Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

neman abinda zasuci karma ayi maganar wurin zama amma kai har lokacin siyan kaya kake yi Baba......? Duk a zuciyata nake wannan tunanin.

Mamana, ya kira suna na, kallonshi nayi ba tare dana ansa ba, tunanin me kikeyi ? Bayan gani a duniya ! Idan har ina nan a raye baki da matsala nayi miki alkawari zan kula dake zan kange miki duk wani bakin ciki da damuwa, idan dan maganar kayan makaranta ne da littafai zan siyo miki komai ma ki daina damuwa, zan miki duk abinda kike so dan kiyi farin ciki Mamana , wallahi da ina da iko ko kuda da sauro da ban barsu sunzo wurinki ba, haka nake alfahari da aihuwarki farar mace lantarkin ciki gida, da nasan zan haifeki wallahi da ban tara wannan yame yamen "ya "yan ba,

A ranar da aka aifeki a ranar naci makudan kudade a wurin wasan caca , tun daga ranar na gane ke mai sa'a ce, wannan dalilin yasa nasa miki sunan mahaifiyata ya karasa maganar yana murmushi, sannan yaci gaba da cewa zuwanki yasa talauci ya guji rayuwata, shi yasa na tattara miki buri da yawa domin nasan kedin mai arziki ce.

Yana fadar haka yace tashi muje, tashi nayi nabishi, yauma cikin wata zakanyar mota muka shiga, ta gaji da haduwa sai sanyin A C ke tashi ga kamshi mai dadin shaka, Babana fa dan gayu ne gashi da wayewa kuma yana da kalar burgewa amma babu halin kirki.

A daren nan saida Babana ya tabbatar duk abinda zan bukata ya siyamin, sannan muka wuce wurin dinki, tela ya aunani Baba ya biya kudi muka dawo gida,

Tunda muka dawo matarshi Mariya ta tada hankali ta fara zagina tare da aibatani, bata san Babana yana tare dani ba da batamin ba, yana shigowa cikin gida yace mata ta tafi ya saketa, maimakon Mariya tayi farin cikin sakin kawai sai ta kama kuka, dani Babana ke aure ya sakeni wallahi sai nayi farin ciki sosai na rabu da rayuwar wahala,

Amma Mariya saita durkushe tana bashi hakuri, wallahi ko sauraren ta baiyi ba, anyi an gama domin Babana idan ya saki mace ya gama da ita har abadan duniya baya maimaita mace idan har ya riga ya rabu da ita, dan yace ko sitira sawa daya yake mata mace kadai yake ma maimaici a rayuwar shi, shi yasa idan har ya saki yake mantawa da babinta a rayuwarshi.

Fita yayi yabar gidan, Mariya kuwa kuka takeyi kamar zata mutu, wallahi ta bani tausayi sosai dandai ba hurumi na bane dana bashi hakuri kuma tabbas nasan zai hakura amma ba ruwana tunda ba hurumi na bane, kuma nasan tsakanin gobe da jibi tabbas saiya karo aure.......

Zaune muke lafiya a gidanmu, rayuwar dai tana nan kamar kullum kowa shi yake cida kanshi, gaba gaba dai yayuna sun fara harkar barikancin su har a cikin anguwa, saboda Baba baya tsawa tawa dan yaga dama ma ya kwana biyar ko sati baya gida,

Bayan sakin Mariya da sati daya Baba ya auro wata "yar fiririyar yarinya wacce zata tsaya iyakar sa'ata, kankanuwar yarinya itama mai zubin karuwai, wankan tarwada ce kallo daya zakayi mata kasan ta gaji da fekewa da bari...

Idan kayi mata magana saita wani yamutsa fuska sannan zata daga idonta dakel tayi maka magana, kai nidai sam tsarinta bai burgeni ba haka kuma bata wani shiga raina ba, dan bata da kunya ko ta misali, caccakakkar "yar iska ce , tasha iskanci ta koshi, amma anyaBaba auro yarinyar nan yayi kuwa ?

Rayuwata nakeyi cikin farin ciki, bani da wata damuwa shi yasa bana gane abinda kowa yake ciki a gidanmu, idan na fito daga dakinmu sai dare nake komawa saboda Innata bata san gani na, dan kishiyoyi sun tisota a gaba da habaici saboda ni, Babana yana kula dani sosai baya barina shiga damuwa, ina zuwa makarantar boko da islamiya , amma boko gugar kaya kawai nake inje, islamiya kadai nake da fahimta.

Tafiye nake a cikin nikaf ina, sauri kawai nake na isa gida saboda hadarin daya taso, sai wani irin iska akeyi mai hade da kasa, walkiya da cidar hadari duk sun karade sararin samani, tunda na biyo santar nan banci karo da kowa ba har na iso inda nake tunanin nan ne gidanmu,

Kamar yanda nayi hasashe haka na yanki hanya domin shiga gida dan bana ganin gabana saboda kasar data shigar min ido, na daga kafata in taka sumintin kofar gidan naji wayam, kara mika kafata nayi dan a tunani na ban tako daidai ba, kamar yanda naji daga farko yanzu ma haka naji,

Da sauri na bude idona dan inga lafiya ? Filin wurin kawai na gani kamar ba'a taba gini a wurin ba, salati nayi na sanar da ubangijina to ina "yan gidanmu suka tafi ?

Makota na shiga na tambayi inda "yan gidanmu suke, aka cemin Alhaji Sabo ya canza mana gida kafin wata ya kare mu tashi, tambayar dalilin tashin da rusa gidan da akayi nayi amsar da aka bani itace, *Dikko* ne ya siyi gidan amma wannan karon anyi ma kowa uziri ya fita da kayanshi.

Bance komai ba saidai na sake tambayarta ina gidan yake ? Kwatanci tamin gida na like da gidan da aka rushe nan muka koma, ban sake cewa uffan ba na nufi gidan.

Daki daya ne tak a gidan saboda haka kowa yana zaune cikin barandar dake tsakar gidan, sallama nayi amma babu wanda ya ansa min sallamar har Innarmu, nima ban sake sallamar ba na samu wuri na zauna tare da jan bakina na kameshi,

Dukanmu a tsakar gida muka kwana yayin da wasu suka kwana a zaure, babban gida ne sosai amma daki daya ne ya gina shima ajiye ajiye yake a cikinsa, gari na wayewa na shirya na tafi makarantar boko, Baba bayanan sun tafi gasar caca, dan bai fadawa kowa sunan garin daya tafi ba, ni kadai yayiwa bankwana.

A makaranta Amisty ta lura ina cikin damuwa, dan haka ta tambayeni abinda ya dameni, ban fada mata ba, saidai nace mata da Allah waye Dikko a garin nan ?

Hmm su Amisty idon duniya saida tayi masa wani irin kirari sannan tace miya hadaki dashi ne ? Nace mata kawai dai labarinsa nakeji shi yasa nake san sanin koshi din waye.

Abinda Amisty tacemin shine, yanda kike takama Babanki yana masifar sanki da kaunarki dan dole wannan misalin da kanki zanyi shi idan ba haka nayi miki ba tou fa lallai nasan baza ki gane ba,

Dikko d'a daya tak a wurin mahaifin shi, yana da yayu mata sosai saboda suna da yawa gidansu suma, amma basu kai gidanku yawa ba, abinda yasa kuwa aka tara yawa a gidansu saboda san haihuwar d'a namiji da basu samu ba,

Akan Dikko ya samu namiji daga shi kuma har zuwa yau din nan ba'a sake haihuwar namiji ba, Dikko gaskiya yana da kirki kuma shi ba dan iska bane amma gaskiya baya san raini,

Yana da alkairi sosai amma shi baya dariya haka kuma baya murmushi, ni bayan wannan bansan komai ba haka dai kawai naji ana fada a gari,

Gyara zama nayi tare da tambayarta shi kuma waye ubanshi ? Murmushi Amisty tayi sannan tace da Allah karki dauki ne wake da shinkafa mana, Dikkon ne a katsina baki san waye ubanshi ba ? Wallahi ban sani ba, na bata amsa, tashi tayi ta barni a wurin dan ita a tunanin na sani jan zance ne.

Har muka tashi makaranta Amisty bata fadamin ko waye uban Dikko ba, ni kuma ana tashi makaranta ban tsaya komai ba na nufi gida tunda nasan Babana baya nan,

Tunda napep ta ijiyeni, na hango kofar gidanmu daddabe da mutane, Dikko yana zaune a saman gaban mota ya kwantar da bayanshi saman gilas din motar kafarshi daya saman daya, ya tallabo kanshi da hannayen shi, kamar kullum yauma cingom yake ci, kananan kayane jikinshi ya dode da gilashi mai saukin duhu.

"Yan gidanmu sun daddabe shi suna bashi hakuri amma ko inda suke bai kalla ba bare su sa a ransu zaiyi magana, sai waso mana kaya akeyi daga cikin gida, yayin da "yan zaginshi ke cewa ai tunda har kuka tabo mai gida a garin nan sai kun rasa gidan zama, wannan dinma ya siyeshi idan kunyi zuciya ku gina naku talakawan banza kuna jayayya da masu katsinar gaba daya,

Inda jakar islamiyata take naje na duka na dauka, na koma gefe nayi tsayuwata tunda ko nayi magana babu wanda zaimin magana kowa haushi nake bashi,

Wani dattijo ne shima makoci ne , yace ni inje in bawa Dikko hakuri duk saboda abinda nayi masa yake ta wannan saye sayen gidanje, dan gajeren murmushi nayi tare da cewa Baba kenan aini wancan dan iska nafi karfinshi wallahi baikai matsayin da zan kalleshi ba bare har na bawa banza hakuri, idan kuma har ka tilasta naje to lallai ina zuwa zan jawo dan iska ya fado kasa,

Lallashi na dattijon nan ya farayi akan lallai sai naje na bawa Dikko hakuri, a lokacin har an gama fito da komai namu an fara rushe gidan.










01/08/2019




🤙🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 4


Ya uzura min sosai akan naje na bawa Dikko hakuri dan haka na tunkari wurin kai tsaye zuciyana tana min tsake tsaken mugunta iri daban daban.

Cike da bacin rai na isa wurin, kamar yanda na fadawa tsohon nan zanyi haka kuwa nayi, dan ina zuwa na kamo kafar Dikko da zumar na fadar dashi kasa ya karya kashin baya,

Amma ina, dan ina riko kafar shi daya, ya tattakura yakai min halbi da dayan kafar da ban rike ba, hanci baya raina duka lokaci guda jini ya ballemin kamar an yanka kosashshiyar kaza,

Yana halbina ya diro daga saman motar shima ashe yayo dagon muguntar shi yana neman inda zan sauketa ya huta, ganin jini yana bimin baki har yana digowa kasa yasa hankalina ya tashi,

Sosai nayo kan Dikko, yaranshi suna kokarin rikeni yace su barni yanzu zai koyamin hankali yanda idan na ganshi da gudu zan canja hanya.

Daga nesa mutane suka fara bashi hakuri dan babu wanda ya isa yazo kusa dashi, babu wanda ya kalla bare kayi tunanin ko zai saurare ka, kusa dani ya matso sosai, yasa hannuwan sa biyu ya riko min fuska, sai yanzu nakejin halbin da yayi min yake ratsa duk ilahirin cikin kokon kaina, gaba daya jikina ya saki ya koma kamar ba nawa ba,

Sama sama nake ganin Dikko har yanzu bai daina cin cingom in da yakeci ba, saida yayi min kyakkyawan riko sannan ya cire gilashin dake fuskarshi ya kalleni ido cikin ido sannan yayi dan kyakkyawan murmushi, wanda ke nuni da mugunta ta tashi...

Sai mun sake had'ewa an mata...yana fadin haka ya k'uma min kanshi da nawa wuri daya wanda haka yayi sanadiyyar daukewar gani na gaba, amma har zuwa wani lokaci goshina da nashi yana hade wuri daya,

Bai sakeni ba saida ya tabbatar na tafi suma, dan tabe baki yayi tare da dage girarsa ta dama sannan ya sakeni ya zura hannuwansa cikin aljihu ya nufi motarsa dashi da tawagarsa suka bar anguwarmu.

Ni kuma na fadi kasa somammiya, Allah sarki dan uwa mai dadi duk "yan gidanmu basu ji dadin abinda Dikko yayi min ba, sun tausayamin iyakar tausayi gashi babu mai kwandalar da za'a kaini asibiti, saidai aka samo kankara aka rika dandan na min a goshina tunda habo ne nayi,

Abokin Babanmu shi yaji labarin abinda ya faru damu, yana da wani gida na Alhaji Sabo da aka saka a caca ya ciwo gidan, shine ya bada makullin gidan aka kawo mana yace mu bude mu shiga,

Daukata sukayi suka shiga hadani tare da bani kulawa ta musamman, amma duk abinnan saida nayi sati daya kafin na dawk daidai,

Babana har yanzu bai dawo ba kuma bamuji labarinsa ba ko ta waya, kuma har yanzu ban yadda na sake fita ba koda zaure saboda zuwa wannan lokacin bana san ganin Dikko ko inuwarsa,

Gaba daya na jingine islamiya da wata bokon banza, daga tsakar gida sai daki, idan ina tsakar gida naji karar mota ma daki nake komawa,

Satinmu ukku a gidan abokin Babanmu Baba baizo ba, kuma baiyo aike ba, shima kuma wannan gida da muke ciki Dikko ya siyeshi, ba'a gidan kadai ya tsaya ba duk gidan da yasan na hayane a anguwar saida Dikko ya sayeshi duk sun zama mallakinsa, tashin hankali da damuwa kowa ya shiga,

Saida abokin Baba yazo yake fada mana cewa an kama Babanmu yana can an kulleshi saboda ya ranci miliyan biyar din wani abokinsu bai bashi kudin ba, shine ya kaishi wurin hukuma suka tsareshi,

Kowa ya jinjina miliyan biyar saboda babu wanda yasan abinda Baba yayi da kudin nan, shiba gida ba, ba mota ba ba fili ba, haka kawai ya saka kanshi rikicin duniya.

Inna na kalla data zabga tagumi tana d'igar da hawaye, cikin yanayin tausayi nace Inna wai da zaki auri Babana bakuyi binciken halinsa ba kafin auren ku? Banza Inna tayi dani bata bani amsa ba, tsoki nayi tare daci gaba da cewa muma mata muna da matsala yayin da muka hangi tilin dukiya da babbar mota hankalinmu, ganinmu da kuma tunanin mu sukan b'ace , idan aka samu kwadayayyar zuciya sai kuma takai mutum ta baroshi, kamar dai ku duk zuciyoyi ne da kwadayin duniya suka kawo ku nan suka barku, kiyi ta addu'a kema Allah sa ya sakeki ki huta. Kunga mutum da arziki bakusan taya yai ya samu abinsa ba,

Inna dai bata tankamin ba, muka fito domin "yan gidanmu sunce muzo mu tafi wata primary school dake bayan gidanmu mu kwana tunda dare yayi kafin mu samu gidan zama, duk muna tsaye a tsakar gida dan Dikko yace wallahi idan muka kara cikakkun mintina biyar saiya kunna mana wuta,

Cikin kyarmar jiki nacewa Maman Fa'iza "yan uwan Babanmu basu da kirki kowa ya zura masa ido dashi da iyalanshi sai wuta mukesha babu mai roka mana sassabci a rayuwarmu, ansa daya ta bani itace, ai babu ubanda yasa shi aure auren kuma basune suka sa duk yayi cikunnan ku aka haifo ku duniyar ba.

Haka tayi ta surutai marasa dadi na bad'ala da rashin kamun kai har muka fita gidan muka tafi makarantar, koda muka fito motoci sunkai biyar masu zafi tsadaddu masu burgewa da daukar hankali, an haska fitilinsu duka, amma yau babu Dikko dan naji suna magana cewa mai gidansu yayi tafiya baya k'asa amma ya umurcesu da su tabbatar bamu kwana gidan nan ba, idan mun fita mun huta idan bamu fita ba a kunnawa gidan wuta, wannan shine sakon da Dikko ya aiko dashi,

A makarantar mukaci gaba da zama cikin azuzuwa, { Classes } idan dalibai sunzo zamu fita waje idan sun gama suka tafi zamu koma mu zauna, ni na gaji na fadawa matan Babana waisu basu da gidan iyayensu ne ? Wannan wulakanci ai ya isa haka, kowa ta tafi gidan ubanta ta huta mana, ai fa yak'ai yak'ai kamar zamu cinyeni d'anyata saboda tsabar masifa, dole naja d'an bawan Allahna nayi shiru.

Satinmu daya kullum sai an koremu kamar karnuka kuma kullum bama tafiya sai mun dawo, da safe kuma su tura yaransu su shiga bara cikin gari, rayuwa dai wulakantattar rayuwa mafi muni da k'ask'anci, Babana baya da adalci kuma baya da imani hakika zai tadda Allah, domin wannan zalincin yayi yawa.

Ranar da muka cika kwana takwas aka koremu da karfin bala'e mukabar makarantar malaman suka kara da cewa gwamnati bamu ta ginawa makarantar nan ba muje can musan inda zamu zauna amma ba makaranta ba, suka kara jaddada mana idan suka sake ganin wata wallahi sai sun kaita an kulleta wurin "yan sanda,

Nanfa Allah ya bamu sa'a cikin malaman wani ya ji kanmu ya bamu kyautar fili dan mun fada musu matsalar mu, shi kuma ya tausaya mana, saifa suka fara yahani akan fili yayin da kowa ke cewa saidai a siyar da filin a raba kudin aba kowa,

Yayin da wasu ke cewa ayi hakuri a zauna, masu cewa ayi hakuri a zauna sun rinjayi wanda keso asiyar, dan haka dole suka hakura, muka dinguma zuwa fili, bayan munje akayi tamalmala ta malmala aka siyo buhunna dasu aka zagaye gidan ,

Wannan fili dai bazai ansu a wurin Dikko ba, nima ganin mun samu mazauni hankalina ya komawa tunanin Babana,

{{{}}} {{{}}}

Bayan wasu kwanaki,
Rayuwata nakeyi cikin jin dadi, nidai Allah ya taimakeni bana bara saboda kanin inna yana kawo mana dauki da abinci, kunsan idan mace ta koshi tou fa lallai bata da aiki sai iskanci da rashin kunya, toni dana koshi nawa iskancin Dikko kadai yake nema ido rufe, kullum ina bisa hanyar zuwa tsohuwar anguwar mu, haka zan hau napep kamar duka kenan saina tabbatar mun kusa zuwa sai in dire abuna, wasu basajin fita ta wasu kuma suna gani idan suka bini basu kamoni ba saidai suyi min Allah ya isa, nima na fara dauko kadan daga cikin dabi'un Babana.

Yauma direwa nayi, da gudu nasha lungu na shige wani gida, zaure na tsaya saida na huta sannan na tattaro natsuwa na shiga ciki da sallama,

Cikin sakin fuska matar ta ansa min, wuri na samu kasa na zauna ina gaisheta, ta ansa lafiya lau, shiru nayi zuwa wani lokaci nace mata hajiya dan Allah kin iya rubutun wasika ? Murmushi tayi sannan tace niko na iya rubutun wasika, nace tou don Allah kitaima min mijin Yayata ne suka rabu shine yayi mata shegen duka ya raba mata kai da tab'arya tana can asibiti rai hannun Allah, kuma sai rubutun zagi yakeyi yana aikowa gidanmu, shine aka rubutomin ansa na maida mishi kuma takardar ta fadi, ni kuma idan na rubuta sabuwa zai gane rubutu na ne , amma ki taimakamin don Allah, ni na karanta wasikar kuma zan iya fada miki yanda take kiyimin rubutun nakai mishi don Allah........!

Ba tare da tunanin komai ba tace tou, daki ta shiga ta dauko jakar makaranta, da gani ta yara ce , a ciki ta dauko biro da paper tace min bismillah, duk ba tare da tayi wani dogon binkice ba ko yin nazarin yin hakan me zai haifar daga baya.

Ni ko dadi naji sosai a zuciyata , tunda ni bazan iya rubuta uwar komai ba, amma nayi farin ciki sosai domin dai yau zanci uwar Dikko kafin in fara kashe dawanki dan iska. Bayani na farayi ta fara rubutawa,

_Ka fita daga rayuwarmu yayin da ni kuma yanzun nakejin farin cikin shiga taka rayuwar, salon ka yana da matukar burgewa dan marasa tarbiyya, taya zaka fara rashin tarbiyya kuma ka gaji da sauri haka ? Ko kudin sayen gidajen ya kare ne ? To tunda kudin sayen gidaje ya kare nasan zakayi kokari ka samo kudin sayen dokuna, ina mai farin cikin sanar dakai daga yanzu d'innan har zuwa ranar da zaka bar zaman anguwar nan farin ciki zai bar zuciyarka, kuma zaman anguwar nan zai haramta a gareka kamar yanda ka haramta mana zama a cikinta, zanyi ta kashe dokunan ka harsai ciwon zuciya ya kama ka idan ka fasa kai ba d'an Babanka bane............_

_Sultana ce, Allah ya bawa mai rabo sa'a, idan kaje Islamiya kace amin......_

Mikomin tayi bayan ta kammala rubutawa, godiya nayi mata sannan na fita, nayi tafiya mai dan nisa ina kokarin bi hanyar da zata sadani da tsohuwar anguwarmu na hango Dikko ya sauko daga saman doki......,

Jar riga ce a jikinshi amma ba irin ja d'innan ba ja mai kyan kallo, sai jar hula akanshi irin wacce matasa ke gayu da ita, fesin cap, bakin wando ya saka wanda suke kira 3quater da rufaffin takalmi, sai bulalar da ake dukan doki a hannunshi, daga gani dai daga kilisa suka dawo,

A fili nace shege mai kama da mata, cin cigom kamar tsohuwar karuwa, duk'awa yayi k'asa ya d'auki wani abu wanda ban iya ganewa ba, bayan ya d'auka ya koma saman dokin yayi mishi diddige tare da tsuke bakinshi irin yanda ake kora doki yayi gaba,

Da gudu ya wuce ya wani d'an jirge saman dokin yayi kyau sosai bazan mishi haddasa ba gaskiya, ci gaba nayi da tafiya, kafin in ida isa wurin kuma naga ya wuce da gudu cikin mota kura tabi bayan motar sosai kamar guguwa ta taso.

Hamdala nayi domin na samu damar farko da zan kashe doki d'aya daga cikin dawakan Dikko, saboda nasan wata mugunta d'aya da ake ma doki, ba'a ba doki ruwa idan aka dawo dashi daga yawo, idan aka bashi ruwa a wannan lokacin tou cikinshi k'ullewa yakeyi ya mutu.

Nikaf ina na ciro na saka tare da gyara tafiyata na tun kari
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

6 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment