Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

albashi duk ƙarshen wata, dalilina kuwa na ɗaukarsu duk yana cikin labarin, sunsha kitso irin na ɗiyan kafirawa kallo ɗaya dai zakayi musu ka tabbatar sunsha iskanci sun ƙoshi...

Saida na gama kallesu tsaff sannan na fara nazari da tunani , na farko dai zamanin ga ya canja rayuwa bata tafiya dole saida ilimi, waye zan samu mai amana da zai riƙa karantawa rubutuwa da fassarawa idan anmin turaci, babu shi zuciyata ta bani amsa tare da cewa karki sake ki yadda da matan bariki dan basu da amana...

Kallon Amisty nayi tare da cewa karanto min ina saurarenki, miƙomin takardar tayi , murmushi nayi bance komai ba na ansa, biro na ɗauka na juya bayan takardar nayi rubutu da labarci kamar yanda nayi a police station miƙa mata nayi bayan na gama rubutawa sannan nace haɗa dukansu ki karanto ina saurarenki...

Zazzare ido ta farayi ta ƙurawa jaddawalin ido, alifun kanshi idan zaki kasheta bata iya karantawa ba, ganin ta kasa nace tou ki kiyayi kanki da duniya duk baiwar ki wani yafi ki, kece kika rubuta kuma kece zaki yaɗa ba kowa ba, karki damu basai naji abinda ke ciki ba, kije kawai....

Ku tashi muje na faɗi maganar tare da miƙewa tsaye, ɗaki na koma na ɗauko gyale na sannan na fito, gaba nayi zugar daba ta da tasha suka biyoni baya harsu Nana ba'a bari ba, ina gaba suna bayana "yan daba kuma suna gaba cikin siga mai kalar bada tsoro,

Gidan da zan siya a cikin anguwarmu mukaje dubawa, ƙaton gida ne sosai akwai ɗakuna birjik ɗaki yakai goma sha ukku, sai bayi guda biyu sai baranda inda ake dafa abinci, amma gidan gidan ƙasa ne irin tsufin ginin da can can, akwai yalwataccen filin tsakar gida...

Nidai gidan yamin sauƙi gaskiya ko dan ina matse na siya ? Miliyan biyu aka masa kuɗi babu gudu babu ja baya gaskiya yayi arha dan da a bakin titi yake bazan iya siya ba , daren jiya na bada miliyan ɗaya da rabi, nace zan cika sauran yau idan Allah ya kaimu....

Shine muka zo gani da kowa , gaskiya sun nunamin farin ciki sosai kuma basu nunamin hassada ba, bayan mun gama dubawa muka fito, tunda muka fito yanayin yadda naga anguwar tayi shiru ya taabbatar min Dikko ya shigo...

Shine kuwa ɗan iskan , ya fito daga gidan dokunan shi na anguwarmu da yake daga get in gidan zaka iya hango komai na cikin anguwar idan aka shigo santar kuma gidan dokunan Dikko yake kallonka,

A tsiyace ya fito kamar yadda ya saba, duk tawagata suka koma da gudu baya suka kauce daga saman hanya yayin da ni kuma na shigo hanya hankali kwance Amisty ta taho da gudu zata jawoni wani mutum ya riƙeta dan a ganinshi biyu babu za'ayi tunda dai ni na tafi sunamin addu'a Allah ya jiƙana, ihu Amisty ta farayi tare da cewa Sultana don Allah karki biye wa zuciya ki dawo ko ki gudu bana so ki mutu yanzu wayyo Allahna, kowa duƙar da kanshi yayi yayin dana tsaya cas kuma Dikko ya sheƙo da gudun tashin hankali, wallahi da bani bace ko wacece sai Dikko yabi ta kanta ya wuce babu abinda ya dameshi...

Gab dani ya taka wani irin wawan birki ya fito cikin tsananin ɓacin rai ko mota bai tsaya rufewa ba , hannushi ya ɗaga da niyar marina kuma ko meye ya hanashi ya mareni Oho, ganin ya juya zai koma mota nace Allah ya auna maka arziƙi yau dasai nasa anyi maka fiɗa irin wacce akewa raguna, daka takani ko ka bigeni dasai naga ko waye ubanka a garin nan...

Uhum yace tare dayin gajeran murmushi da gefen bakinshi sannan yace ake yarinya ce a tunaninki kama nayi miki da ɗan wa a garin nan ? Dake da babanki da kowa naki da kike taƙama dashi talakawan mahaifina ne , ni kuma abinda na ɗauki talaka takalmi na ne zan takashi yayin da nake sha'awa in kuma cire na jefar a duk lokacin dana gaji da ganinshi, ke abinda na ɗaukeki baki da banbanci da dabbar layya a wurina ina kiwonki ne kafin ranar da zan yanka ki , abinda yasa kuma banbi takanki na wuce ba idan na kamaki zaki basu labari...

Murmushi nayi tare da cewa duk takalmi takalmi sunanshi amma ko a cikin takalmin wani baka sakashi yayi maka daidai, talakawa suna taku amma kai da mahaifinka bata tasu kuke ba, duk wadda yace kayi takanshi ne baka zo ba, ba'a saka ka kayi ba'a saka ka daina zakin roba dana sanin mafarauta mugu ɗan gidan mugaye kana mugunta amma kana daɗa suna azzalim baƙin cikin talakawa, kafin ka gama ciwo na ni na gama naka ka saurareni ina dawowa ƙarshen shekaru biyu masu zuwa nan gaba nice maganin tsagerancinka....

Ina faɗin haka ban saurari abinda zaice ba nayi gaba na shige cikin gidanmu da muke haya , tafiya nayi irinta in ka isa wannan ma ka sayeshi....

Murmushin mugunta yayi mai nuni da na gama dake yarinya zaki nemi Dikko ruwa a jallo, juyawa yayi ya koma mota ya fita daga cikin anguwar...

Ban daɗe da shigowa gida ba su Nana suka shigo harda ƙawar Amisty wacce muka haɗu da ita police station tayi cikin shege da aurenta, ɗaki suka sameni ina waya da Bello dan tunin duniya na turawa matarshi hotuna anyi tashin hankali na idon duniya kuma shima hankalinshi ya tashi ya yadda zan iya turawa media hotunan, ya yadda zai bayar da kuɗin anjima bayan sallah isha'i.

Sannu nayi ma kowa bayan na gama waya nace ku zauna mana, wuri kowa ya samu ya zauna, kallon ƙawar Amisty nayi mai cikin shege sannan nace sannu hajiya, murmushi tayi tare da kallon ƙasa cikin yanayin jin kunya,

Ɗan kauda kaina nayi gefe tare da cewa ya akayi da cikin ne ? Ba tare data kalleni ba tace... Wallahi har yanzu bai yadda ba, murmushi nayi tare da cewa bariki da ciki ko goyo wahalalliyar bariki kenan , bariki da tsarin iyali magani ko allura halaka ne saboda baki gwada mahaifarki ba kika tabbatar kina aihuwa ko bakyayi , kallon su Amisty nayi sannan nace tashin farko dai kowa ta nemi gishirinta ta saka a jaka yayin da buƙatar namiji ta gama kammaluwa akanki ki zuba gishiri a bakinki sai ki kora da ruwa,

Nana ta tambayeni maganin me ? Kallonta nayi ido cikin ido sannan nace maganin hana ɗaukar ciki, waye ya faɗa miki haka ne ? Murmushi nayi tare da cewa wani feƙaƙƙen dan bariki mai bariki cikin gidan iyayenshi , tunda kuwa har yasan gishiri yana hana ƙaramin ciki zama a cikin mahaifa ai kinsan ya gogu a harkar bariki.

Dariya kowa yayi tare da cewa wannan dai ai mugunta ce gishiri ai saida yasa maka cuta , ba tare dana kallesu ba nace shigar wata cutar itace take kore wata, Allah dai yasa mu fita bariki lafiya , kowa ya amsa da amin...

Fira dai mukaci gaba dayi daga baya A ` i tace bara suje ita da Saude su anso mukullen shagon da muka kama haya tasan zuwa yanzu sun kammala fenti , sai sun dawo nayi musu suka fita daga ɗakin yayin da Nana da Karima suka fita suma, aka barni dani da Amisty sai Hafsa da ƙawar Amisty matar aure...

Kallona Hafsa tayi tare da cewa uwar ɗakinmu idan babu damuwa nikam ina so na tambayeki. Hankalina yana kan wayata ina ganin rubutun da d c o ya turomin nace ina saurarenki yayin dana kanga wayana daidai saitin bakina nace ni aiki nakeyi ko ka kirani a waya, ko kuma kayomin voice note idan na kunna saina saurara , ina faɗa na tura , yayin da Hafsa tace wai miye tsakaninki da DK ?

Ajiye waya nayi a gefe na sannan na tattara duk hankalina da natsuwa ta wurin Hafsa nace idan na faɗa miki abinda DK yayi min ke kanki sai kinci ubanshi da yake taƙama dashi yana ma mutane iskanci saboda shi , yau ya taɓo ubana yace talakan babanshi ne , nima kuma na taɓo babanshi a cikin magana na, nuna Amisty nayi tare da cewa duk wanda nace ya faɗamin waye uban Dikko a garin nan ba'a bani amsa idan zaki faɗamin Dikko ko waye ubanshi zan faɗa miki abinda ke tsakani na da Dikko....

Hafsa tace Gwamnan garin nan shine uban Dikko, shiru nayi banyi magana ba Hafsa taci gaba da cewa dole sai kunyi haƙuri sannan kuma kunyi ma Dikko uzuri soyayyar da ake nuna masa a gidansu da yadda ake tsoron mishi faɗa yasa yake ganin duk abinda yayi daidai ne a rayuwarshi , wallahi ba'a dakawa Dikko tsawa ba'a masa kallon banza domin mahaifinshi gani yakeyi kamar duk idan akayi masa zai mutu ne , ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗora akan Dikko yana mishi soyayyar da duk duniya babu wanda yake ma irinta a rayuwarshi , fitar da Dikko yake yi da duk wannan iskanci da wulaƙancin da yakeyi ubanshi baisan yana fitowa ba , yasan dai ya baro ɗanshi gida...

Cikin jin haushi na kalli Hafsa tare da cewa nikam bazanyi haƙuri ba kuma bazanyi masa uziri ba , can gidansu ya zama dole suyi masa duk abinda kika lissafo amma badai ni ba , wallahi ko Dikko zai mutu saina tozarta shi , saina wulaƙanta mishi rayuwa a garin nan , ki jira zaki ga yanda zanci uban da ya haifi Dikko saina maida shi abun tausayi da kwatance uban nashi kuma duk daren daɗewa saiya gama gwamna ya sauka tunda gidan gwamnati ba gidan ubanshi bane ba...

Shiru Hafsa tayi bata sake magana ba , bayan wani lokaci tacewa Amisty ku tashi mu tafi , gaba ɗayansu suka fita tare da cemin sai Allah ya kaimu , ban basu amsa ba na ɗauki wayata naci gaba da abinda ya dameni.

Hafsa kuwa kamar ubanta na zaga , tana shiga mota ta fashe da kuka tare da kiran wayar Dikko har ta gaji ta haƙura bai ɗauka wayar ba , daga baya ta yanke shawarar tura masa text duk zagin da nayiwa Dikko komai dana faɗa saida Hafsat ta rubuta ta ƙara da nata dan sharrin ya tafi daidai , bayan ta gama ta tura mishi. Sannan taja motar ta suka bar ƙofar gidanmu...

Su Hafsa basu daɗe da tafiya ba su A ` i suka dawo kuma sun tabbatar min cewa shago yayi yanda ake so an tsara shi gwanin burgewa , naji daɗi sosai suma sunyi farin ciki idan Allah ya kaimu gobe lafiya zamu fara fita aiki , saida akayi sallah magrib sannan suka tafi gidajensu.

Bayan sallah isha'i kamar yanda Bello yayi alƙawari ya kawo min kuɗi , a gurguje ya bani ya tafi dan yacemin suna da wasa jiranshi akeyi , a daren nakai cikon kuɗi kamar yanda nayi alƙawari zan bayar a gaban shedu aka rubuta takarda aka bani ....

Umar ne durƙushe a gaban Dikko cewa mai gida kaga dan Allah tunda kazo gashi har zaka koma gobe don Allah kafin ka tafi ka taimaka ka siya gidan wallahi matar tana buƙatar taimako,

Umar yana magana amma hankalin Dikko yana kan saƙon Hafsa , a fili yayi dariya tare da cewa rigima kenan Allah ya baki sa'a akan duk wani kudirin ki akaina An mata , murmushi yayi sannan yace Umar ni babu abinda zanyi da gida , amma nawa ne kuɗin sai in bashi ayi mata aikin...

Ba'a mugun sarki sai mugun bafade , kuma wani abu za'a bashi a cikin kuɗin gidan idan an siyar dashi, dan haka ya gyara zama tare da cewa mai gida dan Allah tunda dai yafi so ka siya ka siya ɗin kawai , kila gidan ne ya gaji dashi tunda da taimakon yake so da zaice ka taimaka mishi.

Dikko yace tou tunda yanzu yayi maganar siyar da gida ai kowa yasan taimako yake nema insha Allah kafin in tafi zan baka ka bashi , Umar yace mai gida abinda yasa nace ka siya gidan kusa da gidajen daka siya ne kaga idan ka siya sai shima a rushe maka a haɗe wuri ɗaya,

Baiyi magana ba sai ƙara kallon text in Hafsa yake yi yana mamakin ɗabi'u irin na An mata da ba gobe zai tafi ba dasai ya ƙara zuwa ya jawota faɗa kuma yanzu dare yayi dasai ya firgito mata hankali , lallai zai haƙura ya riƙa waya da Hafsa dole kodan dan ya riƙa jin halin da Sultana take ciki.

Umar yace mai gida kayi shiru baka ce komai ba , kallonshi Dikko yayi tare da ajiye wayar shi gefenshi yace wato so kake in ƙara baƙin jini ko ? Cikin rashin fahimta Umar yace wurin wa zakayi baƙin jinin ne ? Ajiyar zuciya Dikko yayi tare da kwantar da bayanshi jikin kujera lumshe idanuwanshi yayi cikin shauƙi sannan yace wai An mata ne tace zataji min mutunci bayan shekaru biyu masu zuwa,

Ya ƙarasa maganar yana murmushi , Umar yace haba ranka ya daɗe ina ma zata ganka ? Kafin shekaru biyun masu zuwa kayi mata tazarrar da baza ta sake ganinka ba har abadan duniya , kai babbar ƙaddara ce da kayi nisa da tazara ga duk wani ɗan ƙaramin sakarai , ka siya gidan kawai ka manta da sha'aninta me zata iya maka ne ? Buɗe idonshi yayi tare da cewa baza ta iya min komai ba kuma badan inajin tsoron tayimin ba kawai dai tana bani tausayi ne...

Umar yace bata da kunya ta raina hankalin mutane ka daina tausayinta shegiyar kanta ce , Dikko yace ba itace shegiya ba nine shegen barni dai da Dikko take wasan , zan bada kuɗin gidan na siya , wani irin farin ciki Umar yayi tare dayi ma Dikko godiya saida ya koɗashi sosai sannan ya fita,

Fitar Umar Dikko ya ɗauki waya ya turawa Hafsa saƙo cewa shifa baima gane yarinyar da take magana ba , tayi masa bayani na yadda ya sani ta tuno masa asibiti da dai duk wani abu daya shiga tsakanina dashi Dikko yace sam bai ganoni ba amma idan tana da hotona ta tura mishi ,

Hafsa tace bata da hotona amma zamu haɗu da safe insha Allah zata ɗauko masa ni ya kwantar da hankalinshi , Dikko yace ai dama hankalinshi a kwance yake amma ya zama lallai zai koyamin hankali ,

Tunda gari ya waye muka sha gayunmu kamar yanda muka tsara , motoci biyu aka ajiye a ƙofar gidanmu ɗaya ta Hafsa ɗayar kuma tawa ce sai kenap ɗaya wacce "yan dabana zasu riƙa amfani da ita kuma ni na siyi ,

Dukanmu a ƙofar gida muka fito , muna ƙoƙarin shiga mota mai gidanmu da muke haya yazo bayan mun gaisa yace ya siyar da gidan nan saboda haka duk abinda muke so zuwa jibi mu kwashe kayanmu,

Cikin ɓacin rai nace wai miya sa kuke abu babu adalci a rayuwarku ? Kai kuma nawa ya baka ya siyi gidan dan nasan za'ayi haka tunda har yaga gidan dana shiga nasan wallahi saiya siya , sakaran banza matsiyaci dashi tou idan ka ganshi ka faɗa mishi nayi gidan zama idan yanajin shi wani mai kuɗine yazo ya sayi anguwar nan duka...

Ina faɗin haka nace ku shige muje , gaba ɗayanmu kowa ya shiga mota , Hafsa ta tuƙa nata , tawa kuma driver na samu saboda har yanzu ban iya mota ba , zugar daba ina kuwa suka shiga napep muka tafi, ashe duk abinda na faɗa Hafsa vidio tamin ta turawa Dikko dan ya gani da idonshi ya kuma ji ina faɗa da bakina , ni kuma bansan anyi ba tasan idan ya gani da idonshi dai zaici mutunci na yadda ya kamata bansan abinda ke cekin zuciyar Hafsa akaina ba...




28/08/2019



*JAMILA MUSA* 🤙🏻


⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 21


Cikin farin ciki muka isa bakin shagonmu wanda yasha fenti kuma aka gwagwaɗa masa tambarin *kwarata* , tsayuwarmu da fitowarmu shine ya jawo hankalin al'umma masu wuce da wanda suke zaune saboda munzo da sabuwar shiga mai matuƙar bada al'ajabi a karon farko da ta zama abin kallo ga jama'an gari...

Takardun da aka gurzo wanda yake ɗauke da tallar karuwancin mu nasa "yan daba suka raba titi biyu duk motar da zata wuce aka ci gaba da basu babu sauƙi babu sauƙaƙawa !

Bakin shago mu mata muka koma muka jera layi amma babu wacce ta zauna tsaye muke , Nana da Karima suna daga gefe suna kallon ikon Allah ,

Waya Hafsat ta fiddo ta fara latse latse daga baya kuma sai naga ta koma gefe guda tana waya , ta ɗauki tsawon lokaci bata gama wayar ba haka nan kawai naji na tsargu da wayar , bayan ta gama sai ta goge number data kira...

Ƙurawa Hafsa ido nayi harsai data kama kanta , tabbas akwai cuta a tare da rayuwar Hafsa akwai abinda take shiryawa ko kuma take so ta aikata idan kuwa na ganota da wani laifi na cin amana babu abinda zai hana na tona mata asiri,

Yana gama waya da Hafsa ya buɗe saƙon da tace ta turo mishi , ɗan soɓaro baki yayi irin na sakatattun "ya "ya sannan ya cire vidio ya ɓoyeshi a gellery vault bayan ya gama gani...

Saman kujera ya zauna ya saka takalmi har yanzu bakinshi a soɓare yake , saida ya gama sannan ya kalli Al ' Ameen yace mu fara zuwa ta wurin An manta sannan mu wuce don Allah ,

Al ' Ameen yace mai gida da Allah ka fita hanyar yarinyar nan , murmushin Dikko yayi sannan yace wallahi sai anje idan baza kuje ba sai ku jirani ina dawowa , yana faɗin haka yayi gaba , Al ' Ameen biyo bayanshi yayi ƙaramin yaron daya girma kawai zai riƙa juya su dandai suna ƙasansu...

Da sauri ya wuce Dikko ya buɗe mota , ɗan ɓata rai Dikko yayi sannan ya shiga ya zauna tare da kwantar da bayanshi saman lallausan kujeran motar , wayarshi ya ciro yayi mata kyakkyawan riƙo da duka hannayen shi biyu , sannan ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya yake faɗawa Hafsat yana zuwa yanzu babu daɗe wa zaizo mata bankwana !

Wata irin kururuwa Hafsa tayi ta farin ciki sannan ta koma motarta da gudu , ƙara barbaɗa powder tayi tare da ƙara shafa turare sosai , sannan ta gyara ɗaurin kallabinta ta fito...

Kallon mamaki nake ta bin Hafsa dashi anya yarinyar nan bazan zameta daga harkata ba ? Tafiyar nan kuwa zata tafi kodai in fita inyi harkata ni ɗaya ? Ina wannan tunanin zuƙa zuƙan motocin Dikko sukayi parking a ƙofar shagon mu...

Cikin rawar kai Hafsa ta tashi tayi wurin motar Dikko , ƙafarshi ya ɗora saman murfin motar , kafin Hafsa ta isa wurin ya zura hannunshi aljihu ya ciro cingom , a daidai lokacin da Hafsat ta isa wurin motar , ko inda take bai kalla ba ya cire cingom inshi a cikin takaddar shi ,

Tahowa ya farayi zuwa wurina tare da ɗora cingom in saman "yan yatsunshi na hannun haggu ya daki tafin hannunshi na haggu da hannun shi na dama , buɗe bakishi yayi cingom in yayi tsalle ya shige ,

Ɗan tsuke bakinshi yayi kamar zaiyi kiss sannan ya lumshe idanuwanshi tare da nuna yanayin kamar abin harin sumbatar nashi yana kusa dashi , muah ya saki kiss a daidai lokacin daya tsaya gabana yaja kujerar rober ya zauna , sai yanzu ya fara tauna cingom ɗin cikin izza da nuna shi wani isashshe ne , ɗago ƙafarshi yayi ya biyo da ita ta saitin fuskata kamar zai takamin fuska naɗan ja baya , murmushi yayi tare da ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya :•

Robar ruwa Al ' Ameen ya miƙowa Dikko bayan ya zauna , ɓalle murfin robar ruwan yayi yakai bakinshi yana kallona , shan ruwan yayi sannan ya cika bakinshi dashi ya miƙawa Al ' Ameen robar ruwan , murmushi yayi da gefen bakinshi sannan ya fara bultso ruwan daga bakinshi suna watsowa saman fuskata...

Ƙoƙarin tashi na farayi dan banda lokacin Dikko a yanzu sai bayan shekarun dana iba , ina ƙoƙarin tashi ya maidar dani ya zaunar da ƙafarshi nayi na tashi na kasa saida ya gama watsa min ruwan sannan na buɗe idona daya cika da hawaye na kalleshi ,

Murmushi yayi sannan yayi magana cikin sigar lallashi haba ke ko an mata komai saurin kuka ke baki san wasa ba ? Karfa ki ɗauki abin da zafi albarka na saka miki , kin zageni tass amma zagin yamin daɗi bayan shekaru biyu idan muka fara farautar juna a ranar zaki gane Dikko ba zakin roba bane , zakin gaske ne farin ciki mafarauta , maganar dana faɗa mishi jiya, cewa zakin roba dana sanin mafarauta, ci gaba yayi dacewa dani dake duk wanda ya fasa , ya jinjina kainshi tare da nunani da hannu ,

Tura kujerar da nake zaune yayi da ƙarfi da bango bai tareni ba babu abinda zai hanani faɗuwa , Al ' Ameen ya kira da sauri yazo tare da miƙo mishi wata "yar ƙaramar jaka tashi yayi ya duƙo kusa dani sosai lumfashin shi yana sauka saman jikina , saman jikina ya ɗora tare da cewa ga cingom nan zai isheki amfani daga nan har zuwa lokacin da zamu fara wasa , ɗan taɓe baki yayi tare da kallon wani wuri daban sannan ya juyo ya kalleni da magana zaiyi kawai sai fasa...

Miƙewa yayi ya juya
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

6 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment