Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba tare daya sake cewa komai ba , bayanshi Hafsa tabi saida ya shiga mota ya zauna sannan yasa Al ' Ameen yayi rabon kuɗi wa duk wanda muke tare dashi har "yan dabana saida Dikko yasa aka basu kuɗi amma nidai bai bani ba kuma ban damu ba saboda dama ni basu nake jira ba !

Al ' Ameen yana gama rabon kuɗi ya koma mota , har yanzu Dikko ni yake kallo gilashin saitin shi Al ' Ameen ya ɗage zuwa sama sakamakon da yake ƙasa , bai daina kallona ba har Al ' Ameen yaja motar suka tafi ,

Goge fuska ta nayi da hannu na , sannan na buɗe jakar da Dikko ya ajiye a gabana , irin cimgom in da yake amfani dashi ne sai farar takarda da akayi rubutu a samanta , suke nan a cikin "yar jakar , ban buƙatar dubawa sabona nasan gani kawai zanyi bazan iya karantawa ba, kuma babu wanda zan ba ya karanta min saƙon Dikko daga nan har lokacin da zan iya karantawa da rubutawa....

Tunda Dikko yayi min wannan wulaƙancin ban sake magana ba har aka gama raba takardunmu muka koma gida ban sake magana da kowa ba , kuma tunda nayi wanka na shiga ɗaki ban sake fitowa ba saida gari ya waye '

Bayan na gama duk abinda nakeyi na fito tsakar gida na zauna saboda ba yau zamu fara fita ba sai an fara kira a waya lokacin zamu tabbatar da cewa tallarmu ta samu karɓuwa a wurin jama'an gari,

Nana na gani riƙe da kwalar rigar mijinta tana zazzaga jikinta irin abin nan da yara keyi idan suna faɗa , zama nayi ba tare dana kalli inda suke ba amma hankali na da kunnuwa na suna wurin su , wallahi sai ka sakeni kalmar da naji ta fito daga bakin Nana kenan kuma har yanzu bata saki rigar mijin ba.

Audu yace ba ƙin sakinki zanyi ba amma sai kin faɗamin abinda nayi miki wanda yasa kike so na sakeki ! Nana tace lallai bama ka da kunya da har kake tambayar abinda kayi , tou na gaji da zaman cida kaina zaman wahala zaman kunci kullin muna can barbaɗe kayanmu a saman kai bama ƙerau bama sabuwar anguwa zama gidan haya , tou wannan aure dai a sahalewa juna uban kowa ya huta...

Daga inda nake zaune nace Audu wai duk meya haɗaku ne wai ? Ku kullum faɗa ke Nana kamar kece kaɗai matar aure a gidan nan ? Duk wadda kika gani da mijinta haƙuri takeyi ko suna wani saɓani basa fitowa tsakar gida ke kullum dake da mijinki kamar abokan faɗa ? Gaskiya ki daina wannan rayuwar kece ƙasan Audu dole sai kin kiyaye idan har kina san ganin daidai a rayuwarki.

Sakar mishi riga kizo kiji wata magana, babu musu ta sake rigar mijinta ta taho wurina, shi kuma Audu fita yayi ba tare daya sake cewa komai ba,

A ƙofar gida kuwa A ` i ce ta tare Audu bayan gaisuwa tace mishi naji shiru ya kamata kayi wani abu don Allah , zama Audu yayi a saman dakali sannan yace ki ƙara haƙuri , murmushi A ` i tayi tare da cewa ba komai Allah ya tsare ya dafa maka akan duk lamuranka , da amin ya amsa sannan ya wuce ita kuma ta shigo cikin gidanmu...

A ƙofar ɗakina A ` i ta samemu ina bawa Nana shawara , amma tana zuwa gaba ɗaya ta jagula komai ta ida firgita Nana har na kasa gano gabanta bare bayanta,

Ajiyar zuciya nayi tare da bin A ` i da kallo ban sake magana ba ina dai jinta tana ta ɗora Nana a hanyar banza ita kuma tana ta karɓewa dan a ganinta shawarar A ` i itace mafita a gareta ,

Ƙawar Amisty da tayi ciki suka shigo da sallama ita da wata mata , inda nake zaune suka nufo gaisawa sukayi dasu Nana sannan sukace wurinki muka zo , miƙewa nayi tare da cewa ku shigo na faɗi maganar tare dayin gaba suka biyo bayana !

Wurin zama na basu sannan nima na zauna muka gaisa , bayan gaisuwa ƙawar Amisty tace Sultana kin ganeni kuwa ? Murmushi nayi ban bata amsa ba , taci gaba da cewa idan da hali nima zan shiga ƙungiyarki , ga ƙawata itama zata shiga, kallo nabi su dashi bayan wani lokaci nace ita ƙawar taki tana da aure ne ?

Dukanmu matan aure ne , Ni suna na Fadeela inji ƙawar Amisty mai cikin shege , sai kuma ta nuna ƙawar da suka zo tare tace ita kuma sunan ta Zalifa , saida na ƙara kallesu tsaf sannan nace miye dalilinku na shiga wannan ƙungiya ... ?

Wacce aka kira da Zalifa tace wato ina da wata damuwa ce ta musamman wacce bazan iya biyanta ba ko cika burina ba dole saina shiga wannan ƙungiya mai albarka , ina so na samu goyon baya da taimakon tantiran dake cikin wannan ƙungiya ,

Murmushi nayi sannan nace wannan wace irin damuwa ce ? Gyara zama Zalifa tayi tare da cewa wato ina da wata maƙociya wacce na ɗauki amana da yadda na bata , bana ɓoye mata sirrina ko kaɗan .

Wata rana ta shigo gidana sai taji muna hayaniya da mijina , bayan mun gama mijina ya fita sai take tambayana abinda ya haɗamu , ban ɓoye mata ba kamar yadda na saba na kwashe komai na faɗa mata ,

Na ƙara da cewa bansan abinda nayi masa ba duk abinda bai taka kara ya ƙarya ba sai yayi ta faɗa akanshi wani lokaci ma hada duka , sai tacemin yadda Allah ya halittani da kyakkyawar siga mai burgewa na kashe aurena zan samu wanda yafi mijina ,

Nuna mata nayi cewa bana iya kashe aure na amma zan haƙura gaskiya na zauna dashi a haka tunda ina sansa wata rana zai gaji ya daina , sai tacemin ai sai anbar zomo yake zama guza , mazan yanzu da asiri ake ladaftar dasu in bada kuɗi taje ta nemo min asiri inyi maganin mijina.

Banji wani komai ba na bata kuɗi masu yawa dan tacemin itama mijinta da yake mata biyayya malamin yayi mata maganinshi , kuma naga yadda mijinta yake mata biyayya sosai kuma yanajin shakkunta dan haka na bata kuɗin nima a samomin asirin in riƙa dawwara mijina...

Haka kuwa akayi tayi ta kawo magani ina barbaɗawa mijina a abinci ina zuba mishi a ruwan wanka da abin sha laya ƙarƙashin filo wasu layun a ƙarƙashin gadonshi , tunda safe kafin ya fita na kunna hayaƙi , shirka dai iri iri da ƙazanta nayi ta barbaɗawa mijina yana lashe wa ,

Haka tayi tamin wayau tana karɓemin kuɗaɗe , murmushi tayi tare da cewa kinsan me ya faru ? Nace mata A , a, tace kwasam sai ta tayar da fitina wa mijinta da yake aurenta , kuma yanayi mata wani irin azababben so yana ƙaunarta fiye da duk yanda zan faɗa muku , amma saida ta kunno masifa ya saketa , har wannan lokaci bata daina kawomin asiri ba ,

A daren ranar data kawomin magani na zubawa mijina a abinci yana gama ci babu laifin zaune babu na tsaye ya gwagwaɗamin saki 3 ita kuma ta aure min miji gani nan na fito bani ga tsintsu bani ga tarko kinji hukuncin da tayi min....

Murmushi nayi kaɗan sannan nace kin aihu da mijin ne ? Tacemin a , a , nace ita ubanta yana raye ne ? Tace min Eh nace ya yanayin samunshi yake ? Tace babu laifi gaskiya yana da rufin asiri , da kyau nace tare da cewa mijinki kina san ki koma gidanshi ko kuwa ya kike so ? Zalifa tace gaskiya bazan koma ba so nake kawai ku riƙe mishi wuya ku jawo shi a cikin ƙungiyarku ku ƙare duk wani tattalin arziƙinshi babu asiri Sultana ki fitar min ita daga gidan...

Jinjina kai nayi tare da cewa ni bana asiri amma sharrina da kaidina yafi asiri bala'e a rayuwar ɗan adam , waya na bata tare da cewa sakamin lambar mijinki ki ajiye min ita da lamba 4 , ansa tayi ta sakamin tayi saving kamar yanda nace , bayan ta dawomin da wayana nace babanta a wane anguwa yake ne ? Zalifa tacemin gaskiya bai cika zama ba , nace to karki damu zai zauna dan dole ki samo numbershi ni kuma nayi miki alƙawari su dukansu zamuyi musu aiki ...

Zalifa tacemin ina da motar hawa idan zakuyi amfani da ita , nace tou yayi kyau mun gode , jakarta ta buɗe ta fiddo kuɗi har naira dubu ɗari ukku tace gashi taba ƙungiya tata gudumawar , godiya nayi tare da ƙwalawa A ` i kira nace ta kawo musu form su cika , Zalifa tace karki damu zan cika anjima idan muka dawo akwai inda zanje yanzu , nace tou babu damuwa sai kun dawo...

Miƙewa sukayi zasu tafi nabi bayansu dan rakiya amma ban wuce ƙofar ɗakina ba , anan na tsaya nayi musu addu'ar sauka lafiya , bayan sun fita na koma ɗaki naci gaba da "yan hididdumu na , na tattara kaya saboda zamu tashi daga gidan yau zuwa sabon gidan da na siya , kuma duk nace matan gidan subini mu koma gidana da na siya , sauran ɗakunan da suka rage zan nemo "yan gidanmu na tattara su wuri ɗaya hadashi gogon wato Babana dan nafi so nayi karuwanci a gaban idonshi ya gane cewa ba'ayiwa iskanci haye....









29/08/2019



*JAMILA MUSA ...* 🤙🏻


⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 22


Saida na tattara duk wani abu da nasan ina buƙata na adana shi a ma'adar da nasan bazai wulaƙantu ba , ko wace macen da zamu koma da ita gidan nice nasa aka kwashe kayan kowa aka kai gidan da zamu koma da zama...

Kafin azahar har mun gama saboda babu mai gado a cikinsu duk dai katifa ne kuma babu macen dake da ledar tsakar ɗaki saini !

Saida na tabbatar an ajiye komai a mazaunin daya kamata , sannan na shiga wanka , kafin in fito an share gidan ƙwal gwanin burgewa , Hafsa tazo sai kashe sulfie sukeyi ita da sauran jama'ar tamu ,

Ina fitowa daga wanka tace uwar room maza ki shirya kizo ayi dake kar a baki labari , Amisty ce tace babu wani uwar room uwarmu ce gaskiya a wani cire room kawai mu kirata da mother , shewa sukayi dukansu lokaci ɗaya suna cewa uwa...

"Yar gajeriyar dariya nayi cikin sigar barikanci na wuce ɗakina banyi musu magana ba , hotuna sukaci gaba dayi har na gama shiryawa nima na fito !

Ina fitowa suka ɗauki sowa domin sun san mother tasu ba daga baya ba wurin iya ɗaukar wanka , banje koya ba kuma babu wanda ya ɗorani nice na koya dakai na kuma ni na ɗaura kaina , banda uwar ɗaki nice uwar ɗakin kaina kuma nice uwar ɗakin wasu ,

Amisty ce ta bani kujerar roba na zauna, da "yan daba da duk wata kwartuwa mun hallara wurin, bayani na farayi musu kamar yadda muka saba a duk lokacin da muka zauna...

Hafsa kuwa ciro wayarta tayi ta faramin vidio kamar yadda naga ta koya kwanakin nan, saboda haka sai nayi shiru yayin da su Amisty suka ci gaba da goga bayani tare da ƙara ƙwarara wa kowa guiwar shi a cikin harkar bariki !

Komai ɓaro ɓaro sukeyi suna sakin maganganu yadda harshen kowa yake iya furtawa, Hafsa kuwa abinda yasa banyi mata magana ba na lura da halayyarta tana da saurin hasala sannan kuma tana da ɗauka da ajiyewa , na ukku kuma abinda na lura da ɗabi'ar ta zatayi tonan asiri haka kuma zatayi cin amana zata tona asirin wanda suke tare idan suka rabu ...

Ni kuma banda haƙuri idan abu ya ɓatamin rai saina bigi mutum nake samun natsuwa , tou zan ƙyale Hafsa amma nasan irin zaman da zanyi da ita , sannan nikam dai sirri na ƙarya takeyi taji shi kuma anƙi a rabun da ita dan idan har na rabu da Hafsa zata yankamin ƙunya biyu dani da "yan team inta zamu zama abokan hamayya , kuma babu abinda zai hana asirce asirice saboda su sun ta allaƙa da malam tsibbu amma maganinta ɗaya shine zan sace wayarta ta ɓace kwata kwata babu layi babu wayar bare kuma tabi tsohon tarihin jerin kira ta samu wasu lambobi, idan taƙamarta sabko tabbas ni a wurin na kwana ,

Har aka gama zaman ban sake cewa umm umm ba, bayan an gama duk suka zagayeni akayi ta hotuna , duk wanda yaga hotunanmu yasan ni iskanci na ya fita daban a cikin nasu, yadda suka bani shugabar iskanci tabbas iskanci ya fito a tattare dani...

Bayan an gama hotuna muka fito ƙofar gida , saman motar Hafsa nayi tsalle na haye , Hafsa tace bari in ƙara ɗaukarki hoto murmushi nayi tare da cewa ngode , ɗaukana tayi nanma kowa ya ƙara yayyaɓeni sai an mana maza da mata duka Hafsa taci gaba da bamu filasha !

Saida ta gaji da ɗauka sannan mukayi sallama da ita , ta wuce gidansu mu kuma muka koma namu gida , dukanmu a ɗakina muka sauka , har dare suna nan domin Amisty zata kwana wurina ne kuma ma dai ta dawo wurina da zama kwata kwata...

Bansan abinda yasa ba kuma ban tambayeta dalili ba , sai dare sosai su A ` i suka tafi gida , Nana da Karima kowa ya shige ɗakinshi muka rage daga ni sai Amisty, addu'a nayi na kwanta bacci ,

A ɓangaren Hafsa kuwa dan ta wulaƙanta ni ta tozarni a idon Dikko idan ina da sauran mutunci ko ƙima ta kakkaɓe a wurin shi , duk hotunan data ɗauka gaba ɗaya ta tura mishi su , da vidio maganar dana fara da kalaman batsar dasu Amisty sukayi , da kirana da uwar gidan kwarata da akeyi duk saida ta bawa Dikko labari bayan ta gama tura hotunan da vidio ',

Idan ran Dikko yayi dubu saida ya ɓaci amma bai nunawa Hafsa ba ranshi yayi mishi babu daɗi ba dan baiyi tunanin irin wannan hotunan zata riƙa kawo mishi ba , kawai dai ya ɗauka hotunan Sultana zata turo sai kuma idan tana zaginshi sune kaɗai zata faɗa , amma wannan vidio ya girmi ganin idanuwanshi maganganun sun girmi jin kunnuwanshi ,

Tabbas zai takawa Hafsa burki da irin wannan vidio kuma zai tsawatar da ita zai gwalashe abun idan ba haka ba irin wannan vidion na An mata zasuyi ta yawo a social media shi kuma idan har haka ya faru baiji daɗi ba,

Tunani dai barkatai a zuciyarshi , amma ranshi da zuciyarshi yafi bashi cewa kayi mata magana gaskiya shekaru biyu idan suka tafi a haka kaga zakayi takon saƙa da karuwa mutuncinka martabarka da ƙimarka zai zube a wurin al'umma ga siyasa bata raina abun magana, sai ka tsaya takara zaka gane abun ya zama shirme, shawarar da zuciyarshi ta yanke shine ya fita daga harkar taron yara don asali nasaba da mutunci gidansu ba iri ɗaya ne dana gidansu Sultana ba.

Burun duniya akan shi ɗaya tal mahaifinshi ya dogara yayi tsayuwar arfa wurin ganin ya zama mutumin kirki ya fito cikakkan mutum ya kashe kuɗaɗe da yawa wurin ganin ya tsaida ni a saman ƙafafuwana , mutane suna cewa duk "ya "yan da aka ɗauki soyayyar duniya aka ɗora musu gurɓatacci ne , mafiya yawansu basu da tarbiyya , ni kam ba lalatacce bane domin idan nayi duba da yadda nazo...

Tsoki yayi tare da kiran Hafsa yayi mata tatas yace daga ita harma Sultana duk zaici mutunci su bayasan maganar Sultana haka kuma itama bayasan ta sake shiga sabgarshi ko kiranshi ta sakeyi ko text wallahi sai yasa an kulle mishi ita , yafa ci uban Hafsa sosai ya ƙara da cewa itama Sultanar ta sake ambatar sunanshi wallahi zaici ubanta ne, saida ya tata iskanci mai isarshi ya kashe wayarshi,

Al ' Ameen yace mai gida lafiyarka kake ta faɗa , idanuwa jajir Dikko yace Al ' Ameen idan aka ce maka na taɓa zina tsakaninka da Allah zaka yadda ? Al ' Ameen yace mema yasa kake faɗar wannan maganar don Allah ka daina abinda ma bazai taɓa yuwuwa bane ba...

Idon Dikko cike da hawaye yace kasan yarinyar dana shaƙe a asibiti ? Al' Ameen yace Eh nasanta mai gida , Dikko yace kaga ai yarinya ce sosai ko ? Al ' Ameen yace Eh , Dikko yace wallahi da nayi auren wuri ina iya haifar yarinyar nan , amma tsautsayi da ƙaddara yasa na saki wani irin ƙatoton layin da inaji kamar in cakawa kaina wuƙa in mutu kawai in huta,

Murmushi Al ' Ameen yayi tare da cewa haba mai gida ina kai ina haifo mai shekarun yarinyar nan , da kayi aure kam da wuri baka tsaya karatu ba kuma gashi har yanzu duniyar nemanta akeyi duk wanda kuɗi yayi ma yawa so kawai yake a kirashi ranka ya daɗe , duk dai haka gaskiya baka haifi yarinyar nan ba , tsoki Dikko yayi tare da ɗaukar wayoyinshi ya shige ciki , gefen gado ya zauna tare da zagba tagumi ya fara tuno wa kanshi ko shiɗin waye.....


*_WAYE DIKKO...?_*

Dikko Umar Kurabau shine cikaken suna na...


Mu cikakkin asalin "yan cikin garin katsina ne , bamuyi rayuwa a ƙauyen kurabau ba haka mahaifina da kakana basu rayuwa a wannan ƙauye ba , amma kakan dadyna shine yayi rayuwa a cikin wannan ƙauye dake ƙarƙashin kauyen rimi local government...

Mutane ne masu cikakken arziƙi da wayewa kuma sarautar kauyen a gidansu kakana take wacce suka gada suma tun iyaye da kakanni , ko a wancan lokacin mutanen kurabawa tuni su wayayyu ne kuma tuni suka waye da ilimin zamani !

Kakan dady na duk da yake bakauye baya da kidadanci haka kuma bashi da jahilci , wayyen tsoho ne da yasan rayuwa , kuma tsohone mai cikakken ilimin addini,

Abinda ya kawo kakana cikin birni shine neman ilimin zamani , kuma shima mahaifinshi shine mutumin daya fiddoshi dan neman ilimi bayan ya tabbatar daya haddace al'kur ani mai girma a saman kanshi kuma yasan littafai na musulinci .

Karatun boko bai wani bashi wahala ba saboda yana da ilimin addini sosai , saida kakana ya gama karatun sikandire sukul { Secondry school } ya koma kauyen kurabau,

Mahaifinshi yace tunda ya ɗagawa ƙauyen na wasu shekaru ya haƙura kawai ya koma cikin garin da zama , dan a samu ci gaban rayuwa !

Mahaifinshi da kanshi yazo ya nema mishi wurin zama sannan ya bashi kuɗaɗe ya kama kasuwanci ya nemi abinda zai dogara da kanshi, dan a wancan lokacin idan mutum yayi secondry sch anan yake tsaya dan duk wanda yazo wannan matakin gani ake an ƙure.

Allah kuwa ya saka ma nemanshi albarka dan kano yake zuwa sarin atamfofi da shaddoji da yadika ,kafin shekar ya zagayo abubuwa sun fara canzawa domin Allah yasa ma neman albarka kuma Allahn ya yaddar mishi ! Dan ubangiji dayace maka zama zaka zama....

Haka rayuwa taci gaba da tafiya cikin ƙanƙanin lokaci sunan Dikko Muhammad wato kakana ya fara zagawa a cikim garin katsina dan zuwa wannan lokaci ya baza yara suna neman mishi kuɗi dan kasuwar tafi ƙarfin mutum yanzu, kuma mutum ne shi mai kauta ,

Shi kuwa Muhammad baban Dikko wato kakan babana ganin dukiya ta fara yawa hankalinshi ya fara tashi gashi har yanzu Dikko baiyi auren farko ba , kuma zuwa wannan lokaci ya rage zuwa gida dan sai yayi wata shidda ko fiye da haka baije gida ba , idan yaje malam yayi mishi magana yana daɗewa baizo ganin gida ba sai yace abubuwa sunyi yawa yanzu ma dakel ya samu yazo,

Ganin haka yasa malam ya yanke shawara aura wa Dikko mata kuma "yar nan cikin ƙauyensu dan malam yace idan "yar gida ce yake aure dole za'a riƙa ganinshi ko baizo dansu ba zaizo dan matarshi,

Haka kuwa akayi malam ya aurowa Dikko mata bada saninsa ba yasa aka kawo mishi amarya har katsina, saida aka kawo amarya akayi masa bayani malam ya auro masa ita , bai wani ji komai ba yace Allah ya basu zaman lafiya,

Zaman lafiya sukeyi da matarshi Binta saboda matace mai haƙuri da kuma kauda kai da duk wani abu na rayuwa , saboda itama sai tayi wata nawa bata ga Dikko ba dan shi ba auren yake saurare ba duniyar kawai yake nema ita kuma Binta bata wani damu ba tunda ci da sha har sutura bata rasa ba , idan Dikko yazo mata as miji zasuyi rayuwar aure idan baizo ba babu abinda ya dameta...

Haka dai rayuwarsu taci gaba da tafiya , kuɗin Dikko kuma har an fara zarginsu a cikin gari cewa tsafi yake yi , dan shima kanshi zuwa yanzu baisan iyakar abinda ya mallaka ba , koda Binta ta samu ciki gida Dikko ya maida ita ta aihu , tunda ya kaita bai sake komawa ba har ta aihu ta gama wanka baije ba, abinda ta aifa ma bai gani ba babanshi yayi duk abinda akeyi ma duk macen data aihu komai anma Binta da ɗanta da yaci suna Ummar wato

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment