Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dikko, har ya shiga motar yaja ya tafi cikin tuƙinshi na ganganci wanda baya kaucewa kuma baya ɗagawa kowa ƙafa idan ya tafi sai yakai inda zaije hankalinshi yake kwanciya, Allah ya tsare hanya Al ' Ameen ya faɗa tare da dawowa wurin gado na ya tsaya, su Hafsa da Saude da A ` i da Amisty sunyi jigum kowa yana jiran farfaɗowa ta yaji abinda ya haɗani da D --- K......

Dikko kuwa tuƙi yake amma yana tunanin maganar Alhaji ranka ya daɗe wato wallahi wata yarinya ce muka ɗan keɓe da ita , tou wallahi bansan yarinyar nan ta shirya sharri ba, ashe duk abinda mukayi ranka ya daɗe tana ɗauka cikin waya ban sani ba....

Dukan sitiyari Dikko yayi tare da cewa tabbas yacemin yarinyar nan shekarunta bazai wuce 16 zuwa 17 ba daidai saitin zuciyarshi ya daka tare da cewa kece .... ?

Akan titi duk ƙurewar wuri Dikko ya juya kan sitiyarin mota ya koma baya ba abinda ya dameshi da halin da wani zai shiga kanshi kawai yakeji amma baya sauraren talakawansu, da gudu ya ibi shararra ya komo asibiti, a lokacin su Al ' Ameen sun fito zasu tafi ganin Dikko ya dawo yasa Al ' Ameen ya dawo cikin ɗakin da gudu yasa aka ɓoyeni, danshi Alhaji tuni Allah ya anshi rayuwarshi har an tafi da gawarshi, duk zunubin da Alhaji ya cacumar ma kanshi an samu wani marar rabo a lahira ya dira gidanshi yayi mishi caccakar wulaƙanci aka kawoshi asibiti dan ceton rayuwarshi Allah yasa ikar ibar da yayo kenan, Allah ya jiƙanshi yasa mu cika da imani ubangiji ya kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo...

Ana ɓoyeni su Al ` Ameen suka fito, a waje suka haɗu da Dikko yana ƙoƙarin shiga suka faɗa mishi mutuwar Alhaji ni kuma an canja min asibiti, Allahu Akbar Dikko ya faɗa tare da cewa ubangiji ya ƙarɓi baƙuncinka Muntari Allah ya kyautata tamu bayan taku, da Amin kowa ya ansa sannan suka tafi a tattare baki ɗayansu...





25/08/2019


Taku a kullum

*MEELAT MUSA...*


⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 19



Har yanzu kalar idon Dikko bai koma fari ba, idon nan jajir kamar yaci bala'e, amma a hankali yake washewa zuwa kalarshi ta ainahi, fuskar nan a murtuke ya jingina bayan shi da kujerar mota kana kallonshi kasan yana tattare da tsantsar damuwa.

Ɗan gajeren tsoki yayi tare da gyara zamanshi, hannunshi yakai ya shafe gefen fuskar shi, tunanin safiyar haɗuwarshi da Sultana ya fara dawo mishi sabo fitikil kamar yanzu ne abun yake faruwa, da sauri ya rumtse idanuwan shi tare da haɗe leɓunan sa wuri ɗaya ya danne su da haƙoranshi ta ciki, buɗe ƙofafin hancin shi yayi saboda lumfashin da yake shaƙa yayi mishi kaɗan ya buɗe ƙoƙofin hancin ne dan iskan ya yalwace shi.

Har suka isa gidan rasuwa Dikko bai sake ma kowa magana ba, tunda dama shi ba ma'abokin surutu bane, mota nayi parking ya fita cikin damuwa danshi dama kullum haka yanayin shi yake , farin ciki da ɓakin ciki duk yanayin iri ɗaya ne a wurin shi, babu wanda ya isa yasan lokacin farin cikinshi kuma babu wanda ya isa yasan lokacin da yake damuwa.

Tunda ya fito aka fara gyara mishi wurin da zai zauna dan zamanin ga mutane basa abu domin Allah basa darata girma shekaru da mutumci amma suna ba naira matsayi na musamma, Dikko yana da rashin mutunci amma alherinshi yasa mutane basa ganin rashin mutuncin nashi dan Allah yayi masa kyauta idan dai kukayi ido ido dashi tou tabbas zai baki kuma baya da kwauro idan zai bayar mai yawa yake baka, tou kyautar itace ta danne rashin mutuncin shi ga idanuwan al'ummar gari...

Sabuwar tabarma aka amso daga cikin gidan aka shimfida mishi, takalman shi ya cire ya taka tabarmar da safa, saida ya zauna sannan kowa ya zauna kuɗi suka fara nuna ikonsu domin masu neman asan dasu sukayi ta zubewa suna bada gaisuwa, saida ya jinjina kai dan shi kaɗai yasan tsutsar baƙin cikin dake lasar masa zuciya...

Wanda suka bawa duniya gaba ne suka fara bawa Dikko labarin yadda abun ya faru amma a zahirance yana jinsu amma a baɗinance hankali shi yana wurin Sultana so yake kawai a dawo jana'iza yaje ya ganota wallahi sai ta faɗa mishi miye tsakaninta da Muntari, inma banda take daƙiƙiya dan ta tona mishi asiri shine zai haɗa kirji da ita taje ita kuma ta haɗa da yaronshi...

Wayarshi ya ciro yayi "yan rubuce rubuce bayan ya gama ya tura, wayar shi ya maida aljihun gaban riga a zuciyarshi kuwa yana tunani Sultana ta gama barbaɗashi a duniya kowa kallon ɗan iska yake mishi,

Mikewa tsaye sukayi gaba ɗaya dan an fito da mankara, sai yanzu wasu keyin alwalla shidai yana da ita takalmin shi ya saka suka fita sarari dan sallatar gawar Alhaji Muntari , Allahu Akbar ubangiji kayi mana kyakkyawan ƙarshe hanyar dai ɗaya ce duk wanda yazo sai ya koma Allah kasa mu cika da imani idan ajalinmu yazo ameen....

A asibiti kuwa ina kwance cikin tsaka mai wuya, ina tafiya ne tsakanin rayuwa da mutuwa, duk wanda ya ganni saiya tausayamin ga hannu na naɗe da bandej wanda na fasa shi a jikin gilashin motar Dikko, su A ` i kuwa suna bani kulawa ta musamman tare da tattalina kamar mun fita ciki ɗaya !

Tsaye suke zagaye jikin gado na hankalin kowa tashe, jami'an tsaro ne suka shigo gaba ɗaya suka fatattaki su A ` i , kujerar da ake tura marasa lafiya aka ɗauko aka ɗorani a samanta suka tun kari hanyar fita dani daga cikin ɗakin, wani irin ihu Saude tayi tare da cewa ina zakuje da ita ne ?

Basu saurari kowa ba suka fito dani, cikin mota aka sakani mazaunin baya sannan aka rataye ƙarin ruwan a jikin kujera yaci gaba da shiga cikin jikina,

A wurin suka bar kujerar duk suka shiga mota sukaja muka bar asibitin, kuka su Hafsa sukayi tayi tare da tambayar kansu wane irin laifi nayi wanda har hukuma bata ragamin ba ina kwance a gadon asibiti, sunsha kuka har sun godewa Allah daga ƙarshe suka haƙura suka tafi gida...

Daga maƙabarta Dikko basu dawo gidan rasuwa ba gida suka wuce kai tsaye, tun a get na biyu ya sauka tare da cewa zai shiga yayi bacci , Al ' Ameen yace ranka ya daɗe bara muje get in ƙarshe sannan mu sauke ka amma daga nan ai zakasha tafiya, ba tare daya kalli Al ' Ameen ba yace nan zan sauka ya ƙarasa maganar tare da kallon Al ' Ameen , tuba nake ranka ya daɗe Al ' Ameen ya faɗa tare da jan motar yayi gaba...

Saida ya daina hango ɓurɓushin motar sannan ya fiddo wayarshi yayi "yan lashe lashenshi sannan ya kara a kunnenshi , bayan wani lokaci yace kuna ina ne ? Magana na cikin wayar yayi sannan Dikko yace ku shigo ta get in baya, yana faɗin haka ya kashe wayarshi tare da kiran wata wayar kuma.

Ta baya ya dawo ya bi wata hanya daban , tafiya mai nisan gaske yayi wurin tsitt bakajin ƙarar komai sai motsin tafiyarshi tunda tsakuwowi ne baje a wurin irin wannan fararen wanda idan ana rana har kashe ido suke, idan ya taka sai kaji tsus tsuss ƙarar tafiyar shi ,

Wata hanya ya bullo sai gashi jikin wani makeken get, masu gadi yayi ma magana suka buɗe motarmu ta shigo cikin gidan, gaba yayi motarmu tanabin bayanshi saida mukayo nisa da get in sannan ya tsaya, shima matuƙin motar tsayawa yayi tare da fitowa Dikko bai mishi magana ba ya shiga mazaunin dirver yaja motar yayi gaba.

A bakin ƙofar falonshi yayi parking sannan ya fito yaje ya buɗe ɗakin, dawowa yayi ya buɗe baya inda nake kwance rai hannun Allah, ciro robor ƙarin ruwan yayi ya fara riƙewa sannan ya ɗaukeni ya shiga ciki, a falo ya kwantar dani saman kujera 3sieter saida ya gyara ruwan suka ci gaba da shiga sannan ya fita tare da rufe ɗakin ta waje...

Motar ya ɗauke daga bakin ƙofar falon sannan ya ajiyeta a inda suke ajiye motoci, motar ta gidansu ce kuma jami'an suma na gidansu ne yayi amfani dasu...

Dawowa yayi tare da rufe ɗakin sannan ya wuce ciki, wanka yayi ya cire manyan kaya zuwa ƙanana, falo ya dawo ya zauna yana jiran lokacin da zan buɗe idona ya haɗa partyn shagalin wulaƙantani,

Zama yayi saman kujera wacce take kallona, ba abinda yake tashin shi a wurin saidai yaje yayi sallah ya dawo, idan yazo ya zauna kuwa lokaci zuwa lokaci yakan kalli agogon hannushi sannan ya kalli inda nake kwance, waya kuwa idan an kishi saida ya duba kawai ya latse,

Ruwa ma daya ƙare shine ya cire min, bai daɗe da zama ba aka fara dukan ƙofar ɗakin, ɗan latse baki yayi tare da cewa waye ? Dikko buɗe nice, muryar yayarshi yaji miƙewa yayi yaje ya buɗe ƙofar suka shigo cikin falon tare,

Salati nayi a daidai wannan lokacin jin muryar Dikko da sunanshi da aka kira, wani irin abu naji ya daki zuciyata, na ƙara lafewa bamma yi gigin tashi ba haka kuma ban kuskura na buɗe idona ba, amma jikina ya mutu murus , zama yayi a saman kujerar da yake itama kusa dashi ta zauna saman hannun kujera sannan tace ina ka samo larabawan daji ? Ta faɗi maganar tare dayin dariya...

Banza yayi baice mata komai ba, dariya ta sakeyi tare da jan gemunshi sannan tace dan ubanka bakaji ina maka magana, tayi maganar cikin sigar zaulaya, tsoki yayi tare da cewa ni bana san irin abinda kikemin yayi maganar cikin haɗe rai kamar dai yanda ya saba, kaiji ɗan iska ni zaka ɗaure ma fuska ko mutuwa zakayi na faɗa maka bazan daina janka ba, duk wannan haɗe haɗen fuskar gabana aka haife saida ma nayi aure dan ubanka kazo duniya wane girma zakayi gabana, ko inda take bai kalla ba, kuma baiyi murmushi ba bare tasa ran zaiyi dariya, sansar wauta dai tayi ta nunawa da sakarci amma Dikko tunda yace mata baya san abinda take mishi bai sake magana ba saida ta ƙari rashin wayanta sannan ta taho inda nake kwance...

Ko kallonta baiyi ba dan hankalinshi ma yana kan wayarshi amma yana kallonmu da zuciyarshi, tsaye tayi gabana idona da jikina suka ɗauki kyarma da sauri na buɗe ido na kalleta a tsorace sai kuma na kallo inda Dikko yake zaune amma yanzu bayacim cingom maido kallona nayi wurinta kawai sai na fashe da kuka....

Sai yanzu ya ɗago kanshi cikin tsawa yace ki rufemin baki, da sauri na haɗe kukan tare da rufe idona dan wallahi a halin yanzu tsoron Dikko nakeji dan na fara tunanin kila mahaukaci ne amma har yanzu jikina bai daina kyarma ba.

Juyawa yayar tashi tayi tai mishi magana da yaren arna { turanci } bansan abinda sukace ba, ɗan ɓata fuska yayi sannan ya ajiye wayarshi shima yayi mata magana cikin irin harshen da tayi masa, Allah ya bata lafiya ta faɗa tare da cewa zan koma wurin momy da Allah kayi ƙoƙari ka shigo, da kanshi ya amsa mata, saida ta ƙara kallona sannan ta kalli Dikko ta sakeyin magana da yaren ɗazu, kyakkyawan murmushi yayi sannan yace ngode ya faɗi maganar tare da ɗauko cingom ya fara ci, abinda na fahimta cin cingom in kila yana da ƙa'ida domin yafi amfani dashi a wasu lokutta wanda shi kaɗai yasan su...

Fita tayi daga ɗakin tare dajan ƙofar garam, har yanzu idanuwa na a rufe suke jikina kuma bai daina kyarma ba, tashi yayi yaje ya kulle ɗakin sannan ya dawo ya zauna, cikin kujera ya tura hannunshi ya zauro wata irin zureriyar wuƙa sai kyalli takeyi saboda sabinta,

Ke zo nan , kamar ina jira na tashi dan nasan babu wata ke a ɗakin sai ni, da sauri na isa gabanshi na durƙusa cikin tsoro na sauke kaina ƙasa, cikin natsatstsiyar murya yace kalli , ɗago kaina nayi na kalleshi amma ba ido cikin ido ba, cikin murya maisa natsuwa yace mi yasa bakijin magana ? Shiru nayi naci gaba da lissafin "yan yatsu na, bana san ina magana ina maimaitawa, raina yana sauri ɓacin ne , banda haƙuri zuciyata a kusa take ina tambayarki kawai ki bani amsa...

Mi ya haɗaki da Muntari kikayi mishi vidio ? Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji kardai Alhaji ya nunawa Dikko vidion nan, Dikko kuwa ɗoro tsinin wuƙarshi yayi daidai saitin maƙoshina, wanda ya shaƙeni a gaban mutane lallai zai iya kasheni tunda babu mai ganinmu sai Allah, ina san ganin idonshi domin ta nan ne kaɗai zan iya gano idan Alhaji ya bashi labarin vidio,

Ɗan kartar min wuya yayi da wuƙar tare da cewa ke nake sauraro, cak na ɗauke numfashina tare da kallon kwayar idonshi sannan nace waye Muntari ? Na tambayeshi ne dan san gano ko gaskiya ne ? Da ƙafarshi ya takamin baki sannan ya halbi daidai saitin hancina har saida jini ya fita.

Ƙasa ƙasa yayo da wuƙar daidai saitin ƙirjina inda daya burma min ita tawa ta ƙare, cikin kuka na riƙe wuƙar tare da cewa to yanzu kuma laifin me nayi maka ? Na ƙarasa maganar hawaye na kwarara daga cikin idona, shima hawaye ne kwance a cikin kwayar idonshi cikin damuwa yace saki wuƙar kinji, sakin wuƙar nayi sannan yace zaki iya kasheni ? Cikin rashin fahimta nace kamar ya zan iya kisa bayan nasan ba abune mai kyau ba ?

Dikko yace tou mi yasa kika zaɓi zunubi mafi muni a rayuwarki ? Kin kuwa san illolin dake tattare da zina ? Kinsan bala'en ta kinsan matsalolin da take haifarwa ? Kina ƙaramar yarinyarki ki tunkari mazan bariki, kinsan bala'e kuwa irin na mazan bariki ? Kinsan haɗarinsu ? Mazan bariki basa taɓa jin tausayin macen bariki kuma basa tattalata basu san darajarta ba haka kuma bazasu taɓa raga mata daidai da ɗigon kwayar zarraba bariki ta fito kuma shi za'ayi da ita tunda sunsan idan sun lalataki gobe ma wata zasu nema, kinga kuwa da wannan bala'e da kika bashi gaba kawai gara ki sokawa Dikko wuƙa ki huta ya ƙarasa maganar tare da miƙomin wuƙar....

Kallonshi nayi amma banyi magana ba, murmushi yayi tare da ciro cingom in bakin shi yace na ƙoshi ko zaki ci ne ? Banza nayi kamar banji ba , ɗaga kafaɗun shi yayi tare da cewa kin huta 🤷🏻‍♂, ya faɗi maganar tare da maida cingom inshi cikin bakinshi yabi ni da kallon rainin hankali,

Shiru na wasu mintoci sannan yace kinsan abinda yasa nazo dake gidan nan ? Keda ke gidanki idan kinyi magana tou na tankawa Dikko, ci gaba yayi da cewa anan kaɗai zanyi magana dake cikin natsuwa, ki daina hayemin kuma ki rage rashin kunya sannan ki taka a hankali duniya taƙaitacciya ce ga kowa amma babu kamar mace,

Ki taka sannu An mata ki faɗamin duk abinda kike so a duniyar nan ko miye zan miki kuma zan baki idan dai zaisa ki kwantar da hankali ki natsu, kuma ba yau kaɗai ba zan ci gaba da kyautata miki daga nan har ranar da numfashina zai bar gangar jikina zanci gaba da kyautata miki dan kiyi farin ciki , ke yarinya ce baki san komai na rayuwa ba, amma zan sake faɗa Allah ya baki sa'ar rayuwa da har kika shigo rayuwata sheɗan kuma ya samu galaba a kaina, tunda ni zina ba aikina bane ban taɓa ba tunda nake wallahi sai a kanki.

Kinsha dani kuma kin gama dani har badan duniya, kina da matsayi na musamman da bazai taɓa goguwa a zuciyata ba kuma kin shiga cikin babban tarihin da bazai taɓa gogewa ba a rayuwata har abadan duniya , duk wacce ta shigo kece farko, ni haɗuwata dake na barshi matsayin ƙaddara kuma bansan abinda ubangiji yake nufi da ita ba.

Daga ni harke babu wanda yasan abinda anjima zatayi bare gobe, amma ina riƙonki da Allah kiyi haƙuri kuma ki yafemin akan duk wani abu daya faru tsakanina dake, taɓe bakina nayi tare dayi magana ƙasa ƙasa amma baiji abinda nace ba, Eye ? Ya tambayani tare da yatsina fuska yace banji me kike faɗa ba ,

Kai tsaye na kalleshi tare da cewa bazan yafe maka ba har abadan duniya, jinjina kai yayi tare da cewa to ba komai Allah yasa rashin yafiyar shine alkairi a rayuwata, kina buƙatar wani abu ne daga gareni ? Ni bana san komai saboda baka da abinda zaka bani ni bakayi kuɗin da zaka taimakeni dashi ba har yanzu, bai sake magana ba, ya ɗauki wayarshi ya kira mutumin daya kawoni yace yazo ya mai dani gida...

Ci gaba nayi da zage zagena ƙasa ƙasa yanda bazai iya juyoni ba, anan nayi ganganci ɗaya kunsan masu iya magana sunce idan mutum matsiyaci ne ko an sakashi a tandun man shanu aka tsamo shi haka nan zai fito jikinshi ƙamas.

Babu wani ɓata lokaci mutumin ya iso, Dikko yana jin tsayuwar mota yaje ya buɗe ɗakin ki ya dawo ya zauna, da sallama mutumin ya shigo tare da kallona yace muje, tashi nayi tare da ƙara kallon Dikko har yanzu bakinshi yana motsawa cikin salo mai burgewa da ɗaukar hankali yana cin cingom inshi cikin kwanciyar hankali , gaskiya nidai yanamin kyau idan yana cin cingom, amma fa bana ƙaunarshi, bai kallemu ba kuma baiyi mana magana ba hankalin shi yana saman wayarshi,

Nayi tunanin DK zaiyi ta haɗani da Allah ko kuma idan yaga zan tafi zai kirani amma ko ɗaya ba abinda ya faru, haka nan naji babu daɗi haƙura kawai nayi na shiga mota muka tafi, 11:30pm a cikin ɗakina tayi min, daga Nana sai Karima kawai a gidan sunata jajantamin.

Kuma sune suka faɗamin mutuwar Alhaji, nayi kuka sosai musamman ma a lokacin dana ga vidion dana ɗauka muna ai kata saɓon Allah wani irin imani da tsoron Allah ya tsargamin zuciya tare da ganin kamar mutuwa zanyi yanzu yanzu,

Na daɗe ina kukan mutuwar Alhaji a cikin kwanaki ukku daga nan kuma na ɓarar da lamarin zance mutuwarshi muka fuskanci rayuwar bariki.....


Bani canzawa, kuma yanzu aka fara....


Muje zuwa....



26/08/2019


*JAMILA MUSA...* 🤙🏻


⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 20


*_Shafin ga gaba ɗayanshi kyauta ne ga group mai albarka da mutanen cikinshi masu mutunci MEELAT MUSA FANS kuna fa sakani nishaɗi idan kuna sharfi nakanyi dariya sosai domin kuma ilimi ne na musamma ngode sosai Allah ya ƙara haƙuri da juriya, wata ma dai wai cewa tayi Oga Dikko ! Star Dikko ubangidan KWARATA , nafa gode Allah ya baku wayoyi masu riƙon caji da caja mai saurin cika hand set amin... Ni Meelat ko ince JAMILA MUSA nake cewa asha karatu lafiya...._*

*_Ina miƙa saƙon ta'aziyya ga "yar uwa kuma abokiyar aiki haziƙar marubuciya Fadeela Lamiɗo ina tayaki jimamin rashin ɗan uwanki Allah ya jiƙanshi ubangiji ya amfani zuri'ar daya bari , Allah ya baku haƙurin rashin sa annabi yasan da zuwanshi, mu kuma Allah ya kyautata namu zuwan bayan nasu ubangiji yasa mu cika da imani idan ajalinmu yazo..... Am3n ya Allah..._*



Duniya sabuwa inji masu iya magana yayin da wani yake kuka a lokacin wani yake farin ciki, kukan mutuwa da jimimmamin rayuwa yana gidan Alhaji Muntari yayin da a gidan da muke haya yau muke shagalewa muna raƙashewa muna cin duniyar mu da tsinke...

Zaune muke a saman tabarma yayin da ni nasha riga da zani na atamfa nayi ɗaurin ɗan kwali na irin na sabbin karuwai, na nemi bakin kwalli na daddaɓawa bakina, ga kitso na matan bariki da aka yanyaramin ɗinki rigata ya kameni sosai duk rabin halittun jikina sunyo waje, kallo ɗaya zakamin kasan ni tantiriyar karuwa ce wacce ta anshi lasisin iskanci bada jimawa ba, yanayi na ya fita a cikinsu kana gani na zaka gane nice uwar gidan *kwarata...*

Miƙe ƙafafuwa na nayi a saman tabarma nayi zama irin na matan da basu da kamun kai, a gefen damata Amisty ce zaune da jaddawalin sabuwar bariki mai fara aiki a cikin satin nan..

Nana , Karima , Hafsa , Amisty , A ` i da Saude duk suna wurin daga gabana suna ta bani wani irin matsayi na musamman sai kace nayi musu asiri zakayi mamakin yanda suke darajani, yaran nawa dai su shidda ne duk dani mun zama bakwai mune sabbin *kwarata* a cikin wannan zamani kuma nice shugaba kuma zanzo da salon da tarihina bazai gogu ba a cikin tarihin birnin garin katsina...

Juyawa nayi gefen hagguna zuga ce ta "yan daba dana ɗauko su haya zan riƙa basu

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment