Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

                  Bismillah........ ✍
Episode 60-61

         """"""""""""""""""""""""""""""""""

Jin muryarsa tasakata saurin komawa da baya tayi saurin buya inda baze ganta ba saida yafito yatafi sannan tafito itama da sanda tashiga saida ta dan saita nutsuwarta sannan tayi sallama amma ba amsa ba saboda ba kowa a falon mama ma ta shiga ciki dan gabatar da salla dakin mama ta nufa lokacin da ta shiga har ta tayar da salla sai tasamu waje gifen gadon ta tana jiran ta idar saboda ita ba yi zatayi ba tana gurin har mama ta idar tayi addu'a ta shafa sannan tayi saurin cewa mama barka da gida bata amsa mata ba sai tambaya fa ta jefo mata daga ina kike sai yanzu  kuma yayanki yace min kindade da tahowa amma shi har yadawo ke baki iso ba muzurai tafara yi da ido tana tunanin qaryar da zatayi a yarda da ita saida mama takara yi mata magana sannan ta dawo daga tunanin da ta tafi sannan tace wlh mama wata adaidaita nahau sai tasamu matsala muka tsaya yana ta faman gyaraya gashi kuma na riga da na bashi kudin gaba daya danace yaban in hau wata dai yace wai inyi bakuri ya gyara kawai dan baze iya bani ba haka naita jiranshi taqi gyaruwa muna haka saiga wata yar makarantar mu ita da yayanta dai sukace inhau surage min hanya shine suka kawoni kinji abun da yasa na dade amma bawani wajen naje ba kallon ta mama tayi sannan tace to ai shikenan tundade kindawo lfy ai har hankalinmu ya tashi kar muje kema murasaki kamar yanda muka rasa mahaifinku tafada muryar ta cike da rauni jikin Azeema ne yayi sanyi gaba daya dan har idonta yadan kawo kwalla saboda tunawa da mahaifinta da tayi ahankali tace Allah sarki baba ko yana raye ko ya mutu Allah masani mama tabata amsa,

saukowa tayi daga kan gadon ta dawo kusa da mama tare da dora kanta kan kafadar mama sannan tace mama wai shikenan da gaske yanzu munrasa baba, baba yatafi kenan bazamu qara ganin sa ba  shafa kanta mama tayi tace in Allah ya yarda ze dawo duk inda yake yana tare da kariyar ubangiji da kuma addu'ar mu in sha Allahu baba be mutu ba kuma zedawo gare mu zamu cigaba da rayuwa dashi kamar da,
dagowa tayi tace mama da gaske ne zedawo garemu tace in Allah ya yarda ni inajin hakan ajikina ko ba dade ko bajima ze dawo tace to mama Allah yasa Allah ya bayyana mana shi nan kusa ta amsa mata da ameen suna cikin haka saleem yashigo bakin sa dauke da sallama amsa masa sukayi su duka sannan yaqarasa shigowa shima kusa da su yasamu ya zauna ganin jikin su duk yayi sanyi yasa shi cewa lafiya nagan ku haka auta me yafaru dake ahanya tashi zaune tayi sannan tace yaya wlh ba komai matsala napep din da nahau yasamu  sai a motar gidan su qawata na dawo ma yanzu yace ok kinga daman ai saoda nace kijira mutaho kika qi gashi yanzu har na rigaki zuwa gida kama ki fasa waryar ki daba sai kikrani ba tace eh wlh yaya nima saida naji haushin hakan mama tace to yanzu de ai shikenan tunda kin dawo lafiya sai abar duk wani zance Allah yaqara kiyaye gaba suka amsa da Ameen Azeema ce taqara cewa yaya wai wadannan mutanan kuwa sunyi cigiyar baban yace eh mana sunyi tun a lokacin ma tace yanzu baza su iya qara yiba ko yanzu za aji wani yace ya ganshi, yace eh to banace eh ba bana ce a'a ba amma banajin zasu iya qara yimana saboda kinga bamu basu kudi ba amma daman inaso idan akai min salary sai inbada kudin waje waje ko Allah zesa adace da murnar ta tace dan Allah yaya da gaske yace zan miki wasane tace a'a amma wlh naji dadin wannan shawarar taka yanzu yaushe za ayi mukun mama ce ta katseta da cewa ke wai me yasa wataran baki da tunani me kyau ne tunda yace zeyi basai kitayashi da addu'a ba kawai ina ruwan ki da ranar da za ayimusu banason shashan ci banza dan turo baki tayi tace kai mama yanzu me nayi wanda bedace ba amma shikenan kuyi hakuri dukanku idan maganata batayi muku dadi ba tana fada ta miqe zata bar dakin har takai ga bakin qofar,
saleem yace kisame ni adaki inason magana dake gabanta taji yayi wata irin faduwa saboda tasan ta tsuniyar bazata wuce ta gizo ba juyowa tayi tace yaya dani kake yace bansani ba shiru tayi sannan murya asanyaye tace kayi hakuri tanafada kuma taqarasa fita daga dakin,

girgiza kai mama tayi sannan ta maida dubanta ga saleem kana tace naga yarinyar nan yanzu gaba daya ta canza kamar ba itaba dan a 'yan kwanakin nan ma na lura da ita  bata fiya fitowa ba inde ba wani aikin zatayiba tanayi kuma zata koma daki wataran har kullewa ma take ko wayar nan daka batace take sata yin hakan ko ta hadu da wasu qawayenne oho nide ban mata maganar ba haryanzu so nake sai na tara ta tukunna zata min bayani idan kwa wayace to zan kwace ta,

dan numfasawa yayi sannan yace nima de kamar abun da na lura da ita kenan amma ban kawo komai ba sai dazu da taqara bani mamaki sosai kuma na fahimci koma mai yakesakata hakan to wayar ce,

Mama face me tayi yace wai kawai na fita sallah na barta a office dina kafin nadawo ina dawowa kuma naga ta ruqe waya gam har naitayi mata magana amma bata jini ba har saida nazo zan zare wayar sai tayi saurin kwacewa da na tambaye ta kuma me yake damun ta kawai sai tasaka min kuka nayi nayi tagaya min amma taqi sai hankalina yabani dole koma meye to acikin wayar yake sai nakai hannuna zan karbi wayar amma wai mama kinsan me tayi mama tace a'a nayi matuqar mamakin ganin da tayi zan karbi wayar wlh da sanan ta sai tayi saurin sakin wayar aqasa tafadi saboda ta fashe kar ingani abun yaban mamaki sosai mama,

itama mama tayi mamakin jin abun da yace kana tace lalle kam akwai abun da yake faruwa dole mugaggauta taka mata burki musan abun da yake faruwa yanzu in wayar tata yace tana dakina baza ta kawo ba dole sai na kaita gyara kafin ta kawo amma yanzu zan sata agaba sai ta gayamin abun dake faruwa inba haka ba kuma zata fuskanci hukun ci mama tace hakanne ya dace da ita ai ita nan atunanin ta wayo take mana bamusan komai ba baza mu iya gane komai ba batasan duk abun da takeyi akan idona bane zatayi min bayani ne idan tazo hannuna yanzu kaje kuyi maganar da ita duk yanda kukayi saika sanar dani yace to mama bari inje da na rabu da itama sai bayan kwana biyu amma tunda abun hakane yanzu zamuyi ta mu qare komai ma yazo qarshe yana kaiwa nan ya miqe tare da barin dakin direct dakin ta ya nufa dan yama fasa bari tazo ta same shi gwara shi yaje ya same ta,,,

   "yana shiga dakin nata yatarar bata dakin  tana cikin
bathroom  bisaga dukkan alamu kuma wanka take dan haka yafita  yajira fitowar tata  dakin sa ya koma inda ya ajiye wayar ya duba ya dauka tare da kunnata ko zata kawo ga mamakin sa kwa sai yaga ta kawo amma ta dan soma cin screen ba aganin screen din gaba daya bude wayar yayi tunda daman ba security akanta call logs dinta yafara shiga amma bega alamun anyi wata waya ba hasalima ba numbers da yawa kuma duk yasan numbobin fita yayi yaqara shiga gallery shima de bega komai ba sai hutunan su sai dan videos da basufi goma shaba suma duk a wayar sa ta tura lokacin da yabata gashi kuma de ya duba yaga bata whatsapp bare ya shiga tsaf yaggama caje wayar amma bega wani abun na alamun rashin gaskiya aciki ba kwafa yayi ya cillar da ita akan gado sai ya dora hannun sa akan gashin kansa yana dan cakudawa dan yanzu kuma gabadaya tunanin sa ya kulle besan kuma ta ina ze faraba tunda gashi abun da yake zargin ze gani kuma bega komai ba zama yayi yana cigaba da tunanin ta inda ze samu mafita yana cikin wannan halin ta shigo dakin da sallama jikin ta sanye da hijabi har qasa saboda zanine ajikin ta taji shigar shi dakinta dan haka tana fitowa bata tsaya yin kamai ba ta zuro hijabi tafito,
be amsa mata ba har ta gama shigowa zuba mata ido yayi yana binta  da kallon qurulla har saida ta sha jinin jikin ta sannan ta qaraso inda yake jiki babu kwari tace yaya gani zaman sa ya gyara sannan yace zauna zama tayi kusa dashi tare da sauke kanta qasa, kallonta yayi kana yace auta dago ki kalleni  dagowa tayi tana kallon sa shima kallontan yake sannan yace auta banason qarya karkiyi min kuma kigaya min gaskiyar abun da zan tambaye ki murabu lfy  kinjini  ko kai tadaga masa sannan yaci gaba dacewa inaso kigayamin abun da yasakaki cikin damuwa har da kuka da kuma abun da yake sakaki yanzu ba kyazaman falo kullum kina daki harda kullewa wataran inason sanin meke faruwa gabanta ne yafadi jin duk wadanan tambayoyin da yake jiro mata kuma wayace masa tana kulle kanta adaki to kode mama ce tace kai a'a nasan da itace da tuni tayi min magana bakiji me nace bane yakatse mata tunanin ta,
lokaci daya wata dabara tafado mata sunkuyar da kanta tayi tana dan wasa da yatsunta irinde na marassa gaskiya saidaga bisani kuma tace yaya dan Allah kayi hakuri karka gayawa mama wlh ta taba hananin tun sheakarun baya danake daukar wayarta inayi ta kamani tace koda wasa kar nasake taqara ganina inayi inma zanyi inbari sai nagama makaranta amma indenayi tunda ni yarinyace sai kuma tayi shiru yadan daga murya tare da dan daka mata tsawa yace ni bawannan na tambayeki ba kifadan abun da na tambayeki amma kintsaya kina min wasu surutai da bansan inda kika dosaba yawu ta hadiye dan ta tsorata da yanayin shi ahankali tace bafa wani abu bane daman karatun novel nake shiyasa nake shigewa daki saboda kar mama ta kamani dazu kuma lokacin  da kaga ina kuka  junaid ne ya mutu tafada kamar zata qara yin wani kukan😂(only readers of abban sojoji can relate)
Wata uwar harara ya zabga mata tare da waro ido yace ke kina da hankali kuwa kode jinnu ne suka shafeki waye kuma junaid?
tace acikin littafin yake wlh duk nafi sonshi aciki amma saboda mugunta haroon ya bitakan shi da mota ko kai kaji abun wlh sai ka tausaya mishi kuma sai kayi kuka kaima,

Wani wawan tsaki yasaki yama kasa ce mata komai saboda takaicin da tabashi yatsansa yadaga ya nuna mata qofar fita yace fita daga dakin nan dan walhi zan iya makeki anan gurin kallon shi tayi tace Allah yaya da gaske nake ko in tura maka ka karanta kaji idan qarya nake miqewa yayi ze kai mata bugu tayi saurin diban 'yan matan qafafun ta ta kwasa aguje bata tsaya ko inaba saida taje dakinta ta fada saman bed dinta tare da kwashewa da dariya dariya take ta tiqa harda riqe ciki sai tayi shiru ta dan tsagaita sai kuma abun yaqara fado mata sai kwa taqara kwashewa da wata dariya haka ta ringayi kamar sabuwar kamu saida tayi me isarta harda hawaye sannan ta tsagaita tare da cewa tab Allah yataimake ni danaci ubana dan yanda naga yaya yana ta yimun muzurai yau dinan da yagane gaskiya da nagayawa aya zaqinta, gwara da na fake da littafinan wallahi yau littafinan da zahra'u take bamu labari yayi min rana aikwa gobe da wuri zan tafi makaranta inqarasa jin labarin nan Allah yasade be mutuba ita kadai sai faman zuba take tana tuna lokacin da zahra'u take basu labarin littafin tunkan suyi hutun makaran ta yanzu kuma tunda suka koma bata qara basu labarin ba 
a fili tace woni azeema na kware aidaman a kwai qarayar da ta halatta ko to wannan ta halatta nazura yaya a kwalba na rufe ruff kuma ya rufu woni woni woni ta tashi tsaye harda rawa tana daga hannu sama tana tsalle akan gadon,
jitayi ance to asirinki ya tonu naji duk abun da kika fada, ahaukace ta juyo hartana fadowa daga kan gadon jikake timmmm tafado qasa........😂

( to murna sai ta koma ciki  ko takwara sarkin 'yan qarya nide ba halina bane naya ma kuwa sunanki ne wannan ba arowa kikayi ba dan masu sunan basa qarya saide sufadi ba daidai ba😜 saura wani yace bahaka bane😎)
     [3/31, 11:21 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode 62-63

         """"""""""""""""""""""""""""""""""

Dasauri ta miqe tsaye amma tana juyawa sai taga ba kowa abakin qofar ashe kunnen ta ne yajiyo mata hakan amma ba kowa ajiyar zuciya ta sauke tare da komawa kan gadon sai kawai ta kwanta tana ta sake sake mutumin tane yafado nan take ta shiga tunanin sa sai taji gaba daya so take taga fuskar sagashi ba halin yin haka ahaka da tunanin sa bacci yazo yayi awangaba da ita ko hijab din bata cire ba,

Saleem ne yayi sallama dakin mama tana inda yabarta bata tashiba tanajiran tahi sallar isha'i shiga yaqarasa yi yasamu waje yazaun daga dan gefenta kallon shi tayi cike da qaguwar jin abun da zece mata tace me yafaru tagaya maka girgiza kai yayi kana yace mama ashe duk abun da muke tunani ba haka bane Allah sarki munshiga haqqinta muna zarginta akan abun da bashi bane mama tace bangane ba kana nufin kace ba abun da take shiryawa yace eh to da akwai amma ba wani abu bane tace meye to kana yace wai ashe karatun novel take shiyasa take shigewa daki saboda karkiganta kukan kuma datayi dazu wai wanine ya mutu a cikin littafin datake karantawa kinji sakarci da sha shsanci irin nata wai ka kamayiwa littafi kuka ni dan haushin ma da naji canai ta tashi taban guri dan bansan ma me zance mata ba ajiyar zaciya mama tasauke da har saida saleem yajiyo sannan tace Allah na gode maka da abun iya nan ya tsaya ashe duk tunanin da mukeyi ba hakabane amma naji dadi wlh duk da nahanata amma hakan be batamin raiba sosai amma duk da haka zan dan nuna mata bacin raina saboda ai nace kar tayi yanzu tabari sai tagama karatu amma taqi ji zatazo ta sameni yanzu ko ka gyara wayar kar kabata har saityi alkawarin bazata sakeba sannnan kabata yace to mama yauwa bangaya miki ba wayar ma dazu na gwada kunnata ta kawo ana dan ganin wani wajen kuma duk na binceke wayar banga kamai na alamar rashin gaskiya ba ba number kowa wanda bansani ba tace to ai shikenan Allah yaqara kiyaye gaba yace ameen daga nan kuma ya tashi dan wucewa masallaci saboda har ankira isha'i yana fita ita ta tashi dan gabatar da tata sallar,
bayan yadawo yabiya dakin Azeema yaga tana ta bacci abunta fita yayi tare da qara jamata dakin yana fitowa suka hadu da mama sai ta tambayeshi me takeyine aciki banga fitowar ta ba sai yace bacci takeyi tace da wuri kuma haka yace wlh amma watakil kodan tsayiwar da tayine dazu yasa ta gaji shiyasa ta kwanta da wuri tace eh hakanne ma daga nan suka koma falo mama tazobo masa abinci ita ma tazubo nata bayan sungama ci suka dan sake taba hira kafina faga bisani saleem yafara tashi dayiwa mama sallamar saida safe tace Allah yatashemu lafiya ta ya amsa da Ameen sannan yawuce dakinsa  ita ma bata wani dade agunba ta tashi dakin Azeema tafara leqawa still de baccin take bata farka ba fita tayi ta nufi nata dakin dan ta kwanta.........,

            **********************
Washe gari da wuri dr.shettima yatashi dan ya matsu yaje yaga yar babyn nan Ameesha kenan dan haka yasaka mata bayan yagama shirya tsaf ciki kana nun kaya da sukai matuqar  amsar jikin shi yayi kyau sosai bayan yagama shiryawa yaje yasamu hajiyar sa adaki yagaida ita dagana kuma yace hajiya ni zan wuce gurin aiki tace bakaci komai ba zaka tafi yace eh wlh hajiya sauri nakeyi ne inada patient ne zanje naganta wannan dinan fa danagaya miki za ai mata aiki to sai jiya akayi mata kuma yau zata farka watakila ta farka tun cikin dare ma shiyasa nake sauri inje kar asamu matsala tace to shikenan Allah ya kiyaye hanya ita kuma Allah yaqara mata lafiya kace ina mata sannu inta farka yace to hajiya ai zanma kaiki kiganta idan tadawo daidai gobe ko jibi tace to Allah yakaimu da rai da lafiya sai muje din yace Ameen daga nan yayi mata sallama ya fita tabishi da addu'a,

yana fita ya fada motar shi tare da jan motar aguje tunkan ya qaraso gurin gate din yake ta fama bugawa me gate din horn  sauri kuwa aka bude masa shikuma ya dannan hancin motar tare da ficewa daga cikin gidan aguje adan kankanin lokaci yaqaraso hospital din ko parking be gama daidai tawa ba kawai yafito daga cikin motar be tsaya daukar komai ba ya shige ciki direct dakin da take ya nufa yana shiga ya tarar da wata nurse tana dan duddubata tana gyara mata kwanciya saboda ita akabawa kula da ita adakin ma ta kwana,
jin shigowar mutum yasa nurse din dagowa dan ganin waye ganin shi yasata saurin cewa good morning sir saida yaqarasa shigowa sannan ya amsa da morning kana yadora dacewa yajikin nata tace da sauki yace har yanzu bata farka bane tace ta farka tunjiya da daddare amma daman dr. yace idan ta farka a qara yimata wata allurar dan ta qara samun isashshen bacci tunda ta koma kuma sai yanzu ta farka yanzu hakama idon ta biyu da azaune ma take sai yanzu na kwantar da ita cike da gamsuwa da bayanan ta yace yanzu kina nufin idon ta biyu tace eh kawaide ta rufe su amma ba bacci take ba matsawa tayi kusa fa ita tace beuty girl saboda bata san sunan taba kuma gata kyakkyawa shiyasa kawai take kiran ta da hakan,
Qara kiran ta tayi beuty kinajina kuwa ki bude idonki amma shiru bata amsa ba sai tajuyo tace sir watakil ta koma bacci fa,  hannu yadaga mata sannaan  yace ok zaki   iya tafiya,
fita tayi kamar yanda ya umarceta din bayan fitarta yaqarasa kusa da ita gefen gadon yasamu yazauna tare da zuba mata idanu ahankali yadaga hannusa tare da dora shi akan goshin ta dan yanso yaji yanayin jikin nata,
duk abun da suke tana jin su tayi shiru ne kawai amma jin antabata yasata fara bude idon ta ahankali ta saukesu akansa shagala yayi da kallonta be dawo hayyacinsa ba saida ta qara rufe idon ta sannan yadawo hayyacinsa sunan ta yakira ahankali taqara bude idon nata saide yanzu bata kallesa ba sama take kallo yajikin naki yatambayeta bata bashi amsa ba sai de yanzu ta juyo tare da maida kallonta gareshi batare da tace mishi komai ba tambayarta yaqarayi inane yake miki ciwo yanzu, nan made shiru ba amsa, sai de kawai ido da takafe shi dashi kamar san gano wani abun duk yanda yaso yaga tayi magana taki kulashi hasalima daga qarshe mayar da idonta tayi ta rufe dayaga haka sai yadauki wayar sa yakira sam yana dagawa yace akwai matsala fa yarinyar nan bata magana kamar ma batajin maganar da akeyi alamun ta kurmance sai kazo ka qara dubata  daga can bangaren sam kuwa cewa yayi zanshigo anjima yana kaiwa nan yakashe wayar,
sauke wayar yayi sai yaga tana kallon sa ashe tanaji yace ta kurum ce ta bude idon ta tana kallonsa hannu yadaga mata yace kinajin abun da nake cewa? kawar da idonta tayi daga garesa duk wani abun na dabaru dazeyi mata saboda yaga tayi magana yayi mata amma bata kulashiba wayar sa yaqara daukowa yakira saleem yana dagawa yace kashigo ne yace masa eh sai yace kasameni a sp room yace ok gani nan yana kashewa ba jimawa saiga saleem ya shigo da sallama qarasowa yayi bakin gadon sannan yace sir har yanzu bata farka bane yace ta farka mana saide taqi magana shiyasa nakiraka ko zatayi maka tunda ta sanka dan murmushi yayi sannan yace Ameesha juyowa tayi ta kallesa amma batayi magana ba kuma bata nuna alamar ta sansa ba shima de duk abunsa bata kula saba saleem yacewa shettima sir 'yan uwanta sun sani kuwa naga ba wanda yazo shettima yace masa a'a wlh inaso inyi musu surprise ne sonake sai tadawo nml tana magana tana tafiya tukunna ince suzo insuka zo sai suganta kawai to amma kuma kaga har yanzu shiru yanzu zuwan sam kawai nake jira yaqaraso sai yaqara dubata muji a inda matsalar take jinjina kai saleem yayi sannan yace hakan ma yayi zasuji dadi idan sukazo suka ganta lafiya lau hakan sai yafimusu akan suzo suganta a wannan halin gwara abari din tasamu lafiya sosai duk da nagama alamar kamar ba wani abu da yake damunta kawaide rashin maganar ne haka suka cigaba da tattaunawa acikin dakin kuma duk tana jinsu kuma tanaso tayi maganar amma sai ta daga bakin ta da niyar yin magana sai taji yayi mata nauyi, sunkai wajen minti arba'in agurin kafin sam yaqaraso asibitin yana shigowa be fito daga motar ba yakira shettima yace masa ya iso gashinan shigowa suna wane room shettima mane yace masa bari yazo ya shigar dashi daga nan suka katse wayar yana katse wayar yafito daga dakin yazo yasameshi a parking space tare suka jera gwanin birgewa suka shiga ciki dakin suka qarasa tare da sa kai suka shiga cikin dakin suna shiga saleem yashiga gaida sam hannu kawai yadaga masa tare da matsawa kusa da ita dan tattabata yayi kafin yace ke tashi bude idonta tayi aikwa sai tayi saurin rufewa tare da kamkamesu kamar taga dodo mamaki ne yakama shi ganin abun da tayi amma hakan be damesaba matsawa yayi daga kusa da ita sannan yadan kalli shettima yace kace bata jin magana gashi kuma nace ta tashi ta tashi yace eh tanaji amma bata iyayin magana yace daman ai bazeyiyu tayi magana koda yaushe ba   saboda bakin ta zeyi mata nauyi sai ahankali zata dawo daidai hakan ba wata matsala bane juyawa ya kumayi gurinta sai yaga tana matsi da hannun ta alamar tana son wani abun fahimtar hakan da yayi yasa shi qarasa kusa da ita sosai tare da dagata cak dinta ya zaunar da ita rumtse idon ta taqara yi jin yatabata harda dagata zamawa taqara yi da niyar komawa ta kwanta yasa hannunsa ya ruqota tare da cewa kar ki kwanta ki zauna zaman tayi bata qara komawa ba amma kuma bata bude idon taba haryanzu ganin hakan yasa shettima cewa baby kibude idon ki mana dubaki zeyi sai yanzu sukaga ta girgiza kai alamar baza ta bude ba sam ne yace ke bude idonki karkibata min lokaci ina da abun yi danshi harga Allah abun da takeyi ta bashi haushi hakan nan yake jin haushin ta daga ganinshi ta wani rufe ido saikace taga dodo banza yar kauye kawai mtsw yaja tsaki da harsaida yafito kuma kowannen su yaji saide ba wanda ya iya tanka masa bude idon ta tashiga yi a hankali ta sauke su akansa ga mamakin su sai suka ga ta maka mishi wata qatuwar harara tare kawar da kanta gefe waro manyan idanun sa yayi yana kallonta dukan su da mamaki suke kallon ta ganin hararar da datayi bare kuma wanda tayiwa mamaki begama kashe suba saida sukaji abun da basu taba zato ba budar bakin ta sai cewa tayi aikin banza

Please Login or Register in order to submit comment