Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suke da yara biyar maza uku sai mata biyu
ABDALLAH, sai muhammad, sannan HASHIM,mata kuma suna da sumayya da ANISA,wanda a halin yanzu matan duk sunyi aure kowace ma da ƴaƴanta suma mazan duk sunyi aure amma banda auwal dake shine auta kuma dan gayune ƴan mata basa gabansa rayuwarsa yakeyi shikadai....

shikuma ibrahim galadima matansa biyu,yana da yara biyu kacal saboda dayar matar bata taba haihuwa ba sai uwargindan shice ta haifa mishi yaran AMINU da AMINA, aminar batai aure ba itama har yanzu sai babba dan shine wanda ya auri karima ƴar biyun munubiya wanda ayanzu suke da yara uku dake suma ƴan biyune sai Allah duk yabasu ƴan biyu itama tana da ƴan biyu amma mazane nata  AMMAR da AMAR sai autarsu RAHMA,

"sai Abdallah miji ga munubiya,sune iyayen sameer wanda akecewa sam sukuma wasu daga gidan  kakanninsa kenan irin su muhammad da qannensa sai kuma matayensu da wasu manya de wadanda suka isa dashi su  suke cemasa  mesunan baba saboda sunan sarkin da yarasu mahaifinsu wasu kuma sukan ce masa uncle sam, wasu kuma abokanen sa na school suke cemasa sas atakaice de yana da sunayen wajen hudu kowa da abun da yake cemishi,

SAMEER ABDALLAH  SAMEER  shima shine babba awajen su sai qannen sa mata da suma ƴanbiyu ne Hamra da Amra su ukune awajen iyayensu,
Sameer bashine kakansa ba a ƙa'ida sunan Alƙasim yakamata yasa ka to amma dayake sarki muhammad yadora duk wani da akan idan yataso to ƙarshen sunanshi sameer ze zama shiyasa kowa na family din da haka gake amafani sai yazama kamar family name dinsu kowa kaji sunan shi ƙarshe zakaji sameer...,

ina fatan kuna riƙewa da sunayen su domin duk wani suna da nafada ze taka muhimmiyar tawa acikin labarin dan haka dole sai kuna ruqewa kuma kuna tantancewa.....,

tunda aka haifi sam kullum yana sashen fulani saboda jininta ya hadu dana sa ko ba akawo shiba zatasa aje adauko mata shi tun bekai watanni yaye ba akai mishi yayan dole fulani ta dauke shi yaye tunda ga wannan lokacin bata maida shiba yadawo wajenta gaba daya shi da iyayensa saidai yaje ganin su ko su suzo sugan shi duk da acikin masarautar suke suma sam tun yana qarami yake da shegen miskilan ci ga taurin kai inya kafe akan abu koda za adake shi sai yayi idan kuma abun da akeso yayi ne nanma inbega dama ba ba wanda ya isa yasa shi yayi saide wani loƙacin yana dan shakkar papa idan yace yabar abun wataran yana bari saboda papa ya iya dabarun zama da yaro da gaka ya siye zuciyar sa har yake iya taƙwara shi yana jin maganar sa sosai,
irin wadannan halayen nasa ne yafara hadasu da fulani ita tana ganin ta riƙeshi kamar da amma ya taso bata isa tasakashi ba ko ta hanashi ba  ga baya shakkarta ko kadan duk irin shakkarta da muatane sukeyi shi bayayi ko kadan saima kamar rainine ya shiga tsakanin ta dashi gashi kuma tumda ta fara gane halayensa ta dena yimasa wasa da sakin fuska wai duk dan kar yarainata amma hakan da takeyi a  banza kamar ma qara zugashi take kuma duk da abun da yake matan bata taba tunanin maidashi hannun iyayensa ba saboda irin son da take mishi bazata iya rabuwa dashi ba,

dan loƙacin da yagama primary zetafi secondry sai mahaifin shi yace shi fiatar da dansa zeyi kamar yanda shima ba anan yayi ba saboda tunyana yaro shima mahaifinsa AlQASIM yakai shi gidan yayan mahaifiyar dan haka shima  bazeyi karatu anan qasar ba amma fur tace inde ba gori zasuyi mata ba dan sunga ba jikanta bane shiyasa zasu rabata dashi sukaishi karatu wata qasar tun yana yaro subari mana yagama secondary din annan inyaso sai sukai shi amma shide mahaifin shi yace duk da haka beyarda ba  kawai tayi hakuri tabarshi yayi abun da yayi niya haka sukai ta fafatawa  sai da ƙyar papa yasa baki sannan  aka kaisa amma badan taso ba loqacin tafiyar sa kwa tasha kuka haka tana ji ta gani bata da iko akai aka dauke shi aka kaisa qasar  England mahaifinshi ne yakaishi gidan yayan mamansa inda shima yayi karatu....✍

Wayata ba caji wlh kuma bamuda wuta idan nace zanyi da yawa to yau bazeyiyu inyi Posting ba kuma banaso ina tsalaken rana banyi ba shiyasa nayi muku dan kadan amma ana yau ko rabi banyi ba I'm sorry...
[3/22, 10:26 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode52-53

         """"""""""""""""""""""""""""""""""

tunda yatafi be dawoba saida ya kammala secondry tsaf sannan yadawo lokacin da yadawo yana dawajen sixteen years acikin halayensa babu abunda ya canza saidai ma ƙaruwa ko magana kayi mishi sai yanuna maka kamar ma besan me kace ba tamkar miskilan ci yaje ya koyo acan gashi baya son mutane inde guri ya wuce mutum biyu to ze tashi daga wajen saboda bayason hayaniya ko kadan saboda inkana mishi magana sai yaji kamar ana mishi ihu akai idan kwa yaro yayi gangancin shiga hurumin sa yofa sai jikin ka yagaya maka abu kadanne yake saurin fusayashi kullum zuciyar sa akusa take kamar ya kuturun jaki shi kwata kwata besan wani wasa ba arayuwar sa komai kayi masa kawai a
serious yake daukar sa ga baya dariya kullum fuska ahade saboda inda yaje ma subiyune agidan dagashi said  dan qanwar kakar sa tasa shikuma babba ne kullum yana aiki dan haka basu fiyama haduwa dashiba shiyasa yataso shikadai yake rayuwar sa acan idan kaganshi awaje to makaranta zeje ko kuma an takura mishi akan sai yafito yaci abinci saboda shima be dameshiba shide kamar ba mutum ba koman sa yasha bambam dana mutane,
Abu da yasani arayuwarsa shine karatu, karatun sa kawai yake duk jarrabwa da za ayi shiyake daukar first yana da qoqari sosai fiya da tunanin me karatu dan wasu malaman har mamakin qoqarinsa tunda yashiga be taba aboki ba duk wasu suna so suqulla abota dashi amma be basu fuskar hakan ba saboda cukulewar da yake musu,
abokinsa daya kaf duniya shine dr shettima,
shima saboda tare sukayi primary wanda tasanadin sa ne shettima ya shiga makarantar saboda basu da hali dagashi sai mahaifiyar sa suke zaune mahaifin shi ya rasu awani farmaki da aka rufar musu na yan boko haram da suka kai musu farmaki a garin meduguri ana ya rasa mahifin shi suma da qyar sukayi hijira zuwa kano,
to lokacin da suka dawo kano yana ba inda suka sani basu san kowaba sai Allah yahadata munubiya a hanya shine ta taimaketa takaita masarauta bayan taji labarin ta kuma tasan baza ataba bari ta zauna anan ba da niyar zama dindindin sai takama mata gida akusa dasu tabata jari amma tana shigowa cikin masarautar sosai sugaisa harde shima shettima yadan fara wayo to sai yaza mana abota ta dan shiga tsakanin su saboda halinsu yazo daya daman ance sai hali yazo daya ake abota har yazamana shettima har kwana yake yi awajensa saboda tasu tazo daya lokacin da aka saka sam a makaranta shine ya takura akan saide asakasu da shettima dake kowa yasan da abotar tasu shiyasa ba ayi musuba aka sakasu tare lokacin kuma daze tafi katatu England ba yanda beyiba akan sukaisu tare amma akaqi akace zade abiya masa yayi anan harda kuka da qyar aka rabasu lokacin da yadawo ba qaramar murnar ganin juna sukayi ba saboda sunyi missing din junan su sosai to awannan dawowar ne kuma tunda yafara hankali da girmansa yatada hankalin kowa akan shifa inde baza akaisu tare ba su dora karatun su tare  to saide shima baze qara komawa ba ze zauna anan harda barin gidan su ya koma gidan su shettima anyi anyi dashi amma yaqi kuma shi yana da wani abu inde yanason abu ba ayi masaba ko aka takura masa akan sai yayi abun da beyi niyaba to har suma yakeyi wataran ma sai ankwantar dashi a asibiti ganin hakan yasa mahaifiyar shettima daman tana dan kasuwancin ta na kayayyaki tana siye da siyarwa saita hada duk kudin ta da jarin da uwara abun amma ta dan rage abun da zata iya juya wata sana'ar amma bawai babba sana'a ba qaramde wanda bazata shiga matsiba sosai da tahada sai taje sukayi magana da munubiya akan ita zata biya masa akaisun tunda suna so munubiya(momma)tace mata ai matsalar ba wai ta kudi bace inde kudine ko ita zata iya biya masa yayi karatunsa tundade sunadashi matsalar itace  gidan da zezauna gidan da sam yake zama matar suna da qabilanci inba jininta ba bazata bari wani ya rabetaba saboda basu da yarda sosai, bayan tagama gaya mata dalilin da yasa basa son danta yaje dan ita atunaninta daman tazata kude ze hanasu yin hakan kuma tasan de suna dashi sai yanzu taji inda matsalar take,

shiru tayi na dan wani lokaci kafin ta sauke numfashi tace to naji dalilin amma ga wata shawara mana me zehana inbashi kudin sai yakama hostel ko kuma qaramin gida kinga aide suna tare kuma hakan zasuji dadi duba da yanda duk suka saka kansu cikin damuwa ni ina ganin gwara kawai muyi musu wannan taimakon bamusan me Allah yake shirya wa ba dalinlin tafiyar tasu tare gashi kuma da shaquwa a tsakaninsu  dan haka kawai mucika musu burinsu idan ba matsala Allah sa hakan shi yafi alkhairi amma yakike gani tafada tana kallon momma danjin amsar dazata bata itama shirun tayi tana nazarin maganar ta saidaga baya tace to shikenan sai muyi hakan zanyiwa abbansu magana inya amince zakijini yanzu kije da kudinki bazan karbi ko sisikin ba ai munfi qarfin yar haka tsakanin mu daku kawai kije duk yanda mukai dashi zan sanar dake kije kawai kifara shirye shirye amma kar kigaya musu inaso muyi musu surprise bakaramin dadi hajiyar shettima tajiba tayi mata godiya sosai harda dan guntun hawayenta dan matar nan tagama yimata komai arayuwar ta ta taimaketa sosai tunda tazo garinnan take dawainiya da ita bata taba kukan wani abuba ta rasa bazatavbiyata da komai ba saide addu'a sosai tayi mata godiya sannan ta koma gida,

bayan sati biyu da maganar komai sun shirya Amma yaran basu saniba kuma sam bekoma gida ba yana gidan su saida ana gobe da tafiyar tasu Papa yazo da kansa yatafi dashi gida da qyar ya yarda,

Washe gari tun wajen qarfe goma daga kowane bangare suka fara shiryawa shide shettima yaga ana ta shiryashi da yatambayi hajiyar sa sai tace masa tafiya zasuyi zuwa meduguri jin hakan yasa shi fara murna ance zasuje meduguri yana son zuwa ganin danginsa amma Hajiya bata taba kaisa ba sai yau yaji dan haka saima yamanta da wani bacin ran rabuwarsu da sam wajen shadaya suka gama komai hajiya sannan suka fito daga gidan zuwa cikin masarutar saboda tsakanin su ba nisa suna shiga suka ga suma sunfito ana shirya kaya acikin boot ga mutane kowa yafito dan yin sallama dashi da gudu shettima yaqarasa tare da rungume sam loqaci guda kuma sai suka sa kuka papa yana musu dariya yace haba wlh kunban kunya manya daku kuke kuka sai kace qana nun yara kunfa zama manya abokai na kowa na gurin sai dariya yake musu saida dady mahaifin sam yace to ya isa haka sai kashiga mutafi kana qara bata mana lokaci wani kukan suka qara saki harda shassheka fulani ce dataga wanasun ya isa haka taje gabansu ta rungume su gaba dayan su sannan tace to ya isa haka adena wahalar min da jikoki albishirin ku yan samari kuban tukuci kafin kuji rabasu tayi da jikinta tana kallon su sannan tace ina sauraron ku me za aban idan nafada shettima mane yace ko me kike so shikwa sam duk taqaici yacika shi sai yawani juyar da kai irin ki fada ko kar kifada ke yashafa kallon sa tayi tace au juyar dakai zakai to shikenan nafasa fadar shettima mana ne yace kar kibiye tashi na ai nace zanbaki komai kikeso na ari bakinsa saida tagama jan lokaci sannan tace burinku ya cika na kasan cewar ku tare yanzu kowa ya amince da tafiyar ku England ai tun kan tagama rufe baki kawai taji sun rungumeta atare qam kamar zasu ballata sannan suka saketa shettima yace dan Allah da gaske kike mama tace daman inamaka wasane?
" yace a'a"
sam ne ya maida kallon kallon sa ga momma dinsa suna hada ido sai yaga ta galla masa harara hakanne ya tabbatar masa dacewa gaskiya ne abun da fulani tafada besan lokacin da yasaki murmushi ba, kowa saida yayi mamaki yau shine da murmushi lalle wannan rana ta da bance shima shettima kallon hajiyarsa yayi ita kuma ta sakar masa murmushi da sauri yaqarasa kusa da ita ya rungumeta hakade duk suka bi iyayen nasu suna rurrungume su tare da yi musu godiya da nuna farin cikin da suka tsinci kansu nande papa yabasu labarin yanrda aka shirya komai sunyi mamaki sosai dajin labarin,dady yace to sai mutafi ko tunda burin ku yacika murmushi sukayi dukan su batare da sunce komai ba,

Papa ne yadora musu da nasiha me ratsa jiki sannan kowa ma yafadi albarkacin bakinsa bayan sun kammala yi musu nasihar kuma sai suka bude mota suka shiga tare da qara yiwa kowa sallama sannan driver yaja mota zuwa airport suna ta dagawa kowa hannu harde sukabar masarautar gaba daya,finally de suntafi tare kuma zasu fara karatu tare kamar yanda suke so,

"Agurguje"

bayan sun kammala degeree dinsu kowa yadawo gida da kwalinsa me kyau kuma acan dinma cos daya suka karan ta bagaren likitanci daga nan kuma suka qara komawa inda suka qaro da masters yanayin kwazon sam yasa yasamu aiki acan dan maganar gasky yafi shettima qoqari Allah ya hore masa kwakwalwa gashi kuma daman gidan dayazauna mijin matar gidan shima babban likita ne tasanadin shi yasamu aiki aacan din,,


da farko de kin amincewa yayi saboda baya so surabu da shettima saida dady yaja kunnen shi da nuna mishi amfanin karbar sannan yakarba amma badan yaso ba ,
duk dahaka kuma yana qara fadada ilimin sa dan be tsaya iya nanba,

Alokacin da shikuma shettima hajiyar sa tace yakamata yadawo sai yanemi aiki awani hospital anan saboda zaman sa acan din beda amfani, hakade ta dan yi mishi nasiha sanna yayarda zedawo din
bayanda suka iya haka ya baro shi acan shikuma yadawo gida,

bayan da wowarsa ba dadewa Allah cikin ikonsa dake kuma karatunsa da na nan badaya ba yana zuwa neman aiki awani babban hospital ya samu ba bata lokaci yafara aiki acan inda yake daukar albashi me tsoka dan kudin da yafara tarawa har yafara ginawa musu gida babba me kyau gaske ahaka har yakammala yamayar da mahaifiyar shi unguwar nasarawa GRA badan tasoba haka suka rabu da momma,

Abangaren sam kuwa yanzu yazama wani babban likita acan saboda yanda yake samun kudi sai dadyn sa yabashi shawara akan ya gina babban hospital anan inyaso sai ana juya mishi tundade kudin ba wani abu yake dasuba haka kuwa akai inda yafara turo kudi aka fara gini ma aikatan ma bana nan qasar bane daga can ya turo su suka zo sukayi aikinsa adan lokaci akayi komai akagama aka tsara shi tsari irin na can,
"Inda aka sanyawa asibitin suna da S.A.S SPECIAL HOSPITAL bayan kammala shi komai ya daidaita anzuba qwararrun ma aikata,

shikuma sai ya dora shettima akai yana kular masa da komai da komai saboda baya zuwa sai yafi shekara ma be zoba sai yasamu hutu yake zuwa sannan ya koma,
saide kuma ko idan wata babbar matsala ce wacce ba kowane likitan ze iyaba kamar de irin ciwon Ameesha brain trauma (haduwar jini da kwakwalwa)
irin wannan ciwon bakowane yake aikin sa ba musamman anan saide inza ayiwa mutum a fita dashi wata qasar ayi masa saboda yana da matuqar hatsari sai kwararre ne yake iyayin sa...........,

Cigaban labari.......

suna qaraswa part din momma kai tsaye suka shiga ciki lokacin da suka shiga ba kowa a falon zama sukayi suna cigaba da hirar su basu dade ba saiga Hamra tafito daga kitchen tana ganinsu ta taho da gudu ta basuga fitowar ta ba sai ganin ta sukayi agaban su da murnar ta ta fada kan sameer ta rungume sa tana cewa bro sai yanzu zaka qaraso tundazu muke expecting din ganin ka amma sai yanzu zamu ganka dan Allah ka kyauta kallonta ya shigayi sannan yace daga ni to ya isa haka da kinason ganina ai da kinje inda nake kin nemeni ko baki san inda nake ba tace walh momma ce ta hana mu zuwa wai mujira kazo amma kasan da tuni nazo saboda nayi missing dinka sosai tafada lokacin da ta tashi daga kansa tana manna masa kiss a kumatu hannu yasa daidai saitin da tayi masa yafara gogewa harda sa gefen rigarsa yana gogewa sai kace ta shafa mishi kashi awajen kallon sa tayi amma bata ce mishi komai ba tasan halinsa daman yasaba wataran kayi masa gwaninta ma sai ya gwaleka amma batayi tunanin wai dan tayi mishi ze goge bmgurin mema yamayar da ita kenan me yamaida ita ,

Ganin hakan yasa dr.shettima yadanyi dariya yace gwanda haka ai Allah ya qara naji dadi wlh tunda abun yar wariyar launin fata ce kallon ta tamayar kansa sannan tace wallahi ba hakabane yace bawani nan ni jeki kiramin mutuniyata nasan da itace bazata min haka ba ni zata fara gaidawa kafin shi amma ke kin nunama kamar baki ganni ba ko nagode tace dan Allah kayi hakuri ni wlh bahaka nake nufi ba yace ke kikasani nide jekikira min ita na matsu inganta tace au ni baka sona ganina yace of course sameer ne yakatse su da cewa kije kisanar da momma zuwan mu juywa tayi ranta duk ba dadi saboda abun da sukayi mata shi ya gwaleta shikuma yace baya son ganinta jiki a sanyaye ta juya zata bar wajen dan har kwalla ta fara tarar mata a ido ganin hakan yasa sameer kiranta yana sane yayi mata haka saboda yasan halinta daman akwai saurin fushi ita bata san wasaba komai inkayi mata sai ta dauka da gaske kake juyowa tayi jiki babu kwari ta dawo sai ta tsaya agabansa kanta aqasa tace gani saboda saura kadan ta fashe cewa yayi dago idonki kasa dagowa tayi saida yace ba magana nake miki ba dagowa tayi ahankali lokacin hawayen da take ruqewa har sun qarasa saukwa buda mata hannun sa yayi alama tayi hugging dinsa ba musu kuwa ta fada kansa sai kuma taqara sautin kukanta yace meye haka kuma daga wasa ke matsalata dake kenan baki san wasaba yafada yana dagota daga jikinsa sannan ya share mata hawayen yace to ga fuskar sai ki qarayi kiyi yanda kike so ko kunya kuwa bata jiba ta qarayi masa guda uku tana dan murmushi sai yanzu taji sanyi aranta suna ahaka kuwa saiga Amra ta sauko daga ita sai best da wando iya gwiwa ta kama gashinta da ribom yasauka gadon bayanta tai kyau gata kuma kyakkyawa(qanen sameer ai daman dole suyi kyau) amma fa bata kaishi ba wayace a hannuta tana tafiya tana cewa baby hamra besty na kiran ki nadaga kuma nace kina bandaki kina turuso😂(kashi😷) da sauri hamra ta sauka daga kan sameer ta nufe ta tana cewa wai ke meyasa baki da hankali ne dan Allah da gaske kike ko da wasa tace da gaske mana ni ai bana qarya kinsan halina tafada tanayimata dariya tare da mika mata wayar tace inkina ganin qarya nake kikirashi ki tambaye shi ze gaya miki ai harara ta dalla mata tace ai ni ina da hankali ba tababbiya bece walh kin kasheni yanzu da wane ido kike so inkallesa wlh baki hadu ba duk mijin da ya aure ki ya auri mahaukaciya tafada tana fusge wayar ta daga hannun ta tace wlh nide ba mahaukaciya bace kar kikara cemin mahaukaciya inba haka ba kuma hmmm tace in bahaka ba me zaki dakenine tace taya zandakeki amma de ni nasan abun da zanmiki kinsan halina innace zanyi tofa sai nayi dan haka kiringa kiyayewa ki iya bakin k.......kasa qarasa maganar tayi sakamakon idon ta dayayi mata tozali da abun da bata taba zata ba dan batayi tsammanin ganisaba tunda ta sauko kuma bata lura da shiba sai yanzu shikenan tasan kashinta ya bushe ai da sauri tajuya da nufin guduwa tajiyo muryarsa yana cewa wallahi inki bar wajennan sai na canza miki kammani marar mutun ci tsayawa tayi cak amma takasa motsawa dan bata da niyar juyowa,
sai nazo na sameki anan kenan?
da qyar ta iya daga qafarta ta juyo kamar wadda kwai yafashewa aciki ahankali take tafiya kamar wata mutuniyar kirki har ta qaraso wajen sa ta tsugunna gabansa kanta aqasa,
Yace sa'ar kice ita da kike mata wannan rashin kunyar ban hanaki yi mata rashin kunya ba kinmata laifi tayi miki magana kuma kin hauta da rashin kunya daman idan ina nan sai kinuna min kinshiryu sai natafi kidora daga inda kika tsaya ko to yau zanyi maganin ki in akace kiyi mata kallon banza ma baza kisake yi mata ba,dan Allah dan Annabi kayi hakuri wlh bazan sake ba daga yau na tuaba bazan qara yimata rashin kunya ba dan Allah kayiwa Allah kar kataba ni kuma kar kabani punishment wlh banda lafiya jiya na farfado daga rashin lafiya saida aka qara min ruwa leda huda sannan nasamu sauki kuma har yanzu banji sauqi ba sosai yace baki da lafiya amma kina da bakin yiwa wani rashin kunya ai idan jikin ki yagaya miki sai kiyi jinyar gaba daya,
Dr. shettima da yake ta binsu da kallo sai yanzu yasa musu baki yace dan Allah ayi mana afuwa baza musake ba tunda de bamu da lafiya idan munji sauki sai ayimana hukuncin koma ahakura gaba daya yajuya yakalli hamra yace ai kin hakura ko sister baki ta turo gaba tace wlh ban hakuraba qarya take lafiyar ta qalau ba wani ruwa da aka qara mata dukan su da mamaki suka bita da kallo dr.shettima yace da gaske lafiyar ki qalau kai ta girgiza masa tace itace take qarya so take kawai adakeni amma banda lafiya ko momma za atambaya aje atambayeta hamra tace wlh ba qarya nake mata ba lafiyar ta qalau kuma aje atambayi momma din hararar ta amra tayi sannan tace kide ji tsoron Allah me qarya dan wuta kan ajima yamutu idan kika mutu wlh ba ruwan mu ke kika cuci kanki cigaba zamuyi da rayuwar mu cikin jin dadi da walwala wata uwar tsawa yadaka mata da tasata hadiye maganar ta yace idan naqara jin bakinki saina zubar miki hakura anan shiru tayi tana muzure da idanuwa, gashin ta yaja da qarfi kamar ze tsige mata shi qara tasaki tare da sa hannun ta akana nasa tanaso tacire nasa hannun nata ya ruqe tare da lankwasawa ya murde mata shi sosai har saida yayi qara sannan yasake ta kuka tasaka tana cewa wayyo Allah na hannuna ya karye wlh ka karya min hannu tafada tana dafe hannun tana cewa momma kizo ki taimake ni hannuna ya karye gida biyu qashushuwa na duk awaje suke momma momma hannu yasa ya buge mata baki ya miqe yana niyar fara dukan ta dr.shettima yayi saurin janyeta yana cewa dan Allah ka rabu da ita haka ai hukuncin yaya yawa be saurare saba ya qara yunqurin kamota shima yayi baya da ita yace Allah baza ka qara tabata ba yarinyar nan fa bata da lafiya amma kaki sauraren ta ka hauta hauta da fada ko sokake ka kasheta ne yace eh kashetan zanyi gara ita tafara mutuwar mu saimuyi murnar sha shasha wlh ina baki wasa ba sai na babbala ki agidan nan kafin natafi ke kwata kwata bakyason kwanciyar hankali rayuwar ki sai jawa mutane masifa hamm yana kaiwa nan yafara qoqarin fita sai ga momma nan tafito tundazu tanajin hayaniyar su tun tana cikin bathroom

Please Login or Register in order to submit comment