Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saida tagama shirya tsaf sannan tafito saboda tasan halin yar autar tata da rakin tsiaya abu kadan zata maidashi babba shiyasa bata damu da fitowa ba lokacin da takejin ihun nata saida tagama tana saukowa tace me yake faruwa ne amra na jin haka ta kwasa aguje ta nufeta tana sakin wani sabon kukan momma shafa bayanta tayi tace ya isa haka gaya min me akai miki wane lafin kikayi da har ake qoqarin ballaki kasa magana tayi saida qyar ta tsagaita kukan nata amma kuma takasa bata labarin abun da yafaru ganin hakan yasa momma zaunar fa ita kan kujera tace shikenan basai kinfada ba zauana zansa azo adubaki anjima sannan ta maida kallon fa ga hamra tace ke kika jamata ko nasan halinki shiru tayi bata ce komai ba saboda tasan ko tafada ba goyon bayanta zatayi ba saboda tafison amra shiyasa kotayi laifi bata ganin ita kuma abun ba qaramin qona mata rai yake ba,

Kai kuma shine daga dawowar ka zaka kamamin ya da duka ko juyowa yayi yace momma wlh yarinyar nan duk ke kikesawa take yin abun da taga dama tace to ba itace auta ba dole tayi abun da takeso kwa yace hmmm aranshi kuwa sai yace aikwa zan kasheta wataran ko yan karkarya mata qasusuwa yanda bazata taba moruwa ba zama yayi be qara cewa komai ba saboda inyaci gaba ransa ne ze qara baci dr. Shettima ne yafar gaida ita ta amsa masa fuskarta dauke da murmushi datambayar sa ya hajiyarsa take kwana biyu bata shigo ba lafyade ko yace lafiyar ta qalau nande tazauna itama suka qara gaggaisawa gaba daya har sameer bayan nan kuma suka saka aka kawo musu dinner me rai da lafiya da ta saka aka dafa masa na musamman saboda shi haka suka zauna gaba dayan su sukaci amma banda amra da tagama cika ta batse taqi cin komai momma na lura da ita amma bata ce mata komai ba so take idan sun tashi Saka ta agaba taci tasan taurin kanta baza ta taba ci agabansu saide idan basanan,
bayan sun kammala kuma sukatashi sukayiwa momma sallama suka fito dagana kuma suka shiga kowane sashe na gidan suka gaisa sannan suka fito dr. Shettima yace shi ze wuce sai gobe sai yace suje tare kawai yagaida hajiya yayi missing dinta yana son ganinta haka suka nufu parkin space suna zuwa drivern sa yazo ya bude mishi qofa sai yace mishi ya shiga shikadai shikuma zasushiga ta dr. Shettima inyaso sai yadawo dashi gida, atare suka fita daga bayan yana binsu abaya har suka qaraso gidan shiga sukayi lokacin da suka shiga hajiya na falo tana kallon labarai suka shiga da fara'a sosai a fuskarta ta amsa musu da cewa lalle yau manyan baqine agidan namu marhaban ku lale shiga sukayi sannan suka samu guri suka zauna sannan suka gaisa da tambayarsa ya hanya da 'yan gidan nasu a hade yabata amsa dacewa komai lafiya nande suka dan taba hira sannan yace bari ya wuce dare yayi dan yanzu shadaya ta kusa sallama yayi mata sannan suka fito tare saida yaga tafiyar su sannan ya koma cikin gida...

Suna tafiya dan har sunyi rabi ma atafiyar tasu suna tsakiyar titi mota ta tsaya cak sai kuma ta mutu drivern yace subahannallah me ya samu motar nan kuma fita yayi yana duddubawa ko ze gano matsalar amma bega kowace matsala ba kuma hargidan ya bude yaga akwai mai da yawa said yadawo yace yallabai wlh na duba banga kowace matsala ba amma ina da wani aboki bakanike ne shi bari inkirashi sai yazo ya duba mana yace ok dagana yamaida hankalin sa kan wayar da yake dannawa after 15 minutes sai ga bakanike yazo shima dubawar ya shiga amma yakasa ganowa wasa wasa de har suka kai wajen minti talatin amma ba bata gyaruba zafine ya ishsahi acikin motar dan haka sai yabude kawai yafito waje saboda yasamu iska sukuma suna ta qoqarin ganin komai ya daidaita amma ba labari agogo ya duba sai yaga har shabiyu ta kusa sai yace dasu wai haryanzu baku gano matsalar bane akira kwararre mana drivern nashine yace ai wannan shine oga awajen su babba ne ya iya aiki shima bakanike dagowa yayi yace wallahi 'yallabai duk gwajin da zan mata nayi amma banga komai wanda yasamu matsala ba komai yana nan yanda yake ni wallahi ma abun mamaki yake ban narashin gano inda matsalar take kowade yayi shiru yana mamakin faruwar hakan drivern ne yayi saurin cewa sir natuna wani abu kwanaki haka ta taba faruwa saidaga baya aka gano sister din kace ta hana motar tafiya ina ganinfa watakil yanzu ma facitace tundade har taqi tashi ka tuna ba laifin da kayi mata a yau bakani kenne ya kalle shi yace yar biyu ce yace masa eh itace wlh haka tayi mana kwanaki qarewa ma Sam agurin mukabar motar ta kwana yace Allah sarki ai yan biyu haka suke nima ina nan ina fama da nawa ba dama kayi musu laifi sai sun huce ta wani bangaren yace hakane haka suke su sai anbisu a hanakali daman suna ta tattaunawa de.....

shikuma yana tsaye yana sauraron sa tab lalle kama biri yayi kama da mutum yafada a zuciyar sa afili kuma sai yace inazuwa itace ma ai wayarsa yadauko sai kuma yafara tunanin wama ze kira shettima ne yafado masa dan haka sai yakira number sa ringing biyu tayi yadaga daga can yace hello shima yace hello kana jina yace eh me yafaru yace komai ma wai kasan yar banzanr yarinyar nan abun da nayi mata dazu gashi tasa motata taqi tashi tun dazu aka kira bakanike yana duba wa amma taqi tashi sadaga baya na tuna abun da nayi mata dariya shettima yasanya masa sannan yace ai wallahi tayi min daidai maganin ka kenan angaya maka kaci banza mu ai bama yafiya sai mun rama kasan halinmu amma kake cin zalinmu shima saura kadan yasaki dariyar amma beyiba ya danne sannan yace to ni bana manta ba amma duk dahaka wlh tayi laifi koyan zu na koma gida saina hukuntata yace to shikenan muzuba mugani maga waye zefi jin jiki yace ka nidallah ba surutu nakeso ba yanzude ka kirata awaya kabata hakuri sannan kace mata tare muke dakai nasan zata bude yace to Allah yasa bari in gwada kiranta bayan 'yan mitina sai yaqar kiran shin yace to wallahi ta kashe wayarta gaba daya nakira ta hamra ma amma itama bata shiga duk akashe suke kakira momma sai kagaya mata.yace "ok" sannan ya katse wayar da mamakin sa itama sai yajita akashi shide tunda yake da momma betaba kiranta ba yaji wayarta akashe sai yau da yake bukatar ta tuna ni ma yafara yi yanzu shikam yama rasa wanda zefara kira yahadasu da momman sa dady yakira shikuma yace baya gida bedawo ba.........✍



Karatu baya muku wuyar karatu said de rubuta comment ne yake baku wahala hmmm
[3/26, 7:11 PM] ~~~~writer~~~~: 💅SARKI SAMEER....💅
           by❤xeemat.....love❤

             🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

                🌹الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر🌹
                             ﷽

                    Bismillah........ ✍
Episode54-55

         """"""""""""""""""""""""""""""""""

Fulani yaqara kira amma itama sai yaji wayar tana ta ringing amma ba adaga ba, haushine ya ishe shi jiyake kamar ya fasa wayar sai kace itace tayi mishi laifin shettima yaqara kira yana dagawa yace sai kafito kazo ka maidani gida duk wanda nakira bata shiga shettima yace ok ganinan zuwa sannan ya katse wayar cikin motar ya koma yazauna sai faman tsaki yake saki,
saida yadau lokaci kafin ya qaraso yana zuwa sameer yafito ya shiga dagan sannan yacewa idi driver yazo su tafi subar motar agun gobe azo adauka shima bakanike aka sallameshi ya hau mashin dinshi ya qara gaba sukuma suka dau hanya tun ahanya yake ta lissafin hukun cin dazeyiwa yarinyar nan da tasa shi tsayiwa agurin nan har tsawon lokaci haka,
sai faman tsaki yake tayi ranshi duk yabi yabaci shide shettima be tanka masaba sai dariyar sa da yake yi a boye kuma abun da besani ba yana kallonsa ta gefen ido kawai rabuwa yayi dashi  dan bashida lokacin sa ahalin yanzu sai wajen qarfe daya suka qaraso gidan yana ajiye shi kuma ya juya ya koma gida,

direct part din Fulani yashige be tsaya bi takan Amra ba yabarwa gobe yana shiga part din shi ya wuce toilet yayo wanka tare da dauro alawala bayan ya shirya ya shiga jero nafil filu kamar yanda yasaba a kowane dare kafin kwanciyar sa bayan ya idar yabi lafiyar gado tare da lumshe idanun sa yayi addu'ar bacci ya shafa yaja  blanket har zuwa kansa  bawani bata lokaci kwa bacci yayi awan gaba dashi,

Washe gari bayan yayi sallar asuba yakoma bacci be tashiba sai wajen goma yana tashi yayi sauri yayi wanka sannan ya shirya kansa cikin qananun kaya da sukai mugun karbar jikin sa
cikin ta kunsa daidai kamar baya son taka qasa haka yake takawa cike da nutsuwa har ya qaraso sashen fulani ba kowa a falon,
da har ze wuce sai kuma yadaka ta yafara nufar inda dakinta yake dan yagaida ita,
yana qaraswa bakin qofar yadaga hannu sa ze kwankwasa amma sai yaji kamar ana magana qasa qasa dakatawa yayi domin jin abun da ake cewa,
Baqaramar razana yayi ba da jin maganganun da yaji fulanin nafada dan har saida ya dafa bango sakamakon ji yayi gaba daya kamar ze kife ne awajen saida yabari yadan samu nutsuwa amma duk da haka yakasa motsawa atake kuma idanun sa suka sauya kala daga farin zuwa launin ja zufa tafara tsatstsafo masa ,

jin kamar mutum ze fito ne yasa shi yunqurawa da kyar sannan yayi saurin barin wajen yana qara mamakin wannan matar shifa daman tuncan yagane wasu take taken nata bata da gaskiya acikin gidan nan shiyasa yafara saka mata ido inde yana gari tofa komai take idonshi akanta kuma dan rashin zamansa ne ma agarin amma da tuni yagama gano ta saide kawai besan abun da take kullawa bane to tabbas ya yafara hasa sho abun da yake zargi akanta yana wannan tunane tunanen har yaqaraso part din momma dinsa fadawa yayi cikin falon ko sallama babu ya shiga mommo dake fitowa daga kitchen taga yanayin da yake ciki da sauri ta ajiye abun hannunta ta qaraso kusa dashi tana duban shi cike da kulawa sannan tace son me yafa ne naga kashigo ko sallama babu ga  yanayin ya canza wa yabata maka rai da farar safiyar nan tafada lokacin da takamo hannun sa suka zauna kan kujera sannan taqara saka hannun ta duka biyu acikin nasa ta ruqo nasa sannan tace fada min me yafaru shiru yayi na wasu lokuta yakasa furta komai saidaga bisani sannan yakira sunan ta a hankali ya furta momma amsa masa tayi cike da maida hankalinta gareshi saboda jin yanayin muryar sa yaqara tabbatar nata da cewa ba lafiya akwai damuwa a tattare dashi numfasa wa tayi sannan tace inajin ka fadamun abun dake faruwa saida yaqara yin dan jimm sannan yace momma inason jin labarin masarautar nan tundaga kan me sunana danajin kunce sunansa naci har zuwa kan wannan banzan sarkin baki tariqe tare da cewa waye banzan sarki shiru yayi be bata amsa ba ta dora dacewa wai kai haryanzu baza ka canza wannan dabi'ar taka ba marar kyau uncle din naka kake cewa banza mahaifi yake agurin kafa inde zaka iya zaginshi batare da kaji komai aranka ba nima nasan watarana sai kazageni tunda ba shakkar uban kowa agaba na bakajin komai idan ka zagar min qannen alhalin suma iyaye suke agare ka wai har sai yaushene zakai hankali yaushe zaka dena samin damuwar daukin magana dakake yi kullum kai idan kazo garinnan sai kabata min rai kakejin dadi ni wallahi zaman kama acan yafiya min kwanciyar hankali akan zaman ka agidan nan tafada ranta abace saboda ta tsani taji ya zagar mata dan uwa shikuma halinsa kenan besan meyayi masa da ya tsane shi haka,

""ahankali iya budar bakinsa sannan yace sorry daga nan kuma be qara cewa komai ba ya mike tsaye tana qoqarin daka tar dashi amma ina har ya bar falon,

ahanya suka kicibusa da Amma (karima) yar biyun momma (munubiya) cike da kulawa take binsa da kallo kawar da kansa yayi yana niyar ratsata ya wuce ta dakatar dashi akallon farko ta fahimci halin da yake ciki dan haka kawai sai tace muje part din inason ganinka kai ya girgiza mata alamar a'a rai ta dan hade tare da yimasa hararar wasa sannan tace yaushe muka fara yat jayayya dakai abun da kakeyiwa mutane yau zakamin kenan nan ma kan ya girgiza mata tace to wuce mutagi inde ba hakabane abun da nafada be qara tanka mataba yabi hanyar part dinsa ita kuma tabin sa abaya,
Ajiyar zuciya momma ta sauke tare da   sakin labulen window da tadaga tana kallon su dan tunda yafota ta bude taga inda zashi dan bataji dadin abun da tayimasa ba tasan tabbass yana da damuwa tunda taga hakan a idon sa gashi kuma yazo yana tambayarta tabashi labari to dole a kwa abun da yagani ko yaji amma bata gaya masa komai ba ta haushi da fada duk da shiyaja amma itama ganin laifinta take da bata tsaya ta saurare saba amma yanzu hankalin ta yadan kwanta tunda de 'yar uwarta tazo kuma har ya yarda yabita to tasan zata iyayin maganin matsalar tashi,

bayan shigar su sashen nata suka zauna sai kuma ta tashi ta nufi kitchen dakanta ta hado masa breakfast ta kawo masa tace maza ci sai muyi maganar yace ya qoshi tace me kaci yace ba komai tace to bana son musu maza dauki kaci ko kadan tea kawai ya iya sha yace mata ya isheshi rabuwa tayi dashi dan tasan halinsa idan ta takura masama ze iya tashi yayi tafiyar sa ita kuma bahaka take soba tana so taji damuwar sa kafin yatafin daukewa tayi da kanta sannaan ta mayar ta dawo sai ta zauna akusa dashi tace gayamin abun da hake damunka ko kaida momma ne ita tabata maka raine ko wanine duk tabi sai faman tambayoyi take jero masa kuma bata samu amsar ko daya ba sai cewa da yayi auntu ba komai kawai garinne banajin dadin sa wata kilma yau ko gobe zan koma, rarrashin shi tayi tare da bugar cikin sa tace dole akwai abun da yake damunka hakannan nasan baza ka tafi ba lokacin tafiyar ka beyiba saide kawai inbaka dauke ni matsayin uwa ba shiyasa bakai matsayin da zan iya sanin halin da kake ciki ba tafada tana miqewa tsaye da qoqarin barin wajen saide tambayar da yajefo matace ta hana ta cigaba da niyar tafiyar  datake yi juyowa tayi dan qara tabbatar da abun da kunnu wanta sukaji sannan bata bashi amsaba ta qara tanbayar sa da cewa magana kake me kace?

sarai yasan taji ne yace amma sai yaqara cewa wace ce GIMBIYA SABREENA?

qara maimaita sunan tayi kamar ma basan sunan ba zama tayi tana fuskan tarshi sannan tace a ina kasanta yace danasani ta ai bazan tambayeki ba tace to a ina kaji sunan nata yace aunty kawai nide kigaya min inzaki gaya min in kuma inje in tambayi papa nasan shi ai ze gaya min tunda ku ba kwaso kufada min dan numfasawa tayi sannan tace shikenan kwantar da hankalinka zan gaya maka nayi mamakin jin sunan abakin ka ne shiyasa kaji ina tambayar ka a ina kaji sunan ta yace ni ba a inda naji tace Allah ko to inbaji kayi ba ko gaya maka akayi  daga sama akayi maka wahahinsa kenan sannu dan baiwa
tafada tana kallonsa,

Qarar ringing din wayarsane ya katse su zarota yayi a aljihu sannan ya duba kan screen din wayar sunan my man yagani be daga ba harsaida kiran ya katse aka qara kira sannan akaro na biyu sannan yadaga tare da yin shiru daga can shettima yafara yin sallama shikuma ya amsa bayan sun gama gaisawa ne shettima ya dora dacewa kataho tundazu fa kai nake jira najika shiru gashi har shadaya ta kusa ahankali yace ganin tahowa anmaida ita tiata room a shirya komai ina zuwa farawa zanyi ba na son bata lokaci,
yace ok sai ka qaraso sannan sukayi sallama dubansa ya mayar ga auntyn tasa sannaan yace inajinki aunty shiru tayi sannan tace ai wannan  long story ne bazan iya baka shi yanzu ba kabari zansaka mana rana kafinde ka koma zan baka labari tunda ga A har Z kaga yanzu kaima jiranka akeyi ko jinjina kai yayi sannan yace eh jirana akeyi amma ai ba sauri nake ba kawai kibani yanzu ba matsala tace a'a ai nagaya maka labarine me tsawo kawai kaje tunda nace zan baka ai zan baka din yace to shikenan naji amma kiban dan aciki dafe kanta yayi tace oh ni karime dole de sai ansaka mutum abun da bayaso to abi biyu zan gaya maka daga nan kuma kar kasake tambayata wani abun ka yarda kai yadaga mata alamar eh ya yarda itakuma ta dora mishi da cewa GIMBIYA SABREENA kamar uwa take agare mu itace matar mahaifinmu tafarko iatace uwargida sai mama fulani sannan mahaifiyar mu katsata yayi da cewa to yanzu tana ina ko ta mutu?
tace gaskiya tun muna yara mahaifiyar mu ta bamu labari tace mana anne meta an rasa tare da danta gaba daya su biyun ba san inda suke har zuwa wannan lokacin suna raye ko sun mutu Allah masani ze qara magana kenan tayi saurin dakatar dashi tace kaje kawai banason wata tambayar zamuyi magana daga baya kamar yanda nagaya maka,

Shiru yayi bece mata komai amma qasan ransa taf yake da tambayoyi iri iri amma yazeyi dole yabari lokacin dace sannan yaci gaba dajin labarin mikewa yayi yace shikenan to aunty hakan ma nagode bari naje Sai naji kiran naki tace to shikenan sai anjima amma fa banason ta kuara yace ba halina bace ai kinsani yanda banaso a takurawa rayuwata nima banaso na kuma banaso na takurawa mutum yana kaiwa nan yasakai yafice daga sashe na,
yana fitowa ya qara shiga part dinshi yaje yadauko duk abun da yasan ze buqata a aikin sa wanda dole daman saida su tunda tundaga can ya taho dasu bayan yagama hada komai yafito daga sashen nasa yana fitowa kuma be qara zuwa ko ina ba yawuce parking space yana zuwa drivern sa yaqaraso wanjen da saurin sa sannan ya karbi jakar hannun sa tare da cewa yallabai naje na dauko motar tun dazu yace ok muje awaccen yanuna masa wata motar daban ba wacce suka fitaba jiya da sauri ya amsa da to tare da nufar inda take yabude yazarota daga ciji sanna ya daidaita ta hanya yafito ya bude masa yashiga ya. rufe yazagaya shima yashiga sannan yabawa motar wuta suka fice daga masarautar suka dau hanyar hospital din,

S.I.S spatial hospital.
yana gama parking ya fito ya bude masa saida yagama sha kamshinsa sannan ya zuro zara zaran qafafun sa sai kuna yaqarasa fitowa gaba dayansa cikin takunnan nasade da yasaba yanzuma shi yake yi driver na bayansa da jakar suna tafiya ana gaidashi amma hannun kawai yake iya daga musu wasuma basa samun damar daze daga musu hannun ahakade har suka qarasa office dinsa bayan sun shiga ya zauna drivern ya miqa masa jakar tare da juyawa yafice daga cikin office din yana fita kuma saiga dr.shettima yashigo bakinsa dauke da sallama amsa masa yayi ciki ciki wanda ina bakinsa ka kalla bama bazakace yayi magana ba zama yayi tare da miqa masa hannu sukayi musabaha sanna yayi masa barka da zuwa daganan kuma suka shiga tattaunawa akan aikin da za ayi mata bayan sungama a gurguje ya tashi yayi shirin shi tsaf nayin aikin daman already dr.shettima yariga da yagama shirya koma anmaida ita dakin daza ayi mata aikin kawai shi ake jira daman dan haka atare suka fito yana shine agaba shikuma shettima yana binsa abaya da kayan atare suka qarasa ciki yana shiga ya zuba mata ido nadan wasu dakiku kafin yajanye daga kanta yamaida kan shettima yace wanna yar qaramar yarinyar me ya haddasa mata brain trauma ko naji kuma kace ba accident tayiba me yafaru da ita shettima yace wlh nima bansani ba lokacinde dasuka kawota bani nakarbesu ba dr. Jamil ne nima sai daga baya nake jin hakan kuma ban taba tambayar su ba yace ok sannan ya matso masa da wani dan desk sannan yadora masa ka yayakin agefe komai de yana kusa da gadon nata saida ya tabbaatar da ba abun da ze bukata sannan yafita dan bashi wake yayi aikin sa yanda yakamata ba bata lokaci kuwa ya shiga yin aikin sa cikin kwarewa da qwazo yake yin sa kana gani yanda yakeyi kasan baqaramin kai bane tunwajen 12 yafara amma bashi yagama ba sai wajen biyu saura wayar sa yadauka yakira shettima yace yazo su maida ta dakin hutu yana gama gaya masa ya katse kiran
Kayan jikin shi yafara ragewa sannan yafita daga dakin zuwa office dinsa yana shiga ya wuce bedroom dinsa na cikin office yana shiga yawuce bathroom yaqara yo wani wankan tare da dauro alwala ya wuce masallaci ahanyar dawowar sa suka hadu da shettima tare suka shiga office din zama suka fara yi sannan shettima yace yanzu komai nml za su iya zuwa su ganta sameer yace eh amma de son samu subari sai gobe sannan ta dawo hayyacinta yanzu nayi mata allurai dole sai gobe ko zuwa cikin dare ma zata iya farkawa amma banda yanzu dr.shettima yaji dadi sosai yace to Alahamdulillah hakan ma yayi bari nasanar da yayan ta yace ok kawai sannan ya miqe yace zan dan kwanta ina bukatar hutu yana fada yaqarasa shiga dakin yabar sa agun be jira amsarsa ba,

ganin hakan yasa shi shima ya tashi ya fita ya nufi office din sa yana zuwa yatarar da saleem abakin office din nasa dasauri saleem yamiqa masa hannu suka gaisa, "" shettima yace masa da ka shiga ai ka tsaya daga nan dan sosa kai yayi yace a'a doctor ba ayi haka ba gwara idan kana nan inshiga na kwankwasa naji shiru shiyasa natsaya anan najira dawowar ka harara ya watsa masa sannan yace to yayi kyau yana fada yashige ciki bayan shi yabiyo suka qarasa shiga tare zama sukayi sannan shettima yace albishirin ka da fara'ar sa yace goro doctor ai tunda naganka na fahimci kana cikin farin ciki bani nasha doctor ,
wani kallo yayi mishi sanna yace meye hakan kuma wai bani nasha sai kace mace to saide in baka kaci qarewar kashs,
Dariya saleem yayi yace to bani naci din wlh autace ta koya min yace wace auta duk da yagane wa yake nufi amma sai ya basar saleem yace auta de danazo da ita ranar nan shima sai yace ok sannan yace Alahamdulillah tasamu lafiya har an gama yi mata dazu yanzu farkawar ta kawai muke jira cike da jin dadi tare da murna yace masha Allah Alahamdulillah Alahamdulillah Allah kaine abun godiya kai kai wlh baka ji yanda naji dadi ba aikwa bari inyiwa auta albishir daman kullum sai ta dame ni da tambayar ta to yaude zataji dadda dan labariyafada tare da dakko wayar sa daga aljihu ya lalabo number ta yakira tana daga wa yasa wayar a hands free tace hello yayana nakai na ya aiki yace Alahamdulillah albishi rinki tace goro yace fari ko ja tace fari kal kal yace wace kyauta zakiban idan kinji tace koma me kake so kaide kawai bani nasha na matsu inji tana cewa bani nasha yadaga kai suka hada ido da shettima sai kawai yayi dariya sannan yace auta Ameesha taji sauki har angma yimata aikin wata uwar qara tasaki tare da cewa dan Allah da gaske yaya yace zanmiki wasa ne da irin wannan maganar ta ce a'a wayyo Allah na dadi yaya bari intaho yanzu wlh dan na matsu inganta yace a'a kibari sai gobe sai muzo tare tace wlh yaya bazan iya ba duk

Please Login or Register in order to submit comment