Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baici ba shege munafikin Allah ɗayan mazinaci ya ɓoye ya saɓawa Allah amma a idon al'ummar gari suna masa kallon mutumin arziƙi bayan ni nasan mazinacin ne kuma shima yasan yayi zinar , hawaye ya cika min ido nace Allah ka kwace kujerar mulki a hannun Dikko babu mulki ma a hannunshi ya wulaƙanta al'umma inaga ya samu,

Wani naji yana cewa yo ai wallahi yaron nan tsaron da zai samu ko gwamna baya samun irinshi kai kana wasa da kujerar kaza , mutumin ya faɗi sunan kujerar da Dikko ya samu nidai bansan ko miye yace ba kuma wallahi bana iya maimaitawa ,

Wani daban naji yace ai naji ance har gwamnan jigawa ya bashi ɗiyarshi , Eh ai mutane basu abu dan Allah Dikkon ne wallahi dole sai ka bashi ɗiyarka ga ilimi gashi ya fito tsatson mutanen kirki ga kyau ga ilimin addini ga ilimin boko Dikko ga kuɗi ga mulki Allah dai yasa muna da rabo duniya da lahira , wani yace kai saidai mu tara lahirar amma a duniya su Dikko duk sun tare komai...

Tsoki nayi tare da juyawa na koma cikin gida ina tsinewa Dikko albarka wallahi idan dai ina da rayuwa ba tsaro ba ko tsoro yake tsare Dikko saina ci mutuncishi kamar yadda na ɗau alƙawari ,

Tunda na shigo ɗaki damuwa ta dameni na rasa inda zan saka raina naji sanyi wuri na samu na zauna a ƙasa na jingina da bango tunanin ta inda zan hudowa lamarin Dikko na farayi nasan ba lallai bane ya sake shigowa anguwarmu ba saidai ya bada umarni a duba dokuna kila ma yanzu babu wani ruwanshi da labarin doki Sultana kuma yasha banza kenan...

Murmushi Dikko yayi a dai² wannaan lokaci sannan ya kalli Al ' Ameen yace bansha ba , ruwa ne aka ajiye shine Al ' Ameen yayi tunanin ya gama zai ɗauke Dikko yace baisha ba , fita Al ' Ameen in yayi Dikko ya kalli hoton Sultana a wayarshi sannan yace ki daina tunani kona manta dake daren daɗewa Dikko baza taɓa mantawa dake ba , kina da matsayi na daban a rayuwata dalilin abu ɗaya yasa nake ɗaga miki kuma bazan daina ganin mutunci ba har abadan duniya zanzo bada daɗewa ba ki ƙara haƙuri kuma ki zama mai yafiya banda yadda zanyi dake haka kema baki da yadda zakiyi da Dikko , ina cikin farin ciki a yau dan haka kema kiyi farin ciki a daren nan An mata....

Wallahi bazanyi ba , ni kuma Amisty ke tambayana abinda ke damuna nace mata babu dan ba wadda yasan abinda ke tsakani na da Dikko ban taɓa bawa kowa labari ba zuciyata da rayuwata kaɗai suka san wannan sirri , Amisty tace tou kiyi shiru kallon Amisty nayi tare da cewa yanzu na fara kuka kuma bansan ranar da zan daina ba , inaji a jikina baƙin ciki da ƙunci na rayuwa banma saka hannu ba zan haɗu da wani gagarumin tashin hankali da bansan ranar zuwanshi ba , zan rasa wani abu mai mahimmaci a rayuwata zan zama abin tausayi da kwantacci wata rana na ƙarasa maganar ina murmushi....

Simi ² Amisty ta miƙe dan a tunaninta na samu warwarewar tunani , a wurin na kwanta naci gaba da kuka har bacci ya ɗaukeni ,

Yauma Amisty saida ta shirya sihirinta ta tunkari gidan Asma'u , cikin farin ciki Asma'u ta tari Amisty tana maijin daɗin zuwanta , yauma ice cream aka bata ta lashe kamar wata mayya , idan babu kwaɗayi ba wahala,

Babana zaune a gaban malamin shi , yace a zana masa ƙasa a duba masa halin da uwar masu gida take ciki ? Waya ɓata min waya faranta min ? Ina cikin farin ciki ko ina cikin damuwa ? Akwai wani dake harina kuwa ? ......






05/09/2019





*MEELAT MUSA CE...* 🧚🏻‍♀


⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 27


Gyatsa malam yayi sannan ya ɗauko wuri ya feshe da turare irin nasu na matsubbata , a saman farin ƙyalle ya watsa wuri in suka watse ko wanne bai haɗu da ɗan uwansa ba sai guda biyu suka haɗe a wuri ɗaya...

Kallon Babana malam yayi sannan yace waye wannan yake tare da ita ? Baba yace Allah ya gyara aikin malam aikai zaka warware mana komai wannan ɗin shine yake tare da ita uwar masu gida kenan ko ?

Girgiza kai malam yayi tare da cewa bana tunanin wani namiji zai sake shiga rayuwar Maryam saidai mu bincika muga waye wannan ! Cikin damuwa Babana yace aiko idan bai fita harkar uwar masu gida ta salama ba zai fita da ƙarfin bala'e ko waye ,

Iyakar bincike malam yayi amma ya kasa gano ko waye yake tare da Sultana , an buga ƙasar an zana an goge an sake rubutawa amma abinda binciken ya nuna wai a kulle yake , wai prvt istihara jama'a kun taɓa ji ?

Hankalin Babana ya tashi yace malam babu abinda ya gagareka ,{ kai jama'a saboda an taɓo ɗiyarshi harya manta da Allah yana iƙirari wai babu abinda ya gagari malam } duba min miye kuɗirinshi akanta malam !

Bincike malam yayi sannan ya ɗago ya kalli Babana yace kaga ka fita harkar rabata da ko waye wannan domin duk wanda akazo istihara aka kasa kamashi shirin duniyarshi ba ƙarami bane gaskiya , wannan yayi zarra kuma yasha gaban duk wani mai tada mishi ƙura abinda yasa nace haka idan har kace zakayi wani sihiri akanshi wallahi zaka lalace...

Babana yace lalacewa kuma na nawa ? Aiko asiri zaka ma mutum idan kaga yana caca kawai ka barshi , tou Binna ba'a caca kaɗai ya tsaya ba ga caca ga neman mata idan akwai lalacewa wacce tafi wannan akan uwar masu gida na yadda zanyi wallahi !

Ƙara duƙufa malam yayi zuwa wani lokaci ya fara magana ba tare daya ɗago ba yace Aliyu wannan mutumin da muke magana yana gaf da Maryam kuma yana zuwa wurinta babu jimawa zaizo da farin ciki amma zai koma da ita yana mai baƙin ciki , abinda zai kawoshi da abinda zaisa ya tafi da ita duk ban gani ba amma tabbas zai tafi da ita kuma zata ɗauki tsawon shekaru babu wanda zaiji labarinta ,

Cikin tashin hankali Babana yace ina zai kaimin ɗiyata ? Malam yace ina zai kaita nima ban sani ba amma tafiya babu makawa , waye shi ? Malam yace sanin ko waye shi da ƙudirinshi duk sai mu jira zuwanshi , cikin ɗimaucewa Babana yace kafin yazo ina tare da "ya ta ina nan ina jiran zuwanka a gabana ka taɓa uwar masu gida saina gana maka azaba mafi girman azaba a duniya , ka fara lissafi daga yanzu kwanakin mutuwarka na tunkaro ka muddin ka tunkaro rayuwar ɗiyata kazo ina jiranka....... Ya ƙarasa maganar jikinshi yana wata irin kyarma idanuwanshi jajir kamar an watsa mishi yaji sai zufa yakeyi kamar wadda maciji ya sara....

Malam ya tausayawa Babana dan haka yaci gaba da bincike amma Allah ya ɓoye mutumin da zai shigo rayuwata , cikin tausayawa yace Aliyu kayi haƙuri tunda nake dakai baka taɓa nema baka samu ba sai wannan , kai kanka kasan iskancin da Maryam ta taro ba ƙarami bane banda muka dage akanta da yanzu bata taruwa a garin nan sanin kanka ne ,

Da sauri Babana ya rufe idonshi dan duk duniya ya tsani a danganani da kalmar iskanci , laya malam ya miƙowa Babana yace gata nan kaje ka samu jaririyar mage sabuwar haihuwa wacce dai bata buɗe ido ba , tou a yage bakinta a saka wannan layar sannan a kashe magen a jefar da ita a tsohuwar rijiya , bazan maka bayanin komai ba zaka zo ka bani labari yadda Maryam zata watsar da kowa da komai ta dawo gareka...

Hahaha Babana yayi dariya irin ta basawa tare da cewa godiya nake malam uwar masu gida zata dawo gareni , zata manta da duk wani abun daya faru a baya ta dawo nutsatsitsiyar ta kamar baya , godiya Babana yayi sannan ya tashi ya tafi....

Baccin dai babu daɗi dan ko da nayi bacci ɗaya farkawa nayi daga nan na shiga tunanin rayuwa da tunanin mutuwana wacce zata iya riska na kai tsaye ba tare dana shirya ba , ina ƙoƙarin koyawa zuciya tsoron Allah na canja halayya amma sam sai zuciyata ta karɓi huɗubar sheɗan cewa yarinya dake ? Duka shekarunki nawa a duniya ? 17 zuwa 18 ne ai mutuwa ma baza ta wani zo wurinki ba ki dage kawai ki more talatarki kafin larabarki ta riske ki....

Karki kuskura ki bar bariki ba tare da kin kafa tarihi ba , ki zuge rayuwarki kaf wata rana zata tofo domin rayuwa ita da zogala basu da wani banbanci kinga dai zogala kullum cikin zugeshi akeyi amma kafin wani lokaci ya sake fitowa , mafita ɗaya ce su Amisty kawai zaki kora sai ki shiga cikin ahalin Baba ki sake haɗo wata daba , yess 🤷🏻‍♀ dama Baba ƙarami yacemin karuwa zan koyawa "yar sa karuwancin idan an tashi kwatance a cikin ahalimu za'ace karuwai biyu idan har na bari na zama karuwa ni ɗaya gori bai ƙare ba har ɗiyan ɗiyana amma idan na taɓo wasu a ciki shiru zakuji ustaz ya samu mace...

Da safe bayan na gama duk abinda nakeyi wanka nayi na shirya cikin riga da zani na atamfa nayi ƙofar gida , dukansu a saman dakali na samesu zaune hada Amisty sallama nayi musu sannan na samu wuri na zauna , a cikinsu babu wadda yaimin magana kuma babu wadda ya ansa min sallama , sukaci gaba da labarinsu ,

Ban damu ba domin dama su ba ma'abota ansa sallama bane ba , cikin girmamawa Amisty ta taso tazo gabana ta durƙusa da wainar filawa an daka mata tashshi mai shegen daɗin ga tumatur da albasa tasha kallo ɗaya nayi ma wainar yawu na ya tsinke , Amisty tace ga abinda kike so nayo miki mother ,

Cikin farin ciki na ansa tare da fara kwararawa Amisty godiya sannan nabi kowa nace yaci , murmushi Amisty tayi tare da cewa ai kowa yaci taki ce ke ɗaya uwar gidan kwarata , jinjina kai nayi tare da miƙawa Amisty nace tou kici kema , no nikam bana ci kinsan waina bai wani dameni haka ba , miƙewa nayi tare da cewa ai wannan shagalin sai an rufe ƙofa ,

Dariya sukayi gaba ɗayansu tare da cewa sai kace dai kin samu mijin zalifa ? Nima dariyar nayi ba tare da shigewa ciki , umm waini za'a cuta da gwangwanin fulawa ɗaya tashshi naira talatin da manjan naira hamsin , Amisty kenan idan har bakisan halina ba har yanzu lallai babu ranar da zaki gane wace ce Sultana...

Ina shiga cikin gida ɗakina na shiga na kwashe wainar na zuba a leda bayan na gama na fito na zubar a bola , ɗaki na koma naci gaba da danƙarar tashshina saida na haɗa zufa na tabbatar bakina ya kama tashshi sosai sannan na fito ƙofar gida da tissue ina goge majina ,

A gaban Amisty na ajiye flet in tare da ƙara fyace majina idona yayi jajir sannan na zauna kusa da Amisty , murmushin mugunta tayi tare da lasar bakinta kamar mayyar da ta daɗe batayi kamu ba , nima murmushin nayi tare da kallon Amisty nace ɗan matsa daga gefe kar ayi abun kunya bisa titi !

Kallon su Hafsa tayi tare da ɗaga musu gira alamar tayi nasara, ɗan cije leɓona na ƙasa nayi tare da ƙanƙance idona na dama , kallona Amisty tayi sannan tace wane irin abun kunya za'ayi ne ? Murmushi nayi tare da cewa ji nake kamar in lashe ki , na nuna lashewar da harshena sannan na haɗe haƙorana na gaba sukayi ƙara ƙass.

Uhum kwarata kenan gaba ɗayansu sukayo kaina kamar an watso mutane a doka daji , yadda namun daji ke kawo hari kowa ya ɗauka karya rasa , murmushi nayi tare da ajiye hannuwana ta baya na jigina dasu ina kallonsu , Hafsa tace uwar room ya kikeji ne ? Rufe idanuwana nayi tare da girgiza kaina sannan nace ai bama zan iya musultawa ba ,

Nana ta riƙo ƙuguna tana kallona bayan wani lokaci tace ɗan daure ki misilta mana yadda kikeji ! Har yanzu idanuwana a rufe yake nace misali kece aka rufe a ɗaki kwana biyu babu ci babu sha idan aka fito dake kika ga abinci wane irin ci zaki masa ?

Amisty tace ai ƙalu bale ga duk abincin dana damƙa , buɗe idona nayi sannan nace tou idan aka ajiye miki farfesun kaji sai aka kawo miki kwaɗon ganzo ko garin kwaki a ciki wane zaki ci ? Hafsa tace ai kowama kazar zaici , dariya nayi tare da cewa me yasa zaki ci kaza kibar ƙanzo ? Amisty tace saboda itace tafi daɗi da amfani a rayuwata ,

Gyara zama na nayi nace to idan kika samu namiji kika samu mace a ciki wannen zaki ɗauka wane zaki bari ne ? Amisty tace ai mace ba'a haɗata da kowa domin ita tafi kaza daɗi ke wane zaki ɗauka wane zaki bari ? Ta ƙarasa maganar da tambayana....

Gyara bakina nayi tare da cewa gaskiya dani namiji amma yanzu mace nake so nima , age agegege..... Kunji wani sabon taken iskanci wai agege , gaba ɗayansu suka faɗi age agege ,

Saida na gama kallesu tsaf sannan nace amma ina da sharaɗi fa ! Amisty tace faɗi sharaɗinki mother , yawwa idan dai zan faɗa harkar lesbian gaskiya sai kun bani haɗin kai na tsaya saman ƙafafuwana mun kora duk wani namijin bariki ta hanyar tambayarshi abinda yake bashi sha'awa a bariki , ta haka zamu gano inda matsalar take zamuyi gyara domin ceto matan auren da suka rasa mazajensu , domin gaskiya bana iya haɗa bariki da harkar mata ,

Shiru sukayi suna kallon junansu , nima ban sake magana ba ina saurarensu abinda zasu ce , Hafsa tace meya shafi harkarki da rashin kula namiji kuma ? Salon nawa ne a haka gaskiya dan idan baku manta ba yanzu maza nake bana mata , amma tunda zan ajiye maza na ɗauki mata dole saina fitar da maza a rayuwata ....

Da ido sukayi magana sannan sukace har zuwa yaushe zamuyi aikin ne ? Na sati ɗaya ne , na basu amsa , tou munji mun yadda suka amsa gaba ɗayansu , jinjina kai nayi alamar na gamsu , Hafsa tayo ta kusa da fuskata da wani banza bakinta zata sunbaceni , murmushi nayi tare da tare bakin ta da ɗan yatsa na nace yi haƙuri hajiyata lokacin naku bai fara ba ,

A hankali taja baya , murmushi nayi a zuciyata tare da cewa Mother ta ibi ruwa ta jefa guga duk wanda yai wannan yazo da zamba , ko akan wannan zasu ɗau misalai , domin Sultana tayi naɗi da lauje , "yar birni tayi nitso da ƙoƙo gani naci banza zan zare adda , kowa yayi ƙuri sai yayi muzu a ƙarshe mu zuba dani daku...

A ƙofar gida muka yini dukanmu amma ni ina tashi naje nayi sallah idan lokaci yayi kuma dana gama nake dawowa domin duk iskanci su Amisty a saman tafin hannuna yake , duk wani barbaɗe² ankare nake dasu domin suna sakin layi cikin magarnarsu , ni banci ɗiyar kowa ba uwata batayi ba babu wanda ya isa yayi akaina kallon biri sukemin ina musu kallon ayaba zasusha mamaki ranar da film in ya ƙare....

Da daddare , kamar yadda ƙofar gidan ya saba a ko wane dare haka ya fara ɗaukar harami motoci suka fara layi ƙamin yadda suka saba , kamar yadda muka saba muma a ko wane dare haka muka fito ina gaba su Amisty suna biye dani a baya , dan yau a gida zata kwana tunda mijin Asma'u gidanta yake yau...

Wani zafaffen Alaji ne yace Allah ya taimaki uwar gidanmu , harna wuce nayo baya dan haka aka ajiye min kujera na zauna suka koma bayana dukansu suka tsaya kamar yadda suka saba , gaisawa mukayi na tambayeshi iyali ? Lafiya qalau yace tare da ɗan maida idonshi ga waya , murmushi nayi tare da cewa Alhaji wai matanka nawa ne ?

Shiru yayi baiyi magana ba yaci gaba da kallon wayarshi , Alaji na sake kiran sunanshi , miƙomin wayar yayi tare da cewa ko kema zaki kalla ne ? A face buk sai maganarshi akeyi Allah dai yasa kar bakin duniya ya kashe shi mutane suke tayin posting hotunanshi suna tayashi murna...

Ya faɗi maganar tare da miƙomin wayar , ƙin ansa nayi Hafsa itace ta ansa bayan wani lokaci tace Alhaji ya naga ana haɗashi da wata mai siffar maguna , dariya sukayi gaba ɗayansu Amisty tace ke kuma mai siffar kisau , duk kallo sukayi dukansu A ` i tace aiko wannan mai kyau ce gaskiya kedai kawai kice kinajin kishi ,

Alhaji yace ai itace zai aure ɗiyan gwamnan jigawa ce , sai yanzu na gane ko hoton waye ake kallo , Amisty tace yaushe za'ayi bikin ne ? Alhaji yace ƙarshen watan nan shi gwamnan keta sauri dan yaga Dikkon so yake ya zuƙe dandai suna da zuminci amma da bana tunanin za'ayi auren nan gaskiya...

Miƙomin wayar Amisty tayi tare da cewa kalli mutuminki zaiyi aure , tsoki nayi tare da cewa ta ina ya zama mutumi na kuma ? Hafsa tace wanda kukayi faɗa asibiti wai mother mema ya haɗaku dan a lokacin naga kuna abu cikin gayya² dadai gani akwai azazza a tsakaniku.

Murmushin ƙarfin hali nayi tare da ansar wayar amma banba Hafsa amsa ba , kallon hoton nayi yayin da wani hadarin baƙin ciki ya taso min , tsoki nayi tare da cewa Hafsa siffar me gareta kika ce ? Hafsa da baƙin ciki ke gurgurawar zuciya tace shegiya tsinanniya mai siffar karnuka ai in Allah ya yadda wannan auren babu ubanda zaiyi shi ,

Kawai dai haka nan nakejin babu daɗi a raina , zuciyata kuma tana kwaɗayin ƙara kallon hoton Dikko , amma na hanata tare da cewa kwantar da hankali keda zakici mutuncishi saurin me kike bayan lokaci ya kusa....

Maida hankali na nayi wurin Alhaji tare da cewa Alhaji matarka nawa ne wai ? Mata ta ɗaya mene ne wai ? Ba komai na bashi amsa tare da cewa tou me yaja ra'ayinka na faɗowa matan bariki haka rana kwatsam ? Kallona yayi cikin ɓacin rai yace me yasa kikemin irin wannan maganar da Allah ? Nima kallonshi nayi ido cikin ido sannan nace haka tsarinmu ya koma dole duk wani namijin dake cikin barikin nan saiya faɗa mana abinda ya kawoshi bariki , idan ya faɗa mu kuma sai mu bashi tsula²n mata ya more daga garesu saboda munyi oder manyan mata daga jahohi da dama , haka tantancewa mukeyi mu gano namijin da ya kamata muje dashi a cikin wannan tafiya tamu mai taken bariki ta giga.....





07/09/2019




Taku a kullum ... 👇🏻


*JAMEELA MUSA...* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 28


Kallo Alhaji ya bini dashi mai nuni da yama rasa abinda zaicemin , murmushi nayi tare da cewa da Allah kar kaga kamar cin fuska ne ko wani abu ko zaka taimakamin naga hoton matar ka ?

Me yasa kike son ganin hoton matana ko zakije ki haɗamu da ita ne ? Ya ƙarasa maganar cikin sigar barkwanci , murmusawa nayi tare da cewa haba Alaji yadda da arne shi yake sa aci yankashi , kuma daɗin aure kesa mata tace miji Baba... Ganin hoton iyalinka bashi ne yake nuni zan faɗa ba , nasan gidanka komai da komai naka na sani hoto kawai zan gani sai nayi gaba abuna...

Amma kafin na tafi don Allah me yaja ra'ayinka ka afkowa matan bariki bayan ka baro naka matar gida ? Ɗaure fuska yayi tare da cewa me yasa kike so kimin haka wai ? Dani dake da ku dukanku taimakekeniyar juna mukeyi manta da lamarin matana da kuma abinda yasa na faɗo barikinku mu fuskanci abinda ke gabanmu !

Miƙomin wayar yayi da hoton zuƙeƙiyar matarshi wacce ta gaji da haɗuwa duk inda ake neman mace takai kuma duk inda ya nuna matanshi abun kallawa ce , gaba ɗaya tafi su Amisty komai na morewa amma bata kai diddigen Sultana ba , danni a tara mace dubu baza'a iya samo ɗaya kamarni ba ,

Caf na faɗa tare da kallon Alhaji sannan nace wannan kyakkyawa ya akayi ka baro kyau siga da nagarta ka faɗowa kwarin mata ? Me matan bariki suka fi matar ka ? Me yasa ka kashe sunna kake ƙoƙorin ɗabbaƙa zunubi ? Me yasa kabaro inuwa ka dawo rana ? Ya akayi kabar rahama ka dawo azaba ? Me matan bariki sukafi matar ka don Allah ? Me ya ɗaukar maka hankali da macen bariki har ka baro taka kazo wurinmu....... ?

Kallo Alhaji ya bini dashi na kece abun tausayi mai ƙaramar shekaru dake kina ɗaukar kayan daya fi ƙarfinki , kamar nasan abinda ke zuciyarshi nace manta dani ka fuskanci taka rayuwar , nasan matsayin zina , illolinta matsalolinta wahalhalunta tashin hankalin dake cikinta da kuma bala'en dake tare da ita , san zuciya da ɗaukar huɗubar shaiɗan ya mantar dani , domin yawan kusantar saɓo yana hana ganin

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment