Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saka jallabiya a jikinsa. Yana ganin Hafsah sai yace, "Hafsan Mama har kin dawo kenan?"

Kunya ce ta kama ta tunda ta san ba sa ƴar haka dashi, musamman yanda ta ga yana mata murmushi, kanta a ƙasa ta kasa amsa mishi sai motsa yatsun ƙafafunta take yi

Sai yace, "haɗa min tea mai kauri ki kawo min ɗaki na yanzu ina jira." Bai jira cewar ta ba ya juya ya fice a ɗakin; hankalin sa a kan wayansa

Bata iya ɗago kanta ba sai da ta ji kamar fitan sa, sannan ta ɗago tana kallon hanyar da ya bi kamar zata saka kuka don jin abun da yace, "to me yasa yau zai ce mata ta kai mishi abu ɗaki?" Ta san bai taɓa ce mata haka ba, ba ya saka ta aiki ma sai idan Fauziyya tace mata, "ta ɗauko mishi abu kaza."
Jiki a sanyaye ta soma ƙoƙarin haɗa mishi tea ɗin tunda akwai flaks a kichen ɗin, kuma akwai ruwan zafi, hankalin ta ya ɗan kwanta tunda ta san Fauziyya ba ta cikin gidan,
Shiyasa tana gama wa ta ɗauki tea cup ɗin ta ɗaura a ɗan ƙaramin plate; sai ta sake shinkafar a cooler tunda ya gama dahuwa, da zummar idan ta kai mishi sai dai ta wuce baza ta dawo ba, tunda ta gama komai, dama suna da sauran miya already ta ɗumama

Lokacin Jibril ne kaɗai zaune a falo yana sana'ar nasa wato Game. Ɗago kai yayi yana kallon inda Hafsan ta nufa cike da mamakin ta, bai iya ce mata komai ba har ta shige, kana ya miƙe da sauri yana nufan ɗakin Sumayya don ya faɗa mata, "ya ga Hafsah ta shiga dakin Dadyn su".
[03/01, 4:46 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼










            *PAGE:21*

_____Yana zaune a kan gado, ta shigo ɗakin da sallama idanunta a ƙasa, kuma ta ƙi ƙariso wa ciki tana tsaye. Sai ya ajiye wayan hannunsa yana cewa, "shigo mana Hafsah."


A hankali ta taka zuwa ciki, sai da ta kusa isa wurin sa sannan ta ɗaga kai ta dube shi, sai ta duƙa a ƙasa ta ajiye mishi tana shirin tashi

Yace, "miƙo min."

Ɗauko wa tayi ta miƙa masa, sai ya haɗa da hannunta ya riƙe yana faman kallonta

Itama sai ta ɗago da sauri tana kallonsa idanunta har sun fara ƙwal-ƙwal

Murmushi yayi sabida ganin yanda ta tsorata, sai yace, "ko Mama ta faɗa miki wata magana ce? Na ga duk kin tsorata da Ni?"

Da sauri ta girgiza mishi kai tana shirin ƙwace hannunta

Sai ya sake tamke ta sosai yana cewa, "kar ki zubar min da tea ɗin kuma, ki bari in janye." Yayi maganar cikin sanyin murya yana ɗauke cup ɗin da ɗaya hannunsa, while dayan na riƙe da nata hannun. Bayan ya ajiye sai ya sake ɗago kai ya tsura mata ido, domin ya tone ta yana murmusawa yace, "ko kuma tsoron Auntyn naki kike yi don kin shigo turakan Mijinta?"

Kai ta sunkuyar cikin kunya tana girgiza mishi kai, ta kasa ma magana tsaban yanda jikinta ke rawa, duk wucewar second tsoro da fargaban abun da zai biyo baya yake biyo ta

Sai ya sakar mata hannun yana jan numfashi a hankali, har yanzu idanunsa a kanta yake cewa, "ba komai zan yi miki ba Hafsah, ki dena tsorata kinji?"

Kai ta ɗaga mishi tana son tashi tsaye, but ta gaza sabida rawan da ƙafafunta suke mata

Ganin halin da take ciki kawai sai yace, "ta tashi ta tafi." Ya so tambayarta wani abun ne, but ya fasa

Da sauri kuwa ta tashi ta fice har tana cin karo

Sai yayi murmushi kawai yana ɗaukar cup tea ɗin ya soma sha a hankali, while yana latsa wayansa da ya dauka

Ita kuma tana fita suka ci karo da su Sumayya suna zaune suna jiran fitowar ta. Basu ce mata komai ba, haka itama tunda tayi musu duba ɗaya ta ɗauke kai tana haɗiyar yawun tsoro, ta fice da sauri har tana harɗe ƙafafu

Da gudu itama Sumayya ta bi bayanta suka fita kusan tare. Babu tsammani sai Hafsan ta ji an riƙe mata wuyan riga ta baya an dawo da ita, "ke dan uban ki, uban me ya kaiki ɗakin Dady da kika shiga?"

Da rawan baki Hafsah tace, "wlh babu komai, shi yace in haɗa mishi tea in kai mishi."

"Cab ɗijam... Momy ta ba ki iznin shiga mata ɗakin Dady ne? Ko mu da muke ƴaƴan shi ba ma shigan masa ɗaki bare ke, to wlh ki ji da kyau yau sai na haɗa ki da Momy tunda ke ƴar iska ce, shegiya da idanu a tsakar ka." Sai ta kifa mata mari

Ihu Hafsan ta saka sabida bata yi tsammanin marin ba, ya saukar mata a ido, shiyasa tayi saurin rufe fuskarta ta saki kuka mai ƙara

"Ƴar matsiyata kawai baƙauyiya, ki jira na Momy itama bari ta dawo." Ta ture ta ta wuce tana ci gaba da zagin ta

Yayinda Hafsah ta faɗi a nan ƙasa sabida ƙarfin turin da tayi mata, kuka kawai take yi ta kasa ɗago wa sabida zafin abun da Sumayya tayi mata, a hankali kuma ta tashi ta nufi sashin su tana ci gaba da kukan

A haka ta je ma Mama, shiyasa hankalin Maman ya tashi ta hau tambayarta abun da ke faruwa?

Nan ta zayyane mata komai tana ci gaba da kuka har da su shashsheƙa


Sai Mama ta bata haƙuri ta rarrashe ta cike da tausayin ta, "ki yi haƙuri Hafsatu, insha Allahu komai mai wuce wa ne, wata rana ma baza su ganki ba ai, yanzu tashi ki yi alwala kiyi sallah kinga na ɗaura mana Macaroni, idan ya gama dafuwa sai mu ci, tashi maza kinga ana kiran Magriba."

Tashi Hafsah tayi tana share hawayenta zuciyarta cike da baƙin ciki, yanzu shikenan ita haka zata ƙare kullum ana cin zalunta? Bata da wata walwala da farin ciki sai idan tana wurin Mama? Wlh ta gaji matuƙa da wannan zaman, haƙurin ta ya ƙare baza ta iya ci gaba da zama a haka cikin wahala da takura ba, kamar wacce bata da gata, da a ƙauyen su ne babu mai taɓa mata lafiyar jiki, abu ɗaya ne kawai zai iya zaunar da ita na sauya musu gida da za a yi, amma wlh ba don haka ba baza ta ƙara zama ba dole sai dai ta tafi ƙauyen su, ta haƙura da karatun.






🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆


           Kukan yarinyar, shiyasa shi saurin ƙarisowa ciki da sauri yana nufan inda take, "Hanan." Ya furta yana ɗaukar ta da sauri ganin yanda ta dungura ta kai, har laɓɓanta sun fashe. Rarrashinta ya soma yi cike da tausayin ta yana shafa mata kai

While ita kuma sai tsandara kuka take yi kamar ana yanka ta, da alamun ta buge sosai ne


Rungume ta yayi sosai a jikinsa yana ci gaba da rarrashinta, sai ya nufi ɗakin Munira yana kwaɗa mata kira, sai dai da alamun babu ita a ciki. Ko'ina ya duba but babu ita, ransa ne ya soma ɓaci, amma kuma ya kasa cewa komai sai faman rarrashin yarinyar yake yi, ganin ta ƙi shiru shiyasa ya fita ya nufi sashin Ummansa

Tana kwance a tsakar ɗakin nata itama ta ji kukan Hanan ɗin, da sauri ta miƙe zaune tana cewa, "ah ah.. wa ya taɓa min Jikalle na haka ta ƙure gida da kuka?"

Shigowa Muhseen yayi da sallama a bakinsa. Ya taho ya zauna a kan sofa yana mata sannu

Ta amsa mishi tana cewa, "kawo ta nan, wa ya taɓa ta haka take wannan kukan? Yau dai an ƙure haƙurin ta kenan?"

Miƙa ta yayi yana cewa, "nima shigowa ta kenan na ganta a dungure a ƙasa, da alamun buge wa tayi."

"Ai kuwa ga bakin ta nan ya tasa, buge wa tayi, to yi shiru mana, yi shiru ƴar Mama, ina ita Muniran ta shiga ne?"

"Ban sani ba Umma, na duba ta ko'ina babu ita."

Kwantar da yarinyar tayi a jikinta tana girgiza ta, tare da faɗin, "to ita haka ake yi ne da zata ajiye yarinya babu kowa? Maimakon ta kawo ta nan sai ta fita? Ko babu su A'isha ai zan riƙe ta. Ɗauko min man can in shafa mata a bakin, ka ga sai tsittar da jini yake yi ma." Ta furta tana ɗan shafa mata bakin, "to yi shiru mana Takwarata, bari kukan haka nan."
Sai faman girgiza ta take yi, itama kuma yarinyar tana ɓare baki har da su ajiyan zuciya, sai tayi kamar zata yi shiru sai ta ci gaba

Muhseen da ya ɗauko man ya bata yana cewa, "Ni fa Umma wlh na soma gajiya da yawon Munira, wai me take ɗauko wa ne a maƙota da baza ta yi hakuri ta zauna a gidan ta ba? Kuma yanzu idan nayi magana a ga laifi na."


"Ai dole ne a ga laifin ka Muhseen, to mene ne laifi don ta shiga maƙotan? Laifin ta kawai don bata tambaye ka ba, amma ka dena ɗaukar abu da zafi haka, ka riƙa lallaɓa ta kana nuna mata ba ka so ai zata dena."


"Tun yaushe nake yi bata dena bane sai yanzu? Kawai Umma ba kya son laifin ta, in an yi magana kuma ki ce ina ɗaukar zafi, kullum ita kenan jawo ma mutane magana ana zuwa ana titsiye ta tsaban surutun ta yayi yawa, baza ta iya saka wa bakin ta linzami ba."


"To ai sai kayi kuma, tunda zancen kake so." Cewar Umma tana yi wa Hanan rawa tare da cewa, "wane ne ya buge min ke inye Jikalle na? Mama ce ta bar min ke kika faɗi ko?"


Yarinyar ta ɗaga kai tana ci gaba da shanye baki, sai kuma ta soma ƙoƙarin miƙa hannunta ga Muhseen tana kiran sunansa

Mike wa yayi, batare da ya ɗauke ta ba ya fice a ɗakin

Umma tace, "to kin gani, wanda kike yi don shi bai ma san kina yi ba, ba take yake yi ba, Maman ki ta ɓata mishi rai. Ɗauko kokon nan in zuba miki ki sha don na san har da yunwa yake ƙwaƙulan ki, yarinya duk ta jajjeme sai ka ce ba a yi miki wanka ba, bari itama Muniran ta shigo zan saɓa mata kuwa".
***

        Kai tsaye part ɗin su Muhseen ya wuce, ganin gab ake da kiran Magriba shiyasa ya fada wanka shaf-shaf ya yi ya fito da alwalan shi. Kaya ya saka ya fita daga ɗakin

A nan ya ci karo da Munira shigowar ta kenan tana kiran sunan Hanan

Kallonta yayi fuska a haɗe, kamar zai yi mata magana sai kuma ya cije leɓe yana wuce wa ba tare da ya kula ta ba, duk da ya ji tana masa magana amma bai ce mata uffan ba ya fice

Sai ta taɓe baki tace, "ka dawo kenan zaka fara haɗe ran naka, Allah yasa ba wani wajen na je ba, takalman Yara na je kaiwa da suka manta." Tayi maganar tana wuce wa ciki tare da shiga kichen, gass ta kunna ta ɗaura ruwan zafi sannan ta wuce ɗaki ta ɗaura alwala

Tana cikin sallan ne ta jiyo hayaniyar Hanan a Falo ita da Amina, ta dawo da ita. Bata ajiye ta ba sai suka zauna a Falon tana jiran fitowar Muniran

Lokacin sai ga Muhseen ya dawo daga masallaci. Bayan ya shigo ya zauna ne yake amsa gaisuwar Aminan da take mishi, yace, "yauwa, yau na dawo ban ganku ba, ina ku ka je?"

"Yaya ba a tashe mu Islamiyya da wuri bane, dayake yau ana taro."

Hanan da ta sauko daga jikin Aminan tana kiran sunan Baba ta nufe sa da gudun ta, ya ɗauke ta ya aza ta a jikinsa yana mata wasa

Sai Amina ta miƙe zata tafi. Yace, "ta dawo ta shiga kichen ta duba idan Munira bata ɗaura abinci ba ta ɗaura. Kin yi sallah dai ko?"

"Eh Yaya nayi."

"To." Ya amsa yana mayar da hankalin sa a kan yarinyar sa yana mata wasa

Lokacin Munira ta fito ta ƙariso wurin tana cewa, "Hanan, kin ji Ni shiru daga in je in dawo?"

Muhseen dai bai ce mata komai ba yana ta ma yarinyar wasa. Itama yarinyar ta ƙi kula sa sai faman washe ma Babanta baki take yi tana masa gwarancin ta

"Husband sannu da dawowa."

Bai ɗago ya kalle ta ba bare ta saka ran zai amsa. Sai tace, "Ni fa ba ko'ina na je ba ina nan maƙota ne, kuma takalma yara suka bari nayi baƙi shiyasa na mayar musu kar su tafi basu gani ba."

"Ni na tambaye ki ne?" Ya furta yana tsare ta da ido

Sai ta tura baki ta ƙi cewa komai

"Kin yi abinci ko yawon gantalin ya fi miki?"

"Ban yi ba, amma yanzu zan ɗaura tunda ina da miya ai, shaf-shaf yanzu zan gama ai." Sai ta miƙe kuma tana nufan kichen din

Ya bi ta da kallon takaici don ya san dama za a rina, haka kullum take yi in har ta fita gantalin ta, har zai dawo bai tarar da komai ba, sai dai ya je sashin Umma ya ci in sun girka, yau kuma ba ya jin zuwa and kuma yunwa yake ji sosai

Amina ce ta fito daga kichen ɗin, tace, "Yaya bari in wuce, ta ce zata ƙarisa."

"Ok." Yace da ita yana miƙe wa riƙa da Hanan ya koma nasa ɗakin. Bai fito ba sai da ya ji kiran sallan isha'i, sannan ya kai mata Hanan yana cewa, "ga ta nan, sauran kuma ki barta tayi wasa ba ki kula da ita ba."
Ya wuce bai jira cewar ta ba ya fice a gidan

Ita kuma sai aikinta take yi don ta ƙi ɗaukar yarinyar, ga shi sai shegen ɓanna da ita; tana ta faman yawo a kichen ɗin tana taɓa wannan ta taɓa wancan, sai gwaranci take yi

Can yarinyar sai ta fice ta nufi hanyar ɗakin Muniran, ashe tana can ta samu toilet ɗin ta a buɗe sai ta shige ta soma ƙoƙarin kunna famfo, ruwa ya zubo shaaa sai kan yarinyar. Yarinyar ta saki ihu tana ƙoƙarin guduwa ta zame tim a ƙasa, kanta ya bugu ta ƙwalla ƙara.
[03/01, 4:46 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A✍️*





                 *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





              *NASIHA*
A suratul Noor aya ta 26, tana nuna mana cewa lallai mata nagari na maza nagari ne.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace; " Idan wanda kuka yarda da addinsa da dabi'unsa yazo neman aure wajenku ku aura masa. Idan baku yi hakan ba, to ɓarna mai yawa zata kasance a bayan kasa. Tirmizi ya ruwaito shi.





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  560
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb.   310
2gb.    620
3gb.    1000
4gb.    1250
5gb.    1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb.  500
1gb.  550
2gb.  1000
3gb.   1450
4gb.   1900
5gb.   2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb.  550
2.9gb.   1000
4.1gb.    1400
7.7gb.     2300
10.0gb.   2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼










            *PAGE:22*

_____Da gudu Munira ta fita sabida jin ihun Hanan ɗin. A Falo suka ci karo da Muhseen shima ya kwaso da gudun; cuz shima ya ji ihun Hanan ne lokacin da ya sawo kai zai shigo Falon

Ɗakin Munira suka wuce a tare suna kiran sunan ta. Sai suka shiga toilet ɗin tunda a nan suka jiyo ihun ta yana tashi

Muhseen yayi saurin ɗaukar ta yana salati sabida ganin yanda jini ke zuban mata a baki, alamun ta fasa bakin ne, ga gefen goshin ta nan da nan ya taso ya kumbura. Yanda ya ruɗe ga kukan Hanan da take ƙara tsandara wa, sai ya fita da ita da sauri ko sauraron Munira bai yi ba. Kai tsaye motansa ya nufa, ya laluba aljihun sa yana ɗaukar key tare da buɗe wa ya shige, a jikinsa ya ajiye ta ya rufo ƙofan ya ja zuwa gate. Ko kaɗan bai bi ta kan Munira wacce ta biyo shi itama a ruɗe cike da tashin hankalin ganin halin da ƴarta take ciki

Ita da kanta ta je da gudu ta buɗe mishi gate saboda dama basu da mai Gadi

Dole Muhseen ɗin ya dakata bai fito daga motan da yake ƙoƙarin fita ya buɗe da kansa ba. Sai ya ja motan ya fice gidan da sauri, kai tsaye chemist ya wuce da ita aka duba ta, yarinyar sai kuka take yi kamar zata haɗiye zuciya, alamun dai ta bugu ba kaɗan bane. Tana jikinsa ake mata treatment a wajen; yana ta famar rarrashinta yana hura mata iska, duk ta haɗa gumi azaba ya ishe ta, daƙyar ta bari ma aka yi aka gama sannan ya biya kuɗin ya ɗauke ta suka fita. Har yanzu ta ƙi yin shirun ya rasa yanda zai yi da ita, sai da ya tsaya a wani shago ya siyan mata su chocolates ya buɗe mata, sannan ya bata yana ta famar lallaɓa ta, daƙyar ya shawo kanta ta amsa tana faman ajiyan zuciya tana lafe mishi a jiki, shi kuma ya sanya hannu yana ƙara kwantar da ita sosai tare da lallaɓa ta, sai a lokacin ya sauke numfashi yana tayar da motan a hankali ya nufi hanyar gida. Bai yi horn ba sai ya kashe Motan daga waje sannan ya fita tana jikinsa ya manne ta a ƙirjinsa, since har tayi barcin wahala ma. Gate ɗin ya buɗe sannan ya shiga da Motan ciki yayi parking, ya fito ya rufe suka wuce ciki

Bai samu Munira a falo ba, shiyasa ya ajiye yarinyar a saman kujera yana ɗan lallaɓa ta ganin tana motsi kamar zata tashi, sai faman ajiyan zuciya take yi har yanzu kamar tana a firgice, sai da ya tabbatar ta dena motsi sannan ya zare hannunsa daga jikinta yana ajiye ledan hannunsa. Tunda ya ga abinci a saman dining ya san Munira ta gama girkin, shiyasa kai tsaye ya shiga ɗakin ta ya same ta a can, lokacin tana sallah hakan yasa ya zauna a gefen gado yana jiran ta idar, kansa a ƙasa yana kallon yatsun ƙafarshi har ta idar

Lokacin ta zare hijabin tana kallonsa da cewa, "ina Hanan ɗin Husband? Babu abun da ya same ta ko?" Tayi maganar cikin tsananin damuwar da ya nuna a kan fuskarta

Ɗago kai yayi yana kallonta, yayinda fuskarsa babu annurin farin ciki yace, "meyasa wai ba kya jin magana ne Munira? Sau nawa zan faɗa miki ki dena barin yarinyar nan ita kaɗai sabida kin san tunda ta samu ƙafafun nan ba ta iya zama wuri ɗaya, kina barin ta tana yawo idan ta je tayi ɓarna ko ta yi wa kanta illa ba ki da asara ko? Yarinya ƙarama amma kin kasa yanda za ki yi ki kula da ita tunda ba ki damu da ita ba, kanki kawai kika sani ba ki da lokacin kowa sai naki dana Mutane..."

Katse shi tayi da faɗin, "kamar ya ba Ni da lokacin kowa sai nawa dana Mutane? Ni fa ban gane me kake nufi ba Muhseen ka dena juye-juye ka fito sak a Mutum ɗin ka, kai baka da magana da an tashi zance sai ka ce ban damu da kowa ba sai kaina, duk abun da nake maka ba ka gani duk wannan abubuwan da nake yi? Dole sai ka nemo laifi na ka yafa min tunda gani kake yi kamar ban iya komai ba?"

Cike da takaici gami da haushin yanda take ɗaga mishi murya cikin zafin ta, sai yace, "idan ina magana na faɗa miki ki dena katse Ni Ko kuma kina ɗaga min murya, wlh Munira muddin kika ci gaba da nuna min wannan ɗabi'ar zan ɗauki mummunar mataki a kanki, ke kenan ba ki san muhimmanci na; ba ki san ya kamata ba ina faɗa kina faɗa baza ki bari in gama maganata ba? Yanzu idan ba sakacin ki ba taya yarinyar nan zata shiga har bayi ta zubar da ruwa ta zame a ƙasa amma ke kina can kina aikin gaban ki baza ki ɗauke ta ƙi goya ta ba? Ina ce dare ne yanzu kowacce uwa ta gari ɗaukar ƴaƴan ta take yi ta goya su a baya ta killace su, amma ke ba abun da kika iya sai dai ki sake ta tayi ta yawo, ko ki tafi gantalin ki ma ki barta ita kaɗai, bayan kin san akwai abubuwan da zata iya jawo wa a gidan nan wanda zai iya mata illa."

Itama Muniran cikin haushin maganar nasa, har da ƙara ɗaga murya fiye da na ɗazu tace, "to so kake yi na kasu da yawa bazan yi abun da ke gaba na ba sai in zauna renon ƴa? Ai naga itama ƴarka ce kai meyasa da ka dawo baka ɗauke ta ka goya ta ba? Kuma da kake cewa ina ɗaga maka murya ai na ga a kan gaskiyata nake, bazai yiwu a ce in zauna kana gaya min abun da ka ga dama ba, don ina da hujjar kare kaina wlh, baka fi Ni baki ba."

"Haka kika ce ko?"

"Eh haka nace, ai kaima ƴarka ce sai ka ɗauke ta ka goya ta tunda nima aikin yayi min yawa."

A fusace yace, "to gidan uban wa kike zuwa da baza ki zauna ki yi aikace-aikacen ki ba har sai dare yayi ba ki gama ba? Sannan idan an yi magana ki ce aiki ne yayi miki yawa, an ce kar ki zauna a naki gidan ne ki yi aikin har sai dare yayi miki? Mu kenan fa mu uku a gidan nan; yanzu ba kya girki da su Umma, amma kullum ba kya gama aiki sai dare ya tsala, lokacin da Bawa yake samun hutu amma ke lokacin ne kike naki ɓuruntum, kuma idan an yi magana ki nemi ki tsige Mutum, haka kika ga sauran Matan suna yi? To wlh zan buga miki babban worning na ƙarshe, don na gaji da iskancin ki, kar ki ga ina ƙyale ki kina abun tsiyan ki ki ce tsoron ki nake ji, duk ranan da kika sake fita maƙota ba tare da izni na ba, wlh kin ji na rantse miki a bakin auren ki, ƙaryan iskanci kike yi Ni na fi ki na shanye ki, ga hanya nan ki fita ki gani." Yana gama faɗar maganar nasa ya tsallake ta ya fice a ɗakin cikin fushi da huci

Yayinda Munira ta raka shi da sakakken baki zuciyarta na mata suya da zafi, kamar an tokare mata wani abu a maƙoshi dan baƙin cikin maganganun sa, miƙe wa tayi da zafin ta ta soma ninke darduman tare da mayar wa ma'adanan ta, sai ta ninke hijabin shima ta ajiye tana zama

Please Login or Register in order to submit comment