Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciwo , ƙaruwa hawaye na sukayi nace da Allah wai ina zanje ? Ki fita........ Ya faɗa cikin murya maisa firgici babu shiri na buɗe mota na fito , sai yaita yin abun kamar wani shafar aljannu ,

Ina fita Al ' Ameen yace muje ciki yayi gaba babu musu na bishi muka matsa , makulli yasa ya buɗe ƙofa sannan ya shiga , nima shiga nayi palo ne mai girman gaske sai wasu ƙoƙofofi biyu da bansan ko ina ne ba , makullin ya ajiyemin a saman hannun kujera yamin saida safe....

Banyi magana ba na saki baki kamar lefen wawiya ina kallonsu suka fice daga gidan , dan daga cikin palon zuwa bakin get ba wani nisa kuma daga cikin palon kana hange duk wanda yake bakin get , wuri na samu na zauna ina maijin takaicin rashin kasancewar wayana a kusa dani ,

A ɓangaren masu party kuwa saidai shagali yayi nisa sannan aka gane bani a wurin , nemana aka farayi amma ina mutane basu ankara ba Dikko yayi layar ɓata dani , wasa ² abu ya zama gaske yayin da wasu ke cewa sunga anmin waya na fita , nemana aka shiga yi amma babu ni kuma babu labarina....

Dikko kuwa asibiti suka fara zuwa ya ƙara duba Sadiya da jiki yayi mata nasiha ya lallasheta , saidai tayi murmushi mai tattare da ƙuna da baƙin ciki tabi Dikko da kallo mai ban tausayi , duk da yawan murmushi ba ɗabi'arshi bane idan tayi murmushi shima sai yayi mata dan ta samu natsuwa domin shi kanshi yasan murmushin shi wani sirrintaccen sirri ne da Allah yayi masa baiwa dashi badan halinshi ba , murmushi yana ma Dikko kyau sosai kuma murmushin shi yana da ɗaukar hankali da burge duk wanda ya gani ,

Saida Sadiya ta samu bacci Dikko yayi sallama da wanda zasu kwana da ita ya wuce gida , yana zuwa wanka yayi bayan ya fito ya saka riga da gajeran wando na jersey palo ya dawo ya zauna zuciyar shi na mishi babu daɗi , gaskiya tunda yake a shakarunshi bai taɓa cin karo da yarinya mai taurinka da rashin ji kanta cike da iskanci ba irin Sultana , a shekarunta har tasan taje ta ɗauko vidion tsiraicin uban wani ta tura ma ɗiyarshi ,

Shi kuma Babanta shima dai anyi tsohon banza ka rasa wacce zakayi lalata da ita sai ƙawar ɗiyar daka haifa , kai abu yayi muni gaskiya , jinjina kanshi yayi shi idan shine duk su Sultana ba mata bane a wurinshi , ko iskanci zakayi da sakarci ai ka samu macen da ta cika mace ta ansa sunanta takai mace ta ko ina da ko ina mai cikakkiyar zarra ba wannan jagwalgwalon yaran ba ,

Ya daɗe yana zaune palo yana tsaƙawa yana kuncewa wallahi zai tsaya saman ƙafafuwan shi ya cusa wa An mata soyayyarshi a zuciyarta idan ya riƙo ragamar rayuwata wato zuciya yasha da ita kuma ya gama da ita har abadan duniya , zata ga girmanshi tasan darajarshi saboda wannan kamun da yayiwa rayuwarta ,

Wayarta ya buɗe yayi binciken duk da zaiyi bayan ya gama ya rufe wayar gaba ɗaya tare da zamewa saman kujera yaci gaba da bacci !

A ɓangaren Babana kuma yana can gidan caca baisan wainar da ake toyawa ba a gidan , yana can ya shawu an zinatu kuma akaci gaba da caca , baya tunanin komai na ɓacin rai bare kuma halin da iyalinshi suke ciki , sabgar gabanshi ya saka a gaba kuma ita yakeyi baiji duk faɗin duniyar nan ba akwai mai iya dakatar dashi akan abinda ya saka kanshi ba....

Gajiya nayi da tsayuwa na tunkari ƙoƙofin biyu da na gani a jere , ƙofa ɗaya a rufe take ɗaya kuma a buɗe , turawa nayi na shiga da sallama a baki na , ɗan madaidaicin palo ne da kujeru masu kyan gaske na leda , sai labulaye masu kyau da tsada wanda suka dace da kujerun , a gefe kuma ga ƙatuwar talabijin girke a tebirin ajiyarta kamar zata ɓaro ƙasa saboda girman ta , abundai zabburgewa , ciki na shiga wato ɗakin bacci babu gado sai ƙatuwar katifa da "yar ƙaramar talabijin liƙe a bango , labulayen suma irin na palo ne , toilet na leƙa sannan na fito daga ɗakin duka nayo waje inga ko ni ɗaya ce a gidan !

Wasu irin murɗaɗin ƙattin mutane na gani marasa kyan gani yanayin duk ko wane ɗaya kamar ɗan rastilin amma su wanɗan nan baƙaƙe ne , suna gani suka yo kaina suna wata irin magana mai tada hankali wallahi saboda tsoro saida na saki fitsari a wurin , saboda wallahi siffar su bata da kyan gani abun tsoro ce abun firgici ce idan kuma sukayi magana sai kaji kamar ba duniya kake ba , tsaye nayi wurin saboda tsoro na kasa gaba na kasa baya , ruɗewa tasa na manta da ina da ƙafafuwa ...

Tunzura babbansu yayi yanayin shi ya nuna yana cikin ɓacin rai dan haka yayi wani irin kuka mai motsa tunani ya ƙara takowa dan ya samu damar matsowa kusa dani , nidai bansan ya akayi na ruga ba saidai kawai na ganni saman katifa har na lulluɓe da bargo ina kuka ! Bansan lokacin da bacci ya ɗaukeni ba ,

Da safe Dikko daga masallaci asibiti suka nufa daga shi sai Al ' Ameen , har yaje ya dawo Sadiya bacci takeyi , bayan ya dawo gida ne ya kira danjin ita kuma An mata ko ta kwana lafiya , lafiyanta qalau suka faɗa tare da bashi labarin abinda ya faru , mugu yaji mugunta , dariya Dikko yayi sosai tare da cewa zaizo anjima ai ,

Ba'a mugun sarki sai mugun bafade , Al ' Ameen bayan Dikko ya gama waya yace mai gida dan girman Allah ka kyale yarinyar nan tayi tafiyarta , sai kace dai itace kaɗai mace a duniya ? Yarinya mara kunya mara tarbiyya mara ɗa'a masu gajeren asali wallahi mutuncin gidanku da nasabarku da kai kanka taka mutuntakar ta wuce ace kana sauraren yarinyar nan wallahi , kana da zarrar da duk macen data ganka duniya sai tayi addu'a ta sameka a matsayin abokin rayuwarta.

Kana babban asali ga cikar zati ga kyau ga kwarjini me zakayi da yarinya mara tarbiyar ? A hankali Dikko ya lumshe idanuwanshi dan duk duniya idan akwai kalma mafi muni da ɗaci a wurin shi bata wuce ace An mata bata da tarbiyya ba , Al ' Ameen yaci gaba da cewa uwa uba kuɗi kana da cikar arziƙin da zaka iya auro mace ko wace iri ce kai ko babu kuɗin sai ta so ka dan kyan ka , abin kunya daci baya ne ka auri ɗiyar ɗan caca mashayin giya manemin mat....

Hannu Dikko ya ɗaga alamar dakatar dashi , shiru yayi bayan yayi shiru yayi masa nuni da ya fita kawai , Allah ya baka haƙuri mai gida ya faɗa cikin girmamawa sannan yabar ɗakin ,

Fitar Al ' Ameen Dikko ya fara nazarin maganganun shi tabbas duk abinda ya faɗa ba ƙarya bane ba , ko wane mai asali yana so ya auro mai asali gidan tarbiyar da mutunci amma miye aibun An mata ? Duk dai haɗa jini da mutane banza bashi da wani amfani dan ba'a gane matsalar hakan sai zuri'a sunzo dan iskanci jini yake bi , tou amma mi yasa ita An mata batajin magana ne ? Wani sashe na zuciyarshi yace ba komai wata rana zata daina , idan har mace tana shakkun namiji idan dai ya shata mata doka tou fa tabbas ba zata karyata ba , wani sashe kuma cewa yayi matsalar ba'a nan take ba , tsoki Dikko yayi tare da cewa da Allah ku barni...

A ɓangare na kuma , da asuba ina farkawa kayan jikina na cire na wanke su saboda na ɓatasu da fitsari na goge katifar dake da leda a jikinta kila ma sabuwa ce , labule ɗaya na ciro na ɗaura , bayan na gama wanke kayan a palo na shanya saman kujera na kunna fanka , ɗaki na koma na shiga nayi wanka tare da ɗauro alwalla , bayan na fito na sake ciro wani labilen na rufa dashi naci gaba da sallah.... 🤔

Bayan na gama na koma na kwanta , ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗaukeni , dan banda wata damuwa saidai kaiwai ina so in tafi gida ,

Ina bacci Dikko yazo kuma tun a palo na fara jin faɗashi wai waye yace kujera wurin shanya ne ? Da sauri na tashi na ɗauki bargo na ƙara lullube jikina a dai² lokacin da naji Dikko yace maza cire wannan tsumman kaje ka jefar dashi a waje , kutumelesi ? 😭 rigata mai tsada itace za,a yadar ? Amma dai wallahi Dikko ɗan iska ne , kuɗi fa masu yawan gaske Alajina ya siyamin ita shine zaisa a yado ta ,

Ina cikin kuka naji ƙarar takalminshi yana tahowa ɗakin da nake , ci gaba nayi da kuka ko zai tausayamin yasa a dawo min da rigata , kwance nake cikin bargo fuskata kaɗaice a waje ina kuka , ƙamshin turarenshi ya ƙara matsowa kusa dani haka ya tabbatarmin yana gab dani dan haka na buɗe idona ina kallonshi ,

Murmushi yayi cikin natsuwa sannan ya fara magana cikin kamun kai da aji , gaba ɗaya jiya da daddare tunaninki nai tayi , da sauri nace me ? Murmushi ya sakeyi sannan yaci gaba da cewa tunanin da nayi tayi cikin dare shine nayi kuskure , sam bai kamata ace na ɗaga hannu na mari mace ba , kiyi haƙuri don Allah idan ma baki gamsu ba zaki iya rama marikin kamar yadda na mareki , ƙoƙarin tashi na farayi dan rama marina , cikin magana mai kama da raɗa yaɗan fiddo kyawawan idanuwanshi yace a haba keko ba'a nan ba kinsan babu kaya a jikinki koma kawai ki kwanta ,

Babu gardama na haƙura na koma na kwanta , fita yayi bai daɗe ba ya shigo da wani haɗaɗɗen kwando ya ajiye a can gefe cikin magana mai laushi da kalamai masu burgewa yace kiyi kalaci ya faɗi maganar tare da nunamin inda kwandon yake , zai fita nace am da Allah idan babu damuwa rigar nan kada a yadar da ita anjima idan zan tafi ita zan saka ,

Ba tare daya kalleni ba yace bama buƙatar ita rigar kayanki yanzu zansa a shigo miki dasu palo , wai ance jibi hutun ku zai ƙare idan zan wuce zan ajiyeki makaranta , kallo ni yayi tare daci gaba da cewa kyakkyawar fuska da kyawawan idanuwa irin naki gararin gari ba nasu bane da ilimi suka dace bada taron murnar zagayowar shekarar aihuwarki ba , yana faɗin haka yayi gaba abinshi , ni kuma nace wallahi aiko babu sakaran da ya isa yakaini makaranta tunda ba cewa nayi ina so ba , dawowa yayi tare da cewa kina magana ne ? Banza nayi dashi naci gaba da hararar ƙasa ,

Murmushi yayi da gefen bakinshi ya fita , yana fita na ƙara cewa kuma ko ka kaini saina dawo dan kaga na kwana nan gidan nan ko an faɗa maka ni ina tsoron waɗanda ka ajiye ne ? Sake dawowa yayi yace kina so ki madani kamar wani sa'ar wasanki ko ? Tou idan kinje makarantar ki gudo mu gani , Dikko ya kaiki saboda haka Dikko zaici gaba da ɗauko ki , ke ɗaya na bayar kuma ke ɗaya za'a bani a ko wane hutu , kuma ko hutu akayi idan ba nine naje ba ko waye wallahi yarinya bazaki dawo gida ba gara ma ki fara kamun ƙafa tun yanzu ko zan riƙa ziyartarki lokaci ² idan kuma kika nunamin yarinta sai ina barki kisha baƙar wahala babu abinci babu kuɗin kashewa , yana faɗin haka ya fice abunshi ,

Ni kuma ƙasa² nace sai inyi ta iskanci da malam su sa fiddoni , in dawo gida , kuɗinkan banza kuɗinkan wofi ko an faɗa maka ni matsiyaciya ce ? Hahaha niko nace da kanki ma zaki riƙa cewa ya baki bari dai kisha azaba yarinya ....

A palon ɗaki na Dikko yasa aka ajiyemin kayana saman kujera , shi kuma yayi tafiyarshi , saida naji fitar motarshi na tashi naje na ɗauko kayan na saka ina sakawa ina mita ni za'a bawa kwance kila ma kayan matarshi ne ya ɗibomin , kona ƙannenshi , niko nace kedai kika sani...

Ɗaki na dawo ina cewa shikenan an yado rigar Alajina daya ji kuɗin rigar shi kanshi nasan sai gabanshi ya faɗi , Allah yasa ya dawo yanzu yace in rama marina saina ci abinci na ƙoshi zan zabgaga mishi mari sai yayi fitsari saboda azaba ,

Gaban kwandon na durƙusa ina ci gaba da surutu babu kai babu misali , kwalin makilin da burosh a gefe da sauri na fara buɗewa dan inga abinda aka kawomin inyi kalacin safe dashi .....




21/09/2019



*JAMILA MUSA...*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 37


Gayu mutanen Allah shine abinda na furta a lokacin da naga shagalin dake cikin food flarks , murmushin jin daɗi nayi wai duk ni ɗaya zanji daɗi na , miƙewa nayi tare da komawa da baya cikin farin ciki na faɗa saman katifa zanci daɗi yau zanyi kalaci da farfesu , ga doya ga farfesun "yan ciki , wannan daɗi da hawa tsaunin rayuwa har haka ? Ɗaga ƙafafuwana nayi sama ina musu shangululu tare da rumgume duka hannaye na a ƙirjina cikin farin ciki nace wallahi madarar ma duka zan juyeta...

Wani irin ihun farin ciki na kurma wanda har na waje saida sukaji ni , da sauri na sauko daga saman katifata naci gaba da aiki dan gani nake idan na tsaya wanke baki a iya shigowa aga kamar na gama a fita dasu ,

ina ci ina kaɗai kai tare da addu'ar rayuwa ta ɗauremin da irin wannan daddaɗan kalaci , naci komai kuma komai nasha nayi hamdala ga ubangiji da ya bani aron lumfashi ya bani baki da ciki da lafiya kuma ya ruboto min wannan babban rabo da alƙamin kudarar shi...

Ina gamawa na tattara komai na fitar palo , labulayen dana ciro na ɗaura na mayar dasu mazauninsu na gyara , saman katifa na dawo tunda dama nayi wanka cike da farin ciki na lumshe idona na tafi duniyar bacci.........!

Tashin hankali a gidan su Sultana , cike da farin ciki Baba ya shigo gida ya dawo da kuɗin shi cike da aljihu domin a daren jiya shi ya lashe maƙudan kukaɗaɗen da aka zuwa a wasan caca , ƙofar ɗakin Sultana ya nufa kai tsaye yana cewa Mamana kin ganni sai yanzu ?

Kowa yayi cirko² domin "yan gidansu Sultana tun jiya suka dawo da labarin ɓatanta , kowa dai yana cikin jimami da tashin hankali , Baba kuwa bayan ya shiga ɗaki shiru² bai fito ba dan a tunaninshi Uwar masu gida tana bayi ne...

Zama yayi har ya gode Allah , komi Uwar masu gida takeyi ai ta isa ta gama ta fito gajiya yayi da zama ya fito tsakar gida yana cewa ina Mamana taje ne ? Shiru kowa yayi ya kasa magana , bin kowa yayi da kallo yanayin fuskar su ta nuna akwai wani abu daya faru , bayan ya gama kallon kowa yayi magana cikin karyewar zuciya cewa ina Mamana...... Take ? Ya ƙarasa maganar yana mai bin bango ya sulale ya zauna ƙasa a hankali ,

Maman Fa'iza ce tace mu saka Sultana a addu'a domin yanzu ba abinda take buƙata sai addu'armu mu dage da roƙon Allah har ubangiji ya bayyana mana ita domin Sultana dai ta ɓata , lokaci guda zufa ta ɓarkewa Baba ya tsurama wuri guda ido kamar mage ta ɗana tarko , bayan wani lokaci kuma yace haka zakimin Mamana ? Haka mukayi dake ? Wannan shine sakamakon alƙawarin ? Ina kika tafi ne ? Inajin babu jimawa mukayi magana dake baza ki taɓa tafiya ki barni ba , shine kika tafi kika barni..... ? 😭 hawaye ya gangaro mishi daga cikin idonshi , daga nan yayi na wani mawaƙi da yace ayye mata a ƙame ƙam , tou Baba shima ya ƙame kamar wayar da tayi hucking....

Tunda na kwanta bacci babu abinda ya dameni kuma bana wani tunanin komai haka kuma banga komai ba a cikin mafarki na , bacci na nakeyi cikin natsuwa da kwanciyar hankali , sai da aka kira azahar na farka nayi sallah bayan na gama na watsa ruwa na koma nayi kwanciyata amma ba bacci nake ba !

Gidan shiru kamar babu kowa ciki sai ƙarar iska irin mai tahowa da ƙasa , a hankali sanyi ya fara saukowa irin mai shiga ƙashin nan , zuwa bayan la'asar sanyi ya sauko sosai wanda yasa mutane suka fara saka rigunan sanyi,

Ni kuma da banda rigar sanyi ina cikin bargo na duƙunƙune , ga azabar yunwa da nakeji na rasa inda zan saka rayuwata , har akayi magrif babu wani labarin abincin rana bare in saka ran na dare zaizo , nasha ruwa har nayi fitsari bansan adadi ba , tun ina daurewa har na fara Allah ya isa a zuciyata...

Tunda nayi magrif ban tashi daga inda nayi sallah ba ina zaune na zabga tagumi kuma ni ba addu'a nakeyi ba , ina cikin wannan tunani naji ƙarar buɗe get murmushin jin daɗi nayi nasan Dikko ne kuma yazo da abinci , tabbas abinci yazo ya kawomin , cike da murna na leƙa ta window kuma wallahi shiɗin ne , sanye da tsadajjiyar baƙar rigar sanyi mai kyan gaske da burgewa tana da farin zif daga gaba , an zageye wuyan rigar da farin ado amma ba irin na mata ba ina ganin dibara ce dan kar rigar ta lalace daga saman wuya , sanye da shuɗin wando da takalmi baƙi amma ba rufaffu bane maɗauri gare su kamar sandals , hannun rigar ya ɗan naɗeshi zuwa guiwar hannu , kanshi babu hula kuma fa gaskiya yayi kyau dake baida ƙiba ko kaɗan amma yana da tsayi daidai burgewa bana zarce misali ba...

Al ' Ameen ke ɗauke da kulolin abinci shi kuma waya yakeyi , ina ganin sun tun karo ƙofar shigowa palon nayi sauri na kowa saman abin sallah na kalli gabas ,

Suna shigowa shi Al ' Ameen ya kunna musu kallo , maimakon ya kawomin abinci sai kawai suka zauna sukaci gaba da kallon kwallo , har akayi isha'e suna zaune kamar asara suna kallon kwallo , inajin maganar Dikko lokacin daya shiga ɗaki mai kallon wanda nake ciki yana cewa bari inyi sallah dai , tsoki nayi tare da cewa andai ji kunya sallah a gida , nima tashi nayi nai sallah dan ina da alwallah ...

Har na gama sallah banji Dikko ya fito ba , kuma naji palon ya fara cika da maza ga dukkan alamu kila gidan dai matattara ce ta maza , tunani na farayi karfa su cinye abinci ban samu ba , tashi nayi na fita ɗan madaidaicin palon na zauna ina jiran fitowar Dikko idan ya manta da ina nan tou ya ganni ya gane ina nan ,

Tunda na zauna ƙarar motoci ke shigowa , hayaniyar sai ƙara sama takeyi maza surutu ga magana babu natsuwa , nafa daɗe ina zaman jiran Dikko bai fito ba , kuma bana so na leƙa babban palon bansan ko su waye a wurin ba , na haƙura da niyar komawa ɗakin da aka ajiyeni naji dai bazan iya kwana banci komai ba yunwa nakeji kamar zan mutu wallahi , dawowa nayi kai tsaye na shiga ɗakin ,

Da sauri ya kallo ƙofar dan yaga waye yake shigowa yana zaune saman abin sallah , murmushi yayi ganina tare da cewa An mata miye ? Ɗan suɓaro baki nayi ina wasa da yatsun hannuna nace dama , sai kuma nayi shiru , ɗauke kallonshi yayi daga gareni yace dama me ? Shiru nayi na kasa magana , shima bai sake magana ba yaci gaba da latsa counter , naci uwar mintuna sha biyar Dikko bai sake kallona ba kuma bai sake magana ba ,

Saida ya gama abinda yake ya ɗauke abin sallar daga inda yayi sallah ya ɗora gefen gado , zuwa yayi zai wuce ya fita dan yayi kamar ma babu ni a wurin ,

Ya kusa fita nace yunwa nakeji , yi yayi kamar baiji abinda nace ba ya fice abunshi , biyoshi nayi a lokacin har ya kusa fita daga palon ya shiga babban palon , nace da Allah nace maka yunwa nakeji nayi maganar a tsiwace , naji ya faɗa tare dayin gaba abunshi ,

Tsoki nayi cikin ɓacin rai na koma ɗaki ina gunguni , shi kuma daya koma kallonshi yaci gaba dayi , sai ihu sukeyi "yan iska kamar mahaukata , amma bana tunanin Dikko yana wurin dan har yanzu ban jiyo maganarshi ba , duk wanda aka ci su sai kuji hayani ta ƙara sama , sai gaddama da magana cikin faɗa² ,

Sai yanzu naji dariyar Dikko yana shigowa cewa ko gobe da fansar kura saidai garin da babu awaki , murmushi nayi cikin yanayin jin kunya nace ashe kaima ka iya karin magana ? A dai² lokacin daya shigo yana dariya ,

Ɗaure fuska nayi kamar ina cikin yanayi damuwa , ko kallonshi banyi ba ya ɓatamin rai ni zai zubowa abinci a gaban bainannasi hmm , ga abinci ya faɗi maganar a daidai lokacin da yake ajiyewa a gabana , kauda kaina nayi na tura abincin na ƙoshi ...

Murmushi yayi tare da ɗaukar abinci zai fita , nace kai nifa wasa nakeyi bani nan nayi maganar tare da nuna mishi ya maidoshi gabana , banza yayi ya fice daga ɗakin da sauri na tashi nabi bayanshi amma kafin in fito harya fice ya koma cikin abokanshi yana dariyar mugunta , a ranshi yace daga yau sai kiyi hankali ni ban iya wasa ba kuma ba'amin wasa ,

Wannan rana saidai na kwana da yunwa nasha kukana har bacci ya ɗaukeni bansan lokacin da suka tafi ba ,

Koda

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment