Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ai baku kaɗai bane a cikin ha'ula'i tunda mu ma muna ciki; kullum farashin mai ƙaruwa yake yi, yanzu shekaran jiyan nan kina ji a rediyo aka ƙara kudin mai, amma har kuna da bakin magana."

"Aka ƙara kuɗin mai; to mu muka ƙara ne? Kawai dai baku da tsoron Allah amma wlh wannan zalunci ne, ai tun ba yau ba kuke wannan abun, idan mutum yayi dare maimakon ku taimake sa, a'a; ƙara masa kuɗi kuke yi don babu yanda za a yi dole a biya ku."

"Hajiya Ni fa ba surutu nace ki hau ki yi min ba, babu dole sai ki sauka min a machine, ha'a ana abu dole ne?"

Duk da Sauda tana tsoron ya sauke ta; amma hakan bai sa tayi shiru ba sai rattafa zance take yi ta ƙi tayi shiru bare ya ga wallan ta

A haka suka ƙarisa anguwan ita ta ƙi tayi shiru; shima haka, kowa bai san ganin laifin kansa

Tana ba shi kuɗin sai ya ja machine ya burga mata hayaƙi yayi tafiyar sa

Ai kuwa ya sha zagi, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, amma baƙin cikin ta tuni ya wuce bai san ma tana yi ba, dole ta ja ƙwafa ta bar wurin tana ci gaba da zagin sa,
A haka ta shiga gidan nasu tana kwaɗa sallama

Su Suleiman da ke cikin daki; da gudu suka fito suna ihun kiran Maman su,
Rungume ta suka yi suna dariya

Yayinda Haidar har ya fara cewa, "Mama ina tsaraban mu? Kawo ledan in riƙe miki."
Yayi maganar yana ƙoƙarin ƙwace ledan hannunta

"Kai bari mana Haidar, ina wasa da kai ne?"

"Mama, Baba ya dawo yana ta neman ki, ya siyo mana tsire har mun cinye."
Cewar Suleiman da yake farin ciki da zumuɗin sanar mata

Inda a lokacin ne Ruƙayya ta fito daga ɗaki tana yi mata sannu da zuwa

Tace, "yauwa Maman Safina, kin ganmu sai yanzu?"

"Wlh kuwa, yanzu ma Baban su Haidar ya dawo yake tambayana ke, nace masa ba ki dawo ba, ai naga kamar ya fita ma."

"Ke dai bari, abun hawa na rasa, shiyasa abun da ke bani haushi kenan in dai wurin su Hauwa ne, kayi ta neman abun hawa baza ka samu ba tunda sabuwar anguwa ne, dole sai ka fito bakin titi; ga shegen nisa."
Sai ta miƙa mata ledan hannunta bayan ta ba su Haidar nasu ledan, "ga wannan Hauwa tace a ba ki, na Safina ne, ina take?"

"Tana ɗaki kwance, yau dai jikin nata babu dad'i wlh, shiyasa ma ban fita ba a haka muka wuni yau tana da kela amai, kokon da na zuba mata ma karshe bata sha ba wlh."
Tayi maganar cikin damuwa

Inda Sauda ta nuna tausayawar ta tana faɗin, "mu je in ganta, kuma ba ki siyan mata magani ta sha ba?"

"Babu ko sisi a hannuna wlh Aunty Sauda, haka nan muka wuni a haka."

Kuɗi Sauda ta ba Suleiman ya fita ya je ya siyo mata maganin zazzaɓi

Sai Ruƙayyan ta amsa ta jiƙa mata sannan ta tashe ta ta bata, tana ta kuka yarinyar duk da kure gidan da ihun ta,
Dayake biscuits da su chocolates ne Hauwa ta basu, sai ta zuba mata a gabanta tana ta rarrashinta tana ɓare wa tana bata, hakan ne yasa ta samu sauƙin ta har ta iya yin shiru ta sha kayan ƙwalamar

Dayake Sauda tayi abincin dare; ƙarshe sai dai ita ta basu suka ci suka kwanta tunda bata da wani sauran abinci a ɗakin,
Yayinda ta kwanta da tunanin inda Sadis ya tafi ya bar su tsawon wannan lokacin, ba ta jin akwai lafiya gaskiya sabida a jikinta haka take ji, duk ta damu, Allah -Allah take yi gobe yayi ta fita ta duba shi ko zata dace ta samu labarin inda ya je

A washe garin ne ita kuma Sauda ta fita maƙota yawon ta da ta saba, a can ta ji labarin da ke faruwa, sai ta dawo gida da sauri lokacin Ruƙayya tana shirin kammala aikin ta ta fita, sai kawai Sauda ta kawo mata labarin da ya bi gari an ɗaure Sadis a station, sakamakon kama sa da aka yi a gidan wani Soja, ashe labari duk ya baza gari

Duk yanda Ruƙayya ta so ta jure ta ɓoye halin da take ciki kar Sauda ta gane, amma ina ta gaza, haka ta fashe da kuka ta shige ɗaki ta zauna tana rera shi, wannan wanne irin bala'i ne? Wanne irin jarabawa ne wannan? Ita kenan a haka zata ci gaba da zama cikin baƙin ciki da ƙunci? Wlh haƙurin ta ya zo ƙarshe baza ta iya ci gaba da zama da Sadis ba, ko don yaranta da zata haifa nan gaba, wannan karon baza ta iya ba, abun kunyar yayi yawa, tun tana ƙaramar ta baƙin cikin sa zai kashe ta,
Shi yasa ta yanke shawaran barin gidan, koda ya dawo sai dai ya biyo ta da takardan sakin ta amma baza ta iya ci gaba da zama dashi ba,
Haka ta tattara kayan ta Sauda na bata haƙuri, amma ina; bata saurare ta ba, ta bar musu gidan tana kuka ta koma gida, ko me zai faru baza ta sake dawowa gidan sa ba, ta bar shi har abada, ta gaji da auren Mazinaci mashayin gida, son zuciya da hawa motar kwaɗayi bai amfane ta da komai ba, tunda ga inda ya sauke ta a tashan wulaƙanci.







🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

        Tana cikin tuɓe kayan makarantar ta; tunda shigowar ta kenan gidan, ta samu Mama na sallah a falo, har ta zauna sai kuma ta tashi ta shige ɗaki sabida fitsarin da ya matse ta, tana yi ta fito ta soma tuɓe kayan school ɗin,
sai ta ji ana buga ƙofan gidan da ƙarfi, hakan ne yasa ta ɗan ƙara sauri ta gama cire kayan, sannan ta dauko doguwar rigan material mai kalan pitch, da design na kalan ruwan zuma da baƙi, kayan sun amshe ta sosai kuma sun yi wa chocolate colorn skin ɗin ta kyau, ko ɗankwali bata tsaya ta ɗauka ba sabida sauri don ta je ta buɗe ƙofan, tunda ta san Mama tana sallah kuma ga shi ana ta buga ƙofan babu jingirta wa,
Da gudun ta ta ƙarisa bakin ƙofan tana faɗin, "ana zuwa don Allah."
Buɗe ƙofan tayi, wa zata gani?

Fauziyya ce tsaye ta cakare cikin wata sabuwar atamfa sai ƙyalli take yi, yayinda ta yafa mayafi har kanta mai shara-shara; fuskarta babu fara'a ko misƙala zarratan, tana riƙe da key din mota a hannunta itama ta zura wa Hafsan idanu

Da sauri jiki na rawa sabida tsoron ganin ta; ta soma mata sannu da zuwa har da duƙa wa tana gaishe ta

Sai dai kamar da dutse take yi, bata ce uffan ba sai ma wani kallo da ta watsa mata tana ƙoƙarin shigowa ciki

Hakan ne yasa Hafsah ta matsa mata daga hanya

Sai da ta gama shigowa ciki tana kallon haraban gidan a yatsine, sannan ta ɗauke kanta cikin yanayin ko-in-kula take kallon Hafsan, sosai ta sake haɗe fuskarta babu annurin fara'a bare mutunci a tare da ita, tace mata, "Maman na ciki?"

"Eh tana ciki."

Juya wa tayi ta tasar wa cikin gidan a gadarance tana hura hanci

Ita kuma Hafsah ta bi ta da kallo jiki a sanyaye, domin yanda ta ga Fauziyyan tana yi daga gani ka san babu mutunci a tare da ita, "Allah yasa abun kirki ya kawo ta." Ta furta a fili tana tura ƙofan tare da bin bayan ta da ɗan saurin ta

Lokacin Mama ta idar da sallanta, hannayenta na sama tana addu'a ta hangi Fauziyya ta shigo ko sallama. Hakan ne yasa ta dakatar da addu'ar nata tana shafa wa tare da yalwata fuskarta da murmushi tace, "Fauziyya ce a gidan namu? Sannu da zuwa."

Wani irin kallo Fauziyya ta watsa mata tana ƙara haɗe fuska da cewa, "eh Ni ce."

"To zauna mana, Hafsah kawo mata ruwa ta sha." Ta ƙare zancen tana duban Hafsah wacce ta shigo ciki a yanzu

Sai Fauziyyan ta katse su da furta, "ba wannan ya kawo Ni ba tunda ba yunwa ce dani ba, ke ma kin sani don na fi ƙarfin hakan."

Sai jikin su yayi sanyi sabida jin furucin ta, yayinda suka bi ta da kallo kawai babu wanda yayi magana a cikin su

Ita kuma sabida tsaban iskanci irin nata, don dama tayi alƙawarin wlh sai ta gaya wa Maman magana, sai ta san cewa ta saka ɗanta ya sake ta, shiyasa cike da fitsara da rashin kunya take furta, "dama kin yi rantsuwar sai kin kashe min aure tunda ba kya so na ba kya ƙaunata, tunda kika shigo cikin rayuwar mu zaman auren mu ya taɓarɓare daga ranan kullum rigima muke yi a kanki; sabida kin shiga tsakanin mu kin rantse sai kinga bayan mu, na tako har wurin ki ne in ji dalilin da yasa kika tarwatsa min rayuwa, mai nayi miki da zafi haka Mama? Me nayi miki?" Ta ƙare maganar cikin ɗaga murya idanunta jawur a kan Maman

Wacce ita tayi kasaƙe tana kallon Fauziyyan ta rasa abun da zata ce, har jikinta rawa yake yi tsaban tashin hankali

Bama ita kaɗai ba, ita kanta Hafsah jikinta rawan yake yi sabida jin furucin Fauziyya, ta kasa motsa wa daga inda ta tsaya tana faman kallon Fauziyyan

Yayinda ita kuma ta sake buɗe murya cikin zafi da baƙin cikin halin da take ciki take furta, "to kwanyan ki ta faɗa tunda kin ci galaba a kaina, amma ki sani na rantse da Allah bazan taɓa barin ki ba sai na rama, sai na rama duk abun da kika yi min, ban san wacce irin uwa bace ke da kike son kanki fiye da kowa, bayan kin yi nasara kin tarwatsa min farin cikina kin raba min aure; sannan kin sa ya ɗauke min ƴata ya kaita inda ban san ina ne ba, don haka tun wuri ki fito min da ƴata don na san shawaran ki ne da sanin ki Jamal ya raba Ni da ƴata, na rantse da Allah komai zan iya yi a kan ƴata idan har ba ki faɗa masa ya maido min da ita ba, kuma ki sani Ni walƙi ce dai-dai da ƙugun guzumar banza; ki sa a ranki ba ki ci galaba ba dole zan dawo gidan Jamal, Jamal nawa ne Ni kadai babu wacce ta isa ta raba mu, domin bai isa ya fita cikin rayuwar mu ba wlh."
Ta ƙare maganar a fusace tana zubar da ruwan hawaye

Wani irin kuka Hafsah ta fasa tana durƙushe wa a wurin sabida tsananin tashin hankali, jikinta sai rawa yake yi tana tsoron tayi magana Fauziyya ta ci ubanta domin ba ƙaramin tsoron ta take yi ba, musamman yanda ta ganta a fusacen nan

Ita kanta Mama hawayen take yi sabida jin irin wannan rashin mutuncin da Fauziyya take mata, Fauziyya ta wuce da sanin ta; bata taɓa tunanin zata iya gaya mata irin waɗannan maganganun ba, shiyasa ta kasa magana sai kallonta da take yi har ta gama gaggaya mata maganar da ranta ke so, ta ja tsaki ta bar gidan

Da sauri Hafsah ta iso wurin ta tana cire mata hannunta da ta rufe fuskarta da tayi, sai ta sake fashe wa da kuka tana cewa, "Inna don Allah kar ki yi kuka ba na son ganin hawayen nan naki."

Ɗaya hannunta Mama ta sanya tana share gudajen hawayen da suke zuba mata, yayinda take kallon Hafsan da cewan, "ba komai Hafsatu, ta yi wa kanta ne ai, ina kuka ne kawai sabida irin wannan cin kashin da ta tako har gida tayi min, ashe Ni ban kai darajar da zata iya raga min ba? Yanda nake tsammanin Fauziyya ta wuce nan, ba komai ita da Allah, ke ma ki share hawayenki ki dena wannan kukan tun kafin Jamalu ya zo ya tarar da mu a wannan yanayin, ba na son ma ya san an yi bare wata ɓarakar ta sake tashi."

"Kina nufin baza ki sanar mishi ba Inna? Shikenan ta ci bulus kullum haka zata zo ta riƙa miki har gida? Wannan wacce irin rayuwa ce? Mun baro mata gidan ma baza ta bar mu ba?"

Murmushi Mama tayi tace, "Ni ban ɗauki duniyar da zafi ba Hafsatu, kuma kina ganin yanda Fauziyya bata da kunya bata san abun da ya kamata ba; idan Jamalu ya sani ban san wanne irin mataki zai ɗauka a kanta ba, gwara mu ƙyale ta komai ya wuce, dama ina tunanin nan gaba zata iya dawowa ko don ta ci albarkacin ƴaƴanta, amma yanzu zan nuna mata Ni na haifi Jamalu ba ita ta haifa min shi ba, wlh ko bayan raina baza ta taɓa dawowa ɗakin ta ba, tashi maza ki je ki yi sallah ki ci abinci kinga lokaci yana wuce wa."

Haka nan Hafsah ta miƙe bayan ta share hawayen ta, ta tafi ɗaki yin Sallan amma a ranta ta ɗauki alƙawarin wlh sai ta sanar da Jamal, wannan abun bazai taɓa tafiya a banza ba, idan ita ta kasa ɗaukar mata mataki; to, baza ta taɓa yin shiru ba dole ta sanar da Jamal ya san me ke faruwa, don haka da ƙwarin gwiwarta tayi sallan duk da bata saki ranta ba, abun gaba ɗaya ya cinkushe mata a rai tana mamakin hali irin na Fauziyya wacce bata da mutunci bata da raguwar sa. Abinci ta sawo ta koma falon suka zauna da Mama

Har Maman tana sake jan kunnen ta, "kar ta soma ta sanar da Jamalun."

Bata san cewa ta bayan kunnen Hafsah yake shiga ba, don baza ta jure Fauziyya ta riƙa zuwa tana cin ma Mama mutunci tana gani baza ta iya komai ba, dole ta raina kanta a wannan lokacin,
Shi yasa tunda ta ga Jamal ya zo, yau ko ɓoye wa bata yi ba, tana gaishe shi ta kawo masa abinci da ruwa, yana tambayarta makaranta? Ta amsa masa, "babu wata matsala."
Sai ta tashi ta basu wuri sabida ta ga suna hira tare da Mama, ta koma ɗaki ta kwanta tana tunanin yanda za a yi ta sanar mishi

Shima a wurin Jamal ya ga sauyi sosai wurin Hafsah, ya fi fahimtar damuwar ta a kan Mama, tunda ita har yanzu babu walwala a kan face ɗin ta, shiyasa har a ransa yake jin babu dad'i, yana son ya keɓe da ita ko don ya tambaye ta me ke damun ta, a yanzu yanda yake jin ta a rai ko ita bata sani ba, daure wa kawai yake yi yana ɗan kama girman sa duk da a yanzu yana bata kula wa ba kamar baya ba,
shiyasa da lokacin Islamiyya yayi, bayan ya je yayi Sallah ya dawo, duk a tunanin su ya tafi ma, ashe zai dawo, yace mata, "ta shirya ya sauke ta a islamiyyan."

Babu gardama Hafsah ta amince sabida samun damar yin magana dashi, don tayi rantsuwa suna shiga Mota zata sanar mishi, da sauri ta shirya ta saka Hijabin ta tare da ɗaukar jaka ta fito,
Bayan sun yi wa Mama sallama suka fito a tare yana gaba tana biye dashi

Sai da ya soma jan motan har ya ɗan fita cikin anguwan, sannan ya juya yana kallonta tare da cewa, "daughter, wai me ke damun ki yau duk ba ki da fara'a?"

Ai kuwa babu zato ya ji ta fashe mishi da kuka

      

Hankalin sa ya tashi, bai san sanda ya tsayar da Motan a gefen titi ba; yana juya wa kacokan wurin ta ya riƙo hannayenta.
[16/01, 9:48 am] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
              _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

         *P.W.A✍️*




           *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._






*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 1000
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb. 500
1gb. 550
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼













            *PAGE:37*

_____Jamal ya rikice sabida ganin yanda Hafsah take kuka, hannayenta ya kamo yana cewa, "lafiya daughter? Me ke damun ki? Me ke faruwa faɗa min inji? Please dena kukan nan don Allah ki yi shiru."

