Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ba barayi bane jin muryar mace kuma tace bakine yasa dadda dan sassauta murya tace baki daga ina kuma baku da suna ne saida Ammi taqara kallon bossay tace to kajide me tace saikagaya mata ni nagama nawa kuma wlh nagaji da tsayiwa zan koma  idan baza kayi mata bayani ba yace Ammi Allah innace mata nine baza ta kulamu ba watakil ta hadamu ta zage suna ta faman tunanin mafita kawai sukaji Ameesha daga cikin dakin tace yaya bossay kushigu kawai ba shikadai harta Ammi abun ya matukar bata mamaki ta akai yarinyar tasan sune tundade basuyi magana da qarfi ba bare tace taji muryar bossay ita kuma datayi maganar tasan basu taba ganin juna ba ko a hanya bare kuma tasan muryarta jin shirun nasu yasa Ameesha qara cewa wai bazaku shigo ba tanadaga cikin dakin take magana saboda dadda ta ruqeta ta hanata fita amma da tun sallamar farko zata fita saboda tasan basu da wani da zezo musu gida yanzu bawanda suka sani kuma daman tunranda yagaya mata zezo da Amminsa take jiransu dan haka yanzu tanajin haka jikinta yabata sune Ammi ce ta dan daga murya tace gamunan tana fada taji dadda tace inkunsan kune kar kusake kushigo min daki bana ce kar kasake inqara ganin qafarka agidan nan babaka jin magana kenan harda dakko min mace kazo min da ita to bazan bayarba jin haka kawai sai bossay yaja hannun Ammi suka nufi dakin Ammi na tajan hannun ta da nufin ya saketa Amma yaqi har saida yakaita cikin dakin sannan yasaketa shikuma ya tsaya abakin qofar  dadda dake bayani hannuta ruqe da Ameesha da taruqe ta gama sai faman kwace kwace take amma takasa saboda ba qaramin ruqo dadda tayi mata ba dadda nata zuba kawai sai ganin mutane tayi tsudum acikin dakitan ta ai ba shiri dadda ta mike tsaye da sauri zata zazzaga musu masifa sai kuma ta tsaya cak tana qarewa matar kallo baza ta taba mantawa da wannan fuskar ba arayuwar ta itama Ammi tsyawa tayi tana kallon ta da mamaki afuskar ta dadda tace AMINA itama Ammi amsawa tayi da cewa daman kina nan dadda tace eh gashima kin ganni kuwa tace to ai shiknanma komai yazo da sauqi ta kwana gidan sauqi ai Bossay da Ameesha kasaqe sukayi suna kallon ikon Allah daman sunsan juna lokaci guda Bossay yaji wani irin farin ciji ya lullube shi ganin yanda dadda ke magana da Ammin sa shikenan da alama bukatar sa zata biya tunda yaga haka Ameesha ce tace dadda a ina kika santa dadda bata amsa mata ba tace wa Ammi bismillah Aminatu zauna mana sai ta kalli bossay da har yanzu yana bakin qofa tace kai kuma kawani tsaya mana abakin daki sai kace dogari sai kashigo ka zauna badan halinka ba ta fada tana hararar sa dukan su saida suka dan dara saboda yanda tayi maganar ita ba farin cikiba ita ba bakin cikiba ita ba fada ba kamar na aborin kunya tayi ta yanda tayi din abun dole yaba ka dariya Shigowa yayi be zauna ko ina ba sai gurin Ameesha yaje kusa da ita datake tsaye tana mamaki ta kasa magan yaja hannuta suka zauna akan katifar ta yana kallon ta itama shi take kallo zasu fara kallon juna kenan kamar yanda suka saba sai dadda tace tasar min daga kusa da jika malam yar dariya kawai yayi amma be da niyar tashi hakura tayi tajuya kan Ammi da take binsu da ido sannan tace wai daman kina da babban da bansani ba Ammi tace ba dana bane dadda ta harareta tace shiyasa ai naga kuna kama ko Ammi tayi dariya batace mata komai nan de suka shiga gaisawa da kuma tambayar bayan rabuwa bayan sun gama kuma sai Ammi tace daman Aliyu ne yataso ni wai Sai nazo nataya shi roqonki akan zancen  Ameesha da yayi miki yana fada dadda ta canza fuska duk dade daman tasan abun da yakawo su kenan kuma itade tai makon da matar nan tayi mata arayuwa da kunya tace mata a a ba amma kuma bata tunanin zata iya bayar da Ameesha amanar Allah agareta Ammi ce ta katse mata tunanita da cewa Amma fa in badamuwa in kinga da damuwa sai mu hakura kinga bama shifa haqqin kiba ko dadda tayi shiru takasa tanka mata saida ta danyi jimmm tana tunani sannan tace to Amina ni bansan me zance miki ba kinga de ita kadaice dani kinga zama baze min dadi ba kuma ta tai maka min tana deban kewa bazan iya zama nikadai ba Ajiyar zuciya Ammi ta sauke sannan tace to amma meze hana kema kidawo gidan sai kuzauna gabasaya daman ni tun a lokacin nace kizauna amma kika qi yarda to yanzuma akaro na biyu inbazaki damuba ina qara roqanki kidawo gidana da zama zaro ido dadda tayi tace ni yar gidan ubana kawai gode gode dani sai in koma gidan mutane da zama ba aiki ba ba komai  gsky ni bazan iyaba kiyi hakuri Ammi ta numfasa sannan tace to dadda na yarda sai kizo amatsayin me aikin tunda haka kike so nanma qin yarda tayi tace nifa kirabu damu muci gaba da rayuwar mu ahaka Ameesha da bossay dasuka zuba kunnuwa suna sauraron su sunajira suji dadda tace ta amin ce amma taki sai suka saka baki suna ta roqonta dan Ameesha harda kukan ta shabe shabe tana cewa dadda inde kina sona dagaske to kiyarda dan Allah kuma inkika qi yarda to wlh sai kinkaini inda iyaye na suke ko kigaya min suna ina jin wannan batun yasa dadda shan jinin jikinta taji wani iri tasan Halin Ameesha inde tace zatai to sai tayi din inde ba ta yarda ba tasan bazata rabu da itaba tunda ta fahimci tanason komawar tasu gidan nasu din dan haka ba tada mafita da yarage ta amince haka suka cigaba da roqonta da qyar ta amince tace ta yarda zata koma din amma da sharadi amatsayin 'yan aiki zasu koma gaba dayansu daga ita har Ameeshan Basu da zabin su amince da sharadin ta indan ba hakaba kuma zata iya canza ra ayi dan haka gaba dan yansu sukai na'am dahakan suka ce sun yarada sun amince  yarda itama tace to ta amince Bossay saboda murna besan lokacin da ya rungume dadda ba har da dagata sama yana juyawa aikwa ta daddage ta buga mishi duka abaya tanacewa kaga marar kunyar yaro nizaka daga wlh kasaukeni ko ranka yayi mugun baci duk da haka be sauke ta tace wlh zance nafasa tafada tana gartsa mishi cizo a dantsan hannun sa aikwa bashiri yasauketa yana cewa dadda mungode mungode sosai dadda de ya wujijigata sai faman  sauke numfashi take tana haki sukwa su ammi da Ameesha sai faman dariya suke mata saida ta tsagaita ta kalle sa tace wlh kaide baka da hankali ko kadan inbahaka ba yaza ayi kadaga ni saboda ka rainani ko to wallahi zamusa qafar wando daya dakai zamu raba gari sai na koya maka hankali kai inta kama ma da duka bulala zansa in zaneka da bakafi qarfina ba shima dariyar yayi yace tab nidin kikafi qarfi wallahi tsaurin ido ne dake tsohuwar nan kiganni babban namiji dani me jini ajika amma kiwani ce banfi qarfinki ba to zamu gwada kwanji nan gaba saikigane idan nafi qarfinki ko banfi ba dan inaji saide a kwashi kasusuwanki akai rami a binne dasauri tayo kansa zata shakoshi yayi saurin gocewa ta kamo iska tana cewa aniyarka ta bika mutuwa so kake so inyi ko  wallahi saide kai abinne ka bade niba saboda sai naga 'ya'yan 'ya'yan 'ya'yan Ameesha sannan zan mutu Ameesha tace kai yaya bakasan dadda ba abun data tsana take tsoro irin mutuwa ba ko yace kuma ko tana so ko bata so  sai ta mutu ba dadda tace bakin ka yasari danyan kashi ko zan mutuma ba yanzu ba sai ka mutu ka barni hakade sukai ta fafatawa shi yafada ita ta fada ko yaki yin shiru saida Ammi ta katsasu sannan suka dena Ameesha tace dadda mu hada kayan mu kinga dare na qara yi dadda tace to aranni muje biki uwar kanzagi ai bayau zamu komaba kuma ba gobe ba tace sai yaushe tace sai na shirya tukunna bossay ne yace haba dadda wani shiri kuma zaki ba kaya bane kawai ni kubarsu ma zan siya muku wasu kar kudau komai wlh kawai kuzo mutafi yanzu dadda tace to sannu qaruna uban yan kudi munqi din sai mundau koman mu ko tsinke baza mu bari ba yace to ai ke sai ki tazama daganan kar ma kizo mu sai mutafi da Ameesha tace itama ba inda zata qafata qafarta Ammi tace dan Allah kutsaya ayi magana tsayayyiya mun wuce dare na qara yi mana fa tana fada ta maida hankalinta ga dadda tace yanzu dadda ke nanda yaushe kike ganin zaki gama shirya wa sai yazo ya dauke ku dadda tace nan da sati biyu Ammi tace haba dadda wane irin shiri zakiyi ne har zuwa sati biyu dagaske kamar yanda Aliyu yagaya miki basai kun dau komai ba dan Allah kawai ku taho da kayan jikin ku sai dan abun da ba a rasaba ta bakin Ameeshan ma ni wallahi da yanzu kukazo muka tafi kawai Dadda ta katseta da cewa Wallahi kwa bazan mu biku yanzu ba Ammi  tace to shikenan ai baza muyi miki dole ba Ameesha tace to ni dadda zan bisu ke kyataho daga baya nan ma kin yarda tayi da kyar de suka shawo kanta akan gobe da daddare yazo ya dauke su da haka suka yarda itade Ameesha ba haka taso ba taso ace daga yauma tagama kwanan gidan amma yazatayi dole ta hakura zuwa goben daga nan Ammi ta mike tagyar mayafin kanta tare da cewa to dadda mu zamu tafi sai Allah yakaimu goben dadda tace to shikenan Allah yakaimu da rai da lafiya Ammi tace amin tare da bude labulen dakin tana fita tsakar gida sannan dadda tabiyo bayanta sai bossay da Ameesha suma suka fito hannun su ruqe da na juna kamar kar su rabu haka suke ji har qofar gida suka rakosu suna qarayin sallama sanna Ammi ta zagaya ta bude tashiga shikuma ya tsaya yaki sakin Ameesha yana cewa dan Allah dadda kibari mutafi da ita wallahi banason rabuwa da ita tace sai kayi kuma in halinka ne danni nagama magana ba yanda ya iya haka yasake ta da qyar badan yaso ba itama kuma bata so yatafi yabarta din saida yashiga mota ya rufe sannan ya zuge glass din motar yana daga mata hannu yace to sai goben itana hannu tadaga masa  dadda taja hannu ta tace dalla malama wuce mutafi nagaji Bossay ne ya leko waje yace wai ke bakya gajiya da masifa abun masifa baya miki wahala kulum hayaya hayaya bakya gajiya sai kace kaza dadda da batai niyar kulashi ba amma jin yace mata kaza yasata juyowa afusace zata sauke mishi magana dede da maganar sa kawai yaja motar yayi gaba yana yi mata gwalo yana dariya  ya buleta da isaka yayi gaba yana ta tiqar dariya Ammi na tayashi tace wlh naga alama daga haduwar ku yanzu yanzu har ka rainata amma nasan zatayi maganin ka tunda dede take da kai kuma zaku zauna guri daya duk abun da tayi maka wlh ba ruwana kai da ita shima dariyar yayi yace ai Ammi inba haka nake mata ba bazata rage masifa ba kuma nima rai nani zatai taringa min masifa ko agaban waye amma idan nai mata haka to bazataiba tasan intayi ma ba barinta zanyi ba kinga daga nan sai ta ringa jan baya dani Ammi tace magani ai ita da halinta ne ai bazata dena saide kai ta hasalata tana maka abun da batai niya ba yace hmm aikwa zamu kwashi yan kallo dan nima ba raga mata zan ba Ammi taci zamu gani ai shima yace zaki gani kuwa ahakade suke ta tattaunawa suna tafiya
Dadda kwa kwafa taja sannan tajuya tana kallon Ameesha itama datake tai mata dariya bata kulata ba ta wuce ta tana cewa wlh yaron nan sai yagane kuransa naga alamar besan wacece ni ba amma muzuba mugani dan halak kafasa Ameesha dake bayanta tace lalle yau naga deden dadda Allah ya kara gwara yaringa yimiki haka wlh ke kullum murya asama duk dahaka da dadda bata kulata ba saboda akufile take wai ita yaron nan ze cewa kaza har tashiga daki tana faman zuba ita kadai itama Ameesha tana shiga kan katifarta kawai ta wuce ta kwanta cikin ranta fari tasss jira kawai take gobe tayi subar gidan sai kuma can ta tuna da bestyn ta Allah sarki yanzu rabuwa zasuyi kenan aikwa gobe da sassafe zataje gidan su acanma zata yini suyi sallama da intana zuwa aqafa tasan yanzu saide ta hau mota saikuma ta tuna da bossay ai yana zuwa zance wajen Rasheeda saita gaya masa duk sanda zezo sai su taho tare yasauke ta agidan su shikuma ta wuce idan yadawo sai yadauke ta sudawo gida haka taita tunane tunanen abubuwa da yawa daga qarshe da taga ta kasa bacci kawai sai ta tashi ta kunna gulf din dakin ta kalli dadda data kaji da mitar tayi bacci  fita tayi daga dakin tayiyo alwala tadawao tayi salloli da qara godewa Allah da nuna farin cikinta akan wannan sauyin dayayi musu lokaci daya tadade tana addu'a sannan ta shafa ta koma ta kwanta bata dade ba kwa bacci yayi awan gaba da ita.............
     
             ***********************
Da safe suna tashi Azeema tahada musu breakfast sannan suka ci gaba dayansu Saleem yau bayi niyar zuwa wajen neman aikin da wuri ba saboda kiran dazeyiwa dad din su Rasheeda shiyasa yabari idan suka gama sai yatafi suna gamawa kuwa ya dauko wayarsa yakira shi sannan yasa wayar a hansfree duk sukayi shiru wayar na ringing suna jira suji andaga amma har wayar ta katse ba adaga ba sai yaqara kira shina no respon saida yayi sau uku ana hudun ne aka daga ana dagawa kuma sai sukaji muryar mace tace yana wanka inya fito za afada masa ana gama fadar haka aka kashe ba ajira amasar suba wayar suka bi da kallo gaba dayan su kamar zasuga wacce tayi maganar aciki  mamace tasamu damar cewa kabari anjima sai ka qara gwadawa yanzu katashi kaahirya katafi ko acan dinma ka kirashi duk yanda kukai inka dawo maji yanda kukai da to ya amsa mata sannan yatashi ya koma part dinshi  daman yayi wanka dan haka kawai sai ya shirya shaf shaf yafito har yanzu suna zaune a falon Inda yabarsu yana be zaunaba kawai yayi musu sallama ya fita suka bishi da addu'ar samun nasara............
         ************************
tana kwance kan gado tayi daidai ya fito daga wanka yana tsane jikinshi da towel kalanshi tayi tace tun dazu aka kiranka a waya amma nace kana bandaki yace ok saida yagama shirya wa tsaf sannan yadauki wayar ya duba yaga new number ce sai yadanna kira tana shiga ko ringing uku ba ayiba aka daga ana dagawa daga can bagaren aka fara sallama shikuma ya amsa saida suka gama gaisawa sannan saleem yafara yimishi bayanin shine wanda yabawa qanwarsa kati akan yakira shi siyi magana akan batan mahaifinsu saida yagama sannan dad yace mishi ok yagane ai harma yayi magana da dan nasa tun jiya da daddare yanzu yaturo mishi full name din sa da kuma kalar kayan da yake ajikin sa da kamannin sa da shekarun su yafadi de komai yanda in anyi bincike duk wanda yagansa ze gane sa amsa masa yayi da yimasa godiya sannan sukayi sallama ba dadewa kwa yaturo mishi duk abun da ya bukata yana turo mishi shima ya turawa khalid bayan ya tura mishi sai kuma ya kira shi yana dagawa yaqara yi masa bayani sosai sannan yace dan Allah yasa ayi cigiyar nan yau kuma akai sati anayi yace mishi to sannan sukayi sallama yana gamawa ya mike tare da kallon mom datana jinshi bata tanka masa kuma ba bacci take yiba yace ni zan fita amma tayi masa banza saboda tanajin haushin sa tunjiya tunda yayi mata bayanin yanda sukayi da su dadda kuma yace mata Ameesha zata dawo aiki duk wanda kuma yaqara yi mata koda kallon banzane sai ya dau mummunan kwakwaran mataki akai ita kuma tace mishi be isaba hakade sukai ta sa insa har saida yabar mata gidan sai can dare yadawo shine tunjiya take tafaman cika ta na batsewa ahiko be kulata ba dan yasan neman fada take dan haka yanzuma da yace mata ze fita ba kulashi ba be kara bi ta kantaba yasa kai yayi ficewar sa.....
Rasheeda ce tafito cikin shirinta na tafiya makaranta jikin sanye da streetgwon da ta kamata kama ta fitar mata da surar shape dinta sosai sai mayafi da ta yafa a kafada sai wayoyinta da key din motar ta dan ko jaka yau bata dauka ba tana fitowa sukayi kicibis da dad dinta da tace dad Good morning yace morning dear how was your night tace fine ok Good girl har ze wuce tace uhm dad yace yes my daughter what d u want tace dad I need a money be tambaye ta me zatai dasuba kawai yace for how much dear tace 80k yace ok I will send u later inna fita zansa miki 1m tace ok dad thanks yace kidena min godiya inban baki abun da kike so ba meye amfanin tara kudin tace hakane dad girgiza kai yayi kawai sannan yace ok let me go sai nadawo tace adawo lagiya bata jira amsawar saba tashige bedroom din mom dinta tana kwankwasa kofar bata jira ambata izinin shigowa ba kawai tasakai tashiga batare da sallama ba tana shiga taga mom kwance ta dauka ma bacci take sai kuma taga ta tashi zaune sannan ta qarasa kusa da ita tace mom I have to go tana shirin juyawa taji mom din tata tace waike naga fuskarki bawata damuwa tace mom me akai min zan sa kaina adamuwa to mom tace oh hakama zakice kinmanta abun da dadyn ki yafada kenan baki ta dan tabe tare da daga kafada irin I don't care it's your fault is not my fault dinnan sannan tace mom wlh you have a problem yanzu meye abun damuwa idan ta dawo sai me abun da ba akan mu take ba kuma nasan baza ta qara gigin yimusu wani abunba tunda tasan intayi me ze faru kama bayan wannan ma dad din ai ba mezaman gida bane koma me zamuyi mata ai baze saniba tundade nasa ai bazata gaya masa dan haka wlh ki kwantar da hankali duk zakibi ki takura kanki akan waccen banzar yarinyar da batasan kinayi ba nide kinsan bazan qi yin abun da dad yake so ba saboda nima yana min duk abun danake so kuma yana nuna min irin son da yake min nima kuma inasonshi dan wlh nama fi sonahi akanki mom de tagumi tayi tana jin abun da yartata take fada saida tagama sannan cikin masifa tace tashi kibarmin before I lose my temper useless girl kawai ubanwa kika taba ji yace yafison ubansa akan mahaifiyar sa sai ke shasha sha kibarni da abun da yake damuna mana basai kin qaramin wani ciwon kan ba ke kwata kwata arayuwar ki ba ruwanki da duk halin da zanshi ke sabgar gabanki kike to tunda yafini agunki sai ki koma gurinsa kar kisake zuwa inda nake taqarasa fada tana nuna mata qofa da hannu tace get out on my side Rasheeda tashi tayi tana cewa ai basai kin koreni ba zan bar miki daki kuma bazan qara zuwa inda kike tunda haka kike so daga cewa nafison dad sai ki kama kishi dashi to kwa zaki mutu dan bazan dena fada ba wlh nafisonshi akanki tana gama fadar haka tabar mata dakin mom jitai kamar anbuga mata guduma akai kamar ta dora hannu akai ta kurma ihu ko zataji sassaucin da zuciyar ta kemata yarinyar nan so take ta kasheta lokacinta beyi ba......

Daman ance kaso naka duniya takishi ka qi naga duniya ta soshi inka nunawa yaro so sosai wai kai baka son bacin ransa inbaka sashi kuka ba wataran shi zesaka.Allah kabamu zuri'a dayyiba masu yimana biyayya kamar yanda mukewa nam iyayen.......


More comment more typing
No comment no typing

❤xeemat....love❤
[2/26, 7:06 PM] ~~~~writer~~~~:   💅SARKI SAMEER......💅
             by❤xeemat.....love❤

              🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Allah yajikan magabatan mu dasuka rigamu gidan gsky mamu intamu tazo Allah yasa muciki da imani Allah yarabamu duhun qabari da azabarsa Allah ya haskaka mana qabarinmu Allah kasa mala ikunka su tarbemu da kyayyawar fuska Allah  yasamu a aljanna firdausi Allah yasa can tafimana nan dadi Ameen...................

                       Bismillah............
Episode 16🖋
                *********************
                      *MASARAUTA*
koda washe gari tayi kamar yanda Fulani ta fada haka a kayi wannan bawan Allah yafara aiki tun aranar wani bafade ya nuna mishi komai abun ma sai yazo masa dasauki saboda su biyu ne abangaren kula da dawakan bashikadai bane haka suke ta aikin basu suka gama ba sai wajen shabiyu na rana kuma zasu qarayi da yamma wannan qa idane sau biyu ake kula dasu ana duba lafiyar su bayan sun dawo ne be wuce dakin da aka bashiba ya hadu da  wannan mutumin da suka tabayin magana dashi lokacin da aka qulleshi akan ze taimaka mishi  yana ganin da sauri yaqarasa kusa dashi zeyi magana kenan yarigashi da cewa baba ina wuni ya aikin da fatande bakaji wahalar sa ba ko baba yace to yaro da saukide za ace kansan bansaba abune da bantaba yinsaba kaga dole yadan ban wahala kafin in saba yace hakane baba to Allah yataimaka yauwa ya maganar da mukayi dakai inaso kafadan yanzu tunda naga kowa yakama aikin gabansa hankalin su baya nan budar bakin baba keda wuya ze fara yi mishi bayani suka ji andaka musu wata tsawa anacewa kai HAMZA uban me kuke yi kai da sabon zuwa ko kazo kaimishi halin naka to wlh idan naqara ganinka dashi sai nafadawa me martaba me maganar  shugaban sune gaba danyansu masu aikin masarautar  shiyake kula da shige da ficen kowannen su kuma bashi da mutunci kana dan qaramin abun zeje yaqara gishiri da magi yasa ayi maka hukunci me tsauri shiyasa suke shakkarsa basa son abun daze hadasu dashi Hamza da sauri yace tuba nake shugaban mu bawani abu muke cewa ba daman tambayata yake inda ze samu razor ze yanke farcen shi shine nake gaya masa yazo ya sameka saikuma gaka kazo wanda aka kira da shugaba yayi tsaki sannan yace ai nasan halinka ne da shegen shishigin abun da ba ruwanka wai kai me tausayi ko to Allah yasa inji wani abun a tsakaniku nan gaba wlh sai nasa  anmaka abun da baka taba tunani ba hamza yace hakan ma baza ta faruba aimin afuwa yana fada yabar wajen baba da taqaici ya gama cikashi yama kasa magana sai da mutumin yace mishi kai kuma kazo muje inbaka kuma kar nasake gabinka da kowa duk abun da kakeso ni zakazo kasama ba ruwanka da shiga cikin wasu mutane saboda duk cikin mu ba sa'anka dan haka ka ringayin iya abun da yake gabanka kar ka bari idona ya sauka akanka dan banda mutunci baba yajinjina kai aranshi yana mamakin yanda yake gaya masa magana kansa tsaye sai kace yana magana da sa'ansa al halin yasan yagirme mishi nesa ba kusaba zema haife shi amma ba ruwansa hakan be da meshi ba yana jinjina ma wannaan halin nashi da yake nuna mishi tun haduwar farko saida yagama tunani nasa   sannan yace amma nikam da ka barni inshiga cikin kowa ma ni na yarda ku zama abokaina tunda banda wanda nasani taya zan ringa zama nikade batare
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment