Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajen ta daya yace ku dauko sa muwuce jin zasufara fitowa yasa nayi saurin lallabawa nafice daga gurin ina fitowa Ameesha tasaki wani kuka da tashinta kenan daga bacci saboda tana bayana agoye sauri nayi naqarasa fitadaga gidan gaba daya can nesa da gidan naje na boye inda zan iya ganin fitowar su sauketa nayi na shiga rarrashinta nabata ruwa sannan tayi shiru cigaba nayi da tsayawa agurin ina jiran fitowar su,

Inaganin su suka fita da malam dan rashin mutunci ma aqasa sukajawo sa suka bude boot suka jefasa suka qulle sannan suka ja motar suka bar qofar gidan a tunani na ko sun fasa qona gidan dan har ina tunani komawa ciki sai kawai naga hayaqi na tasowa taciki ashe kafin su tafi saida suka bude silindar gas tare da kunna gas din sannan suka fita da sauri,

akan idona gidan nam yakama ci da wuta banbar wajen ba har saida naga yabkusa qonewa inaganin mutanen ana ta qoqarin kashe wutar amma taqi mutuwa bangama ganiba naja qafata nabar wajen wata unguwa nasamu ina tunani kuma yanzu ta ina zan fara wane irin taimako zanwa wadancan bayin Allahn mijina da kuma dana dake hannun su wazan fara taimakawa dan sai a lokacin nagane tabbas ba bakinsu daya ba masu yimasa wannan abun na harkar banki daban suma masu naiman sa daban dan bawan da yasan da zaman wasu kowa nasa harin yakai masa ba mutum daya bane yame farautar sa,

da qyar nasamu wata qasan bishiya da ba wanda zai ganni anan nake kwana wajen kwana na biyu agurin ba ci ba sha damuwa babu wacce ban shiga ba ga Ameesha kullum cikin kuka take min dan 'yar madarar da nake batama ta kusa qarewa kadan kadan nake bata saboda idan ta qare bansan a inda zan samo mata wata ba daman ba ruwa take shaba ahaka mukayi rayuwa tsawon kwana biyu da wuni gida danaga de ina niyar halaka kaina sabida yjnwar da nake ji ta gama kamani dan da qyar ma nake iya daga qafata nake tafiya idanuna kwa har rurrufewa suke yi saboda rashin bacci da yunwa haka nafito daga cikin dan dajin ga Ameesha abayana sai kuka take min ahaka nazo bakin titi amma sai na dan rufe fuskata da gefen mayafina saboda kar aganeni......,

***********************
*Azeema*

Tunda safe tagama shirin ta tsafa cikin matattun kaya da kana ganinta zaka san tana bukatar taimako saide idan kallon ta kayi sosai shine zaka ga jikinta ba na neman tai mako bane saide akayane kawai zaka fahimci haka sosai mama tayi mata fada akan ta kula sosai tare da yimata fatan nasara da addu'o'i ahaka sukayi sallama harda dan guntin hawayen ta itama mama saida ta zubar da nata hawayen amma aboye sannan sukayi sallama saleem ya fito da ita suka hau napep suka gaya masa inda zasu daga dan nesa da masarautar suka sauka sannan suka qarasa a qafa tamqamemiyar masarauta ce wacce baka isa ka gano qarshen ta tunda ga waje kake hango titin da aka shimfida aciki daga ciki kuma ga mutane nan ana ta safa da marwa sosai Azeema ta tsorata daganin zubin masarautar kallon saleem tayi tace anya kuwa yaya ba komawa zamuyi ba wallahi sai yanzu nafara jin tsoro kar inje ko ajaline yake kirana tausayi tabashi sai ya ruqo hannuta tare da kwantar mata da hankali da qarfafa mata gwiwa akan zata iya ta cire komai aranta tasa aranta kamar zata kwato musu mahaifin sune sai ta cire tsoro in Allah ya yarda ba abun daze faru da ita kuma zasuyi nasara akansu ta riqe addu'a duk halin da ta tsinci kanta sannan yabata watayar qaramar waya yace ki boye wannan duk yanda ake ciki ki kirani ki sanar dani kuma koda kinga baba kar ki nuna kinsan shi saboda gujewa matsala shima kuma nasan koda yaganki baze nuna yasanki ba to dan Allah kema ki daure kar kinuna kinsanshi nan kusa sosaide ya bata shawar wari akan abun da zatayi batare da ansamu wata matsala ba saida tayi kuka sosai shimade kawai daurewa yake yi amma de abun da yake ji yama fi kukan saida yakaita har bakin gurin sannan yarabata da jikin sa tana kuka da qyar ya iya banbareta daga jikin shi sannan yace kije kawai Allah yabada sa'a kin shiga tayi sai yadawo yace ko mutafi kinfasa taimakon mahaifin namu kai ta girgiza masa yace to dan Allah kiyi hakuri kije kidena wannan kukan nima kima karya min zuciya ji nake kamar insaki kukan kije kar wani yazo ya tarar damu da qyarde suka rabu yajuya da sauri sakamakon hawayen da yaji yana niyar zubo masa tasan abun da zeyi kenan shiyasa tace kayi hakuri yaya kar kazubar da hawayen ka in Allah ya yarda bazan fito daga gidan nan sai tare da mahaifin mu bejuyo ya kalle ta ba kawai ya daga mata hannu daga inda yake yace Allah yasa ganin hakan yasatayi shahada tare da runtse idon ta tayi bismillah tasaka qafar ta ciki dake yanayin wajen daga dan waje babu me gadi sai ka shiga daga ciki kuma zaka qara tarar da wani gate din inda masu tsaron suke,

Jim kamar ta shiga yasa shi juyowa yana kallonta itama juyowar tayi suka hada ido sai kawai ya sakar mata murmushi qarfin hali itama shi ta mayar masa tare da daga masa hannu shima ya daga mata sannan yajuya da sauri yabar wajen yana tafiya yana share hawayen sa da fatan Allah ya fito da ita Allah lafiya dan shima yadan tsorata din kawaide ya dake ne saboda ba yanda zasuyi wannan ce kawai mafita agare su tunda yatafi be qara waiwayen ta ba har ya bacewa ganin ta, tana wajen tana kallon sa saida taga yabacewa ganin ta sannan ta hakura da kallon sa tana hawaye tana cigaba da tafiya tana waiwayen sa ko zataga yadawo amma babu shi ahaka har ta qarasa gurin gate din tsaya wa tayi tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta labewa tayi tana dan hango mutane daga nesa tana gurin taji qarar kamar mota na tahowa da sauri tayi gefe tare da tsugunnawa motar na qarasowa tayi horn aka bube ta shiga ciki ana shirin rufe qofar sai kawai tayi saurin qarasawa wajen me gadin har yakusa rufewa sai kawai yaga yarinya kamar daga sama danshi tabashi tsoro ma marairaice fuska tayi kalar tausayi tace baba dan Allah yunwa nake ji kataimaka min da abinci naji ance nan gidan sarki ne shiyasa nazo ataimake ni abani abinci yau kwanana biyu banci abin ci saida yagama qare mata kallo sannan yace ina iyayen ki tace bani da iyaye,
iyayena duk sun rasu nikadai na rage dangina kuma bansan inda suke ba sabo da ni yar gidan wata mabaraciyace ahaka na taso na ganmu kuma tace mahaifina ya mutu itama kuma wata mota ta buge ta tamutu ta barni nikadai tana qaraswa ta fashe da wani irin kuka wanda kanaji sai ka dauka labarin da ta bayar na gaskiya ne da be yarda da itaba amma ganin irin kukan datake gata kuma yarinya qarama sai kawai yaji ta bashi tausayi fasa rufe qofar tayi sai yace ta shigo sosai taji dadi aranta ganin bata sha wata wahalaba tasamu shiga ciki cikin kwanciyar hankali batare da wani bata lokaci ba
godiya ta shiga yi mishi lokacin shide babu komai da ze bata sai ya nuna mata wata hanya yace idan ta miqe sai tayi kwana zataga wasu mutane awajen tace waye shugaban su idan aka nuna mata sai ta gaya masa abun da yakawota sannan tace mishi shi yaturora ta in Allah ya yards zata samu subata abinci taci ta qoshi itade bahaka taso ba taso yace za abata waje ta zauna aciki ko yace za adauke ta aiki amma hakan ma wata damace agare ta sai kawai ta amsa masa da to sannan tasa kai ta nufi inda yace mata tana yin kwana kuwa ta hadu da wani mutum ta tambaye sa sai yace mata ai shine tagaya masa duk abun da dayan yace mata ba bata lokaci kuwa ya nuna mata inda zataje abata abincin maimakon tayi inda yace sai kawai tayi wani wajen daban saboda ita ba abincine da muwarta ba sosai ta shiga cikin masarautar tare da bin bango tana tafiya tana buya tazo wani wajen kena taji takun muta ne da yawa wani wajen ta samu ta buya tana leqansu idon tane yasauka akan wani mutum dayasa tay saurin zaro ido da mamaki batasan lokacin da ta daga murya ba tace YAYA SALEEM gaba daya mutanen suka juyo gun da suka ji muryar mace shima sarkin dakatawa yayi da tafiyar da yake yi tare da kallon lungun da sukaji an anbaci wani suna daban sosai ta zuba masa ido tama kasa magana saboda tsabar mamakin da yagama daskarar da ita agun ko kwakkwaran motsi takasayi sai..............................✍

(Tofa ana wata ga wata yaya Saleem kuma acikin masarauta bayan kin barosa awaje me zai kawo sa cikin masarauta?)


*TAMBAYA?*
to shin wa Azeema tagani da harvta tonawa kanta asiri tun ba aje ko ina ba me zaifaru idan sarki yaganta shin zamanta zaiyiyu kuwa agindan ko za akoreta zata dawo da mahaifin nata ko bazata dawoba za abarta da ranta ko kuma za adau mataki akanta taya zata hadu da mahaifinta?

Wacece hajiya sarah meyasa tacewa fulani ta gaggauta sa baba yabar gidan nan shin meye alakarsa da gidan dan hartake jaddaddawa fulani cewar yabar gidan lokaci zaiyi halinsa shin me fulani take boyewa me take shiryawa acikin masarautar??,

Shin ina gimbiya sabreena ita da danta me ya fitar dasu daga gidan sarauta meyasa yanzu ko zancen ta ba ayai acikin gidan mutane ma da yawa basu san da ita ba?

Me sam yaji fulani nacewa me yake zarginta dashi wace alama yagani agareta kuma me yasa yake so abashi labari shin a inama yaji maganr gimbiya sabreena meyasa yakeson sani wacece ita ?


taya dadda zata iya shiga cikin garin bayan nemanta ake ido rufe shin waye sameer dan dadda meyasa yake da tarun maqiya haka wacece mahaifiyar sa da ake nema meyasa ake son kashe shi waye yake son yaga bayansa da duk wanda ya rabe shi?

suwaye sukai mishi qazafin satar banki shin yana fitowa daga ciki ko baya fitowa wadancan mutanen daauke nemasa zasu same shi kuwa,

ina dadda takai dukiyar sameer ta boye taya akai ta dawo kano da zama har takai wannan lokacin basu kashe ta ba kuma bata basu abun da suke soba alhalin kuma duk inda tayi suna biye da ita,

mahaifiyar sameer da aka buge amota shin ina aka kaita waye mutumin da yatafi da ita kuma me yasa be kira malam ba tunda yatafi dashi,?

wane irin mataji su sam zasu dauka idan dadda taga basu labari ta ina zasu fara binciken ko suwaye suke bibiyar rayuwar su?

Shin waye mutumin da yacewa bossay yana tare dashi kuma nakusan kusansa wanda zasu hada alakar jini dashi waye nakusan kunsan bossay kenan,?


Shin wai duk akan mema ake wannan bibiyar tasu meye tushen labarin mai mahaifiyar sameer ta aikwata da har yashafi kowa?

tode duk ku biyo ni acikin littafi nabiyu amsoshin mu duk suna ciki kuma zaku same su nan da bayan sallah kucigaba da kasancewa atare dani

SARKI SAMEER na biyu paid book ne duk me bukatar jin yanda wasan zai qare sao yayi min magana.
Alahamdulillah! Alahamdulillah!!

Duka duka anan na kawo qarshen littafin sarki sameer littafi na daya sai kuma bayan sallah in Allah yakaimu da rai da lafiya zan dora daga inda na tsaya zamu shiga littafi na biyu2,

amma littafi na biyu na kudine ban tsauwala ba nasa kudi kadan saboda in sauqaqawa kowa, nasan duk amasu yin littattafe babu littafin da ake siyar dashi haka da araha nayi hakane saboda kowa yasamu damar biya batare da ya takura kansa ba duk me son cigaban littafin zai biya naira dari biyu 200 kacal bayawa duk wanda ya shirya biya sai yayi min magana ta wannan number kamar haka 08124226526 ku hanzar ta biya tun kan lokaci yayi kar kubari abaku labari domin akwai abubuwa anan gaba masu tarin yawa wanda dole sai ka karnta zaka gane,


Godiya gareku ❤ readers din book one bazan manta daku ba godiya ta musamman gareku Allah yabar zumunci inaji daku banzan manta daku ba irin naso fadar sunayen ku saidai bansan sunan wasu ba sai na tambaye su saide mu hadu agaba saboda banason insaka sunan wasu bansa ka wasu ba ammade duk wacce tasan tana yina to nima ina yinta irin sosai dinan banda masu karan ta min littafi basa comment duk ina sane daku sai ku karanta kuyi kememe ku qi comment ko to ba komai ai bazan fasa rubutu na ba dan bakuyi ba yanzu de mutum ko beyi comment ba ai zai biya inde yana son cigaba dan haka kuriqe comment dinku nima inriqe littafina shikenan ai ko.....



Stop and writing

💅💅By❤ xeemat... lov❤💅💅💅💅 💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅



             

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment