Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba tun daga farko ma kenan , soyayya tana faruwa ne cikin wani lokaci mai gushewa da wurwuri wannan shine tabbataccen hasashen da babu irin shi , ina kaiwa nan na juya na shige ɗakina ,

Murmushi Dikko yayi bayan tafiyar Sultana yace yanzu ta gayamun abinda zanyi kenan , duk da abinda na faɗa mata saida tayimin gaddama ta yarinta na faɗa soyayyarta yawancin abubuwa sukan zo da aibi ku tsaya ku gani zata faɗa soyayya ta da wurwuri.......







24/09/2019




*JAMILA MUSA ...*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 40


Miƙewa yayi bayan ya gama surutanshi ya fita babban palo maƙulin motarshi ya ɗauka ya fita , ina tsaye a jikin window ina kallonshi har ya shiga mota ya bar gidan da gudu bansan inda zaije ba , kuma ga dukkan alamu bazai kwana gidan ba , murmushi nayi tare dayin magana ƙasa² nace sauka lafiya.

Yana fita na dawo na kwanta saman katifa naja bargo na lulluɓe na rufe idanuwana ina jinjina irin wulaƙancin da Dikko yayi mana shi mai kuɗi , "yar madara dabbace amma duk lokacin da naji an kira sunan mage ko na ganta sai magena ta faɗon min a rai da Dikko yabi ta kanta da mota bataji bata gani ba ,

Wulaƙancin da yayi ma Babana a ranar daya wankemin ubanda yafi ko wane uba a wurina da ruwan taɓo , lokacin daya bugamin kanshi har na suma , uwa uba ƙarshen wulaƙanci daya keta min mutuntaka ta , idan ma har zuciyata ta bari ƙiyayyar Dikko ta goge a cikinta ban yafewa kaina , ɗaukar fansa ƙudirina ne kuma muradi nane ko ba daɗe ko ba jima saina kafawa Dikko tarihin da bazai taɓa gogowa a rayuwarshi ba ,

Maganar cewa idan na kawo mishi na 20 zai rufe ƙofa dani nayi masa rata har abada nayi masa nisan da bazai iya kamoni ba , yanda Annabi ya gagari arna haka na gagareka Dikko sa'a ɗaya kawai nake nema fita daga hannunka amma da zaran na zare tou kwankin hararka sun soma...

Dukan sitiyarin mota Dikko yayi a daidai wannan lokacin yace wallahi ƙarya kike , dan tunda ya fito daga gidan zuciyarshi tana faɗa mishi Sultana tana sanshi tabbas kuma akwai wannan soyayya domin yaga soyayyashi kwance a cikin idanuwanta !

Da safe tunda nayi sallah asuba nayi wanka na shirya cikin kayan makaranta , jakata na ɗauka da sauran kuɗina da ban kashe ba nayo babban palo ,

Na daɗe dan nafi ƙarfin awa ɗaya amma babu Dikko babu alamarshi kuma babu mota ko ɗaya a gidan , tun ina zama na marmari har na fara gajiya na kwanta saidai na kalli agogo nayi tsoki dan gani ma nake lokutan basa sauri , raina fa ya gama ɓaci sosai dan har nayi tunanin kila bayau zan koma ba ,

Ƙarfe 9:46am ya shigo gidan , a kasalance ya fito daga cikin motar ya nufo palo , kallo 3 nayi mishi kafin ya iso na kauda kaina , kamar yayi kuka dan yanayin fuskarshi ya nuna rai a haɗe kamar hadarin tsakar dare ,

Da sallama ya shigo palon bai ko kalli inda nake ba ya wuce ciki , na ansa sallamar na gaishe shi bai ansa ba ya wuce , murmushi nayi a zuciyata nace kila matarshi taci ƙaniyarshi , mugu kenan sai lahira a gane halinshi...

Yayi fata² da awowi biyu sannan ya fito tunda ya fito ƙaramin palon ƙamshin turarunshi ya fara zagaye cikin gidan nan lungu da saƙo bana tunanin akwai inda ƙamshin bai kai ba , ƙamshin turare mai daɗi mai jefa mutum cikin wani irin baƙon yanayi mai wahalar mantawa ,

Bayan kamar minti biyu ya iso cikin babban palo , wallahi dole tasa na juya dan yanda naji ƙamshi inga wace shiga yayi haka ? Dan nasan bazaiyi wannan ƙamshin a banza ba , yanayin ƙamshin nasan yanayin haɗuwar da zaiyi kuma ba'a magana , dan duk yanda zan musulta muku kyawun Dikko zakuga kamar shiri ne abun , gaskiya Dikko yana da kyau fiye da duk yanda mutum yake zato , tunda nake a rayuwa ban taɓa ganin wayayyen namiji ɗan gayu mai saurin shiga rai kamar Dikko ba , ko ta ina babu inda mutum ya isa ya kushe shi saidai wani halin daban dan ɗan adam 9 yake bai cika 10 ba , Dikko yana da aji yana da natsuwar da ko mace tayi natsuwarshi taci Allah buɗa ,

Baida yawan dariya haka kuma bai cika murmushi ba , idan kuma yaji mugunta ya fara dariya kai kanka sai abun ya burge ka domin dariya tana mishi kyau , haka kuma murmushi ke ƙara ƙawata kawunshi , kuma yanayin ɗaure fuska ma dai yana mishi kyau gaskiya !

Idona na sauka kan idonshi gabana ya yanke ya faɗi , yasha ƙananan kaya abunshi yayi kyau cikar zatinsa da ƙwarjinsa ya ƙara fitowa sosai , bai kalleni ba ya yayi kamar ma bana nan saida yazo dai² inda nake zaune yace muje ,

Ajiyar zuciya na sauke na ɗauka jakata nabi bayanshi dan shi tuni ya fice daga palon , lokacin dana fito harya shiga mota , ina buɗe murfin motar zan shiga baya zaune naga shine zauna , fuska a haɗe kamar an aiko mishi da sauƙon mutuwa ,

Kawai dai naji babu daɗi yanayin yanda yake ta haɗe rai duk na kama kaina haka nan naji duk na takura , jakata na fara sakawa sannan na shiga na rufe na kalli wani gefe daban ba na driver ba kuma bana Dikko ba , yau an sako Al ' Ameen wani mai girman kan bala'e ne , kamar jira yake na rufe ƙofa ya bige mota kamar zai tashi sama ,

Saida muka fara biyawa Alheri clinic acan matar Dikko take shi kaɗai ya fita yaje ya dubota bai wani daɗe ba ya dawo yana gaba wata kyakkyawar budurwa tana biyoshi baya har suka iso wurin mota ,

Buɗe motar yayi ya ɗauki wayoyinshi daya bari lokacin da zaije wurin Sadiya , gaba ya koma ya zauna ita kuma ta shigo baya , kallona tayi ƙasa da sama sannan tayi tsoki tare da faɗin wata kalma da turanci amma ko miye tanayin maganar da zafi ne ,

Ɗaga kaina nayi na kalli cikin madubi inda Dikko yake kallona , sam yau idonshi hankalin shi da tunaninshi baya wuri na , da gudu driver ya sauko daga inda aka tanada dan ajiye motoci ya ibi hanya yaci gaba da falfala gudu babu ji babu gani ,

Saida mukayi tafiya sosai sannan ta sake faɗar irin kalmar data faɗa daga farko tana hararata , shiru nayi banyi magana ba , bayan wani lokaci tace au na manta ashe da daƙiƙiya nake magana jahila karuwar banza karuwar wofi , wani irin ɓacin rai na haɗeye dakel lumfashina ya fara yawo tsakanin duniya da lahira , taci gaba da cewa karya wacce iyayenki suka kasa baki tarbiya balbaɗaɗɗiya dake ɗiyar ɗan caca ,

Murmushi nayi mai cin zuciya amma banyi magana ba dan na fahimci tana da sauran magana , ci gaba tayi da cewa ni sweetheart baya ɓoyemin komai ni nace yayimin rainonki zuwa ranar da za'a ɗaura mana aure zaki dawo gidana kuma gidan mijina da zama a nan zan fara baki azabar tausayin da yasa kika shigo rayuwata Sadiya ma da tamin hawan ƙawara ya kikaga lamarinta ya ƙare ? Zata tafi duniyar mutuwa babu jimawa ,

Murmushi nayi tare da gyara zamana na kalleta sosai sannan nace idan kin isa ki sake maimaita abinda kika faɗa daga farko ! Nace jahila , nace ni ba jahila bace dan abinda na sani ko uwarki bata sanshi ba , ina da ilimin addini sittin ce a kaina sakara izihinki nawa ke ? Tayi shiru nace tou kinga ɗan caca tun nan ya nuna tarbiyarshi tafi irin wacce babanki ya baki ,

Da kika cemin karuwa tabbas ni karuwa ce bazaki shaida hakan ba saina kasa tallata a bakin titi uban naki idan ya gani zai kwasa , ni da kika gani kamar ɗan silif nake ko mutum baici ba saina burgeshi idan kuma harya taɓa kwanon zai taɓo cikin idan baici ba saiya lashe hannu , tabbas zan nuna miki kaidina da kuma illar kirana da karuwa da kikayi ,

Matsalarki da Sadiya ba tawa bace amma tabbas sai ubanki ya taɓa nan da nan ya kuma maida miyanshi , na faɗi maganar tare da nuna mata wuraren da idonta ke iya gani sannan nace dake da Dikko duk nafi ƙarfinku kuma kinyi ganganci shigowa rayuwata abun harina ya koma biyu daga yanzun nan zanci gaba da hararki kuma in hari Dikko , mari takaimin , nima na rama daga nan muma cakume da kokowa daga zaune ,

Da sauri Dikko ya juyo yace miye haka kuma ? Cikin ɓacin rai nace ban sani ba baƙin munafiki dakai , zaro ido yayi yace ai bake nake tambaya ba , cike da masifa nace nima ai bakai nake ba ansa ba , Ashiru yi parking inji Dikko , da sauri ya gurji gefen titi ƙayyyyy yayi parking har lokacin bamu daina bige² ba ,

Ni Dikko ya fara fiddowa tunda ni nake saitin daya buɗe murfin motar yana fizgoni ya mareni yace nine munafikin An mata ? Kafin ya sauke hannunshi nima na zabgaga mishi mari nace kaine mana munafiki dama akwai wani bayan kai ?

Da sauri Ashiru ya kauda kanshi , murmushi Dikko yayi yace An mata ni kika mara ? Nace waye kai ? Dikkon banza Dikko wofi , fitowa tayi daga cikin motar ta kamani da kokowa duk da banda ƙarfi na firgice sosai dan na tsani inji an aibata Babana , kokowa mukaci gaba dayi Dikko ya riƙeni na sake fizgewa mukaci gaba da faɗa , ya ƙara riƙeni sosai hannun damarshi ya riƙo min ƙuguna dashi hannun haggunshi kuma ya ɗagomin fuskata kowa yana kallon kwayar idon kowa ,

Cikin maganarshi maisa natsuwa yace An mata yau kuma Dikkon ne na banza da wofi ? Ni An mata ? Kinmin adalci kenan ? A gaban mutanen dake ganin girmana zaki tozarni ? Mi yasa bakimin jiya ba ? Me yayi zafi haka haba An matana.... Ya ƙarasa maganar kamar zaiyi kuka , cikin kuka nace cewa fa tayi Babana ɗan caca kuma kaine kace mata ni karuwa ce kuma karya fa 😭 jahila fa 😭daƙiƙiya balbaɗaɗɗiya fa wai Babana bai bani tarbiya ba irin wannan shedar zakuyi ma Baba ?

Tsareni yayi da idanuwanshi masu ɗaukar hankali sannan yace tou kiyi haƙuri , rufe idanuwana nayi nace inyi haƙuri a aibata min Babana ? Dikko ya ƙara cewa kiyi haƙuri , buɗe idanuwa na nayi tare da cewa wallahi Babana bai kasa bani tarbiyya ba kuma kai zaka sheda haka wata rana sakeni , sakina yayi baiyi kaddama ba mota na koma na ɗauko jakata nazo gabanshi na zazzageta nace ga jakar ka nan ga sauran kuɗinka nan idan naje gida zan bada cikonka a kawo maka ,

Ina faɗin haka nayi gaba , Dikko yace ina zaki je ? Juyowa nayi cike da ɓacin rai nace zanje gidan ubanda ya hafeni ne , nasan darajar ɗan caca kuma nasan mutuncinshi , kallon inda budurwar take nayi nace sunana MARYAM ALIYU MUHAMMAD BINNA { Sultana } ki fara kuka tun daga yanzu domin kwanakin baƙin cikinki sun soma daga yau , mafita ɗaya kawai shine ki mutu ki huta amma tabbas bazan goge kuɗina akanki ba wallahi ׳ ,

Kamar sakarai haka Dikko ya tsaya yana kallona , nunasu nayi dukansu da ɗan yatsa nace gata nan gatanan ku , goge hawaye nayi nai gaba cikin ɓacin rai , Dikko ya sake cewa wai An mata miye kikeyi haka ? Tsayawa nayi amma ban juyo ba nace idan ka sakemin magana saina tona maka asiri.......





25/09/2019


Kuyi haƙuri don Allah wallahi banajin daɗi wannan ma dakel nayi shi ,



*JAMILA MUSA...*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 41


Dariya Dikko yayi mai shiga zuciya yace tou miye ribarki idan kin tunamin asiri ? Ai asirina da naki a haɗe yake ki tona tunda ban riƙe miki baki ba , amma ki sani idan kin tonashi sai ki fara neman hanyar da zaki rufeshi saboda tabbas wata rana zaki zama ni , ni kuma zan zama ke , kije abunki amma duk abinda zaki kiyi na hankali da tunani , cikon kuɗi kuma da kike magana bake ba da wani abu ya shiga tsakani dake nake ganin mutunciki da ƙimarki saboda kina da wani matsayi na musamma a rayuwata da zuciyata wanda ta dalilinshi kuma nake ɗaga miki ƙafa , duk abinda ya fita hannuna na gama dashi har abadan abada ,

Kuma zuciyata ta faɗamin cewa ko kin tafi sai kin dawo bata taɓa faɗamin ƙarya akanki ba duk abinda ta faɗamin gaske ne , idan akacemin An mata ta mutu ina da yaƙini zuciyata tacemin a , a tou tabbas idan nazo zan ganki kina numfashi , sauka lafiya amma banda kukan dare dan ina buƙatar bacci a wannan lokacin kiyi kuka da safe kiyi da rana amma idan har kikayi kukan dare gani nan zan dawo ,

Kallon budurwar yayi ya nuna mata da hannu ke koma mota muje , shiga tayi mota shi kuma ya biyo bayana , gabana yasha yace An mata karki zo kiyi abunda zai zama matsala a rayuwarmu , ki manta da abinda ya faru baya mu fuskanci sabuwar rayuwa ,

Cikin kuka na kalleshi nace har ƙarshen numfashi na bana fatan na sake kasancewa dakai wallahi , kuma zuciyarka ta faɗa maka gaskiya tabbas zan dawo amma ɗaukar fansa zata dawo dani ,

Murmushi yayi tare da cewa haba yarinya , Dikko ne fa ! Kin manta nine na koya miki ? Nine nayi kuma nine na fara baki idan daɗi kikaji ko zafi duk nine dai , ruwa idan da rabonka cikin sa ko ka zuba a kwando bai maka yoyo , ni ba abin farautarki bane zaki duk jarumtatai yana ganin ƙimar mafarauci a wancan karon suma kikayi , wannan karon ma haka zata sake faruwa dake ba suma ba har jinya sai kinyi , idan kin dawo ɗauka fansa zaki gane Dikko ba sa'ar wasanki bane domin saina baki azabar da sai kinyi fitsarin wahala bayan kin dawo daga duniyar suma , tsoro na zai shigeki a lokacin da kika kasance dani a shifimɗa ɗaya , idan kuma Dikko baya nan zakiyi kuka bacci ya gagareki gidan biki ko suna Dikko yana tare dake a zuciyarki domin zan zame miki garkuwa , da hannun damarshi ya daki na haggu yace wallahi jarumi ɗaya ake a ƙarni nine jarumin wannan lokaci , Dikko jarumin maza ne kuma ke da kanki zaki faɗa keje ki dawo ina nan ina jiranki ,

Idan kuma soyayya ta dawo dake , ƙasa ya kalla yana nazari bayan wani lokaci ya kalloni yace tabbas zaki zo zuwa gareni kina roƙon na baki soyayya ta , nace wa ni ? Yace tabbas ranar zata zo , nuna kaina nayi tare daci gaba da cewa yi haƙuri Dikko ka manta da wannan wasan kwaikwayon naka har abadan duniya hakan bazai yuwu ba , murmushi yayi tare da taɓa daidai saitin zuciyarshi yace ina da tabbacin zaki soni kamar dai yadda na faɗa , ko kina da tabbacin cewa baza ki taɓa so na ba ? Nace Eh har abadan abada , murmushi yayi yace ƙarya kikeyi , nace da gaske nake , yace zaki gani nima nace zaka gani , girgiza kanshi yayi yace jeki abunki ,

Ci gaba nayi da tafiya har yanzu yana tsaye a wurin dana barshi , motoci masu komawa katsina nayi ta ɗagawa hannu har Allah yasa na samu masu ragemin hanya shiga nayi na nufo katsina yayin da Dikko ya shiga suka kama hanyar abuja ,

Budurwar Dikko kuma ga wayarta a hannuna , domin dana koma mota dama ba jaka na koma ɗaukowa ba waya na ɗauko abinda yasa na fito da jaka dan karsu zargi ni na sace kuma nasan idan sukayi gaba zasuyi tunanin wurin fitowa ta yada ita , Baba da Mama da kowa nata yana cikin waya...

Tunda Dikko suka tafi yake kukan zuci daren jiya da An mata tasan irin matsalar daya fuskanta akanta da bata baɗa mishi ƙura ba , abinda ya faru tsakaninsu sirri ne babu wanda ya sani sai shi sai ita sai Allah , yana bata mutuntukar mutuncinta daya ɗauka amma yarinta ta hanata kusantowa gareshi !

Abinda ya faru jiya , bayan Dikko ya faɗawa An mata yana santa tafiyarta kawai tayi ta barshi palo zaune kamar wani sakarai , bata daɗe da shiga ɗaki ba Dady yace yana nemanshi duk abinda yakeyi ya barshi yazo , shine ya tashi ya fita babban palo ya ɗauki makullin mota ya fita kuma a gaban idon Sultana yabar gidan...

Bayan yaje gida a palon Dady ya samu Al ' Ameen gurfane a gaban Dady , kallo ɗaya yayi mishi ya ɗauke kanshi tare da samun wuri shima ya zauna can nesa da Dady , bayan ya zauna ya gaishe da Dady ya ansa shima Al ' Ameen ya gaishe da Dikko , Dikko bai ansa gaisuwar ba , kallon Al ' Ameen Dady yace ya kira mishi Ummar ,

Miƙewa Al ' Ameen yayi kafin ma ya fita daga palon Umar ya shigo saboda dama tuni an kirashi bai samu isowa da wuri bane , bayan kowa ya zauna Dady ya kalli Al ' Ameen yace ga Babana nan ka sake faɗar abinda ka faɗa , shiru Al ' Ameen yayi , Dady kuma ya kalli Umar bayan Al ' Ameen yaƙi magana yace Umar wace yarinya ce take zaune da Baba ?

Da sauri Umar ya kalli Dikko amma shi basu yake kallo ba yana kallon wani wuri daban , cike da fargaba Umar yace wallahi Dady nidai ban sani ba , Dady yace tou aini Al ' Ameen yace min ya ajiye mace gidanshi na goroba road bayan ni nasan Babana baya huɗɗa mata shi yasa hankalina ya tashi , Umar sake kallon Dikko yayi amma har yanzu Dikko fuskar nan tashi dai kamar yadda take kullum kuma har yanzu baya kallonsu kawai dai yana saurarensu.

Dady yace ƙarya zakamin ne ? Ya tambayi Umar , Umar yayi shiru , Dady yace ma Al ' Ameen yanzu ina yarinyar take ? Tana gidan har yanzu ? Al ' Ameen yayi shiru , gyara zama Dikko yayi yace tana gidan Dady , amma lokacin dana fito na barta tayi bacci , nayi kuskuren rashin sanar dakai amma da Allah kayi haƙuri nayi amfani da maganar ka ne da kace na zama mai kyautatawa duk wanda naga rayuwarshi tana buƙatar taimako ,

Yarinya ce ƙarama shekarunta bazai wuce 18 ba kuma na baka labarinta kwanakin baya itace yarinyar da mukeyin faɗa tou yanzu mun daina faɗan ne , a tsawace Dady yace ɗiyar ɗan caca ? Karuwar Babana ? Cikin ladabi Dikko ya sauke kanshi ƙasa tare da rufe idanuwanshi , Dady yaci gaba da cewa duk ƙoƙarin kare martabar ka da nake maka ni zaka ɓatawa siyasa ka ɓatamin suna har cikin jahata ? Ni zaka zubarwa da mutunci ? Ka ɗauko karuwa ka ajiye a gidanka ka bar matarka kaje ka kwana da "yar iska mara tarbiya wacce tafi ƙarfin iyayenta itace wacce kake ganin kaine zaka gyara mata rayuwa ?

Masifar da tasa iyayenta suka yada ita ba ƙarama bace kai shine kaje ka ɗauko ka dawo da ita rayuwarka kai sarkin imani da tsoron Allah ? Kana siyasa zaka ɓatawa kanka suna , ka zubar da mutuncinka a idon duniya ina amfanin mu'amula da karuwa ? Ko zaka dafa Al ' Qur'ani kayi rantsuwa kace baka neman yarinyar nan babu wanda zai yadda , da yarintar ka baka bi mata ba sai yanzu da shekaru suka fara hawanka ? Tou idan dan rashin lafiyar matar ka ne Momynka ta nemo maka auren ɗiyar yayarta shikenan na kashe maganar...

Murmushi Dikko yayi tare da cewa gaskiya Dady ban tsara zama da mace 3 ba a rayuwata itama Sadiyar haƙuri nayi kawai na ansa amma ni gaskiya mata 3 sunmin yawa wannan karon bazan ansa ba kuyi haƙuri , ciki ɓacin rai Dady yace wallahi idan dai ina lumfashi a duniyar nan baza ka auri karuwa ba sakaran banza da baka san macen da ya kamata ka aura ba , shi aure daka ganshi yana buƙatar cancanta mutuntaka asali da nasabar mace , banda kake sakarai ka rasa wacce zaka so sai karuwa ? Karuwar kake tunanin zata zama uwar "ya "yan ka ? Ni wallahi ko jirgi zan siya bana buƙatar na hannu sai sabo shi yasa bazan iya auren zawara ba amma kai dan baka kishin kanka har kake tunanin auren karuwa , wallahi da kasan kanka ko mace baka nema ,na tsani wani yayi amfani da abu nayi amfani dashi saboda tsanar da nayi ma abun yasa bana sauka hotel , duk jahar daka gani babu inda banda gida babu ƙasar da ban mallaki gida ba dan na tsani wani ya shiga a wuri na shiga sakarai wawa dakai idan baka fita harkar yarinyar nan ba zaka haɗu da fushi na ,

Dady kayi haƙuri kasan.... Tsawa Dady yayi masa yace nasan me ?

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment