Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zafi ? Umm umm , to me yasa ki key kuka ? Ba komai , sai yanzu ya gane bada Sultana yake maganar ba , buɗe idonshi yayi da sauri ya ganshi kwance akan sabuwar amaryar shi , kuma "yar uwa a gareshi...

Ko tsakar dare dana farka haka naci gaba da gwada wayar Dikko wanda ya zamarmin kamar hauka dan ƙaranci ban kira wayarshi ba a rana na kirashi sau 200 da wani abu ,

Ina zaune tsakar daren nan ina ta aikin neman wayar naji maganar Baba ƙasa² daga bayan ɗakina dake daga tagar ɗakin sai a fice zaure a fita ƙofar gida , bana iya jiyo abinda Baba yake cewa saidai naji maganar Amisty cikin shagaba tana cewa nidai Dady don Allah... Ta ƙarasa maganar kamar tana kuka !

Da sauri na haska fitila na duba agogo naga 3:45am cikin sauri na miƙe na sake matsawa da kunnena jikin window naji shin da gaske Amisty ce ko kuwa dai wata ce daban ! Wallahi Amisty ce dan duk duniya babu mai irin wannan muryar sai ita , me suke cewa ? Me ya haɗa Amisty da Babana a wannan salasunan daren ? Me ke tsakanin Amisty da Baba ? Duk wannan tambayar banda ansoshinsu nayi yunƙurin yin wani abu tunani na ya tsaya cak domin kaina ya riga da ya juya...

Buga kaina nayi da ƙarfin bala'e a jikin bango na kurma wani irin ihu duk wanda ke cikin gidan saida yayo waje saboda ƙarfin ihun da amonshi ni kuma na fito da gudu nayo hanyar fita , babu Amisty domin tuni ta fice , ina ƙoƙarin fita Baba ya riƙeni da ƙarfi yana lafiya ? Fizge ² na farayi na kwace nayi waje , da gudu ya bini ya riƙoni nafi ƙarfin riƙonshi domin na sake zuƙewa daga riƙon da yayimin , cikin tashin hankali zugar gidanmu suka yo kaina dakel suka kaini ƙasa suka daddanne ni na birkice gaba ɗayansu na watse su , na yanki santa , yayuna maza suka taimaka aka kamani aka mayar dani cikin gida ,

Kowa tambayar abinda ya sameni yakeyi ? Murmushi nayi mai ciwo na kalli Baba nace ina ka ɓoyeta ne ? Cikin rashin fahimta yace wa ? Kafi kowa saninta me takeyi a gidan nan a wannan lokacin me tazo yi me take nema...? Baba yace wai wace ce ? Ga sunan Amisty a zuciyata amma ƙiri² ya gagara na faɗa a baki na , nace ita mana ita wace ce ? Kai ji nan na nunashi da ɗan yatsa nace tana ina karfa ka ɗaukeni mahaukaci nasan abinda nake ina ka ɓoyeta ne ?

Amma Baba sai ya fara tofa min addu'a yana cewa aljannu sun kama uwar masu gida , a taimakamin da addu'a , inaji ina gani Baba yasa aka mayar dani mahaukaciyar ƙarfi da yaji , kowa yayi ta tofamin yawu , banda yanda zanyi dole nayi shiru amma wannan abun bai gogemin daga zuciya ba kuma saina bi salsala na gano abinda ke tsakanin Baba da Amisty , maganar Mamy ta dawo min a kaina kamar yanzu take faɗamin maganar...

_Gaskiya an samu matsala shi kanshi Binna da yasan waye Hafsa a wurinshi daya haɗe zuciya ya mutu , itama bata san wayenta ba , shima Baban Hafsa baisan ke wacecen shi ba , kowa iskanci ² gaba ɗayan ahali sun zaman *KWARATA...*_

Lallai akwai alamar tambaya a wurin nan amma waye zai fiddo maganar daga cikin zuciyata ? Waye ? Waye zai taimakeni ne ? Wai wace ce ni ? Anya kuwa ni mutunce ? Mutane kuwa suna gani na ? Wai meke damun rayuwata ? Me ke damun kwalwata ? Wannan wane irin masifa ne ? Wace irin rayuwa nakeyi ? Ina mahaifiyata wai me Baba ya ɗaukeni ? Me nene ׳ na ƙarasa maganar ina ɗaga muryata wanda ina tunanin duk mutumin dake anguwar nan yaji irin hayagagar da nakeyi...

Fashewa nayi da wani irin kuka nace tabbas ko wace ce ni da sanin wace irin rayuwa nakeyi amsar tana wurinki , kuɗin da Mamy ta bani na ɗauko na irga suna nan yadda ta bani su , maidasu nayi na aje , amma a zuciyata nayi alƙawari zan bautata mata tiƙuru kuma zan bata girmanta kamar yadda take so zan nemo matar nan kuma zan kaita zan bawa Mamy kuɗinta kuma zanci gaba da farauto mata duk wanda take so adalci ɗaya zatamin ta warwaremin sirrin rayuwata wannan shine kawai mafita....

Gari na waye nayi wanka yau ko inda Babana yake ban kalla ba kuma ban gaishe shi ba , makulin mota ta na buƙata ya bani amma sai yacemin wai anci motar a caca , kallonshi nayi nace ni bansan caca ba mota ta kawai na sani kuma sai ka biyata ,

Mamana ni kike cewa saina biyaki mota ? Kaine ka siyata ne ? Ai ko ban siya ba naci albarkacin haihuwarki da nayi , ka maidani ciki idan kaji munin maganar amma sai ka biya wannan motar babu gudu babu ja da baya kuma ba abinda ya dameni na baka daga yanzun nan zuwa bayan sallah isha'e ... Ina faɗin haka nayi waje abuna na barshi ta tagumi...

Ina fita na shiga maƙota na nuna hoton matar da Mamy ta turomin a wayata nace da Allah ina neman gidanta , matar tacemin lafiya dai ko ? Nace lafiya qalau gwamnati tace a taimakawa masu ƙaramin ƙarfi wanda suke shan wahala a gidan aurensu , an ɗauko jaddawalin sunan ko wace macen aure da ƙaramin katin hotonta , sai naga ita kamar tafi kowa shan wahala shine nake so ita a taimaka mata da yawa , mata da kuɗi sai Allah kuma nayi haka dan in rubzata rami itama , ta haka zanji wane irin hali matar take nasan komai nata kafin na isa gidanta , !

Murmushi matar tayi tare da ɗaukomin kujera na zauna tace amma Sultana kunsan kuna da hanyar taimako shine mu ba'a saka sunanmu ba ? Jakata na zuge na fiddo damen "yan dubu² nace kin gansu nan kowa da sunanshi ai bansan kuna buƙata ba , itama banda tabbacin da zataje ko bazata ba ,

Tace zuwa kai , muje na rakaki gidan ta amma don Allah nima kisa a rubuta suna na don Allah , nace baki da matsala , saman ƙyaure ta ɗauko hijabinta tana ba yaranta umarni karsuyi mata ɓarna idan Babansu ya shigo ta shiga maƙota baza ta jima ba ,

Ta gaban gidan Amisty muka wuce gaba ɗayansu suna ƙofar gida hada Asma'u an saka kujeru na roba Amisty kuma tana ta tofi da hayaƙin sigari , yayin da wata tantiriyar "yar iska ke shan shisha tana murza hayaƙin cikin ƙwarewa da gogewa a cikin harkar ,

Har mun wuce naji bana iya haƙuri na dawo da baya , dai² Amisty na tsaya na ciro sigarin daga cikin bakinta na kasheta a saman goshinta , wata irin ƙara tayi saboda zafi ta riƙo hannuna na , da hannun damata na riƙe hannunta saboda dana haggun na kashe mata tabar sannan nace na rantse da Allah duk ranar da hasashena ya zamo gaskiya yadda na murje wannan sigarin a goshinki haka zan murje miki rayuwa..

Gaba dayan su sukayo kaina suna kee.... Nace heeee ku saurara na kaso daku sannan ku ɗauka domin yanzu babu sauran muradin ɗaukar fansa a zuciyata ina neman rayuwata ne amma idan kuka bari na ɗauki zafi anbaliyar wuta zan fara hattaranku domin ni fetir ce kuma sai cikin wuta nake amaina !

Kallon Amisty nayi nace ki fara addu'ar kuɓuta daga sharrina domin na yanzu ba irin na baya bane , na yanzu maciji zansa ya cinye kwansa { uba ne zai kwanta da "yar sa } ki kiyayi haɗuwa ta da ke domin abin bazai miki kyau ba ,

Sakinta nayi na kalli matar nace mata muje... Wuce su mukayi muka tunkari gidan matan , da sallama muka shiga , ta amsa mana cikin sakin fuska tare da shinfiɗa tabarma tace ku zauna sannunku da zuwa ,

Zama mukayi , baiwar Allah ta dama ɗan kokonta da ɗumamen tuwo suna ci ita da yaranta tana ma Allah godiya , amma dole tayi haƙuri domin Sultana ta shigo mata rayuwa , mijinta ya fito daga cikin ɗaki muka gaisa dashi ita kuma tabi bayanshi danyi mishi rakiya , wayyo bawan Allah kayi haƙuri Sultana tazo yanzu zan firgita maka iyalinka ka kasa gane gabanta bare bayanta...








01/10/2019





*JAMILA MUSA....*
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 47


Cikin sakin fuska ta shigo cikin gidan bayan ta dawo daga rakiyar mijinta , a mutunce ta zauna kusa damu saman tabarmar da muke aka gaisa a mutunce suka ɗan taɓa fira a tsakanin su da matar da muka zo tare mai nuni da akwai sanayya mai girma tsakaninsu ,

Bayan sun gama gaisawa da Maman Sadiq itace wacce muka zo da ita , ita kuma mai gidan naji Maman Sadiq in tana kiranta da Ummu Affan , Maman Sadiq tace tou Sultana wannan itace kike nema ko ? Murmushi nayi cikin jin kunya nace itace , kallona matar tayi tace lafiya dai ko ? Nace lafiya lau , Ummu Affan tace ya akayi ne ?

Nace dama ƙungiyace gwamnati ta buɗe domin taimakawa matan aure marasa ƙarfi , an ɗauki sunayen wasu matan da kuma yawan "ya "yansu , mai girma gwamna ya bada izini dan gyara siyasar shi , shin kina da wata sana'a da kikeyi ko bakya da ?

Ummu Affan tace gaskiya bana sana'ar komai , tou mi kike buƙata wannan gwamnati mai adalci ta taimaka miki dashi wanda zaki taimaki kanki da kuma iyalinki a cikin gida ba tare da kinsha wahala ba ? Tace Eh tou gaskiya idan dai san samu da gaske za'a taimakamin a siyamin injin markaɗe da kuma injin taliya domin shine abinda yayi ƙaranci a wannan anguwa tamu , tou amma bashi za'a raba kayan ko kyauta ?

Nace haba wane kuma da gaske Ummu Affan ? Kinga ai ban taɓa zuwa gidanki ba sai yau , kuma duk mutumin daka gani a gidan ka ai da dalili , gwamnati tsaye take a kan ƙafafuwanta dan ganin ta taimaki talakanta , idan zaki amince ma ai sai a naɗaki shugabar ƙungiya ki tattaro mana matan aure waɗanda suke san taimako kinga ke sai ki zama shugabarsu idan yaso sai a baki kuɗin da kuma kayayyanki da gwamnati zata bayar ke kuma saiki riƙa raba musu ya kika gani ?

Maman Sadiq tace to ni me za'a bani ne ? Nace ke kuma sai a naɗaki matemakiyar Ummu Affan amma ban sani ba ko mazajenku zasu riƙa barinku kuje wurin taro ? Dan naga duk lokacin da ake taro dubu goma ² ake bawa duk wacce ta halacci taron , Maman Sadiq ta zaro ido tare da cewa dubu goma ? Nace sosai ma idan ma gwamna yazo wurin taron dubu ishirin ake rabawa ga duk mace ɗaya ga lemu ga ruwan roba hada naman kaji ga abinci mai kyau kici ki ɗaurowa yaranki a leda...

Ummu Affan tace dubu ishirin ? Nace sosai ma , tace idan dai taron bana dare bane wallahi sai muje ko ƙawata ? Suka kashe da Maman Sadiq , Maman Sadiq tace aini ko na daren ne wallahi ina iya zuwa uwar me ake baka auren ƙaddara auren ya zanyi ? Auren cida kai ? Kana gida zaune kullum kamar mai takaba babu wani ci gaban rayuwa sai tsofewa kakeyi kai baka mori rayuwarka ba kazo a wahala ka rayu a ƙunci ka koma a alakoro , nidai gaskiya ina zuwa ,

Nace tou ki bari muji ta bakin shugabar ƙungiya mana ? Na ƙarasa maganar a dai² lokacin dana zage jakata na fiddo irin kuɗin dana fiddo a gidan Maman Sadiq dubu biyar² naba ko wace a cikinsu nace idan kunyi shawara ku neme ni , gaba ɗayansu dubu biyar² ta ruɗasu dan yanayin fuskarsu ya nuna haka , ina basu nayi sallama dasu na wuce gida abuna...

Fitar Sultana daga gidan sukaci gaba da tattaunawa yayin da Ummu Affan tace ni zan faɗawa Abbu Affan idan ya yadda , Maman Sadiq tace ki rabu dashi kinsan mazanmu baƙin ciki garesu su kaɗai suke so su ƙaru da sunga hanyar da zaka samu sai su nemi bulo da suminti su yaɓeta , kiyi shirunki kici gaba da sabgar gabanki gaki shugabar ƙungiya kinga idan aka baki kayan ki raba kina iya danne abunki kice ance za,a kawo amma har yanzu bai iso ba , idan kuma kina ganin zai hana taron sai a riƙayi a gidana , ni nafi ƙarfin mijina dan bai tsaremin ci 3 a rana ba bare ya juyani wallahi.

Ummu Affan tace tou idan kuma akace an ganni a wurin taron fa ? Tsoki tayi tare da cewa banda kike banza ai niƙaf zaki saka waye ya isa ya ganoki ? Ey fa haka ne , tou Allah yasa karta juya tunaninta akanmu ta samu wasu daban , Maman Sadiq tace ai gobe idan Allah ya kaimu sai muje gidansu muce munzo gaisheta sai mu sake tuna mata muce karda ta manta damu , Ummu Affan tace haka ne zanzo , bara na bada a siyomin cefane yau a gidan nan miyar ja kowa zai sha... Dariya sukayi tare da cewa sai sun haɗu goben ta fita a gidan...

A ƙofar gida na samu Babana yana zaune ya zagba tagumi ga dukkan alamu akwai abinda yake damunshi , gaskiya ina san Baba kuma wallahi yana bani tausayi bawan Allah , daga nesa dashi na tsaya nace mike damunka kake tunani kamar macen data rasa miji ? Ba tare daya kalleni ba yace ba kince saina biyaki motarki ba , nace idan nace sai ka biyani mota kuma sai ka zauna ? Ka tashi kaje ka nemomin kayata , nifa saidai kawai in siya miki wata tunda ba ɓacewa tayi ba nace miki a caca aka cita ,

Kiyi haƙuri Mamana , nace idan na ƙyaleka baka biya motar nan ba gobe gidan zaka saka shima a cinyeshi sai mu koma kuma muna raɓe² tunda cacar ta daina yinka basai kayi haƙuri ba ? Baba yace insha Allah nama daina cacar daga yau idan dai hakan zai miki daɗi , zanyi magana naji ƙaraurawar kaina ta buga da ƙarfi , addu'o'i naci gaba dayi dan na fara fahimta sheɗanci na yana cikin kaina ,

Ƙarfin hali nayi cewa daka hutama kanka ina faɗin haka nayi cikin gida , ina tunanin anya kuwa kaina ɗaya ? Koma dai miye Allah yana tare dani ,

Al ' Ameen durƙushe a gaban mai girma gwamna yana gulma , Allah ya taimake ka har yanzu mai gida bai rabu da yarinyar nan ba , kai kace in saka ido sosai kuma duk abinda yake faruwa a tsakaninsu in faɗa maka , tou wallahi wannan motar daya siya kayi mishi faɗan siyenta ita yama ɗauka gaba ɗaya ya bata ita , kuma hada kuɗi yace tasha mai amma kuɗin bansan ko nawa bane ,

Dady yace tou ai ya kyauta ni bansan yadda zanyi dashi ba , mai ɗaki shi yasan inda ruwa ke zubar mishi sai yaje yayi ta tarayyar da ita , ƙara duƙar da kai Al ' Ameen yayi yace Allah ya taimake ka a gani na bai kamata a zuba ido abarshi da ita ba ya kamata a sake dakatar dashi kafin abun ya wuce misali , Dady yace idanma gidansu zai koma da zama yaje ya koma tunda ba yaro bane shi ai yasan abinda yakeyi ,

Al ' Ameen yace ranka ya daɗe ai bazaka so a kaishi a baroshi ba , gara a tari abun tun wuri basai yayi nisa ba a kasa taroshi ba , Dady yace wai ba Dikko bane ba ? Yace Eh , yace tou ka ƙaleshi tasu ta haɗosu kasanshi baida gwani ka basu wasu kwanaki zakasha mamaki , ba haka Al ' Ameen yaso ba amma baida yadda zaiyi dole ya haƙura amma zai faɗawa Momy ita kaɗai zatayi maganin Sultana , daga nan shi kuma ya samu ɗiyar yayarshi ta shigo babu ɓata lokaci ,

Da daddare bayan na gama abinda nakeyi Alaji na kira { Abbu Afsar } ya kaini gidan Mamy tunda banda mota , motar da Dikko ya bani kuma ba yanzu zan fara hawanta ba akwai tanadin da nayi mata nasan duk ranar dasu Amisty suka ganni da ita sai sunyi hawan jini ,

Da sallama na shiga gidan , daga cikin ɗaki ta ansa min sallamar tare da cewa shigo Sultana har ta ɗauki miryata , nace tou ɗakin na shiga da sallama na samu wuri saman daka²n kujerunta na zauna , bayan na zauna na gaisheta cike da biyayya sannan na gaishe da wani mutum dake zaune yanacin abinci , kallonshi Mamy tayi cewa tou ɗauki abinci ka koma waje zamu tattauna da baƙuwa , yace tou Hajiya ya ɗauki abincin ya fita daga ɗakin...

Bayan fitarshi nace Aunty kiyi haƙuri da Allah akan abinda ya faru dani dake jiya , nayi miki rashin kunya wanda haka bai kamata ba kuma ba tarbiya bane ɓatawa na gaba da kai ba , kiyi haƙuri kuma insha Allah bazan sake ba , jakata na buɗe na fiddo kuɗin data bani nace kuma gama kuɗinki na dawo miki dasu , maganar matar kuma zan kawota kiyi haƙuri bazan sake ba ,

Murmishi Mamy tayi tace ba komai Sultana ni dama banji komai ba , Allah ya haɗani dake kuma yasamin soyayyarki a zuciyata kuma nayi ɗamarar taimakonki in Allah ya yadda ,

Godiya nayi tare da matsawa gabanta zan ajiye kuɗin , tace ki barsu ki riƙesu , nace a , a Aunty ki barsu wallahi , tace bani nace ki barsu ba ? Bana so muna jayayya dake ki maida kawai a jaka , nace tou , jakata na buɗe na saka kuɗin , daga nan muka ɗan taɓa fira har take cemin kece kike mamakin ina da aure ko ? Murmushi nayi amma banyi magana ba , mutumin data fitar yanacin abinci shine ta kira , bayan yazo tace tou kinga mijina nan ,

Kallonshi tayi tana cewa wai mamaki take ina da aure , cike da biyayya yace Allah sarki , Mamy tace tou jeka tunda ta ganka , kamar sakarai kuma ya juya ya fita , a kunyace nace tou Aunty ya maganar baƙonmu na gobe ne ? Tace zaizo yanzu ma muka gama waya dashi , nace tou ya maganar yaran gidan Baba ƙarami ? Mamy tacemin komai ya tafi dai² karki damu amma ina ganin tunda ita Hamida tahau layi kawai mu fita safgarta , nace da ina so ta samu kuɗi , Mamy tace manta da "yan gidanku domin dama su tuni suna cikin sahun *kwarata...* tuni sun daɗe a harkar bariki tunda sune suke kula da kansu ki rabu dasu kowa yayi sabgar gabanshi , nace tou ,

Mamy tace yawwa akwai wani Uncle Al ' Ameen lokacin dana saka layin da kika bani yana ta kira babu ƙaƙƙautawa , gajiya nayi da nacinsa na ɗauka waya , bayan mun gaisa yacemin da Allah wannan wayar ta doughter inshi ce aka yadar da ita , ko ina zai sameni ya ansa ? Sai nace masa ni ba waya na samu ba layi na tsinta ,

Gaskiya da nayi niyar mu haɗu na bashi layin dan naji shima yacemin a katsina yake , abinda yasa na fasa yamin burga da cewa zaisa a kamani , nace masa shi ɗan uban waye a garin katsina shine yacemin daga gidan gwamnati , nace gwamnan ya tsaya maka ko waye ? Shine sai yacemin layin wayar matar ɗan gwamna ne , cika bakinsa yasa na saka number a wayata na duba ta whatsapp hoton Dikko ne na gani a d pn inshi , abinda na fahimta wato shi yaron Dikko ne , amma idan na tuna da labarinki kuma idan na fahimta Dikko shine kukayi faɗa a motarshi ! Me ya haɗaki dashi kuma miye tsakaninku ?

Ajiyar zuciya na sauke tare da gyara zamana nace tou kila sato wayar tayi amma ita wannan ai bata taɓa aure ba , shi kuma mai maganar yace miki layin wayar matar Dikko ne , ko kin manta matar Dikko ta mutu ne ? Tace min haka ne kuma fa , nace gaskiya shiri ne abun , naci gaba da cewa yanzu wayau ɗaya zamuyi mishi shine kice masa ya turo miki lambar wayar da za'a iya samunta , domin akwai wasu tambayoyin da zamuyi ma mai layin idan ta bada ansa za'a bata wayarta da layinta wannan shine mafita , nayi haka ne dan na samu ta hanyar da zan turawa yarinyar nan vidion da zamu ɗauki ubanta , naƙi yadda kuma na faɗa mata nasan Dikko saboda gudun bita da ƙulli , bayan kuma Sadiya ta rasu babu wanda yasan Dikko yayi auren ...

Miƙa hannuna nayi tare da cewa Mamy inga hoton , miƙomin wayarta tayi bayan ta kamomin hoton Dikko a wayarta tana cemin yanzu lambar wayar yarinya zansa shi Al ' Ameen in ya turo mana kenan ko ? Banajin ta domin hankalina da duk natsuwa ta ya tafi wurin kallon kyakkyawar fuskar mutumina ,

Wallahi bana gajiya da kallon kyakkyawar fuskar Dikko , yayi min kyau sosai a hoton kuma yayi hoton a cikin yanayin fushi ya ɗan soɓaro leɓonshi na ƙasa , yayi kyau sosai kuma shima Al ' Ameen in yasan hoton ya haɗu shi yasa ya sakashi a whatsapp inshi , idona ya cika da kwalla a zuciyata nace shine dai kayi fushi dani ko ?

Kiran waya ya shigo a wayar dan haka na miƙawa Mamy wayar na miƙe ina cewa sai mun haɗu goben idan Allah ya kaimu , tace tou Allah ya kaimu ki gaida gida , banyi magana ba na fice buzum² zuciyata namin babu daɗi ,

A gajiye na isa gida , koda Alaji ya ajiyeni kawai ce masa nayi saida safe dan banajin daɗi kwata² kuma yaso na tsaya muyi fira na

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment