Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kinqi fadar gaskiya dadda na kuka tace wlh bansan inda take ba bantaba ma ganin taba me yasa shi wanda ya aiko ku baze yarda dani ba wlh bansan taba wai me ta aikata muku ne da kuke so sai kunga bayan ta wani daga ciki yace mu bamu ta aikatawa ba oga ta aikatawa kuma shi ba acin bashinsa azauna lafiya inde kina son ranki kawai kigaya mana inda take sannan abarki da ranki amma jikar ki dole ne mu kasheta wani daga ciki yace kunga muna ta bata lokaci kawai mu aiwatar da abun da aka saka mu inatake ne wani yace tana cikin gidan mana baka ga sai shiri suke ba zasu bar gidan to kisani koma ina kika koma idan mu nakanki ba inda kika isa kishiga bamu nemo ki ba afadin duniyar nan da mamaki ta kalle su tace waya gaya muku zamu tashi yace yana tare da ku wanda yagaya mana kuma duk inda zakije kina tare da shi tunani ta shiga yi to waye yagaya musu kuma yana tare dasu to kode bossay ne yake cin amanar su to inba shiba waye yake kusa dasu wani ne yace kina tunani waye ko to bari kiji shi wanda zezo daukar taku shima dan cikin mune dan haka sai ki kula gaban tane yafadi tace jin ance wanda zezo daukar su tabbas kwa bossay ne shikenan yanzu ina za su dosa daman ta yarda zata koma gidan su bossay saboda ta guje musu daman ashe tayi gudun kura zata tarda zago bata gana tunanin ba taji ihun Ameesha datake waje a guje suka fita daga dakin saboda jin muryarta ita kuma jin ance wanda ze dake sune ze kasheta yasata sakin qara tare da cewa qaryane nasan bossay baze taba kasancewa haka ba sharri kuke mishi da sauri wani yajawo gashin kanta tare da maida ita cikin dakin dadda tabi bayansa tana roqonsa dan Allah yasaketa amma be saurare ta ba Allah yaso ma datayi wankan riga tasaka daman da rigarta ta shiga bandaki saboda saurin da takeyi ta shirya kafin bossay yazo da tuni irin wurgin da yake da ita in zanine da tuni yacire dadda tazo tana qoqarin kwatar ta amma yayi wurgi da ita agurin ta suma da sauri Ameesha ta kwace kanta daga gurin sa ta nufi gun dadda da gudu kafin ta qarasa kuma wani da yake bayan ta yadaga wani qaton qarfe yasauke sa akanta take a lokacin kwa ta baje awajen bata sake shurawa ba ganin hakan yasa suka tattaba ta suka tabbaar da ta mutu sannan suka shiga bincike dakin ko zasu samu wani abun da yakawo su amma basu samu dan haka kawai suka fita daga dakin tare da barin gidan ma gaba daya,

tana fada tasaki wani sabon kukan me tsuma zuciyar me sauraro hajiya ce ta jawota jikin ta ta rungumeta tana dan shafa bayant
gabadayan su babu wanda be tausaya mata ba lokaci nafarko da yafara jin tausanyi mace daman a kwai irin wadannan mugayen be sani ba shettima ba qaramin tausaya mata yayi shi daman ya dade yana jin tausayin ta hakannan ashede tana da abun da za aji taisayin ta din yarinya qarama tana fuskantar irin wadannan abubuwan,

saida kukan nata yadan tsagaita sannan hajiya ta raba jikinta da nata sameer ne yace waye bossay din tace shine wanda yakawo ni asibitin amma wallahi qarya suke masa baze taba aikata haka ba be kulata ba kawai ya miqe tsaye yace muje gidan naku zaki iya ganewa kai ta girgiza masa tace ai bama muje gidan wannan abun yafaru shettima yace muje kawai zan kirashi ai ina da number sa yayi mana kwatance hajiya ce tace a'a kar kuje yanzu kubari abi komai a hankali yanzu ku kirashi nan sai muji ta bakin shi kunga idan iyayen sa basu sani ba zakusaka su cikin wani hali tundade basu suka sakashi ba sameer yace haba hajiya suna da yaro irin wannan amma basu dauki mataki ba dole in koya musu hankali dagashi har su har ita kakar tata ma yau sai tayi bayanin *suwaye su*(my next novel) yaza ayi taringa saka yarinya damuwa bazata fada mata komai ba bani number yaron nidaga nan sai can dan bazan bari maganar nan ta kwana ba Ameesha ce ta sauko ta riqe hannun sa tace dan Allah kayi hakuri wlh ba ruwan yaya bossay aciki kar kayi masa komai da mamaki yake kallon ta yace ni ba abun da zan masa kawaide zan tambaye sane yafadi gaskiya ko kuma jikin sa yakagaya masa karkada masa kai tayi tace ni wallahi ba zarginsa sun fadi hakane kawai dan sunga yana so ya taimaka mana amma ba ahannun sa aciki be kulataba ya kwace hannun sa yace tare da zaro wayar sa ya miqawa shettima yace sakamin number sa karba yayi yasaka masa ya basa sannan yace muje hajiya ce ta qara dakatar da su amma ina basu tsayaba ganin hakan yasa tace sujira ta suje tare sutafi ma gaba daya har Ameeshan hakan ne kawai yasa suka dakata sannan ta shirya ta dan gyara Ameesha suka fito falo motar shettima suka nufa gaba daya shettima ya shiga mazaunin driver shikuma ya shiga gefe yayin da sukuma suka shiga baya sannan shettima yazaro wayarsa ya kira bossay din bugu daya kwa yadaga yana dagawa ya gaida shi ba yabo ba fallasa ya amsa masa daga nan kuma yace kaji nace zan kiraka ko to yanzu de gata nan lafiyar ta qalau tasamu lafiya yanzu haka ma muna hanya kwatancen unguwar ku da gidan zaka yimana cike da jin dadi da gar yana iya jiyo shi ta wayar ya kwatan ta musu daga suka yi sallam sannan yatayar da motar suka fice daga gidan suka dau hanya zuwa gidan su bossay.........✍
[4/8, 10:14 AM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode 85-86-87

         """"""""""""""""""""""""""""""""

sun qarasa lfy kamar yanda ya kwatanta musu haka yabi kwatancen har sukaje unguwar gidan ba a lungu yake ba kuma unguwar ba geto bace shiyasa basu sha wahalar gane gidan ba abakin gate din yayi horn me gadi ya wangale musu suka shiga ciki suna shiga bayan yagama daidaita parking din suka fito gaba dayan su sai shettima yaqara dauko wayar sa yace bossay sun qaraso yazo ya shiga dasu kamar jira yake kwa sai gashi ya fito sai faman wangale baki yake idon sa suka sauka akan Ameesha take yaqara fadada murmushin sa yana zuwa yaqara sakar mata wan wani qayatacen murmushi itama murmushin ta sakar masa duk abun da suke akan idom sameer shima tunda yaron ya fito ya kafe sa da ido

yana zuwa yayi musu sannu da zuwa tare da gaida su amma be qara gangancin qara mikawa sam hannu ba sai ya gaida shi amma yaumade ga mamakin sa be amsa ba sai gudunmawar bazan kallo da yasamu shi daman yama yi mamakin ganin su tare bayan kuma yace zai sauki mataki akan yarinyar to kuma ko meye yakawo shi oho bashida me bashi amsa shiyasa yaja bakin sa ya tsuke ya gaida hajiya da shima yayi mamakin ganin ta duk da kamanni sunnuna masa kamar da suke da shettima,
sameer ne ya dunqule hannun sa yanaso yakai masa naushi duk ba wanda ya lura dashi sai Ameesha da sauri taje gefen sa yanda ba wanda ze fahimta ta zura hannun ta cikin nasa beji riqe hannun sa da tayi na sai jin wani irin shouck da ya kaima sa zira tunda ga qasa har sama wanna ne ya ganar dashi ta riqe shi dan kallon ta yayi ta qasan ido tare da janyewa,

damqe hannun sa tayi sosai tana bude dunqulewar da yayi yagane me take nufi ta qasan ido yake kallon ta amma ita bashi take kallo ba qasa take kallo bayan bossay yagana gaida hajiya sai ya maida kallon sa ga Ameesha da fara'ar sa yajuyo ze yi mata magana amma sai maganar ta ruqe sakamako abun da yagani Ameesha riqe da hannun maqiyin ta to hakan me yake nufi kode ya boye mata be gayamata ba yana gama ayyana tunani ranshi a mugun bace yake kallon idon sa har suncan za kala ga na bakin cikin besan dalilin yin hakan ba ga na kishi dayake jin zuciyar sa nayi masa barazanar fitowa daga qirjinsa shikansa besan lokacin da ya daka mata tsawa ba yace Ameesha kina da hankali kuwa kinsan wanda kika riqe yanzu to kaf duniya baki da maqiyi irin sa ki gaggauta nesantar shi tunbe kai ga halakaki ba,
jin wannan batun sai yaqara harzuqa sameer shi besan daman danshi yazo gidan ba amma zezo yana gaya masa maganar banza kwace hannun sa yayi daga nata tare da shako wuyan sa ze fara kaimasa duka da sauri shettima ya shiga tsakanin su yana cewa dan Allah ya isa haka kabari nuqarasa ciki ayi magana mana ko kallon inda yake beyi ba kuma  yaqi sauraronsa  tare da ture shettima gefe yafara kai masa naushi shima bossay be tsaya kallon sa ba yadaga hannu ze kai masa nasa naushin dan shima zuwa yanzu a wuya yake bayajin ze iya daga masa qafa saide duk abun da za ayi mishi ayi mishi Ameesha ce ta ruqe hannu tana girgiza mishi kai dan Allah yaya bossay kar kayi haka tana qarasa fada ta shiga tsakanin su tare da rungume bossay tace plsss ka qyale shi cak bossay ya tsaya be kara dago idon ma yakalle sa ba idon sa nakan ta,
shima sameer anasa bangaren dakatawa yayi saboda hajiya dake janye sa sakin sa yayi sai yaji ma har yarinyar ta bashi haushi gaba dayan su ji hake kamar yayi musu dukan tsiya daga shi har ita din dan ma ze taimaketa shine take masa irin wannan abun tasan gaskiyar magana amma tana dannewa tana goyon bayan sa,
hajiyace ta kalli su Ameesha tace 'yata muje ciki be kamata mu tsaya anan ba ko raba jikin ta da nasa tayi hajiya tayi gaba shettima yace sameer suzo su shiga sai kawai yace masa yaje shi ba inda zashi bossay ya ruqo hannun Ameesha suka fara tafiya duk yanda shettima yaso samerr yazo su shiga amma yace baza shiba hakura yayi ya rabu dashi yabi bayan su suna daf da shiga qofar falon Ameesha taja burki ta tsaya kallon ta sukayi gaba daya bossay yace ya akai juyawa tayi tana kallon sameer da ya tsaya sai gaban mota sai faman ciccije bakin sa yakeyi bata ce musu komai ba kawai ta kwace hannun ta daga na bossay ta kwasa aguje ta koma inda yake a tsaye,
ganin hakan yasa hajiya cewa rabuda ita muje kawai zasu taho tare shettima yace ai yace baza shiba da ta rabu dashima kawai basai ta wahalar da kanta ba hajiya tace naji muje kawai,
Bossay da ransa keyi masa suya har yanzu yaqi shiga sanan ya kalli hajiya yace idan ya cutar da ita fa ni ba inda zani inbarta anan waje daga ita sai shi yafada yana niyar bin bayanta shettima da yasan muddin yaje zasu iya barkewa da wata kokawar yace masa a'a ba abun da zeyi mata ya janye duk wani qudirin sa akanata baze taba ta ba kaide kayi hakuri muje kawai nan ma kin amin cewa yayi saida hajiya tasa baki badan yaso ba  sannan ya yarda suka shiga yana shiga yana qara waiwayen su ahaka harsuka shige,

tana zuwa tana tsaya tana kallon sa wani banzan kallo ya watsa mata tare da kawar da kansa gefe dan shi haushin ta yake ji ze yake kamar ya bibbigeta ko uban me yakawo ta tayi mishi cikin rairai da murya da take son yin kuka tace dan Allah kazo mushiga kar kayi haka mushiga wlh ni nasan bossay bashida laifi kuma zakace nagaya maka kazo mushiga tafada tana jan hannun sa ko gezau beyiba yace malama sakeni ko dole ne sai na shiga nace bazan shiga sai kin min dole budar bakin ta sai tace mishi eh kallon ta yayi yace dole zakimin eh din taqara ce mishi girgiza kai yayi yace to bissmillah sai kiyi min dolen ingani in kana kaunar iyayen ka in kana kaunar annabin ka dan Allah kataho muje dan darajar annabi bude mota ma yayi yana qoqarin shiga sai kawai ta fashe da kuka wai kai baka qaunar Allah aitayi maka magiya amma kaki ji ace maka dan darajar annabi amma kaqiyi shikenan tana fada ta sake sa tare da barin wajen tana shassheqar kuka ji yayi duk ba dadi abun da yayi har yarinya qaramace take cewa baya qaunar Allah idna beje ba kuma ahaka zata ringa kallon sa marar qaunar Allah dan haka kawai sai ya yanke shawara bin bayanta tana daf da shiga taji motsin mutum abayan ta dakatawa tayi da tafiyar tare da jiyowa taji dadin ganin sa dan haka atake ta saki murmushi tana cewa yau ko kaifa ashede kana kaunar Allah da manzon sa nazata ai baka kaunar sune inje inbada labari kawar da Kansas yayi daga gareta yace ke ni banason surutu muje inkuma surutun zakiyi sai in koma abuna tace a'a yi hakuri wallahi nayi shiru bazan qara magana ba tafada tana shiga inda taga sun shiga,
its hakan nan tunda taga ya damu akan rayuwarta dajin kuma yana fasa yimata komai saboda tausayin ita marainiya ce yasa taji duk tsanar da take masa ta ragu kuma tanaso ya shiga maganar saboda tasan dadda naganin shi idan ya zare mata izata fadi gaskiya saboda dadda akwai tsoro daman gashi zubin samudawa.....,
suna shiga suka ga har sun zazzauna a falo suna jiran shigowar sa suma guri suka samu suka zauna amma Ameesha sai ta koma kusa da bossay ta zauna faruq ne ya fito yace gata nan zuwa dadda ce bata falon akaje aka kirata badadewa sai gata ta fito batayi tunanin ganin jikar ta taba ahalin yanzu tana ganin da murnar ta taqarasa gurin ta tare da rungumeta tana cewa Alahamdulillah ashe shalele nace ta dawo gare ni yaji kin naki Allah yasade babu inda yake miki ciwo de ko duk tabi ta sussuce sai faman tambaya take jero mata tare da dudduba jinki ta ko zata gano wata matsala,
Ammi ce ta katseta dacewa dadda ita kadai kika gani ne baki ga baki ba kuma gurin ki sukazo fa juyowa tayi tana kallon su daya bayan daya batare da tace komai ba sai daga bisani tace nagan su mana amma ni bansan suba nasan de wannan bashine likitan Ameesha ba wannan kuma marar mutun ci nana da bashida tausayi wanda sanadin sa jikata ta kusa tasa ranta duk magiyar da nake mishi be duba girmana ba ya watsa min qasa a ido yanzu kuma me yakawo shi nan wannan ce de bansan taba ta nuna hajiyar shettima,
hajiya ta dan sakin murmushi irin nasa na manya tace haka ne ni baki sanni ba amma wadannan duk 'ya'ya na da mamaki dadda ta kalle ta tace har wannan me jan kunnen me zubin 'yan can amma de beyi koyi dakuba duk da bansan halinkiba amma naga alamar zakiyi mutun ci amma shi ya akai yazo ahaka ko ubansa ya biyo yar dariya hajiya tayi tace eh mahaifin sa yabiyo shiyasa kika gansa haka,
sameer da yagama cika da maganganun dadda yace hajiya kidena biyewa wanna tsohuwar me sufar aljanun da muyi abun da ya kawo danni ina da abun yi,
dadda da taji abun da yace tace saide uwarka ce me kama da aljanun amma bade ni ba ja'irin yaro kai kai ba acemaka me kama da aljanun ba sai kai zaka cewa wani alajani to uwarka uwarka nace ko baka jiba marar kunya kai dadda fa ta fusata dan ji take kamar ta tashi ta rufe sa da duka,
Ammi ce ta katseta da cewa dadda dan Allah ya isa haka kiyi shiru ki rabu dashi muyi abun da ya kawo su shiru shettima ne yadan yi gyaran muray sannan yace daman abun da yakawo mu ba komai bane illa muna son kibamu labarin ki ke da jikarki shin ina iyayen ta suke wani irin faduwar gaba dadda taji bata san lokacin da ta mike tsaye ba tana nuna su da yatsa tace labarina labarina labarina fa kukace da kuma iyayen ta ko to ku shake nin ingaya muka daman abun da yakawo ku kenan ku asuwa to wlh tun muna sheda juna ku tashi kubar gidan nan inbanda muna furcima uban wa yagayawa muku bata da iyaye baka ga iyayen taba ta nuna Ammi kai wallahi ma ban yarda dakuba sai kun gayamin wanda uban da ya turo ku ko kuma hukuma ta rabani daku daga ganin yarinya shine zaku wani sakota agaba wai kunzo neman sanin wacece ita to malafar ubanku kuku duka ban cire kowa ba
tafada sai faman huhura hanci take sai kace zata rufe su da duka,
Sude yau sunga ikon Allah daga magana ko bayanin ma basu gama ba ta hausu da masifa dukan su shiru sukayi kowa na tunanin ta inda ze fara mata magana dan ta basu tsoro har suna tunanin ma kode ba ita kadai bace,,😂 (nace ba ita kadai bata tare da kowa bata tare da komai ba komai akanta kawai iya masifa ce irin tata bakusan halin ta bane shiyasa har kuka kwaso qafa kuka zo maga yanda zaku qare da ita).....✍
[4/8, 11:55 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode 88-89-90

         """"""""""""""""""""""""""""""""

A harzuqe sam ya tashi zeyi kanta shettima yayi saurin riqe shi nunata yayi da yatsa yace wallahi kar kisake zagar min iyaye wai kinma san waye ni kike gayawa mutane magana dan kinsamu ma anzo inda kike wallahi daman tun ranar da na fara ganin ki naso na koya miki hankali kawai na dan daga miki qafane saboda baki san niba amma ba dan haka ba sai nayi qasa qasa dake tunda naga kanki rawa yake notukanki sun fara kucewa kina bukatar a daure miki su (to fa ummu kulsun kina ina  kizo ki taya shi ku daure mata su da kyau lol😃)

kawai sai jin kukan dadda  sukayi zama tayi dirshen aqasa  tana cewa nashiga uku ni hadizato nashiga uku na yanzu kuna jin wannan yaron yake gaya min magana son ransa yana zagina bawanda ze iyayi masa magana ni zaka koya wa hankali saboda baka da kunya ka kalli tsabar idona a haife na haifi uwarka ma amma kake min zagin uwa da uba dake baka da mutun ci baka san meye mutun ci ba arayuwar ka to wallahi iyayen ka sunyi asarar haihuwar ka juyawa tayi ta kalli hajiya tace yanzu kema agaban ki yake yiwa mutane gitsara amma baza ki dauki matakiba kika zuba masa ido kike kallon sa to wallahi kinyi asarar haihuwar sa Allah wadaran naka ya lalace maida duban ta tayi ga sameer da jira yake kawai tagama ya hau kanta dan yaga alamar sai ya koya mata hankali zata shiga taitayin ta,
dadda ce tace dan uwar ka inka cika dan halak kazo ka taba ni anan ka dakeni da wallahi ko dan uban waye kai sai nasa an daure ka wallahi hukuma ce zata rabani da kai idan kayi gangancin tabani ja irin yaro kawai me jan kunne daman ance ku masu jajayen kunnuwan nan baku da mutunci baku da kunya bakusan darajar manyan ku bama bare kuji ta wasu to inka fasa duka na Allah ya tsine maka alabarka kazo ka dake ni nace inga qarshen rashin kunyar taka tafada tana nuna masa kanta da yatsanta kuma har yanzu kuka take bata dena zubar da hawaye ba kuma aranta ashe tana sane take nusu haka so take sum fusata subar gidan batare da sunji abun da yakawo suba amma taga basu da niyar tashin wani zagin ta kuma wawurowa ta maka masa da sauri yayi kanta dan yanzu ta kaishi qarshe baze iya jurewa ba ganin hakan yasa Ammi saurin tashi itama tare da shan gaban sa ta wara hannayenta tana kallon sa tace haba dan albarka rabu da ita kar sharrin zuciya ya debeka kaje kayi abun da zakazo kana da nasani koma kazauna dan Allah ka rabu da ita kabar mana komai a hannun mu zamu ji da ita inma da yiyuwa kaiwai kafita waje karabu da ita sai kayi mata uzuri haka take gigin tsufane yake dibanta muma hakuri nuke da ita idan tafara irin wadannan surutan sai de kayi mata shiru in bahaka ba kuma bakinta baze taba mutuwa ba haka zataitayi bata gajiya  da magana kama hannu sa tayi ta maida sa ta zaunar be mata musuba ya koma yazaun yana ta faman damke hannun sa dan kawai jira yake yasamu ya kaiwa wani bugu saboda hannun sa kaikayi yake masa gashi wancan banzan yaron yabata masa rai an hanasa dukan sa kuma gashi wanna tsuhuwar me kama da albasa tazo itama tabata masa kuma yanzu ma an hanasa hukun tata anya ze iya jurewa batare da yadau wani hukuncin akaiba ammade sunci darajar wannan matar fa tabashi hakuri da kuma darajar hajiya amma badan haka sai ya kunbura musu fuskokin su ta yanda su dakansu basu iya  gane kansu da kansu ba bare wani yagane su sai faman tattaune bakinsa yake kamar ze fasa su duk abun da yake akan idon dadda dan zuwa yanzu ta dan fara jin tsoran sa duk taurin kanta ta dan tsorata da yanayin sa tasan badan anbasa hakuri ba sai yayi qasa qasa da ita kuma daman ita cika baki ne da kurin banza ko agidan ubanwa take da kudin da zata hada sa da hukuma ita ba kowan kowa ba amma dan qarfin hali take yi masa wannan kurarin(hmm kyade ji dashi duk kwace kwacen kide sai ki gaya mana yau dan ba inda zamu sai munji komai)

Ammi ce ta qarasa kusa da dadda ta tsugunna sannan  tace haba dadda wai meyasa kike hakane dan Allah ki tsaya ki qarasa sauraron su daga bekamata kikamasu da fada ba kama ta yayi mubi komai asannu muma nan da ki ganmu muna so muji labarin ko ke wacece daman amma ganin bakya so kifada yasa muka zuba miki ido kuma daman jira naked aban su yadawo watakil shi in yatambaye ki zaki gaya masa kuma daman yanzu lokaci yayi tunda yarinya tafara mallakar hankalin ta kamata yayi ace kin sanar da ita ko wacece tunda abun na damunta har haka amma kinki gayawa kowa kinqi sanar da ita be kamata kiringa riqe komai ke kadai ba tunda yanzu gaba dayan mu munzama daya kamata yayi musan halin da kike cike yanda zamu iya taimaka miki  tunda nasan kina bukatar taimako inbaki manta ba tun lokacin da na taimakeki nasan dole kina cikin wani irin hali amma kinqi gaya wa kowa labarin ki yakamata ki kawo qarshen wannan boye boyen naki taqara sa fada tare da miqewa ta koma kan kuje ra tana jiran taji me daddan zatace,

Dadda de shiru tayi sai daga bisani kuma ta dan tsagaita da zubar da hawayen da take yi sanna tace nifa bansan suba bazan gaya musu ba kude da na dade da ku zan gaya muku na muku alqawari lokaci naked jira lokaci na cika kuma ko baku tambaye ni ba nida kaina zangaya muku dan haka ku kwantar da hankalin ku,
ku kuma zaku iya tashi kutafi mungama magana ba huri min kubane kuje kuyi abun da yake gaban ku in kuma turo ku akai dan kuzo ku cutar damu to bismillah Allah yana tare damu zeci gaba da kare mu kuje kugaya duk wanda ya turo yadena boye kansa yakamata yazo ya fuskan ce ni da kansa a shirye nake

Please Login or Register in order to submit comment