Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma kinaso saleem yazo yaganki anan baki tafi ba ba ruwana dan yana tambaya zan gaya masa gaskiya da sauri ta goge harda kwakwalo murmushi ta aza akan fuskarta sannan tace nagode muje to duk abun da yasan ze dauka ya duba yadauka saboda idan yatafi yatafi kenan ba dawowa zeyi ba yana gamawa yace sutafi fita sukayi atare yaja office dinsa sannan ya nuna mata wata hanya yace mubi tanan yanda bazamu hadu dashi ba binshi tayi yana gaba tana baya har suka zagayo tabaya suka zo wajen parking space din da kansa ya bude mata gaban motar ta shiga sannan yace mata bari ya shiga yanzu ze fito ze dan leqa abokin sane inyanzu zai tafi su tafi tare in kuma ba yanzu ze tafi ba sai suyi sallama ok kawai tace dashi shikuma sai ya rufe mata qofar sannan ya koma ciki direct upstairs ya nufa wajen sam yana qara sawa bakin office din nasa sai ya kwankwasa yadan jira ko za abude amma shiru saida ya buga wajen sau uku amma ba abude ba hakan yasashi murda qofar sai yajita a kulle juyawa yayi ya koma,
wajen motar yakoma sannan yabude ya shiga da sallama amsa masa tayi ciki ciki kallon tayayi ganin idon ta arufe yake sai ya share ta kawai be cemata komai ba yayi wa motar key tare da yin reverse yajuyata suka fita daga cikin hospital din sai da ya hau kan titi  sannan yadauko wayar sa  yadan lallatsata ya lalubo number sa yadanna mata kira sai yakara wayar a kunnen sa yace ana dagawa yace hello Sam kana ina ne ko ka tafi naje office dinka ban ganka ba naji ma a kulle yake bansan amsar da akabashi ba kawai yace ok sai gobe to nima na wuce gida daga nan kuma yakashe wayar ya ajiyeta gefe batare da ya kalle ta ba yace wacce unguwar tace kurna wajen masallacin na kowa yace ok daga nan sukayi shiru tafiya kawai  suke kowa da abun da yake saqawa aransa saida suka danyi nisa bazato ba tsammani taji yace kiyi hakuri dan Allah bude idon ta tayi tana kallon sa sannan tace sorry for what yace for everything tace like how kai da bakai kayi min laifiba meyasa zaka bani hakuri yace namiki mana haduwar mu ta farko da ta biyu nasan na bata miki rai amma kiyi hakuri dan Allah kiyafe min duk abun da nayi miki bakiji dadi ba,
dan murmushi tayi saboda taji dadin wannan maganar tasa dan haka kai tsaye tace bakomai wlh ai ni bankullace kaba kuma tuntuni na yafema nima kayi hakuri bisa rashin kunyar danayi maka sharrin zuciya ne ka yafemin tafada tana dan satar kallon sa aikwa karaf suka hada ido dashi da sauri ta kawar da kanta tare da basar wa bata jira yayi magana ba ta dora dacewa wai nikam in tambaye ka mana yace fadi kanki tsaye wani murmushin ta qara saki jin abun da yace sai kuma lokaci daya murmushin yabace saida tayi shiru na wasu lokutan kafin wai ya akai ka ganni awajen nan kuma aya ka ganni?

Juyowa yayi yadan kalleta sai kuma yamayar da dubansa kan titi sannan yace bayan fito warki da kikace kintafi gida nikuma da na koma office sai nake ganin kamar nine sanadin dayasa kika shiga damuwa kika qi sakin jikin ki saboda abun da nayi miki da kuma wanda nagaya miki awaya shiyasa naji bankyauta ba sai na biyo ki ko zan sameki a titi sai inbaki hakuri sai kuma da na fita na nemeki na rasa nazatama kin tafi shiyasa na dawo bayan nadawo kuma nayi parkin nafito har zan wuce sai idona yafada wajen wani lungu sai naga kamar hannun mutum awajen hakanne yasa ni qarasawa dan ganin waye sai kawai naganki kwance awajen nazata ma ko mutuwa kikayi saboda yanda jikin ki yasaki gaba daya saida nasaita kunnena sannan naji alamar kina numfashi sumane kawai sai kuma yayi shiru kallon sa tayi tace sai kuma me ya akai naganni a office din ka tana gama rufe baki yace daukar ki nayi mana nakai ki zaro ido tayi tace dauka ta kuma yace eh mana to me kikeso inyi miki ko sokike inta tashin ki tace a'a yace to ina kaiki na yayyafa miki ruwa amma still baki farfado ba sai da nasa bakina anaki na toshe miki hanci na hura miki iskar bakina sanna kika kawo numfashi danazo kuma cire bakina sai kika riqe kika qi sakar min saida kika gama abun da kikeso sannan kika saki dan kanki qarasa fada yayi tare da satar kallon ta ta gefe yana boye dariyar sa,

azabure ta juyo tana kallon tare da ware idanuwanta akansa tace dan Allah da gaske yace nataba yi miki wasane tace a'a amma wlh nide banyi ba gaskiya bani Wlh banyi ba Allah sharri kayi min ni me zanyi da bakin ka da har zan ruqe wama yace kasaka min baki bada a kwai abun busa iska ba me yasa baka busamin da shiba zaka busa min iskar baki me wari ni har kasa ma nafara jin amai tafada tana kakarin yin amai wani wawan burki yaja da saida ta buge da gaban motar da sauri ta juyo a tsorace tace so kake ka kashe nine zaka ja irin wannan burkin harara ya galla mata sannan yace waye me warin bakin tace nifa ba da kai nake ba yace ko to fitar min amota  kije kishiga motar da ba me warin baki ba tace dan Allah yi hakuri da wasa fa nake katseta yayi da cewa wlh bazan qarasa dake ba intaimakeki kuma kishigo motata kiringa gaya min magana nine me warin baki ko to nagode fita yafada yana nuna mata qofa hakuri ta qara bashi tana yar dariya ciki ciki yanda duk taga yabi yayi wani kicin kicin da fuska shi adole yaji haushin maganar ta shi yamata abun da yace mata itama ramawa tayi daman ance ramuwar gayya tafi ta gayya zafi juyowa tayi tana dan magana dariya nason kwace mata tace haba doctor ya da fusata haka maida wuqar to da wasa nake ramawa nayi kaima kasan abun da kafada ba daidai ban shiyasa nima nayimaka haka kayi hakuri muje kaga har magariba tayi kar amin fada yace ayi miki mana ai bada muwata bace ni malama kifitar min intafi ina da abunyi agida kafada ta maqale masa tace Allah ba inda zanfita tunda ka dauko ni sai ka kaine gida yace haka kikace to muje zuwa zankaiki gidan mu wlh kuma idan nakaiki zancewa hajiya sona kike shiyasa kika nace wai sai kinzo ki gaisheta daga nan kuma zan qara wasu abubuwan dariya tayi sosai har haqoranta na fitowa tace lalle baka san wacece niba sharrina yafi naka kasan nifa macece kar kamanta mata qannan shaidan dan haka kabini ahankali tafada ta na nuna kanta tana qara yimasa dariya shiru yayi kawai ya zuba mata ido yana kallon ta har mamaki take bashi yanda tasake dashi lokaci daya kamar ba itace ta gama kuka dazu ba kamar bata da wata damuwa shikuma daman yanasane yake ta janta da hirar duk dan saboda tasake yamantar da ita damuwar da take ciki shiyasa yake tayi mata haka kuma zaici gaba dayi mata har sai yaga komai daidai sannan zai maida ita gida tsagaitawa tayi da dariyar ganin irin kallon da yake mata, gira daya ta daga masa tare da cewa yade ko ka tsorata ne shima girar ya daga mata budar bakin sa sai cemata yayi tunda hakane bari inyi abun da nasan zaki iya yimin sharrin dashi kinga sai kifada adaidai yanda zatafi yarda tsoro ne yakamata saboda tasan halinsa ba kunya ce dashi ba bata gama tunanin ba taji yasawa motar luck tare da matsowa kusa da ita dasauri taja baya tace nifa matsala ta dakai kenan yanzu fa kagama ban hakuri da neman yafiyata amma shine zaka qara aikata haramun to ni duk abun da nafada dawasa nake taqarasa maganar cike da jin tsoron sa dariya ya kwashe da ita sannan yakoma inda yake yace matsoraciya ashe baki cika qanwar shedan dinba ai da sai in nunamiki nine shedan din ke kuma qanwata itama dariyar tayi tace to naji nide dan Allah muje kawai kallon ta yayi yace ina zamuje tace gidan mu mana yace dawa tace da wanda nake magana yace ai nagaya miki bazan kaiki gidan kuba saide gidan mu kuma nagaya miki abun da zance idan naje marairaicewa tayi tare da yin qasa da murya tace plsss mana zan siyamaka alawa a shagon qofar gidan mu inada canjin goma agida jajjiga kansa yayi sannan yace me kika maidani ni yaro ne da zan sha alawa tace to da maye tafada ciki ciki yace me kikace tace hakana nace a'a kai babbane be kamata kasha ba yace hmmm kiran sallar da akeyini yasa shi tayar da motar sannan yace gwara nakaiki ba huta kar kinyeni mutum anata korar sa amma yana makalewa yafada yana hawa kan titi yaci gaba da tafiya shiru tayi saboda taga alamar idan tabiye masa zasu dade basu gama ba gwara tayi shiru su qarasa gida duk abun da ze faru sai yafaru amma de taganta agida tundaga nan ba wanda yaqara yiwa wani magana har suka qarasa unguwar tasu layin su ta nuna mishi yashiga daidai qofar gidan su yayi parking din motar luck din yacire sannan yace to bismillah nasauke nauyin da na dauka sai afitar min amota kallon sa tayi sai kuma ta kawar da kanta tare dacewa thanks tafada tana bude qofar tasa qafar ta zata fita ya tsaida ita da cewa alqawarina fa dan ban manta ba ok tace masa sannan ta qarasa fita qofar ta rufo masa sannan ta dan leqo tace nagode sosai Allah yasaka da alkhairi yace Ameen har ta juya zata tafi yayi saurin cewa nace ba tsayawa tayi sannan tace kace me yace ki kula da kyau kuma arage damuwa da tunani beda amfani ze iyayi miki illa wacce bakya tunani jikin tane yayi sanyi sannan tace in sha Allah zan kiyaye nagode tana fada ta juya tatafi saida yaga shigarta sannan ya sauke numfashi tare da jan motar sa yabar wajen acikin ransa yana ta tunani kala kala har yabar unguwar gaba daya ya nufi hanyar gidan su...

tunkan taqarasa shiga cikin falon tajiyo muryar saleem nacewa amma mama tafa dade da tahowa dan saida nace ma tajirani tace aiki take baza ta iya jiranaba amma shine kuma bata dawo ba har yanzu to ina ta tsaya?
Mama tace to wayasani sai muzuba ido zuwa bayan sallar magariba mugani ko zata dawo Allah yasade lafiya yace Ameen nibari na wuce masallaci Allah yasa kafin nadawo tadawo mama tace Ameen yafada ya nufar hanyar fita daga falon........


PLS COMMENT AND SHARE
[3/30, 10:08 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode58-59

         """"""""""""""""""""""""""""""""""

Jin muryarsa tasakata saurin komawa da baya tayi saurin buya inda baze ganta ba saida yafito yatafi sannan tafito itama da sanda tashiga saida ta dan saita nutsuwarta sannan tayi sallama amma ba amsa ba saboda ba kowa a falon mama ma ta shiga ciki dan gabatar da salla dakin mama ta nufa lokacin da ta shiga har ta tayar da salla sai tasamu waje gifen gadon ta tana jiran ta idar saboda ita ba yi zatayi ba tana gurin har mama ta idar tayi addu'a ta shafa sannan tayi saurin cewa mama barka da gida bata amsa mata ba sai tambaya fa ta jefo mata daga ina kike sai yanzu  kuma yayanki yace min kindade da tahowa amma shi har yadawo ke baki iso ba muzurai tafara yi da ido tana tunanin qaryar da zatayi a yarda da ita saida mama takara yi mata magana sannan ta dawo daga tunanin da ta tafi sannan tace wlh mama wata adaidaita nahau sai tasamu matsala muka tsaya yana ta faman gyaraya gashi kuma na riga da na bashi kudin gaba daya danace yaban in hau wata dai yace wai inyi bakuri ya gyara kawai dan baze iya bani ba haka naita jiranshi taqi gyaruwa muna haka saiga wata yar makarantar mu ita da yayanta dai sukace inhau surage min hanya shine suka kawoni kinji abun da yasa na dade amma bawani wajen naje ba kallon ta mama tayi sannan tace to ai shikenan tundade kindawo lfy ai har hankalinmu ya tashi kar muje kema murasaki kamar yanda muka rasa mahaifinku tafada muryar ta cike da rauni jikin Azeema ne yayi sanyi gaba daya dan har idonta yadan kawo kwalla saboda tunawa da mahaifinta da tayi ahankali tace Allah sarki baba ko yana raye ko ya mutu Allah masani mama tabata amsa,

saukowa tayi daga kan gadon ta dawo kusa da mama tare da dora kanta kan kafadar mama sannan tace mama wai shikenan da gaske yanzu munrasa baba, baba yatafi kenan bazamu qara ganin sa ba  shafa kanta mama tayi tace in Allah ya yarda ze dawo duk inda yake yana tare da kariyar ubangiji da kuma addu'ar mu in sha Allahu baba be mutu ba kuma zedawo gare mu zamu cigaba da rayuwa dashi kamar da,
dagowa tayi tace mama da gaske ne zedawo garemu tace in Allah ya yarda ni inajin hakan ajikina ko ba dade ko bajima ze dawo tace to mama Allah yasa Allah ya bayyana mana shi nan kusa ta amsa mata da ameen suna cikin haka saleem yashigo bakin sa dauke da sallama amsa masa sukayi su duka sannan yaqarasa shigowa shima kusa da su yasamu ya zauna ganin jikin su duk yayi sanyi yasa shi cewa lafiya nagan ku haka auta me yafaru dake ahanya tashi zaune tayi sannan tace yaya wlh ba komai matsala napep din da nahau yasamu  sai a motar gidan su qawata na dawo ma yanzu yace ok kinga daman ai saoda nace kijira mutaho kika qi gashi yanzu har na rigaki zuwa gida kama ki fasa waryar ki daba sai kikrani ba tace eh wlh yaya nima saida naji haushin hakan mama tace to yanzu de ai shikenan tunda kin dawo lafiya sai abar duk wani zance Allah yaqara kiyaye gaba suka amsa da Ameen Azeema ce taqara cewa yaya wai wadannan mutanan kuwa sunyi cigiyar baban yace eh mana sunyi tun a lokacin ma tace yanzu baza su iya qara yiba ko yanzu za aji wani yace ya ganshi, yace eh to banace eh ba bana ce a'a ba amma banajin zasu iya qara yimana saboda kinga bamu basu kudi ba amma daman inaso idan akai min salary sai inbada kudin waje waje ko Allah zesa adace da murnar ta tace dan Allah yaya da gaske yace zan miki wasane tace a'a amma wlh naji dadin wannan shawarar taka yanzu yaushe za ayi mukun mama ce ta katseta da cewa ke wai me yasa wataran baki da tunani me kyau ne tunda yace zeyi basai kitayashi da addu'a ba kawai ina ruwan ki da ranar da za ayimusu banason shashan ci banza dan turo baki tayi tace kai mama yanzu me nayi wanda bedace ba amma shikenan kuyi hakuri dukanku idan maganata batayi muku dadi ba tana fada ta miqe zata bar dakin har takai ga bakin qofar,
saleem yace kisame ni adaki inason magana dake gabanta taji yayi wata irin faduwa saboda tasan ta tsuniyar bazata wuce ta gizo ba juyowa tayi tace yaya dani kake yace bansani ba shiru tayi sannan murya asanyaye tace kayi hakuri tanafada kuma taqarasa fita daga dakin,

girgiza kai mama tayi sannan ta maida dubanta ga saleem kana tace naga yarinyar nan yanzu gaba daya ta canza kamar ba itaba dan a 'yan kwanakin nan ma na lura da ita  bata fiya fitowa ba inde ba wani aikin zatayiba tanayi kuma zata koma daki wataran har kullewa ma take ko wayar nan daka batace take sata yin hakan ko ta hadu da wasu qawayenne oho nide ban mata maganar ba haryanzu so nake sai na tara ta tukunna zata min bayani idan kwa wayace to zan kwace ta,

dan numfasawa yayi sannan yace nima de kamar abun da na lura da ita kenan amma ban kawo komai ba sai dazu da taqara bani mamaki sosai kuma na fahimci koma mai yakesakata hakan to wayar ce,

Mama face me tayi yace wai kawai na fita sallah na barta a office dina kafin nadawo ina dawowa kuma naga ta ruqe waya gam har naitayi mata magana amma bata jini ba har saida nazo zan zare wayar sai tayi saurin kwacewa da na tambaye ta kuma me yake damun ta kawai sai tasaka min kuka nayi nayi tagaya min amma taqi sai hankalina yabani dole koma meye to acikin wayar yake sai nakai hannuna zan karbi wayar amma wai mama kinsan me tayi mama tace a'a nayi matuqar mamakin ganin da tayi zan karbi wayar wlh da sanan ta sai tayi saurin sakin wayar aqasa tafadi saboda ta fashe kar ingani abun yaban mamaki sosai mama,

itama mama tayi mamakin jin abun da yace kana tace lalle kam akwai abun da yake faruwa dole mugaggauta taka mata burki musan abun da yake faruwa yanzu in wayar tata yace tana dakina baza ta kawo ba dole sai na kaita gyara kafin ta kawo amma yanzu zan sata agaba sai ta gayamin abun dake faruwa inba haka ba kuma zata fuskanci hukun ci mama tace hakanne ya dace da ita ai ita nan atunanin ta wayo take mana bamusan komai ba baza mu iya gane komai ba batasan duk abun da takeyi akan idona bane zatayi min bayani ne idan tazo hannuna yanzu kaje kuyi maganar da ita duk yanda kukayi saika sanar dani yace to mama bari inje da na rabu da itama sai bayan kwana biyu amma tunda abun hakane yanzu zamuyi ta mu qare komai ma yazo qarshe yana kaiwa nan ya miqe tare da barin dakin direct dakin ta ya nufa dan yama fasa bari tazo ta same shi gwara shi yaje ya same ta,,,

   "yana shiga dakin nata yatarar bata dakin  tana cikin
bathroom  bisaga dukkan alamu kuma wanka take dan haka yafita  yajira fitowar tata  dakin sa ya koma inda ya ajiye wayar ya duba ya dauka tare da kunnata ko zata kawo ga mamakin sa kwa sai yaga ta kawo amma ta dan soma cin screen ba aganin screen din gaba daya bude wayar yayi tunda daman ba security akanta call logs dinta yafara shiga amma bega alamun anyi wata waya ba hasalima ba numbers da yawa kuma duk yasan numbobin fita yayi yaqara shiga gallery shima de bega komai ba sai hutunan su sai dan videos da basufi goma shaba suma duk a wayar sa ta tura lokacin da yabata gashi kuma de ya duba yaga bata whatsapp bare ya shiga tsaf yaggama caje wayar amma bega wani abun na alamun rashin gaskiya aciki ba kwafa yayi ya cillar da ita akan gado sai ya dora hannun sa akan gashin kansa yana dan cakudawa dan yanzu kuma gabadaya tunanin sa ya kulle besan kuma ta ina ze faraba tunda gashi abun da yake zargin ze gani kuma bega komai ba zama yayi yana cigaba da tunanin ta inda ze samu mafita yana cikin wannan halin ta shigo dakin da sallama jikin ta sanye da hijabi har qasa saboda zanine ajikin ta taji shigar shi dakinta dan haka tana fitowa bata tsaya yin kamai ba ta zuro hijabi tafito,
be amsa mata ba har ta gama shigowa zuba mata ido yayi yana binta  da kallon qurulla har saida ta sha jinin jikin ta sannan ta qaraso inda yake jiki babu kwari tace yaya gani zaman sa ya gyara sannan yace zauna zama tayi kusa dashi tare da sauke kanta qasa, kallonta yayi kana yace auta dago ki kalleni  dagowa tayi tana kallon sa shima kallontan yake sannan yace auta banason qarya karkiyi min kuma kigaya min gaskiyar abun da zan tambaye ki murabu lfy  kinjini  ko kai tadaga masa sannan yaci gaba dacewa inaso kigayamin abun da yasakaki cikin damuwa har da kuka da kuma abun da yake sakaki yanzu ba kyazaman falo kullum kina daki harda kullewa wataran inason sanin meke faruwa gabanta ne yafadi jin duk wadanan tambayoyin da yake jiro mata kuma wayace masa tana kulle kanta adaki to kode mama ce tace kai a'a nasan da itace da tuni tayi min magana bakiji me nace bane yakatse mata tunanin ta,
lokaci daya wata dabara tafado mata sunkuyar da kanta tayi tana dan wasa da yatsunta irinde na marassa gaskiya saidaga bisani kuma tace yaya dan Allah kayi hakuri karka gayawa mama wlh ta taba hananin tun sheakarun baya danake daukar wayarta inayi ta kamani tace koda wasa kar nasake taqara ganina inayi inma zanyi inbari sai nagama makaranta amma indenayi tunda ni yarinyace sai kuma tayi shiru yadan daga murya tare da dan daka mata tsawa yace ni bawannan na tambayeki ba kifadan abun da na tambayeki amma kintsaya kina min wasu surutai da bansan inda kika dosaba yawu ta hadiye dan ta tsorata da yanayin shi ahankali tace bafa wani abu bane daman karatun novel nake shiyasa nake shigewa daki saboda kar mama ta kamani dazu kuma lokacin  da kaga ina kuka  junaid ne ya mutu tafada kamar zata qara yin wani kukan😂(only readers of abban sojoji can relate)
Wata uwar harara ya zabga mata tare da waro ido yace ke kina da hankali kuwa kode jinnu ne suka shafeki waye kuma junaid?
tace acikin littafin yake wlh duk nafi sonshi aciki amma saboda mugunta haroon ya bitakan shi da mota ko kai kaji abun wlh sai ka tausaya mishi kuma sai kayi kuka kaima,

Wani wawan tsaki yasaki yama kasa ce mata komai saboda takaicin da tabashi yatsansa yadaga ya nuna mata qofar fita yace fita daga dakin nan dan walhi zan iya makeki anan gurin kallon shi tayi tace Allah yaya da gaske nake ko in tura maka ka karanta kaji idan qarya nake miqewa yayi ze kai mata bugu tayi saurin diban 'yan matan qafafun ta ta kwasa aguje bata tsaya ko inaba saida taje dakinta ta fada saman bed dinta tare da kwashewa da dariya dariya take ta tiqa harda riqe ciki sai tayi shiru ta dan tsagaita sai kuma abun yaqara fado mata sai kwa taqara kwashewa da wata dariya haka ta ringayi kamar sabuwar kamu saida tayi me isarta harda hawaye sannan ta tsagaita tare da cewa tab Allah yataimake ni danaci ubana dan yanda naga yaya yana ta yimun muzurai yau dinan da yagane gaskiya da nagayawa aya zaqinta, gwara da na fake da littafinan wallahi yau littafinan da zahra'u take bamu labari yayi min rana aikwa gobe da wuri zan tafi makaranta inqarasa jin labarin nan Allah yasade be mutuba ita kadai sai faman zuba take tana tuna lokacin da zahra'u take basu labarin littafin tunkan suyi hutun makaran ta yanzu kuma tunda suka koma bata qara basu labarin ba 
a fili tace woni azeema na kware aidaman a kwai qarayar da ta halatta ko to wannan ta halatta nazura yaya a kwalba na rufe ruff kuma ya rufu woni woni woni ta tashi tsaye harda rawa tana daga hannu sama tana tsalle akan gadon,
jitayi ance to asirinki ya tonu naji duk abun da kika fada, ahaukace ta juyo hartana fadowa daga kan gadon jikake timmmm tafado qasa........😂

( to murna sai ta koma ciki  ko takwara sarkin 'yan qarya nide ba halina bane naya ma kuwa sunanki ne wannan ba arowa kikayi ba dan masu sunan basa qarya saide sufadi ba daidai ba😜 saura wani yace bahaka bane😎)
                


******************
[3/30, 10:09 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

 

Please Login or Register in order to submit comment