Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk suka fito suka nufi cikin asibitin suna shiga suna qoqarin shiga bangaren da aka kwantar da Ameesha sukaji ance dadda gaba dayan su suka juyo suna kallon wanda yake kiran dadda dukan su basu sanshi ba Ammi da bossay amma ga mamakinsu sai suka ga dadda ta dan saki murmushi tace ashe kaine harkasa na tsorata
saleem ne ya qaraso inda suke yace haba dadda daga kira kuma sai tsorata sai kace a daji kike yagama fada yayin da ya yagama iso wa gurin
tare da miqawa bossay hannu suka gaisa sannan ya gaida Ammi itama fuskar ta da fara'a ta amsa masa"

baya nan yace dadda ina Ameesha sai shekaran jiya Azeema take gaya min wai kun tashi ashede zan qara ganin ku bejira amsar ta ba yaqara dorawa da cewa amma dadda lafiya naganku anan waye bashida lafiya??
dadda kamar tayi kuka tace Ameeshan ce ai bata da lafiya yau kusan satinta biyu ma akwance anan wai sai likita yadawo zasu duba min jika salon su kasheta....
Saleem yace ya salam me yasameta haka wlh bamu sani ba ai kuma nima anan nake aiki bamu taba haduwa ba tace ai tun ranar da muka kawo ta sai yau muka dawo nazo inga lafiyar tane wlh sai anbude min ita naganta yace to dadda ki kwantar da hankalin ki bari inyi wa wani dr.. magana in Allah ya yarda zezo ya bada umarni ki ganta kar kidamu kinji ceke da jin dadi ta fara washe baki tace kai gaskiya naji dadi Allah yayi maka albarka dan Allah yi sauri kaje kafada mishi ko inzo muje tare yace a'a yi zamanki bari inje yanzu zan dawo yafada yana barin wajen....
Hamdalah su Ammi suka yi tare da sauke ajiyar zuciya sunji dadin zawan wannan yaron dan ba qaramin taimaka musu yayi ba saboda basu san ta inda zasu fara cewa wai sunzo suga Ameesha bayan kuma sungaya musu ba wanda ze ganta sai gashi Allah ya kawo musu dauki.....
kallon dadda sukayi Ammi tace to dadda ai sai kizauna ko yanzu hankalin ki ya kwanta bata kula suba tasamu waje ta zauna tare da kawar da kanta sai kace sunyi mata laifi.......


الحَمْدُ ِلله الحَمْدُ ِلله الحَمْدُ ِلله الحَمْدُ ِلله الحَمْدُ ِلله
[3/12, 11:59 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER......💅
            by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

             🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                           ﷽

                 Bismillah.........✍
Episode 34-35

               ***********************

Saleem na shiga office din dr. Shettima yayi nocking daga ciki akace come in tura qofar yayi ya shiga da sallama dauke abakin shi,
Dr shettima ya amsa sannan yace au baka tafi ba kenan?
Yace eh wlh nazo fita na hadu da wata kakata yanzu haka dan Allah inba damuwa taimako zakai mana sai kuma yadan tsagaita dayin maganar dr shettima ya dan gyara zama yana fuskan tarshi sannan yace ina sauraronka fadi abun dakakeso,
Shima gyara zaman yayi sannan ya dora dacewa yanzu wacce na hadu da ita take gaya min ankawo jkkarta nan wai har takusa sati biyu amma bansan ta kamai mai abun da yak😍 damun ta ba ance de wai likita ake jira sai yadawo ze yimata aiki ko kansan da zancen dr shettima saida yadanyi jimm sannan yace eh to gasky bansan taba saide tabbas dr.. Jamil yayi min maganar rannan amma banje naganta ba gskiya kuma ansanar da wanda zeyi mata din ai zuwa jibi ze dawo yakusa dawowa ,,
Amma wane taimako kake nema kai
Saleem yace wallahi kasan ance wai bawanda ze ganta har sai bayan anyi mata aiki to yanzu wajen kwana goma kenan ba wanda yazo din daga cikin su shine sai yau kakarta ta dage wai ita sai sun kawota taga jikarta dan tana tunanin wai ankashe mata jika shiyasa aka hanata ganin ta kasan tsoho da rikice in yadage akan abu sai anbisa ahankali,,yadan tsagaita "sannan ya dora dacewa dan Allah ba wata matsala ina neman alfarma abarta ta ganta ko zataji dadi ammafa inkana ganin hakan baze haifar da wata matsala ba,,"
Dr shettima yace to bazan ce da da matsala ba kuma bazance ba matsala ba amma de zata iya ganinta sanan kuma kar tayi wani motsi daze haifar da qara suyi ahankali bari nasanar da dr jamil din sai yazo yakaiku,
Saleem yace gaskiya naji dadi godiya nake Allah yabar zumunci Allah saka da alkhairi dr shettima yace bakomai nace maka kadena yimin godiya bakaji ko dan murmushi saleem yayi yace yaza ayi kamin abu kuma inqi godiya ai bazan taba yin hakan ba,
Shikuma yace oh hakane to shikenan nikuma sai indena yi maka abu daga yanzu kaga basai ka gode min ba watakil ma saide ka zagebi kace wancan mutumin beda mutunci ko,saleem yayi saurin cewa kai kai haba yaza ayi inzageka ai ko bakamin nasan kamin abaya kaga kwa ai bana ga laifinka ba barema nasan bazaka taba yin hakan ba ai kaidin me mutun ci ne baka wulakanta mutane duk da irin girman da allah yabaka ga kudi ga mukami bakowa bane me irin matsayin ka watakil ko kallon inda nake ma baze yi ba bare har yatsaya ya ringa sauraron duk abun da nazo masa dashi ga taimakon da kakeyimin kaidin na musammune yaqara sa maganar yana fadada murmushin shi tare da kallon shi sai da yayi shiru sannan dr shettima yace idan kagama zagi nawa sai katashi ka fita kuma kar kasake dawo min office yafada yana nuna mishi qofar fita da hannu shi saleem miqewa yayi yana yar dariya sannan yace tuba nake ayi hakuri yanzu de dan Allah akirashi din inje nasan suna can suna ta jirana,,
Dr shettima yace ai nafasa sai kaje kasan yanda zakayi da ita da sauri saleem ya tsugunna a gabansa yace dan Allah kayi hakuri bazan sake fadar komai ba nayi shiru wlh naje nacewa matar nan baza tasamu ganinta ai nashiga uku kataimaka dan Allah nanma de qin amincewa yayi saida qyar saleem ya shawo kansa sannan yadau waya agabansa ya kirashi suka gama magana sannan saleem ya miqe yanzu de bece ya gode ba gudun qara samun matsala sai yamiqe yace mishi yatafi,,
"kai kawai yadaga mishi be kalleshi ba"
gani haka yasa saleem nufar hanyar fita saida yaje dede ze fita dan har ya bude qofa sai kuma yajuyo yana kallonsa yaga shima shi yake kallo"
  Sannan ya dan daga murya yace nagode nagode nagode  daman ku masu mutunci da kyawawan dabi'u ba kwaso ana yabanku sai kuce wai anzage ku to wallahi ba zagibane mutuncin naka ne yasa ake fada wallah kana da kirki sosai da sosai kaifa na dabanne acikin dari da kyar za asamu biyar irinka kuma wallahi .....
Beqara saba saka makon ganin shi da yayi yataso ze zo wajensa aikwa wuri yasaki qofara ya fuce duk dahaka yana tafiya yancewa ina qara godiya fa daga nan zan tafi gida sai gobe yana tafiya yana dariya ,,,
Dr.shettima da yayi sauri dan ya cimmasa amma besamu dama ba kawai kwafa yayi yakoma yace ai zaka dawo kasame nine dan kaga ina maka dariya shiyasa ka fara rainani hmmm zakasan nace banaso ka qarayi ka  tafi katafi kama maidani abokin wasan ka hakade yayita surutun shi daga qarshe yakoma kan kujerar sa yazauna"....

Saleem yana dariya ya qarasa gurin su dadda,    dadda na ganinshi ta miqe tace yawwa yaron kirki muje ko naga kana ta Dari ya ko ance maka taji sauqi ne kai ya girgiza mata yace a'a dadda ande ce zaku iya shiga dukan kuma amma ba aso ayi motsi me qarfi saboda gudun matsala amma yanzu de wanda ze shiga daku zezo mudan jira shi yana nan zuwa godiya dadda tayi mishi bossay ma yaji dadin jin dukan su zasu shiga dan shima daman yayi missing dinta yana so yaganta yaga halin da take cike Ammi ta kalli dadda tace to dadda yanzu hankalinki ya kwanata de ko dadda tace wallahi be kwanta ba harsai na ganta da idon na tabbatar kuma bata mutuba bossay yace waike baza kidena kiramana mutuwa bane to ita bazata mutuba saide in kece zaki mutun,    "dadda najin haka tayo kansa tace wlh saide kai ka mutu tana fada tana qoqarin kai hannu kanshi Ammi tayi saurin riqeta tace haba dan Allah wai anan dinma baza ku saurara manaba tunda muka koma gida kunqi saituwa fadan yau daban na gobe daban yanzu kuma munbar gidan ma baza kuyi hakuri ba ku ko halin da yarinyar nan take ciki be dameku ba za hau yimana fada a asibitin taqarasa maganar tare da sakin dadda sannan tace to kuyi in akazo aka koramu gida kinga sai hankalinki ya kwanta kinzo baki ganta ba ta juya kan bossay tace kaima kuma wallahi na qara jin bakinka awajen nan sai na saba maka tunda ai duk kai kake jawo fadan kasan halinta ba hakura zatayi ba ina lafiya kura bare ta 'ya'yanta baka kulata bama tanayi ina kuma ga ka tsokanota ta qarasa magana cike da jin haushin abun da suke shirin yi
Bossay ne yace kiyi hakuri Ammi ai duk itace da laifi meyasa kullum bakinta baze fadi alkhairi ba saide kiran mutuwa"*
Dadda itama da takaici ya gama cikata tace bazan fada din ba kuma wlh inbaka fita daga idona ba sai munhaura gadon mahaukaciya  da kai saide akoreni daga gidan tunda har anfara yimin fada yanzu kamar ni kamar ni da girmana Amina takeyiwa fada ba komai ni najawa kaina ni daga yanzu ma kubarni anan kuyi tafiyar ku bazan sake binku ba bare har wannan ja irin yaron yaringa gaya min magana son ransa taqara sa fada tana matse yar kwalla,
Ammi ce ta ruqota tace kai dan Allah dadda nifa ba fada nake miki ba amma tunda kince haka kiyi hakuri bazan sake ba,
Saleem de na tsaye yana kallon ikon Allah be tanka musu ba ",
Bossay ya bude baki zaiyi magana kenan saiga dr jamil ya qaraso gurin su da sallama tare da mikawa saleem hannu sukayi musabaha sanna ya miqawa bossay shima suka gaisa yagaida Ammi da dadda,  Ammi ce kawai ta amsa amma banda dadda da har yanzu bata dawo daidai ba taki sakin ranta
bayan nan dr jamil yace musu bismillah su shiga su ganta sai lokacin dadda ta dan saki ranta, gaba yayi suka bishi abaya har bakin qofar da take a kwance ahankali ya shiga tura qafar tare da saka qafa cikin dakin saida yagama shiga sannan suma suka shigo gaba dayan su mayar da qofar yayi ya rufe sannan ya qara nufar wata qofa dake ciki inda ze sadasu da ainahin inda take kwance suna shiga suka ganta kwance an daura mata wasu na'u'ro'ri  da suke taimaka mata wajen kare duk abun da zesa ta farka kuma kullum ana zuwa aduba lafiyar ta,
Dadda naganin ta ta fashe da kuka saide tasa hannu ta toshe ba ajin sautin sosai ganin haka yasa dadda kamata ta fito da ita waje suma basu dade ba dr.. yace musu suzo su fita suma saleem ne yafara juyawa cike da tausayin yarinyar ya tausaya mata matuqa ganin halin da take ciki yana so yaji me yasame ta amma ba halin yin hakan yaji daga baya idan komai ya daidai ta
Dr. Jamil ne yasake yiwa bossay magana da yatafi duniyar tunani firgit yayi yadawo cikin hankalinsa da ya bar gangar jikinsa azahirance inka kalleshi zakace Ameesha yake kallo amma a badene abun ba haka yakeba ,
Cike da rashin kwarin jiki yajuyo yabiyo bayan dr. jamil suka fito tare suna fitowa Ammi tacewa bossay su wuce gida kawai haka kuwa sukayi basu wani bata lokaci ba sukayiwa dr jamil godiya tare da yi masa sallama tare suka fito da saleem inde shima yayi nasa wajen yakama hanyar fita bossay yace yazo suje suyi dropping dinshi amma sai yace mishi a'a ya gode ba yanda suka iya dashi dole suka rabu dashi yatafi suma suka shiga mota bossay yaja suka fita daga hospital har zuwa lokacin dadda bata dena kuka ba tun Ammi na rarrashinta har tagaji tadena shikam bossay daman ko kallom inda take beyi ba bare ya kulata ahaka har suka qarasa gida suna qarasawa lokacin ana kiran sallar mfagrib bossay nayin parking suka fito tare suka shiga suna shiga kowa yakama gabansa amma banda dadda da tayi zamanta a falo tana cigaba da kukanta ba jimawa bossay yafito ya dauro alwallarsa ze wuce masallaci ta gabanta yazo ya wuce be kulata ba yayi ficewar sa yana fita ba dadewa...
faruq  shima yafito da shirin wucewa masallacin sai yaci karo da dadda tana kuka da sauri ya qarasa kusa da ita tare da ruqo hannun ta yana cewa ya salam dadda me yasameki kike kuka ko ance muku  ta mutune dadda ta jinjina masa kai alamar a'a yace to meyasaki kuka nanma shirun tayi mishi bata bashi amsaba yace dan Allah dadda ki gayamin wlh duk kinsa hankalina yatashi,.......
Shikuma hakan nan jininsu ya hadu da dadda tunda tazo gidan bazaka taba jin kansu ba..
ganin da gaske ya shiga damuwa yasata dan tsagaita kukan nata sannan tace mishi babana wlh ba mutuwa tayi ba amma wasu wayoyi da suka saka mata kamar wayar wutar nefa ze iya sawa ta mutu din kaga kwa yanda sukayi mata duk an rurrufeta sai kace ba yar musulmai ba to ko kafirwa akayi wa haka ai ba a qaunar su saboda abun ba imani aciki wlh mutanen nan basu da tausayi da imani ko kadan...
Saura kadan faruq ya tuntsire da dariya amma sai yayi saurin riqe abarsa gudun qara taso da wata matsalar tunda ya fahimci yau da rigima take ji gwara yabita ahankali su rabu lafiya
Saida ya dan sassaita muryar shi yanda bazata vane dariya yakeson yi mata ba"
  "Sannan yace haba dadda da adan wannan abunne kika bi kika tayar da hankalinki harda zubar min da hawayen ki me tsada hawayen kifa daraja ce dasu bawani abu da ze sameta kinga mafa gobe jibi ze dawo daga gobe fa sai jibi kinga jibi sai mu koma asibitin da sassafe ayi komai agabanki idan doctor din yazo kinga tunda kina wajen bazasuyi wasa ba bare har susa ta mutu kikayi hakurin kwana goma ma sai kwana biyune baza ki iyaba nida kaina jibi zankaiki asibitin muna idar da sallar asuba sai mutafi ko ya kikace yafada tare da daga mata gira dan murmushi tasaki wanda be qarasa zuciba iyakacinsa kan labba sannan ta daga masa kai alamar hakan yayi shima murmushin yayi mata sannan yace yauwa ko kefa dan Allah ki kwantar da hankalin ki yanzu kije kiyi sallah nima zanje inyi imadawo wa zanzo muyi hira me dadi nasamo mana labari me dadi.
    "yanzu kwa murmushin da ta saki har cikin ranta tayi shi sannan tace to shikenan babana sai ka dawodin nima yanzu zanje inyi inajiran da wowarka tafada tare da miqewa daga wajen"
Shima miqewa yayi yace to shikenan yanzu kwa zanje nadawo kinji Sweet hart dina tace kai kasani ni nace bana son irin wadannan sunayen dakake fada mun kullum na yau daban na gobe daban to ni banaso  tafada tana qarasa barin wajen..
Be kulata ba Saida yagama dariyarsa sannan ya wuce masallaci lokacin har an tayar da sallah ma.........

          """"""""""""""""""""""'"""""""""

Saleem nakomawa gida cike da damuwa ya sanar da mama da Azeema aikwa ba qaramin tashin hankali Azeema ta shiga ba dan harda kuka shabe shabe sannan ta hada Saleem da Allah gobe zata bishi taganta da farko qin yarda yayi saida yaga halin da ta shiga kuma sai yace to shikenan ba matsala Allah ya kaimu goben amma ta tashi da wuri ta shirya kara ta bata masa lokaci tace to ta yarda...

Washe gari kwa kamar yanda yace mata hakan akayi tun wajen bakwai tagama komai takwas saura kwata suka yiwa mama sallama suka wuce
mintina kadan sunkaisu da suka shiga sai yace da ita ta zauna anan tajirashi yanzu ze dawo tace to sannan shikuma yayi gaba be dawo wajen ba saidata jirashi almost 20 minutes sannan yadawo yace ta ta taso yana gaba tana binshi abaya har suka qaraso bakin wani office kwankwasawa yayi daga ciki akace come in shiga sukayi tare da sallama amma saleem ne yayi kawai banda Azeema dr. Shettima najin muryar shice sai ya hade rai tare da sunkuyar da kansa dan baze kalli inda yake bama sannan yayi shiru yayi masa banza kamar ma besan da shigowar saba
"saleem ganin haka yasashi sakin qayataccen murmushi dan shi sai yanzu ma yatuna da abun da yaayi mishi jiya qarasawa yayi yazauna yana shirin magana kenan yaji yace fitar min daga office bance kar nasake ganin qafarka acikin nanba
Saleem yace ai bazan iya hakan ba daman zuwa nayi na baka hakuri,
Kayi hakuri dan Allah kaji banza yayi da shi tare da cigaba da aikin gabansa
ganin hakan yasa saleem juyawa yakalli Azeema da ke tsaye tana sauraron su da hannu yayi mata nuni da kujerar gabansa yace ki zauna mana kinyi tsaye ko baki gajiba turo baki tayi tare da cewa haba dan Allah yaya tunda mukazo munkusa awa daya da zuwa wajen nan amma kaki kaini inganta sai jamin rai kake ta qarasa maganar kamar zata saki kuka saboda tagaji da jiran shi ita a tunanin tama da suka taho ta dauka zata ganta adakin da aka kwantar da Ameesha amma sai ta ga akasin haka...
"""Dr. Shettima ya tsaya da abun da yakeyi sakamakon jin muryar mace kuma kamar yasanta hakan yasashi dagowa dan ganin ko wacece saleem ya shigo masa da ita har cikin office batare da izinin shiba dagowar sa ke da wuya idonun sa suka sauka akanta itama ayanda take ta bata fuska tare da turo bakin da tayi bayan ta qarasa maganar...
cike da takaici ta daga idanunta aikwa karaf idanun su suka sauka akan nashi da shina yaka binta da kallon mamaki yana gasgata abun da gaske ne kokwa mafarki yake ko kuma gizaune......
Itama anata bangaren hakan ce take faruwa domin tayi suman tsaye takasa ko motsi sai kallon shi take...........✍🏿


*kunjini shiru kwana biyu na posting ko wllah matsalar wuta muke fama da ita shiyasa kukaji shiru Amma in Allah ya yarda yanzu tazama nml zakuji ni ko da yaushe in kuma bata tsaya ba to saide kuyi hakuri posting ba kullum ba saboda rashin caji*
[3/13, 8:34 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER......💅
            by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

             🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                           ﷽

                 Bismillah.........✍
Episode 36-37

              ***********************

kamar Wanda aka tsikara haka ya mike tsaye yana cigaba da kallonta,
Saleem miqewa yayi yana binsu da kallo saboda ganin irin kallon da sukewa junan su alamu kamar sunsan juna kasa jurewa yayi sai yaqada kallon dr. Shettima sannan yace sir kasanta ne jin maganar saleem tasashi dawowa daga cikin hayyacin shi sai kuma ya basar yace a'a bantaba ganin ta ba yau nafara ganinta kawajde nayi mamaki me da naganka da ita a ina ka tsintota dan naga kamar batada tarbiya bata iya gaida mutane ba ko sallama ma batayi ba shiyasa kaga natashi da zanmata magana sai kuma kamin yaqarasa maganar tare da komawa mazaunin sa ya zauna " sai lokaci saleem  yace ayya sorry she is my blood sister mu biyu ne agidan mu daga ni sai ita daman kawota nayi zataga qawarta da aka kwantar wacce jiya nazo na roqeka muka je muka ganta shine ita ma takeso taje ta ganta shiyasa na fara kawota kagan ta kugaisa kafin mushiga dan naga dr. Jamil din kamar  be shigo ba har yanzu duk wannan jawabin da saleem yakeyi besan yanayi ba yatafi tunanin to kode wacce yake ta so ya gani ce tun ranar da suka fara haduwa dasu gaban shi yaji yafadi yana addu'ar Allah yasade ba ita bace to inba ita bace ai tare yataba ganinsu to ita tana ina kenan bashida me bashi amsa saboda shide baze iya tambayar saleem ba dan besan tayanda zefara ba wacce kuma yataba ganin su tare itama yayi alkawarin tunda qanwar saleem ce baze taba kulataba bare ya nuna wani abun ya taba shiga tsakanin su agaban saleem ba,
       "Saleem yadan buga table tare da cewa sir lafiya kuwa naga kayi shiru me kake tunanni ina ta maganna baka jini ba hankalin sa ya tattaro gaba daya sannan yace a'a bakomai inajinka ai kawai haushinka nake jine tunjiya yayi hakane  dan ya mantar dashi  mganar aikam saleem ya bar maganar be qara cewa komai ba akai sai kawai yajuya gurin Azeema da itama ganin yanda wannan mutumin da yaci mata mutunci kwanakin baya tagane shi kuma tasan shima yagane ta amma da yake shi dangaba da wes ne ya wani basar harda cewa wai besan ta ba yauma yafara ganin ta tunda hakane zata nuna mishi itama ba kanwar lasa bace dan haka sai tacire duk wata damuwa a fuskar ta ta aro jarumta ta aza asaman fuskarta har da dan sakin murmushi,
kafin saleem yayi mata magana ta rigashi da cewa oh yaya mutumin da kake ban labari  yana da mutunci ko tafada tana kallon saleem kai yadaga mata tare dacewa eh wlh shine ,
kai ta girgiza tare da maida kallonta kansa tace sannufa yaya me mutunci barka da safiya da fatan ka tashi lafiya tafada ta qurawa fuskar sa ido da taga yadan hade rai gudun kar saleem ya fahimci wani abu yasashi saurin sakin fuskar shi tare da cewa lafiya lau ashe qanwar muce ai na dauka badurwar sace ince beyi dace ba yayi subutar baki sai kuma yayi saurin cewa da yayi dacen budurwa dan kallo daya nayi miki nagane cewa kina da hankali da sanin yakamata da girmama nagaba dake ga kyau saida yagama fada sannan ya balla mata harara ta gefen ido sarai kuma ta ganshi tasan duk abun da yake fada mata yana nufin opposite ne da ita ma'ana duk abun da yace tana dashi a fili to a zuciyarsa bata dashi dan haka kuwa taji ba dadi amma sai ta dake bata qara tanka masa ba,
Saleem sai faman sakin murmushi yakeyi yaji ana yabon qanwarsa dan haka sai yace kizauna anan tare dashi yana da kirki sosai bari inje induba ko ya qaraso yaqarasa maganar tare da nufar qofar fita yana qarasa wa kuma bejira cewar ko wanne su ba ya fuce abunsa yana fita kwa kamar jira suke atare sukayi tsaki tare da bankawa junan su harara jin tsaki da tayine yasa dr.shettima fusata ya taso da hanzarinsa gadan gadan yayo kanta yana cewa ni kikeyiwa tsaki ni sa'an wasankine yana magana yana tunkaro ta ganin shi cikin wannan yanayin yasata dan tsorata dashi sai tafara ja da baya tana baya yana binta harta kai jikin qofa tana qoqarin juyawa ta bude qofar kafin  takai nata hannun ya rigata kai nashi hannun ganin haka yasa ta juyo a fusace itama tace malam wai meye haka nifa bana son iskanci wannan ai salon iskancine
da wayon taba jiki ta qarasa fadar haka tana maka mishi harara,
jin hakan yasashi gyargyada kai kawai yayi be tanka mata ba tare da sakin wani shu'umin murmushin gefen baki sannan yasa hannun sa na dama ya tokare da jikin bangon haka yayiwa dayan hannun ma sai yazamana tana tsakiya wuqi wuqi tafara yi da ido tare da hadiye wani yawu me kauri da ya tsaya nata a makogaro"
tunda ga qasa yafara binta da kallo har zuwa saman ta saida yaqare mata kallo tsaf sannan yace nine dan iska ko ranar nan kinfada na rabu dake shine yanzu ma zaki qara fadamin to yanzu bazan kyaleki ba ranar ni nakai kanai dana kulaku to yanzu fa dole indau mataki tunda ke kikazo har inda nake har cikin office dina sannan kika min tsaki abun da na tsani inji ko babba yayi min bare wacce na girma qanwar qanwa ta saboda baki da kunya ko to

Please Login or Register in order to submit comment