Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi cewa nice , yace ai banji kin fara kuka ba yau naji kinyi shiru , a daidai lokacin daya fara duba littafai na , haka yayi ta cirosu ɗaya baya ɗaya yana dubawa har yazo kan report ina , warwareshi yayi ya duba , gaba ɗaya annurin fuskarshi ya ɗauke ya ƙurawa report in ido , cikin muryar ɓacin rai yace tsaya , tsayawa Al ' Ameen yayi Dikko yace fita ki koma gaba ki zauna , da sauri na fita na koma gaba na zauna , ina ta mazurai kamar nayi wa sarki ƙarya duk yanda akayi a cikin waccan takarda yaga ɓacin rai...

Shiru yayi tun daga nan ba saike magana ba har muka iso katsina , ko waya aka kirashi baya ɗauka , lokacin da muka iso har an fara sallah magrib , Al ' Ameen na tsayawa na fita da sauri zan wuce cike Dikko yace ke zo nan , da sauri na dawo shi kuma Al ' Ameen fita yayi ya ɗauki buta ya zagaya can bayan gida dan yayi alwallah ,

Buɗe murfin motar yayi ya fiddo ƙafar ɗaya ɗayar kuma tana ciki , tsareni yayi da idanuwa dan haka na sauke kaina ƙasa shiru yayi na wasu mintuna sannan ya ɗago report in yace dan kin ɗaukeni sakarai ni zaki kawo ma wannan abun ? Shiru nayi banyi magana ba , tsawa ya daka min yace baki ji ina miki magana ne ? Cikin rawar murya nace yi haƙuri , fitowa yayi daga cikin motar da sauri nayi baya , shima takowa yayi ya matso kusa dani , da sauri na sake ja baya , ya sake biyoni , yana sake matsowa na ƙara ja baya , idan na sake matsowa kika matsa wallahi saina zaneki , tsayawa nayi jikina ya fara kyarma ina kallonshi ,

Cike da ɓacin rai yace wannan iskanci zaki kawomin ? Girgiza kaina nayi ba tare da nayi magana ba , cikin tsawa yace shin kinyi rantsuwar magana ne ina miki magana kina girgizamin kai , da sauri nace a , a , jinjina kai yayi tare da tillomin report in yace ɗaukarshi ki shiga gani nan zuwa zaki faɗamin iskanci da kikeyi makaranta har kika ɗaukomin na 20 , na ƙarshe ke jakar da baki kishin kanki ya ƙarasa maganar tare da nannaɗe hannun rigarshi dan Al ' Ameen ya kawo mishi ruwa zaiyi alwallah...

Duƙawa nayi na ɗauki report in zan shiga ciki yace kije ki fiddo min jakar banzarki daga mota , da sauri naje na ɗauko jakar na wuce ciki a lokacin shi kuma har ya gama alwalla ya biyo bayana yana ci gaba da faɗa ,

Ɗakin da yake shiga ya wuce ni kuma na shige ɗakin da nake zama , yana nan kamar dai da babu wani ci gaba a cikin ɗakin , alwallah nayo nayi sallah ina roƙon Allah ya bani mafita Babana kaɗai nake ciwon san gani ,

Har nayi sallah isha'e Dikko bai fito ba , su kuma uwayen ƙwa² har sun cika gidan sun fara gardamar kwallo , gajiya nayi na kwanta a inda nayi sallah gaskiya rashin ahali masu mutunci bai ba , duk wanda ya rasa iyaye masu daraja ya zama sai a hankali , ita kuma Inna ko wane irin ahalin suka raine ta ? Soyayya tana rufewa mata ido dasan duniya har su kasa gane aibun namiji , irin wannan rayuwar bata dace dani ba , da na fito daga zuri'a masu mutunci da duk haka bata faru dani ba ,

Inayin rayuwa irin ta dabbobi kuma ni ba dabbar ba , mahaifi ya haifi zuri'a wai ya barsu da cida kansu wannan ba komai bane sai rashin tsoron Allah , caca neman mata shaye² shine wanda na samu a matsayin ubana , rayuwata tazo a garari zata ƙare a raɓe² , na ɓarar da mutuncin da yasa har wani namiji yake da damar shigowa rayuwata ya ɗaukoni daga cikin ahalina ya maidoni cikin rayuwarshi , wannan wace irin rayuwace na samu kaina a cikin ta... ?

Dariyar Dikko na jiyo sai kyalkyatawa yakeyi duk yadda akayi waccan dariyar wallahi mugunta yaji , palon yayi shiru sai salati akeyi ƙasa² amma Dikko sai dariya yakeyi yana ƙarawa , maganar Al ' Ameen naji yana cewa mai gida tou ya za,ayi , miƙewa Dikkon yayi yana dariyar mugunta yayo ɗakin da nake kwance ,

Cikin dariya yace ya miƙo hannunshi yana cewa An mata taso mu tafi , da sauri na taso kallona yayi yace wai duk me kikeyi baki cire kaya ba , ba tare dana kalleshi ba nace ba komai , tou zo mu tafi kina zuwa ? Ya tambayeni , girgiza kai nayi alamar a , a dan Dikko baida saiti abinda na fahimta idan dai yana cikin mugunta zaiso yayi ta zalinci yana dariyar cuta ,

Dariya ya sakeyi cikin sigar cuta yace da Allah kizo mu tafi , kyaleshi nayi na koma na kwanta , murmushi yayi sannan yace to tunda baza ki ba karki bacci ki jirani yanzu zan dawo kinji ko ? Nace tou , kallona yayi cikin wani irin yanayi sannan yace kinsan yau zan hanaki baccin dare sai kin faɗamin abinda yasa kika je kikayo na 20 , nace tou , har ya fita kuma ya dawo yace kiyi wanka kafin in dawo ga kayanki nan palo ki kwashe su ki dawo dasu ciki naga ma duk sunyi ƙura , yana faɗin haka yayi gaba abunshi , ina kallonsu ta window kowa ya shiga mota amma ba'a fita da motar Dikko ba kuma ba'a tafi da Al ' Ameen ba , saida suka gama fita na wuce bayi dan inyi wanka.....




23/09/2019




*JAMILA MUSA ...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 39


Ina fitowa daga wanka na wuce palo inda kayana suke ajiye , ɗagasu nayi ɗaya bayan ɗaya naga babu wata ƙura da kayan sukayi nidai a gani na dan an lulluɓe su da towel , zani da hijabi kawai na ɗauka na koma ciki ,

Zanin na ɗaura wato ɗaurin ƙirji , na saka hijabin na nufi palo dan naga Al ' Ameen yana waje har yanzu bai shigo ciki ba , inda kulolin abinci suke naje na buɗe na zuba abinci naci na ƙoshi sannan na dawo ɗaki nayi kwanciyata !

Babana ne yazo ya tsayamin a rai gaskiya ina cike da kewarshi soyayyarshi ta hanamin zaman lafiya , duk duniya ban haɗa soyayyar Baba da kowa ba , ko ina yake ? Ko a wane hali yake yanzu ? Yana tunani na ko shima bayayi... ? Haka nan naji hawaye sun cikamin ido cike da rauni nayi magana a bayyane ina kake ... ?

Murmushi nayi mai cike da ɓacin rai zuciyata cike da kudurirrika akan Dikko duk runtsi duk wahala komai daren daɗewa sai Dikko yayi nadamar sani na , yanda ya takura ma rayuwata nima saina takura ma tashi rayuwar saina mishi zargen da bazai iya warware kanshi ba , da wannan tunanin bacci ya ɗaukeni.

Su Dikko kuwa sai 12:30am suka dawo hayaniyar shigowar motocinsu ta tasheni daga bacci , tunda suka fara fitowa daga cikin mota suke gaddama har suka shigo palo , bayan kuma sun shigo haya² ƙarar filets da cokula kowa yana zuba abinci amma har yanzu banji maganar Dikko ba danshi baya da ƙoƙari wurin magana saidai dariya itama sai yaji mugunta yakeyi...

Zuwa wani lokaci kuma palon yayi shiru bakajin maganar kowa sai ƙarar tv dan sun fara cin abinci , bayan wasu mintuna kuma naji wani yana cewa kai ubangiji ya fishshemu tsaka mai wuya , gaskiya na tausayawa kaina na tausayawa Saminu wallahi , Dariyar Dikko naji yana cewa niko wallahi bai bani tausayi ba aishi ya siya tsautsayi da kanshi maganin ganganci da rayuwa kenan kaga garin neman gira an rasa ido , anso ayi suna sai aka samu matsala...

Hayani taci gaba da tashi , yayin da wasu ke cewa wannan tashin hankali da suka gani yau basu iya bacci , Dikko yace badai anan gidan ba ku gama cin abinci kowa ya kama gabanshi wallahi yau babu mai kwana a gidan nan , dariyar wani daban naji yana cewa sai An mata , Dikko yace koma "yar tsohuwa ce sai kunbar gidan nan ,

Kusan mutum biyu suka haɗa baki wurin cewa wai da gaske akwai mace yanzu haka a gidan nan ? Dikko yace mai maganar zaka tambaya dan nima dai ban sani ba , wai wace ce ita An matan nan ni na daɗe wallahi inaji Dikko yana kiran An mata ko itace ɗiyar ɗan... Sai naji kuma yayi shiru , murmushi nayi nace ɗiyar ɗan caca ,

Duk yanda akayi wani ya dakatar dashi ta hanyar hanashi yayi maganar shi , gaba ɗaya kuma palon yayi shiru har suka gama cin abincinsu babu wanda ya sake magana , bayan sun gama suka fara saɓewa ɗaya bayan ɗaya , bayan kowa ya gama fita naji Al ' Ameen yana ma Dikko sai da safe , banji abinda Dikkon yace mishi ba , ya fice kuma da motar Dikkon ya fita ,

Bayan Al ' Ameen ya fita daga gidan Dikko ya fara kirana , ban ansa ba na taso na fito palon daga bayanshi na tsaya nace gani , shima bai juyo ba yace kinajin yunwa ne ? Nace a , a me kikaci ne ? Nace ba komai , a , a ƙarya kike yarinya me kikaci dai ? Nace maka ba komai , tou zo nan yayi maganar a daidai lokacin da yake kwanciya saman kujera ,

Gabanshi naje na durƙusa cike dajin haushin shi , bai kalleni ba dan hankalin shi nakan tv amma dan tsabar ya ɗaukeni kidahuma yace kinmin kyau fa , zanyi magana ya tsareni da idanuwanshi tare da cewa bafa ina nufin kina da kyau ba ko kin birge ba kawai dai dan bakyajin yunwa nace da kyau , kallonshi nayi amma yanayin fuskata ya nuna banji daɗi ba , murmushi yayi tare da taɓe bakinshi ya kauda kanshi gefe guda yana ci gaba da cewa ni mace mai kyau haushi take bani , dan mafiya yawansu jakuna sunyi yawa a cikinsu kalloni yayi yana tambayata ko nayi ƙarya ?

Kallon da yayi mani yasa nace a , a , murmushi yayi yace ɗaukomin report inki , tashi nayi jiki suku² na fara tafiya , tallabo kanshi yayi da duka hannayen shi yana kallona , zuwa can kuma yayi tsoki wai ji mace na tafiya , babu wani tsari mai jan hankali babu wata zarra mai burgewa a tattare dake , shi sakaran waccan rana kome ya gani a tattare dake zance har 12ndare , ya gane sarai banji daɗin abinda yake faɗa a kaina ba , naje na ɗauko report in na kawo mishi ,

Ansa yayi tare da tashi zaune yana kallona , yace wallahi kina burgeni sosai saboda kina da kyau , murmushi nayi tare da kallonshi , gyara zama yayi yaci gaba da cewa kyawawan idanuwan ki inajin natsuwa yayin da kika kallene ni dasu saboda kyawunsu da sheƙinsu ko a duhu kikayi kallo dasu abun ɗaukar hankali ne , ƙarajin daɗi nayi tare da ɗanyin wasa da idanuwana dan ina so inji an yaba surar da Allah yayi min , kyakkyawan murmushinki yana tafiya da hankali na a duk lokacin da naga kina cikin nishaɗi dan yanayin yana sakani cikin wani irin shauƙi mai wahalar misultuwa , ƙara yashe bakina nayi inajin daɗi , hankalinshi nakan report in yace kike ta wani kwashe baki da ita fa nake ba ke ba , ɗan kama kaina nayi sannan nace wace ce ? Matata mana dan tafi ki haɗuwa yayi maganar tare da ɗaure fuska yaci gaba da kallon report in..

A dibarance na kalleshi shi kuma hankalinshi yana kan report yana kallo ko kyaftawa bayayi sai gemunshi dake motsawa a hankali saboda taunar cingom in da yakeyi cikin kwarewa da salon ɗaukar hankali...

Naɗe takardar yayi tare ɗago ƙafarshi ya takamin kafaɗa yana wasa da report in yace tunanin me kike a makaranta ? Kin rame , kuma cikin ku 20 kika yo na 20 , tunanin me kike ? Duƙar da kaina nayi ƙasa ina wasa da kafet banyi magana ba , jijjigani yayi da ƙafarshi yace baki ji wai ina magana ne ?

Cikin ladabi nace babu komai , to ko aure kike so ne ? 😳 aure kuma ? na tambayeshi tare da zaro idanuwana ina kallonshi , wani irin kallo yayi min mai tsarga zuciya wanda saida tsikar jikina ta tashi naji wani irin yanayi mai wahalar fassarawa na kasa daina kallon idonshi ,

Ɗan kauda kanshi yayi cewa tou daina kallona haka nan , gyara bakina nayi na sauke idona daga fuskarshi , yaci gaba da cewa zan miki haƙuri na yau saboda bance miki kar kiyomin na 20 ba , ban faɗa miki irin position in da nake so ki kawomin ba , amma zan faɗa yanzu..

Kalloni yayi sannan yace wallahi ׳ nayi rantsuwa kuma bazanyi kaffara ba , idan har kika sake kawomin 20 bazan dakeki ba , kuma bazan zageki ba haka bazan sakeyin fushi ba , kinga gidan nan dagani sai ke , sassauta muryarshi yayi ƙasa² yaci gaba da cewa babu wanda zaiji kuma babu wanda zai gani , duk lokacin da kika zo min da na 20 nasan abinda kike tunani , duk lokacin da naga 20 ni kuma zan sakaki a ɗaki irin abinda nayi miki a gidanmu ai kin tuna ko ? Ba tare da ya jira na bashi amsa ba yace tou wallahil azim irinshi zan ƙara miki ,

Kinga idan baki so in miki sai ki dage kiyi karatu , idan kuma kina so sai ki sake kawomin na 20 ni kuma ina ganin 20 tou sai mu shige daga ciki in rufo ƙofa in baki abinda kike tunani kuma ince karki sake ki faɗawa kowa...

Lallai Dikko digirarran ɗan iska ne kuma baida kunya ko kaɗan , kasa haɗa ido ma nayi dashi naci gaba da kallon kafet , komawa yayi ya kwanta tare da cewa kashe tv n can kije ki kwanta , simi² na tashi naje na kashe tv in na wuce ciki ,

Tun daga wannan rana Dikko ya zama siriki na , nafi sati ɗaya ban yadda mun sake haɗuwa dashi ba , idan basu nan zanje in zuba abinci inci , idan kuma yana nan saidai in yini kuma in kwana da yunwa , da kuma naji maganarshi ya shigo ƙaramin palo zan gudu bayi in zamana , idan kuma akayi sa'a ya shigo ɗakin dan ya jira in fito ya ganni to shi da kanshi zai gaji da zaman jirana ya fita , ni kuma idan zasu fita daga gidan zan laɓe jikin window inyi ta kallonshi wallahi bana gajiya da kallonshi kwata²

Gidan kuma kullum sai ya cika da maza suci su asha suyi ta gaddama mara amfani , amma zaiyi wahala kaji bakin Dikko , idan sun gama sun tafi kuma zaiyi kwanciyarshi ne kawai a palo , dan yanzu gidan yake kwana tun ranar da abokinshi yace wai da gaske akwai macen dake zama a gidan nan ? Amma naji ranar nan yana waya da wata wai yaushe zata dawo zai kawo mata amanar wata ɗiyar tsintuwa , nidai haka naji daga nan ban sake jin maganarshi ba , shin nice ɗiyar tsintuwar ko kuma wata ce daban oho...

Kwance nake saman katifa sai juyi nakeyi saboda azabar yunwa , na rasa inda zansa kaina cikina sai zafi yakemin har na gaji da kwanciya kuma gashi duk yau Dikko bai fita , yanzu haka palon ya cika da mutane kuma wallahi ko jiya babu abinda naci tun daga kalacin safe.

Na rasa inda zan tsoma rayuwata inji sanyi , sai hamma nakeyi ga bacci inaji amma yunwa ta hana inyi bacci duk jikina ya mutu bana iya tsinana uwar komai sai kwanciya nake kamar ruwa ,

Ta dubu nasha na fita ƙaramin palo na zauna ko Allah zai kawo min Dikko , amma mi har 11:30 bai shigo ba kuma babu wanda ya fara tafiya har yanzu dan naji sun tashi daga firar kwallo sun dawo labarin "yan danbe , har yanzu banji maganar Dikko ba kila baya gidan gaskiya ,

Daga firar "yan danbe suka faɗa maganar Saminu , wani ne yace bawan Allah Saminu wallahi ana maganar danben nan shi ya faɗo min a rai , me ya sameshi ne ? Wani daban ya tambaya , cikin muryar jimami yace bakaji ba ? Yace wallahi banji ba kuma ban sani ba miya faru ? Yace wallahi tsautsayi da rabon ayi , yaje kallon danbe .

Dariyar Dikko naji yana cewa babu wani tsautsayi kuma babu rabon ayi , kawai ka faɗa mishi matar wani ya nema , kuma dan hauka ya tashi ya bita har gidanta , Allah yasa mijinta ya ritsasu shine yayi ma Saminu shegen duka har saida idonshi ɗaya ya fita , innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wannan masifar Dikko kema dariya ranar da na dawo daga makaranta kenan ?

Shima mutumin da ake ba labari salati yakeyi , Dikko yace wato mu mutane muna da wani hali na daban , kai da kanka zaka siyawa kanka matsala sai kace wai Allah ya kawo maka ? Ko ƙaddara ne ko meye ne , kaje ido ya fita wurin zina , kuma abin takaici ma Saminu matanshi biyu amma saboda masifa sai ya nemi mata , waye ya aike shi ? Wa ya saka shi ? Waye ya sashi neman matan aure ni wannan masifa da ta samu mutane bansan irinta ba , wannan tsautsayin dai Saminu shine ya kawo ma kanshi abunshi ba wani ba ,

Mai tambayar yace wa Dikko ina suka haɗu da matar tou ? Dikko yace an faɗa maka kallon danbe yaje , dariya sukayi dukansu , yace nifa ban gane kallon danbe ba , dariya Dikko yayi yace nanfa aka tsaya , wurin kallon danbe suka haɗu ,

Shima naci gareshi mai tambayar yace don Allah wai ya wurin danbe suka haɗu ? Tasowa Dikko yayi ya taho ciki , yana shigowa ya ganni zaune saman kujera yace baki bacci ba kenan ? Yayin da naji "yan palo sun ɗauki ihu duk yanda akayi an fassara kalmar dambe ,

Ba tare dana kalleshi ba nace Eh , zama yayi kusa dani yace mene ne tou ? Nace yunwa nakeji , kallon agogon hannunshi yayi sannan yace kuma wallahi banajin sun rage abinci amma bari su fita mu gani , nace to , wayarshi ya ciro daga aljihu ya ƙura mata ido yana danne ² yayin da nakejin kamar in tambayi Dikko miye dambe ? Dan ina so naji yanda labarin yake tiryan² kuma gashi palo labarin suke amma zuwan Dikko yasa banaji ,

Haka dai rayuwata taci gaba da tafiya zamana tare da Dikko , kullum da tunanin Babana nake kwana dashi nake tashi , bani da wata damuwa ta rayuwa dan Dikko ya shigo cikin rayuwata sosai kuma babu abinda na nema na rasa ,

Daren yau kuwa da kanshi yake tayani haɗa kaya saboda gobe zan koma makaranta idan Allah ya kaimu , sai nasiha yakemin cikin lallashi cike da tausayina da kuma nuna tsantsar soyayyar a gareni , kamar ya buɗe kaina ya zubamin ilimi haka yakeji bawan Allah , saida muka gama haɗa kayan muka fitar dasu ƙaramin palo , duk yanayin Dikko yana nuna bayajin daɗi zai rabu dani , duk inda na motsa zai tsareni da kallo mai tattare da tsantsar ƙauna da shaƙuwa.

Murmushi yayi yace idan kika koma makaranta zaki riƙa tunani na kuwa ? Ya mutsa fuska nayi tare da taɓe baki nace wai ni ? Na nuna kaina ! Yace Eh , nace Allah ya sawaƙamin mema zaija min nayi tunanin yin tunaninka ma ? So ya bani ansa , murmushi nayi tare da cewa tirr Allah ya sawaƙamin in faɗa Soyayyarka , wani irin kallo yayi min mai tsarga zuciya harsai da naji jikina ya mutu sannan yace ke komai sai kinyi wasa ni banajin daɗin haka ,

Jan hannuna yayi muka zauna saman kujera ya tattaro duka natsuwarshi sannan yaci gaba da cewe , ni ina sanki , da sauri na tashi tsaye nace me ? Dikko yace ƙwarai ina sanki kuma kema kina so na wannan shine gaskiya ina ta ɓoyewa kwarai , ya faɗi maganar tare da kauda idonshi daga kaina , dariya nayi tare da cewa wasa kakeyi ne ? Yace a , a da gaske ne fa , ba yanzu na faɗa soyayya dake ba tsawon lokaci , duk lokacin da nazo kusa dake sai inyi ta zuba miki ido wannan ai soyayya ce ,

Idan kina magana ni kuma kawai sai nayi shiru natsaya nayi ta kallonki inajin daɗi wannan shima ai soyayya ne , dakatar dashi nayi ta hanyar ɗaga mishi hannu ya isa , ya isa haka :•

Abinda ka bayyana wannan shine ƙimar matashi kamar ka ? Ba shi bane ba , tsawon wane lokaci muka ɗauka da zamu fuskanci juna ? Fari yaro da yarinya ko wannen su yasan damuwar ɗan uwanshi wannan shine so , sannan fahimtar juna ,

Dikko yace sani da kuma fahimta da kike san ko bakya so kina da damuwa ko bakya da , yayin da kika samu wannan sannan ki so ni ? Wannan shine so ? Soyayya fa ita ba tsarata akeyi ba kawai faruwa takeyi , kinyi waya kuma kina saka mata kati ki siya data sai ta baki duk abinda kike buƙata kinga faruwa hakan yakeyi ba shiryawa akeyi ba , tou wannan shine so , bana so na rasa damata yayin da nace kece sarauniyar mafarkina , kina da damuwa kuma kina da riƙe abu a ranki ,

Duk da haka inayinki , ina sanki , tsoki nayi tare da cewa kayi haƙuri Dikko ba kamar yadda kake tunani bane ni banma yadda da soyayya

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment