Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nana da Allah kije kice waye ya d'aukomin "yan sanda ? Cikin farin ciki ta koma zaure sannan ta tambayi d'an sanda waye yake k'arata ?

Fad'a mata yayi tayo cikin gida da har yanzu tanajin dad'in k'arata da akayi, a bakin k'ofar d'aki ta tsaya sannan tace wai abokin Babanki Bello, jinjina kaina nayi tare da cewa tou ina fitowa....

Data na bud'e na nemo lamba 2, hotunan dana d'auke shi jiya na tura mishi tare da yin voice note na antaya ma banza, ina gamawa na kashe wayata, saida nayi wanka naci gayuna na watsa turare na d'auku iyakar yanda hankali baya tunani duk wanda ya ganni saina burgeshi, fitowa nayi banma kowa magana ba na tunkari zaure, dan zuwa wurin hukuma a yanayin talauci yana jawo ma mutum raini....

A k'ofar gida na samu d'an sandan nan ya gama shak'e b'acin rai daga gani yana jira muje can yaci uwata, a yangance na fito cikin aji na kalleshi tare da cewa "yar labai barka da aiki......

'Dan sakin fuska yayi tare da cewa yawwa, gaishe shi nayi tare da ce masa nice Sultana, kallona yayi sama da k'asa sannan yace tou hajiya muna gayyatarki zuwa ofishinmu ai anyi miki bayanin mai k'ararki ko ? murmushi nayi tare da cewa babu damuwa muje amma Allah yasa ba'a cikin motar "yan sanda zaka d'aukeni ba, murmushi yayi tare da cewa ai hajiya napep zamu shiga, ajiyar zuciya nayi cikin sigar jan hankali sannan nace tou ai har naji natsuwa.

Napep muka hau muka nufi c p s , kuma nice na biya kud'in 1k ne na bayar kuma daya anso canji nace ya rik'e yasha ruwa, tunda muka fita a napep gaba d'aya wurin saida hankalin kowa ya dawo kaina, na farko dai ga wanka ga gayu ga k'amshi uwa uba kyau Allah yayi min kyawun da mutum baya gajiya da kallona, ga gashina na tik'ashi nayi mishi wani irin parking irin na wayayyin mata, baka isa ka rainani ba ko waye kai domin sitirar dana saka ita kad'ai ta isa ka gane ni ba sa'ar wasan yaro bace ba.....

Ofishin d c o muka nufa, a ciki na samu Bello zaune tare dashi da wasu abokan Babana, sallama nayi sannan na gaishesu dukansu cikin kyakkyawan yanayi, bayan mun gaisa nima na samu wuri na kame kamar yanda naga kowa yayi.....

Kallona d c o yayi bayan ya gama karanta wata takarda dake gabanshi sannan yace Maryam miya had'aki da Bello ne ? Murmushi nayi tare da gyara zamana nace ranka ya dad'e ai Baba Bello abokin kasuwanci ne, halak'a ta mutunci ne a tsakani na dashi bayan wannan babu komai....

D C O yace tou jiya ina kika had'u da Bello ne ? Ranka ya dad'e majalissar su naje gaishe su, bayan mun gaisa kuma ya tambayeni nayi aure nace masa A , a, yace yanzu ina nake zama ? Nace masa ina zama a tsohuwar anguwarmu daya sani, ya tambayeni ko ina kasuwanci ne ? Nace masa Eh yace me nake siyarwa ranka ya dade nace masa karuwanci nakeyi, tsakanin mai saye da mai siyarwa ai babu fushi anan muka daidai suka d'aukeni muka tafi wani gida, nuna yawan duka abokan Babana nayi sannan naci gaba da cewa ranka ya dad'e dukansu nan babu wanda baiyi ba kuma duk saida suka k'ara zagayawa "yar labai, kuma gasu nan ka tambayesu idan nayi musu k'arya. Kuma cikon kud'in ma har yanzu basu bani ba..

Kowansu zaro ido yayi tare da dafa k'irji cikin yanayin mamaki yace ke mune mukayi iskanci dake ? 'Daure fuskata nayi kamar gaske nace aini banajin kunya tunda dai banji tsoron Allah ba nayi zina wallahi banajin kunya gaban kowa in fad'a nayi, kunyi mana ko k'arya zan muku ne ? Lokacin da bakuyi ba nace kunyi ?

Gaba d'aya wurin hayaniya ta tashi har bakajin bakin wani, d c o ya dakatar dasu tare da cewa suyi mishi shiru, bayan kowa yayi shiru ya kalleni sannan yace ke Sultana Bello yana tuhumarki kud'in shi da kika d'auka. Cikin natsuwa nace wasu iri kud'i kuma ranka ya dad'e ?

Bayani d c o yaimin kamar yanda na sani, jinjina kai nayi tare da cewa idan sun gama k'arata nima zanyi k'ararsu saboda b'atamin suna da sukayi, ranka ya dad'e a gaban idon waye na d'auka kud'in ne ? Nifa bana sata amma ina neman maza gaskiya, duk abinda nakeyi bana jin kunyar asan inayi domin dai duk sana'a sunanta sana'a, idan ma na d'auka aka tambayeni idan nasan na sata kawai zan dawo musu da kayansu in basu hak'uri tunda karuwanci da nakeyi ai ban b'oye ba na fad'a tunda ba abun kunya bane....

Tambayar Bello D C O yayi ko yana da wata sheda ne ? Baida ita tunda an tambayi mai gadi yace shidai bai ganni cikin mota ba, duk iyakar binciken da akayi dan asamu wata sheda babu ita, dan haka aka rubuta takarda cewa an janye k'ara, bayan an gama rubutu aka bani na saka hannu da larabci nayi sigining ina, an mik'e za'a tafi nace ma d c o naga fa sunamin wani kallon hadarin kaji sufa fita ido na, d c o yace ai duk an rubuta, nace to ranka ya dad'e cikon kud'ina kuma sai yaushe zasu bani ?

Hak'uri d c o ya bani tare da nunamin tunda anyi masa sata inyi hak'uri inma barshi da ramuwar biyan kud'in mutane, babu kunya ba komai nace kenan ni yanzu ranka ya dad'e sunci banza ? Duk wanda ke cikin office in saida ya kalloni, nace ranka ya dad'e kafa duba lamarin nan gaskiya ni ba'amin adalci ba, shiru wurin yayi wutar kowa ta d'auke, murmushi nayi tunda basu da amsa nace nawa ake yankar sammaci ? Sammaci ma ake cewa abin ko miye ?

A kotu ake yankar sammaci d c o ya bani amsa tare da fad'amin abinda ake kiran nasu da turanci, oho dai da yake kan baya ganewa kasa maimaitawa nayi saidai kawai nace nawa ne ? Kud'in aka fad'amin na bud'e jakata na bada sannan nacewa d c o ga wanda nake k'ara nan Bello ina tuhumarshi akan b'atar mahaifina daya tafi babu wanda yasan ina yaje..........








21/08/2019


*JAMILA MUSA...*

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 15


*_Had'inkai group ina tare daku aminan albarka, Allah yabar so da kauna ubangiji ya k'ara yadda da aminci, HALIMATU SADIYYA {{ Leema }} HABIBA IDRIS {{ Hubbie }} HAUWA'U USMAN {{ Smasher }} MAIMUNA O . G {{ Aunty Munari.... }} muna tare_*

*_Mrs Abdul-aziz ina godiya sosai da dogon sharhi kuma ngode sosai page 14 na baki shi kyauta...._*


Lahaula walakuwata illah billah, kiji tsoron Allah ke uwar masu gida a ina na b'atar da mahaifinki ? Sharri zaki min ? Kiji tsoron Allah in babu nan akwai ranar hisabi duk wanda yaci zalin wani daidai da kwayar zarra ubangiji bazai barshi ba, ki daina ganin kin samu dama ta tak'in lokaci yasa ki manta da rayuwar gaba, karki biyewa zuciya ki kafa abinda zaisa kiyi nadama wata rana.....

Gaba d'aya jikina yayi sanyi tsoron Allah ya kamani nasan k'azafi da sharri ba abu ne mai kyau ba, kuma addini na bai koyar dani haka ba, amma d'an kamewa na sakeyi sannan nace ni rayuwar dad'i baza ta tab'a zama takaitacciya a wurina ba, jin dad'i na d'aura insha Allah daga nan har zuwa ranar da numfashi na zai k'are, ina Babana yake wai ina ka kaishi ne............?

Cikin nadama Bello yace na rantse da ubangiji daya bani aron lumfashi ya bani aron lafiya nake ganinki nake kuma saurarenki ya bani hankali da tunani idan nasan inda mahaifinki yake Allah ya tsinemin albarka. Wallahi Uwar masu gida bansan inda ya tafi ba na rantse miki da girman Allah. Tausayi ya bani yana rantsuwar yana wani kwantar dakai kamar an ritse macen da tayi cikin shege ta haihu kuma ta kashe d'an....

Kallon D C O nayi tare da cewa "yar labai shikenan tunda yayi rantsuwa baiyi ba kawai na janye, zan iya tafiya ? Na tambayi D C O, cewa yayi na zauna zamuyi magana, zama nayi su kuma su Bello aka sallamesu suka tafi ni kuma naci kud'in banza Ehe....

Ta wutsiyar idona na kalli d c o bayan fitarsu Bello domin ina son na gano tashi manufar a kaina, murmushi nayi bayan na gama fahimtar shi, a bayyane nace lamba 3 tazo kenan, ajiyar zuciya ya sauke tare da tattaro duka hankalin shi wurina yace ranki ya dad'e ya hak'uri da jama' a ? Kallonshi nayi ba tare da nayi magana ba domin wallahi tsarin bakinshi kwata kwata bai burgeni ba. Amma ba komai zan hak'ura nayi maleji dashi haka nan saboda idan na taro watan aug zai gina min gada nabi na wuce ba tare dana sha k'ashin ruwa ba....

Wayan cewa nayi tare da gyara zama na nace Allah dai yasa aiki zaka d'aukeni mai girma d c o, murmushi yayi tare da komawa ya kwanta saman kujerarshi irin masu juyawa d'in nan, sannan yace wai gida zan saukeki idan ba matsala, d'an yamutsa baki nayi tare da cewa na gode amma ni ba gida zanje ba...

Ina zakije haka da rana ? 'Daure fuska nayi dan ya fara cika min ciki nace wurin aiki zanje, wane irin aiki ? Tsoki nayi tare da cewa kai komai sai anyi maka b'aro b'aro kake ganewa ko ? Tou abokin lalata zanje nema.....

Murmushi yayi tare da cewa ke bakya gajiya ? Cikin wuta wuta nace ka tab'a ganin inda mutum yake rayuwa babu abinci ? Yace a , a, nace tou ni da kud'i da karuwanci sune abokan rayuwata, domin sai nayi nake samu sannan naci nasha na kuma d'aura har in fito na burge abokan harka , idan kuma kaima d'an hannu ne karka wani cuci kanka kawai kayi magana idan kajira sai an maka tayaki tou fa lallai zaka kwana da yunwa, amma kayi hak'uri da tambayar da zan maka tsakanin ka da Allah nawa ne albashin ka...... ?

Kallona yayi tare da cewa hajiya maryam kenan , miya shafi albashi da harkar bariki ne ? Bai shafa ba amma ni ina duba nasabar namiji da cancantar shi kafin wata sahihiyar mu'amula ta shiga tsakani na dashi, dan duk wanda ya jawo maganar aure a rayuwarshi tabbas ya tara abun hidima, bata yuwuwa na biye maka ka k'ok'ar dani ba tare da ka sake bani kud'in da zan sabon fenti ba, dan kai kanka da ban d'aukar maka ido ba duk yanda nake barikin baza ka taya ba,

Kallon agogon dake d'aure a tsintsinyar hannu na nayi tare da cewa zama wuri d'aya tsautsayi inji kifi, malam d c o zan wuce ka rubutamin number ka a jikin takarda idan ayyuka sukamin sauk'i akwai dawowa......

Babu musu kuma ba tunanin komai ya d'auki biro da takarda ya gwagwad'amin number wayarshi, ansa nayi tare da mik'ewa tsaye sannan nace sai ka jini, baki bari mu tafi in ajiye ki ? Ya tambayeni, juyawa nayi na fara tafiya tare da cewa ban hawa mota sai napep a daidai lokacin dana fice daga ofishin....

Ina fitowa wuri na samu na tsaya, wayata na fiddo nayi saving in no d c o da lamba 3 , sannan na kira wayar Alhaji, babu b'ata lokaci ya d'auka tare da cewa ranki ya dad'e tun jiya inata kiran ki wayarki a kashe ko yau da safe ma na kira a rufe.... Ban bashi amsa ba nace kawomin kud'in yanzu nan ina nan c p s ina jiranka kuma karka b'atamin lokaci, ina fad'a na kashe wayata......

Lambar Bello na kira amma bai d'auka ba, daga kira d'aya nima ban sake kira ba, domin dai nasan idan yaga abunda na tura mishi shi da kanshi zai nemeni, k'ok'arin maida wayata nake cikin jikka naji ana cewa shegiya k'awata kece kika koma wata hajiya haka ? Da sauri na d'ago kaina domin jin muryar Amisty da nayi...

Cikin farin ciki muka rungume juna, bayan gaisuwa sai kuma muka shiga firar duniya, yayin da nake tambayarta wane ci baya ta samu na bariki naga har yanzu bata fara hawa mota ba, ajiyar zuciya Amisty ta sauke tare da cewa kinsan mazan babu kud'i hannunsu kullum tsuwwa da kukan babu......

'Daure fuska nayi tare da cewa waye ya fad'a miki ana hawan jirgin sama bashi ne ? Ai filin jirgi ma baka shigarshi dole sai kana da tikitin tafiya, haka nan kike basu suna hayewa basu baki kud'in mai, tou ina uwar d'akin taki ne ko bata nan bata fad'a miki illar maza ba ? Haba Amisty idan baki ridowa da yawa wallahi bariki kasheki zatayi, niko kin ganni nan ni zanyi gwanjo bariki kafin ta wurgar dani gefen titi, kinsan bariki bata da tabbas d'auka da ajiyewa gareta, ni zan kashe bariki bazan yadda ta kashe ni ba, zanyi amfani da talata ta kafin laraba ta, ta riskeni, wannan uwar d'aki taki k'atuwar jahila ce batayi karatun komai ba haka nan ta tara yawan dalibai, har yanzu kuna da dama ki nemi canji makaranta ki dawo makaranta ta zan baki ilimi akan namiji, kud'i kike so ko suna ......?

Horn Alhaji yayi da mota wanda tun d'azu yakeyi amma magana ta hana na saurareshi, juyawa nayi tare da nuna mishi da hannu ina zuwa, ni kuma naci gaba da magana da Amisty, wata matace ta fito daga ciki tayo wurinmu kuma ga dukkan alama tare suke da Amisty, gaisawa muka yi yayin da Amisty ta fara tambayarta ya aka k'are, basu bani labari ba suna ta maganar ne cikin munafinci, ni na fahimta suna magana ne kamar tayi ciki..

Datsar maganar nayi da cewa keko ya akayi kikayi cikin shege ? Gaki a fuska kamar wayayya taya akayi haka ta faru ? Ita kuma a tunaninta Amisty ta fad'amin dan haka tace kin gane ni bawai cikin bane matsala a, a mijina yau watanshi bakwai baya nan kuma ga ciki wata hud'u, kuma nayi a zubar da cikin shi wanda yayi cikin yace wallahi bazai yadda ba saboda bai tab'a haihu ba, idan wannan abu ya fito ai kinsan akwai matsala.....

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na fad'a tare da cewa ke matar aure kike zina ? Hasbinallahu wa ni'imal wakim, amma kinyi k'atuwar asara, kallon Amisty nayi tare da cewa zance zaune ba na tsaye bane idan kuna neman taimako ku sameni gida, ina nan tsohuwar anguwarmu idan kika shigo ki tambayi gidan da nake haya za'a kawoki, ina fad'in haka nayi wurin motar alhaji ina zuwa na kama na bud'e na shige nace muje...

Har muka isa gida banyi ma Alhaji magana ba domin ni yau naga macen da tafini kafirci kina k'ark'ashin bautar aure amma kina aikata sab'o, wannan wai wane irin zamani ne muke ciki lallai ya kamata nasan ita kuma wane rud'un duniyar ne yaja mata neman mazan waje ga nata mijin da yake hak'k'inta amma ta tsallake shi ta tafi wurin na wasu , gaba d'aya jikina yayi sanyi kuma na dawo daga rakiyar duniya....

Ansar jakar da Alhaji ya zubomin kud'i nayi tare da direwa daga motar, zaiyi min magana nace mishi muyi waya kawai nayi gaba abu na, lokacin dana shiga gida bana ko ganin gabana saboda bak'in ciki da kishin aure, d'akina na bud'e na shiga, saida na adana kud'ina sannan naje nayo alwalla nayi sallah azahar, yinin ranar haka na yini sukuku kamar wata mara lafiya, koda nayi sallah isha'i kwanciyata nayi , duk yau banda ruwan shayi babu abinda ke cikin cikina, haka na kwanta da tunani iri iri, ko bacci nayi na farka abun yakan fad'omin a rai har gari ya waye da tunanin matar nan a zuciyata..

Da safe bayan nayi kalaci na gyara d'akina naje nayi wanka na shirya cikin doguwar riga ta atamfa da tasha d'inki buba, hula mai raga { net } na saka kaina na fice tsakar gidan....

Kujera na sa a k'ofar d'akina na zauna tunda fitowa wajen ya zamar min dole, kallon inda Karima take nayi sannan na maida kallo na wurin Saude dake zaune saman turmi, babu ko breziya jikinta kuma babu kaya sai siket ondie da taja saman kirjinta, amma komai na halittar ta babu abinda ya b'oye duk a bayyane yake.....

'Dauke idona nayi gefe na kallo inda Nana take kwance A ` i tana durk'ushe ta duk'a samanta sosai suna k'ushin k'ushin, jinjina kaina nayi sannan na sake kai idona wurin Saude nace ke Saude wai da Allah in tambaye ki ?

Murmushi tayi tare da cewa tambayarni kanki tsaye, b'ata rai nayi sosai sannan nace nan gidan ubanki ne wai da zaki zo ki rik'a zama mana tsirara dan baki da kunya ?

Gaba d'ayansu dariya sukayi ,sannan Saude tace tou ke mai tambayar gidan ubanki ne ? Ni nan ba gidan ubana bane amma ya zama na ubana tunda na biya kud'in haya, d'aki d'aya na kama amma ina da hurumin da zan sauke ubana a ciki, ke ko fa ? Nana ta anshi maganar da cewa yanda kike tak'amar kin kama haya muma kamawa mukayi kuma muma muna da hurumin da zamu kawo mutanen da muke so su zauna tare damu, kedai kawai kice kina so ayi dake.

'Dan gajeran murmushi nayi tare da cewa duk wanda yaci naman arne tabbas zai iya cin mushen alade , banda abinki miya had'a makaho da ganin wawan zama ? Ni bana iya cin naman jaki amma idan na samu doki zanci duk da an yanka shi nasan wata rana zanyi hazaka, ko banyi gudu ba tabbas nasan zanyi tafiya, magana ce na fad'a miki a jimlace idan kina da ilimi sai ki warwareta banzanye da ku masu wahalallen bariki.....

Gaba d'aya wutar kowa d'aukewa tayi sukayi shiru babu wanda tace komai, murmushi nayi tare da cewa ba'a bariki dole saida ado kuje ku ibi ruwa kuyi wanka kusa toka ku wanke baki ko ya rage k'annin koko, daga haka ban sake ma kowa magana ba kuma suma babu wanda ya sake cewa komai,

Bayan Alhaji ya bani kud'i ya dad'e k'ofar gidanmu ya kasa tafiya, hankalinshi a tashe saboda yaso yayi magana dani na goge vidion nan kuma yaji ina na dosa ? Amma samsam ban saurare shi ba, kuma yasan lallai saina sake tambayarshi wasu kud'in tunda akwai vidio a hannuna ban goge ba,

Rasa yanda zaiyi yayi zuciyarsa ta yanke mishi kawai ya fad'a wa Dikko komai yasan babu mai iya magani na saishi amma fa a nashi haukar , d'aga waya yayi ya kira Dikko kuma har zuwa wannan lokacin yana k'ofar gidanmu bai tafi ba.

Bayan Dikko ya d'auki waya Alhaji ya gaishe shi cikin girmamawa kamar yanda ya saba, Dikko ya amsa shima cikin mutuntawa, dan a haife Alhaji ya haifi Dikko amma igiyar naira tasa yana k'ark'ashin Dikko kuma k'asan k'asa ma, dan ubangidan Alhaji na ainahi shima yaron Dikko ne na biyu, tou abinda yasa Alhaji yake kiran Dikko kai tsaye saboda yanajin dad'in yadda yake kularmishi da dokunan shi, shi yasa shi Dikko da kanshi ma ya anshi number Alhaji ko wata matsala ta taso ga dokunan shi, dan dama ubangidan nashi na farko kafin yasan Dikko wurin kula da dokuna ajiye shi Alhajin....

Alhaji yace mai gida kayi hak'uri don girman Allah wallahi jiya daka kirani ina cikin yanayin da bazan iya magana ba, cikin jimami Dikko yace meya faru haka ? Wato ranka ya dad'e ina cikin tashin hankalin dana zab'i mutuwa ma da rayuwa, salati Dikko yayi tare dayin murmushi domin shi yaji mugunta, sannan yace Alhaji duk dad'in duniyar wato tai maka d'aci ko ? Alhaji yace Eh wallahi ranka ya dad'e, Dikko yace tou Allah ya kyauta...

Da sauri Alhaji ya fara bayani wa Dikko dan yasan daga Allah ya kyauta kawai zai kashe wayarshi ne yasan baya doguwar waya, ranka ya dad'e wato wallahi wata yarinya ce muka d'an keb'e da ita, tou wallahi bansan yarinyar nan ta shirya sharri ba, ashe duk abinda mukayi ranka ya dad'e tana d'auka cikin waya ban sani ba, tou ta rik'e vidion sai wahalar dani takeyi tana ansar kud'ad'ena, yauma na bata kud'i kuma a police station nakai mata kud'in inaji wani ne ya d'aure mata gindi take iskanci a garin nan....

Murmushin mugunta Dikko yayi tare dayin kamar bai gane ba, yace wane irin vidio ne ? Gyara zama Alhaji yayi tare da goge zufa yace wato ranka ya dad'e harka daice irin wadda muka saba, Dikko yace wadda ka saba dai , wato ka samo daidai dakai ko ? Tou turomin vidion in gani ya fad'i maganar cikin sigar zaulaya, Alhaji yace ranka ya dad'e vidion fa irin na kafirawan nan ne masu d'aukar tsiraicinsu suna yayad'awa a duniya.......

Dikko yace tou banda abunka kace taje ta yad'a ba hada ita a vidion ba ? Alhaji yace ranka ya dad'e ina za'ayi wannan abun kunya tsiraicina a yanar giza gizo cewa tayi fa har "ya "yana zata tura su gani, Dikko ya gaggab'e da dariyar mugunta tare da kashe wayarshi, irin wannan abun Dikko kadai yake ma dariya a duniya, duk abin burgewa ko na nishad'i Dikko baya mishi dariya kuma baya murmushi idan kaga murmushin shi ko dariya yaji ko yaga k'eta, amma kai kana iya ganin abinda zai baka tausayi kayi kuka wallahi Dikko sai yayi mishi dariya saboda tsabagen shi cikakken mugune....

Cikin sanyin jiki Alhaji yaja motarshi ya tafi, Dikko kuwa saida yasha dariyarshi ya gaji sannan ya sake kiran Alhaji, bayan ya d'auka yace tou waikai kawai sai tayi maka vidio ? Alhaji yace Eh ranka ya dad'e Dikko ya sake shek'ewa da dariya sannan yace kai amma wallahi yarinyar nan tantiriya ce

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment