Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki Dikko yayi a zuciyarshi yace tace bata so na , kuma fa ba'a soyayya dole Allah ma yasa bansha wahalar shawo kan kowa ba dasai nasha wahala na shawo kan iyayena tace bata aurena , gara kawai na haƙura nayi nesa da rayuwarta na barta ta huta , Umar kallon motar yayi Al ' Ameen ma ƙwalalo idanuwa yayi cikin tashin hanki yace mai gida wannan motar zaka bata ?

Cikin ɓacin rai yace Ey ita zan bata , cike da hassada yace ko ka manta nawa ka siyota ne ? Dikko yace kila babanka ya nemomin kuɗin shi yasa na manta , dan wani irin haushin Dikko yakeji kuma Dady yace idan yayi masa wani abu bai yafe masa ba , Al ' Ameen ya kalli motar ya ƙiyasta kuɗinta tou ai wallahi kaf garin katsina wannan motar ita ɗaya ce tak , bazai manta ba lokacin da Dikko ya siyo motar wallahi ganinta ake zuwa yi ana mata hoto ko wata motar batayi ba kuma Dikko bai taɓa hawanta ba , shine zai ɗauka ya bawa karuwa ? Kai amma yarinyar nan ta shanye mai gida da yawa , motar miliyoyin kuɗi haka ?

Kaf ma'aikatan gidan nan suka haɗu suna ma Dikko addu'a Allah ya tsare , wallahi game da kyauta dai Dikko baisan darajar kuɗi ba , yana kyauta maisa mutum ya kasa gane bacci yake ko idonshi biyu ? Bayan ya gama sallamarsu ya shiga mota Ashiru yaja suka bar gidan ,

Al ' Ameen kuwa sai ƙara kallon motar yake hada kukan baƙin ciki ina ma ɗiyar "yar uwarshi ta samu wannan mota ? Mai gida baisan abunshi haka nan yake neman kuɗin baisan darajarsu ba wallahi , yo wannan mota ai daya sani siyar da ita yayi ya sayi gidaje masu kyau kawai ya ɗauki mota ya ba shegiyar yarinyar da Z bata tantancewa , lallai zaima Yayarshi waya idan har Mai gida ya dawo nigeria Haneefa taje Abuja wurinshi...

Daga gidanshi gidansu ya wuce kai tsaye , danyi musu sallama , momy tace idan an ɗaura aure matarka zata isko ka , cike da biyayya yace tou , bedroom ta koma ta ɗauko maganinshi tace gashi nan saura idan ka tafi ka yadda shi , ansa yayi ya saka a aljihun wandoshi , addu'a tayi mishi tare da mishi fatan alkairi harya fita , Dady kuma baya nan ,

Cike da soyayya tabi bayanshi da kallo , haka nan taji dai bari ta mishi rakiya , bayanshi tabi har inda ya ajiye motarshi , saida zai shiga mota yaga Momy ta biyoshi , kallonta yayi yace inzo ? Murmushi tayi tace a , a , kusa dashi ta matsa tace karka zo rakiya nayi maka , taci gaba da mishi addu'a Allah ya tsare tana ɗaga mishi harya shiga mota suka tafi ,

Tun a mota ya goge hotunan Sultana , bayan yayi musu kallon ƙarshe dayi mata addu'a Allah ya bata miji na gari , ya kuma sa ta yafe masa karta riƙeshi a zuciyarta , shi kuma Allah ya bashi haƙuri da dangana akan ta...

Bayan ya gama goge ²nshi da addu'a shi ya anshi tuƙin motar dan gani yakeyi Ashiru ma baya sauri , tuƙin ganganci da wauta Dikko na fama da iskanci cike da kwalwarshi , ga raini ga rashin ganin mutuncin mutane amma yana da tausayi da taimakon wanda baya dashi ,

10:09pm suka isa kano , anan aka canja abokan tafiya , saida jirginsu Dikko ya tashi Ashiru ya juyo katsina bai kwana ba , sauka lafiya mai gida Dikko Allah ya tsare....