Kasa dena kukan tayi duk da irin rarrashin da yake mata, sai ma duƙar da kanta da tayi tana ƙoƙarin ƙwace hannunta

Amma sai ya ƙi sakin ta yana sake furta, "Hafsah, meke damun ki ne haka ki faɗa min mana? Ko wani abun ne aka yi miki? Ba ki da lafiya ne?"
Sosai fa Jamal ya rikice yana tambayarta sabida ganin yanda take ɓarza kuka abun da bai saba gani ba, ji yake yi kamar ya rungume ta don tsananin tashin hankali da damuwar ganin halin da take ciki

Daƙyar ya samu tayi shiru duk da wasu hawayen ne ke fita a cikin idanunta, kuma ta ƙi mishi magana sai faman jan majina take yi tana tunanin ta inda zata fara sanar mishi da maganar,
Hakan ne yasa ya gaji ya miƙa hannu ya janyo ta babu tsammani sai jinta a jikinsa tayi, "wai baza ki faɗa min meke damun ki ba duk kin bi kin tayar min da hankali? Ko so kike nima ki ga hawayen nawa?"
Yayi maganar yana duban fuskarta da tuni ta runtse ido jikinta sai faman rawa yake yi

Bata yi tunanin zai iya janyo ta jikinsa ba shi yasa lokaci ɗaya duk ta rikice kukan ya tsaya cak; tana rufe idanunta sabida tsananin kunya ta kasa ko motsi bare ta tashi

Shiru yayi yana kallonta, sai ya ɗan yi murmushi yana ɗaukar hannunsa ɗaya ya shafa face ɗin ta tare da furta, "oh! Tun farko da abun da nayi miki kenan tunda kin ƙi yin shiru, amma yanzu kina jin ki a jikin Mijinki har kukan ya ƙafe, buɗe idonki to."

Maimakon ta buɗe sai ta manne fuskar nata a ƙirjinsa tana ɓoye wa cikin kunyan sa

Dariya ya ɗan yi yana ƙara sanya hannu ya rungume ta tare da lumshe ido, shiru suka yi su dukkan su yana sauraron hucin ta da ke fita da ƙarfi, kasa motsa wa yayi illa ƙanƙame ta da ya ƙara yi yana jin wani irin yanayi a tare dashi, tamkar su dauwama a haka gaba ɗaya yanayin ya soma rikitar dashi, musamman yanda yake jin hucin ta da ke saukar masa a ƙirji

Ita kanta ta gaza janye jikinta ne sabida sabon yanayin da ya soma riskar ta, tamkar an manne ta ta kasa motsawa duk da son sauka da take yi, sai ta sake lafewa tana ɗaura tafukan hannunta ta sake ɓoye fuskarta

Tsawon lokaci suna a haka, ganin kamar zai iya samun wata matsala sabida kusancin su, shiyasa ya buɗe idanunsa yana sauke wa a kanta, a hankali ya raɗa mata, "ko dai mu ci gaba da zama a haka ne? Ba kya so mu je makarantar?"

Saurin buɗe nata idon tayi, sai dai bata iya ɗago kai ta kalle sa ba sai tayi ƙoƙarin janye jikinta

But ya ƙi sakin ta sai yace, "No, zauna a nan baza ki je ko'ina ba sai kin faɗa min dalilin kukan ki?"

Kamar zata yi kuka tace, "babu komai fa."

"Babu komai kike min kuka? Ko duk Shagwaɓa ne Hafsah?" Yayi maganar cikin ware ido

Kallonsa tayi da sauri, ganin sun haɗa ido sai ta janye nata idanunta cikin jin kunya ta rufe fuskarta da hannunta, tare da girgiza mishi kai tace, "a'a wlh."

"To ki faɗa min abun da ke damun ki in har ba so kike mu ɓata ba, tell me please what's wrong um?"
Ya ƙare maganar yana janye hannunta tare da leƙa fuskarta


Sake duƙar da kanta tayi ƙasa tana jin kamar ta nitse don kunya, Wai ita ce yau ɗare-ɗare a jikin Dadyn su tana shaƙar ƙamshin sa, ga shi ya riƙe ta babu damar tashi, duk jikinta ya saki wani irin baƙon yanayi take ji wanda bata taɓa jin irin sa ba, ta kasa magana sabida duk a daburce take bata san me zata ce mishi ba

Sai shi ne ya gaji yace, "wai baza ki yi magana ba? Kin fi son mu kwana a nan ne? Da alamu wannan kunyar naki baza ki dena min ita ba, na kula sai na dena tausaya miki na soma amsar haƙƙi na sannan za ki gane matsayina a wurin ki."

A zabure ta ɗago ta kalle sa, ita kanta bata san sanda ta furta, "wanne haƙƙi kuma?"

Ya so yayi dariyan yanda ya ga ta razana, amma sai ya kirne ya haɗe fuska yace, "wanne haƙƙi kuwa? Ai na san ke ba yarinya bace kin san me nake nufi tunda ana muku a school, haƙƙin Miji a kan Matarsa mana."

Ƙwalƙwal tayi da ido tace, "wlh zan faɗa maka."

"To faɗa min ina jinki?" Yayi maganar yana tsare ta da ido ga shi ya matso da face ɗin sa sosai kusa da nata yana sakar mata hucin sa

Gaba ɗaya ta rasa kuzari da natsuwarta, amma tsoron abun da ya furta yasa ta daure ta soma zayyane mishi abun da ya faru jikinta na ta faman rawa, lokaci guda wasu sabbin hawayen suka soma kunno kai suna sauka a kan kuncin ta

Sauraron ta yake yi idanunsa kafe a kanta har ta gama zayyane mishi, yanda ran Jamal ya ɓaci ya kasa furta kowanne word illa baza idanu da yayi a kanta idanunsa har sun soma canza kala

Shiru tayi tana mirza hannunta tana jiran ta ji yayi magana, amma jin shiru tsawon lokaci sai ta ɗago tana kallonsa, yanda ta ga ya kafe ta da ido sai da gabanta ya faɗi, sai tayi saurin ɗauke kanta tana sake duƙarwa

Dakakkiyar muryansa ta ji yana furta, "ta taɓa zuwa gidan ne ko yau ta soma zuwa?"

"Yau ta soma zuwa." Ta ba shi amsa da sauri jin yanayin muryansa

Hannun sa ya janye a jikinta tare da bata umarnin, "ta koma inda take."


Jiki a saɓule ta koma mazaunin ta, sai dai bata sake kallonsa ba tana tunanin Allah yasa ya ɗauki mataki, amma har ranta ta ji haushin shirun da yayi mata tamkar bai damu ba, shiyasa har ƙara satan kallonsa tayi tana son gano yanayin sa but bata fahimci komai ba, duk da ta ga fuskarsa babu walwala amma a ganin ta ba haka ya kamata ya nuna ba, dole ya nuna ɓacin ransa fiye da haka, amma ko dai mene ne ita dai ta faɗa mishi hankalin ta ya kwanta, kuma tana da yaƙinin zai ɗauki mataki tunda Uwa; Uwa ce, babu ɗan Halak ɗin da zai bari a wulaƙanta mishi Uwa,
Tana jin ya tsayar da Motan; ta ɗago tana duban haraban makarantar, sai ta kalle sa suka haɗa ido dashi, da sauri ta janye idonta don ba ƙaramin kunyan sa take ji ba, take a nan abun da ya faru ya soma dawo mata har ta kasa furta komai bare ta fita a Motan


"Ki shiga makaranta, na san yanzu haka kun yi latti, na gode da kika sanar min da abun da Fauziyya ta aikata; kuma zan ɗauki mataki a kai." Sai ya saka hannu ya riƙo nata but bai sake furta komai ba sai kallonta yake yi, kamar yana nazarin ta

Ita kuma a tunanin ta wani abun zai yi mata duk ta takure ta kasa kallonsa

Ɗan matsa mata hannun yayi before ya janye nasa yana ƙoƙarin tayar da Motan yace, "sauka ki shiga."

Bata tsaya ce mishi komai ba tayi saurin buɗe Motan ta fice, ko juya wa bata yi ba har ta nufi bakin gate ɗin kamar zata tashi sama, a jikinta ta ji kamar yana kallonta sabida yanda take harɗe wa, kuma har zuciyarta tana son juya wa ta sake kallon koda Motan nasa ne, duk da tana jin ƙaran Motan alamun ba tafiya yake yi ba, sai da ta buɗe ƙofan gate ɗin sannan ta juya a hanzarce tana kallon sa

Karaf suka haɗa ido dashi; shima yana kallonta, murmushi yayi mata

Tayi saurin

Please Login or Register in order to submit comment