Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kawai muci gaba da addu'a kamar yanda yace din ai ba abun da yafi qarfin Allah idan su sunfi qarfin shi suna takama da mulkin su ai Allah yafisu tunda shi yabasu kuma ze iya kwacewa dan haka kawai mucigaba da addu'a ta qarasa fada fuskarta ciki da damuwa,
saleem ne yace mama gaskiya be kamata ba mu tsaya zaman jira yanda auta tace ina ganin hakan shine kawai mafita ita macece zata iya shiga gidan batare da kowa yagane da wata manufa tazo ba inaganin kawai mushiryata taje ta gano mana shi inda yiyuwa ma zata iya fito dashi din koda za adau lokaci kuma zata tafi da waya duk halin da ake ciki sai ta ringa sanar damu in Allah ya yarda ba abun da zai sameta sai alkhairi kuma in Allah ya yarda zamuyi nasara akai mama tadan numfasa sannan tace to ni baqin yarda bane banayi ina guje mana abun da kanje yadawo kar muje ganin naiman gira arasa ido hakan yazo yazame mana wata masifar tundade kunji abun da mutumin nan yafada kuma yafimu sanin masarautar tunda kukaji ya hana kowannen mu zuwa to yasan masarautar tana da hatsari dan haka mubar komai agurin Allah ,
Azeema tace mama dan Allah kar ki hanani in Allah ya yarda ba abun da zai farau kawai mude amincewar ki muke bukata danni a yanzu ma ashirye nake da tafiya dan ganin nagana da mahaifina ina so inganshi kuma koda bansamu gurin zama ba agidan ai zanganshi kuma lokaci zuwa lokaci zan ringa zuwa gidan daga haka har nasaba amma dan Allah mama kar ki hanani kinji mama mama shiru tayi bata ce komai ba shima saleem baki ya shiga bata suna tabata hakuri da roqon ta yarda ta amimce da zuwan nata,
bayanda ta iya dole suka shawo kanta ta yarda ta amimce saboda itama tanaso taji ahalin da yake da kuma wane irin aiki yake musu Allah yasade ba me wahala bane,
sunji dadin amincewar tata sosai Azeema harsa dan taka rawar jin dadi bayan tagama ta zauna kusa da yayan nata tace yaya to ya kake gani taya zan shiga gidan mama tace kingani ai shiga gidan ma madai wata matsalar ce tundade gidan sarauta ne dan haka ko ina za asa masu tsaro kuma suna ganinki dole sai sunsan daga inda kike da abun da gakawo insun tambayeki me zaki ce musu saleem ne ya gyara zaman sa yace hakan ba me wahal bane mama sannan ya maida dunbasa ga Azeema yace auta kinsa taya zaki shiga tace karkada masa kai tare da cewa a'a yaya cigaba yayi da cewa zakije qofar masarautar ne ki tsaya azin me neman alfarma dan kayan jikin kima sai kin canza ki samu tsofaffi sosai kisaka sannn kiyi kalar tausayi kar kibari wani me tsaron yaganki ko dan aikin gidan kibar har sai kinga wanda yayi kama da dan gidan wanda kina ganinsa kinsan daga ciki yake inda so samune ma kisamu mace mace sai tafi tausayin ki akan namiji idan kuma baki samu macen ba ki gwada yiwa namijin magana inbaki dace akansa zaki dace akan wani kingane me naked nufi tace eh yaya nagane kuma zanyi qoqarin yin hakan in Allah ya yarda shiga gidan kamar anyi angama ne mama de najin su har suka gama shirye shiryen su bata saka musu baki kawaide tana addu'a aranta Allah yasa adace batare da wata matsalar ta qara faruwa ba miqewa Azeema tayi tace bari inje inshirya yaya kallon ta mama tayi tace ke baki da hankali ya za ayi kije daga gama magana saurin me kike kibari sai gobe ko jibi ma ba sai a shirya komai a tsanake ba ki fita da sassafe tace mama yanzu ma ai rana batayi ba zan iya zuwa wlh ko yaya tafada tana kallonsa kai yadaga mata sannan yace hakane ai gwara ayi komai da wuri mama tace Allah ba inda zata yau sai gobe in kuma kuka takuramin a fasa zuwan ma gaba daya da sauri Azeema tace a'a mama baza ai haka ba na hakura zuwa goben wallahi naso zuwa yau din amma tunda baki amince ba to na hakura nabarwa goben mama tace karma ki yarda din ina ruwana saleem yace ti shikenan Allah ya kaimu da rai da lafiya ai goben karma yauce zakiga tazo ba wuya agurin Allah daga nan de suka cigaba da tattaunawa akan yanda lamarin ya faru da mahaifin su agidan sarauta ta wani bangaren sunji dadin jin inda yake ta wani bangaren kuma basuji dadi ba yanda yazamo bawa gashi ance baze yaba fitowa ba saide wani ikon Allahn hakade kowa da abun da yake ciwa sun kasa barin hirar kuma basu tashi daga wajen ba dan saleem ma cayayi baze je aikin ba yau yafasa fita basu bar wajen ba har saida akafafara kiraye kirayen sallar azhar suna gun azaune sunma manta da zasu dora abin ci rana saida sukaji kiran sallah sannan mama tacewa Azeema taje ta dora musu ko taliyace ita kuma bari taje tayi sallah shi kuma saleem ya tashi ya nufi masallaci nande kowa gakama gabansa,

_______________*bossay*

gaba dayan su babu wanda labarin be girgiza shi ba amma banda dadda da ita daman ba yau tafara jin irin wannan barazanar tasu ba,
hajiya ce tafara cewa to kinji shiyasa nace mufara sauraron sa yanzu gashi ba shida laifi aciki Ammi tace yana da laifi mana me yasa be sanar damu ba ko nikadai yasanar taya za ayi sugane ya sanar dani inde bada aljanu suke aikiba ai ba yanda za ayi su sani da da yafada ai da tuni mun magance yanda za ayi da ita yarinyar da tun aranar zansa adauko ta da bata shiga halin da tashiga ba yanzu,

Ammi kiyi hakuri wlh ina tsorone shiyasa ban fada miki amma kullum abun yana raina dan Allah ki fahince ni wlh babu komai araina cewar bossay dan Allah kuma ku gafar ceni yafada tare qarasawa kusa da Ameesha da ta durqushe agun tana faman kuka dan Ameesha kiyi hakuri ki gafar ceni ki fahimceni banyi komai dan ganin na cutar da rayuwar ki ko kadan bani da niyar yin hakan a cikin raina girgiza mishi kai tayi cikin kuka tace babu komai ni banga laifin ka ba bakai min komai ba ni daman na yarda dakai nasan bazaka taba cutar dani dan haka inde akain nane kabar damuwa rungumeta yayi sannan yace nagode nagode miki Ameesha Allah ya kareki daga sharrin su sannan ya sake ta ya qarasa kusa da dadda itama yabata hakuri fuskarta ba yabo ba fallasa tace nasan baza ka taba cutar damu ba shiyasa na yarda dakai tun farko kuma daman nasan hakan zata faru duk wanda suka ga nayi kusanci dashi sai sunsan yanda sukai suka rabani dashi shiyasa da suka gaya min bakin ku daya da farko har nafara tunanin ko kaine amma daga baya nagane bakai bane sunyi hakane kawai dan su shiga tsakanin mu muqi zuwa inda kake shiyasa ni kuma na amince daku amma yanzu komai ya wuce ka kwantar da hankalin ka tunda sukayi haka yanzu wasan namu ze fara tumda gaku nasan zaku taimakamin na cika burina tafada tana binsu da kallo daya bayan har ta sauke su akan sameer da yatafi tunani yana yiwa maganar bossay dalla dalla dan yanso yayi nazari sosai yagano wani abun game da maganganun bossay bema san tana kallon sa ba saida tace me jan kunne yasan da shi take dan haka sai kawai yadan kalleta kadan murmushin yake ta sakar masa sannan tace ka basai ka kaini gun hukuma ba ka gyara zan baku labari na saboda na yarda daku amma fa ba komai zan iya warware muku yanzuba kai ya daga mata kawai hankalin ta ta mayar ga sauran ma taga kowa ya ita ya zubawa ido suna jiran suji ta bakin ta,
sameer ne ya kalli bossay yace zamuyi magana dakai sannan kuma dole ka zafafa tunanin akan sanin waye na kusan kusan ka sai kaduba agaba daya wandan da kake tare dasu waye kukafi mu'amala dashi wanda har za ku iya hada alaka dashi kamar yanda yace tahakane kawai zamu iya gano ko waye saboda yayi maka magana me harshen damo nasan inde ka zauna ka nutsu zaka gano waye inma baka gane ba ni zanyi maka wasu tambayoyin in mun zauna kagane ko kai yadaga masa cike da gamsuwar maganar sa shettima ne yace nima abun da nake tunani kenan dole ma yakasan ce koma waye yasanshi din kamar yanda yafada sannan kuma kayi tunani tunda ka fara tunanin dauko sun ba da wanda ka zauna kayi maganar da shi ba wanda yasan zakaje ka dauko tan bakuyi maganar da kowa ba yanzu ba lokacin tunani bane cewar sam kawai zamuyi wannan maganar daga baya yanzu muna sauraron ki yafada yana kallon dadda dan murmushi tasaki da basu gane ma'anar sa ba itakadai tasan ma'anar abunta saboda dan tattaunawar dasukayi ita harta dan gano wani abu amma itama zata qara tunanin akai bayan tagama basu labarin dan gyaran murya tayi tare da gyara zamanta tana fuskan tar kowa,
duk shiru sukayi suna jiran jin tabakinta kowa ya qagu da yaji labarin.......✍


*YANDA LABARIN YAKE*

kamar yadda kukasani de ko ince nake gaya muku nice kakar khadija "khadija shine asalin sunan Ameesha wanda yayi daidai da sunanan sunan mu daya iyayenta suka saka mata Ameesha ba 'yar shigiya bace kuma ba 'yar tsuntuwa bace kamar yanda wasu suke tunani itama kuma take tunanin hakance saboda kinsanar da itan da nayi game da iyayen ta Ameesha jinina ce jikata tace nice na haifi mahaifiyar ta asalina ni 'yar garin damaturece a bagwadas nake dazama daga baya kuma aure ya dawo dani gombe saboda kasuwancin mijina tunda muke dashi Allah be bamu haihuwa ba ahaka muke rayuwar mu cikin kwanciyar hankali kuma muna da rufin asirin mu daidai gwargwado saide ba da mubiyu muke rayuwarmu daga ni sai shi muna cikin haka wataran kwatsam me gidana ya shigo min da wani kyakkyawan yaro cikin gidan dan da farko ma nazata aljanine dan qinyarda nayi da yaron saboda kyan shi saida gabaya malam yayi min bayani akansa sannan nayarda muka shiga cikin falo da yaron anan yake sanar dani cewa ankadai madai mahaifiyar sa ne abakin titi yana kan hanyarsa ta dawowa gida yaci karo da mutane antaru akanta yake tambayar me yafaru ake gaya masa ga mutumin da yakadaita yanzu za azo da motar asibiti atafi da ita yaron tunda yagansa sai ya makale masa yaqi yarda yaje gun kowa sai gurin shi ahaka har motar ra qaraso aka dauki matar inda yake tambayar inda matar da yaron suke wasu daga cikin mutanen suke suma basu san daga inda take ba kawai wayar gari sukayi suka ganta agun ita ba me hankaliba kuma ita ba mahaukaciya ba dan haka babu wanda yasanta alokacin da motar ta iso wajen me gidana ya mika musu yaron amma sai yaqi zuwa ya maqale masa daga nan kawai sai mutumin ya karbi number me gidana yaceze kirashi duk yanda akeciki ze sanar masa idan ta farfado sai yaje ya kaimata danta sannan aji daga inda take ahaka sukayi sallama saide kash ansamu matsalar tashin sanin mutumin a ina yake kuma shi me gidana beye azancin karbar number mutumin ba suka rabu tundaga ranar shiru shiru shiru muna tajira tsammanin kiran bawan Allahn nan amma be kira ba tun muna sa rai har mukazo muka cire rai da kiransa tunda daman bamu da 'da bamu taba haihuwa ba kawai sai muka cigaba da kula dashi tamlar dan da muka haifa da cikin mu haka muke bashi kulawa har yakai lokacin shiga makaran ta muka saka shi makaran tar masu kudi dan yafi samun ilimi sosai muhaka kwatsam sai ga ciki ajikina Allah yaban alokacin da muka gama cire rai da haihuwa amma sai gata ahaka muka cigaba rainon cikin har Allah ya saukeni lafiya muka haifi mace wacce muka saka mata suna NADEEYA, muka ci gaba da kula dasu gaba dayansu kamar yaran mu da suka taso sai suka taso da shakuwa me qarfi kullum suna tare suna manne da juna har suka girma inda alakacin yaron yagama makarantar sa har jami'a ita kuma lokacin ta gama primary tun lokacin muka fahimci dukkanin su basu da abokan rayuwa ita bata kula ko wane saurayi shima kuma baya kula mata duk da irin kyaun da yake dashi ga 'yan mata nata rububunshi amma shi kwata kwata basa gabansa har sukai wani minzali munyi munyi kuma akan kwannen su ya fito da wanda yake so ayi musu aure amma bawanda yayi ko yunqurima saide ma suce su basu samu wanda suke so hasalama ita nadeeya cewa takeyi ita bazatai aure ba ganin haka yasa muka yanke shawara ni dashi akan mu hada su aure kawai tunda sunqi fito da wadan da suke so sameer da bamu taba sanar dashi ko waye shiba sai lokacin muka sanar dashi asalin sa lokacin yasha kukansa muka bashi hakuri daganan kuma muka gaya masu abun da mukeso muyi duk bamusha wahala ba dukansu suka amince ba dau lokaciba muka daura musu aure duk da alokacin yafara samun kudinsa nakansa saboda be samu aiki ba sai me gidana ya dora shi kan harkar kasuwan ci akasuwa duk da yana da kudi kuma hakan be hana me gidan cigaba da yi musu hidima ba dan hatta gida ma shi ya siya masa sannan muka zuba musu komai duk abun da zasu bukata saida muka zuba musu acikin gida hatta abincima me gida nane yake ajiye musu ahaka suka fara rayuwar aure tun basa son junan su har suka fara so soyayya me qarfi ta shiga tsakanin su............✍


*naso inyi yafi haka yawa amma matsalar wayata ba caji dole intsaya anan saide zuwa dare kuma idan Allah yakaimu zan qoqarta in qarayin wani saboda gobe make so ingma hada komai intafi hutu sai bayan sallah kuma*
[4/11, 6:46 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode 97-98-99

      """""""""""""""""""""""""""""""""""

  Bayan auren su da yan watanni yasamu aikin banki ga kuma kasuwan cinsa da ya bunqasa Allah yakawo masa kudi ta ko ina saide masha Allah alokacin ya canza mana gida tanka meme gaba dayan mu part dinmu daban nasu daban anan muke rayuwar mu cike da farin ciki da kwanciyar hankali adan qanqanen lokaci kuma komansa yaqara bunqasa ga kasuwan cin sa da yakeyi ya dora wani akai inda gefe kuma yake zuwa aikin sa harde yafara ajiye kudaden tare da filaye babu abun da be taraba dan aqalla yana da wajen gidaje goma sha filaye kuwa bansan adadin su ba saide matar sa tun alokacin mukai mukai da shi akan yaqara aure amma yaqi yace shi mata daya ma ta isheshi haihuwa kuma ta Allah ce Allah ze basu za suyi hakuri shi ko ba da ma ze iya rayuwa hakan be damesa ba duk wata da wai niyar mu shi yake dauka koman mu kansa ya koma dan zuwa lokacin ma me gidana ya daina fita kasuwa yace yayi zamansa duk abun da yake samu namune gaba daya tunda be da wadanda suka fimu a rayuwar sa mune iyayen sa kuma duk abun da zaiyi mana tamkar yayiwa iyayen sane dan haka kar muqara cewa komai akai ko kuma muyi masa godiya ana haka kwatsam saiga ciki ajinkin nadeeya munyi murna sosai da samun sa haka muka cigaba da rainon sa cikin ta ya cika wata yara haihuwa yau ko gobe,
Ana haka saiga wasu mutane da sune kusan shiga halin da muke ciki duk dade bamu san mafarin sa bamusan daga ina suke ba wata rana muna zaune afalo nida me gida na saiga wasu mutane sun fado ciki dukan mu muntsorata da ganin su muka tambaye su ko lafiya me suke nema sai sukace sunzo su gargade mu akan yaron da muka tsinta muke riqewa kuma mu sanar dashi suna nan suna bibbiyar rayuwar sa duk abun da yakeyi idon sa akansa dan haka ya kula ya iya takunsa dan yana daf darasa rayuwar sa domin kwanan sa ya kusa qarewa munyi mamakin jin hakan saboda a iya zaman mu a unguwar ba wanda yasan ba dan mu bane sai nakusa damu suma kuma basu san tsintar shi mukayi ba kawai de munce musu dan yayata ne hankalin mu ba qaramin tashi yayi ba mukace me kuke nema awajen sa me yayi muku sai sukace babu ruwan mu da abun da yafaru kawaide suna so munesan ta dashi sannan kuma mugaya musu inda mahaifiyar sa take mukace musu muma bamu sani ba shi kadai muka tsinta basu yarda ba sukace ko mu fada ko kuma mu rasa ranmu sun bamu da gayau zuwa sati daya idan bahaka ba zamu rasa rayuwar mu gaba daya domin zaman mu da yaron nan tare babba hatsari ne agare mu nida malam ba wanda ya iya tanka musu har suka gama suka fita daga gidan malam ya kalle ni yace me kika fahimta game da zuwan su anya kuwa sunsan sa ba kawai damfarar sa suke so suyiba dan sunga yana da kudi nace masa banajin hakan amma de ni anaganin kamar sunsan shi ko kuma aiko su akayi tundade har suka san ba danmu bane kuma suke tambayar mahaifiyar sa ga kwa ai dole sun sanshi amma mubari yadawo muji ko wani abun ya taba hadasa da wani acikin kasuwar ko awajen aikin sa da har ake yimana wannan barazanar ko watakil 'yan hassadane sai malam yace ka mu sanar dashi kar muje musaka shi cikin damuwa mubari muga abun da hali zeyi ko garinne sai muyi qoqarin bari kafin su ankare da wannan shawarar muka bar zancen anan de muka bar maganar da yadawo kuma bamu yi mishi maganar ahaka har wajen kwana uku suka qara dawowa da zancen mugaya musu inda mahaifiyar sa take nan made mukabqara sanar dasu abun da muka sani game dashi haka suka qara hakura suka fita da qara yimana gargadi da tare sa cewa wannan shine zuwan qarshe idan suka sake dawowa baza muji dadi ba nan made bamu yimasa zancen ba saide ma zancen yakamata mubar garin saboda akwai wadanda suke kawo masa hari amma bamu gaya masa ainahin abun dake faruwa ba da farko qin amincewa yayi saida yaga de munaso sannan yace to muka fara shirye shirye aranar kuma da daddare saiga nakuda ta riske nadeeya dalilin da ya dakatar damu kenan daga tashin da muke shirin yi muka kaita asibiti har washe gari bata haihu ba tana naquda tun tana naquda take kiran sunan mijin ta tana cewa yazo suyi sallama bata jin zata iya rayuwa mutuwa zatayi tun adaren muke neman layinsa amma bamu samu ba kuma be dawo gida ba kuma har yanzu da safem ma be dawo ba ita ma kuma bata haihu ba munshiga tashin hankali sosai rashin sanin halin da yake ciki ga kuma yarmu da itama ba lafiya ga nakuda kuma sunqi yimata cs dan mu munyarda muce kawai suyi mata amma sunqi yarda sunce wai kawai doguwar na quda ce zata iya haihuwa da kanta haka mukai ta zuba ido muna addu'ar ta sauka lafiya tare da fatan dawowar sameer suna waje suna ta zagaye sunqi zaune sunqi tsaye sai zirga zirga suke abakin qofar dakin da aka kwantar da ita suna jiyo ihunta kuma ahaka har muka kai wajen qarfe goma na dare ba wani labari wajajen sha daya muna de wajen a tsaye saiga sameer ya shigo wajen afujajan gaba daya baya cikin nutsuwar sa kansa mukayi gaba dayan mu mana tamyar sa lafiya me yasame shi daga ina yake Allah yaso muma zuwa lokacin babu kowa agurin sai mukadai babu wanda yagan mu muka ci gaba da tambayar sa amma sai haki yake yakasa yimana magana sai kawai yayi saurin janmu gefe murya qasa qasa yace kamani sukayi bansan suba yanzu haka gudowa nayi basu sani ba kuma nasan zasu biyo ni dan Allah ku gaggauta dauke ta daga wannan asibitin saboda sun nuna min video din halin da take ciki hakanne ma yasa nagane kuna asibiti duk bakinsu daya dan doctors din dake kula da ita kuma su suka hanata haihuwa suna so tarasa abun dake cikin ta sannan itama sukashe ta bansan me nayi musuba suke son tarwatsa min rayuwa ba dan Allah kuyi yanda zakuyi kubar nan gaba dayan ku ni nasan tawa ta qare sai sun kaishe ni amma dan Allah ku kubutar da rayuwar ku da yar da za tahaifa kar kubari su rasa ransu na roqeku kutai maka nasan duk daren dadewa gaskiya zata bayyana zaro wani mukulli yayi ya danqawa malam yace wannan mukulayen bangare nane idan kunje ku bude ku shaga a kwai wata drawer acikin wardrobe din Nadeeya idan kun budeta sai kuyi amfani da wannan mukullin ku bude duk wani abuna yana ciki da takaddun gidajena da filayena da kuma atm din ma duk suna ciki ban fito da ko dayaba komai na mai muhimmaci yana ciki ku kula dasu ku kwashe kubar garin nan idan yata ta girma a mallaka mata su natane ita da mahaifiyar ta na barmusu tare daku sosai na shiga kuka sannan nasanar dashi muma barazanar da akayi mana akansa shiyasa muka ce masa mubar garin shikenan yanzu de kafin suzo kuzo mufita da ita kafin su riske ni anan gaba dayan mu munshiga tashin hankali dajin wannan batun nasa haka muka lallaba muka leqa dakin sai muka ga har yanzu de likitocin suna ciki tunanin yanda za ayi mu shiga batare da sun ganmu ba malam ne yace ku kubuya ni zan shiga ciki insan yanda zanyi su fito daga dakin ku kuma said kushiga ku fito da ita sameer yace a'a baba kar kasaka rayuwar ka cikin wani hali kabari ni zanyi ku kushiga yace a'a ai kaga ni bazan iya daukan ta ba kawai kabari inyi hakan ba abun da ze faru kuje kawai da haka muka koma da baya muka buya shi kuma yafara tunanin ynada za ayi ya bude qofar ya shiga amma yakasa said kawai sameer ya fito yace baba ga wata dabara zo muje wajen fiyus nasauke nuna maka sai ka sauke wutar nikuma anan zanyi sauri inshiga in dauko ta kafin su gyara mun gudu gaba daya mukayi na'am da shawarar sa kuma har zuwa lokacin babu wanda Allah yabawa ikon zuwa wajen mukadai muke lissafin mu sukuma suna ciki sunqi fitowa saboda sun san basu da gaskiya ahaka muka sake gita daga asibitin muna tafiya muna boye boye saboda kar wani yagan mu ahaka har muka fito da qyar muka samun gurin da fiyus din yake tare muka je wajen na dauko yar qaramar wayata muka haska da ita shikuma yatafi yace insaka wayata a silent ina gani kiranshi in ya shigo to malam ya sauke wutar ahaka yaqara komawa wajen mukuma muka tsaya agurin lokacin da yashi ga sukuma doctors din da suke ciki da suka leko waje sukaga ba kowa kawai said suka fito da niyar zasuje su dawo yana labe a gefe yana kallon duk abun da suke saida ya tabbaatar da tafiyar su sannan yafito tare da tura qofar ahankali ya shiga ciki hanmdalah ya sauke tare ganinta kwance ido suka hada da ita ganin sa yasa ta bude baki zatayi magana amma sai yayi saurin rude mata baki tare da nuna mata alamar tayi shiru da qyar ya iya dagota zaune tare da sabata a kafada yana shirin fitowa kenan yaji surutun su sun kusa qarasowa ma cikin dakin a gigice yayi saurin koma da baya tare da zaro wayar sa a aljihu dan yama manta ze kirasu
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment