Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba, ba na son ki sha wahala a rayuwarki, ba na son ki faɗa hannun Mijin da zai gaza tallafa miki a rayuwa, amma na san Jamalu zai taimaka miki ko babu idon mu, mahaifi ne a wurin ki mai share miki kukan ki, na san baza ki taɓa dana-sani ba muddin kika samu Miji kamar Jamalu, ke kanki shaida ne da irin halayen sa na ƙwarai, kiyi hakuri kin ji da irin hukuncin da na yanke miki ba tare da sanin ki ko amincewar ki ba."

A wannan lokacin tuni hawaye sun soma sintiri a kan fuskar Hafsah, sai ta kifa kanta a saman gwiwowin ta; ta soma shashsheƙan kuka a hankali

Wanda hakan ya tayar da hankalin Mama, ta taso ta dawo kusa da ita tana tambayarta dalilin yin kukan? Har tana faɗin, "idan auren ne ba ta so za a iya kwance wa in har zata fi samun farin ciki da walwala, bata yi hakan don ta ɓata mata ba, tayi tunanin duk abun da ta yanke a cikin rayuwarta zata amshe shi hannu bibbiyu, kuma hakan ya bata ƙwarin gwiwa ne ta yanda iyayenta suka nuna murna da son abun, kuma nayi tunanin auren ki da ɗana zai kawo sauyi a rayuwarsa, zai samu farin cikin da ya gaza samu, Hafsatu ke yarinya ce ta gari, wadda kowacce Uwa zata so ta haɗa zuriya da irin ki, idan ban aura wa ɗana ke ba? To wa kike tunanin zan nema mishi?"

Ɗago kai tayi tana kallon Maman, yayinda tausayin kanta dana Maman ne ya ɗarsu a zuciyarta, tana tausayin kanta ne ba don komai ba sai irin mummunar hukuncin da zata fuskanta; muddin Fauziyya ta san cewa ta aurar mata Miji, ya makomar ta zai kasance a gidan da tana ganin bata da wani gurbi a cikin ta? Tabbas bak'ar azaba da uƙuba su zasu yi sanadin barin ta duniya. Tana matuƙar tausaya wa Mama saboda ta san cewa ta damu da irin halayen da Fauziyya da yaranta suke nuna mata; tsangwama da kyara da rashin soyayya, a matsayin ta na Uwar Miji, ta san dole Mama tana cikin damuwa tsanani da halin da suke ciki, musamman kowacce Uwa in har ta gari ce, baza ta taɓa farin ciki ba muddin aka ce mai halayya irin na Fauziyya tana aurar ɗanta, a koyaushe zata kasance cikin fargaba ne da tunanin wata rana dole ɗan nan nata zai bar ta, zai rabu da ita na har abada, in ba a yi dace ba irin masu halayyar Fauziyya, suna raba soyayyar ɗa da Uwa ne, sai dai a lahira in an haɗu, babu kuma wata Uwar da zata zauna kullum tana fuskantar wulaƙanci da tozarci daga wurin Matar ɗanta; sannan kuma ta kasance cikin farin ciki, dole abun zai riƙa damun ta, musamman irin Mama wacce ba ta iya bayyana halin da take ciki, tana barin abun a cikin ranta yana mata ciwo tana shanye duk wani ɓacin rai. Baza ta so ta watsa ma Mama ƙasa a ido ba, a kan idanunta ake yin komai kuma tana gani, ita shaida ce a kan irin halin da Mama take ciki a gidan ɗanta, idan har wannan zai faranta ran Mama kuma zai kawo sauyi a cikin rayuwarsu, bata da wata matsala zata amince, duk da bata ga hanyar da zai sa Mama tayi wanann gangancin na haɗa su aure ba, ita a ganin ta tamkar ta ƙara jagula tsakanin ta da Fauziyya ne, muddin ta san da auren nan kamar an kunna yaƙin basasa ne na biyu, meyasa Mama bata samo wata daban ta haɗa auren su da Jamal ba sai ita? Meyasa sai ita? Wacce iriyar gudummawa zata bayar?
Dole ta buɗe baki domin ta kwantar wa da Maman hankali, tunda aikin gama ya gama, abun da aka rigada aka yi mene ne amfanin kwancewan? sai ta furta mata, "ita ta amince saboda ko me ta nema a wurin ta zata iya bata bare wannan da take da damar yanke kowanne hukunci a kanta, Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi a rayuwar su gaba ɗaya."

Ba ƙaramin farin ciki Mama ta nuna mata ba, ta ji dadi matuƙa da yanda Hafsah ta amince da auren nan take; babu ɓacin rai bare tunanin damuwa a kan fuskarta, sai ma murmushin ƙarfin hali da ta ara ta yafa wa fuskarta da nufin ta kwantar wa Mama da hankalin ta, ta yarda cewan har zuciya ta amince da auren. Sosai Mama ta sanya mata albarka har da ƙwallanta, tace, "Insha Allahu baza ta taɓa taɓe wa ba, sai Allah ya ɗaga ta a cikin rayuwar nan, albarkacin biyayyan da tayi musu Allah zai saka mata, zai sanya mata albarka a rayuwarta da auren su baki ɗaya."

Ita kanta Hafsah ta ji daɗin addu'o'in da Mama tayi mata. Amma da ta koma ɗaki sai ta koma tunanin yanda rayuwarta zata canza daga yanzu, wai ita ce ta auri Jamal wanda take ganin sa a matsayin Uba a gare ta, Mahaifin su Intisar? ta san cewa ko ya'yansa idan suka ji zancen baza su bar ta da ranta ba bare a ce Fauziyya, haƙiƙa tana matuƙar tsoron abun da zai biyo baya, ga fargaban sake tozali da Jamal, to da wanne ido zata kalle shi? Ba ta tunanin zata sake haɗa ido dashi.



Har dare Hafsah ta kasa sakin jikinta da maganar nan da Mama ta faɗa mata, duk yanda ta so ta cire damuwar abun amma abun ya faskara, musamman in ta tuna wai ita ce take da aure, auren ma ba na kowa ba sai na Dady, har yanzu tana mamakin cewa ita Matar aure ce, yanzu da igiyoyin wani a kanta, abun ya ɗan saka ta cikin wani mawuyacin hali wanda yasa ko runtsa wa a daren ta kasa yi, tunda suka kwanta da Mama a gado ɗaya, sai ta juya bayanta tayi lamo idanunta a buɗe tana kallon duhun da ya bayyana a cikin ɗakin, ta kasa ko motsin kirki sai tunane-tunanen da ya bi ya cinkushe mata a ƙwaƙwalwa. Ta jima a wannan yanayin da sai da ta tabbatar Mama tayi nisa a barcin ta, sannan ta soma juye-juye tana canza kwanciyar ta, duk don ta kawar da tunanin da ke ranta ta samu ta runtsa, amma hakan ya faskara, sabida baƙon al'amarin da ya zo mata mai girma a cikin rayuwa, har fargaba tare da bugawar zuciya take ji duk in ta tuna haɗuwar su da Jamal

Shi yasa washe gari har addu'a take yi Allah yasa kar ya zo gidan. Kamar kuwa Allah ya amshi addu'ar ta, har yamma bai zo gidan ba, shiyasa tace ma Mama, "zata je Islamiyya yau."

Mama tace, "ta bari sai an kwana biyu sai ta koma, tunda ta jima bata je ba, ta bari ta huta na kwana biyu; inyaso Jamal sai ya mayar da ita ya faɗa musu wani dalilin da zai sa su yarda da rashin zuwan nata."

Amma firr Hafsah ta ƙi yarda, saboda zaman ta a gidan ne ba ta so, sabida kar Jamal ya zo su haɗu, shiyasa ta dage tace mata, "ita zata je, idan ta je in zasu buge ta sai ta faɗa musu rashin lafiya tayi shiyasa ta dena zuwa."

Yanda ta dage da zuwan nata, dole Mama ta hakura ta bar ta, sai ta miƙa mata kuɗin machine kasancewar yanzu sun yi nisa sosai da Islamiyyan, dole sai ta koma can anguwan da suka baro, since a can Islamiyyan take. Haka Hafsah nan da nan ta shirya ta fice a gidan; tana Allah -Allah ta tafi kar su ci karo da Jamal

Ilai kuwa tana fita gidan Jamal ɗin ya zo, har ya tambayi ina Hafsan? sabida ganin tunda ya zo bai ga gibtawar ta ba

A nan Mama take ba shi labarin tafiyar nata Islamiyya

Murmushi kawai yayi yace, "Allah Sarki."
Daga nan hira suka ɗan taɓa, ya faɗa wa Maman, "zai yi tafiya na kwana biyu."
Sai ya bata kuɗi masu ɗan kauri koda matsalolin Hafsah sun taso, da kuma na transport both islamiyya and Boko, sai a riƙa zara ana bata a ciki tana yin kuɗin mota

Har ya tafi Hafsah bata dawo ba, sai bayan awa daya sannan ta shigo gidan. Koda Mama ta sanar mata da zuwan Jamal ɗin, tare da tafiyan da zai yi, farin ciki tayi a ranta, ko banza zata samu kwanciyar hankali da natsuwar zuciyan da ta rasa daga jiya zuwa yau, sai kuma idan ya dawo ta shirya da fuskantar haɗuwar su, wadda take matuƙar fargaba da tsoron hada fuska da shi, don har ga Allah ba ta jin cewa zata sake haɗa ido da shi, har dana-sanin sanar mata da Mama tayi take yi, da ta bar maganar kawai daga su sai su ba tare da an sanar mata ba, da ta fi samun kwanciyar hankali, tunda ga shi yanzu har ta canza daga irin kallon da zata riƙa mishi, ada tana mishi kallon Dady, yanzu kuma fa?.
[03/01, 4:53 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
               _(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

         *P.W.A✍️*





          *TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 1000
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days

9mobile
500mb. 500
1gb. 550
2gb. 1000
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 days

Glo
1.35gb. 550
2.9gb. 1000
4.1gb. 1400
7.7gb. 2300
10.0gb. 2650
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼












                *PAGE:27*

_____Kamar yanda Muhseen yayi ƙudirin canza wurin aiki, ai kuwa bai samu matsala ba tunda Ogan shi yana sonsa sosai, shiyasa da ya nuna yana son a canza mishi wurin aiki, babu ɓata lokaci ya ce, "ya zaɓa kowanne gari yake so, cikin garuruwan da suke da reshe, shi kuma zai san yanda zai yi ya sama mishi."

Muhseen ya zaɓi Katsina tunda ya fi son can, musamman ma kasancewar garin ya fi nisa a kan Kano. A cikin satin aka ba shi damar fara aiki,
Shiyasa ya soma sanar da Umma domin ya ji mai zata ce

Har ranta bata ji daɗin nisanta kansa da su da zai yi ba, duk da yace mata, "a wurin aikin ne aka canza mishi, ba shi da yanda zai yi." Shi yasa bata ce komai ba duk da a ranta hankalinta bai kwanta ba, domin ji take yi dama ya ajiye aikin ya nemi wani kawai, amma ta san hakan zai yi wuya, da aikin nan nasa suka dogara, sannan in ya ajiye ba lallai bane ya samu wani mai gwaɓi-gwaɓi kamar wanda yake yi ba, shi yake ɗaukar ɗawainiyar su, har ƙanninsa da yanzu ya saka su makaranta suna ci gaba, A'isha yanzu haka tana polytechnic ne na nan Kaduna, ajin farko, sai kuma Amina da ke SS 3 bata ƙarisa ba, shi yake musu komai na buƙatu tunda Allah ya hore babban albashi yake amsa, ga nauyin iyalansa Munira da ƴarsa Hanan, to basu da yanda zasu yi in bai tafi inda aka tura sa ba, addu'a kawai tayi masa da fatan samun nasara, sannan ta tambaye shi, "yanzu in ya tafi sai yaushe zai riƙa dawowa?"

Yace, "Umma Ni dai na yanke shawara in na tafi zan riƙa yin wata ɗaya before na riƙa leƙo ku, tunda gari ba kusa ba, nan da Katsina akwai tafiya, kuma kinga ba wai na saba da tafiye-tafiye bane ba na son ina yawan zirga-zirga a kan hanya."

"Eh hakan babu dad'i ai, amma duk da haka Ni dai idan zaka bi ta shawarata, sannan idan hakan bazai janyo maka wata matsalar ba, wata ɗaya dai yayi yawa, ina laifin ma sati biyu ka riƙa leƙo mu? Ko baka zo don mu ba zaka zo don Munira; tunda wannan tafiyar ba saba wa tayi da shi ba, nan gaba idan kana son ka kai wata ɗayan sai ka riƙa kaiwa tunda an saba, amma yanzu kwatsam ka tafi har tsawon wata ɗaya abun zai yi mana yawa, zaka bar mu da kewar ka."

Murmushi yayi yace, "to Shikenan Umma, zan yi sati biyun; mu ga yanda hali zai yi."

"To Allah ya yi albarka, ya bada sa'ar abun da aka je nema."

"Amin ya Allah."

"Ina dai ce ka sanar da ita Muniran ko?" Tayi maganar tana kallonsa

"A'a Umma, yanzu idan na shiga zan sanar mata, na soma faɗa miki ne sabida in ji ta bakin ki."

"To Shikenan sai ka sanar mata itama, Allah ya kaimu ranan tafiyar."

"Amin."
Mike wa yayi; yayi mata sallama ya fita ya wuce nasu sashin

Munira na zaune a saman couch tana kallo, while Hanan tana tsakar falon a saman cerfet, sai wasa take yi da kayan wasanta da ta barbaza

Shigowa yayi da sallama a bakin sa. Hakan ne yasa Hanan tunda ta ji muryansa ta miƙe da sauri ta nufe sa tana faman kiran, "Baba.. Baba."
Ɗaukar ta yayi yana shilla ta sama tare da ɗaura ta a bayansa, idanunsa a kan Munira wacce ko ɗago kai ta kalle sa ta ƙi tayi, sallaman nasa ma sai dai ta amsa a zuciya tunda ta san muhimmancin amsa sallaman. Girgiza kansa yayi yana tako wa a hankali ya samu wuri ya zauna, sannan ya sauko da Hanan ya daura ta a saman ƙafafunsa, sai da ya ɗan yi wa yarinyar wasa yana sauraron gwarancin Hausarta da ta cika sa dashi, sannan ne ya sake kallon Muniran yana cewa, "Uwar rigima, sai ka ce ba ki ganni ba, na shigo babu sannu da zuwa bare in samu tarba mai kyau ko? Ke yanzu wannan hanyar da kika dauko ma kanki hakan kika ga ya dace ko?"

Banza tayi dashi, sai ma ɗaura ƙafa kan ɗaya da tayi tana sake tamke fuskarta

Ƙwafa yayi yana jan numfashi, wlh ba kaɗan ba ya soma ƙuluwa da halin Munira, amma daure wa kawai yayi ya share ta tunda ba ya son wata tsiya ta sake haɗa su har yayi tafiyar nan, shiyasa ya tashi da kansa ya dauko ruwa a fridge ya sha, sannan ya lallaɓa Hanan ta koma wurin wasan ta, shi kuma ya wuce ɗaki yayi wanka ya saka riga da wando na shan iska, har ya dawo tana zaune a wurin ta ƙi tashi, dama ya san bazai samu abinci a gidan ba since tun lokacin da suka yi tsiyan nan ya gindaya mata fita maƙota; ta dena mishi abinci. Yanzu ma don ya san dole tana da haƙƙin ya faɗa mata tafiyar nan nasa ne, shiyasa ba shi da yanda zai yi illa zama da yayi yana kallonta tare da furta, "wlh Munira kina matuƙar bani mamaki da irin waɗannan halayyar naki, idan an ce min za ki aikata duk Wadannan abubuwan a lokacin baya kafin in aure ki; bazan taɓa yarda ba, amma kuma ashe kallon da nake miki ba haka bane, sai da na aure ki na san cewa na tafka babban kuskuren da babu yanda za a yi in gyara, har cikin zuciyata nake faɗa miki wannan maganar sabida bazan iya barin ta tana ƙona mini zuciya tare da saka Ni cikin ƙunci ba, na faɗa miki ne ki san cewa Mijinki ba ya alfahari da kasancewar ki Mata da irin wannan halayyar naki mara sa kyau, kuma idan za ki gyara ki gyara tun kafin lokaci ya ƙure miki, domin wlh ko bayan raina za ki ce na faɗa miki ba hanya ce mai ɓille wa ba wannan saran da kika ɗauka, don haka Ni yanzu na samu solution ɗin matsalar mu, tunda na ga ba ƙaunar gani na kike yi a tare da ke ba, to na samu aiki a Katsina kuma zan koma can da aiki na, zan riƙa yin two weeks ina dawowa, kafin mu ga abun da hali zai yi."

Sosai maganganun sa suka soki zuciyar Munira, yayinda ya sanya mata wani irin ɓacin ran da ya turniƙe ta, shiyasa cikin ƙunan rai ta dube sa tace, "ai Ni baka burge Ni ba idan har baka dauwama a can gaba ɗaya ba, tunda ba na buƙatar ganin ka a nan, Ni ban ce na tafka babban kuskuren auren ka ba sai kai ne zaka faɗa min haka?"
Sai ta miƙe cikin tsantsan fushi idanunta har sun kaɗa tace, "bari ka ji Muhseen wlh tallahi nayi nadamar auren ka, nayi nadamar auren Mijin da bai da wani amfani a cikin rayuwata irin ka, ina mukatar dana-sanin auren ka, kuma Ni Munira na fi ƙarfin ka zauna kana gaya min maganganu son ranka sannan in zuba ido ina kallon ka, meyasa baka sake Ni ba idan ka san cewa ba kalar Macen da kake so ka aura ba?" Sai ta ja dogon tsaki tana wuce wa hanyar ɗakin ta, tare da furta, "ai Ni ta fi nono fari dama baka san takura ce kai a gare Ni ba, kuma wlh bazan taɓa sassauta maka ba tunda ka hana Ni jin dad'i a cikin rayuwata, mu zuba da Ni da kai."

Kansa Muhseen ya kama ya riƙe gam, da ba don ya san abun da zai biyo baya muddin ya saki Munira, wlh babu abun da zai hana bai yi mata saki uku cif a yau ba, sosai zuciyarsa ke tafarfasa gami da jin wani ɓacin rai tun daga can ƙasan zuciyarsa, musamman idan ya tuna kalaman ta na ƙarshe, wato shi ya zame mata takura ne a cikin rayuwarta, iya baƙin ciki ya ƙunsa a lokacin, sai dai kasancewar nan da nan ya kama faɗin, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un." Take ya dena jin ɓacin ran da ƙuncin da suka mamaye mishi zuciya, a hankali ya soma jin sanyi a ransa. tsawon lokaci yana a wurin a zaune dafe da kansa, daga ƙarshe sai ya miƙe ya shiga Kitchen domin ya sama wa kansa abun da zai ci, since yanzu da kansa yake shiga Kitchen kasancewar ba kasafai yake son abun siyarwa a waje ba, ko ciman abubuwa ba son su yake yi ba, ya gummaci ya girka da kansa ko ya je wurin Umma ya ci, kuma gaskiya yanzu ba sosai yake zuwa ci ba gudun tambayoyin da zai samu daga wurin Umman, sai dai in ya je sashin an yi mishi tayi; to, wannan fa ba ya wuce tayi dole zai ci, in kuma bai samu ba sai ya dawo nan ya girka,
Haka ya ɗaura taliya yana tunanin halin Munira da abubuwan da take mishi a gidan, bai san ya zai yi ba, kullum matsalar taƙi ci taƙi cinye wa, lokaci ɗaya idanunsa har sun kaɗa sun yi jazur tamkar ya kurma ihu haka yake ji a ransa, ya rasa yanda zai yi da yarinyar nan, abun nata ya wuce misali,
Shiyasa yake jin gwara ma ya tafi a goben zai fi, domin bai ga amfanin zaman shi ya kai kwana uku yana ƙunsan bakin ciki ba, cuz zaman su ba sauya wa zai yi ba, dole zai koma ya sake sanar da Umma zai wuce gobe ana buƙatar sa ne a goben,
Da wannan shawaran ya kammala girkin nashi,
Lokacin an kira sallan Asar, don haka ya fice don zuwa ya gabatar kafin ya dawo ya ci abincin. Har zai rufe ƙofan kitchen ɗin, sai ya ga Hanan tayi barci a tsakar falon, shiyasa bai rufe ba ya wuce yayi alwalan a ɗakin sa ya tafi masjid.







🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆🔆

               Ranan da Jamal ya dawo daga tafiya, bayan ya koma gida har ya ci abinci ya ɗan runtsa barci, sannan ya tashi yayi wanka ya saka blue shadda wacce ta ji aiki ta fito da kyawun sa ainun, yanda shaddar tayi masa kyau ta fito masa da zallan ƙuruciyar sa; baza ka taɓa cewa yana da ƴan Matan yara ba, bare a kai ga har ya aurar ma. Gaskiya yayi kyau duk da ba wani kwalliya yayi ba, amma ya saka hulan da ta dace da kayan ya mirza ta sosai ta zauna a kan nasa, sannan ya saka sandal shoes kalan ruwan goro; wanda ya kasance da kalan a cikin aikin rigan, sai ya shafa turare ko'ina a jikinsa before ya fito riƙe da key ɗin Motan sa, ganin babu kowa a falo kai tsaye sai ya wuce ɗakin Fauziyya ya shiga da sallama a bakin sa

Tana zaune itama tayi wankan, har ta saka kamfala ɗinkin doguwar riga mai ruwan zuma da fatsi-ftsin Fari a ciki, tana mirza jan jan-baki ta ɗago kai tana kallonsa, sai da ta gama shafa wa before ta amsa mishi ba tare da ta ɗauke kai a kansa ba, don babu ƙarya yayi mata kyau; fuskar nan nasa sai walƙiya take yi, musamman sajen sa da ya sha gyara baƙi siɗik da ɗan sirƙi fari-fari a guntun gemunsa, alamun manyanta ya soma kama sa

Shi kansa yanda ya ga tana kallonsa sai da ya tsargu yace, "wai lafiya Malama?"

"Ganin ikon Allah nake yi, ina zaka je da yammacin nan ka ci kwalliya haka? Kai da ka dawo daga tafiya kana buƙatar hutu?"

"Zan je wurin Mama ne, don na sanar mata dawowa na kuma na ce mata zan shigo a yau. Kinga tunda ke ma da shirin ki; sai mu wuce tare ki ga gida."

Nan da nan ta haɗe ranta tana ɓata fuska, tare da furta, "haba Jamal, wai ba ka da magana ne sai na Mama koyaushe? Yanzu daga dawowar ka bamu gama gaisawa mun saka ka a ido ba, tunda ka dawo kake barci; amma kuma daga tashi zaka ci uwar kwalliyar nan ka ce zaka tafi wani wurin, wannan ka yi mana adalci kenan? Yaran nan ma ko ganin ka basu yi ba, baka bari sun dawo ba amma kana haba-haba zaka wuce tunda mun zamar maka guba ba ka bukatar mu."

"Wai Fauziyya ban san meyasa kike da ƙorafi kodayaushe a kan Mahaifiyata bace, ya ci a ce a yanzu kin saba kin dena duk wadannan ƙorafe-ƙorafen naki tunda baza ki iya raba mu ba, sannan duk daɗewan nan da nayi hakan bai ishe ki ba? Ko kuwa dole ne sai na zauna Yaran sun dawo sannan nake da damar barin gidan? Wani ya ce su je gidan Intisar ɗin? Idan baza ki je ba ban ce ki zauna kina min gutsiri tsoma ba kina jina?" Yayi maganar shima da ɗan zafin sa yana juya wa; ba tare da ya jira cewar ta ba ya fice a ɗakin

Hakan ya ƙara fusata Fauziyya ta furta, "lallai ma wannan Mutumin, na kula dole sai na ƙara tashi tsaye a kansa, in dai a kan mahaifiyar sa ce bakin sa bazai taɓa rufuwa ba kenan? Dole sai ya tanka." Sai ta jinjina kanta ta ƙara da faɗin, "shikenan, da Ni kake zancen, ka tafi, daɗin abun ma kai kaɗai ta haifa balle a takura min da dole sai na je wurin ta, baza ta taɓa gani na ba kuwa."
Ta ƙare maganar ranta a ɓace tana miƙe wa a gaban Mirror ɗin, tare da wuce wa wurin gadonta ta ɗauki wayanta ta soma ƙoƙarin neman layin da zata kira.
***

         While Jamal tuni ya wuce ya shiga dakin sa ya dauki ledan tsaraban da ya yi musu, sannan ya shiga motansa ya ja ya bar gidan, yana zuwa bakin masallacin anguwan su ya tsaya yayi Sallan Asar sannan ya wuce anguwan su Mama, bayan ya faka motan a waje ya shiga daga ciki tunda ƙofan a sakaye yake

Mama tana zaune itama idar da sallanta kenan ta jiyo sallaman sa, nan da nan ta yalwata fuskarta da murmushi tana amsa mishi tare da bin sa da kallo, sai da ta ga ya gama shigowa sannan ta soma mishi maraba tana cewa, "yanzu nake zancen ka a raina."

Murmushi yayi ya zauna tare da ajiye ledan a gabanta; sannan ya gaishe ta

Ta amsa da,

Please Login or Register in order to submit comment