Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

dan yanzu bana tsoron sa muzuba nidashi dan halak ka fasa nida man nasan da biyu kuka zo nan in bahakaba taya akai kukasan yarinyar ba yar nan gidan bace harda wani cewa ina iyayen ta shi wanda ya turo ku besanar daku ko wacece ita ba sai zuba take dan alokaci daya taji wani qwarin gwaiwa yazo mata dan har da mikewa tsaye tazo gabasu tace kutashi kutafi,
gaba dayan su bawanda maganar ta bata tsaya masa arai ba dan basu san inda zancen ta ya dosa ba duk sun kasa bata amsa,

shiru falon ya dauka na 'ya dakiku kafin daga bisani hajiya  tayi qarfin halin cewa baiwar Allah kiyi hakuri mu bada wani mugun nufi muka zo miki ba alkhairine yake tafe damu batun jikarki muma bamu san komai ba itace dazu take bamu labarin halin da take ciki har take gaya mana musababbin abun da yasa ta kwanta a asibiti sakamakon muta nen da suka kawo muku farmaki har suke ikirarin kema zasu ka sheki tabamu labarin duk abun da taji kuma tasan tabbas kina da masaniya da zuwan su kuma kinsan daga inda suke shiyasa muka zo domin mu kubutar da ku wannan da kike gani yana da hanyoyi da yawa a agarin ba dana bane kamar yanda nagaya miki da farko a gidan sarkin garinnan yake jika ne ga sarki  nasan inma baki san gidan ba kina de jin sunan sarki na yanzu sarki salahuddeen Muhammad sameer to acikin gidan yake da zama sannan kwararen likita ne kamar yanda kika gansa asibiti hasalima asibitin nasane  shine me asibitin gaba daya,
kuma....😜😜😜🙈 sai gobe nima namanta me zan qara cewa said na tuno🙇‍♀️🙇‍♀️🤦‍♀️
(furairah ga shinan nayi me yawa karatu har sai kin gaji dashi saboda yawan sa🫣🫣)           
[4/9, 11:29 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode 91-92-93

         """"""""""""""""""""""""""""""""

kuma akwai dalilin dayasa muka zo da wuri sakamakon abun da jikarki tafada nacewa ance kuna tare da wanda yake bin daddiginku shiyasa muke so afara magance matsalar tun yanzu ashirya yanda za a bullowa al'amarin amma wlh mu bada wata manufa mukazo ba kinji dalilin zuwan mu har muka tambaye ki amma in hakan ya bata miki rai kiyi hakuri baki fahimce mu bane shiyasa,

tunda tafara bayani dukan su suka zubo ido da mamaki akan fuskar kowannen su dan basu taba tunanin sameer daga gidan sarauta ya fito ba no wonder yake faman jijji da kansa ashe yasan me yataka shiyasa yake abu kansa tsaye na ko dar baha shakkar kowa, dadda kwa tasha jinin jikinta da magan ganun da tagaya masa sai taji dama bata gaya masa Allah yasa de kar yace zai hadata da sarki yace  ta zage shi wayyo Allahn ta jitakeyi dama batayi ba sai faman sunnar dakai qasa take

Ammi ta kalleta sanan tace mata yanzu wanan daga gidan sarauta yake wlh bamu sani ba tafada tare da maida kallon ta ga sameer da ya hade girar sama da ta qasa, kollo daya tayi masa sannan ta janye idon ta ta mayar kan hajiya  sannan tace  gaskiyA nagamsu da bayanin ki  abun da yakama ta muyi kenan
Amma dadda ke ya kika ce kinji de daga inda suka fito ba wadanda kike tunani bane zaki iya fada mana ne ko kuwa har yanzu kina kan bakarki ke muke sauraro dadda da har yanzu kanta na qasa tace zan fada muku amma dan Allah ku qaran lokaci ba yanzu ba,
Sameer ne ya katse su da cewa wai kuna ta wani boye boye ke bakisan wanda yake tare daku ba yanan yanzu haka yanajin tattaunawar da kuke ni bangama amfanin da yasa kunsan shi kuma kuka amince kuka biyo shi ko a tunanin ku bazai iya aikata hakan ba to mutum beda tabbas ba a yarda da  da kowa  awannan zamani bakowa kake yarda dashi ba,

su Ammi basu fahimci inda ya dosa ba dan haka Ammi tace dan Allah me kake nufi bamusan me kake nufi ba waye yake tare dasu da yatsansa ya nuna bossay yace wannan gashi nan danki yana aikata mugunta abanyan idon ki wayasani ba ko kema bakin ku daya yafa yana maida dun ke bake kikace sunce wanda zezo ya dauke ku duk bakinsu daya ba nan de yaqara basu labarin yanda abun yake da tabasu labari  yakara sa fada yana kallon Ameesha kai ta shiga girgiza musu sannan tace wallahi beda hannun aciki haka de sukace amma nasan sharri suke mishi gaban bossay ba qaramar faduwa yayi ba yake kuma zufa ta shiga wanke masa jiki atsorace yace ni kuma ni wallahi qarya suke min niban san suba ma wallahi qarya suke min nande yafara yi musu rantse rantse,
Ammi da taji abun kamar almara kamar a mafarki abun da bata taba tsammanin jiba yazo mata abazata gashi kuma yanayin yanda yake rantsuwa ze tabbatar maka da bashi da gaskiya take ji zuciyar ta ta harba idan hakan ta kasance gaskiya ya zatayi a rayuwar ta dan cikin ta da irin wannan harkar batare da tasani ba take, ranta yagama baci  iya baci bata san lokacin data daka masa tsawa tace rufewa mutane baki sakarai kawai da da sa hannun ka shine kake nuna kana kaunarsu alhalin qarya kake tashi tayi daga inda take ta koma kusa dashi tace kagaya min gaskiya kana da masani akai ki baka da ita idan kamin qarya nagano wani abun daga baya bazakaji dadi ba dan sai na mugun saba maka kagaya min gaskiya tun wuri ina sauraron ka tafada tana nuna sa da yatsa alamun gargadi wani irin wahalallan yawu ya hadiye tare da bude bakin sa ze yi magana ,
dadda  ta katsesu da cewa kar kitakurawa danki akan abun da bashida sa hannu aciki nima da shi nake zargi amma daga baya nagane qarya suke mishi suna sone kawai mufara zargin sa daga qarshe kuma naqi yarda da su saboda basa son dawowa ta  nandin shiyasa suka biyo tanan amma ni bana tunanin ze iya aikata abun da sukace din,
Sameer da tunda aka fara maganar ya zubawa bossay ido yana nazarin sa kuma yagano wani abun dan haka sai yace musu ya isa haka dole yaron nan yana da masaniya akan wani abun kuma sai yafada yanzu ko kuma yasa a kulle sa dan baze barsa haka ba saboda yaga raahin gaskiya a tattare dashi shettima ne yace haba sameer be kamata ka ringa zargin shiba akan abun da baka da tabbas akai suma daman ai ba cewa sukayi shibane kawai de suna zargin shine kuma kaji abun da ita daddar tace kaga yakamata mubi wata hanyar inda zamu fi samun  solution sameer yace wlh ko rantsuwa nayi baza tacini ba yaron nan be da gaskiya ka kalli kwayar idon sa zaka gane hakan,
Ameesha ce cikin kuka tace dan Allah kudena zarginsa wallahi ninasan beda sa hannu aciki amma kunqi yarda ku yarda dani tafada tana tashi daga inda take ta koma gurin bossay tace yaya dan Allah kayi hakuri kagaya musu bakasan komai ba kallon ta yashiga idon sa duk sun canza kala tsabar tashin hankalin da yake ciki dan ture ta yayi gefe daga gurin sa sannan ya sunkuyar dakai ahankali ya shiga furta basuyi qarya ba gaskiya suka gaya muku amma ina neman gafarku kuyi hakuri ku yafemin nasan na tabka kuskure abaya amma yanzu nayi da nasani tabbas kamar yanda kuke zargina hakane zarginku gaskiya ne amma kuma inaso kusan bada son raina hakan ta faruba ina da dalili na naqin fada tun farko san...be gama fada ba Ammi takwashe shi da wani irin mari Ameesha kwa mutuwar tsaye tayi ko motsa hannun ta takasa saboda bata taba tsammanin jin haka daga garesa ba, gaba dayama dakin kowa saida yayi mamakin jin abun sa yafada kamar ruwa ya cinyesu haka suka dauke gurin yayi tsit ko kadan bakajin motsin abun kowa da abun da yake saqawa aransa ,

Ammi bayan ta maresa ta kuma daga hannu tabashi wani tace meyasa me yasa meyasa zakayi haka meyasa zakaci amanar su sundau yarda sun baka ashe kai ba haka bane awajen ka ka cucuni Aliyu bansan haka kake ba harda kuka take magana saboda bacin rai daga hannu tayi zata qara sauke masa hajiya tayi saurin riqeta tace ya isa haka ki rabu dashi kamata yayi ai mutsaya muqarasa jin ta bakinsa ki kwantar da hankalinki tunda yafara bada hakuri kuma yayi da nasani ai ne kamata ki haushi da fada ba sai kiji ta yanda akai hakan ta faru kamata tayi ta zaunar da ita akan kujera, sannan ta maida hankalinta ga bossay da yadafe kumatunsa kwalla na sauko masa tace dannan muna sauraron ka ya akai hakan ta faru saida ya goge kwallar da ta zubo masa sannan murya cike da rauni yace wallahi nima badan son raina hakan ta faru tun aranar da mukaje gidan su nida Ammi da daddare muka tambaya bayan dadda ta amince za sudawo nan nace musu gobe zanzo na dauke su to awashe garinne bayan nayi sallar magariba natafi da niyar inje indauko sun ahanaya wani mutum ya tare ni tare da  shan gaban motata sai na tsaya ina kallon wanda yafito fusakar shide a rufe take ban gane kowaye ba bayan ya kwankwasa min qofa sai nafito ina fitowa nace masa malam lafiya yace lafiya lau amma idan naso ta zama lafiyar gaba na yafadi dajin hakan sai nace masa to me yafaru sai yake cemin muta nen da zanje na dauko kar na kuskura na naje na dauko su idan ma inason in tsira da lafiya ta to in gaggauta nisantar su kar inshi ga cikin rayuwar su saboda bajin dadi sukazo yiba musamman ita yarinyar da nake rawar qafa akanta rayuwar ta tan garari zata iya mutuwa yau ko gobe akoda yaushe ma zata iya rasa ranta dan haka inrabu da ita tun wuri  kar nasake nace zan taimaka musu inrabu dasu a yanda nagansu nikuma sai nace masa gaskiya abun da bazeyiyu ba kenan saide dan nariga da nayi niyya kuma bazan iya fasawa va sai yace to shikenan inje inyi duk abun da nashirya din sukuma zanji nasu shirin saide kuma ga wata hanya mafi sauqi zasu bani duk abun da nake so duk adadin kudin danake so zasu bani abu daya zanyi musu zuwa uku idan nai hakan zansamu kudi kuma zasu rabu dani lafiya baza sutaba lafiyata ba in bahaka ba kuma bani kadai bama dangina ma sunshiga uku jin hakan yasa na tsorata sai nace musu nayarda wani abu suke buqata sai mutumin yace nafarko suna so idan na dauki yarinyar duk wani motsin ta irin ga gaya musu na biyu kuma koda yaushe zasu iya bukatar in kaimusu Ameesha gurin su sannan kuma idinga nuna mata so sosai innuna mata kaf duniya ba wacce nakeso irin ta saboda ta yarda dani sosai yanda kowa ze sheda hakan saboda koda anrasa ta ba wanda zeyi zargin ni nakaita saide kawai ace ta bata daga nan kuma kowama yamanta da ita sannan ba ruwana da me zasuyi mata na qarshe kama akwai wasu takaddu dasuke bukata agurin dadda suna so in lalabo inda suke suma inkai musu idan nayi musu haka to nagama yi musu komai kuma zasu rabu dani da dangina bawanda wani abun da zesamu daya daga cikin mu idan kuma nace zangaya wa wani to gabadaya dangina sai sun rasa rayuwar sa ko iyayena kar na kuskura nagaya musu wannan zancen inbarsa da nan kuma suna kula da ni idon su yana kaina koda wasa nayi wani kuskure to zasu aiwatar da abun da suka gayamin ba yanda na dole na amince musu alokacin saboda kubutar damu gaba daya saida yaqara jaddada min da zamin kunne akan kar inbari kowa yasan wannan zancen amma ni wallahi bawai na amince  dan son rainaba kokuma dan inaso har cikin raina ba tsorone yasa ni amincewa kuma atake a lokacin ya karbi account number dita da kuma phone number na amma shi beban tashiba danace yaban sai yace baya bada number duk lokacin da ze kirani ze kirani da private number alokacin yasakamin 2.5 million aciki yace min wannan somin tabine idan nayi musu aiki yanda yakamata zasu bani ninkin baninkin din su kudi sai nace nagaji dasu kuma dangina bazasu qara yin talauci ba daganan har qarshen rayuwar mu sai lokacin na tsorata dasu sai naji dama nace ban aminceba tun farko bansan ta yanda yagane tunanin me nake yi ba kawai sai naji yace qaddara ta riga fata kar ka canza tunani ka riga ka amince kuma dole kayi ko kana so ko baka so in ba haka ba kuma hmmm a tsorace nace dashi ni nafasa zuwa ma dauko sun daga yau bazan qara zuwa inda suke ba sai yace dole inyi mun riga da mungama magana saboda yace min wai dadda taurin kaine da ita bata yarda ta zauna da kowa ba amma tunda sunga ta yarda damu to dole ta Han ya ta zasu qarasa aikin su da suke so nace masa dan Allah yagaya min me suka aikata masa kuma waye shi sai kawai yace min na kusan kusanka nan da wasu watanni wanda zezamo jigun rayuwar ka zamu kulla alaqa tajini kasanni kuma kasan waye ni nima kuma nasanka nasan waye kai dan haka kar ka wahalar da kanka akan gano koni waye dan zaka jefa rayuwar ka cikin garari shawarar da zan baka ka ajiye tunani akaina kayi abun da nasaka kawai kuma daga yau aikin ka zefara ka kula sosai ina tare dakai jin akoda yaushe hakan yasa naqara tsorata da lamarin sa wani kwarin gwiwa ne yazo min a lokacin zuciyata tabani kawai injanye abun dake fuskar sa dan ganin kowaye tunda yace nasanshi besan lokacin da nakai hannu na ba kan fuskar sa har na fara cire wa amma bangani ba atakaicede sai farkawa nayi naganni agadon asibiti bansan ma wa ya maida ni gida ba aranar shine lokacin da na tambayi Ammi tace in bari zata gaya min kuma haryanzu bata gaya min ba to kunde ji abun da yafaru iyakar gaskiyar abun da nasani kenan.....,

**********************

*Azeema*
yaya dan Allah kajirani mutafi tare kasande inason idan ta farka mu fara haduwa da ita amma tunjiya nace maka zanje kahanani kuma yau ma kace bazan jeba nide dan Allah ka yarda mutafi tunda mama tace bazan qara fita nikadai ba da sai inje kone kadai ce inma tafiyar ce dani baka sonyi kaji yayana nakaina Allah ya barmin kai,
tana sane take tayi masa haka saboda yaqi kulata tunjiya da tayi masa wannan abun wai shi adole fushi yake da ita shiyasa ma yayi mata haka na hanata zuwa gurin Ameesha yasan ta hakanne kawai ze iya hukun tata taji haushi,

cigaba tayi da takura masa har da ruqe qafar sa daman tana zaune akusa da qafar sa girgiza qafar sa tayi tana kwakwalo kukan muna furci dan hawayen ma yaki fitowa sai faman makyar makyar da ido take amma sunqi fitowa,
saleem dake gefen mama yana karyawa yace mama ki mata magana nace bazata ba kuma tana tafaman damuna wai danma kinci sa'a bantaba kiba ko yafada yana ture ta daga kusa dashi,
mama ce ta kalleta tace ke bakyajin magana ko tashi daga nan kibawa mutane waje cinki qunar rai ta tashi tana turo baki gaba zata wuce dakin ta sai aka kwankwansa qofar gidan nasu hartakai bakin qofa mama tace zo kibude gida ana kwankwasawa batare da ta amasaba ta juyo bata kalli kowaba ta wuce waje dan budewa me kwankwansawar tana zuwa kafin ta bude tace waye daga can taji muryar na miji yace nine dan daidai ta nutsuwar ta tayi sannan ta bude gidan binsa tayi da kallo saboda batasan shiba dan murmushi yasakar mata sannan yace sannu yarinya da fatan nasame ku lafiya tace lfy kawai, tana jiran qarin bayani ganin yayi shiru tace kayi shiru ko wani kake nema yace eh inason kimin sallama da mahaifiyar ki idan tana ciki tace eh tana ciki amma duk abun da zaka gaya mata nima zaka iya gayamin dan haka fadi maganr ka kanka tsaye kamar kana tsaye da itane nida ita duk daya muke bazato ba tsammani taji rankwashi a tsakiyar kanta juyawa tayi tana kallon saleem tace kai yaya me kuma nayi maka ni wai duk kabi ka tsaneni bansan me nayi maka ba kuma harar ta yayi yace dalla matsa nidaman nasan da abun da ya tsayar dake daga bude gida zaki zauna kina masa surutun banza ko sa'ankime da zaki gaya masa haka dan hade rai tayi sannan tace a'a kayi hakuri tana gama fada ta koma cikin gidan tana ta faman kunbura fuska,

Saleem ne ya gaida mutumin yace dan Allah kayi hakuri tazo tana yimaka shirme mutumin yayi murmushi yace ai yarinyace ba komai wallahi bata bata min ba, tunda gakama daman aikoni akai amma indamuwa inaso ka fara sanar da mahaigiyar ku sai mutattauna saleem yace ok ai ba damuwa shigo kawai muje yace a'a shigade kafara sanar da ita yace to shikenan bari inje yana kaiwa nan ya juya yaje ya sanar da mama tare suka fito tana sanye da hijab dinta har qasa tunda tafito take bin mutumin da kallo tanaso ta gano ko tasanshi amma taga batasan shiba ta danyi mamakin jin yana neman ta din alahalin bata sanshi ba fuskar ta ba yabo ba fallasa ba fusss ba asss suka gaisa sannan yace inba damuwa zam iya zama da zuciya daya ta karbe shi dan haka sai tace eh bismillah mushi ga daga ciki atare suka qara komawa cikin falon lokacin Azeema ta samu guri ta zauna tana jiran shigowar su,
Dylan su zama sukayi tare da zubawa wannan bawan Allahn da basu san daga ina yazo ba mama da ta qagara da taji maganar da takawo shi tace bawan Allah muna sauraron ka ka barmu a duhu dan qayataccen murmushi yayi sanna yace yanzu kuwa zakuji abun da yake tafe dani tace to munajin ka saida ya gyara zama sannan yace abun da ya kawo ni wajen ku daman shine an aikoni ne dan inzo in sanar daku halin da mahaifin ku yake yana nan da ransa da lafiyar sa gaba dayan su suka miqe tsaye atare dan yanda maganar ta dake su bazato ba tsammani maganar kamar a mafarki........✍


*Pls I need your prayer bana danjin dadi dan gobema da kyar inzan iyayin posting watakil sai jibi in kuma nasamu sauqi in Allah ya yarda zanyi kutayani da addu'a plsss*
[4/11, 9:06 AM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode 94-95-96

         """"""""""""""""""""""""""""""""

_________________*Azeema*

Azeema ce data rigasu dawo cikin hayyacin ta da sauri tazo gabansa tace dan Allah da gaske kake bawan Allah ba marki nake ba kamar yanda nasaba dan murmushi yayi yace bawani mafarki 'yarnan maganar da kikaji gaskiya ne yana ina dan Allah me yasameshi me yasa yaqi dawowa wajen mu meyasa ya tafi yabarmu duk tabi ta rude hawaye har sun fara wanke mata fuska mama ce tazo takamata ta zauanar da ita kusa da ita sannan tace bawan Allah munajin ka saida ya kuma gyara zama sannan yadan numfasa sannan yace me gidanki yana gidan sarki da mamaki suka maimaita gidan sarki to me yakaishi gidan sarki nasan zakuyi mamaki ko to nide abun da aka ce nasanar daku shine ku kwantar da hankali ku babu abubun da ze sameshi saide wani hanazari ba gudu ba a kwai babbar matsala dan baze yiyu kugansa ba ko yagan ku saboda inda yake din ko da wasa yayi qoqarin fitowa zasu iya kashe shi saboda basu da imani muta nen nan saide kawai kuyi hakuri kucigaba da addu'a har lokacin da Allah zesa yafito inkuka maida komai ga Allah sai kuga ya kawo muku mafita ta cikin sanyi saboda sun riqeshi yazama bawan su agidan kuma in kunga fitowarsa to saide a fito da gawar sa saboda inde suka maida kai bawa to babu shaka kazama nasu har abada nima yanzu fa kyar aka sanar dani inzo in sanar daku saboda ku dan samu kwanciyar hankali kudena wahalar neman sa tunda yace yaji lokacin ma da kuka bada cigiyar sa dan haka kutaya shi da addu'a dukan su babu wanda be zubda kwalla ba jin halin da mahaifin su ya koma saleem ne yayi qarfin halin tambayar sa dan Allah bawan Allah me yayi sukai mishi haka mutumin yace nima wlh bansani ba nide iya abun da aka gaya min kenan yace to waye ya aiko ka yace wani dan gidan ne shima bawane shine yasamu damar fitowa daman kuma nasan shi tunkan ya shiga gidan amatsayin bawa to shine yake sanar dani dan Allah inzo insanar daku shima kuma mahaifin nakune yace yazo ya fada asan inda yake amma ni baya ga haka bansan komai ba game da shi dan ko kamannin sama bansaniba mama ce tace Alahamdulillah Alahamdulillah hakan munji dadi sosai da jin baya nin ka mungode Allah ya saka maka da alkhairi yanzu hankalin mu zefi kwanciya dan akullin da kalar yunanin da mukeyi akan sa dan har muna tunanin ma ko ya mutu me ashe da ransa kuma in Allah ya yarda ze dawo gare mu mama bata gama rufe baki ba Azeema tayi caraf tare da miqewa tsaye tace in sha Allah mama sanin inda baba yake daidai yake da dawowar sa garemu ni da kaina zanje har cikin gidan kuma zan dawo dashi da yardar Allah dukan su zuba mata ido sukayi mutuminne yace a'a yarinya karkiyi haka kibari kar kishiga gidan nan saboda inde kika shiga to banajin kema zaki fito da lafiyar ki bayama in akasan me yakawo ki dan Allah nide shawarata agare ku itace kuci gaba da addu'a kawai saboda itace zata magan ce muku komai Allah ze kawo muku mafita amma ina ganin tunkarar cikin masarautar nan da daya daga cikin zeyi inaganin kamar zaku kuma jefa kanku cikin wani halin,
saleem yace gaskiya ne maganar ka gaskiya ce zamu ci gaba da addu'ar in Allah ya yarda kuma munsan Allah yana tare damu zai amsana mungode sosai da sosai sannan dan Allah idan kaje kagayawa wanda ya aiko ka kace mungode masa sannan yagayawa baba muna gaidashi kuma ya kwantar da hankalin sa muna cikin qoshin lafiya nama samu aiki kuma muna nan muna masa addu'a sannan kaima Allah yabika da mafificin alkhari Mutumin ya amsa da Ameen daga nan ya miqe tare da dan kallon Azeema yace jaruma ayi hakuri naga kin fusata da yawa ki kwantar da hankalin ki babu abun da ze samu mahaifinku matsalar de kawai itace da baze dawo wajen ku ta cikin sauqi saide addu'a dan kai ta daga masa kawai amma bawai tana jin zata hakura da zuwa ba kawai zata rabu dashi ne azin ta hakura din,
sallama yayi musu suka qarayi masa godiya sannan ya tafi zama sukayi gaba dayan su tsawon 'yan mintina ba wanda ya iya yin magana acikin su kowa da abun da yake saqawa,
Azeema ce ta katse shirun nasu da cewa mama yanzu kuna ganin hakan zamuyi mu zuba ido munazaman jiran dawowar sa alhalin bamusan lokacin dawowar sa ba kuma munsan inda yake nide gaskiya ina ganin gwara kawai inje din ko ya kuka gani mamace ta dan numfasa kana tace ke baki ji me yace bane mazama ya suka qare idan sun shiga bare kuma ke mace ina ganin
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment