don shi a yanzu babu wacce ya tsana sama da ita a duniyar nan, jin takaici da baƙin ciki yake yi duk sanda ya kalle ta ya tuna da Yaran sa da tayi masa sanadin mutuwar su, shiyasa cike da kakkausar murya yace, "daga yau sai yau zan buga miki babban worning, muddin kika sake takowa ƙofar gidan nan nema na ko da wata magana, wlh za ki sha mamaki na, bani da sauran alaƙa da ke tunda na datse igiyoyin auren mu ba na son sake tozali da ke, kuma idan kika ci gaba da tunzura Ni za ki ga mai zan yi, wlh nayi dana-sanin sanin ki a rayuwata Zeena, ba ki amfane Ni da komai ba sai baƙin cikin da ba na jin zai iya gushe wa a cikin raina har sai idan na koma ga mahaliccina, Yara biyu fa. Yara biyu kika yi min sanadin su kuma kike tunanin zan iya ci gaba da zama da ke? Ke wacce iriyar Jahila ce? Ai Ni sai yanzu ma nake nadama a rayuwa, da ban kasance Mazinaci ba babu yanda za a yi in haɗu da Mace kalar ki mazinaciya fasiƙa, annamimiya, mayaudariya, kin cuce Ni kin cuce Ni Zeena, bazan taɓa yafe miki ba kin yi sanadin raba Ni da ƴaƴana..." Dole yayi shiru sabida jin wani kuka ya taho mishi, tuni ya kasa tsayar da hawaye a kan fuskarsa, yayinda yake jin wani irin ƙunci na sake tabaibaye masa zuciya, idan ma ya ci gaba da tsaya wa yana kallonta ko yana sauraron kukan ta, komai zai iya faruwa da shi, don haka ya juya da sauri ya shige gidan su tare da datse ƙofan da ƙarfi

Zeena kuma kuka sosai take yi a wurin ta kasa ko motsa wa bare ta tashi, sai ma zama dirshan da tayi tana ci gaba da tsage baki tare da kurma uban ihu sabida shi kaɗai ne sauƙin ta a yanda take ji a ranta

Aliyu kuma sai da ya share hawayen sa sannan ya shiga ɗakin Mahaifiyar nasu yana kwaɗa kiran Usman

Da sauri Usman ɗin ya tashi daga kwancen da yake yana amsa wa

"Daga yau kar in sake ganin ka shiga harkan yarinyar nan, babu ruwan ka da ita, idan kuma ka ƙi wlh zan mummunar saɓa maka tunda ba wurin ka ta zo ba."

Tura baki yayi yana kawar da fuska bai ce komai ba

Inna kuma da ke zaune tana sauraron su tace, "nima dai abun da na gani kenan, Yaro kamar yana jira daga jin an ce ita ce ya zari ƙafa ya fita, to da me zaka yi mata idan ka fita? Kai ba wurin ka ta zo ba ina ruwan ka da ita?"

"Ki bar sa Inna, yana ganin wasa nake mishi ya sake kula ta ya gani." Ya ja ƙwafa yana juya wa da ninyar fice wa daga ɗakin

Amma sai Inna ta kira sa tana faɗin, "dawo Aliyu ka zauna muyi magana, don nima na soma gajiya da ganin ka haka babu aure, tun yaushe ku ka rabu da yarinyar nan amma har yanzu shiru babu wani labarin maganar auren ka? kayi shiru ƙememe ka ƙi neman Mata, haka zaka zauna kenan?"

"Inna Ni fa a halin yanzu babu wata Mace da zan sake kallo bare har in ji sha'awar auren ta, abun da ke damu na ya ishe Ni, ki bar Ni kawai."

"Ai kuwa baka isa ba, ya zama dole ka nemi Mata kayi aure don bazan bar ka haka nan kana zaune babu Mata ba, ba shiyasa Zeenatun take maka zirya ba kodayaushe tunda jahilci ke damun ta; an yi mata saki Uku bata san ta haƙura ba kamar wata mayya? Idan kana da Mata ai baza ta sake waiwayan ka ba bare ta tako ƙofar gidan nan."

Shiru yayi yana sauraron Innan ya kasa cewa komai

"Kayi shiru ina magana, ko baka ji mai nace maka bane? Tun wuri ka nemo mata kayi aure; idan kuma ba haka ba Ni zan nemo maka wlh."

"Shikenan Inna na ba ki zaɓi ki nemo min da kanki, amma Ni bazan iya nemo wata Mata in aura ba yanzu."

"Ato! Da dai ya fi maka, ai Ni kam mai sauƙi ne zan nemo maka mata duk inda take, ga su nan Yara da yawa a gari ƴaƴan mutunci, Ni ina ga ma gwara ka nemi Yaran gidan Hanne don yaran suna da kamun kai wlh babu laifi, don na san kaima ka sansu Yaran da suka tashi a maƙotan mu har suna shigowa gidan nan? Ƙannin Muhseen?"

Shiru Aliyu yayi mata don shi kwata-kwata bai gane su ba, in fact ba bai san wanne Muhseen take taɗi ba

Yayinda Usman kuma da murnan maganar ta cika sa yace, "wlh kuma Inna zasu dace don Yaran akwai tarbiyya babu ruwan su."

"Nima abun da na gani kenan, sai ya nemi Babbar A'isha ya aure ta, kai na san ka san gidan da suka koma sai ka raka sa har gida ya duba yarinyar."

"To Inna Insha Allahu, ko yanzu ma wlh idan ya shirya sai mu tafi."

Harara Aliyu ya watsa mishi yana miƙe wa tsaye tare da furta, "in na shirya zamu je ya nuna min gidan, Ni zan fita."

"To Shikenan sai ka dawo, amma dai kar ka ɗauki maganata da wasa, ka shirya a gobe ma ku je wurin ta ka ganta; tunda babu tabbas zaman ka koyaushe zaka iya barin garin."

To kawai yace mata yana fice wa don shi ba daɗin zancen yake ji ba

Yana fita su kuma suka dasa hiran maganar da yanda komai zai kasance da zaran sun daidaita kansu, don in har sun samu yanda suke so nan da nan za a yi auren a huta. Inna ma da kanta tace zata je ta nema mishi iri wurin Umman su A'ishan, tunda sun zauna a anguwa ɗaya an yi zaman mutunci da juna.
[03/01, 4:54 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼














            *PAGE:31*

_____Washe gari kamar yadda Inna tace su Aliyu su shirya su je wurin A'isha, shi har ya manta da maganar amma sai da ta tilasta mishi babu yanda zai yi haka ya shirya, suka fita da Usman ya raka sa har gidan tunda shi ya san gidan


Bayan sun je; sai Usman yace, "to yanzu Yaya Ni zan wuce kallon ƙwallo ga gidan nan na kawo ka, sai mun haɗu a gida, Allah yasa a dace ku daidaita."

Wani kallo Aliyu ya watsa mishi yace, "kana nufin bari na zaka yi a nan? Uban waye zai kira ta?"

Dariya yayi yace, "ah! Yaya ga Yara nan suna gifta wa; ka aike su sai su kira maka ita, ko kuma bari in sauka sai in aike su, amma Ni tafiya zan yi gaskiya ina da kallo."

Shiru Aliyu yayi masa don takaici bai ce komai ba

Shi kuma Usman ya ƙumshe dariyan sa yana sauka a machine ɗin tare da kwaɗa wa wani Yaro kira; da ya hango shi can nesa zai shiga wani gida, "zo nan Yaro, don Allah shiga nan gidan ka ce ana kiran A'isha."
Yaron yana tafiya sai Usman ɗin yace, "Ni Yaya zan tafi, sai mun haɗu a gida."

Aliyu bai yi mishi magana ba, sai ma sauka da yayi a kan machine ɗin yana tokare ta, tare da jingina bayansa ya sunkuyar da kansa ƙasa


Usman kuwa tuni ya bar wurin har da ɗan gudun sa, ganin time ɗin kallon ya wuce zai iya rasa wasan

While Aliyu yana nan jingine a machine Yaron ya dawo ya faɗa masa

"wai tace in ji wane ne?"

Shiru yayi yana kallon Yaron, sai kuma ya ɗan ja tsaki yana haɗe fuska tare da furta, "ka ce Aliyu."
Har Yaron ya tafi sai kuma ya kira sa sabida tunanin da ya zo mishi a rai, in har bai manta ba ya ji Inna tana faɗin yarinyar tana karatu, sanin cewa ko ya faɗa haka ba lallai ta fito ba shiyasa yace mishi, "ka ce ɗan makarantar su ne yake kiran ta."

Yaron ya shiga gidan har Falon Munira tunda suna can a zaune ne, dayake Umma ta tura shi can tace, "ya je ya faɗa mata tana can sashin Munira."
Dawowar Yaron na biyu sai ya sanar mata saƙon Aliyu

Amina tace, "to fa! Wa kike tunanin zai zo wurin ki da yamman nan Aunty A'isha?"

A'isha tace, "ba wannan ba, Ni wa ya taɓa zuwa wuri na da za a ce ɗan makarantar mu ne? In fact ma babu namijin da na taɓa magana da shi tun zuwana school ɗin nan bare har muyi sabon da zai zo gidan mu, anya Ni A'ishan?"

Dariya Munira ta fashe dashi tana cewa, "kai Aunty A'isha, ashe har yanzu halin nan naki na miskilanci yana nan? Tun fara karatun nan naki babu namijin da kike kula wa? Gaskiya akwai gyara a lamarin ki."
Sai ta dubi Yaron tace, "Sagir, jeka ka faɗa masa ga ta nan zuwa."

"Wai Aunty wlh ban san shi ba, ina ga fa ba Ni A'ishan bane, sai dai ko Amina ta leƙa ta gani."

Da ƙarfi Amina tace, "wa? Ni? A kan me zan leƙa ba Ni ake kira ba? Wlh babu inda zan je."

"Don Allah Aunty A'isha ki tashi ki je, ya za a yi ki san wanda ya zo in ba ki je kin duba ba? Ta yiwu wani abun ne ya kawo sa na maganar school ɗin, ki je ki duba don Allah."
Cewar Muniran tana kallonta

Sai A'ishan taɗan margaya kai alamun amincewa, duk da a zuciyarta tana mamakin a ce wani ya zo wurin ta daga school, to waye ta sani ita da ba ta kula kowa? Ko Matan ajin su bata san sunayen su dukka ba bare Maza da ba sa gabanta. Littafin hannunta ta ajiye tana mike wa tare da furta, "to Aunty Munira ara min Hijabin ki."

Mike wa Munira tayi tana wuce wa dakin nata da cewan, "wanne Hijabi kuma? Sai dai gyale, ke dai wlh har yanzu baza ki waye ba, kina ƴar jami'a amma kanki har yanzu yana cikin tukunya."

Dariya Amina ta kwashe dashi

While A'isha tana faɗin, "eh dai na ji, don Allah ki bani Hijab ne domin dashi na saba bazan iya fita da gyale ba."

Munira bata kula ta ba har ta shiga ta fito, ta ɗauko mata farin gyale tana miƙa mata tace, "ga shi ki saka, kar ki wani saka Hijab."

"Wai Aunty sai ka ce wajen saurayi zan je da za ki ɗauko min gyale? Ni fa ban ma san kowaye ba, don wlh ina ji a jikinta sai dai ɓatan kai yayi ba wuri na ya zo ba, ki bani Hijabi in sa bazan iya fita da gyale ba tunda ban saba ba."

Hararanta Munira tayi tace, "Allah bazan bayar ba, ki yafa ki tafi ko ki tafi a haka babu gyalen."

Tsayawa tayi tana kallonta baki a sake

While Amina ta samu abun dariya, sai ɓaɓɓaka wa take yi har da su tafa hannu

"Za ki ɓata mishi lokaci fa."

"To wai taya ya zan saka gyalen ban iya yafa wa ba? Ba kya ganin kayan da ke jikina ne? Gaskiya bazan iya fita a haka ba ko kuma in koma daki in ɗauko nawa."

Tsaki Munira ta ja tana miƙe wa tace, "wlh ke fa banza ce Aunty A'isha, ban san sanda za ki waye ba, Allah ba don ina ganin girman ki ba sai in ɗuɗɗura miki ashar."
Sai ta ƙwace gyalen tana ƙoƙarin yafa mata tare da yin mata rolling ɗin sa tana ci gaba da yin mata tsiya

Ita kuma A'isha ganin tayi mata rolling kamar Hijab shiyasa ta dena ƙorafin since at least ya rufe mata ƙirjinta, "ba dai yanda zan yi ne an fi ƙarfi na, bari in tafi."

Ta wuce ta fita ta bar su nan suna mata dariya tare da gulman ta, amma bata kula su ba ta fice zuwa wajen

Aliyu har ya gaji da tsayuwa ya koma kan machine ɗin ya zauna, sai ya ɗan kwantar da kansa a saman hannunsa ya rufe idanunsa
    

Ita kuma fitowar ta ta hange sa daga nesa da gate ɗin, duk da ba ta ganin fuskarsa amma ta san bata sanshi ba gaskiya, wurin sa ta nufa tayi masa sallama cikin zaƙin muryanta da ke fita kamar tana yanga.





_Babu yawa na yau, sai a yi manage, da babu gwara ba yawa ko?_


[03/01, 4:54 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼













            *PAGE:32*

_____Ɗago kai yayi ya zuba mata ido yana kallonta; tare da amsa mata sallaman cike da sanyin murya

Itama idanunta a kansa, duk da yanayin kallon da yake mata amma haka ta jure tace, "sannu Malam, kai kake nema na?"

"Ni nake neman ki, ke ce A'isha?" Ya furta ba tare da ya ɗauke ido a kanta ba yana ci gaba da ƙare mata kallo

Ita kuma sai ta ɗaga masa kai ba tare da tayi magana ba; tana ɗauke kanta sabida yanda ya zuba mata idon a yanzu ta kasa jure wa

Shiru ya ɗan yi sabida shi dai bai san me zai ce mata ba, duk da a fakaice ƙare mata kallo yake yi

Doguwa ce samɓal kuma tana da kaurin jiki, don tana da cikan halitta sosai wanda ba don tsawon da take dashi ba za a iya saka ta a sahun masu jiki, sai dai kasancewar tana da tsawo sosai shiyasa sai jikin ya bi ya shanye; tsawon nata ya shige, kuma fara ce jawur da ita tunda asalin Mahaifinsu Shuwa'arab ne, zama ya kawo sa nan ya auri Umman su, daga ƙarshe kuma bai yi tsawon rai ba Allah ya amshi abun sa ya barta da Yara Uku tana ta ɗawainiya dasu a ƙauye, Allah da ikonsa da rabon zasu ji dad'i a kuma sanadin Yayansu Muhseen, sakamakon hazaƙa da Allah ya basa a makaranta ya samu scholarship; ya zo birni yayi karatu har ya samu aiki ya kwaso su suka dawo birnin su ma, amma dai sun sha wahala a rayuwa, sai dai kamar komai bazai wuce ba

Allah ya basu kyau daga ita har su Amina, a taƙaice basu da bambanci da Amina sai ma haske da Aminan ta fi A'isha, tunda ta fi ta jawur kamar irin zabiya-zabiya ne hasken ta ya kasance, amma komai nasu iri ɗaya ne duk wanda ya gansu ya ga Yaya da Ƙanwa, kawai shekaru A'isha ta fi ta kasancewar suna da ɗan tazaran shekaru,
Kuma ita A'isha tana da ƴar yanga a ɗabi'a da maganar ta ma, ko yanayin ta ka kalla sau ɗaya zaka iya fahimtar haka a tattare da ita, saboda nature ɗin ta ne

Shi kansa Aliyu kallo ɗaya sai da ya ɗan fahimci hakan musamman da tayi magana, yayi mamakin kyawun ta don bai yi tunanin ganin yarinyar a haka ba, in fact ma bai ga bambancin su da Zeena ba, don kyawu iya kyawu A'isha tana dashi babu abun da Zeena zata nuna mata, hakan ne yasa ya ɗan sha jinin jikinsa ya kasa magana don gani yake yi kamar ya dawo gidan jiya ne, sam yanzu Mace mai kyau ba ta burge sa, ya kasa magana sai ma shiru da yayi yana sake nazarin yarinyar a ransa

Ita kuma ganin yayi shiru bai ce mata komai ba, ga kallo da yake mata kamar zai haɗiye ta, abun da ta tsana kenan, shiyasa ta sake ɗagowa tana kallonsa tare da furta, "wai ko baka da abun faɗa ne zan shiga gida?"


Wannan maganar nata ya ƙara tabbatar da cewan alamun tana da tsiwa, don shi mai saurin fahimtar Mutum ne, amma in wani ne lokaci ɗaya zai saka ta a sahun irin Matan nan masu ficchi da wulaƙanci sabida yatsina fuska da kuma iyayi a magana, kuma exactly ɗabi'ar ta ne hakan,
"I'm sorry. Ni kaina ban san ta ina zan fara ba that's why nayi miki shiru."
Sai ya ɗan ja numfashi yana dauke idanunsa a kanta a karon farko tunda ya aza kallonsa a kanta

Shiru tayi ita kuma bata ce komai ba, amma har ga Allah mamakin sa take yi da kuma tunanin yanda zata yi ta juya ta shige gida, don gani take yi har da rainin wayon irin nasa

"Suna na Aliyu, kuma na zo wurin ki ne sabida Mahaifiyata da ta buƙaci in zo in duba ki; na san maybe Ni ba ki san Ni ba, amma ba ki manta Malama Adama; ta tsohon gidan da ku ka tashi ba?"

Haba sai yanzu take ganin kamar ta shaida fuskar, tabbas ta taɓa ganin fuskarsa amma ta manta, tunda ba wai ta san shi sosai bane bai wuce sau biyu ta taɓa ganin sa ba, shima daga nesa, shiyasa ta ɗan saki fuska tace, "Allah Sarki! Na tuna ta."

Murmushi yayi yace, "ok ina fata su Umman naki suna nan lafiya?"

"Lafiya alhamdulillah."

"Masha Allah." Sai ya ƙara yin shiru

Itama shirun tayi tana ɗan wasa da yatsun ta, tare da tunanin maganar nasa duk da bata fahimci mai yake nufi ba

"To zan wuce, ki bani numban ki sai muyi magana idan na je gida."

Kallonsa tayi, sai ta ɗan yi jim kamar baza ta ba shi ba, sai kuma tace, "ok."

Wayansa ya ciro ta karanto masa numban, sannan tayi masa sallama ta wuce ba tare da ta jira ya sallame ta ba

Inda ya bi ta da kallo kamar zai haɗiye ta, don babu ƙarya tana da abun kallon, shi kansa bazai ce ga inda ya ajiye ta ba, amma a hakikanin gaskiya bai yi zaton ganin kyawun ta har haka ba, halin Zeena yasa ya kasa tantance son A'isha yake yi a faraɗ ɗaya ko akasin haka, shin zai iya amince wa da ita ko a'a? Ga dai shi ta tsaya mishi a rai kuma da tunanin ta ya koma gida, babu abun da yake gani sai fuskarta wadda yake jin wani yanayi daban a kanta, amma kuma yana ji a ransa bazai iya auren yarinyar ba, kawai yana mata kallon cutarwa ce a gare sa, Mace mai kyau tana da hatsarin gaske, shi nan ya ga zahiri, ba ya son kuma ya koma ya ƙara tafka babban kuskure a rayuwarsa, musamman ma wannan da zata fi saurin fizgar Maza, ba ya son ya yanke hukunci a kanta amma ya san baza a rasa Maza masu bibiyanta ba, an sha shi ya warke gaskiya bazai iya ba. Don haka kai tsaye ya sanar wa Innan su, "ya ga yarinyar, amma bazai iya auren ta ba."

Da mamaki Inna tace, "to Saboda me?"

"Inna yarinyar gaskiya irin su babban hatsari ne a cikin jama'a, kinga dai yanda son zuciya da kyawun Zeena ya ruɗe Ni, na makance a kanta na aure ta duk da na san wace ce ita, to wannan ma ba na son a samu wannan matsalar, daga ƙarshe in zo ina dana-sani da auren ta."

"Ashsha! Gaskiya baka kyauta da kayi wannan tunanin ba, wlh baka kyauta ba da kake haɗa halayyar A'isha da Zeena, yarinyar da babu ruwan ta shiru-shiru da ita, ga kirki da sanin ya kamata, amma kake haɗa ta da wancan fitsararriyar, ina ka taɓa ganin an cakuɗa ruwa da wuta wuri ɗaya?"

Shiru Aliyu yayi

"To ka saurare Ni da kyau, Ni na san A'isha tunda sun zauna a nan mun yi rayuwa da su, wlh babu ruwan ta magana ma wannan bai dame ta ba, don har gwara Amina tana shiga mutane da surutu amma ban da A'isha, ko saurayi ban taɓa ganin ta tsaya dashi ba har suka bar anguwan nan, babu wanda ke zuwa wurin su sabida Yayansu da ke tsaye a kansu, idan zaka aure ta kawai ka aure ta da zuciya ɗaya, wannan ba irin tarbiyyar gidan su Zeena bace, kai ka san inda ka je ka nemo ta kuma ka san yanda gidan su yake, babu ɗaya ƙwaƙƙwara mai hali mai kyau a gidan su, su da suke kamar Ƙaruwai kana ganin idanun su a tsatsatsaye taya ya zaka haɗa su da su A'isha? Kuma na ga kai kake son kyawawan shiyasa tun farko nayi maka sha'awar su tunda su ma in kyawun ne suna dashi."

"A'a Inna, Ni ban ce ina so ba."

"To ko ma mene ne tunda ka rigada ka je har ka ganta, kawai ka riƙi zaɓin Allah ka tsayar da zuciyar ka wuri ɗaya, Allah zai dafa maka baza ka taɓa dana-sanin wannan auren ba, fatan mu dai Allah ya haɗa kanku kawai, ka ci gaba da neman ta in an dace shikenan, nima zan je muyi magana da Mahaifiyar nata domin su san da kai."

Shi dai Aliyu bai sake furta komai ba har ta gama maganar nata, sannan yayi mata sallama ya wuce ɗakin sa na gidan, since ya dawo nan suna kwana da su Habib, gidan sa kuma har an soma gyara wa an gama gini ya kai linta, ana ɗan gyare-gyaren a hankali.
***


       Tun daga ranan Aliyu bai sake koma wa wurin A'isha ba, a wurin ta ita ta manta dashi ma tunda babu shi a gabanta, zahiri bata san ma meye amfanin zuwa wurin ta ba, tunda ita akwai kamewa da miskilanci in dai a kan Maza ne, duk haɗuwar ka da kyawun ka ko kallo baka ishe ta ba karatu ne kawai a gabanta

Yayinda shi kuma Aliyu tana ransa maƙale, duk yanda ya so ya cire ta amma ya kasa, domin ita ba kalan Matan nan bane da naMiji zai gani ya ƙyale, dole sai ta shiga ran ka, duk da shima Aliyu akwai taurin rai ya ƙi yarda sonta yake yi, amma kuma ya kasa cire tunanin ta a ransa,
Tun ba ya biye wa Inna in tana mishi maganar ta har dai ya soma tankawa ya soma samun ra'ayi a kanta, daga ƙarshe ya nuna Innan ta je ta nema mishi auren ta, in sun amince ya yarda zai aure ta, don shi ba ya son a ja wani lokaci kuma ba ya son zuwa wurin ta tunda bai san me zai ce mata ba, kawai in ta amince dashi zai aure ta a haka

Allah da ikonsa kuma da Inna ta je wa Umma

Please Login or Register in order to submit comment