Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muke dashi, yayin da wasu suke ganin rainin hankali ne......

Ko a aji naso na bawa Amisty labari amma na manta sunan wanda zan fada mata, Amisty itace kadai abokiyata duk a ajinmu, abinda kuwa yasa na zabeta tana da kokari sosai kuma idan ana jarabawa tana bani satar amsa,

Amisty irin yaran nan ne da idonsu ya waye tun suna cikin zanin jarintaka, bata da labari sai labarin maza, bata da aiki sai kallon B F, duk hotunan da zaka gani a cikin wayar Amisty hotunan tsiraici ne, walau nata walau na wasu, babu mai tarayya da ita saini kadai domin an dade da canfata cewar tana lesbian, nikam babu abinda ya dameni idan dai zata bani shayi nasha a tashi jarabawa ta bani satar amsa idan anyi rubutu nima tayimin a littafina shikenan banda wata damuwa.

Lokacin dana shiga aji har malami ya shiga ya fita, ga rubutu nan a saman allo, bana gane sunan subject haka nan kawai na kalli allon nadan basar tare da cewa ashe malam harya fita.

Da Eh kusan rabin ajin suka amsamin dan ina da masoya sosai, wasu saboda kyauna suke sona yayin da wasu kuma gashin kaina yake daukar musu hankali, okey shine abinda na fada kamar wata shegiyar baturiya dan itama okey din na dade ina koyonta a bakin Amisty dakel dai na samu ta zauna ram a cikin kaina, idan na fadi okey zakayi tunanin nasha turanci na koshi, amma babu abinda nake ganewa duk duniya sai sallolina biyar da Allah yasa na iyasu saboda nacin zuwa islamiya.

Ina zuwa mazauni Amisty tace yau ina kika baro mana Baban namu ? Wata irin faduwar gaba naji dan nasan Babana shima ba karamin tantirin dan iska bane, kodai itama Amisty Baba ya zagaya ne ?

Kinyi shiru, Amisty ta katsemin tunani na, maganata daukewa takeyi duk lokacin da ake tambayata abu, ina da nawar magana akan magana karama sai inja lokaci sosai, inayin in ina kadan wannan dalilin yasa ban cika yawan magana ba.

Dan gajeren murmushi tayi tare da matsawa, zauna tacemin tare da maida hankalinta akan allo taci gaba da kwafar note. Zama nayi tare da cewa wane malami ne ya shigo ?

Malama dai , wace malama ce ? Malamar English ! Me take koyawa na tambayi Amisty, turanci ta fadamin a takaice, murmushi nayi tare da cewa yarinya ai na gane dama dan inji idan zakiyi min karya.

Kedai kika sani, ni ciro littafinki na rubuta miki idan kin gama rainin hankalin naki, Amisty ta fada........ Bude jakata nayi sawon wani lokaci na kasa gano littafin da Amisty tacemin, tun ina dubawa a cikin jaka har na fito da duka littafan banga littafin turanci ba, dan gajeran tsoki nayi tare da cewa Amisty inajin nabar littafin a gida gaskiya.

Daukar littafin tayi domin shine a sama, ajiyar zuciya nayi dan nima ta gane wata jar wuya ce , nace da yake jiya nayi karatu na dauka na barshi a gida ne, tou kawai tacemin bata sake magana ba,

Haka malamai mata da maza sukaci gaba da shigowa har aka tashi daga makaranta, a bakin get din makaranta na tsaya ina jiran isowar Babana , tabbas nasan zaizo duk inda yake naji yana kusa dani yana zuwa bada jimawa ba.

Banfi minti 2 ba Babana ya iso cikin wata irin kafirar mota yanzu ma yasha wanka ya murza wata irin dakekiyar shadda, sai kasaita yakeyi, murmushin jin dadi nayi domin dai Babana ya kankaro min mutunci na idan yayo wanka saboda dan gayu ne na koyi a idon duniya.....

Cikin farin ciki na isa jikin motar na bude gidan gaba na wani kame abuna, zugar kawayena ne sukayo kanshi suna gaishe shi kamar yanda suka saba idan yazo daukata,

Dan murmusawa kawai yakeyi tare da karkacewa cikin izza ya jawo wasu irin "yan dubu dubu wanda shi kanshi baisan ko nawa bane , Amisty ya mikamawa tare da cewa ku saka kati.

Yana basu bai jira godiyar da suke mishi ba yaja mota muka tafi......, ba'a hana alkairi amma inajin bakin cikin abinda yakeyi, yabar gida da yunwa yazo waje yana alkairi, gida bai koshi ba yakai ma na waje banda gori da zagin iyayenmu babu abinda akeyi a cikin anguwa cewa Babanmu yana tsaye akanmu amma duk mu tsinannin Allah ne mu , haka zaisa ayi ta shiga da buhun na, na shinkafa gero masara katin katin na madara sugar da komai na sarrafawa idon duniya sun gani haka zai biyo dare ya kwashe abinshi yaje ya siyar wannan rayuwar zalinci ce, kuma bai sani ba kanshi kawai yake yaudara,

Kasa hakuri nayi nace gaskiya Baba ni kadaina zuwa daukoni makaranta daga yau, ba tare daya kalli inda nake ba yace miyasa Mamana ? Kawai banajin dadin abinda kake ne , me nakeyi wanda bai miki dadi ba ? Wannan kudin da kake bayarwa dama gida kabawa su Inna sukaci abinci gidan kowa yunwa ta kamashi babu mai wani sahihin abinda zaici maganar daya ce kullum daga gari sai kanzo.

Dariya yayi sosai tare da cewa Mamana kenan, aisu wannan mutane basa godiyar Allah, kima daina biye musu dan kona basu kudin cefane makalewa sukeyi, duk wanda kika gani a cikinsu daga mai tumaki goma sai mai shanaye babu adadi, idan na basu kudi boyewa sukeyi su hana ku abinci, suna can sun sayi dabbobi sunkai kauyika an boye musu, idan kuma kina magana akan abinda akayi ma wani kuma wannan halin shi ake kiran da hassada idan kikaga anyi ma mutum alkairi koya samu wani abu kikaji bakin ciki a zuciyarki shima hassada ne, kuma ita hassada tana cinye kyawawan ayyuka ne kamar yanda wuta takecin karmami, kuma yawan surutu yana sa mutum ya zama sakarai , ki daina hassada kuma bakinki shiru akan fadar wasu maganganu akaina idan kinki ji kuwa jahannama tsaye ko kina san ki shiga wuta ne uwar masu gida ?

A , a Babana, amma zan fadawa su Inna gaskiya su daina irin abinda sukeyi zalinci ne, abun tausayi Baba kaji yaran nan suyi ta kukan yunwa wallahi ni har tausayinsu nakeji, kyalesu Mamana kina iya fada musu gaskiya suji haushinki barsu da halinsu................Maganarsa ta kare ne a daidai lokacin da muka tsaya wata majalissa.

Fita muje, fitowa mukayi daga cikin motar muka tunkari taron dandazon mazan, kallo daya zakayi musu kasan cikakkin "yan tasha ne ko wannensu ya koshi da iskanci,

Gaishe su nayi tare da matsawa daga gefe na zauna, kai bata abincin nan taci mu wuce, Babana yayi maganar a daidai lokacin da yake zama,

Mikomin abinci akayi a cikin ci ka yada, { take away } gyara zamana nayi tare da juyawa inda babu mutane naci gaba da aiki, daga nan bansan abinda yaci gaba da faruwa ba, saidai naji hayani tayi yawa sosai anata bawa Babana hakuri ana rirrikeshi.

Cikin tsananin bacin rai yake cewa da Allah ku sakeni wallahi saina kwakwale mashi idanuwa tunda nayi rantsuwa saina makantashi duk cikar garin katsina babu wanda ya isa ya hanani aikata abinda nayi niyya, da sauri na tashi nayi wurin Babana ina bashi hakuri,

Abokin fadan Babana yake cewa, yo kai "ya "yan wasu nawa ka batawa rayuwa, saini kawai dan na kalli diyarka nace babban lambu zaka nunamin rashin kunya, cewa nayi zan shiga ciki ? Yabawa fa kawai nayi.... Sai kawai hankali ya tashi ?

Sanin kanka ne duk kasuwar data burgeni saina ci ta hanyar shiga inyi siyayya a cikinta, duk gidan giyar daya burgeni idan na shiga saina sha kwalba biyar karanci kenan idan banda kudi, haka kuma idan naga gidan karuwai zan shiga ne inyi ta ciyayyar abinda ya sawwaka ba tare dana gajiya ba,

Ka sani nima nasan haka, tunda saina gama nake ma gwanjon mata, banyi maka shamaki da matana ba haka diyana, kenan yanzu idan nace ka bani aron Sultana mu bata dare haka zakazo bakin kofa kayi tamin babatu ?

Da sauri Babana ya rufe idanuwan shi tare da kauda kanshi gefe guda, tunda ni bansan abinda ya assasa fitinar ba, tou miye b'ata dare ? Kila shaye shayen su suke nufi,

Jinjina kai Babana yayi tare da cewa kaci sa'a Mamana tana kusa amma zan maida ita gida na dawo na nuna maka karyar barikanci, yana fadar haka yaja hannuna mukayi gaba, har muka iso gida baiyi min magana ba, saida ya tabbatar na shiga gida sannan ya koma,

Da sallama na daga buhun kofar gidanmu na shiga, gaba daya gidan suna tsakar gida uwaye da yara, yaran mazansu da matansu sun gurfana gaban wani dakekin mutum bakikkirin da cikinshi kamar ace Allah saukeshi lafiya, ni a tunani na assembly ake musu saida naga Inna na tuna ba makaranta bace.

Saida nazo daidai inda suke nayi musu sallama kamar yanda na saba, ina kokarin wuce yace ke zonan, ban kalleshi ba kuma banzo ba haka kuma ban tsaya ba naci gaba da tafiyata na kusa shiga dakinmu naji yace waccan yarinyar ta raina mutane wallahi da nayi niyar yin hakuri amma na fasa sai kun tashi kunbarmin gidana.

Hayani ta kwace bakajin maganar wani duk maganar ta koma iri daya yi hakuri , Allah ya taimake ka Allah ya kara arziki ka taimaka dan Allah karka tashemu, kaji hauka akan wannan rubabben gidan suke wani hadashi da Allah yayi hakuri, Allah ma yasa ya tashemu nayi addu'a ta a bayyane,

Zainab ce ta tashi taje wurinshi tana wani irin karye karye, sai kace karyar gidan karuwa taga maza, magana tayi mishi babu wanda yaji abinda tace, saidai suka fita da mutumin, ganin tafiyarshi yasa kowa ya tashi yaci gaba da sabgar gabanshi,

Babana da Zainab bansan yanda suka kare da mutanen su ba, haka Dikko bansan inda yake ba, dan an dauki wani lokaci banji labarin yazo anguwanmu ba,

Kwanaki da dama sun shude, rayuwa tana tafiya babu abinda yayi gaba sai ci baya ake samu, amma ni na samu ci gaba na rayuwa domin dai Babana ya siyamin sabon machine kamar yanda yayi alkawari, a cikin matanshi kuwa maman fa'iza ta samu karuwa ta aihuwa, yanzu mun zama mu hamsin da takwas cas a gidanmu,

Zaune nake a kofar dakinmu ina yanke farce na, "yar kyakkyawar magena tana shan madara, Baba ne ya siyomin madarar da yawa nake bata danni yanzu na daina tausayin "yan gidanmu tunda na gane duk munafikai ne, Kuma Babana ina gani duk safiya yana basu kudi amma bansan ko nawa bane,

Kadangare ne ya fado daga saman bango fef, yana ganin mage ya ruga, ita kuma daina shan madarar tayi tabi kadangaren da gudu, nima binta nayi ina kiran "yar madara' dan bana so tana cin kwarika, kadangare ya rugawa mage, ni kuma nabi magen haka muka fita a guje mu dukanmu muna gudu a tsakar santa....

Shima a guje ya shigo kamar yanda ya saba, ganin yanda mutane ke rike yaransu, masu tumaki na kamawa hakan ya tabbatar min dashi dinne ya sake dawowa,

Nima kokarin kama "yar madara nakeyi, amma kafin in isa wurinta tuni dan iskan yabi ta kanta da mota ya wuce, jininta yayi tsartuwa a saman fuskata, yana wucewa na ruga na durkusa wurin magen, saida tayi miyau.......... Sannan ta daina motsi, wata irin ashariya na babba tare da kurma wani irin ihu dan naji bakin cikin takata da mota da akayi.

Cikin kuka na nufi inda yake, dama ina jiran zuwan shi saboda marin da Babana yayimin ta dalilinshi, shima din jirana yakeyi saboda zagin da nayi mashi waccan ranar, kowa yana jiran kowa,

Bayan yayi parking ya fito ya zauna saman bayan mota, yauma bulalace a hannunshi yana wasa da ita, sai wani cin cingom yake sai kace karuwa...

Abokan da yazo dasu waccan ranar yauma sune ya dawo dasu, mutum biyu tsaye a gefen damarshi biyu a haggunshi daya kuma tsaye ta gabanshi ya dade da bakin glashi,

Lafiyayen kato ne mai kirar "yan dambe, singileti ce a jikinshi sai wani maski maski yakeyi kamar anyi mishi wanka da mai, dan nesa dasu na tsaya tare da cewa a cikinku waye yake tuka motar nan ? Na nuna motar da hannuna,

Nine nan, mai kirar "yan dambe ya bani amsa, sannan yaci gaba da cewa ko wani abu ya faru ne ? Saida na kalleshi sama da kasa sannan nace da Allah mi yasa ka takamin mage ? Nayi maganar cikin sanyin murya, bashi ne ba nine na taka ta, kema idan kika tsaya a hanya gobe haka zanbi ta kanki in wuce kinji ko an mata, duk shi Dikko yayi maganar.

Mai kirar "yan dambe ya anshi maganar cewa, ubangida na yanajin dadi yayi da yaga yana wulakanta talaka irinki, yana farin ciki idan ya zauna daga nan muka fara watso kayanku daga cikin kangon can, da nayi niyar murde miki wuya ki mutu , mutuwa irin ta beraye a ranar da kika wa mai gida rashin kunya, abu daya yasa ban kasheki ba kasancewar ke ba kowa bace,

Murmushi yayi tare da cewa ta hanya mafi sauki za'ayi miki hukunci, juya kisha kallo, juyawa nayi a hankali dan inga abinda yake so na gani, babu gidanmu tuni wurin ya koma fili, lokacin da na juyo babu su Dikko babu alamarsu dan tuni sun jima da tafiya daga wurin.

Salati nayi tare da tunkarar inda "yan gidanmu suke tsaye cirko cirko domin babu abinda aka bari suka fitar dashi komai an danneshi cikin kasa, sai motaci dake ta kwashe kasar wurin,

Ina zuwa kusa da Inna da zumar tambayarta abinda ya faru ta rufeni da duka tare da cewa miya hadaki da Dikko kin dauko mana fitina kin jawo mana masifa Allah kadai yasan karshen wannan masifar.

Cacai cacai kowa hayani yakemin a saman kai babu damar a dakeni Babana yaba mace rasid'i, ke kuma diyar gida kimin magana kijawa uwarki masifa, dan haka abinda kawai suke cewa miya hadani da *DIKKO ?* ................







{{{}}} {{{}}} {{{}}}



31/07/2019



Kubi sannu ku kasance da wannan labari,


Taku a kullum Meelat Musa 🤙🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 3


Saida na gama kallesu daya bayan daya sannan nayi murmushin takaici da gefen bakina, kallon inda gawar "yar madara take na kalla wani makoko yazo ya tsamin a makoshi wanda ko yawun zan hadiye sai naji kamar lumfashi na zai dauke.

Dikko......................! Saida na jinjina sunan a zuciyata da kuma bakina, sannan na kalli dandazon taron ahalin gidanmu, nu na su nayi da dan yatsa manuni, sannan na dafa daidai kirjina da hannun haggu na , zanyi magana sai kuma maganar ta kasa fitowa dan bana iya magana a cikin yanayin bacin rai..

Wuri na samu na zauna ina ta sauke ajiyar zuciya, tsinuwa da zagi da Allah ya isa bansan iyakar adadin dozinan da suka saukemin ba, zagin ne dai kawai amma nasan bazan daku ba,

Har yanzu babu wanda nayi ma magana kuma babu wanda na sake kallo, zama nayi na sauke kaina kasa, yayin da wasu suka gaji da tsayuwa suka durkusa wasu kuma suka bazama neman gida, dan su zasu nemo shi dan ko sun tsaya jiran Baba ko yazo bazaiyi wani abu ba,

Bayan sun zauna ne sukaci gaba da tattauna maganar abinda Dikko yayi, ashe tun waccan ranar zagin da nayi masa ranar da zamu tafi makaranta tare da Babana bayan an bashi hakuri ashe baiyi hakuri ba.

Da zai jira har na dawo daga makaranta ya takeni da mota ya wuce abinshi, tou bayan ya fito daga gidan da yake kiwon dokuna yaga Babana ya fito daga gidanmu,

Shi Dikko mugune na gaskiya da gaskiya, duk duniya babu abinda ya raina yake kyankyami irin talaka, Dikko baya dariya haka kuma baya murmushi kullum fuskar nan tashi a hade take kamar hadarin tsakar dare,

Bakya ganin dariyar shi kwata kwata, idan kuwa har Dikko yayi murmushi tou tabbas yaga cuta, idan kuma yayi dariya tou tabbas ku idan kuka ga abun sai kunyi kuka saboda tsabar tausayi. Danshi sai yaga mugunta yake dariya.....

Bayan Babana ya wuce, Dikko ya kalli gidan ya sake masa kallo babu abinda baya gani na gidan daga nan waje inda yake tsaye,

Kallon rainin hankali yayi ma gidan tare da bata fuska ya juyar da kai ya kalli daya daga cikin wanda suka zo tare sannan ya kalli agogon hannushi yace waye shi.... Ya nuna Babana da gidanmu...

Bai tsaya yin magana ba ya bazama cikin anguwa, a cikin kankanin lokaci yaje ya samowa Dikko duk wasu bayanai daya kamata akanmu da rayuwarmu,

Jinjina kai Dikko yayi bayan yaji komai tare da cewa karta mutu, amma barsu na jikatasu zata gane Dikko ba sa'ar ubanta bane daga wannan rana tsoron Dikko zai shiga zuciyarta maza a nemo min mai gidan daya basu hayar gidan, dan gajeren tsoki yayi tare da cewa talaka banza a banza, za'a nuna mata su kudi jigo ne masu nuna ishashshen iko. Daga wannan rana zata gane mai kudi ba'ayi masa hawan kasa,

Cikin anguwa ya sake komawa dan binciken mai gidan da muke haya, aka fada musu anguwar da yake zama, da kuma wurin da yake zama dan kasuwancin shi,

Bayan sun gama daukar duk bayanin da suke bukata, sukayi tafiyarsu, ashe Dikko gidan da muke haya yaje ya siya, kuma mai gidan da muke haya yace wa Dikko Babana baya biyan kudin haya tuni yayi niyar tashinmu sai wata yayata take biyanshi kudin haya daga cikin kaddarar rayuwarta,

Tun wannan ranar Dikko ya biya kudin gidanmu, bayan ya biya tafiya ta kamashi, saida yayi wata biyu baya nan, shine fa yana dawowa babu notice kawai yasa aka rushe gidan......

Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama jin duk bayanan su, yanzu ita Zainab zuwa takeyi anayin iskanci da ita kenan ? Amma ta bata wayanta,

Yawwa an samo gida ku taso mu tafi, gaba daya sowar farin ciki suka dauka tare da mikewa suna cewa a ina gidan yake ? Gidan Alhaji Sabo ne yace mu zauna dan yaji abinda ya faru damu kuma ya tausaya mana sosai, amma duk watan duniya yace zamu rika biyan dubu goma,

Eh hakan yayi babu wani damuwa, ku tashi mu tafi, yeay yara da manya sukayi ta shewa muka tafi dukanmu yayin da wasu ke cewa dan uwar Dikko yazo ya anshi wannan idan ya isa.

Haka muka koma gidan Alhaji Sabo dake makotan gidanmu da Dikko ya siya, bamu da komai haka muka shiga gidan, kowa daga ita sai kayan jikinta,

Nidai har yanzu banyi magana ba, abun duniya duk ya dameni kuma babu wanda yabi ta kaina ko Inna bata sake shiga sabgata ba sunyi ayari wuri daya ana ta shawarar yanda za'ayi a samo kudin Alhaji a bashi dan ya basu daga yau zuwa jibi su kawo mishi kudin shi.

Har safiya basu samu mafita ba, haka kuma Babana bai kwana gida ba, bansan yanda akayi ba suka shiga suka fita suka bawa Alhaji kudin hayarshi ba,

Kwanan mu hudu a sabon gida Baba yazo gidan, bai tambayi yanda akayi muka dawo ba haka kuma baibi takan kowa ba zance ya akayi aka biya kudin haya ba, haka kuma baiyi ma kowa magana ba saini daya,

Uwar masu gida lafiyar ki qalau kuwa ? Lafiya qalau Baba na amsa masa, yace kwana biyu bakije makaranta ba har kawarki ta tambayeni ko lafiya ? Nace mata lafiya qalau gaskiya, kinsan nima bana nan naje Abuja,

Allah sarki na fada, tou miya hanaki zuwa makaranta ne ? Ya sake tambaya na, saida na tattara bakina sannan nace Baba ai an rusa gidan, komai namu kuma an tattarashi an kwashe anje an zubar, banda kayan makaranta da littafai,

Wayyo Allah Mamana, taso muje waje muyi magana, mikewa nayi nabi bayanshi, yana gaba ina binshi har muka fita kofar gida,

Wuri muka samu muka zauna, muna zama Babana yace in fada masa dame dame nake bukata ? Nace masa ko kayan sakawa dukanmu gidan bamu da, kowa kala daya yake dashi, amma makota sun dan tattara mana kaya, murmushi yayi tare da cewa wallahi Uwar masu gida bata saka kwancen kaya, na dawo garin nan jiya da kudi fiye da tunaninki Mamana,

Tunda naji abinda ya faru tsakanin shadda da yadi da boyal saida na siya kusan kala arba'in, takalmi da agoguna da hulana duk babu abinda ban siya ba, kayan suna can na kai dinki,

Tsare Babana nayi da ido, a zuciyata kuma ina ganin rashin adalci irin na Baba, amma Baba bakada imani iyalinka na nan suna

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment