Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare na fad'a mishi inda zanje, ciniki mukayi na shiga yaja muka tafi. Yau babu inda zan sauke zango sai wurin Alhaji mai gidan "yanci, wato inda Umar yakai ni da farko ban shiga ba na dawo, dalilina na haka kuwa yanzu zakuji.......



18/08/2019



*JAMILA MUSA Ce* 🤙🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 12


Abinda yasa banbi Umar mukaje gaban Alhaji saboda na shirya lafiyayyar yaudara da zanyi masa, sana'ar karuwanci tayi min kad'an gaskiya dan haka dole sai na had'a da sata, shekaru biyu kacal zanyi a cikin wannan mummunar d'abi'ar, ina so na shigewa Alhaji sosai a rayuwa idan ya saba dani zan kunce dawakan Dikko duk in siyar dasu, nasan duk doki d'aya za'a siya da kud'i masu yawan gaske.

A wancan lokacin da munje tare da Umar Alhaji yaga fuskata tou kud'in Umar da nayi wayau na kwace masa tou Umar zai koma ya fad'awa Alhaji cewa wannan yarinyar b'arauniya ce ayi hankali da ita...

Bani da tabbas kuma bani da alkibla nima kaina tsoron kaina nake bansan abinda yake damuna ba umarni kawai zuciyata ke bani ni kuma ina biye da ita.....

A k'ofar gidan Alhaji napep ya sauke ni, kud'inshi na bashi ya wuce nima na shige ciki, kaina tsaye na tunkari gidan babu wani tsoro fargaba bare kuma jin kunyar kowa amma har yanzun ban cire nik'af ina ba.....

Ko mai gadi baiyi yunk'urin dakatar dani ba domin dai yasan mata abokan hud'd'ar ubangidan nasa ne... Hanyar da Umar yabi dani hanyar nabi naci gaba da tafiya har na shiga cikin palon gida....

Saida na shiga cikin palon na cire nik'af ina, d'an kallon palon nayi sannan na kallo inda hotunan mak'iyi Dikko yake raina ya b'aci sosai tsinan ne duk shine silar rushewar gidanmu kowa ya bazama ya shiga duniya, duk da bai sissiye ba da muna zamanmu cikin farin ciki, idan dai kud'i yasa kayi mana haka nice zan mayar dakai talakan k'arfin da yaji, uhum da kinsan waye Dikko da baki ce haka ba .....

Sallama na kwarara daidai yanda nasan za'a iya jiyoni, daga ciki naji ance shigo mana ! Inda naji sautin maganar ya fito nabi na shiga, kwance mutumin yake saman gado ya wani baje sai kace anyi b'arin asara...

Kallo d'aya nayi masa tare dayin murmushi na zauna a gefen gado, kuma nayi karatunshi tun shigowa ta bakin gwargwado kuma na fahimci wasu d'abi'u nashi, da gani zaiyi sauri fushi kuma yana da saurin sauka, yanayin shi ya nuna abun duniya bai rufe mishi ido ba, amma wannan da ganin idonshi mayen mata ne lallai wannan idan ya dafi mace aradu mai ansarta sai Allah...... !!!

Alhaji barka da yini, cikin sakin fuska ya amsa min da cewa barka dai malama ya kike ? 'Dan gyara zama na nayi tare da cewa lafiya qalau ya aiki ? Kallo na yayi tare da cewa ki ganni kwance kuma kice min ya aiki ? Murmushi nayi tare da cewa ai na kwance kuwa shi yasha aiki Alhaji inba ba'ayi tuk'in zaune ba ai anyi na kwance....

Kallo na yayi tare dayin dariya irin tasu ta gogaggin "yan bariki sannan yace wace ce ke ? Kama kaina nayi tare da tattaro natsuwa ta dan ni nawa ba kalar nasu bane, saida na tattaro class ina sannan na d'an rage yawan fara'a , suna na Maryam Aliyu Binna........ Amma anfi sani na da Sultana.

Talla na kawo maka da fatan zaka siya ? Na k'arasa maganar tare da kashe mishi ido d'aya.... Dariya Alhaji yayi tare da gyara zaman belt inshi sannan yace yarinya me kike siyarwa ne ?

K'addara......... !!! Kasan kowa da irin tasa k'addarar haka kuma kowa da irin k'addarar da yake siyarwa, idan talauci ya ishi mai rai yakan siyar da duk wasu abubuwa nashi daya siya ya adana, manoma sukan b'oye hatsi yayin da sai yayi tsada suke siyarwa, dillalai kuwa sukan adana k'addara ta k'asa sai tayi kud'i su siyar, macen da kud'i suka kama idan tayi ajiyar d'an kunnen zinari zobe ko awarwaro wannan talaucin zaisa ya ziyarci kasuwa, yayin da duk macen da tasan ciwon kanta take k'ok'arin adana tata k'addarar da Allah ya bata kyauta sai taje gidan mijinta,

Ni kuma talauci ya dameni ba gidan zama bare motar hawa, kuma ban ajiye hatsi ba ban aje gold ba, shi yasa na d'auko nawa mutunci zan siyar amma sai na lura babu wanda zai siya da daraja idan ba kai ba, dare d'aya tak zaka more amma farashin farko kuma ba tayi miliyan d'aya ne,

Ka ganni dai a fuska gwanin burgewa, masana sirrin mata sunce duk macen data cika muni zaiyi wuya tayi wani armashi, sai kuma sukace kyakkyawar mace kuma wannan riba biyu ce harda gyara ma, karfa kaga kamar ina yaba kaina ne fuskar gida ba itace take nuna tsarin sa da haduwar sa ba, sai an bud'e an duba ake ganewa....

Duk mota sunanta mota amma wata motar bata kai mota ba, tou haka take ga mata duk mace sunan ta mace amma wata macen muna mata ce..... Na k'arasa maganar tare da kallon Alhaji nayi masa kyakkyawan murmushi mai tattare da jan hankali. Saida na kauda kaina sannan nace amma ina da sharadi d'aya , idan anyi ba'a sake maimaici wannan shine sharad'in kasuwata idan zaka zuba hannun jari bisimillah, na mik'a masa hannu na da niyar mu k'ulla alk'awari....

Gyara kwanciya Alhaji yayi da niyar magana amma na lura da yanayin fuskarshi kamar bai yadda dani ba, dan haka na tare maganarshi da cewa karka cuci kanka wannan harka duk taimakekeniya ce , ka bani gishiri in baka mand'a , kaga masanya ce za'ayi fa ni wannan ba matsalata bace kud'in ne kawai damuwa ta, ka yadda na rana d'aya tak 👌🏻........

Kallo na Alhaji yayi tare da cewa tou ai ked'in ce kin tsananta miliyan d'aya fa..... Kin kuwa san girman miliyan Sultana ? Idan na baki ita ina zaki zuba ta ? Waye zai d'aukar miki ita ? Me zakiyi da ita kuma ? Ajiyar zuciya na sauke tare da cewa, wurin zubata da d'aukarta da abinda zanyi da ita duk ba huruminka bane ba, kayi kawai ka bani idan kuma baya yuwuwa in hak'ura inyi gaba kila na dace.......

Tashi yayi zaune tare da tattaro duka hankalinshi gareni sannan yace karki k'i fad'amin, kika sani ko zan iya miki maganin damuwarki ne ? Kuma kike maganar miliyan d'ayan d'aya kika sani ko in baki abinda yafi miliyan d'in ? Ni kud'i ba matsalata bane amma ina san sirri dan duk wannan harkar da kikaga inayi gaskiya banayinta da d'anyar kwalwa saboda gudun b'acin rana.....

Alhaji kenan idan na fahimta kallon yarinya kake min ko ? Tabbas a zahirance ni yarinya ce amma a bad'ini ni mai tunani ce, babu wanda ya koyamin yanda ake bariki ni na koya da kaina, ban yadda da zama k'ark'ashin kowa ba nima saboda gudun b'acin rana, "yanci na, mutunci da kowa yake tak'ama dashi ya siyar akan kud'i k'alilin k'arshen wulak'anci da tozarci mak'iyina da bana k'auna shine ya taka ruwan ciki na, a cikin gidansu ya keta min hijabin da nake ta boyewa shine yayi mata kaca kaca.... Shiru nayi saboda idan dai har naci gaba da magana zan iya kamo sunan Dikko in d'ura wa uwarshi zagi.

Hak'uri Alhaji ya bani tare da jawoni jikinshi yace kiyi hak'uri ku matan ne baku da amana sai a had'a kai daku a cuci mutum, murmushi nayi tare da cewa ai ko zanyi cuta bana tsaya inda aka sanni ba, kana dai da kud'i kusa dakai dan bana amfani da banki danma karka wani ce zaka turamin.....

Cikin raunanniyar murya yace karki damu Sultana d'akin nan cike yake da kud'i, zan sake magana ya had'e bakina da nashi wuri d'aya labari ya fara canja salo.....

Murmushin mugunta nayi tare da bawa Alhaji duk abinda nasan zaisa ya samu natsuwa.... Ya dad'e yana gurje kud'inshi kuma ban waniji wata damuwa ba, har saida ya gaji dan kanshi ya kyaleni.

Sauka yayi daga saman gado ya nufi toilet ni kuma ina nan kwance, yana shiga na zaro wayata dana soke a jikin gado wanda duk abinda mukayi da Alhaji saida na d'auka, dariya nayi bayan na gama kallo sannan na mayar da wayata cikin jaka...

Kafin Alhaji ya fito har na gama saka kayana na maida nik'af ina na zauna bakin gado.... Ina jiran fitowarshi ! Bai wani dad'e ba ya fito da sauri ya nufi wurin wayarshi saboda tun dazu ake kiranshi banyi gigin dubawa ba saboda ko na duba bana gane suna....

Kayi hak'uri mai gida shine dai abinda yake ta maimaitawa, bansan abinda abokin wayar yace mishi ba naji yace Eh an basu ranka ya dad'e , tou insha Allah, Allah ya tsare ubangijj ya k'ara taimakawa. Sallama sukayi dashi Alhaji ya ajiye waya sannan ya kalloni tare da cewa ke yanzu ya zamuyi ne ?

K'afa d'aya a saman d'aya na d'ora sannan na ajiye hannuwa na ta baya nace bani zakayi in wuce marece yanayi, tou baza kiyi wanka ba ? 'Dan girgiza k'afata nayi sannan nace bana sauke najasa a wurin da bai kamata ba ka bani kawai na wuce.....

Tou waike taya zaki d'auki miliyan d'aya ne ? 'Daga nik'af ina nayi tare da cewa karfa ka raina min hankali ka bani in wuce kana b'atamin lokaci kaji.... Murmushi yayi tare da cewa ya zaki d'auki zafi da wuri haka ? Tou ya zakiji idan na hanaki kud'in nan, murmushi nayi tare da cewa kai kuma ya zakaji idan ka samu hotunan vidio abinda mukayi a yanar giza gizo ..... Na k'arasa maganar ina masa kallon rainin hankali.

'Daure fuska yayi tare da cewa sai in kashe ki, murmushi nayi da gefen bakina tare da cewa tou da suka shiga duniya kuma ya zakayi da duk wanda ya gani ? Ta ina zaka bi ko gogesu a cikin wayar kowa ? Akwai "ya "ya akwai surukai ga kuma matanka abinda kake b'oyo tou gashi a cikin wayar "yarka ko d'anka tou ya zakayi dasu.........

Zufa ta keto mishi sosai, dariya nayi tare da cewa tou goge ai haka ma bazata tab'a yuwuwa ba, kawai nima nayi maka barazana ne kamar yanda kake neman hanani kud'ina, kaga abinda bazai yuwu bane bani na wuce,

Ya kama kanshi sosai dan haka yace zan baki dubu dari biyar yanzu anjima ki dawo ki amsa sauran, gaskiya idan na tafi bana dawowa ka bani kawai sai mu rabo lafiya, tou wai babu zan baki ? Nace itama babun idan tana kamuwa ka bani ansa zanyi ba cemin kayi d'akin ka cike yake da kud'i ba ?

Mutum cikakke mai arzik'i kamar ka ai bai kamata ya rik'a d'aga murya ba akan miliyan d'aya kacal ba, miliyoyin da suka tafi babu dalili baka san iyakarsu ba bare wannan idan ka bada ita ai kasan ta inda tabi ta wuce...

Dubu d'ari biyar ya bani yace muje in baki sauran suna cikin mota, cikin jakata na zuba dubu dari3 muka fita dubu dari biyu na hannu na, muna zuwa ya bud'e mota ya bani sauran kud'in, bud'e gaban mota nayi na shiga tare da cire kallabin kaina na d'auresu a ciki nace ka ajiyeni bakin titi....

Baimin magana ba ya tada mota muka tafi, saida muka tsaya inda zai saukeni nace da Allah rubutamin number wayarka, har yanzu baiyi magana ba ya ciro biro a gaban aljihunshi ya rubutamin a jikin takarda ya bani,

Nima ban sake magana ba na bud'e mota na fita, napep na tare dan zuwa gida, a k'ofar gida ya saukeni na shige, da sallama na shiga gidan sannan na wuce d'akina ina shiga na ajiye kud'in na zuba ruwa na tafi dan tsarkake jikina banyi ko azahar ba kuma ga la'asar ta kusa..

Saida na gama sallolina sannan na dafa indomie naci, bayan na gama na zazzage buhun kayana na zuba kud'in a k'asa sannan na d'auki kayan na maida daga sama, fitowa nayi tsakar gida na nufi majalissar matan aure....

Barkan ku da hutawa mata masu duniya, Karima tace wai ke duk yau ina kika shige ne ? Ban bata amsa ba na canja tambayar da cewa yau kuma zawarawan anguwar nan dame suka zo mana ne ?

Karima tace ai gasu nan sai ki zauna ayi dake, zama nayi saman takalmana sannan na kalli inda Nana take kwance a saman cinyar A ` i wai tana kakkab'e mata dandirof,

Karima kuma sai cewa takeyi Allah dai ya tsinewa talauci albarka, kullum a rasa abinda za'ayi ta baka sai tuwo maganar d'aya dai tuwo tuwo babu wani ci gaba kullum zance kenan, shi yasa gani nan kullum sai bushewa nakeyi ina k'armashewa kamar mai cutar kanjamau.

Niko da bani da zuciya nace aiko Karima ki godewa Allah, domin dai Allah yayi miki rufin asiri ke kin raina tuwo ko ? Na tambayeta, bata bani amsa ba naci gaba da cewa yo aike cin tuwo yanzu basai wanda Allah yaso yake ci ba ? Da safe kina dama d'an kokonki da rana idan Allah ya hore zakiyi d'an wanke ko teba wata rana ma har taliya kuke dafawa, da daddare kuyi tuwo kuci ku k'oshi keda "ya "yanki kuma duk daren duniya naga sai mijinki ya shigo miki da fura, tou ina laifi ? Aike tsakaninki da Allah saida kice Alhamdulillah bawai ki zauna kiyi ta tsinewa talauci ba ai ina ganin haka kamar rashin godiyar Allah ne.....

Saudatu tace, { itama ba'a gidan take ba shigowa takeyi } ai rayuwa tana san canji kullum abinci d'aya an kama dindindigau kamar kukan mutuwar uwa, ai ya kama a samu sauyi mana Sultana.

Nace haba Saude ai duk namijin da kikaga ba'aci mai dad'i a gidanshi ba tou baya dashi babu namijin da yake so a tsarewa iyalinshi, Saudatu tace ai wallahi k'arya ne mijin Karima yana da kud'in da ko naman rago saiya ciyar da ita dashi, dandai kawai had'in fad'a baida dad'i amma wallahi dasai na fad'a mata abinda yakeyi da kuma inda yake kai kud'in nashi , ita ya rainawa wayau ya barta nan tana ta sassak'ar tuwo sai kace matar ladar noma.

Daga wannan maganar har Karima ta kawo wuya, ta fara zazzaga luk'a luk'an zagi tana cewa ai da ganin biri yayi kama da mutum tsakanina da Nuhu sai Allah ya isa ban yafe mishi ba, kuma zai dawo gidan ya sameni saina ci uwarshi....

Kallon Karima nayi tare da cewa idan dai kuna biye ma zawarawan anguwar nan wallahi duk sai sun kashe muku aure, baku san maganar d'auka ba baku san abinda kuke fad'a musu ba ku biye musu su kaiku su baroku, su basuyi aure ba kullum suna biye daku suna halakar daku,

Karima tace ai wallahi Sultana na yadda da maganar Saude saboda rabon da muyi kwanciyar aure dani da Nuhu yau anfi k'arfin wata d'aya, dama idan ba neman mata yakeyi ba ai kema kinsan abunda bazai yuwu bane ba....

Tsoki nayi tare da cewa ai wallahi saina fad'a miki ko zatai miki zafi, ba Nuhu ba wallahi koni dakel nake iya zama kusa dake, mace da aka santa da gayu da kwalisa da k'amshi da tsafa da tsaftacewa tou ku matan gidan nan ba haka kuke ba, kullum safiya kunzo kun jibge a k'ark'ashin inuwa ba wanka ba wanke ido babu sallah bare salati, baki cuwai cuwai ba abinda kuka sani saidai inuwa ta k'are ku ja tabarma ku k'ara gaba,

Kun fito tun kafin mazajen ku su fita daga d'akin ku kun rigasu fitowa, yara sun kwana zabga fitsarin kwance baku tsaya kun gyara kun wanke ba, yanda namiji yabar d'aki haka zai dawo ya taddashi, baku iya magana da mazajenku ba kuna ma mazanku magana muryarku ta kere tasu mace da aka sani da sanyi, kina ma miji magana tsawa tsawa kamar yaron gidanki, duk daren duniya idan Nuhu ya dawo sai yayi wanka ya tsaftace jikinshi a haka zai rungumeki ki b'ata mishi wanka ?

Kalli kanki Karima ji k'afafuwanki waike matar aure ! A haka har kike tunanin namiji zai samu kwanciyar hankalin da zai baki natsuwa ? Aini wallahi ko toilet na shiga mara tsafta banda natsuwar da zanyi komai a cikinshi wuta wuta zan fito dan kar in d'aukowa kaina cuta, gashin hamatarki ma kad'ai wallahi abin zubar da yawu n....... Mik'ewa Karima tayi tare da kaimin duka dan uwarki ni kike cewa kazama ce ?

Rik'e mata hannuwa nayi duka tare da cewa saurara kiji ni bance miki k'azama ba kawai dai ina fad'a miki matsalarki ne, amma kiyi hak'uri ni ba'a fad'a dani gaskiya ce baki so kuma daga yau na daina insha Allah, amma duk da haka zan baku shawara d'aya dake da Nana wala Allah tayi muku dad'i wala Allah tayi muku zafi Nana tace ki rik'e banzar shawararki kila ta miki amfani can gaba..... Murmushi nayi tare da cewa tou ba damuwa na gode amma kuma ku sani bazan daina zaman majalissar nan ba, yanzu ma sallah magrib zanyi na dawo...

Babu wanda ya bani amsa dan haka naje na d'auk'i buta ta naje nayi alwallah, saida nayi sallah isha'e sannan na fito majalissar su......






19/08/2019



*NICE DAI...*


*JAMILA MUSA...* 🤙🏻


⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 13


Sallama nayi musu amma babu wacce ta amsamin, na maimaita sallamar har sau ukku amma dukansu babu wacce ko kallona tayi bare nayi tunanin zasu amsa min, murmushi nayi tare da cewa aikin banza kare da gudun layya.

Wuri na samu na zauna, ina zama gaba d'ayansu suka tashi suka bar wurin aka barni zaune ni d'aya kamar mayya, banji wani damuwa ba haka banji bak'in ciki ba domin dai nasan gaba d'ayansu nafi su ta ko ina da ko ina, tunda kuwa nafi su ai babu dalilin ni na biye musu muyi gaba, bawai dan ban iya ba na iya kuma idan na fara nawa bashi da kyau....

Ban tashi a wurin ba na haska wayata na fara kwafar lambar Alhaji daga saman takarda zuwa cikin wayata da nayo mishi vidio, nafi minti biyar ina rubutawa karantawa ne dai bana iyawa amma ina kwafar abu, idan kuwa zan kwafa da guda guda nake d'aukarshi, kuma zansa a bud'emin whatsApp amma ya zamar min na "yan gaisuwa saidai duk wanda zanyi magana dashi inyi masa voice note, na ajiye number shi a wayata, abinda na saka mishi shine lamba 1

Mik'ewa tsaye nayi tare da cewa bak'in ciki da fushi ba naki bane Sultana tunda kina da aikinyi, d'aga muryata nayi tare da cewa waye yake san k'amshi mu bashi turare ? Tou tabbas maik'o saidai a barwa balangu ansha gaban mai tsiri......

Kujerata na d'auko na zauna k'ofar d'akina tunda na lura suna neman su haramta min zaman tsakar gidan ne kuma aradu basu isa ba, watsa kunnuwa na nayi ina jiyo firarsu k'asa k'asa bana iya cewa naji abinda akace duka ba amma da yake Saude bata iya maganar sirri ba, bama itama ba duk matan gidan ga haka suke, ji nayi tana cewa ai wallahi ki had'ani dashi in nemi taimako....

Daga inda nake zaune nace hattara dai matar aure, idan dai an ciza a busa, ki kiyayi duniya da rayuwar mutanen cikinta, ita duniya da kika ganta juyi d'an magwaro takeyi yayin daya fad'i k'asa zai kwaso k'asa da tsakuwa, idan kika wanke zak'in zai fita idan kuma kika sha baki wanke ba zaki ci da k'asa duniya tafi karfin kowa, wanda yafiki iskanci yazo yayi ya koma ki kama kanki kuma kiyi k'ok'ari ki koma gaban Allah kina mai kamanta gaskiya, amma na horeki da ki kiyaye darajar aurenki tun kafin duniya ta juya miki baya....

Cikin hayagaga Nana tace ai ba tsoronki akeyi ba a gabanki ma za'ayi maganar dan kutumar ubanki idan kin isa ki hana wani abu in gani, tirr na fad'a tare da cewa kutumar ubana tafi k'arfin kaff zuri'arku wallahi, saboda ko da yake raba kutumar wa mata badai irinku masu tsamin daud'a ba...

Kaina Nana tayo da gudun bala'i kafin ta iso na d'auki kujerata na rik'e nace wallahi kika kuskura kika iso nan saina raba miki kai gida biyu, tsoro ya hanata ta iso taja tayi tsaye, tsoki nayi tare da cewa k'aryar rashin kunya sakarkarin banza daku, insha Allah ko gani nayi zaku shiga wuta saina watsa muku fetir, ina fadin haka na shige d'akina na kyale jahilai, dan gaskiya na lura wallahi jahilci ne kawai yake cizar musu kwalwa, inma banda b'atar basira matar aure za'a kai wurin wani namiji ta nemi taimako.....

*** *** ***

Sati na d'aya kenan bana shiga safgar kowa a gidan da nake haya, ni dama fil'azal magana bai dameni ba, shigowa na ma gidan nan ne naga har na

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment