Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka daukota kafito da ita inajiranka awaje bejira amsar  sa saba ya juya yafice saboda bayaso bossay yagane halin da yake ciki saide abun da besaniba ko a iya muryar sa zaka gane akwai matsala

yana fitowa sukayi kici bus da sameer a wajen hanyar fita  bai kalli inda yake ba yace gaba da tafiyar sa maganar sam ce ta dakatar dashi daga saurin da yake yi sameer ne ya kira sunan sa be jira ya amsaba ya dora dacewa kai yanzu ka zabi mace akaina ko to ina so kasani abotar mu bazata hanani yin abun danaga dama ba kuma idan bakayi ahankali ba zan iya hadawa dakai nagaya maka kuma kasan halina banason katsalandan acikin lamura na karkayi abun da zesaka danasani kafita daga harkar yarinyar nan naga kanka na rawa akanta da yawa tun ranar da nadawo muka fara samun matsaka dakai kuma duk adalilin ta yakamata kashiga hanklain ka tunkan lokaci be qure maka yaqara fada yana jaddada masa maganar da hannu,
duk atunani sa shettima ze bashi hakuri yace ya janye amma ga mamakin sa sai yaga yasaki murmushin gefen baki tare da shafar gemun fuskar shi,
sannan yace bismillah duk abun da kaga na cancanta da kayi min kayi min shi ka isa ai harkayi yawama  wlh kaban mamaki sosai ai duk abun da yafaru kai kajama abotar mu bata da amfani bakadauke ta da amfani ba dan haka nima dana dauketa da amfanin yanzu na ajiye kowa yayi rayuwasa inga hakan sai yafi da shiga harkar yarinya yanzu ma nafara inde akan aikin lada ne da sanin darajar dan adam yanzu nafara kuma bazan dena ba saide hakan yazama sanadin rabuwar tama rabuwar mu kuma ta har abada inde bazaka canza ba nikuma bazan canza ra ayina ba nima yana kaiwa nan ya qara gaba yana mishi magana amma be sauraresa ba

bossay da yatsaya a dakin yaqi fitowa yana tunanin me yake faruwa dazece ya dauko ta ganin bashi da me bashi kuma bayan da ya iya tunda akace yayi hakan  illa yabi umarnin da yabasa duk da yana buqatar qarin bayani amma a halin yanzude babu wannan lokacin ,

ciccibota yayi yafito da ita yana gama fitowa waje sukayi kicibus da sameer gaban shi yaji yafadi ganin yanda ya watsa masa wani mugun kallo me cike da fassarori be tanka masa ba dan ya lura shimade a kwai matsala watakil sun samu matsala a tsakanin su shiyasa yaga fuskokin kowannen su babu annuri cigaba yayi da tafiya har yaqaraso inda shettima yake a tsaye abakin motar sa ya bude masa baya yace sakata anan beyi musuba yasaka ta a back seat tare da rufewa sanna yamaida hankalin sa ga shettima yana jiran qarin bayani shettima ganin irin kallon da yake mishi yasan me yake nufi dan haka be jira ya tambaye sa ba yace nasan kanajiran bayani ko zankaita wani asibitin ne amma  yanzu de bani da lokaci zamu tattauna awaya yanzu kawai kaje gida zan kiraka zuwa dare amma kar kasanar da iyayen ta halin da ake ciki kawai kace ka barota lafiya sannan kuma duk yanda zakai kayi kar kabari suzo gobe idan  sunce zasu kahana su hakan kagane yace masa eh in sha Allah zeyi kokarin yin haka Allah ya tsare ku yakai ku lafiya Ameen ya amsa masa da ita daga haka  yabude motar sa ya shiga sannan sukayi sallama yaja motar sa ya fita daga asibitin a guje,

Sai da bossay yaga fitar su sannan shima ya nufi tashi motar ranshi taf cike da tambayoyi kala kala saide bashida wanda zeyiwa,

Yazo daidai ze gifta ta wajen da sameer yake a tsaye ya hade hannu wasa akan kirjinsa yana binsu da kallo daya bayan daya ze wuce kenan yaji yace kai dakatawa yayi da tafiyar tare da juyowa sannan yace na'am saida yagama binsa da kallon banza sannan ya bude bakinsa a yagune yafara yi mishi magana meye alakarka da waccen yarinyar yace mishi qanwata ce yace ok ina so kasani duk halin da kuka tsinci ta nine sila  domin ta shigo min rayuwa kuma bazan rabu da itaba dole zan dauki kwakkwaran hukunci akanta sai tayi danasanin sanina arayuwar ta duk wanda yayi sanadin shiga ta damuwa ko yanemi yadaga min hankali to dole shima hankalin sa ya tashi kuma baze taba kwanciwa ba yagama farin ciki a rayuwar sa kuma bana tsoron uban kowa kaje kafada agida ni SAMEER ABDALLAH SAMEER gaba sarauta baya saruta nace ajirayi hukuncin da zan dauka akanta in kuma akwai wanda ya isa ya hanani to yazo yasameni agidan mu inafatande ai kasan gidan sarki ko to inaciki duka ahalina suna ciki azo ataddani yafada cike da gadara,

jin batunsa ba qaramin tsoratar da bossay yayi ba ya shiga tashin hankali matuqa dan daga ganin sa yasan ze iya aikata abun da yace din zema iyayin fiye da haka kallo daya yayi masa yagne bashida imani bashi da tausayi ko kadan gashi kuma yaji daga inda yafito kuma daman ba wanda besan masarauta ba saboda rashin adalcin da akeyi aciki shiyasa ba wanda yake rabar su dan dakatawa yayi da tunanin da yake,

sannan yace naji duk bayanin ka amma inason sanin abun da tayi maka idan ka cutar da ita batare da tayi maka komai ba to kasani kaima Allah baze barka ba domin wannan yarinya kamar marainiya take hasalima bata san kowa nata ba bata san ita kanta wacece ba bata da kowa bata da komai  abun ka tausayawa rayuwar tane ba wai kadau alwashin cutar da ita ba akan abun da be taka kara ya karya ba duk da bansan me tayi maka ba amma ina da yakinin cewa bawani babban kuskure ta aikata maka ba da har zesa kadauki wani qudiri akanta ba har kana ikirarin za kahana ta farin ciki a rayuwar ta hakan da zakai baqaramin kuskure bane,

Sannan kuma ni da da ka ganmu tare ni kaina bansan taba bansan ita wacece ba bani da wata alaka da ita kawai taimakon ta nayi kaima yakamata ka ji kanta ka janye wannan qudirin akanta kayi hakuri da abun da tayi maka koma menene ubagijin mu ma muna masa laifi kuma ya yafe mana bare kuma dan adam yakamata ka duba maraicin ta ka tausaya mata itadin ba yar gidan uban kowa bace kamar yanda kake tunani bekamata ka zuba makaman yakinka akan yar ta tsitsiyar yarinya kamar wannan ba marar gata inkai hakan duk wanda yaji ma dariya zeyi maka wlh karasa wa zakasa rayuwar ta salwan ta sai mace macen ma yarinya yarinyar marar gata nide shawarar da zan baka itace kaje ka qara yin tunanin akai nasan bamu da halin da zamuyi jayayya dakai koda munkai qarar ka bamu da hujja saboda zaka iyayin amfani da mulkin ka da kudin ka wajen kaci nasara daga qarshema abun yazo ya juye damu aciki nasan halin masu kudi marar sa tausayi ba abun da bazaka ku iyaba akan burinku ya cika ammafa kayi hakuri idan magan ganuna sun bata maka rai banyi dan haka nafada maka gaskiya ne kawai kuma ina guje maka daukan alhakin baiwar Allah da bataji ba bata gani ba yakamata kacanza tunani kadena daukar kanka da yawa kaima mutum ne kamar kowa duk daya muke agurin Allah babu wanda yafi wani sai me tsronsa da yin abun da yace kudi ko kyauwu ko mulki takama dakai babu wanda zekaika aljanna sai ayyukan ka suna zasukai ka alajnnan wadannan abubuwan su duk a duniya zaka tafi kabarsu yakamata kaduba maganata na barka lafiya yarinya kuma gata nan agunku kuyi duk yanda zakuyi da ita Allah yana tare da ita kuma ze kareta aduk inda take yana kaiwa nan yajuya yayi tafiyar sa ko waogensa be qara yiba har yaqarasa gurin motar sa yabude ya shiga tare da janta yabar wajen zuwa bakin gate aka bude masa yafice daga asibitin zuciyar sa na mishi quna arayuwar sa baya son tashin hankali ko fada yafison zaman lafiya shiyasa yayi masa haka yasan inde ba dusa bace acikin zuciyar mutum duk wanda aka yiwa wannan maganar dole ya hakura ya sauke makaman sa yana tafiya sai faman tsaki yake ja duk wannan bayahuden yabi ya bata masa rai dan shi a tunanin sa wani yarenne can daban dan bemishi kama da hausawa ba amma de yaga alamar musulmi ne kawai iya shege ne irin nasa da girman kan tsiya yasashi qin amsa sallamar sa dazu gashi kuma yaji daga gidan da yafito shiyasa yaji ya qara tsanar sa,
sai yanzu kuma yaji ma baze iya hakura ba kamar yanda yagaya masa gata nan suyi mata duk abun da suka ga dama ina hakan bazata taba faruwa ba matuqar ina numfashi a doran duniyar nan yafada da qarfi tareda dukan sitiyarin motar, sai yaji duk hashin kansa yakamasa da be nuna masa bacin ransa ba duk dashi name son hakan bane kuma yama tsoron abun da kanje yadawo azo ganin neman gira arasa ido,
yana tunani Ameesha sai ta kuma bashi tausayi fiye da yanda yake tausayin ta da baiwar Allah itade ahaka rayuwar ta tazo daga wannan sai wancan sai za amagance wannan matsalar sai kuma wata taso yanzu suna murna ta dan samu sauqi shikuma ze bullo da tashi matsalar to Allah ya fishi duk muguntar sa ta qare akansa bade kan Ameesha ba yanzu dole sai ya qarfafa kula da ita saide ta kasance kullum suna tare daga zuwa gobe in suka hadu baze qara bari tayi nesa dashi ba har Allah Allah yake gobe tayi yaje yadau kota saide yayi hakuri amma baze iya barma shettima itaba a hannun sa duk da yaga ba halinsu daya da sameer ba amma duk dahaka ze karbota shi ze nema mata magani sa inda za a kula da ita, kuma ze zauna da ita duk runtsi duk wuya yana tare da ita ze bata kulawa koda ze rasa ransa asanadin hakan saide yahada dashi a hukuncin da zemata yayi musu tare,

Abangare oga sam kwa tunda yafara yimishi magana akan yarinyar tunanin sa ya tsaya cak shi ba magan ganun da yafada masa ne sukayi tasiri a zuciyar sa ba kodaya beji zedena abun da yake ba hasalima haushi suka bashi danji yake kamar ya shaqoshi lokacin da yake saide kuma maganar da ta tsaya masa arai itace tahana sa daukan mataki akan maganganun da yagaya masa dan yana ganin bekai matsaya da ze tsaya agaban sa yana gaya masa magana irin haka ba kuma ya rabu dashi,

jin ance marainiya ce tasa jikin sa yin la'asar ashe duk rashin mutuncin sa yana tausayin marayu hakannan yake tausayin su hasalima yana da gidan marayu da yabude yana yiwa kowa wulakan ci ya taka wanda yaso amma in akace mutum maraya ne to ze daga masa qafa akan duk abun da ze yimasa musamman da yaji yace bata da kowa bata san kowa nata ba sai yaji ta dan bashi tausayi amma fa kadan tausayin bawani can me yawa ba rasa tunanin dazeyi ya shiga yi shin dame zaiji da abun da yafaru tsakanin sa da abokin sa zaiji ko da wannan yaron da yazo shima yagaya masa magana san ransa yatafi ko da kin kula da yayi da yarinyar nan yanzu kuma besan ina shettima ze kaita ba kar yaje kafin suje yarinyar ta mutu yazama shine silar rasa ran marainiya gashi arashin sani ya kori abokin sa abun da betaba yi ba arayuwar sa yau shine yakama sa fargaba ya shigayi lokaci guda zufa ta tsatstsafo masa shin yanzu ta ina ze fara warware abun da ya kulla dagske fa kansa ya daure yarasa mafita mutanen dake wucewa kowa sai kallon sa yake ganin ya dade agurin a tsaya gashi ya cije baki kowa saide ya wuce saboda basu da kwarin gwiwar tunkarar sa danji abun da ya tsaida shi awajen in sukayi haka tamkar sunyi mishi shishshigine kuma yin haka zai iya sawa ma akori mutum daga aiki gaba daya dan haka kowa yaja bakinshi yayi shiru tare da qarawa motar sa mai ya wuce yabarsa agurin,

Saida yadauki lokaci me tsawo awajen kuma a tsaye batare da ya motsa ko hannun saba drivern sa da tundazu yana daga dan nesa dashi duk da dare ne amma saboda fitilun da suke a zagaye da gurin yasa ba abun da baza ka gani ko allura kajefar saika ga abarka domin gurin kamar rana haka yake
tunda yafito yagansa ya zatama tafiya zasuyi kuma sai yaga ya tsaya be qaraso ba yanaso yazo yaji meye ko tafiya zasuyi amma yana fargabar masifarsa kasa jurewa yayi qarfin hali yanufo inda yake gabansa na dukan uku uku yaqarso inda yake kansa aqasa yace 'yallabai tafiya zamuyine jin maganar sa ce ta dawo dashi daga tunanin da yafada be bashi amasa ba kawai sai yayi gaba yabarsa agun da sauri yabi bayansa har ya wuceshi ma yaje ya bude masa qofa yana zuwa ya shiga shima ya zagaya ya bude driver seat yazauna tare da yiwa motar key suka juya gate man yabude musu yadannan hancin motar suka fita tare da hawakan titi suka fara tafiya tunda suka fara tafiya kawai ya kwantar da kansa akan hannun kujera tare da lumshe idon sa be bude ba har said da yaji motar ta tsaya sannan ya bude su a hankali yasauke su akan driver da ya bude masa kofa yana jiran da fito warsa ahankali ya zuro zara zaran qafafunsa yasauke su qasa da kyar ya iya miqewa jikinsa duk ba dadi be nufi bangaren fulani ba yau sai yanufi bangaren dayar kakar sa tawajen uwa wacce ake cewa maman 'yan biyu ita kuma amfanin ta kenan idan anbata masa rai ko kuma yana neman mafita ya rasa sai yaje ta warware masa dan haka yanzuma ya nufi bangaren ta dan ta magance mishi da kyar yake jan qafarsa har yaqara sa bejira anbashi izinin shiga ba kawai yasaka kai ya shiga ciki lokacin da ya shiga babu kowa a falon sai kawai yanufi dakinta kansa tsaye yana shiga yatarar da ita suna hira da papa tsayawa yayi abakin qofar jin anshigo ne yasasu duban inda suke tana ganin shi ta washe baki tace ja'iri qaraso mana ka tsaya anan tun da kazo sau daya muka gaisa baka sake waiwayen inda nake ba ko sai yanzu yanzu made ince ko batan hanya kayi be papa yace wane irin batan hanya yaro yazo zai gaidake kuma kina wane cemishi yayi batan kai sai kace qaramin yaro qarasa shigowa yayi fuskar sa dam ahade babu walwala zama yayi kawai be tanka musuba tare da kwantar dakan sa akan cinyarta sai kuma yayi shiru papa ne ya kalle sa yace me sunan baba meya faru ne nagan ka haka shiru ba amsa maman 'yan biyu ce ta dora da cewa ainasan daman ba lafiya ba tunda naganshi haka ni daman nasan bahaka nan akazo wajena ba da abun da akenema dan haka papa kabamu waje zamu tattauna bamuso kowa yaji nasan sirrine papa yace aikwa saide in baza ayi ba amma inan zama daram yaqara gyara zama harda dan kishingida kallon sa tayi tace to kwa duk min sa idon mutum baze jiba kagama zaman kafita baka ji mayi anjima ko jikalle tafada tana kallon tana shafa gashin kansa suna dan hirarsu tun yanajin su sama sama har yadena bacci yayi awan gaba dashi.........✍
[4/6, 9:15 AM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode 76-77-78

         """"""""""""""""""""""""""""""""""

ahaka sukaci gaba hirar su basu tasheshiba har saida shadaya ta wuce sannan papa yace mata ta tashe shi inba sotake ya kwana anan ba murmushi tayi sannan tace to inya kwanan ma meye aciki yace qafarki ce zatai tsami ai kato dashi yakwanta miki akan cinya ko zafima bakyaji sai kintashi kinji qafar ta riqe maga tayanda zakiyi tafiya kaide kaiwa kace kana kishi da sabon mijin to kwalelenka de murmushi kawai yayi be kara ce mata komai ba yashiga tashin sameer da hannu dan bude idon sa yayi ahankali yasauke su akan papa qara murza idon sa yayi dan shi yama manta  a inda yake a kwance papa ne yace sai katashi haka ai kar ka karya ta  kawani tsare mutane da ido ko anan kake shirin kwana ne lumshe idon sa yaqarayi sannan ya budesu da qyar ya yunqura ya iya tashi zaune shafa fuskarshi tayi sannan tace ka shiga bandaki ka wanko fuskarka da baki zanje insamoma abun da zakaci nasan kanajin yunwa ga cikin kanan yana kukan yunwa tafada tana dan shafo cikin nasa sannan ta sauka aikwa tana dira qafar tata taji tayi tsamin amma sai ta dake kawai saboda kar papa yagani yayi mata dariya tana fita shima yatashi yashiga yayi abun da tace masa din sannan ya fito zuwa lokacin papa har yafara gyangyadi bayan fitowar sa itama tashigo dakin fuskar ta dauke da murmushi tace yau yaron kirki zo muje idan kaci sai muyi maganar saboda yan sa ido tafada tare da ruqo hannun sa sukafito shikwa papa bema san sunayi ba dan bacci me nauyi ne yadebe shi kamar yanda tace bayan yagama cin abin cin ne yafara yimata bayanin abun da yafaru tundaga A har Z ya kwashe komai yasanr da ita dan jinjina kai tayi sanna tace kaima kayi kuskure ai yarinya qarama ka tsaya kana biyewa shirmen ta a kullum ina gaya maka ka ringa kai zuciyar ma nesa akan wasu abubuwan amma ba kaji yanzu haka ka zaba gashinan ai zaka rasa abokin ka dannasan kaf duniyar nan baka da aboki irinsa kuma baza ka taba samu ba yaro me hankali da gaskiya da riqon amana duk halayen ka yana iya jurewa ku zauna lafiya amma gashi yanzu ka kaishi qarshe kuma kazo kana regretting dan bata fuska yayi yace maamaa nifa ba fada nace kimin ba kawai kifadan yanda zan shawo kansa har insan inda suke banason ta mutu ta sanadin qin dubatan da nayi marainiya ce kawai ni solution zaki ban kallon sa tayi tadan saki murmushi irin nasu na manya kana tace hmmm babana kenan kaide baka bin komai ahankali to yanzu masalaha ta farko shine ka kirashi awaya kabashi hakuri sannan ka nemi yagaya maka inda suke sai kaje kasame su acan din zuwa gobe ko yagani hakan yayi ma tunda ta ambaci kalmar bada hakuri yake binta da wani irin kallo irin kinsan me kike fada kuwa ganin hakan yasa tace ka tsareni da ido hakan beyi maka ba ko to nide inde bata wannan hanyar zaka biba nasan baze dawo din ba kamar yanda yafada din sannan kuma itama yarinyar bazakaji halin da take ciki ba in kuma kana ganin akwai wata hanyar to sai kafada dan numfasawa yayi tare cije lip dinshi na qasa sannan yace gaskiya hakan baze taba yiyuwa ba me nayi mishi da zan bashi hakuri saide kar yadawo wlh zande kirashi inji inkuma yaqi shikenan zan rabudashi yaje duk inda zashi yafada cike da qarajin haushin shi katse shi tayi da cewa yanzu idan yarinyar ta mutu kasande kaine sila kuma me zakacewa mahaliccinka kasande Allah baze barka ba sai yasaka mata dan haka ina qara baka shawara kaje kayi yanda nace maka din hakan shine daidai kaji baba na kayi hakuri kajekayi din in sha Allah ze sauko kaji "ok" yace mata kawai sannan ya miqe yace ni zan tafi sai da safe har bakin qofa ta rakosa tana qara jaddada masa lalle lalle yaje ya kirashi din to yace mata amma bawai dan ze bayar din ba shibega girman laifin da ya aiakata ba da har zebada hakuri hakan bata sabuba budunga aruwa zede bi wata hanyar amma banda ta bada hakuri baze iyaba tunani me kake yaji tace da sauri yace bakomai saida safe tace Allah ya tashemu lafiya sannan sukayi sallama ya nufi sashen fulani inda part dinsa yake yana shiga yarage kayan jikin sa ya shiga yayo wanka tare da alwala yazo yayi nafilfili sannan ya kwanta akan makadeden gadon sa yabaje har ya rude idonsa sai kuma duk abun da yafaru tsakanin sa da yarinyar ya shiga dawo masa cikin brain din sa lokacin da zemata allura da magiyar da take mishi duk de wani abu da yafaru tunda suka hadu harzuwa lokacin da yarabu da ita babu abun da be tuna ba sannan yadawo kan fadan sa shettima da maganganun bossay yakasa dena tunani daga ya tuna wannan sai wancan ya fado masa da yagade beda mafita sai yajawo wayarsa lokaci ya duba yaga daya harta wuce amma hakan be hanasa lalubo number shettima ba kiransa ya shigayi amma ba amsa beyi qasa agwaiwa ba yaqara kiransa dan atunanin sa ko yayi bacci amma yanzuma ba amsa saida yakira sa har saubiyar sannan ya hakura yabarwa gobe tare da yin cilli da wayar gefe ya kifa kansa qasa yana taso yayi bacci amma yakasa ahaka bashi yayi bacciba sai wajen uku bacci ya dauke shi,
washe gari da gudu ya shiga wani daki akidime yace tana ina yarinyar tana ina tanbayar ka fa nake kamin shiru kagaya min inda take be gama rufe baki ba yaga anturo ta akan gadon asibiti za asaka ta a mota bisa ga dukkan alamu kuma bata nufashi da da gudu yayi kanta azafafe shettima yayi saurin da katar dashi idonsa duk ya canza kala kamar ma kuka yayi da kyar ya iya bude bakin shi yace yanzu burinka ya cika ka kasheta ko to kasani baka ta mutu abanza ba dan sai na bimata hakkin ta nima da hannuna zankasheka yanda kazama sanadin mutuwar ta to nima nine sanadin rabaka da duniya yana gama fadar haka yayi kukan kura ya cakumo shi yashiga naushinshin ta ko ina tare da shaqe mishi wuya hannu yasa yana qoqarin kwace kansa amma yakasa saboda irin ruqon da shettima yayi masa bana wasaba ne tun yana gani har ganinsa yafara daukew kuma yana taso yaay magana amma maganar ta makale taki fitowa hannu yasa suka fara kiciniya shi yanaso ya kwace shikuma ya riqeshi gam ya hana sa damar yin hakan tafiya yayi luuu zefadi da sauri ya bude idon sa tare da miqewa zaune yana tattaba wuyan sa ko zeji hannun mutum saide ba komai ajiyar zuciya yasauke tare da katanto addu'a idan mutum yayi mummunan mafarki ashe tunda yatashi yayi sallar asuba ya koma kuma sai yafara wannan mafarkin dan shi duk atunanin sa gaskiya ne agogo ya duba yaga har goma ta kusa wayar sa yadauko akan bed side drower kiran shettima yashiga yi amma ba adaga daga qarshe ma sai yaji wayar sweach up akansheta gaba daya ta kaicine ya cika shi yanzu yanaji yana kiransa amma ya kashe wayar yana sane lalle akwai matsala kenan betaba tunanin haka daga garesa ba ya dauka duk cika baki hake ashede ze iyadin text ya dan tafa ya tura masa sannan ya ajiye wayar yaje yayo wanka yafito ya shirya sannan ya baro part din be je ko inaba agidan kawai ya nufi inda motar shi take yanazuwa driver ya bude masa ya shiga sanan yace masa nasarawa zasu tunda yaji haka yasan inda zasu dan haka yadauki hanyar gidan su shettima ,

Shettima kwa jiya yana barin asibiti da ita a tunanin sa yatafi da ita abuja sai kuma ya tuna wani abu da sauri ya zaro wayar sa wata number naga yasaka ana dagawa bayan sun gaisa yake cewa yake cewa ya kashigo nan ne naji kace zaka shigo tun wancan satin daga can najiyo wata murya ance na shigo mana gobe na zan koma ai yace ok yanzu kana gida yace yace to dan Allah zankawo ma patien ka duba min ita ko zakazo gidan mu ka dubata kawai yace ok ba matsala bari inzo din kawai amma

Please Login or Register in order to submit comment