Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai take yi yayinda zuciyarta ke amsar saƙon nashi tana sake bugawa da ƙarfi kamar zata faso ta fito tsaban yanda maganar ta duge ta. Sai dai a zahiri baza ka taɓa fahimtar halin da take ciki na firgici gami da ruɗewa ba. Ƙirƙirar murmushi tayi sa'ilin da ya gama bayanin nasa ya koma bata haƙuri yana faɗin, "wa ya mutu wa ya tashi". Irin dai ƙaryan su na Maza da daɗin bakin su a lokacin da suke son abu. Sai tace, "Haba Mijina mene ne kuma na bani haƙuri bayan Allah ne ya baka damar yi? Shi ne fa yace muku idan kuna da dama kuma kun tabbatar da zaku yi adalci to ku aure mu daga biyu zuwa huɗu, idan kuma baku da hali ku zauna da ɗaya, to yanzu Allah ya buɗa maka kana buƙatar ƙari Ni ɗaya nayi maka kaɗan, wlh babu komi idan har don Ni ce kar ka taɓa damuwa na amince da auren ka kuma bazan taɓa baka kunya ba, ina goyon Bayan duk abin da kake so domin na aure ka ne don soyayya ba wai don ƙiyayya ba, farin cikin ka shi ne nawa, abinda na tabbatar zai saka ka farin ciki da samun kwanciyar hankali shi zan yi, bazan taɓa baka kunya ba Ya Mijina, Allah ya bamu zaman lafiya baki ɗaya."

Haƙiƙa zancen nata ya sake girgiza shi tare da sakar mishi wani irin sanyin jiki, yana ganin tamkar be mata adalci ba but ya zai yi? Yana ƙaunar Afnan bazai iya rabuwa da ita ba yanzu, idan ma ya rabu da ita ya ci amanar ta ne, sannan kuma ga shi yana shirin ƙuntatawa Matar shi ta gida, idan da yana da halin fasawa wlh da ya fasa saboda kalaman ta sun saka tausayi da ƙaunarta sun sake ratsa shi, musamman da ya ji tace, "yana buƙatar ƙari ita kaɗai bata ishe shi ba." Shiyasa ya riƙe mata hannu yace, "ba zancen wai ba ki ishe Ni bane Hauwa; hasali ma abun da yasa zan yi auren daban ne, ina son haihuwa a halin yanzu kinga idan Allah ya kawo me albarka sai kiga mun soma samu a wajen Amaryan ko? Tunda mu ga shi shiru Allah be bamu ba kuma babu matsalar komai."

"Haka ne Mijina. Allah yasa a dace." Tafaɗa a fili fuskarta yalwace da fara'a yayinda zuciyarta cike take da hatsaniya baƙin ciki da masifan kishin Mijinta, amma sosai tayi ƙoƙarin haɗiye kukan ta dake shirin kufce mata tana yaƙen dole, ga shi tun ba'a je ko ina ba yana mata zancen haihuwa dalilin da zai ƙara auren kenan, kenan ya soma gajiya da rashin haihuwar su?

Ce mata yayi, "su kwanta gobe idan Allah ya kai su rai da lafiya sai su ci gaba da maganar, zai faɗa mata ko Wace ce yarinyar da yake so zata san komai a game da ita, itama tana da hali me kyau baza ta taɓa cutar da ita ba."

Tunda taga ya juya baya sa'ilin da ya kwanta itama sai ta juya bayan, nan da nan kukan da take danne wa ya taho mata, bakinta ta toshe ta hana bayyanuwar fitowar sa, sai dai tuni hawaye sun soma tsere a kuncin ta suna sauka a saman katifan. Kukan zuciya take yi domin ta kasa barci a wannan ranan, daga ƙarshe da ta tabbatar yayi nisa a barcin sa sai ta tashi ta sauka a kan gadon ta koma can bakin ƙofa ta dinga kuka tana shashsheƙa tana rufe baki don kar ya ji, tayi kuka sosai domin a yanda take ji baza ta iya jurewa ba, Allah ya gani tana ƙaunar Mijinta ba ta son abun da zai raba su, tana tsananin kishin shi sai dai baza ta hana shi abin da yake so ba, baza ta taɓa hana shi auren da yayi ninya ba tunda shi yake so, to a kan me zata hana shi? Bayan idan ta tayar da husumar ma ƙarshe zai yi abun sa kuma ya zauna da Amaryar tashi bata da yadda zata yi, idan kuma ta matsa ita ta rasa auren ta wancan tazo ta rayu da shi bayan duk Baƙar wahalar da suka sha a tare ƙarshe wata ta kwace mata shi, haka nan zata yi haƙuri domin haka Allah yaso dole sai an mata Kishiya, ta yarda da ƙaddara me kyau ko maras kyau, zata jure duk wani kishin ta a zuciya ta taya shi farin ciki da abun da ya kawo yana so.... Sai gab da asuba sannan ta buɗe ƙofan ta fita taje tayi alwala ta dawo, sallah tayi nafila ta roƙi Allah ya basu zaman lafiya, Allah ya kaɗe musu duk wata fitina ya bata damar danne kishin ta, Allah ya cire mata duk wani ƙunci da ke zuciyar ta.... Ta jima tana zaune tana kai kukan ta ga Allah sannan ta tashi ta soma yin sallan asuban jin an soma kira

Shima a lokacin ya tashi ya tarar da ita tana sallan, fita kawai yayi yaje yayi nashi ya wuce Masallaci. Daga waje suka haɗu da Bilal ya fito da su Sulaiman suka tafi tare.



Washe gari da zancen ya je kunnen Sauda ai ruwan bala'i ta dinga zubawa tamkar ita aka ce za'a yiwa kishiyar, har da cewa, "dama na faɗa miki Mijin ki na gani da wata kwanakin baya; amma kika ƙaryata Ni tunda ke daɗi Miji ko? Ba ki san su ba'a musu gwanin ta ba muna-fukai ne, kin ɗauki yardan ki kin ba shi gaba ɗaya, ji be yanda don Allah kike faranta mishi da daɗi babu daɗi amma ya rasa da me zai saka miki sai da kishiya? Wlh Mijin ki babban muna-fuki ne Hauwa kar ki ga laifi na sai na faɗa abin da ke cikin raina."

Hauwa wacce ta saki baki tana kallon Saudan, duk da ta san halin ta ciki da bai, but mamaki ne ya cika ta saboda yanda ta haƙiƙance sai surfa bala'i take yi kamar zata ari baki, tamkar ita ce ma aka ce za'a yiwa kishiyar? Ta san Sauda sarai kuma ta san masifan ta a gabanta baza ta ƙi faɗar duk abin da ke ranta ba

Saudan sake kaɗa kai tayi cike da kumfar baki irin wacce masifa yaci ya cinye tace, "wato tunda yayi kuɗi a tunanin sa wai shi yayi arziƙi shi ne bari ya saka miki da wannan butulcin? Ai wlh idan da Ni ce na rantse da Allah zaman lafiya ya ƙare a wajen mu, yo wani arziƙin yayi da har yake tunanin cin miki mutunci da yin kishiya? Arziƙin banza arzikin hofi. Ke Ni wlh idan da za ki bi ta shawarata na rantse da Allah ki tafi gidan ku, ki ɗaga masa hankali dole sai ya fasa."

Ita kanta Ruƙayya da ke zaune tana sauraron Saudan mamakin halin nata kawai take yi, a ɗan zaman nan da tayi dasu ta soma fahimtar halin Sauda, fitinanniya ce na bugawa a jarida, ba ta shayin ko me zai faru idan tana masifa, irin Matan nan ne waɗanda basu barin ko ta kwana, abun da ke zuciyar su suke sanar maka ko bazai maka daɗi ba, kwata-kwata suna da wuyan sha'ani wlh, duk arzikin ki da ita idan har wani abun ya haɗa ku baza ta taɓa miki da sauƙi ba. Ai ita Ruƙayyan sai dai shiru tayi tana kallon ta kamar ta samu t.v

Inda ita Hauwa da ta gaji da jin zancen ta sai tace, "Sauda idan har na ɗagawa Mijina hankali a kan abun da yayi ninya riban me zan samu? Kar ki manta duk wani namiji idan ya dage zai yi aure babu me hana shi, su auren kawai suke hangowa har sai sun yi kafin hankalin su zai kwanta, to kinga kuwa babu zancen wani in ɗaga hankali tunda ba a kaina zata zauna ba Ni kam."

"Oh! to ki zauna kar ki ɗaga, shiyasa wlh wata rana kike baƙanta min rai Hauwa, sam-sam ba ki da zuciya a jikin ki, ina ga anya ba rako Mata kika yi ba? Ki duba fa yanda kike wahala da Mijin nan naki da daɗi babu daɗi kin rufa masa asiri kin zauna, sai ga shi da abun da zai saka miki, amma har yanzu ba kya ganin laifin shi, anya kin san abun da kike yi kuwa? Gaskiya halin ki akwai ban haushi billahil lazi."

Ajiyan zuciya Hauwa ta sauke tana cire tagumin fuskarta, ta san baza ta fahimta ba idan har Sauda ce gwara ta ƙyale ta kawai, ita kuma tana da hankali baza ta taɓa biye shawaran ta ba, bata ga abun ɗauka a ciki ba. Miƙe wa tayi tana cewa, "Ni kinga Sauda bari in je in ɗaura abinci lokaci na ƙure wa, Allah yasa mu dace kawai."

"Amin. Ai kin kyauta tunda abun da za ki ce kenan, kuma wlh bari Anwar din ya shigo sai na tanka mishi."

Murmushi ne ya suɓuce a fuskar Ruƙayya jin abinda Saudan tace, "wannan mata! Ko ina ruwan ta?" Tafaɗa a ranta tana ci gaba da murmusawan ta; sai dai har yanzu ta kasa magana tunda dama ita ba me son hayaniya bace

Hauwa wacce itama take jin Saudan bata juyo ba bare ta bata amsa sai ma wucewa ɗaki da tayi

Inda kuma ita Saudan ta ci gaba da tsiyan ta, wanki ne a gaban ta take yi but fitina ya ɗauke mata hankali ko riga ɗaya ta kasa wanke wa, sai ma ta koma kan Ruƙayya tana ta mata zuba duk a kan auren da halayen Maza, shiyasa take ce mata, "ita ta tashi tsaye ta ƙwaci ƴancin ta, su Mazan ne sai da wuta ake iya sarrafa su, yanzu ita ga abun da Mijin Hauwa yayi mata duk da halin ƙwarenta. Wai ita me son Miji me biyayya sahu da ƙafa, amma ji be me yayi mata".

Surutun nata ya ƙi ƙarewa shiyasa itama Ruƙayyan ta tashi tayi mata wayon, "zata je tayi aiki." Duk don ta gaji da jin zancen nata da be ƙarewa, sai ta shige ɗaki



To a nan ne fa Saudan tayi shiru tunda ba me kula ta, sannan ne ta soma aikin nata sai kuma ta koma ƙorafin, "ga shi komi bata yi ba na gyaran ɗakin ta, ga wannan masifan wankin da yake cin mata tuwo a ƙwarya, yanzu idan su Haidar suka dawo ya zata yi da su ko abincin bata ɗaura ba? Kodayake sa ci bakin su tunda duk su suka bata wahalar wankin, kullum yara ayi su ba sa jin magana su yi ta ɓata kaya sai kace ƴaƴa gari guda ne da ita? Yara biyu kaɗai duk sun bi sun ishe ta kullum saka ta wanki suke yi ga shegen dattin tsiya kayan nasu. To wlh sai na gama wankin nan kaf zan yi girkin; zaku dawo ne ku same Ni, har Baban naku sai dai ya nema a waje idan ya matsu, bazai zo ya ishe Ni ba a kan taliyan banza da hofi da ya ajiye min babu ko kayan cefanen arziƙi, ban san sanda Bilal zai jin tsoron Allah ya gane Allah ya faku ba ya tuba ya riƙa bamu cefane ishashshe ba, kullum shi babu a gindin shi ya ƙare, Allah dai ya kyauta wlh".
[03/10, 7:42 am] OumƊahira نفيسة: 🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱

*RAYUWAR CIKIN AURE*
_(True Life Story)_

🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱🌱


*Story & Writing:*
_Nafisat Isma'il Lawal_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*





*TSOKACI*
_Wannan littafin tsokaci ne a kan rayuwar ma'aurata, abubuwan dake faruwa yanzu a gidajen Auren mu, da kuma matsalolin dake cikin auren. Duk wanda yaga labarin nan yayi iri ɗaya da rayuwar sa to yayi haƙuri domin ban yi don cin zarafin sa ba, nayi ne domin gyara, domin rubutu da gyara shi ne buri na, Faɗakarwa ita ce tsari na, Ilimantarwa kuwa muradi na ne. Isar da saƙon amfana ga al'umma shi ne tunani na. Alƙalami na a kullum yana bin hanyar da zai riƙa gyara ne._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 560
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days

Airtel
500MB 160
1gb. 310
2gb. 620
3gb. 950
4gb. 1250
5gb. 1550
Verlid for 30 days



9mobile
1gb. 500
2gb. 100
3gb. 1450
4gb. 1900
5gb. 2200
Verlid for 30 days

Cheap in safety.👌🏼










*PAGE:13*

_____Zaman Shureim da Intisar gunun sha'awa tamkar zasu ɗaure a haka sabida yanda suke kula da juna sosai, shi Shureim Sarkin iya soyayya ne ga shi ya haɗu da yarinya mara kunya ko kaɗan bata da nuƙu-nuƙu biye masa take yi suna shan love sosai, duk rayuwar su suna tsara shi ne irin na wayayyun ƴan boko masu koyi da turawa. Sun shafe kusan wata ɗaya suna gurzan soyayyar su tamkar zasu haɗiye juna, ko nan da can babu me fita a cikin su kullum suna liƙe da juna. To dayake shi Shureim a companin Dadyn shi yake aiki sai ya ga dama yake fita, sai da suka shiga wata na biyu ne sannan ya soma fita har yake iya daɗewa a wajen aikin; but da zaran rana tayi zai dawo gida sai kuma can bayan sallan la'asar sai ya sake komawa. Matsalar da suka soma fuskanta shi ne rashin iya girki da Intisar bata iya ba, and sai aiki domin ba ta iya taɓuka komai kullum bata da aiki sai latsa waya sai kuma soyayya idan Shureim ya zo yana buƙatar hakan, shiyasa ya je ya yiwa Momyn shi magana tunda suna da kuɗi kuma Intisar tana barin mishi sashi da datti kullum ba ya jin daɗin hakan, ya yiwa Momyn shi magana, "a samo mata me aiki."

Shiyasa Momy ta samo mata wata yarinya ƙarama wacce zata iya taya ta aiki

Sai dai ita Intisar son jikinta yayi yawa komai yarinyar take sakar mawa, ita take yin komai sai dai ita ta ci ta sha ta kwanta, shiyasa nan da nan part ɗinta ya soma lalacewa tunda aiyukan ya fi ƙarfin ƴarinyar

Shureim yayi mata magana, "ta gyara ta riƙa yin aikin da kanta." But sai tace mishi, "ita baza ta iya ba." Shiyasa ya ƙyale ta ya fita harkanta yana ci gaba da lallaɓa ta a haka tunda ya ji ya gani shi ya auro ta, sai dai sam-sam a ransa ba ya jin daɗi, abun da ya soma ɓata mishi rai yanda ba ta ɗaukar Momy da wani mutunci, sai a shafe sati bata je ta gaishe ta ba, kuma ko kaɗan be jin tana zancen ta ko ta ce, "ya Momy take?" A misali ta riƙa nuna damuwarta a kanta, shiyasa ranan nan ya zauna yayi mata faɗa, "shi fa bazai jure ba, iyayensa kaɗai yake dasu a halin yanzu bazai ɗauki rashin girmamawan ta a kansu ba, gwara tun wuri ta gyara tun kafin su saka ƙafan wando ɗaya da ita."

To dayake yanda yayi mata faɗan ya sa ta shiga taitayin ta sai ta soma gyarawa. Idan an kwana biyu tana leƙawa sai dai a tsaitsaye take iya zama daga baya ta tashi ta tafi. Shiyasa har yanzu babu wani sabo tsakanin ta da Momy. Ita Intisar tana ɗaukar ta a Uwar Miji wacce ba a sakar musu fuska kamar yanda ta taso a gidan su ta ga Uwarta tana yi, yanda ba ta daraja Mama haka itama ko kaɗan ba ta ganin girman Momy, gani take yi duk halin su ɗaya in dai aka ce uwar Miji to ba sa ƙaunar matan ya'yan su, ta taso bata ga ana girmama su ba bare ita ta koya. Yanzu kuma sai ta taso da maganar komawarta makaranta tunda a yanzu hankalinta gaba ɗaya ya karkata a kai, abinda take so a yanzu already tayi wato aure, to yanzu kuma burinta ace ta koma karatu ta zama big Girls irin matan nan wayayyu, tana son ta ganta a jami'a a yanzu tana watayawa, shiyasa ta sami Shureim da zancen komawarta makaranta, har tana cewa, "kawai ya biya mata jamb ta rubuta ta wuce jami'a don wlh ita burinta a yanzu kawai ta ganta a cikin manyan yan mata."

Bata san maganar nan ya baƙantawa Shureim rai ba, shi gaba daya sai yayi mata wata fassara daban, cikin ɓacin rai da ya ji ya taho mishi ya kalle ta yace, "wato so kike Yi ki je jami'a kina haɗa kafaɗun ki da ƙartin banza shi ne burin ki? To ba dai a nan gidan ba, wlh kamar yanda Dadyn ki ya cire ki nima bazan taɓa barin ki ba, gwara ki mayar da kwaɗayin ki a ciki don baza ki taɓa cin nasara ba, wannan ai shirmen banza ne shirmen hofi."

"Me kake nufi ne wai Shureim? Meye ma'anar maganar ka Ni kake zargi kuma yau?" Itama tafaɗa a cikin ɗaga murya domin ba kaɗan ba maganar nasa ya ɓata mata rai

"Eh ke nake zarga duk abinda ke ranki shi ne, Ni dai na faɗa miki baza kiyi min harkan akuyanci a gida ba, tunda har kika sake kika zo min gida ba ki yi karatu a can gidan ku ba; haka zalika nima a nan baza kiyi min ba, bazan jura ba gwara ki cire shi a ranki."

Kuka ta fashe dashi jin abinda yake cewa, cike da ɓacin rai tana kuka tace, "Ni...Ni ce zan yi maka halin akuyanci a gidan nan? Ni kake zargi saboda kawai na ce zan koma school? To ka faɗa min da wanda ka kama Ni ina iskanci sai in san eh da gaske Ni yar iska ce kamar yanda kake jifa ta da kalman?"

Yace, "tsare Ni kike yi kenan sai na faɗa miki?"


Cikin ɗaga murya da tsawa tace, "eh ɗin, wlh sai ka faɗa min da wanda ka kama Ni ina iskanci tunda zargi na kake yi."

Ransa sosai ya ɓaci, ya kawo iya wuya but idan ya biye mata zai iya zane mata jiki shiyasa ya miƙe daga bakin gadon da yake yana nufan ƙofa zai fice

But sai ta biyo shi tana janyo mishi Singlet ɗin jikinsa, cikin kuka sosai a yanzu ɗin take faɗin, "wlh sai ka faɗa min da wanda ka kama Ni ina iskanci, ba kai ne ɗan Iskan ba tunda kai ka koya min, ai kai ne babban ɗan iska..."

Bata ajiye numfashi ba ya galla mata mari, bata gama tantance wancan zafin ba ya sake kifa mata wani sai ga ta a ƙasa a durƙushe tana tsandara kuka tamkar zata fasa gidan, kuka take yi sosai nan da nan ta gama firgicewa hannayen ta dukka a kan kuncinta wanda har tashi yayi tsaban yanda ya shige ta, kasancewar ta fara tuni wurin yayi ja sosai

"Mara mutunci kawai Ni za ki yiwa iskanci? Dan ubanki idan ba ke ƴar iskan bace meyasa za ki biye min Ni da nazo? Dama can kin saba ne kuma ba ki isa kiyi min karatu a gida ba, idan kinga baza ki iya auren ba ga hanya nan kiyi gidan ku, banza shashasha mara tarbiyya." Yana gama faɗar haka ya shure ta ya fice a zuciye ya shige nasa ɗakin har da garƙame ƙofa

Kuka sosai Intisar take yi tana birgima tsaban marin ya shige ta, nan da nan ta haɗa majinu da hawaye suka yi caɓe-caɓe a fauskarta. Ta ƙi tashi a wajen kuma ta ƙi yin shiru haka take ƙara volume ɗin kukan, daga ƙarshe sai ta miƙe ta haɗa kan kayanta a Trolly tana ci gaba da kukan ta fice, baza ta iya zama ba tunda har ya soma dukanta gwara ta koma gida. A haka ta je gida tana wannan kukan tamkar ana yanka ta, idanunta sun kaɗa sun yi jazur sai zubar da yawu da mijina take yi

Shigowar ta cikin parlour'n nasu tuni Fauziyya ta miƙe tunda ita kaɗai ce tana zaune tana kallo, cikin tashin hankali take kallon Intisar ɗin da ta riƙe mata hannu, yanda ta ga fuskarta ta kumbura har da shatin hannu bata san sanda ta liliyo ashar ba tana cewa, "ƙundum uban can kayyasa... Uban waye yayi miki haka? Waye ya fasa miki fuska Intisar?"

Cikin kuka daƙyar take iya maganar ma ta sanar mata da, "Shureim ne ya mare ta."

"Mari?.. Mari?.." ta maimata ya kai sau huɗu sabida yanda maganar ta girgiza ta, "shi dan kutmar ubansa mahaukacin ina ne da zai mare ki? Uban me kika yi masa ne?"

Cikin kuka take faɗin, "kawai don nace zan koma school shi ne yace min wai bazan koma ba; ya hau Ni da faɗa har yana ce min Ni ƴar iska ce gidan mu babu tarbiyya." Sai ta sake fashewa da wani sabon kukan. "Cewa yayi zan je jami'a in riƙa iskanci da Maza."

Salati Fauziyya tayi; tana sake ɗauka ba tare da ta dire wancan ba jin abun da Intisar ɗin ta faɗa, "lallai ko Yaron nan be da mutunci duk yanda aka yi be gaji arziki ba, ɗan iska mara mutunci zai zo ya same Ni kuwa, tunda ke ba Jaka bace zai gane darajan ki, yo idan ba ki yi karatun ba uwar me za ki zauna yin mishi a gida? Ba sai da karatun bane za ki tallafi kanki ba? Zancen yake yi ki je ki wuce ɗaki babu inda za ki koma tunda ba jaka na haifar mishi ba, zai zo ya same Ni." Da haka ta tura ta ɗaki ita kuma ta koma ta zauna tana karkaɗa ƙafafu cike da ruwan bala'i a ranta, mini-mini kaɗan kuma sai ta buga tsaki tana aika mishi zagi tamkar zata ganshi a gabanta ta ci masa mutunci.



********

Shureim ko kaɗan be damu ba da tafiyar Intisar domin ransa a ɓace yake da ita. Sai daga baya ne da ya je part ɗin Momyn shi take tambayar sa, "ina Intisar ɗin?" A nan ne yake sanar mata, "ta tafi gida."

"Gida kuma kamar ya ta tafi gida? Faɗa ku ka yi ne da zata tafi gida da yammacin nan?"

"A'a tun ɗazu ta tafi. Kuma Ni ba Ni nace ta tafi ba."

"Ok wato faɗa ku ka yi? Faɗa min gaskiya My Son?"

Tura baki yayi yana shafa kansa yace, "Ni Momy wlh ta ishe Ni ne yarinyar nan, a kan kawai na ce baza tayi karatu ba shi ne take son yin min rashin kunya."


"To kai My Son mene ne don ta ce tana son komawa karatu? Ai inaga wannan ba abun tayar da hankali bane tunda nan dai gidan boko ne, kayi karatun nan ka ji daɗin sa itama kamata yayi tayi tunda muna da kuɗi babu abinda zai gagara."

"Momy Ni fa bazan yarda tayi karatu ba, wlh idan har zata yi karatu sai dai mu rabu don bazai yiwu ace tana zuwa makaranta tana haɗuwa da ƙattin banza ba."

Momy baki kawai ta saki tana kallon ɗan nata domin ba ƙaramin mamaki ya bata ba, kishi kawai take hangowa tsagwaron ta a cikin idanunsa, shiyasa ta ƙyale sa yana ta tukuburcin sa yana ƙunƙunai. Sai da ya gama sai tace, "to ka je ka dawo da ita don Allah Shureim kar ka bar min abun kunya, yanzu auren naku duka-duka yaushe aka yi har yarinyar nan ta soma yin yaji? Sannan kai kuma kana iƙirarin saki ko? To kar in sake jin hakan daga bakinka. Ai auren gaba ɗaya ɗan haƙuri ne haka nan zaka yi ta lallaɓa ta har ku saba, Maryam yarinya ce ƙarama dole kai zaka riƙa nuna mata hanyar da ya dace da kuma abun da kake so, ka tashi ka je yanzu ka dawo da ita."

"To." Ya furta kaɗai yana miƙewa duk da ba da son ransa bane,

Please Login or Register in order to submit comment