Cikin farin ciki na wayi gari kuma nayi alƙawari yau zan faɗawa Dikko nima ina sansa , duk wanda ya ganni yasan inajin daɗin wannan rana , saida hantsi ya ɗaga na sheƙaƙa wanka na , naci gayuna dan nasan yau Dikko yayi kwanan haƙuri nasan ya ƙagara gari ya waye zai fara zarya ganin dokuna ,

Cike da farin ciki nayo ƙofar gida na zauna ina jiran isowar jarumina , har lokacin zuwanshi yazo ya wuce babu Dikko babu labarinshi , gida na koma na ɗauko wayata na kunna , bayan ta gama kunnuwa na fara neman layinshi , amma dai inajin maganar ɗaya ce kodai wayar tana kashe ko kuma babu kuɗi a wayata ,

Gida na koma nasa aka dubamin ko banda kati , kowa sai yacemin akwai idan nace nawa ne sai su kasa lissafomin , Babana na bashi ya dubamin yace akwai kuɗi , nace nawa ne Baba ? Yace dubu ɗari biyu ne , nace tou kiramin wannan lambar na ƙarasa maganar kamar zan faɗa masa ,

Duba sunan da akayi saving in number yayi yai murmushi tare da cewa iye Mamana ta fara soyayya ya ƙarasa maganar yana kallona kuma cikin zaulaya yayi maganar , cikin jin kunya na zauna kusa dashi ina dafa kafaɗarshi nace aini bana soyayya , yace ai ba wani ne ya bani labari ba nine na gani da idona , tou me yasa kace haka ? A dai² lokacin da yacemin wayar a kashe take ,

Cikin rashin jin daɗi na anshi wayar kaina ya fara min ciwo haka nan naji ɓacin rai ya lulluɓemin zuciya , cike da damuwa na fito tsakar gida , amma sai naga gidan kamar yana juyawa , Baba kuma yana min magana daga bayana wallahi kwata² banajin abinda yake faɗa ,

Wai ance ana kiran Sultana , da sauri na fara kakkaɓa idona daya cika da hawaye inayin dariya cikin farin ciki , nayi ƙofar gida da gudu Babana ya fito da sauri ya biyo bayana yana lafiya ? Turus na tsaya ganin Umar , nayi tunanin zanga Dikko babu shi , sake cika da hawaye idona yayi nace ina yake ? Miƙomin makullun mota yayi a dai² lokacin da Baba ya fito yace gashi yace a kawo miki kuma akwai kuɗi a but wai kisha mai , sai ki bani tukuwici in wuce , nace tou ina shi Dikko yake ya aiko ka ? Umar yace yayi tafiya ,

Kallona Baba yayi yace waye ya kawo wannan motar ? Hawayen da suka taru a idanuwa na suka samu damar gangarowa daga saman kumatu na , da sauri na juya na rumgume Babana ina kuka , ɗagoni yayi daga jikinshi yace wai miye ? Waye ya baki wannan motar ?

Cikin kuka nace Dikko ne , kallon motar Babana yayi sannan ya kalli Umar yace wai wane Dikko ne ? Da hannunshi yayi mishi nuni da doki , kallona Baba ya sakeyi yace meke tsakaninki dashi ? Goge hawaye nayi na anshi makullin na buɗe but in motar , bandir in "yan dubu² ne guda goma , guda biyar na ba Umar nayi godiya , shima godiya yayi ya wuce abunshi...

Umar yana tafiya Babana yace wai Mamana ke ya akayi ya baki wannan motar ne ? Nace shi yaga dama ya bani ita ba roƙarshi nayi ba , kallon motar Babana ya sakeyi yace aiko wannan motar bata hawuwa wurinki garin nan saidai a siyar da ita kuma duk ma garin nan bana tunanin akwai mai siyenta shima ƙuruciya tasa ya siyeta , { ba rashin kuɗi baba yake magana ba da yace baya tunanin akwai mai siyenta } babu dai wanda zai ware wannnan kuɗaɗen ya siyi wannan motar kawai dan dai ya hau , murmushi nayi kaɗan nace baza'a siyar da ita ba gaskiya ,

