Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

? Ta tambaya , aka ce mata Sultana , tace nan ne mazaunin mu , juyawa nayi da niyar feƙe mata uwa saidai banda isashshen lokaci dan ina so nayiwa mijin Mamy ta'aziyya , ina ƙoƙarin fita matar ta biyoni ta cakumoni ta baya tana cewa akace ina zakije ? Baki ga inda karuwai suke zaman gaisuwar su ba ? Ban mata magana ba na fiddo wayata daga cikin jakata nace ki duba zaki ga an rubuta Sultana itace lambar wayata ,

Kallona tayi sosai kuma kome tayi tunani Oho sai ta sakarmin hijabi ba tare data anshi wayar ba , ɗan gajeren murmushi nayi da gefen bakina na juya na fito ba tare dana sake mata magana ba , a ƙofar gida nayi ma mijin Mamy ta'aziyya da "ya "yanta maza Bello kuma sai kallona yake , murmushi nayi mishi na miƙe shima ban mishi magana ba ,

Tunda na fito daga barandar ƙofar gidan Mamy ake nunani nice nazo a motar Dikko , wasu kuma na cewa ni karuwa ce amma meya haɗashi dani bayan baya harkar mata , wasu kuma na cewa ɗiyar ɗan cacar nan ne shege mashayin giya ya haifo wannan kyakkyawar , wani yace ai yarinyar shegiya ce tana burgeni domin tanayin karuwancin cikin tako ne , kowa dai da abinda yake faɗa akaina abundai babu daɗin saurare ,

Murmushi mai ciwo nayi yayin dana tunkari mota ta , wato shi karuwanci babban tambari ne da baya gogewa har "ya "ya da jikoki kayi ƙoƙari ka zama na gari domin gori akan karuwanci ciwo gareshi yau mutane da sun san zasu taɓani su kwana lafiya inajin dasai sunci ubana kafin na fito , mota na shiga na karce duk wanda bai ga zuwa na saida yaga fita ta ,

Wuta ² na iso anguwarmu , a ƙofar gida naga motar shi , lokacin 10:33am kai tsaye inda na ɗauko motar na maida ta , lokacin dana fito ban sameshi ba kenan yazo da kanshi yaga lokacin da zan dawo ? Da sauri na wuce cikin gida dan inada abinda zanyi ,

Wuri ɗaya naje da mota amma yau gari magana ta kawai akeyi wata karuwa take tare da ɗan gwamna ta gama dashi ta tsafeshi har ya bata motar daya siyo ta miliyoyin kuɗi , duk inda ka saƙa a gari Sultana ɗiyar ɗan caca kafin wani lokaci kuma hotuna na sun fara yawo a social media da motar dana hau ɗiyar ɗan cacan da yafi ko wane ɗan caca sa'ar rayuwa ,

Al ' Ameen kuwa tuni yaje ya samu mahaifiyar Dikko ya faɗa mata halin da ake ciki dan yaga Dady yayi sanyi , Momy kuwa tayi zafi har ta wuce tafasashshen ruwa , matar Dikko data zo gaisheta itama ta cika ta kawo wuya , tace ma Al ' Ameen ya bari Dikko ya tafi a kamo Sultana zata ƙagi azabar da zata bata , Al ' Ameen yace ai ko yanzu ina iya kawota , Momy tace kudai bari yabar katsina dan koni baya so kamar yadda yake san mayyar yarinyar nan ,

Wane dalili yasa Dikko ya matsamin nahau motar daya bani yau ? Tabbas dan yasan za'ayi magana ne kuma haka yake so dama kowa yasan ina tare dashi shima yana tare dani dan idan babu wata alaƙa dani dashi mai girma me zai haɗani da motar shi.... ?

Yau kuma idan akwai wanda yafi *Jiddah* baƙin ciki bai wuce Momy ba kuma sun tanadin shaglin partyn wulaƙanta ni , Jiddah bata ƙara jin takaici ba saidai Dikko ya tura Ashiru ya maida ita gida , tace bata komawa , koda Ashiru ya faɗawa Dikko tace bata komawa cewa yayi ya barta idan ta gaji ta koma da kanta ,

Tunda naje gidan rasuwa ban sake komawa Dikko ya hanani , sai yau sadakar 3 yace inje amma yau mintuna 10 ya bani , Umar ya aiko ya kawomin kuɗi in bada sadaka idan naje , kuma har yanzu yana gari bai tafi ba saboda kullum rana muna tare ,

Ina ta shiri zan fita saiga Ummu Affan wai tazo min gaisuwa , bayan ta gama ta'aziyyar tacemin ashe kuma sai kikayi mota ? Murmushi nayi ban bata ansa ba naci gaba huɗɗar gabana kenan ba gaisuwar ta kawota ba dan kawai taji labarin mota , saida na gama shirina kaf nace tou zan rufe ɗakin , tace tou bari in tafi idan kika dawo na dawo , fita tayi nima na fita na rufe ɗakin .

Ina fita naga Baba zaune a tsakar gida duk yayi wani kalar ban tausayi , nace Baba baka lafiya ne ? Kallona yayi yace wallahi Mamana gabana keta faɗuwa , nace miya faru ne ? Yace nidai nayi miki alƙawari nabar caca har abadan duniya nace Eh Baba , yace tun daga ranar da mukayi maganar dake da na saka motarki a caca wallahi ban sake zuwa koda wurin caca ba haka duk abokai na bana tare dasu tun ranar ban sake shan giya ba haka kuma ban sake neman mata ba ,

Nace to yanzu meya faru ne ? Yace abun ya dameni ne tun ranar da nayi wannan maganar idan na kwanta bacci sai inga wani mutum tsaye a gabana yana cewa idan baka koma caca ba ajalinka ne zaici gaba da fuskantar ka , ka koma caca kaci gaba da neman mata kasha giya idan ba haka ba zamuyi maka kisan wulaƙanci domin zaka lalatamin duk wani tsari na ,

Shine nace bazan koma ba , jiya itace rana ta ƙarshe daya bani kuma yace yau idan banje gidan caca ba wallahi kasheni zaiyi , murmushi nayi nace Baba kenan wannan ai duk shirmen bacci ne , yace Mamana ba shirme bane da gaske ne dan har sunanki naji an kira a mafarkin yace shine ya toshe miki rayuwa wai ya rufe ƙwalwarki a bakin mataccen kwaɗo , dariya nayi sosai nace ji wani magana Babana ni na tafi saina dawo ,

Saida na fita daga anguwarmu zuciyata ta fara tabbatarmin da ba shirme bane , maganar Baba abin dubawa ce da tunani iri ² na isa gidan rayuwa , ban jima ba na fito bayan na basu kuɗin da Dikko ya bani duka ban rage komai ba ,

Jiki a sanyaye na dawo gida ban samu Baba ba , dan haka na shiga ɗakina kaina sai juyawa yakeyi , wayata na ɗauka na kira Dikko kaf na rattafa mishi abinda Babana ya faɗamin , yace baya nan yaje kano amma idan yayi magrib zai taho in Allah ya yadda , nace tou don Allah daka dawo kazo wurina , yace insha Allah An mata ki kwantar da hankalinki babu abinda zai faru sai alkairi , nace tom saida ya kwantarmin da hankalina sannan ya kashe wayar ,

Ina gama waya da Dikko wayar Mamy ta fara kuka , da sauri na ɗauki wayar ba tare dana san mai kirana ba , ina ɗauka nace Hello , mai magana a waya tace Mamy na samu duk bayanan da kike buƙata , kila bata san Aunty Mamy ta rasu ba , akwai wani kwaɗɗo da aka rufe gawarshi a kwalbar lemu kuma gawar kwaɗon saida aka zuba kwata a cikinta , akwai bokan dake gyara aikin kullum amma yace abu ya warware komai zai iya faruwa tunda har Binna ya fita a caca ,

Anyi ƙoƙarin juya al'ƙamin tsafi ya sauka akan yarinyar da kike magana bokan yace sai ta tsallake sallar isha'e da asuba idan har batayi su ba tana dai cikin tsarki ba jinin al'ada ba itace zata maye gurbin ubanta , yarinyar tana da addu'a gaskiya kuma bata wasa da sallah , kiyi sauri yanzun nan suka kira Binna zasu kashe shi.... Kwalbar da akayi asiri gata a hannuna , amma kiyi gaggawar zuwa gidan........ Ihun matar naji ina ta hello ׳ amma cikin wahaltacciyar murya tace kiyi gaggawa zuwa bayan gidan caca acan za'a kashe Binna ni kuma zanci da sauran....

A firgice na fara kiran wayar Dikko amma sai akacemin a kashe take , wayar Babana na fara kira sai ringing take amma ba 'a ɗauka , wayyoni Allahna na sake faɗawa wata rayuwar , me yasa Dikko ya kashe wayarshi ? Su waye suka kirashi ya fita ? Me akayi ma wacce nake magana da ita a waya ? Wayyo Allahna rayuwa me yasa zakiyimin haka ne .....⁉ 😭




06/10/2019




*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 51



*_Godiya ta mussaman gareku ma'abota mutunci da mutunwa , ngode ׳ ina godiya sosai wanda idan nace zanyi ta rubuta ngode ² sai cajin wayana ya ƙare ban gama rubuta godiyar ba ,_*

*_Hassan 80k_*
*_Hassana Masko_*
*_Hafsat Sa'idu Galadima_*
*_Muhammad Musa Muhammad { Na Allah... }_*
*_Halimatu Musa { Uwa }_*

*_Gaba ɗayan shafin nan na yau sadaukar wane ga masoyana a duk inda kuke a faɗin duniyar nan ina sanku ina ƙaunarku kuma ina alfahari daku , fatan alkairi a gareku_*

*_Kuma na gaishe ku..._*

*_Abdulrahman & Ja'afar , Allah ya tabbatar da farin ciki da kwanciyar hankali a gareku ubangiji ya jiƙanku yasa ku gama da duniya lafiya , Am3n_*


Juyawa ɗakin yakeyi dani kamar anayin hajijiya dani , wayyo Allahna ina zan dosa ? Mi zanyi ? Ya Allah ka kawomin mafita ka tausayawa rayuwata kuma ka tabbatarmin da alkairin ka , banda zaɓi sai naka banda wurin gudu ko tsira sai yadda kayi dani ya ubangiji al'arshi taimakon ka nake nema bana san taimakon kowa sai naka , duk abinda ya faru da Babana dani haka yazo a rubuce kuma babu wanda ya isa ya goge,

Da gudu na fito daga cikin ɗaki ina cewa yaku taron "yan uwana kuzo kowa ya biyoni domin dai yau wata baƙuwar rayuwa tana tunkaro mu , ciwon ba nawa bane ni ɗaya , babu babba ba yaro ba matar Baba ba mace ba namiji yau tashin hankalin gaba ɗayan gidan ya tunkaro ku taho Baba yana buƙatar taimako !

Ina faɗin haka nayi gaba da gudu , namiji ɗaya ya biyoni shine babban yayanmu yana ke Sultana ina zaki ? Banda lokacin bashi ansa gudu nakeyi kamar taɓaɓɓiya shima da gudu ya biyoni ina fitowa bakin titi na samu napep nace muje , Yaya yana fitowa tuni mun tafi , shima dafe kai yayi tare da riƙe ƙugu , ganin hakan ba mafita bane yasa ya tari mai machine yace yabi mishi bayan napep inmu.

Muna isa tun kafin napep inmu ta tsaya na dire na tun kari inda nake hango mutanen da basu wuce su biyu ba , sunyi rami sun saka hannun takobi cikin ƙasa tsinin kuma yana sama , bayan sunyi wa Babana wani irin duka a kai ya tafi duniyar ɗimuwa jini sai bin jikinshi yakeyi , bana iya gane fuskar kowa a cikinsu saboda rufe take idanuwansu kaɗai ake gani ,

Mai napep yana ganin haka ya gudu babu shiri dan tsira da rayuwarshi yayin da ni kuma na tunkari wurin haiƙan ina cewa kai na rantse da Allah idan wani abu ya sameshi gaba ɗayanku sai tsinuwar Allah ta tabbata kanku , ku barshi me yayi muku ne ? Me rayuwar shi ta tsone muku ko kune kuka bashi aron lumfashi ne ? Ubangijin al'arshi shine ya bawa Babana aron numfashi kuma shine ya bashi lafiya ku ɗin nan banzaye da ku baku isa ku fitar da ransa ba sai Allah yaso ,

Dariya sukayi sosai tare da cewa tou Allahn ne yaso shi yasa ma ya kirashi kuma yanzu zai tafi domin ansa wannan kiran idan kina iyawa ki kamo ran ki dawo dashi cikin jikinshi , suka ƙarasa maganar tare da ɗauko Babana suka birkitashi saitin zuciyarshi suka ɗagashi sama suka dakoshi saman takobin da ƙarfi , sai kuma suka ɗagoshi suka juyashi yana kallon sama suka sake sokeshi...

Da gudu na isa wurin Babana na durƙusa saman guyawu na , nace Babana karka sake ka rufe idanuwanka babu abinda zai sameka kallarni gani nan nazo Mamanka Uwar masu gida jikina yana ƙyarma na fara ƙoƙarin ɗago Baba amma na ƙasa idan kuma nace zan juyoshi ina tunanin inda bai yanku ba ma zai yanku ,

Babu abinda ke ɗiga daga cikin idanuwan shi sai hawaye yana lunshe ido nace kar kayi bacci ka rufamin asiri karka rufe ido idan ka rufe ido tawa ta ƙare , waye ? Waye wai waye mutumin da kake gani a baccin ka ? Waye ya kiraka wurin nan ? Karfa ka rufe ido yi murmushi yimin murmushi Babana , dakel ya ɗago idonshi ya kalleni cike da soyayya sannan yayi murmushi da gefen bakinshi la'elaha illallah muhammadur rasulillah ya ƙarasa tare da rufe idanuwanshi , nice na ida da S. A. W ,

Kai........ Na shiga 3 na bani na lalace wayyoni Allahna wayyo rayuwa ina zan sa kaina , nace kar kayi bacci shine kayi bacci me yasa ? Me yasa kayimin haka haba Babana , shine zaka tafi ka barni ? Bayan kamin alƙawari baza ka tafi ka barni ba , shine ka tafi ka barni ? Ya ubangiji ka farkar dani wannan mafarki ka tausayamin badan halina ba dan darajar manzan tsira kasa bacci nakeyi ,

Isowar Yayana shima da gudu ya iso wurin cikin tashin hankali yaga Babanmu soke a saman takobi dan suna soke Baba suka gudu , shima wani irin ihu ya kurma hakan ya jawo hankalin jama'a , kafin kace me ? Wuri ya cika sai kuka nakeyi ina ƙarawa tare da cewa wai Allahna , wai Allahna , Allahu Akbar ,

Sauko Baba akayi daga saman takobin har yanzu murmushin da yayimin yana nan akan fuskarshi bai goge ba , kamar kace taso ya taso sai kayi tunanini bacci yakeyi , duk wanda yazo saiya haskashi saboda duhu yayi sosai , ganin ana ta kallemin Babana yasa na cire hijabina na lulluɓeshi a lokacin har Yayana yayi waya an kawo mota ,

Allah mai girma da ƙafafuwan shi yazo wurin nan amma gashi yanzu baya iya tafiya sai an ɗaukeshi , bayan an saka Baba a mota Yayana ya kamoni nima ya shigar dani duk muna zaune a baya yayin dana kwanta saman gawar Baba inaci gaba da kuka ,

Zuwan Mamy gidanmu na tuna ranar data zo ta samu Baba zaune a saman dakali tana bi bi biyyyy , murmushin da Baba yayi mata na tuno da alamar da yayi mata da ido , yau gashi daga Baba har Mamy duk basa cikin wannan duniyar , kai.... Wani irin ihu na sake kurmawa daga nan ban sake sanin abinda ya faru dani ba saidai na farko na ganni a ɗakina Dikko durƙushe a gabana idanuwan shi sunyi jajir Ashiru da Umar suna tsaye a bayanshi .

Tashi nayi cikin kuka na rungume Dikko nace me yasa ka kashe wayarka ? Kiyi haƙuri har yanzu wayar a kashe take banda caji , kauda maganar nayi da cewa kaga Babana ko ? Ranar da nayi faɗa dakai na dawo gida shine Baba yayi kuka yace Mamana shine kika tafi kika barni ? Ni na goge mishi hawaye da wannan hannun nawa na nunama Dikko hannun naci ga da cewa nace masa ai na dawo ,

Nace Baba kana tunanin zan tafi na barka ne ? Bayan bana iya rayuwa saida kai ! Dare da rana safe da yamma yanayin farin ciki ko damuwa halin yunwa ko ƙoshi babu kowa a zuciyata sai kai , farin ciki ya dawo rayuwar ƙunci da damuwa zata kama gabanta , cikin kuka nace shine ya tafi ya barni , ni in rayuwar ƙunci da ɓakin ciki wayyo Allahna , wai Allahna.....?

Inajina kamar inayin rayuwar da bana cikin sahun mutane yayin da farin ciki yake tunkaro rayuwata sai mutuwa tazo ta shafe wannan farin ciki , duk wanda yazo da niyar ya taimakeni sai a shafe labarinshi a duniya , bana so ka rasa rayuwarka ka tafi daga rayuwata kada kaima su kashe ka....

Juyawa Dikko yayi yace ma Ashiru ku jirani waje , fita sukayi , Dikko ya ɓanɓareni daga jikinshi ya zauna kusa dani yace ina Mamanki ne ? Cikin kuka nace ta gudu tabar rayuwata banma san ita ko "yar gidan wane ahalin suka haifota ba , ni ɗaya nake rayuwata a wannan ɗakin babu ruwan kowa dani nima banda ruwa da kowa babu mai so na sai Allah banda wanda zai nunamin kyakkyawa ko mummuna duk rayuwar dana ɗauko ita nakeyin abuna gani yau na zama marainiya.....

Kallona Dikko yayi yace ke ba marainiya bace Allah yana tare dake kuma Dikko yana tare da rayuwarki , duk wanda kika ga ya mutu kwananshi ne ya ƙare ki daina mishi kuka kiyi mishi addu'a , nace to , Dikko yana gidanmu shi ya tayani zama a ɗakina yana min nasiha sai 1:39am yabar gidanmu ,

Bayan tafiyarshi ma na tuna banyi magib ba bare isha'e , fita nayi nai alwallah nazo nayi sallah nayi karatun al'qur ani mai girma tare da roƙawa Babana rahma a wurin ubangiji , har gari ya waye banyi bacci ba kuma banje ɗakin da aka kwantar da gawar Babana ba ,

Tunda safe gidanmu ya fara ɗaukar mutane su Amisty da suka zo ɗakina suka sauka , suna shigowa ni kuma na tattara wayoyina da tawa data Mamy na fita , ɗakin da aka kwantar da gawar Baba na nufa , har anyi masa wanka an shiryashi yana kwance a mankara , ina tsuguniya abinda ya tunomin shine ,

Ranar da muna zaune dashi a ƙofar gida nace Babana ina sanka ina kuma tausayawa rayuwata ranar da za'a wayi gari babu ɗaya a cikinmu , murmushi yazo ya tsayamin a rai da maganarshi da yace min ai bazai tafi ya barni ba , a bayyane nayi magana cikin kuka nace shine ka tafi ka barni...

Naci gaba da kuka mai tada hankali , ina Allah ya jiƙanka ubangiji yasa ka huta , Allah yasa can yafiye maka nan Allah ya sadaka da mala'ekun rahma ubangiji ya kauda kai akan duk laifukan da kayi masa ya yafe ma ya gafarta maka ya baka aljanna dan arziƙin annabi muhammadur rasulillahi sallallahu alaihi wasallam....

Zainab ce ta riƙeni duk gidanmu Zainab tafi kowa tausayi na tana so na , tace Sultana kiyi shiru don Allah , cikin kuka na rungumeta nace don girman Allah ki tasheni daga baccin nan haka nan wallahi zuciyata ta kusa ɓarewa ,

Haƙuri kawai take bani , ina nan zaune a ƙasa kusa mankarar Baba sai kuka nakeyi , bayan wani lokaci kuma maganar Baba ta faɗomin a rai da yace idan har na mutu karki sake kimin kuka addu'a zakimin shine kaɗai zai tabbatarmin da soyayyar da kike min , shiru nayi naci gaba da gumji ina addu'a wa Babana ,

Misalin 08:50am gidanmu ya gama cika duk ta inda baka tunani , 09:00am aka ɗauki mankarar da Babana yake sama kwance za'a fita dashi domin salla tar gawarshi shi , shikenan Baba zai tafi inda bazan sake ganinshi ba bazan sake jin muryarshi ba har abadan abada duk soyayyar da yakemin ya tafi da gaske ya barni.... Sake ɗaukewa nayi na ƙara somewa !

Har akayi ma Baba sallah aka kaishi gidanshi na gaskiya Sultana bata san inda kanta yake ba , zata dawo² shiru har la'asar babu Sultana babu labarinta , duk wani taimako daya kamata ayi mata anyi amma har 5 na yamma bata dawo ba ,

Dan haka yasa Dikko yace a fito da ita a kaita asibiti , Zainab ce akan Sultana sai firfita take mata dama itace ta kula da ita a asibiti lokacin da Dikko ya farke mata mutuntakarta , da taimakon wasu matan aka fitar da Sultana aka sakata a mota da Zainab kaɗai aka tafi sai Ashiru dake tuƙi saishi Dikkon.

Asibiti mai kyau aka kai Sultana likitoci suka rufa akanta dan ceto rayuwata , amma duk yadda akayi saida Sultana ta kwana huɗu bata cikin hayyacinta , ga dai ido tana kallon kowa amma ƙiri² bata iya magana , bata ci bata sha sai kuka , hankalin Dikko idan yayi dubu ya tashi ya lallashi Sultana har ƙarfinshi ya ƙare amma Sultana taƙi tayi magana da kowa , da tsiya² Dikko ke bawa Sultana ruwan tea shima idan tasha saita amayar dashi ,

Zainab itace ta bawa Dikko shawara ko a riƙa ba Sultana fura duk tsiya dai ko tayi amai wata zata tsaya , Dikko yasa Ashiru ya samo fura ake ba Sultana amma ko tasha sai ta dawo da ita ,

Dikko yace haba An mata wai me yasa kikeyin haka ? Gaskiya banajin daɗin abinda kike yi ko nima so kikeyi in mutu shikenan sai ki huta ? Kiji tsoron Allah ki tausayawa rayuwata haka nan mana , ke shikenan abu baya wucewa wurinki ? Kina nufin ke Allah bazai jarabce ki ba ? Ko akanki ne aka fara rashin iyaye ? Ba'a fara a kanki ba , ba kuma za'a gama akanki ba , mutuwa tana nan tana zagayawa tsakanin rayuwar kowa kuma babu bararre a duniya duk wanda yazo sai ya koma , ina ilimin naki da kike alfahari kina dashi ? Wannan shine sakamakon da zaki sakawa rayuwa dashi ? Shi kukan mutuwa da kika ganshi ba'a gamashi kuma baya ƙarewa har sai ranar da rai ya ƙare kiyi haƙuri don Allah .

Murmushi Sultana tayi mai ciwo dan gani takeyi Dikko baima da hankali , ya za'ayi ta daina kukan rashin Babanta ? Ubanda ya ɗauki soyayya duniya ya ɗora mata , cikin "ya "ya sattin da wani abu itace kaɗai ya ɗauki duk soyayyarshi ya bata , taya ma zata manta Baba ? Taya zata daina kukan rashin shi ? Duk ma wanda yace tayi haƙuri ta daina kukan rashin shi

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment