Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

gidanmu babu mai k'ara amfani dashi, duk wacce na zauna kusa dashi sai ya tashi, idan na fito mutane da sun ganni sai su dare....

Ko a familyn mu kowa baya shiga sabgata, kyara da tsana ake nunamin kamar mayya, ga mahaifiyata tayi tafiyarta garinsu, Baba bansan inda ya tafi ba, na rasa abinda yake min dad'i a duniya, banda mai bani abincin da zanci duk wanda naje wurinshi saiya koreni, azaba ta isheni na fara sana'a babu mai siye,

Koda naje na fad'awa Amisty abinda rayuwata take ciki da fyad'en da aka min amma ban fad'a mata Dikko bane ba, shawara d'aya ta bani, shawarar kuwa itace, sana'a d'aya zanyi inyi arzik'i ba H I V gareni ba ko kabari ce ni sai an shigeni,

Wace sana'ace ? Murmushi Amisty tayi tare da cewa zan kaiyi wurin uwar d'akina in yankar miki form zata baki lectures, lokaci guda zaki goge idonki ya bud'e zaki ga yanda maza zasu rik'a layi akanki,.....

Idan sunyi layin me zan basu ? Abinda kika bawa wanda yai miki fyad'e,...............







Taku a kullum.
*JAMILA MUSA*


03/08/2019

Ku kulle marecen ku da wannan..........

Ku biyoni sannu a hankali danji dalilin da yasa na kira wannan labari da *KWARATA* nazo kuma nayi masa in kiya da *KALU BALE GARE KU MATAN AURE.............*

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

*_Ina miki sannu da gajiya fatan kin koma gida lafiya ? Ngode sosai Allah ya bada ladar zuminci ya kuma hutar da gajiya RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE_*


🅿 ------ 7


Haba Amisty wannan ai ba mafita bace, Sultana kenan wannan kuwa itace babar mafita, domin mazan yanzu yawancin su yanda kika san kura da nama haka suke akan mata, d'aid'aikun su ne Allah yatsare su, sai kuma wanda suka had'u da jajirtaccin mataye.

Ni nan da kika ganni Sultana nasan abinda nakeyi kuma haka nasan irin mazan da nake tarayya dasu, banajin kunya asan ni "yar iska ce haka kuma bana b'oyon iskancina dan ta haka ne kad'ai za'a san ni karuwar gidan ce har na samu costomers.

Na samu dubban kud'ad'e ta hanyar karuwanci ban san adadi ba, dubu goma dubu ishirin ga kud'ina kuma inji dad'i abu na babu wanda yaji ba wanda ya gani, in rik'e babbar waya irin wacce nake so haka kuma in d'inka sutura da talakalmi da jaka, abu d'aya yasa ban sayi motar hawa ba saboda bana so Baba ya harbo jirgina da wuri amma badan babu ba,

Gyara zama nayi tare da tattara hankali na wurin Amisty, nace to ke mi yasa kike sha'awar karuwanci ne ? Murmushi tayi sannan tace gaskiya daga kalle kallen B F tun inajin tsoron abun har ya fara bani sha'awa,

Tsare ta nayi da ido sannan na tambayeta a ina take samu ? Tsoki tayi tare da cewa tambaya kamar "yar jarida, idan zakiyi na had'aki da wani mak'ocinmu sakaran banza baisan darajar kud'i ba, kije yai miki yaimin muci gaba da k'wak'wale banza tunda matar tasa sakaryar banza ce, kud'i gareshi na tashin hankali amma matar bata wani iya sauk'e hak'k'insa kinji yanda yake tona mata asiri ? Gata da kyau kamar ita tai kanta amma kyan ya zama hoto tunda mijinta ke neman mata.

Tou ke Amisty ya akayi kuka had'u kuma ya akayi yasan kina neman maza ? Hmm yarinya kenan ! Amisty tace min sannan taci gaba da cewa....... Gidan nake zuwa ita kuma bata da wani sirri bud'e take shegen surutu kamar an sakawa radio sabon battery,

Kullum naje sai ta bani labarin mijinta d'an jaraba ne, da a tunani na mafad'aci ne, sai nace mata niko sai naga yana da kirki sosai bashi da wata damuwa, sai tacemin ba fad'a na baki ba jaraba kullum zai nemeni daga dare zuwa asuba yakai sau biyar.

Cikin rashin fahimta na tambayeta, ban gane ba..... Tamin bayani na gagara fahimta shine ta fahimtar dani ta hanyar nunamin vidio a wayarta,

Tana kunna min ta tashi dan zuwa duba girki, ni kuma tuni dama na fara iskanci na amma a lokacin ban dad'e da farawa ba, dan haka tana tashi na sace number mijin a wayarta, tunda iskancin kawai nakeyi a lokacin amma bansan fa'idar abun ba......

Tana madafar abinci naje na bata wayarta nayi mata sai anjima, ina fita ba gida na tafi ba kawai na sharce wurin uwar d'akina, wadda nace miki zan had'aki da ita kema ta mayar dake gahurtacciya kuma abun kwatacce a harkar barikanci. To ita naje ta sake bani haske a harkar, dan haka ina dawowa gida na fara tura masa sak'on gaisuwa ta whatsApp.

Shareni yayi bayan yaga sak'on baiyi reply ba, ni kuma na nace na kwakwafe banyi zuciya ba naci gaba da aika sak'on, kusan sati biyu babu wani bayani, dan haka na fara tura mishi da irin vidios in B F da nake kallo na tura mishi masu zafi da yamutsa tunani dan wani lokaci sai yakai 1:30am yana online.

Wai wace ce ? Ya tambayeni bayan yaga vidio inyi, nima basar wa nayi ban bashi amsa ba na sauka online, ina sauka yana kirana a waya..... Murmushi nayi a bayyane nace ashe kuwa mayen ne ? Mu zuba dani dakai..... Kuma ban d'auki wayar ba,

Text ya turomin ta inbox, kamar haka....

_Wai wace ce ke ? Ki hau Online muyi magana don Allah !_

_Ai nayi fushi nima....._

Shine amsar dana bashi,

_Kiyi hakuri don Allah ki hau online muyi magana_

Shareshi nayi na kashe wata duka nayi kwanciyata...... Saida na kwana biyu wayata na kashe, ranar dana bud'e wayar kuwa sak'onsa ne yai ta shigo babu iyaka, wasu na duba wasu kuma na share.

Ko online dana hau sak'unan sa birjik, dan haka naci gaba da tura vidion iskanci, kuma idan natashi sai tsakar dare nake turawa, jakar tana can tana bacci,

A hankali ya saba dani, amma ban fad'a mishi kaina ba, yau da gobe bata bar komai ba, har na tambayeshi dalilin da yake kai tsakar dare yana chat, kawai cewa yayi yana da damuwa da iyalinshi, bata bashi hak'k'inshi wai tace yawan sex da mace yana sa tayi saurin tsufa....

Amsar dana bashi itace, ya barta can ta k'unshe abunta har yayi wari, indai yana da buk'ata tou ni zan rik'a bashi nawa duk lokacin daya buk'ata, kinji shine fa idan bata nan nake zuwa gidan muyi komai namu cikin sirri.

'Dan gajeren murmushi nayi sannan nace Amisty kenan...... Idan dai har bin maza zanyi tou pha tabbas babu macen data bini ilimin iskanci, kinji hausa suna cewa d'an gado saiya zarta, nawa ba kalar naku bane, saboda naku iskanci mai arha kukeyi, tunda har banji kunyar mahalicci ba na tsab'a masa babu abinda zaisa naji kunyar wani banza,

Hannu na nakai saitin prvt prt ina sannan nace idan dai wannan ne abinda maza suke buk'ata ni kuma duk saina halaka da yawansu dashi, kallon Amisty nayi sannan nace, babu wanda ya koya min saishi d'aya, ban fara ba shine ya fara, ban iya ba yayi da k'arfin bala'e, ba'ayi da zafi yayi min saboda k'eta, ke Amisty karki manta a caca aka sakani duk saboda talauci idan har ban tara kud'i ba ta sanadiyar karuwanci nayi suna a duniya lallai ni ba d'iyar Aliyu Binnaa bace,

Tunda har ya bada budurci na saboda san duniya ni kuma zanci gaba da basu su bani dan na tara mishi abunda ya buk'ata,

Amfanin zunubi roma Amisty, tunda zanyi kawai zanyi amma babu fashi, saidai ki sani akan sab'awa Allah babu namijin daya isa yaga ko pant ina da naira dubu goma ko ishirin, kud'in shigar ciniki naira dubu d'ari ne shine harajin da na yankawa duk mai sha'awar yin iskanci dani, idan kuma zaka shiga gidan dubu d'ari biyar, idan har haka yayi tou na siyar idan haka baima mutum ba tou ya tattara buk'atarshi ya koma,

Amma tabbas duk namijin da yace zaiyi, saiya bada dubu d'ari, idan na yadda yayi idan kuma ban amince da dashi ba zai koma, amma dubu d'arinshi tazo kenan kamar gawa tazo lahira.

Ki sani bana iskancin wahala, kuma bana iskancin cini incin tuwo, zan zauna gida bazan bar k'asata ba amma zan zama tarihi a duniyar nan, ki fad'awa uwar d'akin taki cewa ina gayyatar ta shigowa k'ungiyata da nake fatan kafuwarta daga yanzu zuwa ranar da numfashina zai k'are, ki sanar da ita cewa ni banda ilimin boko amma akwai na tsoron Allah kuma sanin ilimin bazai hanani bujire masa ba, nasan hukuncin mazina daga wacce tayi aure har wacce bata tab'a ba, hukunci kisa ga masu aure, bulala ce ga irinmu "yan mata, to anan duniya zan sameta ko sai naje can ? Duk na sani, kuma nasan a ina ake amso su, mik'ewa tsaye nayi tare da dafa wa Amisty kafad'a sannan nace bana buk'atar shiriya, kuma bana so a tausaya min, daga yanzu zuwa lokacin da zan gama kammalawa........, *BARIKI ASSALAMU ALAIKUM*

Murmushi nayi sannan nace wa Amisty suna na , MARYAM ALIYU BINNA, na bud'e k'ungiyata daga yanzu, idan kina sha'awar shiga bisimillah, na barki lafiya......... Ina fad'in haka ban sake magana ba na juya na fita daga gidansu......

Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, shine abunda Dikko ya fad'a adaidai wannan lokacin, tare da cewa Allah na tuba.......... 🙏🏻

Ina fita na tare napep nace malam ka kaini kambarawa, can ne anguwar da muke zama. Abinda zan bashi ya fad'amin bayan ni ban tambayeshi ba,

Shiga nayi yaja muka tafi, duk inda yaga fasinja ya tsaya zai d'auka cewa nakeyi muje bana so ka d'auki kowa, har muka iso filin gidanmu da yasha ado da darnin kara......

Ina fita na wuce abuna, malama kud'in fa ? Juyowa nayi tare da ce masa nawa ne ma ? 250, murmushi nayi tare da kallonsa k'asa da sama sannan nace naci na Allah bud'a, da kuma tsarinka yamin dana baka wani abu ka kalla sai kayomin ciko,

Fitowa yayi daga cikin napep d'in yana fad'in ke zanci uwarki ko ki bani kud'ina, murmushi nayi tare da cewa tayi maka tsufa...... Ina fad'in haka nayi gaba abuna, haya haya ya fara hayani tare da ci gaba da d'uramin zagi irin na "yan tasha. Ja nayi na tsaya ba tare dana juyo ba.

Saida ya gama zage zagensa sannan naci tou ka zagi kud'inka, kuma naci na cinyesu duk garin nan inga mai amsar su wurina, kaina yayo da zumar kaimin duka, nace ka dakeni ka dako ma kanka bala'e da kabi ta hankali daka tsira amma tunda iskanci ne abun dani dakai dan iska ka fasa,...

Wani mak'ocinmu ne yazo wucewa, na fashe da kuka tare da cewa malam lawal kaga wannan shine yayi min fyad'e, dama nace muku ina ganeshi, yana jin zance fyad'e ya ruga zai nufi napep malam lawal ya fara a kawo d'auki, a tak'aice dai kafin ya bar anguwar bayan yaci shegen duka saida aka fasa mishi gilashin mota na gaba sannan suka k'wak'ule masa cini kin da yayi yabar anguwar a wahalce......

Yana tafiya na shiga gidanmu natashi masifa cewa sai an siyar da filin nan an bani hak'k'ina, yanda na birkice lokaci guda ya bawa al'ummar anguwarmu mamaki, an nuna min cewa ayi kud'i wa filin sai a fitar min da kud'ina su kuma su zauni fili, nace bansan wannan zance ba duka nake so a siyar uban kowa ya kama gabanshi,

Tambayata akayi me zanyi da kud'in ?Babu kunya bare shakku nace, karuwanci zan fara shi yasa nake so a siyar a bani kud'i na naje na siyo kayan da zan zama karuwar......

Gaba d'aya wurin salati aka d'auka ! Yayin da wasu dattawa suka fara sulalewa suna barin wurin, ni kuma na shiga cikin gidan naci gaba da yanyara ruwan iskanci na san raina,

Bayan kwana biyu mak'ocinmu ya kawo kud'in filin gidanmu domin shine ya siya, aka raba aka bani nawa, sallama nayi musu tare da cewa kuyi k'ok'ori kuna ziyarta na domin inaji a jikina nan da kwanaki kad'an zanyi muku wahalar gani.......

Babu wanda ya bani amsa, murmushi nayi tare da tafiyata dan dai nasan nasha dasu.... Nima bak'in ciki yasa nace duka filin za'a siyar dan kar na shiga gararin rayuwa ni d'aya kowa ya lalace dan zuwa yanzu gaba d'aya na koma kamar wata kafira dan babu sauran tausayi a zuciyata......

Bakin titi na fito na samu mai abin hawa, inda zanje ya tambayeni........... Shiru nayi na wani lokaci sannan nace masa gidan karuwai zaka kaini,

Kallona yayi sosai sannan yace ina ? Nasan yaji sarai iskanci ne yasa ya sake tambayata, dan haka nace gidan da "yan iska ke zama wanda suka gagari iyayensu,

Jinjina kai yayi amma baiyi magana ba, ko har yanzu baka gane ba ? Na tambaye shi ? Shiru yayi baicemin komai ba, ni kuma nace tou ina nufin inda maza da mata ake had'uwa ayi bad'ala, kallona yayi cikin yanayin tausayi sannan yace ke yarinya ki rufawa kanki asiri rayuwar bariki tafi k'arfin ki, aure shine yafi dacewa da rayuwarki,

Kai malam zaka kaini ko kuwa dai ? Tashin napep inshi yayi tare da cewa Allah ya shiryaki, amma nikam bana kaiki gidan karuwai, tsoki nayi tare da cewa jeka d'an munafika shege marar rabo... Gaki nan katuwar marar rabo duniya da lahira, indai mazan bariki ne sai sun kasheki murus kin kasa morawa rayuwarki, dan mace bata kashe namiji saidai ya kashe ta, baki san dafin namiji ba da baki hayewa mazan zamani ba kin koma gida, basu da imani haka kuma basa tausayi tunda sun san kud'insu suka biya, tou fa basa sassafta wa kamar mai gidan haya ne da "yan haya, tunda sun san ke ba tasu bace hawa d'aya zuwa biyu zasu tashe ki aiki kina kallon maza suna kallonki amma dan uwarki bazasu ciwu gareki............ Yana kaiwa nan yaja napep inshi yayi gaba.

A bayyane nace komi zakace kaje kace saina zama cikakkiyar karuwa, kuma ni karuwanci nawa mai aji zanyi ba irin wanda kowa yake tunani ba.

Bai dad'e da tafiya ba na samu abin hawa, kuma na fad'a masa gidan karuwai zai kaini, yace min na ina gidan karuwai d'in ? Nace inda fek'ak'k'un suke can zaka kaini, shigo muje, shiga nayi yaja muka tafi.........







05/08/2019


⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*


*_Ku nemi naku fitowa ta farko daga shahararriyar kungiya mai san farin cikin makaranta wato BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION, sabon salo ne daga shahararrin marubuta biyu, MAI JIDDA daga alkalamin MARYAM MUHAMMAD HASSAN, MAFARKIN NANAH, sabon sauyi na SA'ADATU LAWAL maman ilu, kar ku sake ku bari a baku labari......_*

*_ZAINAB ATTAHIRU B ' K sakonki yazo gareni ngode sosai ina miki fatan alkairi, ki kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali har a busa kaho............_*


🅿 ------ 8


Tafiya mukeyi daga ni harshi babu wanda yayi ma wani magana, saini da a zuciyata nake ta addu'a, Allah na rok'eka ka bani farin jini ka zubamin kwar jini kasa na rik'a bud'ewa mutane ido duk wanda yayi ido dani, Allah kasa wannan kyawun nawa ya zamar min babban jari, kasa nayi suna sosai a harkar karuwanci.

Tafiya mai nisa mukayi har muka iso k'ofar gidan, sai yanzu yayi magana cewa ranki ya dad'e anzo, ba tare dana fito ba nace masa, malam ya sunan anguwar nan ne ...... ?

Sanin da nayi ma anguwar a da yanzu karuwai sun canja mata suna, gidan na sani ba sunan wurin ba, ki sauka ki bani kud'ina sauri nakeyi.

Ina k'ok'arin fitowa nace kasan kana sauri ka bari aka haife ka ? Ka iya tafiya domin dai ni d'abi'ata idan nahau abin hawa gaskiya bana iya biyan kud'i, amma Allah ya taimaka sauka lafiya !

Fitowa yayi daga cikin napep in ya fara ke bansan rashin kunya bani kud'i na ko in wulak'anta ki a wurin nan, d'an gajeran murmushi nayi tare da cewa banda haukar ka wanda ya fito bariki ai baya tsoron wulak'anta, ai ta wulakanta ta kare tunda har na fito daga gidanmu na taho yawon karuwanci........!

Shiru yayi ya rasa abin cewa, dan haka nace ko kana da sauran magana ? Jinjina kanshi yayi tare da cewa jeki kya gani...... Dariya nayi sosai irin ta cikakkin "yan duniya na kashe dariyar da rangad'a gud'a, sannan nace shege kaji uwar bari ko ?

Tou babu uwar da zan gani dan duk wani gagararren d'an iska dake fad'in garin katsina nice uwarshi nice ubanshi, duk wani kangararren dan iska da "yar iska da iyayensu sukace jeku kun gani, to wallahi idan suka taho ni zasu gani.....

Sauk'i ya nemar min sannan ya koma cikin napep inshi, yana k'ok'arin tashin ta nace malam dakata, tsayawa yayi yana kallona, kana da waya ne ? Rik'e waya ai sai ke da kika fito neman haramun, to naji ba komai, kadai ganni sosai ko ? Kuma zaka iya ganeni gobe idan mun had'u, tsoki yayi sannan yace taya zan manta da fuskarki azzaluma kawai, yawwa ina so dama ka gane ni gobe idan ka ganni, ni suna na Sultana idan kayi gaba ka bada labarina dan ina san cikin d'an k'ank'anin lokaci suna na ya zagaya kaf fad'in garinnan, sauka lafiya.......... ! Ina fad'in haka na shige gidan karuwai,

Tun a zauren gidan na farajin kuruwar wata karuwa, karuwinta ne yake dukanta da belt kamar uba yana hukunta d'iyar sa, babu ji babu gani yana dukanta yana cewa dan ubanki sai kin bar gidan nan, wallahi na gama zama dake, d'an murmushi nayi a bayyane nace Allah sarki duniya yayin da wasu ke shigowa yayin wasu ke fita,

A hankali nabi gidan da kallo ga mutane nan iri iri, yayin da wasu ke caca, wasu na lido, wasu na shan sigari yayin da wasu ke kwance saman jikin maza babu kunyar Allah bare tsoranshi, wato abinda dai na lura duk abinda kake so shi kakeyi babu mai ce maka dan mine ne ......?

K'arewa gidan kallo nayi sosai, d'akuna ne k'asa da sama, bene ya zageye k'asan gidan yayi masa rumfa sai yanayin gidan ya tabbata kamar irin hadari ya taso. Wani irin ihu na zabgaga tare da kashe ihun da gud'a, wanda haka yayi sanadiyyar jawo hankalin duk wanda ke cikin gidan na waje da wanda ke d'aki babu wanda aka bari kowa saida ya fito....... Kirari na fara kwararwa bari ba tare dana kalli dandazon mutanen dake kallona ba.

Bariki ba'ayi miki tilas babu wanda ya rako wani kowa da k'afarshi yazo kuma in yaji wuya shi zai koma, baki duba mai kyau ko mummuna, haka kuma babu ruwanki da maye ko mayya mai lafiya da mai cuta duk wanda yazo kina da masaukinshi, baki san inda kowa yake ba amma kowa yasan inda kike, gani nazo ki sakamin albarka, baki da tabbas bariki haka nima bani da tabbas, matsalar ubace ta kawoni amma ina tare da had'ari guda d'aya, bana san shiga sabgar kowa karki sake ki bari wani ya shigo rayuwata, ilimi nazo d'auka a cikinki amma ni nafiki rashin tabbas, ina da masaukin kowa amma banda na mata.....duk namijin da uwarshi ko ubanshi yace jeka ka gani tabbas idan yazo ina da masaukin shi nima,

Kija da'irarki ki bani tawa, bana shan sigari bana cin goro, abu d'aya ya kawoni shi zanyi na koma, bansan bincike haka kuma bana san bin kwakwaf, kar ku sake naji bakin wani nan, idan ba amsa zai bani ba, kuma magana d'aya nake so ta fito bakinku akwai ko babu, itace amsar da nake so a bani, tambayata itace kawai d'akin zama ko nayi gaba.........?

Wani daga can saman bene yace ke "yar cakulkula dake har kin san dad'in namiji ? 'Daga kaina nayi sama na kalleshi sannan nace daga ganinka gidan haya aka haife ka, kaine matsala da kanka bakaji abinda nace ba ? Akwai ko babu kawai nake so naji.

Daga bayana wani yace ki bashi amsar tambayar shi mana sai mubaki taki, murmushi nayi sannan na d'aga kaina sama na kalleshi tare da cewa, duk tayar abun hawa sunanta taya, amma kaga tayar daf tafi ta jirgi girma amma abinda jirgi zai d'auka daf bata iya d'auka, jirgi ya d'auke ka kuma ya d'au kayan ka, kamar dai kai kaga ga
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

6 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment