Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai ya kai kasansu yace agidan su Rasheeda yariyar take aiki tanan muka saba da ita harna nagane wasu abubuwan daga garesu karka ta kuma tana aiki tanayi yan kulle kulle nakayan yara tanakai wa makaranta tasiyar  sannan kuma tana kula da yaran makaran tar itace de kamar nani din makarantar tace to yanzu kai yanzu ta ina kakeson mutai maketa yace sonake tadawo gidan nan da zama tace to ita kuma kakar tata kana ganin zata yarda tabayar da ita shiru yayi yakasa bata amsa saida tadan taba shi sannan yasauke ajiyar zuciya yace ai abun sa yasa kenan nagaya miki ke zakije da kanki ki lallabata dan wlh rikitacciyar tsohuwa ce bata da yarda kinga abun da tai min kwa danaje dakaina na tambaye ta nasha tijara da zagi dan wlh da har nayi zuciya ma akan bazan kara wai wayarsu ba amma danayi tunani sainaga be kamata inyiwa yarinyar nan haka saboda tadan saba dani dan da kyar ma tabarni nataho dan catai ai ko kakarta bata barta ba sai tabiyo ni saida nai mata wayo sannan ta rabu dani na taho akan zankoma in dakko ta gashi yau kwana uku kenan amma banje ba duk sai nake jin badadi Ammi tace me kace mata da har tazage ka yace wlh Ammi bawani abu nafada ba kawai rikicine irin nata harda min kuka fa wai zan rabata da jikarta inje insiyar da ita ko in lalata mata jika nan de ya kwashe duk dramar da sukayi da dadda yabata labari aikwa Ammi tasha dariya tace gaskiya kasha tijara nikuma ahaka da kake cewa muje so kake nikuma tayi min duka ko yace Ammi ai ke babba ce bazatai miki abun da tai minba wlh na dade ina tunanin tsohuwar nan tace yanzu yakake so ayi yace kawai kishirya gobe muje amma wlh bazan shiga ba tace aikwa sai ka shiga taya kakeso inshiga nikadai alahalin bata sannni ba kawai shahada zakai mushiga tare inta yarda to in kuma bata yarda ba shikenan  kaga ai baza muyi mata dole ba yace hakane Ammi Allah yakaimu goben sai muje Allah yasa tayarda tace Ameen amma zanso inji labarisu gaskiya daga ji akwai wani abun da yafaru da rayuwar su abaya taya za ai ace sukadai suke rayuwa basu da kowa yace wlh nima de abun yana bani mamaki inaso inji suwaye su tace to mubar komai de sai goben kaje ka kwanta dare yayi yace to shikenan saida safe yafada yana tashi tsaye tare da nufar hanyar part din itama ta tashi ta wuce nata sashen kowa yatafi da tunanin yanda zasuje gidan dafatan samaun nasara..........

       *****************************                                         
             **********************
     *MASARAUTAR SARKI SAMEER*

Kamar yanda sarki yace hakance tafaru acikin kwanaki ukun da suka wakana yau ce ranar da za a fito dashi
bayan sallar isha'i sarki yabada  izinin aje afito dashi bayan kowa ya hallar acikin fadar sukaje suka fito dashi Allah sarki kana ganinshi kasan baqaramar wahala yasha ba dan daman ance wuya bata kisa sai lokacinka yayi dan da tanayi da tuni bawan Allah nan yadade da mutuwa saboda ba qaramar wahala yasha ba dan har rama yayi ga duhu da yaqara yi duk yabi yazama wani irin dashi kamar bashi ba  lokacin da aka shigo dashi cikin fadar duk wani me imani inka ganshi sai ka tausaya masa yana shigowa sarki me murabus ne yadago yana kallon sa aranshi yana tunani shiko a ina yasan fuskar bawan Allah nan kamar yasanshi ko kuma me kama dashi yasani oho yakasa tunawa har mutumin yaqaraso ya gurfanar da kansa  agaban sarki  tare dayin gaisuwa ga sarki sannan yajuya kan duk yan cikin fadar ya gaida su duk yasan da yawan mutanen wajen ya girme su wasu ma ya haifesu amma ahaka ya qasqantar da kansa agaban su yana gaida su wasu suka amsa ba yabo ba fallasa wasu kuma suka amsa a wulakance wasu ma daga ciki ko kallo be ishesuba bare yasamu su amsa koda awulakan ce nan be damuba yayi shiru yana jiran hukunci  da zeji saida kowa yayi shiru gun yayi tsitt kamar ba mutane aciki Fulani  ce tafara yin gyaran murya kowa kuma ya maida hankalinsa gare ta sannan tafara magana kowade yasan abun da yatara mu anan basai naqara bayaniba dan haka ni matar sarki me murabus kuma uwa ga sarki ma yanzu nayarda da hukuncin da sarki ya yanke da kuma zaman wannan mutumin a masarautar nan  kuma daga yau yazama bawa agidan nan daga nan har sanda ze bar duniya ina fatan kowa yaji duk suka jinjina kai cike da gamsuwa da bayanan ta sannan ta dora da cewa gobe ze fara aiki za a bashi kula da bangaren dabbobi da doku na da basu ruwa da abinci ina fatan kowa yaji inda me magana kuma nabaku minti biyar me magana yayi kowa shiru yayi ba wanda ya iya cewa komai bawai dan basu da abun cewa ba sai dan kawai gudun idan mutum yayi bayarda za ayi ba saide ma yajawo wa kansa wani fadan dan haka bawanda yace komai jinahiru nasu yasa Fulani cewa kowa ze iya tafiya sannan kuma azo adauke sa akaishi bangaren bayi abasa kayan bayi yasaka gobe a nuna mishi yanda zeyi aikin wani bafade da yashigo dazu yace to ranki yadade sannan yakalle sa yace taso muje ko ahankali ya yunqura ya tashi yana tafiya da qar  bayan fitar shine sarki me murabus yace yakalli Fulani zeyi magana amma sai ta daga masa hannu alamar bata so yace komai haka kuwa yayi duk wannan abun da suke yi sarki be tsoma musu baki ba  bece qala ba daman haka suke inde Fulani na gurin tofa baya cewa komai saboda tun kafin azauna zasu tattauna komai da mahaifiyar sa sai abun da tace za ayi dan sai yazama na ma kamar itace sarkin komai a hannun ta yake ba a isa anyanke hakunci ko wani abun yafaru batare da ansanar da ita ba komai ita take gudanar dashi ba wanda yake da iko acikin masarautar sai da amincewar ta sai yanzu sarki yace mama angama ai zan iya tafiya tace eh nagama zaka iya tafiya sarki ya miqe yafita dagaron sa suka mara masa baya zu sashensa inda iyalain sa suke daman kowa ya watse daga cikin fadar sai yarage daga Fulani sai sarki me murabus sai dayar matar sa me suna *SA'ADATU* wacce ake kira da maman 'yan biyu, maman yan biyu itama mata ce gurin sarki kishiyar Fulani Amma ita halinta ya dan bambamta da na Fulani ita bata dauki duniya da zafi ba mata ce me hanakali da nutsuwa da sanin yakama ta bata shiga kuma abun da ba ruwan ta hasali ma bata da yawan magana bata da surutu kwata kwata komai zataga Fulani nayi bata taba tanka mata saide tabita da ido koda tasan kwa abun da take yi din badede bane saide ma taqara kawar da idonta daga abun da taga tana yi shiyasa ma basa samun matsala da Fulani dan Fulani matace meson a girmamata kuma duk abun da mutum yaga tanayi to ya zuba mata ido batasan ana shiga lamarin ta in ba ita taso hakan ba sai kuma Allah ya hadata da irin wacce take so yanzu made kamar koda yaushe haka maman yan biyu batace komai ba akan al amarin ta sai ta miqe tace ni na wuce sai da safenku sarki kawai yace mata Allah yakaimu sannan tace Ameen tayi ficewarta tabarsu agun sarki ne yace to gimbiya muma ai sai mutafi ko anan zamu kwana ne batace mishi komai ba kawai ta miqe tace muje ko yace to haka ya mike tasashi agaba kamar danta sukabi tabayan qofar inda ze sadasu da nasu part din.................
   
                **********************
    *WAIWAYE ADON TAFIYA*
Kowa yagyara zama domin fahimtar yanda labarin ze kasance
            
MASOMIN LABARIN masarautar sarki sameer

SARKI SAMEER shine sarki nawajen hamsin da wani abun yagadi sarautar ne awajen baban sa wandan shima gada yayi tundaga sarkin farko sarau tar taringa tafiya harzuwa kansa shima kuma tun kan yamutu yabawa babban dansa sameer kenan sameer yana da qanne hudu kuma duk mazane shine babba shiyasa babansa yabasa sarautar kuma ya yaba da hankalin sa yasan kobayan ransa ze ruqe al'uma zeyi adalci a sarautar sa kuma hakanne yafaru domin yayi adalci sosai iya kacin iyawarsa duk wanda yake awannan lokacin ze yaba da sarautarsa kama daga yan gari yan cikin masarau tar har bayi ma da jaka diyu babu wanda akabari kowa alfahari yake da mulkin sa sarki sameer yana da mata uku uwar gidan sa me suna *KARIMA* karima tana da yaya uku danta na farko shine *MUHAMMAD* na biyu kuma *ALKASIM* na ukunsu kuma *IBRAHIM* sai matar shi ta biyu me suna *ASIYA* itakum tunda suke bata taba Allah be bata haihuwa ba ta ukunsu kuma Amarya agun sa sunan ta *SHAMSIYA* ita kuma  yayanta biyu duk mata kuma daya tarasu saura daya me suna *HANNATU* kan matansa duk ahade yake bakajin kansu saide abun da ba a rasaba yau da gobe sai Allah zo muzauna zo musaba daman zama yagaji haka tun yana aiki da qarfin sa har yafara gajiyawa domin tsufa yazo mishi gashi babban dansa da yake so ya dora akan karagar mulkin shi ya nuna mishi baya ra ayin sarautar tun tasowarsa bayaso dan hakama yaroqi me martaba akan shi bazeyi karatu anan ba a Egypt zeyi karatu ba musu kuwa sarki ya amince da qudurinsa yabarsa yatafi acan yayi karatunsa gabadaya lokacin da yadawo yanaso yafara aiki sarki yace be isa ba dole ya karbi mulki ko yana so ko baya so da farkode kin amincewa yayi har saida mahaifiyarsa ta sa baki akan inbe karba ba ransa sai ya baci kuma akace mishi kafin lokaci nadin sarautar yayi suna so yafara aure inkuma bashi da ita zasu zaba aikwa dasauri yace ai yana da ita akace a ina take a Sudan take tun farkon fara karatun sa suka hadu sundade tare kuma iyayen tama sunce zasu bashi yaturo da iyayensa dukan su sunyi farin ciki sosai dajin batun dan nasu dan haka ba bata lokaci akaje aka nemo masa auren ta yakasa wata daya tal sannan suka bayan sundawo ne kuma aka kara ce mishi saifa yayi hakuri dan dole sai yakara da wata matar domin qa idane sarki yakasance da mata biyu yace shi gaskiya bashi da wacce yakeso abar shi da iya wannan ma ta ishe shi suma kuma sukace baza suyarda ba dole yayi hakuri ya amince akace za abashi yar qanwar Asiya kishiyar mamansa kenan yace to beyi musu ba yakaba itama rana daya akasa da na *SABREENA* sunan wacce ze aura kenan ita kuma tabiyun daza a aura mishi itace *MARYMA* rana bata qarya yau kadaura auren Muhammad da matan sa Sabreena da kuma maryama dana din sarautar sa yau yazama ango kuma sarki ba a wani dadeba dayin hakan Allah yayiwa sarki sameer rasuwa kowa yaji mutuwar nan sosai ta girgiza mutane da yawa ahaka har aka dauki kwanaki duk da baya son sarautar hakan be hanashi gudanar da mulkin sa ba cikin adal ci kamar yanda mahaifinshi yake yi dan harma yaso yafi mahaifin nashi komai yana tafiya yanda yakamata.................

        ****************************
daga sabuwar marubuciyar ku🖋
                       By
            ❤xeemat....love❤

don't forget pls comment and share it
My WhatsApp number 08124226426

https://www.wattpad.com/user/xeemat?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
      [2/23, 10:23 PM] ~~~~writer~~~~:   💅SARKI SAMEER.....💅
             by❤xeemat....love❤

           🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Allah ya gafarta mana ya yafeman kurakuranmu wanda mukasani da wanda ma bamu saniba Allah ya shige mana gaba aduk kanin al amuran mu yabamu yanda zamuyi Ameen..........

                   Bismillah........
Episode13🖋
          **************************
Tunda yake zaune da matansa be taba jin kan matansa ba suna zaman lafiya da juna har sukai wajen shekara biyu amma gaba dayansu bawanda Allah yabawa ciki ko batan wata bawanda yataba yi dan har mahaifiyar shi Karima tafara yi mishi maganar ko ze kara aure ne amma sai yace mata tayi hakuri sukara hakuri zuwa nan gaba ko Allah zesa wata daga cikin su tasamu bata takura mishi ba ta rabu da shi ta cigaba da zuba musu ido ahakade har suka qara daukan lokacin kwatsa saiga amaryar sa SABREENA da ciki saboda lokacin da akayi aure duk da yafi sonta amma bada ita yafara kasance wa saboda ita ba aranar aka kawota ba shiyasa yafara kasance wa da MARYAMA amatsayin itace uwar gida kenan abun ba a magana saboda tsabar murnar da ahalin masarautar nan suke dan har wata yar walima aka hada na farin cikin samun cikin kowa sai nan da nan akeyi da gimbiya sabreena sarki kwa har wata soyayya yake kara nuna mata wacce bata taba ganin irinta har wajen kishiyar ta ma tana samun kulawa haka wajen surukar tama har kishiyo yin surukar tama ba abarsu abaya ba saboda wannan cikin idan Allah yaraya shi shi ze zama magajin sarki domin anyi scanning anga namiji ne kuma ana fatan Allah yasa hakan ta kasance a haka akai ta rainon cikin har Allah yasa ta sauka lafiya ranar suna yaro yaci sunan baban sarki Muhammad aka saka mishi sameer yaro yana cikin wata na daya kenan wani gagarumin abu ya afko musu sunshiga tashin hankali marar musaltuwa sama ko qasa annemi yaro an rasa itade gimbiya sabreena bayan tayi mishi wanka ta kwantar da shi akan gado tashiga bandaki domin tayi wanka fito warta ke da wuya taga ba yaro da farko de bata kawo komai a ranta ba saboda tayi tunani ko sarki ne yashigo dakin yafita dashi ko kuma   gimbiya MARYAMA tashigo ne bata jiba oho tana ta tunani har tagama shiryawa tafito tana fitowa kuma bata ga kowa ba afalo jakadiyar ta KANDE tashiga kwalawa kira  amma itama taji shiru bataji ta amsa ba saida takirata wajen sau uku sannan tashigo falon da sauri tace gimbiya gani na danje wajen balaraba ne kiyi hakuri na fita bansanar dake ba tace ba komai daman tambayar ki zanyi ko wani yashigo dakina ne lokacin da na shiga wanka ban Annur shine sunan da suke kiran sameer dashi kuma gashi kema kince bakya nan yanzu kije kitambayo min bangaren gimbiya MARYAMA ko ta shigo sannan inkin fita kafin ki wuce  kigayawa Salisu yaje fada yagani ko yana can tace to sannan ta fita da sauri sauri taje ta tambayo akace mata baya can tana hanyar shigowa bangaren ta hadu da salisu shima yadawo yace mata shima yaje ance baya can tana shiga ta sanar da gimbiya cewa duk sun duba ance ba a ganshi ba nande aka shiga cigiya sarki ma yabaro fada domin jin yanda akayi aka rasa yaron acikin masarautar nan yana zuwa yatambayi yanda akai gimbiya duk tagaya mishi yanda akai kafin kace me magana ta zagaya har wajen gari kowa hankalin sa ya tashi neman sa ake lungu da sako amma babu shi babu labarin sa gimbiya Sabreena tasha kuka dan har kwantar da ita akayi agadon asibinti saboda tsaban shiga tashin hankali sai da qyar sarki yake rarrasheta dan shima dauriya kawai yake amma ba karamin tashin hankali ya shiga ba gimbiya maryama ma tasha nata kukan kamar itace ta haifi dan kowade yashiga damuwa kuma a yanda suke zaman mutun ci gaba da familyn ba wanda yazargi wani akan shi yadauke yaron Amma sarki ya dauki alkawarin duk wanda dasa hannun sa akan faruwar lamarin sai yagane kuransa dan baze hakura ba sai ya dau babban mataki wasa wasa de ahaka har aka dau lokaci me yawa babu labarinsa zuwa yanzu kuwa kowa ya hakura duk sun fidda rai ma gaba daya sun rungumi qaddara Allah cikin ikonsa sai ga wani cikin taqara samu nanmade sunyi murna da farin cikin da samun sa shima de haka akai ta renon sa shima kuma Allah beyiba yabare amma da aka kaita asibiti sai akace tasha abun zubda ciki ba qaramin mamaki sukayi ba dajin hakan itade tasan bata sha komai ba to ya akai hakan ta faru daman doctor gimbiya maryama ya gayawa ita kuma tagaya mata sarki be saniba saboda be qaraso ba dan haka sai kawai gimbiya Sabreena duk da tasan bata sha komai ba amma tana tsoran sarki yaji saboda tasan idan yasani ba koda ze yarda da ita tofa dole yadan zargeta ita kuma batason zargi ya shiga tsakanin su dan haka sai ta roqi gimbiya maryama akan dan Allah subar maganar anan bataso sarki yaji saboda batasan yanda ze dauki maganar ba dan wlh itade bata sha komai ba qarewa ma ita wata sani agarin da zatasa yabata maganin zubar da ciki qarewa ma neman sa take Allah yabata kuma sai ta zubar tayaya ma hakan zata faru gimbiya maryama batai mata musuba tace nima tuna nin danake kenan tayanda za agayawa sarki cewa ciki ya zube kuma ta hanyar shan kwaya hakan ba karamar matsala ze haifar ba dan haka nake tunani gara abarshi kawai azin Allah ne yakawo zubewar cikin da wannan shawar warin nasu suka bar maganar akan bawanda zeji bayan sarki ya qaraso kuwa aka gaya masa cewa cikin ya zube yayi jimami sosai amma ba yanda ya iya dole yayi hakuri wanda yabashi shi yakarbe abunsa kuma shi ze qara basa saida tayi kwana biyu sannan suka tattara suka koma masarauta kowa yana zuwa duba ta dayi mata jaje bayan komai ya lafane mahaifiyar sa taqara yi masa magana akan ya qara aure tundade abun da haka yake zuwa beyi mata musuba dan shima zuwa yanzu abun yafara damunsa shima yanaso yaganshi da yara koda magajin sane yasamu dan haka ya amince aka nema masa auren SA'ADATU yar sarkin gombe ce dan haka ba dadewa akayi auren aikwa bata dadeba ta samu ciki da haka har watan haihuwarta yayi ta haifi 'ya'yanta 'yan biyu kuma duk mata ranar suna aka saka musu daya taci sunan babar sa watakon Karima amma ana cemata mama dayar kuma akasaka mata munubiya yara kyawawan farare ne tas saboda sundakko mahaifiyar su data kasance buzuwa gasu da shiga rai kowa sai yabon kyawun su yake suna da shekara ta biyu Allah yaqara bawa Sabreena wani cikin nanma de basuyi qasa agwiwa ba sukayi murna tare da bawa cikin kwakkwaran kulawa saboda kar yasake zubewa Allah kwa yatai maka be zube ba har Allah yasa tahaife danta me kyan gaske dan da kowa mamakin irin kyan da Allah yabashi duk dade mahaifiyar shi ma kyakkyawa ce amma sai yafita kyau sarki yace ta zabi sunan da za asamasa tace akara samata Sameer saboda tana son sunan haka aka qara samishi sunan wanda ya bata kawo yana sonshi bayama yayyanshi su munubiya kullum suna manne da shi haka suka cigaba da gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da sin junan su sameer yana cikin shekara ta daya dan bekaiba ma kwatsam wani abun mamaki kuma abun al ajabi lamarin Allah ba acewa komai sai ga gimbiya maryama da ciki aikam kowa yayi murna da sarki kwa yafi kowa farin ciki addu'ar sa ta karbu yau gashi da yaya uku gakuma cikin na hudu ya godewa Allah kawai yake yi atakai cade itama ta haifi dan ta namiji amma abun mamaki yaron sai yasance baya kama da kowa daga cikin iyayen nasa anrasa dawa yake kama amma ba wanda yace komai saboda ba ajayayya da lamarin ubangiji watakil ma kamannin kakansa nawajen sha wani abun yadakko kunsan dan haka bawanda yace komai ranar suna aka saka mishi *SALAHUDDEEN* SALAHUDDEENI MUHAMMAD SAMEER shine sarki na yanzu kuma da ga gimbiya MARYAMA wacce ake kira da FULANI...................

Ina fatande kuna fahimtar yanda labarin yake tafiya kuma kuna riqewa dan yanzu baza ku gane komai ba sai nan gaba, kuma zakuyi mamakin ya akai salahuddeen yazama sarki bayan bashine babban da ba ga Sarki Muhammad sameer muje de zuwa.......

*************************
CIGABAN LABARI.....

Su Ameesha suna dab da qarasawa gaban gate din gidan sukaji dadda tace gidan qawar taku kenan cak suka tsaya suka kasa juyowa har taqaraso inda suke tace ba magana nake muku ba Ameesha ce ta hadiyi wanni yawu da ya tsaya mata a makogaro sannan tace uhm uhm dadda bafa wani abu zamuyi ba daman abu zan karbo a gurin aunty lami yanzu zamu fito dadda tayi mata wani irin kallo irin to sannu makaryaciya saida taga qare musu kallo sannan tace to kuwuce mu koma gida munafukai wlh baza kushiga ba Ameesha tace dan Allah kibarmu mushiga wlh wani abu me mahimman ci zamuyi tace wane abune da ni baza kufadan ba zaku min qarya kufito tace dadda wlh zamu gaya miki amma kibari mufara shiga mufito tukunna tace wai yarinyar nan wace irin zuciya gareki ke duk wulakancin dasukai miki amma kike qoqarin qara komawa gurin su tace dadda nifa ba wajen su zanjeba tace koma gurin waye bazaki shiga cikin gidan nan ba Azeema dataga abun nasu ba qarewa zeyi ba sai tace dadda dan Allah kibari mushiga yau wajen kwana uku kenan da rasa mahaifin mu ya bata bamuganshi ba shiyasa nazo Ameesha ta rakani muyi yaya musbahu magana akan yatai maka yagayawa yayansu acigita mana a gidan radio ko Allah zesa agano inda yake inma mutuwa yayi zamu sani dadda da taji labarin kamar almara tace yanzu dan baki da hankali wannan babban abun yafaru amma kika kasa sanar dani abun dake faruwa saida na tambaya da bantambaya ba kenan ma baza ku gaya min ba ko Azeema tace dan Allah kiyi hakuri dadda batace mata komai ba tana tunani mafita dan ita wlh bata so sushiga gidan gashi kuma bukatar hakan ta taso yanzu meye mafita to bata gama tunani ba Horn din mota ya katseta mata tunani juyawa sukayi dan ganin wanda ze shiga gidan ganin me gidanne yasasu matsawa su bashi guri dan yasamu damar shiga yana matsowa kusa dasu sai ya tsaya tare da sauke gilas din motar yana kallonau tsaf yagane su dan haka sai yace musu kushiga daga ciki mana kuntsaya anan dadda ce tace mu bashiga zamuyi ba kai tafiyar ka tafada tare da hade rai dan ita duk 'yan gidan ma haushi suke bata dayaga haka sai kawai ya bude motar ya fito ya qaraso inda suke yace baba kiyi hakuri dan Allah ni daman inaso muyi magana tun ranar nan naso muyi duk sunba labarin abun da yafaru kuma na dau mataki akan su dukan dan Allah kuyi hakuri hakan baza tasake faruwa ba nasan basu kyauta muku ba abun dasukayi muku kuzo mushiga daga ciki dan Allah baba kar kice bazaku shiga ba dadda da mutumin yayi mata kwarjini kuma daman ga kuma bukatar da ta kawo su dan haka tace ni basai munahiga ba daman wannan yarinyar ce mahaifinta ya bata shine mukazo atai maka mata abada cigiyar shi ko Allah zesa adace asamu labrin sa awani wajen yace ayya Allah sarki tun yaushe ne kuma a ina nande Azeema tabashi duk labarin yanda akai ya tausaya musu yace in sha Allah zesa Khalid yacigita musu gobe amma su shiga daga ciki dadda fiu taki yarda haka ya rabu da ita sannan yace to dan Allah yana roqon alfarma ta taimaka tabar yarinyar taci gaba da aikin ta kamar da komai ya wuce yajawa iyalansa kunne bawanda ze kara yi mata komai dadda tace itafa jikarta tabar aiki a gidan sa yayi hakuri kawai yabar wannan maganar shima kuma be bar maganar ba haka yaringa yimata dadin baki da rarrashin ta har ya shawo kanta ta amince akan yabarta zatayi tunani akai yace to hakan ma ya gode sannan yace musu yana zuwa ya koma cikin motar sa ya dakko katin number

Please Login or Register in order to submit comment