Baba yace ki hauta ace miki wa Mamana ? Nace idan na hauta kaji yadda za'a kirani , tou ina zaki ajiye wannan mota ? Nace gidan dokunanshi zata riƙa kwana ... Allah ya tsare Babana ya faɗa , na ansa da Amin ,

Da kaina nakai ma masu gadin gidan ajiyar mota , suma kansu mamaki ya kamasu ya akayi motar mai gidansu tazo wurina ? Saboda kowa ya sani tashi ce shi ɗaya yake da ita duk kaf cikar faɗin garin katsina , dan anyi surutun motar sosai a lokacin daya siyota kuma har yanzu ba'a gama ba , wannan ansa basu da mai basu ita....

Na shiga cikin ɗimuwar rayuwa nayi kukan rashin Dikko nayi harna gode Allah , na rasa ina zan saka kaina naji daɗi , "yar jakar daya bani a lokacin da muka kama shago dasu Amisty na ɗauko na zazzage , cingom in daya bani nashi na ɗauka nayi ta ci ina haɗiyewa , saida naji zan mutu na haƙura na tattara sauran na mayar ,

Na faɗawa iska ina san Dikko bansan adadin kalamai nawa suka fita daga sautin bakina ba , baida wani amfani dan Dikko dai baya nan kuma bazaiji ba , nayi kukan rashin Dikko har tsawon sati ɗaya ina zubar da hawaye duk nabi na rame na susuce , na kira wayarshi kullum dai maganar ɗaya a kashe , duk lokacin dana kira wayarshi naji kashe sai nayi kuka kuma bazan daina kukan rashin ka ba Dikko har abadan duniya....


Bayan wata ɗaya ,

Abubuwa da dama sun faru , Babana ya warke tas kamar bai taɓa wani rashin lafiya ba , su Amisty kuma an ƙaro iskanci domin dai suma a anguwarmu suka sayi gida ,

Ta siyi motar hawa ta baro iyayenta tana zaman kanta , Nana ma ta tashi daga gidanmu ta koma nasu Amisty , Saude A ` i Zalifa Karima ma duk sun tare a can , Hafsa ma nan take yini amma bata kwana , itama Asma'u anyi mata register kuma suna faɗa cewa yanzu zanga yanda ake shugabar duk wani ɗan iska daya kwana a katsina suna da masaukinshi , idan inajin nima wata ƙwaro ce na kafa manya ²n karuwai kamar nasu...

Lokacin da naji saƙon su Amisty dariya nayi , bana san komawa ruwa dan naji kwata bana sha'awar karuwanci dan zuciyata bata da lokacin sauraren kowa saboda Dikko yabi ya mamayeta da soyayyarshi , kafin inyi wani nazari na yanke hukunci naji gam × ³ a cikin kaina , kamar wacce aljannu yake shiga jikinta haka jikina ya fara fizge² idanuwana sunamin zafi sosai , kaina ya juye , nace tabbas zasu san nawa ba kalar nasu bane mu zuba mu gani dani dasu.

A wannan halin Mamy ta sameni , bayan mun gaisa ta fara rattafomin bayani akan Baban budurwar Dikko , wacce mukayi faɗa da ita a mota.....




30/9/09/2019






*JAMILA MUSA....*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 46


Tsare Mamy nayi da ido na kasa magana duk saida ta gama buɗemin komai ta ƙare da cewa harma ta gayyato shi zaizo katsina jibi , har ta gama kallonta nakeyi saida takai nunfashinta ƙarshe nayi murmushi amma har yanzu idona akanta yake , kuma banyi magana ba ,

Mamy taci gaba da cewa tou ya kike ganin za'ayi idan yazo ? Zance gaki ko kuwa ? Shiru nayi na ɗora wayata a saman goshina na rufe idona na dama ina nazari ,

_Kije abunki amma duk abinda zaki kiyi na hankali da tunani ,_


_Ni bana zarginki har abadan duniya anma dan Allah karki sake ki bari zuciya da sharrin shaiɗan yasa aimin wasan danbe dake , ni ɗaya tak na isheki bana gajiya kuma bazan taɓa gajiya dake ba har ƙarshen numfashi na,_

_Jarumi ɗaya tak akeyi a ƙarni nine jarumin wannan lokaci , Dikko jarumin maza ne kuma ke da kanki zaki faɗa kije ki dawo ina nan ina jiranki....!_

Hawaye ya gangaromin daga cikin ido nace a ina kake jirana inzo ....? Murmushi Mamy tayi tare da cewa soyayya ? Shiru nayi ina hawaye , dariya tayi sosai tace har kin bani tausayi Sultana uban waye ya shiga zuciyarki har kike kuka ?

Saida nayi shashshekar kuka sannan na kalli Mamy da ido ɗaya nace ni kike tausayi ? Tace Eh ai soyayya babu abinda ke cikinta sai wahala da dana sanin da bashi da amfani , murmushi nayi mai ƙuna nace gara ki tausayimin dan a halin yanzu banma san a babin da nake ba ,

Yana so na har yanzu ko ya goge ni daga zuciyarshi banma sani ba , dama yace idan bana sansa zai tafi kuma bazai sake dawowa ba , yazo a lokacin da bansan waye shi ba , kuma ya tafi ya barni a dai² lokacin daya koyawa zuciyata soyayyarshi , bazan gaji ba , ba kuma zan daina faɗa ba har kalma na ƙarshe a duniya , ina sanka ׳ Na ƙarasa maganar ina goge hawaye ,

Tsoki Mamy tayi tare da cewa yanzu kinji abinda na faɗa miki , sai magana na gaba , akwai wani mijin ƙawata yaga wata anan anguwar yana so ya ɓata dare ɗaya tak da ita , tou na biyota bayan nayi bincike sai akacemin matar aure ce , dana faɗa mishi sai yace min dama matar auren yake nema shin zaki iya kawo mishi ita ? Akan wane farashi ? Na tambayi Mamy , tacemin 50k nace kai haba zunubin fa akwai girma , yadai ƙara wani abu...

Mamy tace Sultana haka zai baki , kallonta nayi ido cikin ido nace gaskiya ƙarya kikeyi ke kika rage kuɗin da za'a bani , Sultana ni nake ƙarya ? Nace yo wace ce ke da baki ƙarya ? Mamy tace dama naga kin raina ni ko girma na baki bani ? Murmushi nayi da gefen baki na , nace babu wanda ya kawoni bariki ni na shiga da kaina , bana ƙarƙashin kowa ina bisa ƙarƙashin ikon zuciyata ne , banda uwar ɗaki haka kuma banda ubangida , bana nema wurin kowa dan kowa baida abin bani , wannan harkar ra'ayina ne yasa na shiga badan ra'ayin kowa ba , abuna yana jikina naki yana jikinki , tayuwu ke ki bada naki a baki 1k wannan ra'ayinki ne kuma kinji kina iyawa ne , niko babu dalili na buɗewa namijin banza ƙafata ya hauni ya sauka ya bani kuɗin da bazasu kashemin kwarnafi ba ,

Ban kawo ki bariki ba baki kawoni ba ,baki koyamin ba haka nima ban koya miki ba , a rana tsaka muka haɗu kin gama gogewarki nima idona biyu kika ganni ba bacci nake ba , tuni na bushe fitilar idona , banda Aunty banda Yaya banda Mama haka kuma banda uwar ɗaki a bariki wallahi , ta yuwu ma kila namiji ɗaya ya nemu a tare yana gamawa dake ya jawo ƙafata , wane girma gareki a wurina ? Sana'ar fa iri ɗaya ce , uwar data haifeni ma data ga bata iyawa kayanta ta tattara ta kama gabanta tou bare fa ke banzar bazara kashi a masai , na faɗa kuma zan sake maimaitawa idan bakiji ba kiji , idan kuma kin manta ki sake fahimta ,

Matar aure bana kawota a dubu 50k wallahi idan dai yana so tou dubu ɗari biyar zai bani nayi miki alƙawari kuma ki mishi albishir a cikin sati ɗaya tak zan kawota babu asiri babu bori , idan haka yayi miki to idan bai miki ba a daina cinikin dan bana san rainin hankali da yawa....

Shiru Mamy tayi tana kallona ni kuma naci gaba da gwada layin Dikko , can kuma tace tou za'a baki rabin kuɗin idan an gama sai a cika miki , ba tare dana kalleta ba nace ni bana da sasshen jikin mutum , Mamy tace kamar ya kuma ? Nace tou kamar yadda zaki bani rabin kuɗi ! Me zan ciro na fara kawo mishi ? Mamy tace Sultana zan baki rabin kuɗi idan aka gama na cika miki , tsoki nayi nace kinga da Allah ki tashi kina ɓatamin magana a banza , kije idan kun shirya ansar mace kuzo da dubu ɗari biyar na gama magana....

Jakarta ta buɗe ta ɗauko dubu ɗari biyu tace gashi zan cika miki anjima , ai banma da lokacinta bare kuma tayi tunanin naji abinda tace , can kuma tace kin cika kafiya gasu bara na ranta cikin kuɗin ƙawata idan naje banki na cire ita saina bata , da gefen idona na kalli kuɗin , miƙomin tayi na ansa na tusasu fes sun cika , hoton matar ta turamin a wayata tace gata nan kuma bama so sai tazo tayi ta wani noƙe ² nace inki so kije abunki ,

Har zata fita nace , maganar mai zuwa katsina kuma jibi akwai Hamida akwai yaran gidan Baba ƙarami ki taimakamin suma su shigo sahunmu tafiyar zatamin dai² , Mamy tace baki da damuwa , godiya nayi mata ta wuce abunta , ni kuma naci gaba da nazari akan hanyar da zan fiddo matar aure a kaita wurin mijin da ba nata ba kuma banma taɓa magana da ita ba ina dai ganinta tana wucewa !

*America...*

Mai gida Dikko ne kwance a gefen gado , ya ƙurawa waya ido ko kiftawa bayayi , daga can ƙarshen gado kuma amaryace sanye cikin wata irin tsadajjiyar alkebba , mutum biyar suka kawota kuma kwanansu biyu yau suka juya bayan sun ƙara gyarewa ango amarya suka shiryata cikin shiga ta alfarma da ɗaukar hankali , bayan tafiyar "yan rakiyarta ta dawo ɗakin da take tunanin nan ne ɗakin mijinta ta tsareshi da kallo kamar kwarton namiji yaga wawan zama..

Tafi minti 15 zaune bataji yayi magana ba , dan haka ta tashi tsaye ta zare alkabbar ta ajiye a gefen gado , cikin gogewa da buɗewar ido ta fara tafiya cikin natsuwa ta zagaya inda Dikko yake kwance.

Kafin ta iso Dikko ya tashi da niyar shiga toilet , da sauri tasha gabanshi tace haba ina ne kuma zakaje ne bayan kayi wanka , kallonta yayi sannan yace zan tsaya kiyi ta kallona ne kamar banda aikin yi ne ? Haba Yayana aiko kaine kake da aikin yi a gabanka , nuna kanta tayi daga sama har ƙasa tace mai wannan zundumemiyar mace inashi ina bacci a daren nan ? Ga kallo kuma ga aiki , kasan yanzu ba'a sake da miji mai mummuna ma ta tattala abinta ina gani mai tsadajjiyar fuska da ƙira mai ɗaukar hankali kamar ka ? Ai banga ta zama ba aiki ya sameni harsai na goge tambarin ɗiyan ɗan caca a zuciyarka...

Wace ce ɗiyan ɗan caca ? Dikko ya tambayeta yana mata kallo mai nuni da zaici ubanta ! Haba Yaya DK kana tunanin bansan komai ba ? Kaf labarinta a hannuna yake , me zakayi da wannan yarinyar ? Yarinya mara tarbiya , marar asali jahila da bata gane komai sai karuwanci..

Murmushi Dikko yayi maicin rai dan duk duniya ya tsani a famo mishi ciwon tunanin An mata , haka kuma ya tsani a soketa , cikin ƙunar rai yace ni na sanki tun baki san kanki ba , haka kuma nasan waye ahalin babanki ciki da waje , idan har zan duba girma da tsatson ahali da tarbiyar iyaye ke ko matsayin mai aikin gida na baki ba , da cancanta aka bimin wurin auren da aka yomin ke kinsan baki kai cikin layin matan da zanbi hanya ɗaya dasu ba , An mata bata sanki ba kuma baki gabanta dan bata san da zuwanki ba , tana can tana rayuwarta bake ba ko ni bata da lokacina bana san munanan kalamai yana fitowa daga bakin ki akanta , ba ƙoƙarin gogeta zakiyi ba domin bata gogowa har abadan duniya a zuciyata , idan dai zaki iya kiyi ƙoƙari ki kafa soyayyarki a zuciyata shine abinda zakiy farko kenan ,

Sassauta muryarshi yayi sannan yaci gaba da cewa , tana da tarbiyya , nine zan bada wannan shedar , asalinta kuma yana tare da asalina , tabbas bata gane komai sai karuwanci , nine na yanka mata tikitin karuwanci nace ta koyo dan tamin riƙo da bazan taɓa tunani wata mace a duniya ba sai ita , ta shafe kaf illahirin zuciyata , tabi cikin kwalwata da jinin jikina , yarinya ƙarama mai tafiya dai² da irin rayuwar da nake so , zan bata labarin ki , kuma ince kina mata gori itama ta goranta miki tunda dai uba baifi uba , sa'arki ɗaya ma da mamanki ta haɗo da momy ai da ina ganinki sai nayi amai...

Goge maganar tayi dai tare da nunawa Dikko ya bata haƙƙinta , shareta yayi ya shige toilet, bai daɗe ba ya fito da alama alwallah yayo , itama shiga tayi tayo alwallah ya gabatar da komai kamar yadda yayi a daren farkonsu da Sadiya cikin natsuwa , bayan sun gama suka koma gado anan Dikko ya farke sabuwar amaryarshi kuma ya sameta a cikakkiyar budurwarta ,

Yayi farin ciki dan a tunaninshi yadda take ta nuna haɗama tana zalama baiyi tunanin zai sameta a cikakkiyar mace ba , komai yaji gaskiya amma Dikko yace gishiri yayi yawwa , { tasha kayan mata sosai } dan shi Allah ya bashi ilimin gane tsurun mace idan ta haɗa da "yan dubaru ya sani , amma wallahi An mata itadai ta dabance...

Sai kukan kissa matar Dikko keyi , cikin nuna tasha wahala , Dikko kuwa ɗan jirgiwa yayi ya kifar da kanshi saman katifa tunanin yadda darenshi ya kasance da Sultana yakeyi , wallahi ya cuci budurcin An mata daya karɓa ta ƙarfi da yaji , ƙaramar yarinya da ƙananan shekaru ya saki ƙarfinshi ya haɗa da magunguna yaje mata a gigice , bata taɓa gani ba kuma bata taɓa ji ba sai a gareshi , me yasa ....?

Me yasa? Me yasa haka ta faru ? Dole kice bakyasan Dikko saboda Dikko ya zama mugu a wurinki , An mata da kinyi haƙuri kin bani dama a karo na biyu da kinyi alfahari dani , da bazan barki kiyi kuka ba , bazan barki kiyi baƙin ciki ba , shi kenan kin fita a hannuna zaki tafi wurin mai rabo ya ɗaukeki ya dasa wasan sa daga inda na tsaya...

A hankali ya lumshe kyawawan idonuwanshi a bayyane yace Allah ya sanyaya miki zuciyarki , a tunaninta da ita ake tace amin mijina , har yanzu idonshi a rufe yace kin yafemin kenan ? Ummm ai bakamin komai ba ma , kenan babu

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment