Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rasheeda ce tsaye abakin qofa da ta fito cikin shirinta na zuwa makaran ta saboda yau da wuri zata fita saboda test zasuyi shigowar ta kenan dan ta dan samu wani abun taci kafin ta fita shine kunne ta yajiye mata maganar da tasa zuciyar ta bugawa da qarfi tana shirin fitowa waje kuma ba komai taji azancen nasuba sai maganar lami ta qarshen da tace wlh har yanzu nakasa yarda wai gidan su bossay zaku koma amma nataya ki murna dan wlh kakarki ta yanke saqa  jin an ambaci abun sonta yasata jin faduwar gaba Qarasowa tayi inda suke ta qara daka musu tsawa dacewa wane bossayn naji kuna magana akai Ameesha da har tafara ruwan hawaye tace aunty dan Allah kiyi hakuri wata tsawar taqara buga mata tace dan ubanki hajuri nace kiban ba tambayarki nake ba amsa zakiban wuqi wuqi ta farayi da ido takasa magana dan bata san ta yanda ma zata fara yi mata bayani ba suna cikin haka sai ga mom tashigo tana tambayar su me yake faruwa dukan su ba wanda yaba ta amsa saida tace daughter wai neke faruwa duk tunda natshi nake jin muryar ki daga hannu tayi ta na nuna mata Ameesha da yatsa tana cewa mom wannan munafukar yarinyar ce sai kuma tayi shiru tana hararar Ameesha Mom batai mamakin ganin Ameesha ba saboda da dad yagaya mata zata dawo aiki to amma abun da yadaure mata kai me yasa yarta haka hartake kunfar baki alahalin kuma jiya da kanta tace ita bata damu da dawowar tata ba amma gashi kuma tazo ta tarar dasu to me ya hadasu bata da wanda ze bata amsa
dan haka ya ta maida kallon ta ga lami da ta rakube gefe guda tana tsoron kar adawo kanta mom ce tace ke lami me yake faruwa yimin baya ni cike da tsoro tafara yi mata bayanin duka tattauna war da sukayi ita da Ameesha wata uwar shaqa takaiwa wuyan ta tace dan uban wane bossayn kike nufi bade bossay na ba har yanzu bata ce komai ba saboda shaqar da tai mata mom ce tace wai kin tabbatar da shidin take nufi shi me zesa shi yin hakan qara shaqeta tayi tace baza kigaya min ba sai na halakaki agun nan da kyar ta iya bude bakin ta tace eh shi yaya bossayn ki da qarfi tace what! how dare you mom kinji me tace ko mom tace naji meye abun tada hankali aciki kinsande dad dinki na gida idan kika bari yazo yasame ki ahaka baza kiji da dadi ba kuma zaki gayawa aya zakinta dan haka nide ba ruwana jiki magayi tana gama fadar haka tai ficewar ta daman so take tasamu damar rama abun da tayi mata jiya kuma ta rama dan kwa Rasheeda ba karamin shaqa tayi ba ganin yanda mom din tata ta nuna bata damu da ita ba hasala ta qayi tana kallon Ameesha tace to wlh yau sai kin gaya min alakar ki da shi da har kika samu damar komawa gidan su gaya min shegiya munafuka me kama da 'ya'yan aljanu fada min ko kuma in kasheki kowa ma ya huta ko kuma maular da kikasaba kikaje gidan su yar matsiyata kawai to wlh baki isaba ba inda zaki fita daga cikin gidan nan dan acikin store zan sakaki in qulle daga nan ki mutu aciki inga uban da ze tsaya miki banza shegiya yar gidan shegiya tana gama fadar haka ta fara kokarin janta Ameesha tayi saurin katse ta cikin shashekar kuka tace nifa wlh aunty da wasa nake mata ba gidan su bossay za mukoma bafa a unguwar sune de gidan dazamu koma shima kuma aikatau zamuje saboda dadda tace bazan qara zuwa aiki nan gidan ba shine nikuma bazan iya zama ba aiki ba shine nafito ko zan samu wani gidan su dauke ni saida naje wajen gida biyar amma bansamu ba ina kan hanyar komawa gida sai na hadu da wata qawata yar makaran tar mu itama aikatau take yi sai nagaya mata tace inzo muje unguwar da take aiki bazan rasaba zan iya samu haka tayi mana kudin mota muka je shine muna zuwa muka tsaya muna tunanin inda zamu fara shiga saiga yaya bossay ya fito yana fitowa na gaida shi yake tambayata me muka zo yi unguwarsu nace ai bansa ma nan unguwar suba sai yanzu daga nande mukai mishi bayanin aiki nake nema sai ya nuna mana wani gida yace mushiga gidan su abokin shine yaji suna neman me aiki mushiga muce shi ya turo mu mukai mishi godiya ni tunda ga ranar ma ban qara ganin shiba ba har yau bayan munshiga gidanne kuma suka ga nayi qarama sukace min ina iyaye na suke nace musu banda su ni da kakata muke zaune shine suka ce inzo da kakar tawa suyi magana da ita danaje gida nagayawa dadd.....bata qarasa ba ta daga mata hannu tace dalla malama yimin shiru sai wani yimin dogon jawabi kike sai kace na tambayeki tana gama fada ta kama kunnen ta da qarfi taja tace Allah ya taimakeki amma wlh wlh kinji na rantse koda wasa nakama ki da shi na lahira sai yafi ki jin dadi duk wani abu da kikasan zesa ku hada hanya karki bari hakan tafaru kar kiga ba unguwa daya muke ba duk wani motsun ki da zakiyi acikin unguwar za asanar dani dan zansa asaka miki ido a ringa min bincike akanki dan haka ki kiyaye ni nidin nan da kike gani ba kanwar lasa bace duk yanda kike tunani na na wuce haka tana gama fadar haka ta turata gefe tare da ficewa daga kitchen din dan tama manta abun da yakawota kitchen din Ameesha zubewa tayi awajen tana sauke ajiyar zuciya lami dake makale gefe guda taje ta dakko mata gorar ruwa ta kawo mata tana bata kwa ta karba ta bude tunda tadaga bata ajiye ba saida ta shanye tas sannan ta ajiye robar aqasa lami ce ta tsugunna agaban ta tana yi mata sannu kai kawai ta daga mata saida ta dan samu nutsuwa sannan ta mike tace aunty lami saduwar alkhairi lami tace muje in rakaki tare suka fito saida suka dan yi nesa da wajen kitchen lami da abun ya daure mata kai to me yasa tayi mata qarya tace agidan su bossay zata zauna alahalin tasan qarya take yi kasa daurewa de tayi tace wai nikam intambaye ki me yasa kikai min qarya da kikace agidan su zaku zauna yanzu kuma ga abun da kika gaya wa Rasheeda saida Ameesha taja wani lokaci kamar ma baza ta bata amsa ba sai kuma tace duk abun da kikaji nagaya musu qarya nake wanda nagaya miki ne gaskiya lami kasake tayi kamar wata sokuwa tace wai kina nufin duk wannan uban labarin da kika bayar qirqirq kikayi ba gaskiya bane tace mata eh tace gaskiya na jinjina miki zubaida kin iya tsara labari kamar gidan radio Ameesha tace ko kece kika ga ana shirin rabaki da duniya akaiki barzahu sai kinyi irin wacce tafi tawa lami tace rabani ina ni ina iya wannan qaryar ai tayi yawa fada fa kike tayi bawanda zece zancen ki akwai karya aciki Ameesha tace ni dan Allah kibar ni da abun da yake damuna da jikin zanji ko kuma da surutun ki lami tace nidin kuma yau ake gayawa haka lalle manya sunji shaqa bata kulata ba tayi gaba har de suka qaraso bakin gate din sannan sukayi sallama lami ta dawo ciki ita kuma tafita dan ko baba me gadi batayiwa sallama ba ta wuce ta tafi abin ta saida ta fito ta qara fashewa da kuka tana tunani wai ita kam me tayiwa aunty Rasheeda ba da bata sonta kwata kwata bata qaunar ta ta tsaneta arayuwar ta duk sanda zasu hadu sai taci zalinta ko kuma tayi mata zagin wulakanci da cin mutun ci yanzu yazatayi idan kuma tagane qarya ta shirya mata gashi kuma tace zata sa ayi mata bincike in aka gaya mata ga agidan datake fa yazatayi wata zuciyar ce tace mata sai ki zamanki basai kin fito ba bare ma aganki agaya mata bashike nan ba tana wannan tunanin har ta qaraso qofar gidan su sai kuma abun da tayiwa dadda ya fado mata ashe fa dadda batace taje ba tafita gashi kuma taje ta jawowa kanta wulakanci Allah yasa de dadda kartayi mata fada sadaf sadaf tayi ta leka cikin gidan sai taga ba kowa dan haka sai tashiga da sallama ciki ciki da inba akusa da ita kake ba baza kataba jin me tace ba tana shiga saiga dadda tafito daga bandaki sai kawai ta tsaya bata shiga dakin da take shirin shiga ba dadda tunda taga fuskar ta tasan tasha kuka dan haka tace daga gidan uban wa kike kasa bata amsa tayi tana wasa da yatsun hannuta dadda tace wai ba magana nake miki ba dagowa tayi zatai magana dadda naganin fuskar ta kawa sai ta fashe da dariya saida tayi me isarta sannan tace Allah yaqara ya qara qarawa wanda beji bari ba ai bayaji hoho ba tana kaiwa nan tayi gaba abunta tana qara yi mata dariya ganin haka yasa Ameesha zaman dirshen agurin harda bubbuga qafafu aqasa me yasa dadda zatai mata haka me makon ta rarrasheta amma kawai sai takama yi mata dariya haka ta ringa kuka me sauti dadda da tundazu tana jinta bata kulata ba sai yanzu da kukan ya isheta tafito Ameesha baji fitowar dadda ba kawai sai jin saukar doruna tayi agadan bayan ta aikwa wata mahaikaciyar qara tasaki da kwanciya agun tana burgima dadda sake dagawa tayi ta qara tsula mata bulalar tana cewa uban wani ya aikeki saida nace karkije kidawo amma kika ki da na biki abayama sai ki ka buya ainasan halinki sarai kawai rabuwa nayi dake jikin ki yaga miki ni naso ma kindawo wani sashen jikin naki aballe da ma sun karkar yaki da sun burge ni wlh tana gama fadar haka tacqara daga bulalar zata zuba mata aikwa ta kwasa aguje tayi qofar gida tana kuka dadda taja tsaki ta koma daki tana cewa gwara da sukai miki hakan dan kinga ina lallabaki shiyasa kike min iskancin da kika ga daman to muzuba nida ke sha shasha kawai wacce bata da zuciya
Ameesha nafita tasamu waje tazauna taci gaba da kukanta sai yanzu take kewar iyayen ta Allah sarki tasan da suna nan da bazasu taba yi mata haka ba amma yanzu gashi ba me rarrashin ta saitaji gaba daya kamar duniyar ta juya mata baya ba me kula da ita haka taci gaba da kukanta gwanin ban tausayi kamar wacce tarasa gata gaba daya yau daya dan dadda ta dake ta shine take ganin kamar ma kowa ya tsane ta tana cikin kukan taji tsayiwar mutum agaban ta tazata dadda ce tazo ta lallasheta ta bata hakuri shiyasa taqi dagowa sai da taji andafa ta sannan sannan ta dago idon ta sai tai tozali da..........


Allah sarki yau ga yar shalelen dadda awaje dadda ta rufe ido ta dumama mata jikin ta da bulala 😂


❤xeemat....love❤
[2/28, 9:57 PM] ~~~~writer~~~~:   💅SARKI SAMEER.....💅
             by❤xeemat....love❤

              🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Ya ubangiji ka karemu mugunji mugun gani tsatsayi da asara fatara talauci annuba cin bashi gulmar mutane manufurci da duk wan abun da babu kyau Allah ya karemu daga aikatasu Allah ganar damu gaskiya duk abun da yaahige mana gaba Allah ya haskaka mana shi Allah ya dora mu ahanya madede ciya Allah yasa mudace duniya da lahira Ameen

Bismillah.......
Episode18🖋

******************
Dagowar da zatayi idanun ta suka sauka akan Azeema dake tsaye akanta da sauri tamike tare da dan waro ido sai kuma tadago zara zaran kyawawan yatsunta fari tas kamar ka dauka kadawo dashi jikin ka ta dora akan kyakykyawar fuskarta tashiga goge hawayen da suke zubowa suna wanke mata kan lausassan kumatunta sai yanzuma ta tuna da ashefa zata je gidan su tamanta na gabadaya wlh batagama tunanin ba Azeema da tun dazu ta zubamata ido takasa magana dan tana tsoron taji abun da zata fada mata dan ita tuna ninta bata yayi ko dadda ce ta rasu adan kidime tace subhanallahi kimin bayani wai meke faruwa me akai miki ne kike irin wannan kukan haka cigaba tayi da kukanta taqi bata amsa tambayar duniya Azeema tayi mata amma taqi bata amsa da taga haka kawai sai ta ruqo hannun ta tana janta zuwa cikin gidan suna shiga bataga alamar komai ba daze nuna mata cewa mutuwa akai saboda ba kowa sallama tayi taji shiru ta qarayi nanma shiru sai da tayi ta uku sannan dadda ta amsa daga cikin dakin sannan tace ku koma inda kuka fito idan tagama haukan nata kwashigo sai yanzu Azeema tagane abune ya hadasu da dadda ya akai yau aka gansu a rana ita da jikar tata jinjina kai tayi tace besty me yahadaku da dadda yau naganku arana wane zunubin kika aikata mata harta kaiki ga fita waje kina kuka yanzuma de banza tayi mata bata ce mata komai ba saide yanzu ta dena kukan sai faman ajiyar zuciya take saukewa na irin wanda yaci kuka ya koshi gana bata da niyar yin magana yasata qara jan hannu ta suka qarasa shigowa har bakin qofar dakin sannan tace dadda mushigo tace da ni na hanaku shigowa ne nacede kar ta shigo min daki da kuka dan wlh zan qara bata mata rai banaso sakarcin banza Azeema ta dan kalli Ameesha da sai faman sauke ajiyar zuciya take sannan tace dadda bakijita ba ai tayi shiru dadda tace bismillah zaku iya shigowa riqe da hannuta suka shiga ciki Ameesha na bayan Azeema tana ta faman rarrakubewa ta sunkuyar da kai taqi yarda su hada ido da dadda Azeema nagama shiga ta tsugunna ta gaishe da dadda da ta amsa mata taci gaba da cin fanken ta da ta soya musu tana ci tana korawa da ruwan bunu amma yaji kayan kamshi fuska adaure dadda ta amsa mata shiru dakin ya dauka na wasu 'yan dakiku sannan Azeema tace dadda wai me yahadaki da yar shalelen taki yau tace ni ba ruwana tagaya miki inda taje da bakin ta qara tambayar ta tayi saida ta jima sannan tagaya mata amma bata fadi abun dayafaru ba tsakaninta da Rasheeda kawai tagaya mata fitar ta da kuma buyan datayi sannan ta shiga cikin gidan sai kuma tayi shiru tana tunanin tagaya musu gsky ko tayi shiru wata zuciyar tace kifadi gsky kar kizo ki qara shiga damuwa da wannan tunanin na zuciyarta ta aminta dan haka kawai sai ta kwashe duk wani abu da ya wakana tagaya musu bata rage komai ba sai ta dorawa Azeema dace wa bayan ta dawo kuma dadda ta qara yimata shegen duk dadda tafa hannu tayi tace nashiga uku sharri kuma zakimin dan dukan danayi miki gida biyu shima bame yawa ba shine zaki ce namiki dukan tsiya to bari na qara miki sai kifi jin dadin bada labarin ta fada tana qoqarin tashi Azeema ce tayi saurin dakatar da ita tana bata hakuri komawa tayi ta zauna tace wlh sai mun fara sa qafar wando daya dake tunda rashin mutuncin naki kullum gaba yake bakya yin hankali idan bakida zuciya ma yanda sukai miki dukan kwanaki ko wani yace ki koama ai kyace baza kiba amma da qafar ki kika koma gidan wai harda buya dan kinganni ko Allah yaqara ai naso wlh suyi miki sukan da sai kin zauana jinya inyaso sai kidena zuwar musu gida Azeema ce ta ari bakinta taci mata albasa tace dadda kiyi hakuri dan Allah nasan ai daga yanzu baza tasake komawa ba kuma kinji ma ai ba girinsu taje ba dadda tace ai koma gurin uban wa taje aide cikin gidansu taje tace kinsan yarinya ce saikin mata uzuri sai a hankali zata ringa gane abin da kike nusanda ita dadda tace ni ina ruwana tama ci gaba ai jikinta ne zegaya mata itade Ameesha yau baki ya mutu ba bakin magana takasa cewa komai sai dana sanin fitar datayi take da taji maganar dadda da hakan duk bata faruba dadda data gama cin abincinta ta taahi tafita da kwanan tana fita Azeema tajuyo tace ke wai da gaske ne abun da naji kince tashi zakuyi da wasade kike ko tace mata wlh da gaske nake daman nima niyata ina dawowa daga gidan nasu inzo gidanku dan canai ma wuni zanyi saboda sai dare zezo daukar mu sai kuma gashi kinzo cike da mama ki Azeema tace nashigan gadi amma wlh baki da mutun ci yanzu kinsan zaku tashin shine sai yau zaki gayamin daman haka zaman tare yace Ameesha tace wlh bahaka bane nima bansan da taahin ba sai jiya daddare suka zo nikuma kinga ba wayace dani bare inkiraki Allah sarki Azeema akwai saurin kuka kawai sai ga ta tana hawaye tace wlh besty banji dadi ba wlh yanzu tafiya zakiyi ki barni shikenan nadena ganinki ita cikin raurau da murya tana shirin fara nata kukan taahiga gogewa bestyn tata hawayen sannan tace habade zan ringa zuwa akai akai ma saboda duk sanda yaya bossay zezo zanbiyo shi yasaukeni in yadawo sai ya dauke ni mutafi gida kuma koma banzo ba kullum fa zamu na haduwa a makaranta dan zance mishi yabarni ana basai ya canzan makaranta ba tace yauwa har na danji sanyi wlh amma wai ya akai ma zaku koma gidansu ya akai haka ta faru zaman ta ta gyara sannan ta fara bata labarin duk yanda sukayi tace gasky na taya ki murna Allah yasa qarshen wahalar ku kenan Allah yasa zaman can alkahairi ne agare ku tace Ameen de besty suna haka dadda ta kawo musu nasu karin kumallon tace gashi nan idan mutum yaga dama yaci inbega dama ba kuma yazauna da ciki badamuwa ta bace dan murmushi Azeema tayi tace haba dadda abun har ya akai haka ke da zakizo ki bata abaki taci ta qoshi amma zakice mata haka dadda tace ta mutu bata ciba Azeema tace to ai shikenan dadda yau dadda ashe tashi zakuyi to Allah yasanya alkhairi Allah yasa kuje a sa'a wlh na taya ku murna sannan ta dora da cewa muma abun farin cikine yasamemu wlh jiya shine dalilin zuwana gidan nan yanzu Ameesha cike da zumudin abun da ya faru tace besty me yafaru dan Allah gaya mana da sauri na matsu inji saida ta danyi dariya sannan tace wlh yaya saleem yasamu aiki awannan babban hospital din S.A.S spatial hospital baki bude cike da murna Ameesha tace dan Allah da gaske kike besty tace mata to zanmiki wasa ne kinsan yana ta nema besamu ba sai jiya aka dauke shi gobe ma ze fara zuwa taqarasa fada tana dan dariya daganin yanda Ameesha duk tabi ta kidime kamar ba itace me kukan mutuwa ba Ameesha tace besty tashi mutafi inyiwa yaya saleem Allah sanya alkhairi tace kin manta me yafaru dake yanzu ko amma tambayi dadda inta barki sai muje satar kallon dadda tayi aikwa karaf idonta ya hadu da nata da sauri tajanye tayi qasa da kanta dadda aranta tayi dariya tace almura ashe kina da kunya basarwa tayi kamar batasan me yafaruba tace kicewa mamanki ina taya ku murna Allah yasa albarka tace Ameen dadda daga nan dadda tayi shiru bata qara tanka musu ba Ameesha de duk tasha jinin jikinta tanaso tayiwa daddar magana amma bata san ta yanda zatayi mata ba Azeema ce ta taba Ameesha ganin ta tafi duniyar tunani tace kinga yanzu kici abincin inkingama sai kiyi wanka kizo kabawa dadda hakuri kitambayeta idan ta barki sai mutafi ko daga mata kai tayi sannan tafara ci tacewa besty kisa hannu muci tace mata wlh ta qoshi kafin tafito takarya bata ta kura mata ba akan sai taci sai tayi shiru taci gaba da cin fankenta daga nan kuma bawanda yaqara cewa komai ba kowa da abun da yake tunanin har tagama ta mike tafita da kwanon sannan tadawo ta daura zanin wanka taqara fita ta dau bokiti ta debi ruwa tashiga wanka
Azeema ta kalli dadda tace dadda dan Allah kibarta mutafi tare nima zanso hakan tunda kinga daga yau bazamu sake zama irin haka ba kibarmu muwuni yau daya de dadda tace ba komai kuje mana amma karki gaya mata sonake ta tambaya da kanta dariya tayi tace to dadda hakan ma mungode bata dade ba ta shigo dakin har ta gama wanka ahirya wa tayi shaf shaf sannan ta koma kusa da Azeema tace to besty nagama ki tambayeta mutafi kallon ta tayi itama mirya qasa qasa sannan tace ki tambayeta da kanki sai tafi yarda zaro ido tayi tace nifa gasky bazan iyaba tace to shikenan sai ki hakura da zuwan hade rai tayi ita adole haushin dadda take ji dan haka bazatayi mata magana gefe ta koma ta zauna tana ta faman hade rai kuma taqi cewa komai itafa taba tunani saide ta hakura da zuwan dade ace sai ta tambaye ta dan ayau batayi niyar yi mata magana ba kuma idan ta zauna har Azeema ta tafi gidan ba dadin shi zataji ba to yanzu yazatayi meye mafita......


                ********************
                     *MASARAUTA*
suna qarasawa bakin sashen dogaren suka tsaya daga waje shikuma ya shiga shikadai yana shiga bega kowa a falo ba dan haka Sai yasamu kan wata luntsume miyar hadaddiyar kayatacciyar kujera data gaji da kyau ga ado da akayi mata ita ba irin saraun kugerun falon bane an banbantasu da sauran duk da suma ba baya bane agun kyau din amma ita ta kere musu zama yayi yana zama jakadiya taho da hanazarin ta taqaraso gaban sa ta gurfane tana kwasar gaisuwa zata fara yi masa kirari kamar yanda ta saba saboda itace amintacciyar baiwar fulani shekaru da shekaru hannu yadaga mata dan yau baya buqatar jinsu tana gama wa tashi tace bari asanar da gimbiyar tafada tana nufar wajen corridorn da ze sada ta da dakin fulanin tana zuwa ta dakata tare da dan danna belt din dake gefe hakan yasa wadan da suke cikin dakin taji ance meke tafe dakai tace dan nazo insanar dake cewa me martaba ya qaraso yana yana falo yana jira tana gama fadar haka tabar wajen saboda tasan ba amsa zata samuba kuma hakance ta faru ba ace komai ba tana fitowa tace sarkin sara kuna daya tamkar da dubu kai sarki dan sarki kuma uban sarki kakan sarki in Allah ya yarda Allah yaqara maka lafiya da tsawon kwana Allah ya tsare gabanka da bayanka ya kare gabas da yamma kudu da arewa sama da qasa Shide yanzu be hanata ba har tagama sannan ta qara tsugunnawa ta gaidashi sannan ta tashi ta koma inda tafito tana fita kwa saiga sarki Muhammad SAMEER me murabus wanda yanzu suke kiranshi da PAPA qarasowa tunda yafito yake sakin qayataccen murmushi da ya lullube akan kyayyawar fuskarsa duk da ya tsufa amma kyanshi yana nan ba inda yatafi kuma kana ganin shi tun atafiyar sa zaka gane shidinfa jinin sarauta ne gaba da baya sarauta tabi sassa da gabobi da lungu da sako najikin shi da jinin yabi ko ina da ina yana qarasowa yazauna yana kallon dan nasa yace a'a Allah ja da ran sarkin mu ya qoqari ya fama da jama a ana wahala ko sarki yace papa ai rabin qoqarin ma ai ku kukeyi ni kadan ne nawa ni wallahi ma yan kwanakin nan nagaji da sarautar nan gaba daya bana jin dadin jikina gyara zama yayi sannan yace

Please Login or Register in order to submit comment