Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba ya fara da ganin dokuna, jiya da aka fidda dawakunan doki ɗaya ya kare a ƙafa shine ya fara da ganinshi kafin ya wuce.

D --- K ne ya fito daga cikin palon yana magana daga ganin yanayin maganar shi faɗa yakeyi, saida ya fito tsakar gidan sannan ya riƙe ƙugunshi da duka hannuwan shi biyu yaci gaba da magana amma bana iya jiyo abinda suke cewa saboda tazarar dake tsakaninmu.

Zubinsu da yawansu ya bani tsoro gasu ƙosasshi, inda Dikko yake tsaye na kalla, gaskiya Dikko ɗan gayu ne wankakken namiji yasha wanka ya ƙoshi tsaftatacce dashi ya cika ya fito cikakken namiji har wani gemun rainin hankali ya ajiye kamu ɗaya gaskiya duk da bana ƙaunar shi jarumin namiji ne duk inda mace take san namiji Dikko yakai tsakani da Allah zan faɗi gaskiya, domin Allah Dikko yana da kyau mai burgewa da ɗaukar hankali , sauke hannunshi ɗaya yayi daga riƙon da yayi mishi ya saka a aljihu ya ciro ibadar tashi, ya ciro cingom in daga cikin takardar shi ya jefa a bakinshi sannan suka fara taho wurin motocinsu...

Murmushi nayi kaɗan yayin da wani sashe na zuciyata yake cewa kira sunanshi idan ya juyo ki caccakawa uwarshi zagi komai zai faru ya faru idan ma ta tafasa ta ƙone, yayin da wani sashe na kwalwata yake bani shawara cewa duk abinda zakiyi kisa nazari da lissafi kiyi ma takonki linzami mai kyau duk daren daɗewa Dikko sai kinci ubanshi.

Zuciyata tace kiyi masa magana dan ya tunaki kuma yasan kina nan kuma ki faɗa masa cewa zaki ci ubanshi idan babu yau akwai wata rana....

Sallama nayi da matashin daya faɗa min Dikko ne yazo sannan na wuce ciki, a lokacin dana isa wurinsu tuni D --- K ya zauna cikin mota ana ƙoƙarin rufe masa mota na riƙe murfin motar ,

Kowa kallo wurin hannun daya riƙe murfin mota yayi dan ganewa idonsa ɗan rainin hankali daya isa yayi wannan iskancin, kwantar da kaina nayi saman murfin motar cikin tausasashshiyar murya nace Dikko, kallo na yayi tare da cewa na'am ya tsareni da idanuwa, shiru na wani lokaci ya ratsa wurin bai daina kallona ba kuma nima ban daina kallonshi ba haka kuma babu wanda yayi mana magana...

Nice na fara cire idona daga kanshi dan idan har ina kallonshi tou lallai babu abinda zai hana in burma mishi wuƙa, kaina yana kallon ƙasa nace ka kuwa gane ni ? Na ƙarasa maganar tare da ɗago fuskata amma ban sake kallon idonshi ba...

Cikin ɓacin rai yace Al ' Ameen mtsww muje ya faɗi maganar tare da jan murmufin motar da ƙarfi ya rufe, zuciya bata da ƙashi ganin Dikko zai maidani sakara yasa na dunkule hannuna na kaiwa gilashin motar duka saida ya tarwatse , jini kuwa yace gashi nan zuwa...

Duk da haka Dikko baiyi niyar tsayawa ba saida nace kai ƙaramin ɗan iska yau itace rana ta ƙarshe a gareka kamar yanda na dasa lissafin kwanaki mutuwarka , idan har kayi nasarar guduwa ina nan tafe gareka sai ka ɗanɗani azaba kwatankwacin irin wacce ka ganamin baka da aiki sai cin cingom kamar wata karuwa sakaran banza daƙiƙi ɗan gidan matsiy......

Wanda aka kira da Al " Ameen shine ya ɗaga hannunshi da niyar kwarara min mari Dikko ya riƙe hannunshi tare dayin murmushin mugunta yace waye yace maka irinsu ake duka ? Tsaya daga gefe kaga maganin ta, Allah ɗaya nake tsoro amma yau dasai nayi mata allurar natsuwa, amma ka barta nayau zan mata kaɗai idan na sake ganinta tou nasan abinda take buƙata, Al ' Ameen yace mai gida ka sakeni in koya mata hankali, murmushin mugunta Dikko yayi tare da cewa bari in bata abinda ta roƙa...

Sakin hannun Al ' Ameen yayi sannan ya matso kusa dani, ɗan kauda kanshi yayi gefe kamar yana nazari fuska a ɗaure ya juyo ya kalleni ni juyowar da yayi gaba ɗaya wurin kowa ya juya baya, hannuwana ya haɗa duka biyun ya maidasu ta baya ya riƙe, hannu ɗayan kuma ya riƙe fuskata, ƙasa ƙasa yayi magana cewa.

Naga dai kina san cingom in nan kinsan kwanaki da muka haɗu ban "yan maki shi ba, kuma sai kiyi ta abu babu kawaici a gaban jama'a sai kiyi ta wani zalamar Dikko kuma ko an baki ni nayi miki yawa ba inda zaki je dani dan ruwa ba sa'ar kwando bane, kina da daraja ɗaya a wurina kuma albarkacinta kike ci amma wallahi dasai na nuna miki ni tantirin ɗan iska ne, darajar tasa kawai bazan wulaƙanta ki ba, amma idan kina neman rainin hankali da tsantsagwaron rashin mutunci daga kaina an rufe littafi.

Tattaunawa yayi cingom in cikin salon jan hankali saida ya busa cingom in yanda ake cewa kwai, sannan ya kalleni da wani iri salo sai kuma yayi murmushi da gefen bakinshi, hannun daya riƙe min fuska ya ciro cingom in sannan ya tura minshi cikin bakina, tuf tuff na fara tofar da cingom in , murmushi yayi tare da rufemin baki yace ai ƙarya kikeyi sai kinci....

Iya ƙoƙari nayi na tofar yaƙi fita ga kuma ya riƙe min hannuwa duka, daidai saitin maƙoshi na yayi min wani duka wanda yasa dole saida na haɗi cingom in, dariya yayi sannan ya sakeni tare da turani baya yace sai mun sake haɗewa an mata....

Tangal tangal na tafi kamar zan faɗi su kuma suka shige motocinsu suka tafi aka barni a filin tsakar wurin daga ni sai Alhaji, dakel na iya haɗiye yawun bakina saboda azaba da raɗaɗin da maƙoshina yakemin saboda nushin da yayi min.

Kallon hannu na nayi da jini yake ta ɗiga sannan na kalli Alhaji nace kaini asibiti, cikin damuwa yace muje, dani dashi muka nufi wurin motarshi muka shiga gaba ɗayanmu muka nufi asibiti,

Muna zuwa babu wani daɗewa akamin diresin , bayan an bincike hannun kaf ko akwai wani gilashin a ciki, magunguna aka bani sai kuma allurai da akayi min duk Alhaji ne ya biya kuɗin bayan an gama komai ya ɗaukeni muka tafi gida !

A ƙofar gida yayi parking duk muna cikin mota daga ni harshi, shiru mukayi na wani lokaci sannan Alhaji yace hajiya dan girman Allah ki goge wannan vidio dan darajar manzan Allah S. A. W, ki taimaki rayuwata ki goge don Allah, badan halina ba,

Ajiyar zuciya nayi sannan nace tou nima ka taimakeni dan darajar manzan Allah S. A. W dani dakai duk mu taimaki juna daga yau nayi maka alƙawari zan goge vidio sannan kuma zan fita rayuwarka babu dawowa...

Tattaro hankalinshi yayi wurina sannan yace faɗamin me kike so idan har ina da hali zan miki ! Ba tare dana kalleshi ba nace mota kawai zaka bani daga ita na rantse maka da Allah na fita sha'anin ka vidiwo kuma zan goge...

Goge zufa Alhaji yayi sannan yace wace iri kike so ne ? Ni bansan mota ba amma dai mai kyau nake so, kallon motarshi yayi sannan yace kina san wannan ? Ba tare da ɓata lokaci ba nace Eh tamin kuma ina santa,

Alhaji yace tou na baki ita, kina da wurin ajiyarta ne ? Yanzu ma zan ajiye miki ita insa azo a tafi dani amma ki goge hotunan nan dan Allah, karka damu zan goge wallahi, a , a nidai ki goge a gabana don Allah, tunda nace zan goge ai zan goge, Alhaji yace tou bayan wannan sai me ?

Abu na gaba ina so ka faɗamin waye Dikko ? Miye asalinshi waye babanshi a garin nan ? Wane irin matsayi gareshi kuma wane dalili ne yasa yake ɗagawa ta rayuwa ina san ka faɗamin asalin Dikko da kuma tarihin rayuwarshi.....

Gyara zama Alhaji yayi sannan yace fara bani mazaunin motarki na ajiye ki goge vidio sannan sai muyi magana kinga lokacin ina cikin natsuwa, ba damuwa na faɗa tare da buɗe mota na fita na shiga cikin gida !:',



Kuyi haƙuri don Allah yau ina can gidan uwar ɗakina nima inacin shagali da miyar mutunci, wurin uwar ɗakina wato *RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE* ina alfahari dake uwar ɗaki ɗaya tamkar da dubu banda kamarki kuma kina da matsayi na musamma a zuciyar *MEELAT MUSA*.....




24/08/2019



*JAMILA MUSA CE...*

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 18



*_KOMAI DADIN DUNIYA KIYAMA TA FISHI , daga alƙalamin Ummerherny Nerserllerh idan kika bari aka barki baya bazan baki labarin wannan ƙayataccen labari ba wanda ya fito daga alƙalamin haziƙar marubuciyar zamani, Allah ya taimaka surukuta yasa a kammala lafiya amin..._*


Ina shiga gidan ko sallama banyi ba yaro ya shigo da saurinshi wai ance Sultana tazo Alhaji yana kiranta , Nana ta fara miya sameki naga hannunki a ɗaure ... ? Duk hankalin su A ` i ya tashi sunga uwar ɗakin kwarata hannu da ɗamara, murmushi nayi tare da cewa yawwa A ` i da Allah inda zan ajiye mota nake so nayi maganar dan kauda tambayar abinda yaji min ciwo, Hafsa tace ina motar take ne ?

Ba tare dana kalleta ba nace tana waje, dan haushin Dikko ya fara shafar Hafsa saboda soyayyar da take mishi bana san Dikko haka kuma bana soyayya wa duk wanda yake ƙaunar Dikko, Hafsa tace sai in ajiye miki a gidanmu, ban bata amsa ba nabi yaron muka koma waje...

Motoci biyu na gani a ƙofar gida , wurin motar Alhaji na tsaya daidai saitinshi sannan nace gani, wani wuri ya buɗe ya tattaro wasu takaddu ya bani ansa nayi naɗan basar ina kallo a zahirance karatunsu nakeyi amma wallahi a baɗinance bansan ko na miye ba...

Fitowa yayi daga cikin motar ya bani makullin tare da cewa ga motar nan zanje mai gida yake kirana dana gama zan dawo insha Allah amma ki rufamin asiri Sultana ki goge vidion nan don Allah, wallahi karkaji komai Alhaji zan goge amma kaɗan bani na kati plz, yace ina zuwa bara in gama tattara tarkacena a motar nan...

Komai nashi ya kwashe a mota ya zuba cikin motar dana gani, bayan ya gama ya ciro wayarshi yace kalli ki gani, kallon wayar nayi yace kinga na goge nawa ko ? Nace Eh nima zan goge insha Allah, godiya yayi sannan ya bani kuɗi amma basu da yawa yace idan ya dawo anjima insha Allah zai bani tukuicin goge vidio, godiya nayi masa sannan mukayi sallama ya shiga mota tare da cewa karfa kiyi wasa da takardun motar nan ki adana su kinji ko ? Sai yanzu na gane abinda takardun suke nufi godiya nayi masa suka wuce ni kuma na koma gida...

Ina shiga gida Hafsa na ba makullin nace kije ki ajiyemin zan ɗauko ta ƙarshen satin nan insha Allah, ansar mukulin tayi taci gaba da maganar ta, kallonta nayi sannan nace saurara kiji, kije ki ajiyemin mota ki dawo, tashi tayi ita dasu Saude suka tafi ni kuma na shiga ɗakina, ban daɗe da shiga ba Nana ta shigo tare da bani number matar Bello amma bata samo na ɗanshi ba , ansa nayi da nayi niyar bata 500 sai wata zuciyar tace kawai in bata 1k in ka nema ma ka samu ai arziƙi ne...

Jakata na buɗe na bata 1k nayi godiya, itama godiya tamin ta fice a ɗakin, tana fita na kulle ƙofa na kwanta saman katifa na fashe da kuka mara sauti , duk duniya babu wanda ya taɓa wulaƙanta ni kamar Dikko nice zai bawa cingom in bakinshi da yawun bakinshi na haɗe a cikin cikina , duk duniya babu abinda yakai miyau saurin sadar da shaƙuwa, shi yasa masu wayau ko bariki suke basa yadda suna haɗa bakunansu da na wasu, waccan ranar bai haɗa bakinmu ba amma shine yau ya ciro abu daga cikin bakinshi ya bani, yana da wata manufa ta daban shine dalilin da yasa yace ma Al ' Ameen bara suga magani na, wato wannan dalilin ne yasa kowa ya juya mana baya ko ? Saida na goge hawaye na sannan nace ƙarya kakeyi yawun bakin ka bazai taɓa zama hukunci a gareni ba...

Nayi kuka har na gode Allah daga baya kuma bacci ya kwasheni wanda bansa lokacin daya zo ba kuma baiyi shawara dani ba,

Washe gari koda na tashi nayi sallah bacci na koma bayan na gama kwashewa Dikko karama , misalin 09:30am Alhaji yasa aka kirani a waya, bayan na ɗauka nayi sallama dakel Alhaji ya amsamin sallamar cikin nishi yace Sultana ina federal medical center { F M C } saida ya sake yin nishi cikin yanayin wahaltuwa sannan yace ina nan Accident & Emargency kizo yanzu don Allah inasan zanyi magana dake....

Har a zuciyata banji daɗi ba cikin muryar tausayi nace kayi haɗari ne ? Hawaye ya gangaro masa daga cikin idonshi yace kizo dai dan bana tunanin zan ƙara awa ɗaya a cikin duniyar nan....

Subahanalla da Allah ka daina wannan maganar gani nan zuwa insha Allah, cikin rawar jiki na kashe wayata, da sauri na sauko daga saman katifa na zuba ruwa, a gaggauce naje nayo wanka tare da wanko bakina, mai fauda da kwalli kaɗai na shafa, baƙar riga ta jallabiya na saka na yana gyalen a saman kaina na zagoyo dashi har gashin kaina saida ya fito ta ƙasan gyalen jallabiyata, gilashi mai saukin duhu na saka sannan na wanke jikina da turaruka masu sanyi ƙamshi, masha Allah na faɗa a lokacin da naga kaina a cikin madubi, nayi kyau sosai na fito kamar baƙuwar balarabiya a nigeria,

Wayata na ɗauka da jakata, na fito ina tsaye ina kulle ɗaki Hafsa ta shigo, ita ɗaya ce babu abokan nata su Saude, su Nana ma duk basa tsakar gida, ɗan gangarowa tayi da wani irin salon tafiya, ta wutsiyar idona na kalleta sannan na ɗaure fuskata na kallota dukanta a daidai lokacin dana gama rufe ɗakina...

Wow uwar ɗakin karuwai kinyi kyau fa kamar dai ba'a mutu ba, share maganar nayi tare da cewa da mota kika zo ne ? Eh ta faɗa tare da bina da kallon cin wanka , gaba nayi tare da cewa muje ki saukeni f m c biyoni tayi muka fito a tare, a ƙofar gida muka haɗu dasu A ` i hada Amisty da Saudatu....

Amisty tace wurinki zamuje munji shiru har yanzu, kuma mun rubuto takarda an tsara jaddawalin yanda zai ƙawatar ya kuma tafi da hankalin maza gaki kuma zafi fita, buɗe gaban mota nayi na kame sannan nace ku shigo muje kuma, baya suka shiga, Hafsa kuma ta zauna mazaunin tuƙi taja muka tafi....

Saida muka fara tafiya sannan nace karanto min ina saurarenki, Amisty fa tasan komai tasan bana ganewa bana rubutawa kuma bana iya karantawa amma sai tace kidai duba ki gani Sultana, basar da ita nayi tare da miƙa hannuna ta baya na anso takarda ko buɗewa banyi ba na ajiye shegiya ban sake bi ta kanta ba kuma ban sake magana ba har muka isa asibitin...

Wani irin tuƙin ganganci Hafsa tayi tare da sakin sitiyarin saboda taga D --- K , a tare muka iso dasu sai leƙawa take tana kiranshi, wato abinda na fahimta idanma ka nunawa mutum ka damu dashi sai yayi ta ɗagawa, kallon Hafsa nayi tare da cewa ke kuwa baki da aji a haka kike tunanin zan riƙa haɗaki da zafafan mata babu class, raina ya ɓaci sannan nace uban waye Dikko da kike ta hauka kina kiranshi mutane suna kallonki kamar wata zararriya....

A daidai lokacin da muka fito mu dukanmu daga mota shima Dikko ya fito kuma yaji zagin da nayi masa , bai kallemu ba yayi gaba ana take masa baya nima gaba na shiga su Hafsa suka rufomin baya, murmushi Dikko yayi a daidai lokacin da muka tsaya bakin ƙofar ɗakin kowa da muƙarrabenshi a bayanshi, kallona Dikko yayi tare dayin murmushi sannan yace zaki ci ne an mata yayi tambayar tare da ɗaga gira ? Ya ƙarasa maganar tare dayimin wani irin kallo mai tattare da mugunta, yaci gaba da cin cingom inshi cikin salon jan hankali gemunshi yana motsawa a hankali cikin salon ɗaukar hankali , murmushi nayi saboda gaskiya yanayin da yayi ya burgeni, ƙarshen harshenshi ya kawo cingom in yayi wasa dashi a daidai lokacin da aka buɗe mana ƙofa duk muka shiga, daga waje bai sake kallona ba kuma bai sake murmushi ba babu magana har muka isa gaban gadon Alhaji...

Duk matan da muke tare ihu muka farayi saboda tsoron yanayi da Alhaji yake ciki yayin da wasu suka nufi hanyar fita, dani da A ` i aka bari yayin da A ` i ta duƙushe tana kuka ni kuma na cire gilashi na wurgar a gefe na rufe idanuwa na naci gaba da dire dire ina kuka saboda na kasa gaba na kasa baya....

Shi kuma Alhaji burinshi inje wurinshi in taimaki rayuwarshi na goge vidio sai kirana yake cikin dasasshiyar murya da yayi magana sai jini ya kwararo , Dikko yace ya daina magana amma yaƙi saurarenshi Sultana kawai yake kira,

Kusa dashi Dikko ya ɗuka sannan ya tambayashi me zan mishi ne ? Hawaye na zuba a idon Alhaji yace ma Dikko ya rufa mishi asiri ya kawoni wurinshi magana zamuyi ta sirri, Dikko yace faɗamin na faɗa mata kaga ta firgita wani abu zai samunta, cikin wahaltacciyarar murya Alhaji yace kayi min wannan arziƙin na sauran mintunan da suka ragemin a duniya lokacina yana tafiya zan iya mutuwa ko wane lokaci, yanda yayi maganar ne yasa Dikko ya kallo inda nake tsaye ina ta direre kamar anyi ma lafiyayyan diko allurar hauka.

Ɗauke idonshi yayi daga kaina sannan ya kalli zugar daya zo da ita, Al ` Ameen ya faɗa cikin wani irin yanayi kamar bashi ne yayi maganar ba, gaba ɗaya waje suka fita harda A ` i aka fita, inda gilashina yake Dikko yaje ya ɗauko sannan yazo kusa dani, ta gaban rigata ya jawo ya sagala gilashin sannan yace buɗe idonki, jikina yana kyarma na buɗe na kalli Dikko, dakel ya haɗe yawun bakinshi sannan ya tofar da cingom in bakinshi gaba ɗaya yanayin Dikko ya canza ɗaure fuska yayi sosai sannan yace miye tsakaninki da mara lafiyar nan ? Miye dalilinki na zuwa ganinshi ? Me kikaje yi gidanshi ? Kema "yar iska kike so ki zama ko ?

Cikin gatsali nace Ey "yar iska zan zama ina ruwanka da iskanci na ne ? Jinjina kai yayi tare da cewa Allah ya sawaƙe wuce muje yana kiranki, tirjewa nayi tare da juya zan fita da gudu ya riƙoni yace ai ƙarya kike sai kinje, har gaban Alhaji ya jani ya kaini sannan ya zaunar dani saman kujera ya tsaya ta bayana yace gata nan me tayi maka ne ? Ko kaima taci kuɗinka kamar yanda taci na Umar ?

Ɗaga kaina nayi na kallo Dikko ɓacin rai kwance a cikin idonshi zare min idanuwa yayi tare da cewa bari kallona kar fashe miki kwayar ido wallahi, jiki a sanyaye na sauko kaina daga kallon da nake ma Dikko naci gaba da kallon Alhaji ina kuka, dafo kujerar yayi ya duƙo kusa dani sosai saitin kunne na yace na rantse da girman Allah idan na gano akwai wani abu tsakaninki dashi saina kashe ki, ya faɗi maganar tare da shaƙemin wuya sosai na fara ƙoƙarin ƙwalƙwale hannunshi na kasa, tun ina iyawa har nasa wani abu na fara halbe halbe har na faɗo daga saman kujera Dikko bai saki wuyana ba naci gaba da halbe halbe, yanda nake halhalbe ya jawo hankalin mutane suka yo kanmu amma an kasa cire hannun Dikko daga wuyana,

Hayani tayi yawa sosai wanda yasa su Al ` Ameen suka shigo ciki da gudu amma wallahi duk yawan mazan nan suka kasa ɓanɓareni daga hannun Dikko harsai dana suma, riƙe Al ` Ameen yake da hannun Dikko yana cewa don girman Allah mai gida ka ƙyale yarinyar nan karta mutu, zaro jajayen idanuwan shi yayi kamar yaci mutuwa yace fita idona Al ` Amenn ya faɗi maganar yana fitar da wani irin lumfashi kamar ranshi zai fita, Al ` Ameen kuwa ƙin sakin hannun Dikko yayi saboda tunda yaga Dikko a wannan yanayin yasan komai zai iya faruwa....

Yace mai gida karta mutu, Dikko yace ta mutu idan ta mutu kaine ka kashe ta ko kaine zakayi azumi ? Ya ƙarasa maganar tare da kwalalo idanuwanshi waje , sannan yace duk abinda ya faru da ita nine ya ƙarasa maganar tare da nuna kanshi, haƙuri akayi taba dikko dakel aka samu ya sakeni ,

Bakin gadon Alhaji ya koma ya ɗauki wayarshi iyakar bincike Dikko yayi bai samu komai ba, kuma number na dama Alhaji baiyi saving ba, jerin kira ya dawo yaci gaba da binke, saida ya gama sannan ya ajiye wayar , kallo gadon da nake kwance yayi har an sakamin ƙarin ruwa da taimakon Al ' Ameen dayayi tsaye yace a bani taimakon gaggawa,

Kusa da Al ' Ameen yaje tare da cewa bani makullin mota, cikin girmamawa ya ɗauko ya bashi baiyi mishi musu ba saboda yasan Dikko baya san gardama idan yace ayi kawai ayi mishi idan yace a bari barin kawai za'ayi sai a zauna lafiya,

Cingom ya ciro daga aljihu ya ɓanɓare ya saka bakinshi yaci gaba daci, Al ' Ameen kuwa bin Dikko yayi da kallo harya fita daga ɗakin yana mamakin hali irin na Dikko zuciyarshi tayi yawa idan ya burkuce wani lokaci kamar bashi ne yakeyi wasu abubuwan ba...

Ta jikin window ya leƙa

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment