Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

girman zunubi , kasan surar da Allah ya sauke akanmu mu mazinata , ina matsalar take tsakanin kai da matar ka ne ?

Gyara zama Alhaji yayi sannan yace :• me yasa matan bariki suka fi iya jan hankalin namiji ? Ba tare dana kalleshi ba nace shaiɗan ne yake ƙawata maka su domin yasan zina hanyace da take kai mutum ga halaka , zina tana zubar da mutinci tana rage ma mutum daraja a wurin ubangiji sannan mutuncin shi zai ragu a wurin al'umma kuma zina tana rage ƙwarjini fuska ,

Har yanzu baka bani amsar tambaya na ba , miya ja ra'ayinka shiga harkar bariki wai ? Alaji yace matan bariki kullum a shirye suke basa taɓa gajiyawa da ansar buƙatarka duk lokacin daka zo musu zasu anshe ka cikin farin ciki ba tare da gajiyawa ba , zaka kwanta da mace babu wari a jikinta babu ƙarni ko zarni bare kuma hayaniyar "ya "ya , yayin da zaka kwanta da matarka lokacin zata fara cewa batayi ma yara shimfiɗa ba , kana mata magana tana wani fiffizge kai tun kana sha'awar abun har yazo ya fita akanka ,

Kallon Alaji nayi sosai sannan nace , filawar bisa hanya tasha banban data cikin gida , mace kamar filawa take idan ta samu wuri mai kyau kuma akayi mata ban ruwa yanda ya kamata idan dai tasha ruwa ta ƙoshi duk wanda ya gani sai ta bashi sha'awa , lokacin da filawa ta rasa ruwa zata bushe ta soye duk wadda ya kalleta baya sha'awar ƙara kallonta , to haka mace take , matan bariki wayau suke muku kuna basu kuɗi suna gyara jikinsu a cikin kuɗin da kuka basu a ciki suke siyan abunda zasu ja muku hankali dashi , matarku ta sunna tana can viseline in da zata shafa wahala yake mata , taya zata gyara bare har ta baka sha'awa ? Idan baza ka damu ba zanyi magana da matarka idan Allah ya kaimu idan har tabi shawarata tabbas zaku samu rabauta , kai kuma zan koya maka yadda akewa mace ban ruwa ....

Shiru Alaji yayi zuwa wani lokaci yace babu damuwa kije na yaddar miki , godiya nayi masa sannan na miƙe ɗauko kujerar sukayi suka biyoni da ita yayin dana tsaya wurin wata motar...

Ajiye min kujera akayi na zauna , motar a buɗe take dan haka na ɗora ƙafata ta haggu a saitin mazauni driver tare da cewa malam barka da dare ! Allah ya taimaki uwar ɗakinmu ya haƙuri damu ? Alhamdulillah na faɗa tare da cewa ya iyali ? Kamar jira yake yace tana can shegiyar saida nayi mata jakin duka na fito , kallon agogon hannuna nayi ba tare dana kalleshi ba nace me tayi maka ne ? Ta rainani idan na shigo da leda takemin sannu da zuwa idan banzo da itaba ko daga ɗaki bata fitowa , yau na yanka rago dake duk sati nake yankawa , mahaifiyata tazo nace a ibar mata shine tayi mata rashin kunya ni banji daɗin abunba shi yasa nayi mata duka na baro gida ,

Kallonshi nayi sannan nace to me kazo kayi nan ? Dariya yayi irin ta sakarkari sannan yace nazo a ban natsuwa , jinjina kai nayi sannan nace tou yau babu maganar bariki kaje gida ka lallashi matarka muna zuwa gidan idan Allah ya kaimu , ina faɗin haka na miƙe nayi gaba , ɗauko kujerar sukayi suka biyoni domin cikin gida na nufa...

Hayani mazan suka farayi tare da cewa ya zanyi musu haka ne ? Ai haka ma babu adalci , a zuciyata nace wannan matsalarku ne ba nawa ba ,

Ina shiga gida na shige ɗakina , Amisty ta rufomin baya , itace ta kulle ɗakin domin dare yayi kowa a gajiye yake babu abinda yake buƙata sai bacci , kayan jikina na cire na ɗaura zanin bacci , Amisty kuwa da kayanta tayi kwanciyarta ,

Tunda na kwanta fuskar Dikko kezomin a idanuwana , ya ƙara kyau abu ga farar fata ga hutu ga gayu gemunshi yasha gyara sai kyalli yakeyi , an gyara ƙasimbar ta kwanta sosai dake farine sai abun ya bada wani irin sirrintaccen burgewa , shi ba wani tsoho ba amma dole sai ya zama tsoho me yasa yakeyin haka ne ? Dan yaga gemun yana mishi kyau gaskiya fa yayi mishi kyau shi yasa yake ɗaukar hankalin mata , gemu da ƙasimba make up in maza kenan...

Ajiyar zuciya na sauke tare da gyara kwanciyata , damuwa nakeji sosai ina ta ƙoƙarin molaƙe rayuwata ashe shi Dikko yana can yana ƙoƙarin gyara tashi , zaiyi aure ya barni ina cikin karuwanci , ina ganin zan masa rata ashe shine zaimin rata , ya zama shugaban al'umma ta wani gefen ni kuma na zama shugabar rusa rayuwar farin cikin wasu da tawa rayuwar ? Hawaye ya cikamin ido bayan sun gangaro na maida numfashi dakel sannan naci gaba da zancen zuci ! Me yasa na zaɓi na zama karuwa ? Me yasa banyi ƙoƙarin zama ta gari ba ? Mai makon na zama waraka ga al'umma sai na zama cuta a garesu...

Kukan zuci naci gaba dayi irin mai kartar zuciyar nan wanda kesa mutum yaji kamar zai mutu shi naci gaba da yi numfashi na naji yana ƙoƙarin fita daga jikina dolena na tashi zaune da sauri naci gaba da fita dan ceto tawa rayuwar....

Zaune yake ya hakince irin zaman nan da yakeyi na ya raina mutane , ɗage yake kallon kowa yayin da bakinshi ke motsawa a hankali cikin kwarewa da goguwar iya cin cingom , Al ' Ameen ya kalla sannan ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi yace wai mema zance mata idan tazo ? Murmushi Al ' Ameen yayi tare da shafa kanshi yace tuba nake ranka ya daɗe , dan tunda akayiwa Dikko kyautar Sadiyya bai taɓa zuwa ba sai yau , baya ko waya da ita yauma Dadynshi ne ya matsa mishi shi yasa yazo !

Dan ko hotunansu dake yawo a social media haɗawa akayi bashine da ita suka jera suka ɗauka ba , Dikko baiyi magana wa Al ' Ameen ba Sadiyya ta shigo cikin palon , gaisheta Al ' Ameen yayi sannan ya fita...

Cikin karairaya da kwarewa da bariki tayo inda Dikko yake zaune , ɗan taɓe baki yayi a zuciyarshi yace bari inga rashin kunyarki , bai gama tunani ba ta zauna tare da ɗora kanta a saman kafaɗarshi tana mai sauki ajiyar zuciya cikin yanayin mai nuni da tana cikin shauƙi, daga waje har ciki Dikko baiji wani shock ba , dan haka yace sauke kanki mace bata hawana , na miki uziri nayau idan kika sake zaki samu matsala....

A shagwaɓe tace haba diye { dear } ... Yanayinka sch ne amma ya kake abu kamar class ? Banza Dikko yayi baice komai ba , jinyayi shiru yasa tace ya hanya da mutane ne ko ? Nan ma bai bata ansa ba , zagba surutu taci gaba dayi tare da cewa idan sukayi aure zata mishi soyayya , ba komai kake ta wani jan allo dana fara rubutuna zaka sauke , hauka dai tayi ta zuba mishi tare da son ƙara kwanciya jikin Dikko amma abun ya mata girma ,

Bayan ta gaji da surutun tayi shiru , can kuma taci gaba , kasha drinks mana , ta ci gaba da lissafo duk abinda aka kawoma mashi , har ta gaji ta sake ɗaukewa , ganin Dikko bazaiyi magana ba yasa ta fashe da kuka cikin kuka take cewa haba Yaya wai me yasa baka so na ne ? Ina ta magana amma kamin shiru ka mayar dani kamar wata mahaukaciya ! Nifa "yar uwarkace ka soni dan Allah kodan zumunchin dake tsakaninmu....

Kallonta yayi sannan yace ya isa , kije ki kwanta a gajiye nake muyi magana anjima , goge hawayenta tayi tare da cewa ai ko na kiraka ma baka ɗauka , karki damu zan ɗauka insha Allah , murmushi tayi tare da miƙewa cikin farin ciki , shima murmushin yayi zuciyarshi tace dama An matane a wannan yanayi , wata "yar jakace a gefenshi ya nuna mata yace ɗauka...

Ɗauka tayi babu ko godiya ta fice a palon , wayarshi ya ɗauka ya nuno hoton Sultana , ya ɗauki tsawon lokaci yana kallonshi bayan wani lokaci yayi magana a bayyane cewa kuka kikayi , ina gane yanayin farin ciki da damuwa idan na kalli hotonki , duk yanayin da naji na shiga tou kin shiga yanayin meke damunki ne ....?

Banda ajiyar zuciya babu abinda nake saukewa har yanzu zaune nake ban kwanta , ɗan ɓata rai Dikko yayi a daidai wannan lokacin ya kalli hoton Sultana sannan yace ki daina damuwa ki zama mai farin ciki a ko wane lokaci , taɓa screen in wayarshi yayi tare da cewa kiyi bacci cikin aminci da salama ....

Ajiyar zuciya na sauke tare da komawa na kwanta , ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗaukeni , .....

Koda Dikko ya koma masauki wanka ya farayi duk saida ya gama abinda yakeyi sannan ya cire wayarshi daga airplane mode , kamar wani munafiki wai ba'a kunna waya sai dare sosai zai duba saƙon da aka turo masa , a lokacin zai shiga yanar gizo , a lokacin zai ansa waya idan aka korashi itama sai wacce yakeji zai iya ɗauka , da zaran kuma ya gama abinda yake zai sake rufewa sai kuma wani daren , wayarshi ɗaya kuma da ake samunshi ba kowa yake da number ba , daga gidansu saida wanda shine yaga dama ya bashi , dan dayaji an kirashi da wayar to yasan kirane mai mahimfaci ,

Wani vidio ya buɗe da abokinshi ya turo mishi , kafin vidion ya buɗe ya fara karanta rubutun ƙasan vidio da akayi ,

_Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , Allah yayiwa Fatima rasuwa sakamakon fyaɗe da akayi mata , abun babu kyan gani kuma ko su waye da gayya sukayi mata sun wulaƙanta yarinya bataji bata gani ba , sannan suka ɗauki vidio a waya suka bada wayar a cikin envilop aka kaiwa Babana har Office dan lokacin kwananta ɗaya da yini ba'a ganta ba , gawar kuma suka zo suka jefar a ƙofar gida..._

La'ilaha illa anta sub'hanaka inne kuntu minaz zalimeen Dikko ya furta a lokacin daya gama karanta saƙon ya fara kallon vidion , ƙattin maza ne sunkai su biyar amma duk sun rufe fuskarsu da maX , ihu Fatin keyi amma babu abinda ya damesu kowa burinshi ya biya tashi buƙatar , wani irin motsi Dikko yaji kwalwarshi tayi kanshi ya yamitsa da sauri ya ajiye wayar tare da dafe kanshi da dukan hannuwanshi biyu abinda yakeji da game da Sultana ya dawo mishi sabo....

Lahaula wala kquwwata illa billahil ' aliyyil azeem , Dikko yake ta maimaitawa ya ƙurawa kafet ido kamar Sultana ce a wurin , saida natsuwa tazo mishi yaci gaba da zancen zuci lallai ya cuci rayuwar Sultana shima bashi da banbanci da mutane biyar ɗin nan domin magungunan daya sha sun bashi wani irin ƙarfi wanda ko allura hauka akayi ma doki iyakar abinda zaiyi kenan dan nuna shi mai ƙarfi ne , hawaye ya cikawa Dikko ido tausayin Sultana ya ƙara kamashi lallai ya cuci yarinyar nan !

Yau wane irin baƙin ciki iyayen Fatima suka shiga ? Wane irin ɗaci sukeji idan sukaga wannan hoto ? Ya Abbakar zaiji yayin daya ga wannan hoton akan ƙanwarshi ? Da nine ya zanji idan haka ta kasance akan ahalina ? Kwantar da kanshi yayi a saman hannun kujara ya rufe idanuwanshi duk yanda akayi akwai abinda Baban Abbakar yayi suka ɗauka fansa dan yanayinsu ya nuna a lokacin da suke aikatawa kamar biyan bashi ne sukeyi , Allah na tuba ka gafartamin ka sakawa An mata soyayya ta mai girma a zuciyarta , sona ya hanata bacci da tunanin kowa a duniya saini , ta daina jin maganar kowa sai tawa , ka saka mata san kasancewa dani inuwa ɗaya kasa mata firgici idan ta yini ko ta kwana bata ganni ba , ka ɓadda mata tunanin kowa da komai na duniya saini , ka saka mata san jin muryata ka goge mata kuɗirin fansa akaina , nayi alƙawari zan zamar mata natsuwa zan zama uwa da uba data rasa masu kishinta bazan barta tayi kuka ba haka kuma zanyi ƙoƙarin sakata farin ciki , duk wanda ya ɓata mata ko yasa taji damuwa nine zan tsaya harsai naga tayi farin ciki , Allah ka gafar tamin ka goge damuwata a zuciyar an mata ta zama soyayya mai ban al'ajabi ga kowa ,

Buɗe idanuwanshi yayi tare da goge hawayenshi , sannan ya ɗauki wayar ya goge vidio ba tare daya gama gani ba , wayar Abbakar ya fara kira dan jajanta mishi kafin yaje mishi ta'aziyya , Sadiyya koda ta kira Dikko text ya tura mata idan ya gama zai kira , koda ya gama abinda yake ba wulaƙanci ba da gaske ya manta da labarin kiran Sadiyya , da tunanin An mata yayi bacci....

Da safe wanka nayi na shirya cikin riga da zani na atamfa , hijabi na saka sannan nacewa Amisty zanje in dawo ! Ina zakije tunda safe haka ? Ta tambayeni ! Takalmi na saka tare da ce mata zanga wani a bakin hanya , addu'ar a dawo lafiya tamin ni kuma na fice daga ɗakin...

A ƙofar gida na anshi makullin mota na dana sa aka ɗaukomin , ɗan daba ɗaya na dawo dan ya rakani gidan Alaji koda an samu ɓacin rana , abinda yasa ban tafi dasu Amisty ba saboda kar ya zama naje gyara kuma gyaran ya zama ɓarna.....

Tafiya mai nisa mukayi zuwa gidan Alaji , a ƙofar gida nayi parking sannan na fara kiran wayarshi dan dama banzo ba saida izininshi.........







09/09/2019






*JAMILA MUSA.....* 💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 29


Bai ɗauka wayar ba ya fito daga cikin gidan , ina cikin mota zaune nima ban fito ba , shine yazo har wurin mota ya buɗe gidan baya ya zauna amma bai rufe ƙofar ba , juyawa nayi ina kallonshi tare da cewa dana kira naji baka ɗauka ba nayi tunani ko baku tashi bacci ba !

Gyara maɓallin rigarshi yayi tare da cewa ai ina ganin kiranki nasan kina ƙofar gida shi yasa nace kawai bara na fito basai na wani tsaya ɗaukan waya ba , murmushi nayi na juyowa ina kallon gabana wato na juya daga kallon Alaji nace muje ciki to...

Tou muje amma bata nan ta shiga maƙota , ɗan zaro ido nayi amma banyi magana ba , a zuciyata nace maƙota tun wannan safiyar ? Lallai akwai ƙatuwar matsala , sauka nayi daga cikin motar tare da cewa muje *Wane Yaro* ɗan daban da nazo dashi ,

Rufe mota ta nayi muka nufi cikin gidan dukanmu , a ƙaton palon matarshi ya saukemu gafa kujeru har kujeru amma datti yasa sun tashi aiki , bakajin wani ƙamshi ko na tsitsiyar ƙamshi bare kayi tunanin zaka samu turaren wuta banda zarnin fitsari palon kaca ² a firgice babu abinda ke tashi sai wani ƙanni² a palon....

Saman hannun kujera Alaji ya zauna ni kuma kallabin kaina na ciro na shimfiɗa a matakalar da zata gangaro dakai cikin palon dan wannan kujerun idan har na hau su yau babu abinda zai hana ƙurajen ƙyama su fito jikina....

Fira muka farayi da Alaji ya ɗan fara karanto min matsalolin da yake fuskata , yace ga ƙazanta ga rashin ragowa ga fita babu gaira babu dalili , ga rashin godiya ko zai kashe kanshi ya bata bata taɓa masa godiya ba , wallahi idan har zai kwanta da ita sai ankai ruwa rana sannan kuma babu wanka bare yayi tunanin zai ji wani ƙamshi da zaisa mishi yaji wani shauƙi yayin da yake kwanciya da ita...

Uhum har ga Allah ba sasanci ya kawoni gidan Alaji ba a wannan lokaci , ina da wani ƙudiri nawa na daban , ina so inga yanayin yadda yake hidima da gidanshi , surutar da matarshi take amfani da ita kuma har store insu yau sai naje dan inga idan naci gaba da tarayya da Alaji zai iya ɗaukemin duk wasu buƙatu na ? Dan nima in samu wanda zai tayani kula da tawa rayuwar , zan kuma bigi cikin matarshi ta faɗamin komai nasu da wasu sirrika na Alaji daga nan ni kuma zan ɗaukeshi sai tayi da gaske ma zata sake ganinshi...

Babu ko sallama ta faɗo cikin ɗakin daga ita sai ɗaurin gaba hijabinta riƙe a hannunta , Abbu Afsar ka tashi kenan ? Bai kalleta ba yace na tashi daga ina kike ne ? Kallona tayi sannan tace wallahi gidan Naja naje tace zata shigo bata samu damar shigowa ba kusan kwana biyu mijinta ya hanata fita shine nace ta bari ni nazo , kallonta Alaji yayi tare da cewa ita da bata raina mijinta ba ! Ya hanata ta hanu ke kuma da kika raina naki sai kika fita babu izini na.

Tsoki tayi tare da zama saman kujera tana cewa baka gajiya da tsegumi haba da Allah dan naje tou miye ? Murmushi nayi ina mai kallonta , gaskiya kyakkyawa ce sosai , ga kyawu har kyawu amma an kashe kyawun da ƙazanta , yarinyar mace kamar wannan tana zama da ɗaurin gaba , gashin hamatar ta kanshi idan kika kamashi zaki iya kitsashi saboda yawanshi , tana da haƙora masu kyau amma ta kashesu da rashin wankewa , kanta kuwa ƙaramar ƙarya kila yayi shekara rabonshi da a kwance , kitsone saman kan amma baka isa ka gane ta ina aka ɗauko tsagar kitson ba ,

Tou bamu dai gama maganarmu ba da Abbu Afsar Ummu Afsar ta shigo gidan , tsokin da tayi masa yasashi tashi ya fita daga ɗakin , ina kwana na gaisheta , ansawa tayi tare da fyace majina da gefen zaninta , sannan tace ban gane ki ba ,

Uhum ai baki sanni ba na faɗa ina sadda kai ƙasa cikin nuna mata ni ta gaskiya ce tunda nasha hijabi daga sama har ƙasa , kallona tayi sannan tace Allah sarki sannu da zuwa , ki dawo saman kujera mana !

Nan ma yayi na bata amsa , bara na kawo miki ruwa , tou na faɗa yayin data miƙe tabar palon , babu wani ɓata lokaci ta dawo da wasu irin haɗaɗɗin kulololi masu matuƙar kyau da tsada , ta wuce taje ta ajiyesu a saman tebirin cin abinci ,

Saida ta ajiye sannan tace bisimillah mana , ta faɗi maganar cikin sakin fuska , banyi magana ba na tashi na nufi tebirin cin abinci yayin da Wane Yaro ya zauna a wurin dana tashi ,

Kujera taja itama ta zauna kusa dani sannan muka sake gaisawa, ɗora hannuna nayi saman kular da take ƙoƙarin buɗewa nace suna na *Sultana* ɗiya ga Aliyu Muhammad Binna , Babana sananne ne kuma ya shahara a harkar caca , dani da Babana da kowa nawa muna zama a gidanmu cikin kwanciyar hankali , nazo wurinke dan gyara miki wani kuskure Allah dai yasa banyi shishshigi da yawa ba.....

"Yar gajeriyar dariya tayi sannan tace ke kuma me yace miki nayi masa ne ? Kallonta nayi sosai dan na fahimci yanayin rayuwar tata , bata da babbar ciwon dake damunta wanda ya wuce rashin ɗaukar shawara , tana da taurin kai sannan kuma abinda taga dama shi takeyi babu wanda ya isa ya sa tayi ko ta bari sai ciwon rashin wayau dake ɗawainiya da rayuwarta...

Kauda kaina nayi daga kallonta sannan nace ni bai faɗamin komai ba , gyara zama tayi tare da cewa baya da aiki sai kai ƙarata bana san wanka bana shara bana goge ɗaki ban iya girki ba , ban iya kwanciyar aure ba , cikin hayani tace yaje ya nemo wacce ta iya duk wannan abun dana lissafo ban iyaba ta ƙarasa maganar da dukan tebirin data ajiye kulolin da ƙarfi...

Cikin tsoro nace saurara kiyi haƙuri ba hayani ta kawoni ba , shin ko kina fama da matsalar rashin abinci ne ? Ko rashin sutura sabun wanka ko na wanki ? Rashin turare ko man wanke baki ? Cikin ɓacin rai tace babu abinda na nema na rasa dalili dai bazai yuwu ba kullum namiji yayi ta sussukata ni ba gero ba ,

Dariyar mugunta nayi mata tare dayi mata kallon wawiya , data riƙe mijinta ram a hannu da bai kallo matan waje ba , wannan ba matsalar Alaji bace itace ta kai mijinta ga halaka , na rasa abinda yake damun matan ƙarshen zamani , babu biyayyar aure ba ladabi mace ta mayar da mijinta kamar almajirin gidanta baida wani mutunci ko daraja a idonta....

Yake "yar uwata ki sani aure yana da babbar matsayi haka kuma namiji yake da babbar daraja , mijinki shine sirrinki suturarki aljannarki sai kin gyara rayuwar aurenki sannan zaki samu rayuwa mai daɗi a gidan duniya da ƙiyama dan miji ba abin wasa bane , mijinki ba abin wulaƙantawa ba ne sannan kuma mijinki ba abokin gabarki bane , abin ƙauna ne abun tausayawa ne a gareki , ki kwantar masa da hankalinsa sai Allah ya kwantar miki da naki , ki bashi natsuwa sai Allah yasa kema ki samu natsuwa , kisa mishi farin ciki sai Allah yasa kiyi farin ciki a gidan duniya da lahira....

Matan bariki suna da illa kuma suna tattare da masifun dasu ma kansu basu san suna dasu ba , bariki wuta ce mai azabar raɗaɗi da wahala , zina halakace kuma babbar cutace , me matan barike suke dashi wanda baku dashi ne ? Komai iri ɗaya ne abu ɗaya suke dashi wanda matan aure suka rasa , kuma suma matan auren suna da abu ɗaya wanda matan bariki basu da irinshi !

Wannan abu ba komai bane sai sakaci , shine abinda matan aure garesu , matan bariki kuma basu dashi , matan bariki basu da sakaci abinda matan aure suka rasa kenan...

Ummu Afsar

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment