Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanda yaso yaganar da ita qin yarda tayi sai zuba take tana masa magana tana cewa yaya ai har na dakko hijabi ma yanzu zan fito jin hakan yasa dr.shettima kwace wayar daga hannun saleem tare da cire ta daga hands free ya kara akunnen sa lokacin tana cewa mama sai nadawo kimin addu'a hello yaya kanajina yace uhm jin duk dahaka bata gane waye ba saida yace bashi bane diff tayi ta hadiye maganar ta dan sarai tagane muryar waye yace auta kingane me magana dayan yayan kine karba nayi intaya shi baki hakuri kiyi hakuri kibari sai gobe kinji yar qanwata shiru tayi bata ce komai ba kwan kwasa qofa akayi hakan yasa saleem barin wajen dan zuwa yabude qofar,
Shikuma hakanne yabashi damar cewa ance kar kizo kinqi ji ko to bismillah maza kizo inajiran ki daman nasan danni zaki zo ko.......
[3/27, 7:35 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode56-57

         """"""""""""""""""""""""""""""""""

Shikuma hakanne yabashi damar cemata ance kar kizo amma kinqi ji ko to bismillah maza kizo inajiranki daman nasan danni zakizo ko sannan yadan dakata danjin amsar da zata bashi,
ita kwa daga can bangare tanasa ne da ga mamakin sa saiji yayi tace dan Allah waye ni bangane me magana ba dan murmushin gefen baki yayi kafin yace shikenan sai kinzo inkinzo zakigane ko waye be jira amsar taba yayi rejecting kiran saboda da shigowar su saleem shi da wata nurse saleem yazaun ita kuma tana tsaye tace sir good evening yace fine tace sir daman ankawo wata patient ne za'ayi mata cs ammade yanzu tana labor room saboda ana tunanin zata iya haihuwa da kanta kuma haryanzu de bata haihu ba shine akace asanar dakai kazo kaga halin da take ciki yace gani nan daga nan ta juya ta tafita duban sa yamayar ga saleem sannan ya miqa mishi wayar sa ya miqe yace bari inje in dubata yana kaiwa nan yayi gaba saleem ma tashi yayi yabi bayansa suna fita kowa yayi nasa bangaren daban,

wayar saleem ce taqara yin ring yana dubawa yaga auta ce dagawa yayi tare da cewa autar mama kinde haqura da zancen zuwan ko tace ai har nakusa qarasowa ma shiyasa nakiraka in tambayeka a ina zan sameka kar nazo nai ta bilayi yace kai auta saifa danace kar kizo amma ba kyaji ko tace kayi hakuri yaya wlh bazan iya hakura bane yace to ai shikenan sai kin qaraso din daga nan ya kashe wayar yaqarasa gurin da office dinsa yake zedan qarasa wani aiki kafin ta qaraso din,


Tana shigowa taqara ciro waya tana qoqarin kiranshi karaf idon ta yafada akansa da batai zaton ganinsa ba yanzu batare da tabari yagan taba tayi saurin buya awani dan lungu tana leqensa harsaida ta dena ganin sa sannan ta fita tana sauke ajiyar zuciya tana cewa Allah ya soni be ganni ba da nashiga uku wlh ya takurawa rayuwata faga haduwa yabi yasakamin ido mstwww taja tsaki,

Saide abun da bata saniba tuni yariga da yaganta kawai ya rabu da itane saboda aikin da yakeyi bashi da lokacin ta office dinsa ya koma yadauko wani dan qaramin box ba dadewa yadawo lokacin da yaqara dawowa ita kuma har takira saleem yazo suntafi office dinsa gurin yakalla yaga bata nan kawai ya wuce yaje yaci gaba da aikin sa,

Yaya nifa ba zama nazo yiba kazo muje naganta na wuce gida yace to aide duk gaggawar asara ai tajira samu sai kijira in qarasa abun danake tukunna kuma doctor din ma ya Shiga aiki sai yafito zakije tace, "waye"? tsoron ta kawai kar acemata wannan mutumin da bata qaunar haduwa dashi,

Amsa mata yayi da cewa dr.shettima mana wanda kika zauna agurin sa ranan "ok" kawai tace
sunan ta qara maimai tawa aranta itabata ma san sunan saba sai yau tabe baki tayi alamar sunan be mata ba, kallonta saleem yayi yace me kike tunanine haka kai ta girgiza tace ba komai kawai ina tuna yanda mukai rayuwa da Ameesha Allah ya tashi kafadun ta Allah yasa mu dawo yanda muke ni yaya wlh dama su dawo gidan mu ko ya kagani banaso tayi min nisa nafiso kullum mukasan ce tare nayi missing dinta sosai taqara sa maganar muryarta ciki da rauni kamar zatayi kuka kallon ta yayi yace Allah sarki ai in Allah ya yarda gobe iyanzu kuna tare zakiganta har sai kingaji tace wlh yaya bazan gaji da ganin besty naba nafiso ma kullum muna tare da juna,
To yaza ayi kinga yanzu sun riga sun dauke su ba yanda za ayi muzo muce subamu ita ina ganin basu iyaba bamuba tace hakane yaya amma ni ina ganin mugwada tambaya amma sai komai ya daidai ta tasamu lafiya sosai ni sai in fara yimata maganar ma kafin maganar taje sama nasan idan ta amince komai zezo da sauki yace to Allah yasa nima zanso hakan kinga ma qara cika gidan tace eh wlh tafada sai faman murmushi takeyi kamar zancen ya tabbata haka suka ci gaba da tattaunawa har wajen la'asar sannan yace mata bari yaje yayi sallah daga nan ze duba idan yagama sai yazo suje tace shikenan sai yadawo yana fita ta qara gyara zama saboda ba sallah zatayi ba wayar ta dauko qirar hauwie y 6 da saleem yasiya mata tun satin baya da yasamu wasu kudi daman yayi mata alkawari dan haka yana samu ya siya mata gallery ta shiga ta bude wata folder ta shiga ta qurawa wasu hotuna ido tana kalla ahankali ta shiga shafa hoton da hannun ta tare da manna masa kiss ahankali tace ina sonka ina sonka ina sonka a kowacce rana sonka qaruwa yake a cikin zuciya ta narasa yazanyi da son wanda besan da zamana ba aduniyar nan sonka kaddara ce agare ni ina azabtuwa da sonka a ina zangan ka awace duniyar kake mutun ne kai ko aljani bansani ba Allah yabayyana min kai a gaske ko sau dayane arayuwata nasan zan samu sassaucin radadin da nake ji araina duk da nasan hakan baza ta taba faruwa ba wanda yake awata duniyar daban dabansan ta ba ta ina zamu taba haduwa lumshe idonta tayi sai hawaye kuma hannu tasa ta share tana qarajin radadi a zuciyar ta kamar yanda tasaba aduk lokacin da ta zauna irin wannan tunanin akan wannan bawan Allahn da bansamu damar ganin fuskar shiba kwanatar da kanta tayi akan hannun kujerar tare da manna wayar akan kirjinta tana rungumeta kamar me rungumar mutum ita kadai tasan abun da take ji aranta,

A wannan yanayin saleem ya shigo ya tarar da ita mamaki ne yakama sa ganin qanwar tasa ahaka sunan ta yakira amma shiru bata amsa ba hannu yasa ze karbi wayar hannunta firgigit tayi ta dawo hayyacin ta tare da qara damqe wayar a hannun ta kollonta yashiga yi cike da mamakin ta sai yace auta lafiyar ki lau kuwa me yake damun ki saurin kawar da damuwar ta tayi dan kar yagane halin da take ciki amma ina duk yanda taso hakan ya gagareta budar baki tayi da niyar cemishi ba komai amma kawai sai hawayen da take ruqewa suka shiga sauko mata da sauri yanzauna kusa da ita yace subhanallahi auta wai meke faruwa me kika gani awayar ban muga hannu yasa ze karbe yagani,
ganin hakan yasata saurin sakin wayar aqasa saboda hakane kawai mafitar ta muddin basakin wayar tayiba ta fadi ta fashe tasan sai asirin ta ya tonu saboda wayar ta babu password idan yakarba sai yagani kuma bata dabakin yi mishi bayani,

Dasauri ya tsugunna ya dauko wayar da tayi kwatsa kwatsa ta fashe kallon wayar yayi yace innalillahi kinga kinfasa wayar taki,
Wai me yake damun ki ne kiyi min bayani duk kinbi kinsa hankalina yatashi dan Allah fada min,
Shiru tayi takasa magana kuma bata dena hawayen da takeyi ba,
hannu yasa yashiga share mata hawayen ta sannan yace shikenan is ok kukan ya isa haka kinsan bana son ganin hawayen kiyi kishiru anjima mayi maganar amma kinde na kukan jin hakan yasata yin shiru din kamar yanda ya buqata kartaje kuma ta kaishi qarshe yace dole sai ta gaya masa, miqewa yayi tare da kamo hannun ta sannan yace shiga ki wanko fuskar ki kizo muje ko bakison ganin bestyn taki ahankali tace ina so yace to kiyi sauri ki wanke fuskar ki sannan inganta kamar da da fara'a akanta yanda duk wanda yaganki ma baze ce kinyi kuka ba kinji ni kai ta daga masa sannan ta shige bathroom din ta wanko fuskar sanna tace muje duk yanda yaso yaganta cikin walwala tasakin jikinta amma hakan ya gagara rabuwa yayi da ita kawai saboda ya lura ba qara min abubane yake damun ta ba da har yasashi mamaki yabar ta lafiya amma yazo yaganta cikin wani irin hali davya kasa gane kanta amma baze ta kurata akan sai tagaya masa yanzu ze bata lokaci kafin ya kuma tayar mata da maganar,

Fitowa sukayi atare suka nufi office din shettima bayan sunyi nocking anbasu izinin shiga da sallama suka shiga yana zaune kan kujerar sa amsa musu yayi idonsa nakan Azeema amma ita kuma tunda ta shigo bata daga kai ta kallesa ba har suka qarasa zama qasa qasa da murya kuma kanta aqasa batare da ta dago ba tace ina wuni saida yagama qare mata kallo sannan yace qanwar mu laifi nayi ne naga ana gaida ni kai aqasa kai ta girgiza mishi alamar a'a shiru yayi yana qara nazarin ta yaga kamar bata cikin walwala kallon sa yamaida kan saleem sannan yace me akai mata ne saleem yace wlh bansani ba nima lafiya qalau na barta amma da na dawo naganta haka kuma taqi gayamin me akayi mata nade rabuda ita idan ta sauko tagayamin,
karkada kai shettima yayi tare da cewa hakan yayi sai kuma yayi shiru yana qara nazarin ta sai daga bisani kuma yace ok muje ko taga qawar tata kode ma itace sanadin damuwar tata yafada yana kallon ta amma still de bata yarda ta dago sunhada ido ba duk da shi anasa bangaren yana so su hada idon ko ze fahimce wani abu amma taki bashi damar hakan fita sukayi gaba da yansu sannan suka nufi dakin da Ameeshan take da shettima mane yafara tura qofar yashiga sai saleem sannan itama tabi bayansu agaban gadon duk suka tsaya suna kallon kyakkyawar fuskar ta da tayi wani irin fayau da ita taqara haske tayi haske sosai ga yar rama da tayi amma sai taqara mata kyau jikin ta sanye da rigar asibiti light blue color datayi mata kyau sosai taqara fito da hasken jikin ta,
duka qura mata ido sukayi bawanda ya iya yin magana,
Shettima besan lokacin da yakai hannun sa kan gashin da yadan zubo mata wajen goshi ahankali yafara mayar mata da su baya sai fuskar taqara fitowa dass duk wanda yakalle ta sai yaqara kallon ta gata yar qarama da ita kamar kasace ta ka gudu,
Saleem ne katse shirun nasu da cewa to auta gaki ga besty kinga tade kamar ki kirata ta amsa gata nan sai bacci take abun ta dan murmushi tasaki sannan tace naganta wlh qarasawa tayi kusa da ita tazaun a bakin gadon tare da ruqo hannun ta cikin nata tana qara binta da kallo sai faman murmushi take amma kana ganin murmushin kasan qaqaloshi akeyi dan kana gani zakayi zaton dole akayi mata akan sai tayi shi dukan su kuma suna kule da ita amma ba wanda yatanka mata saleem yace to taso mutafi ko tunda kin ganta hankalin ki ya kwanta tace eh sai yanzu nasamu nutsuwa da naga farin cikin raina tafada tana kallon ta sannan tace Allah yaqara miki lafiya besty na...

saleem yace ameen ya Allah
daga nan kuma sai ta miqe tsaye tace mutafi ko dukan su mamaki sukayi dajin maganar ta matar da waya take ta ihu da murna amma kuma gashi yanzu da ta ganta bawani farin ciki da tayi gashima harda cewa sutafi atuna nin su idan taganta sai zatace baza tatafiba sai sun hadata da Allah zata tafi amma ita take cewa ma sutafi lalle akwai lauje cikin nadi,

"Yanzu made bawanda yace mata komai saleem yace to muje ita tafara yin gaba ma sannan suka bi bayanta kuma tana fita batayi hanyar office din su ta juyo tace yaya ni bari na wuce gida sai ka taho yace a'a kibari mutafi tare ai na kusa gamawa ma sai muwuce kawai tace a'a wlh kataho aiki nakeyi nataho zanje inqarasa ne duk yanda yaso amma taki amincewa dole yarabu da ita shima shettima saida yasa baki akan tabari sai anjiman amma taki yarda kuma har zuwa wanna lokacin bata bari sun hada ido dashi ba sallama tayi musu tatafi sukuma kowannen su yayi nasa office din kowa cikin ransa cike da mamakin sauyawar tata,

Shettima nashiga office sai kawai yakasa zauma yana ta tunanin yanayin yarinyar nan dan tabashi mamaki matuqa kode shine sanadin wannan kukan nata tunda gashi taqi yarda ta hada ido dashi gaba daya ta canza sai yaji duk baba dadi dan aganin sa abubuwan da yayi mata ne kwanaki sune suka sakata damuwa haka inkwa hakane ze bata hakuri dan shi mutun ne da bayason shiga hakkin mutum bayaso yaga mutum ya kullace sa saboda yana tsoron ya mutu yabar wani najin haushin shi batare da yane mi yafiyar saba bayaso ya mutu da alhakin wani akansa ganin tunanin nasa ba me karewa bane yasa shi daukan key din motar shi yafito da sauri dan bin bayanta, sauri yake tayi be ganta a harabar asibitin ba dan haka kawai ya shiga mota tare da fita daga gate din bakin titi ya tsaya ko ze hangota amma ba ita ba alamun ta cike da taqaici rashin ganin nata ya juya ya koma ciki parking yayi sai kuma yakasa fitowa duk jinshi yakeyi wani iri,

abangaren Azeema kuwa ashe tana fitowa sai ta samu wani lungu tayi zaman dirshen tana qara sakin wani kukan qasa qasa me tsuma zuciya babban abun da yasata wanna kukan shine fasa wayar ta da tayi shikenan yanzu ta dena samun damar kallon sa aduk lokacin da taji kewarsa idan ta kalli hotonsa tana danjin sauki amma yanzu ba yanda za ayi taringa kallon sa tafasa wayar ta da kanta wanda sai yanzu take ta danasani dama bata fasa ba ita wama yakai ta yin wannan gangancin kallonsa awaje duk sanda taji tana kewarsa daki take shiga ta kulle kanta tagama haukanta ta idan yan kukan sunkama tayi abunta ta qoshi ta godewa Allah sannan tayi wanka tafito bawan da ze gane halin da take ciki amma yau tayi ganganci gashi kuma ankusa ranfota dan tasan tabbas sai yayanta ya tambayeta ko ba yauba dole tasan amsar da zata bashi,
Bakin ta ta bude cikin sauti a fili take cewa nashiga uku ni Azeema wai meyake shirin faruwa dani ne waddannan abubuwan suke faruwa dani tunda nake bantaba ganin inda aka taba yin hakaba daga ganin mutum ka kamu da matsananciyar soyayyar sa wace take shirin tarwatsa farin cikina gaba daya inazan saka raina yazanyi dashi araina taya zancire shi daga cikin zciyata me yasa zuciyata zata min haka meyasa bata da hankali bata san abun da yake daidai ba da wanda ba daidai ba hannu tadaga sama tafara jero addu'a
Ya Allah naroqeka badanni ba badan halina ba Allah ka cire min sonsa araina Allah ka kawomin mafita acikin ala mura na Allha ka kawo min dauki Allah ka taimake ni Allah kataimakebi bani da wanda zan gaya damuwata saikai kaikadai kasan halin da nake ciki Allah ka yaye minshi kabani abun da yake daidai arayuwata kacire min abun da ba daidai ba idan kuma jarrabawace wanna Allah kabani ikon cinyeta dan dakatawa tayi tanaci gaba da kuka sannan ta dora cewa , Allah ka kawo min dauki kacireni daga wannan haukan da nakeyi tana gama rufe bakin ta taji ance" Ameen Ameen"

Ahakace tajuyo tare kidimewa lokaci guda kuma taji zuciyar ta ta wani buga da qarfi waiwayowa tay danganin me amsa mata addu'ar da take yi idon tane sukayi mata tozali da abun da bata taba tsammani ba tsaba tsoron da taji ne yasata sumewa awajen ...........✍

(Tofa meke faruwane takwara wakika gani haka kuma wakike so)

who guess? kowaye wannan waze iya gaya min wanda tagani next page nashine nayi alqawri💃



Azumi fa yazo sai kunyi min uziri yanzu ba kullum zakuna samun posting ba sai sanda kuka gani kawai


Story and writing
by
xeemat love
[3/28, 10:52 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode58-59

         """""""""""""""""""""""""""""""""


💋Spacial thanks to you all ❤wannan page din naku ne saboda ku nayi da wadanda suka canka daidai da wadanda basu canka bama duk ina miqo saqon gaisuwata gareku,
irinsu 👇
sabreena,
it'z hauwee,
halyma,
kirawa,
Gbemisola abdulrasheed💋💋💋

******************
__________________AZEEMA

bude idonta ta shiga yi ahankali dishi dishi tafara gani kafin ta qarasa ware su tar ganin inda takene yasata saurin tashi zaune tana murza idon ta dan tabbatar da inda take,
idon ta tasauke akan shettima dake gefen kujerar datake zaune ido ta zuba masa tana kallon sa shima itan yake kallo ko kiftawa basayi ita fafara janye idonta daga kansa sannan shima yajanye nasa yayi sai daga bisani kuma ya katse shirun nasu da cewa "ya jikin naki?
bata bashi amsa ba saima tunanin yanda akai tazo nan take shin to wai ina wanda tagani ne kode da gaske ne alajanine kamar yanda take zato,
to hakan na nufin aljani take crushing bata sani ba tabbas idon ta yagane mata wanda take son gani to amma kuma tunda ta ganshi bata qara sanin inda kanta yake ba sai yanzhaka0mta farka taganta anan to me yafaru da ita bayan ta ganshi din batasan lokacin da fili ta furta aljani ne kenan jin abun da tace ne yasa shettima juyowa shima da mamaki sannan  ya maimaita abun da tace aljani kuma a ina?
juyowa tayi tace uhm alajani ne wlh aljani ne yace ke wai aljani a ina kasa amsa mishi tayi kawai sai ta fashe da kuka sosai ta tsoratar shi yakasa gane inda ta dosa kafadun ta yadafa yana dan jijjigata yana cewa ke malama ki nutsu me yake damun kine jikin yaji yadau bari na tsoro ganin hakanne kawai  yasashi jawota jikin shi yasakata a faffadan kirjin shi ya rungumeta qama ajikinshi yana shafa bayanta alamar rarrashi sannan yace shiiii pls kidena kukan haka bawani alajani anan nine fa ,
cikin shashsheqar kuka tace wlh naganshi dazu aljanine tafada gaba daya tafita hayyacin jikin ta sai faman karkarwa yake qara riqeta yayi sosai dan ya lura a tsora ce take sai kuma yafara tunanin to kode aljanin ta gani dagaske tunda ayanayin da yaje yaganta bisa ga dukkan alamu dayagani kamar furgita ce tasata suman inba haka ba to meyasa ta suma awajen gashi kuma fuskar ta shabe shabe da hawaye to me yake damunta yatambayi kansa amma beda wanda ze bashi amsa tabbas akwai wani babban al amari da yake damunta amma ze bincika gurin yayanta yaji ko ta taba yin irin hakan ko kuma yanzune aljanun suka shafeta har suke bude mata ido,
cigaba yayi da rarrashinta har saida yaji tayi shiru ta dena kukan amma hakan besashi dagata daga jikin shiba ya rabu da ita ta tashi dan kanta saida suka dauki lokaci ahaka kafin ta yunqura ta raba jikinta da nashi saita qara komawa jikin kujerar ta jingina kanta da hannun kujerar tare da lumshe idon ta kamar meyin bacci

zuba mata ido yayi yana kallon ta kamar yasamu tv shi kansa yayi matuqar daure wa da lamarin yarinyar nan na farko tazo tanayin kuka taqi fadar abun da akayi mata na biyu kuma tace bazata zauna ba kuma ta tafi nanma kuma bata tafi ba ta tafi can wani waje alhalin tace ta tafi gida to me yakaita can wajen kuma me tagani da har yakaita ga sumewa hannun sa yazura a aljihu ya dauko wayar sa yafara daddan nawa ,

Adaidai lokacin ita kuma ta bude idon ta ganin abun da yake yi yasata saurin cewa in roqeka wani abu dakatawa yayi da abun da yakeyi tare da dagowa ya kalle ta sannan yace inajin ki saida ta danja dogon numfashi kafin tace dan Allah kar ka gayawa yayana abun da yafaru yace me yasa tace banason yasan komai saboda banaso hankalin sa ya tashi kuma idan yaji ze gayawa mamana itama zata shiga damuwa kuma zasu tambayeni dalilin damuwata ni kuma bazan iya gaya musuba dan haka nake roqonka dan Allah kar ka gaya masa kaji plsss ta qarasa maganar tana marairaice fuska,
sosai jikinshi yayi sanyi dan haka yace gaskiya kiyi hakuri bazan iyaba halin da kike ciki dole su sani domin a nema miki magani watakil aljanune suka shafeki suke bude miki ido yakamata susani sai a gaggauta nemo miki magani,
Murmushin takaici tasaki jin furucin dayake sannan tace hmmm baza ka gane bane amma ni bana tattare da shafar aljanu nide kawai alfarmar da nakeso kayi min kenan wannan yazama sirri tsakanina dakai, kallonta yayi sannan yace zan amince amma abisa sharadi kin amince?
daga masa kai tayi alamar eh ta yarda  cigaba yayi da cewa sharadin shine zaki gaya min abun da yake damunki da kuma abun da kika gani da harkike tunanin aljani ne..

wani busashen yawu ta hadiye da ya tsaya mata a maqogaro sannan tafara girgiza mishi kai tana cewa kayi hakuri wannan sirrin zuciya ta ne nayi alkawari koda zan rasa rai nane babu wanda zan iya gayawa inde ba abunne ya tabbata ba bare ma nasan har abada baze tabbata dan haka zanci gaba da ajiyeshi acikin zuciyata daga nan harzuwa lokacin da ze zama ajalina dannasan shine ajalina sanadin sane zanbar duniyar nan wani irin kukane ya taho mata da yasa takasa qarasa maganar takeyi saida tayi me isarta sannan ta dora da cewa dan Allah naroqeka karka takura min akan sai kaji dalili na karabu dani kawai, yace to na rabudake amma kisani dole susan halin dakike ciki sai sudau mataki akai nida kaina zanje har gidan ku ingaya wa mamanki da abban ki ko so kike nasan halin da kike ciki inzuba miki ido har kimutu idan nayi haka ko agurin Allah ina da laifi gwara nagaya musu nafita sauran yarage nasa yana kaiwa nan ya miqe ze bar wajen da sauri itana ta miqe tare da shan gabansa ta hada hannuwan ta biyu waje daya fuskar ta kuma hawaye sai sintiri suke akan kumatun ta dan Allah fa nace baka da tausayi ne ya kakeso inyi da rayuwata ne da damuwar da take damuna ko da wacce kake son kunno min yanzu yace ai ke kika zaba duk ma abun da yafaru mafita daya ta rage miki zabi biyu nabaki ko kigaya min ko kuma in fada musu sai kigaya musu da kanki dafe kanta tayi sannan tace naji na zabi ingaya maka amma kamin uzuri ahalin yanzu da nake ciki bazan iya gaya maka ba kabari idan nasamu time zamaka magana sai muhadu ingaya maka kayarda kai yadaga mata sannan yace yanzu naji magana zan daga miki qafa amma fa na tsawon sati daya idan baki fada ba kuma kinsan sauran ina fatan kin gane,
Eh tace masa yace good girl yanzu ki share hawayenki ki muje nakai ki gida in

Please Login or Register in order to submit comment