Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wai papa dan Allah wai ba ayin murabus kafin lokaci ya ciki danni wlh nagaji daman nifa tunda ma bason wannan sarautar nake ba bansan ma ya akayi na karba ba ya gama fada da iya gaskiyar sa maganar har cikin ransa yafada dariya papa yayi yace kai yanzu deeni banda abinka a ina kataba ji anyi murabus lokaci beyi ba ai abu uku zuwa hudune suke sa mutum ya sauka daga kan kijera lokacin saukar su beyi ba saide ko in mutuwa ko rashin lafiyar da mutum baze qara iya kkmai ba ko ka aikata wani gagarumin lafin da zesa asauke ka amma banda haka ba abun dazesa ka ajiye sarauta hakan nan dole sai lokacin murabus yayi papa nagama rufe baki sarki yaqara cewa to kawai insauka sai agayawa mutane bani da lfy nikuma sai in fita qasar waje kaga ba wanda zeyi magana akai ko, papa wata dariyar yayi sannan yace Allah sarki lalle bakaso din nayarda amma ba me goya ma bayan yin hakan nima lokacin da nayi tawa baso nake ba haka akayi min dole nayi har nayi murabus na baka kaima kuma ba yarda zakayi dole kayi hakuri kaci gaba dayi kai da bakai kadai bama kake gudanar da mulkin ba gyatumar ka tana taya ka ita sarauta da mulki sai kayi hakuri kuma saka tsaya tsayin daka domin Allah ne yabaka kuma anaso kayi adalci aciki saboda rana gobe kiyama Allah sai ya..... fulani ce ta katsesu da cewa to hirar ta isa haka tayi hakane saboda batason yafara yi mishi nasihar da har zatakai cikin zuciyar sa ta canza mishi tunani akan yarda ta dora shi daman kuma tasaba yi mishi haka duk sanda taji su zefara yimishi wata hirar daban ko yayi mishi gyara akan wani abun da yake ba daidai ba to zatai saurin dakatar dashi tana guri tasamu tazauna itama sarki ne yafara gaishe da ita fuskar ta adan tsuke tace mishi me yakawo ka nan har kuka zauna kuna hirar da ta dace da warda ma bata dace ba sarki yanazaune ya dan kishingida kansa da majinginar kujerar da yake kai yana lumshe ido bece mata komai ba dan shima nashi mulkin yake ji da shi saida yagama shan qamshinsa kamar ma ba agaban ta yake ba sannan ahankali yace daman nazo mugai sane sai kuma dawowar me sunan baba yace min wani satin ze dawo insanar daku fulani tace gashi ubanka ko yana dan cikin ka amma shi ze aikoka ko kunya bakaji ba harda debo qafa kazo fada mana shiga dan rainin hankali yafi qarfin yakira mu yagaya mana to kar yadawo ifiritun yaro kawai kwata kwata yaron nan bashida ta ido baya ganin kowa da gashi ni wlh kace mishi kar yadawo yamansa acan har yagama rayuwarsa bama bukatar sa papa ne yayi dariya yace inke bakya bukatar sa ai iyayen sa suna bukatar sa hade rai ta qara yi tace to nide idan ma yadawo kar yasake yazo inda nake kar naga qeyarshi a sashena ya koma can wajen uwarsa dan baze qara zamar min a part dina dan ban manta abun dayayi min ba kafin yatafi gaba dayan su dariya sukayi mata sarki yace nima daman bacewa yayi ingaya muku ba ni kadai yagaya wa kuma bece ingaya kowa ba shine naga ya dace ingaya muku danna san halinshi baze gaya wa kowa ba shiyasa nafada muku sai a tarbeshi fulani tace wlh ba abun da zan mishi dan intanice ma ko airport ma baza aje dakko shiba saide ya hau motar haya papa yace Allah ya tsare shi da hawa motar haya bawanda yataba haka saishi hakan ma baza ta faru ba sarki yace papa kabarta kawai kasan de ba shiri suke ba lokacin ma da za a dakko shi bata saniba saide kawai ta ganshi a part dinta daga nan kuma sai suyita su qare ita da shi itama tace ai nagaya muku baze zauna min a part ba saide ya nemi wani wajen daban amma ba nan ba papa yace to ai zamu gani muna mu kallone ba ruwan mu acikin abunku haka de suka dauki tsawon lokaci suna tattauna wa akan me sunan baba har sarki yatashi yana gyara zankadediyar babbar rigar shi da taji uban aiki kamar ba dinkata akayi ba saida yagama kimtsawa papa na taya shi sannan yafara takawa cike da qasaita da izza kana ganinshi kaga cikakken mutum me cikar haiba bana mijin wasa bane daman shi yana da jiki kuma ga tsaho irinde jaint dinnan ne ga kuma kayan sarakai da suka qara mishi girma inde ka kallesa dole ne kaji yamaka kwarjini cikin takunsa daidai na sarakai yafito waje dogaren dasuke jiran shi suka mara mishi baya izuwa cikin fada fulani da duk suka bata mata mood dinta yau tana jin farin ciki amma suka zo mata da zancen wannan banzan yaron duk sun bata mata rai sai faman cika take tana batsewa papa da yaga haka sai yace me sunan baba na maryama maryama ta me sunan baba Allah yabarku dashi ko kallon inda yake bata yiba ta tashi ta bar wajen da murmushi yabita yana dan girgiza kai....


More comment more typing🖋
No comment no typing......
Likes &share
[3/2, 4:49 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER.....💅
           by❤xeemat....love❤

           🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

               
Allah ya gafartawa iyayen mu Allah yasaka musu da gidan aljanna Allah yabiya musu bukatunsu na alkhairi Allah yasa murabu dasu lafiya Allah yabamu ikon cigaba dayi musu biyayya   👏

                      Bismillah........
Episode 19🖋

               ********************

Azeema ce takalli Ameesha tayi mata alama da ido akan ta tambaya sutafi itakuma sai ta qara make lafada alamar taqidin dadda dake tafaman hada kaya tana kallon su duk abun da sukeyi tana ankare dasu amma ta nuna batasan ma da zaman su adakin Azeema ce ta mike da nufin tatafi amma ba tafiyar zatai ba tanaso taga yaya Ameeshan zata tambaya sutafi dinne kozatayi shiru ne ta barta tatafi ita kadai din aikwa tana mikewa tace dadda nizan wuce dadda tace kigaida maman taku kar kimanta kice mata ina mata Allah sanya alkhairi tace dadda zangaya mata tana fadar haka kuma tajuya batabi takan Ameesha ba tayi waje aikwa a sukwane Ameesha ta mike ta tari gaban tana cewa wai da gaske tafiya zakiyi kibarni tabata amsa dacewa to me kike so inyi nace ki tambaya kinqi kuma kinyi shiru kinqi magana so kike kawai inzauna ina kallonki to ni ina da aikin yi inke baki da shi tana gama fadar haka ta ratsa ta gefenta zata wuce nan ma taqata saurin tare ta tace to tsaya zan tambaya Azeema tsayawa tayi tana kallon sannan tace kiyi sauri kifada acikin minti biyu inba haka ba kuma inta fiyata tace naji to sannan tashiga tunanin ta inama zata fara ganin bata lokaci take qara yi yasata yin dan gaba kadan kusa da dadda sannan ta juyar da kanta gefe tana hade rai tace zanje gidan su besty kinji banza dadda tayi mata hakan kuma ba qaramin qara bata mata rai yayi ba haka dan haka itama sai tayi shiru kuma bata juyo da kanta ba muryar Azeema ce ta daki dodon kunneta da cewa zantafi ba rintse ido tayi sannan tace wai yakike so inyi ne kinajifa nagaya mata tayimin banza AZEEMA tace inkuma bata ji bafa kiqara tambayar ta mana wani irin kallo ta watsa mata tare da wurga mata harara aranta tana cewa yama za ayi ta wani ce batajiba bayan gata ga ita kusa kusa amma ta wani ce batajiba kawai de rashin mutunci dadda take mata qara tamke ido tayi sannan tace zanje gidan su besty kinji nanma shiru tace kinji ta qara maimaita mata dadda dake tafam aikin gabanta tace inbakisan sunana ba sai kitashi kibar min waje ba inda zaki iya qololuwa Ameesha ta kai amma ba yanda ta iya sai ta miqe tsaye kawai ta daga murya tace wai dadda sai wulakanci kike min kawai akan dan wannan abun da yafaru bafa tsoron ki nake ba wlh zan iya qasa qafata infita kuma bazan qara dawowa ba daga gidansu duniya zanshiga daman nagaji da zama dake nagaji nagaji burinki kullum kiganni cikin damuwa ina kuka baki da matsala da hakan saboda bake kika haifeni ba nasan da yar kice da bakiyi mata haka ba to wlh to wlh nagaji ki maida ni inda kika dauko ni inma tsintata kikayi ko akan bola ne to ki maida ni inda aka haifeni tunda daman ance akan titi aka haifeni ni banda uba ni shegeya ce tana sauke maganar taji wani kyakykyawan lafiyayyun maruka har biyu akan kyakkyawar fuskarta wanda suka sata dauke wuta gaba daya kawai ta dafe kumatun ta ta tsaya cak ko motsi bata yi kamar wacce aka kafata awajen dadda ce cikin bacin rai da bata taba ganin irin shiba afuskar dadda hannu dadda tadaga zata qara kaimata duka Azeema tayi saurin shiga tsakanin su dadda da har kwalla ta cika mata ido ta daga yatsanta ta nuna Ameesha da shi tace ke harni zaki gaya wa wadannan maganganun dan ke baki da hankali duk irin dawai niyar danke dake tun haihuwar ki har zuwa girman ki baki gani ba duk qoqarin  danake akanki shima ba kya gani to kulawar da nake miki ko yar cikina ban mata hakaba kuma wlh inki qara kiran kanki da shegiya saina karkar yaki agidan nan ni kinsan halin da nake ciki kinsan bakin cikin da yake kwance aqasan zuciyata shekaru da shekaru tun kan kizo duniya nake fuskan tara tashin hankali har kawo yanzu ta nuna kan qirjin ta saitin zuciyar ta tace kinsan meye acikin zuciyar nan taf take da bakin ciki kodan kinga bana nunawa bana son nunawa saboda banason inga kinshiga damuwa tun kina yar qaramar ki duk sanda kika tambayeni bana ce miki zan gaya miki amma saikin qara hankali duk wani abu danasan kina so shi nake qoqarin inga nayi miki duk dan inganki cikin farin ciki na gwammace in rasa koma meye inde ke zaki mallake shi hankalina ze kwanta kigaya min abun da nake miki na bata miki rai ko kuma kigaya min abun da kika taba nema kika rasa inde ina da halin yi kinsan ba abun da bazan miki ba amma ke kullum da kalar  tashin hankalin da zaki zo min dake saide in lallabaki inbaki hakuri bantaba daga muki murya ba bantaba dukan ki ba kuma bawai dan bakya min laifi ba kawai ina rabuwa dake ne saboda banason kina yawaita tunani wani abun amma duk da haka banyi miki ba ni kike kira da kingaji da ni ko in maida ke gurin da na dakko ki to bazan yi hakan ba in kin cika yar halak kije kiyi duk abun da zakiyi duk matakin da kika ga yadace da rayuwar ki kije kiyi duniya ce ta isheki riga da wando wanda bezo bama jiranshi take bare kuma  wanda yake cikin ta bazan qara hanaki abun da ranki yakeso ba inde harkinga hakan sai yafi miki dadi akan zama dani kina da wanda yafini aduniyar nan kuma kina ganin gwara kiyi nesa dani to qofa abude take kuma kisani daga yau ko kitafi kinzauna ni hadizatu ba abun daze qara hadani dake zan  zare hannuna akanki zan zuba miki ido bazan taba saki ba ko in hanaki bare kiringa ganin na takura miki kiyi duk abun da kika ga dama daman kice zaki bi bossay to inyazo kibishi ni ba inda zani kibar ni a inda kika ganni idan na zauna ba ke ai ba mutuwa zanyi zanci gaba da rayuwata har zuwa ranar da numfashi na ze qare inkoma ga mahallici na ta qarasa fada tare da sa gefen hannun rigarta tana goge hawayen da take riqewa amma saida ya zubo Ameesha da jikinta da gaba daya yamutu ba ita kadai bama hatta Azeema saida taji wani iri gaba daya abun be mata dadi ba Ameesha ce tashiga daga qafarta da tayi mata nauyi tashigawa  takawa ahankali zuwa gaban dadda tana zuwa kuma ta ta rungumata kamkam tare da fashe mata da wani irin kuka me tsuma zuciya cikin kukan tashiga cewa dadda ta dan Allah kiyi hakuri kiyafe min wlh sharrin shedanne nasan nima kaina nasan wasu abubuwan danake miki be kamata ba amma nima wataran bada son raina hakan take faruwa ba nima bansan me yasa nake yin hakan ba amma nasan kina qoqari dani kin riqeni kamar yanda iyayena zasu ruqeni amma nima dan Allah kifahimce ni dole fa indinga tunanin iyayena ba wanda zezo duniya bega iyayen saba kuma ba ace mishi komai akan suba kinsan dole ya shiga damuwa da tunani iri iri amman tunda ba kyaso daga yau in Allah ya yarda bazan qara yi miki maganar ba bazan qara cewa komai ba akai inde har hakan zeyi miki dadi nikuma nayi alkawari bazan qara taso miki da maganar ba kiyi hakuri dan Allah in Allah yarda daga yau bazan sake yi miki duk wani abun da ba kyaso ba shiru tayi taci gaba da kukan da takeyi dadda dafa bayanta tayi tare da dan bubugawa sannan ta dago ta daga jikinta tana share mata hawayen ta sannan tace kukan ya isa haka da sauri Ameesha ta girgiza kai alamar baza ta dena ba tace dadda kice kin hakuara kin yafe min sai inde na dadda tace na hakura Allah ya yafemana baki daya nima kiyi hakuri da maganganun da nayi miki rainane yabaci da har yasan gaya miki haka amma badan son raina ba Ameesha tace ni ba abun da kikai min nasan kowaye ma aka yimishi haka abun dazeyi kenan tana gama fadar haka tajuya tana kallon Azeema da suka manta da ita agurin tana tsaye tazama yar kallon tan kallonsu cike da tausayawa zataso taji me yasa suke rayuwa haka sukadai babu kowa atare dasu Ameesha ce ta katse mata tunanin ta da cewa besty kiyi hakuri dan Allah nabata miki lokaci kije kawai nazo wataran murmushi Azeema ta qaqalo tare da cewa laa besty wlh ba komai  nim daman ba tafiyar zanyi ba dan wuni natambayo agida danna ji kince zaki ne shiyasa amma yanzu tunda kin fasa shikenan muyi zaman mu anan tare da dadda

Ameesha tace to shikenan ma na gode besty dadda ta katsesu da cewa me yasa zaku fasa kuje mana ba komai ai komai ya wuce
Ameesha tace a'a wlh dadda ba inda zan sake tafiya inbarki inde ba makaran taba ko kuma kin aikeni amma ba inda zanje ina tare dake ako da yaushe
Dadda tadanyi murmushi sannan tace to ai shikenan nima daman nafison hakan yanzu kuzo ku qarasa awannan aikin kusa min duk abun da kukaga naware shi ta nuna musu inda ta ware wasu kayan tace kusakamin su acikin bakkon nan da to suka amsa mata ita kuma tace bari taje ta hade kayan tsakar gida tana gama fada ta fita
Suma zama sukayi suna ta aikin da aka sasu bawanda yaqara cewa komai a tsakanin su kowa da abun da yake tunani.......




#Comment
and
#share

More comment more typing
No comment no typing
Pls Likes


❤xeemat.....love❤
[3/2, 10:10 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER.....💅
           by❤xeemat....love❤

           🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

               
Allah ya gafartawa iyayen mu Allah yasaka musu da gidan aljanna Allah yabiya musu bukatunsu na alkhairi Allah yasa murabu dasu lafiya Allah yabamu ikon cigaba dayi musu biyayya   👏

                      Bismillah........
Episode 20🖋

               ******************

Saida suka gama komai harta katifar dakin su dagata sama babu komai aqasa komai sun kukkule wanda kuma zasu bayar sunfito dasu wajen tsakar gidan suna gamawa kuma suka fara taya dadda sai da suka gama koamai abun da suka bari awaje kawai wadanda zasuyi amfani dashi ne daga nan zuwa dare suna gamawa kuma suka hadu dukansu suka dora abincin rana saboda Azeema kuma suna da guntuwar fulawa bata qare ba sai sukayi dan wake da manja suka daka yaji Ameesha tace dadda kikawo dari muje musiyo salad da cabbage da sauran kayan hadin sai yafi dadi ko yakika ce besty daga mata kai tayi alamar eh dadda daki ta koma ta dakko musu dari da hamsin ta basu karaba sukayi kowacce tasaka hijabi suka fita atare kamar ya da qanwa saboda Azeema ta girmi Ameesha dan ita akalla zata iya yin ashirin amma bata da jiki sosai shiyasa ba aganin girmanta amma de duk da haka tafi Ameesha dan cika suna tafiya suna dan hirarsu Har sukazo bakin titi suna ahirin tsallakawa sukaji ance yan mata dukansu suka juyo suna kallon yaron da yayi musu magana da murmushi akan fuskar shi yace kuyi hakiri fa na tsare ku ahanya daman wancan mutuminne yace inyi muku magana yafada yana nuna musu inda wata jibgegiyar mota me tinted glass daga ganin ta ma kasan sabuwa ce yace musu wai kuje yana son magana da wannan yanuna Ameesha da hannu gaba dayan su kallon juna sukashiga Azeema ce tasamu qarfin halin cewa kaje kace mishi baza muzo ba yaron da aka aiko yace baiwar Allah gsky bazan iya zuwa ingaya mishi hakaba bakisan ko shi waye ba Sai yanzu Ameesha tasaka musu baki tace mishi ko ma dan gidan uban waye baza mu jeba tana gama fadar haka taja hannu suka bar wajen saida sukayi gaba Ameesha tace kefa ni tsoro nake ji wlh kar muje yayi mana wani abun Azeema tace ke matsalata dake wlh wataran tsoro yayi miki yawa ya isa yayi mana abun da Allah beyi manaba ne irin wadannan yan iskanne masu daukan mutane suje suyi lalata da su to mu ba irinsu bane ni wlh ma hakannan duk da banga mutu min ba naji natsane shi kawai haushin shi nake ta gama fada tare da buga tsaki kawai jitayi anjawo hijabin ta tabaya ashe tun lokacin da take bawa yaron amsa yana lure da ita yana ganin shishigin da takeyi saikace ita akace tazo da beyi niyar zuwa ba saboda daman ba halinsa bane shida duk tarin yan matan dasuke binshi baya kula su amma besan meyasa yarinyar tunda yaganta yaji ta burgeshi kuma shi bada so ma yace akirata ba kawai yanaso yayi magana da ita shiyasa ma yace akirata amma shine wannan banzar yarinyar zatazo tayi mishi hauka abun da yaron yafada mishi shine yasashi fitowa daga motar yana daf dasu kuma yaji still yarinyar tana zaginshi ranshi ba qaramin baci yayi ba dan ayanda zuciyar sa take raya mishi kawai ya jawota ya kikkifa mata maruka amma saide kash baya dukan mata arayuwarsa kwata kwata baze iya kai hannusa kan mace ba da sunan duka hakanne yasashi jawo hijabin ta saboda tafiyar dasuke yi shikuna bayaso yay tabinsu abaya shiyasa  yaja hijab dinta domin su dakata da tafiyar dasuke yi,
aikwa a fusace ta juyo dan ganin waye me yimata wannan iskanci hada ido sukayi da mutumin da ya wani hade rai kamar ma be taba yin dariya aduniya ba ashe duk yaji abun da suke cewa ita da tajiyo dan yin masifa amma kuma sa tafasa saboda ganin yanda fuskarsa tayi ba annuri maganar gsky yanzu ta dan tsorata da ganinshi dan ko ba agaya mata ba tana tunanin mutumin da take zagi ne kuma tunda taga haka tasan yaji duk abun da suka fada akansa tana tunanin taji ya kaseta da cewa ke yar gidan uban wacece kinsan waye ni dakike kwatan tani da yan isaka ko ke nace ina so uban me zanyi dake kucaka kawai me kama da zombie ko matan duniya sun qare aka ce miki zan iya kulaki da kike cewa kintsaneni nima ai bance ina sonki ba ni tunda nake arayuwata ma banta jin tsanar mutum ba irin wacce nake miki banza shasha sha mezubin aladu da wata mummunar fuskarki duk wanda ma yasoki wlh yayi asara sa arki daya ke macece nikuma bana dukan mata amma wlh da namiji ne yau sai yagayawa aya zakinta sai na canza miki kamanni Yanda ko uwar da tahaife ki bazata gane kiba itama cike da takaicin maganganun da yake gaya mata harda sako uwarta azancen yasa fusge hijab dinta da be saki ba sai yanzu da ta kwace cikin daga murya itama tace dakata malam karka kuskura ka qara sako iyayena azancenka yace innaqifa ko zaki dakeni wlh idan kika qara magana agunnan saina yi qasaqasa dake
itama daga murya tayi tace anyi din kayi duk abun dazakayi hannu yadaga Ameesha da tun dazu tazama yar kallo saide ta kalli wannan ta kalli wannan takasa magana
dasauri taruqe hannun shi tace dan Allah bawan Allah kayi hakuri ka rabu da ita na roqeka kaji plsss Azeema tace dalla kirabu dashi yayi duk abun da yaga zeyi da sai yayi danasanin taba ni wlh be kulataba kawai Ameesha ce takara cemishi kaji dan Allah plsss tsayawa yayi cak ko motse yakasa kuma bece mata komai kawai yatsaya yana kallonta sai can kuma yamaida idanun sa tare da azasu akan kyakkyawan hannuta yana kallon su ganin hakan da tayi yasata sakin shi ahankali tare da dan ja baya sannan tace I'm sorry sir tare da sunkuyar da kanta qasa shikam ya bushe agun ya kasa magana saida kyar ya iya daidaita kansa sannan yakalli Azeema dasai faman cika take tana batsewa nuna ta yayi da yatsan sa yace kinci darajar me daraja amma wlh da sai na canza miki kamanni marar kunya fitsarar riya shasha sha ballagaza yana kaiwa nan kawai ya juya yabarta yasan ko ba komai ya rama zagin da tayi mishi yatafi yana tunanin wlh da ba dayar yarinyar nan ba sai ya koya mata hankali sai ta kirashi da dan iskan da hujja yana qarasa wa wajen motar sa yabude ya shiga yatayar da motar ranshi na mishi quna da shi har yanzu bedena takaicin abun da tace mishi gaba dayama sai yaji ya tsani kansa duk shi yajawa kansa da ya kulasu da be kulasuba da duk hakan bata faru ba bare wannan banzar yarinyar tagaya mishi magana son ranta kuma ya rabu da ita be dauki babban mataki ba haka yaringa tafiya yana ta faman doka tsaki shi kadai.........


Bangaren su Azeema kuwa da ta gama cika da haushi harda kuka wai yazo yaci mata mutunci alhalin shine da laifi amma yayi mata haka Ameesha itama fuskarta da damuwa tace dan Allah kiyi hakuri ki manta da komai shima watakil ranshine ya baci akan zaginshi da kikayi kuma yajiki shiyasa shima yayi miki haka dan ya huce haushin shi tace kuma sai yaringa zagina ni irin haka nayi mishi basai ya rama da abun dana yimishi ba harda cemin fa ballagaza menayi mishi ko yaganni ina yawo da mazane ko ya ganni da wata shiga da bata dace ba Ameesha tace dan Allah kibar wannan maganar yafada ne kawai dan yabata miki rai kinsan daman ramuwar gayya tafi ta gayya zafi shiyasa tun farko nace miki murabu lfy muje kikace kar muje Yanzu gashi nan yazo yabata miki rai yabata mana lokaci dan Allah muje kar dadda taga mundade janta tayi zuwa inda me kayan miyar yake suna zuwa suka bashi kudin Ameesha ta gaya masa duk abun da suke bukata shikuma yabasu Ameesha tasa hannu ta karba suka juya suka nufi hanyar gida suna tafiya Azeema nacewa wlh in Allah ya yarda sai ya hadu da daidan sa ahanya sai ya hadu da wanda zeci mutun cinsa fiye da yarda yaci mutuncin ta itade Ameesha banda bata hakuri ba abun da take yi mata har suka qaraso gida Azeema bata dena mita ba da sallama suka shiga dadda dake daki

Please Login or Register in order to submit comment