Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

bai huta ba tou wannan miliyoyin kuɗin nashi ne shi zai lashe su , tou ai irin *DANBEN...* mijin Asma'u yakeyi, shine sana'arshi...

Haka nan naji raina ya ɓaci wato Dikko kallo yake zuwa shima shi yasa naji yana cewa Saminu a wurin wasan danbe ya haɗu da wata ya bita baisan matar aure bace ba ,

Cike da ɓacin rai na koma cikin gida , ina shiga ɗakina na ɗauki wayata na fara kiran lambar Dikko , na kirashi yafi sau a irga amma bai ɗauka ba , zuciyata tacemin yana can kallon Danbe , raina ɓace na koma ƙofar gida na ɗauki mota ta na ibi hanyar goruba road , dan nasan irin wannan lokacin suna can suna kallon kwallo , 10:29pm na isa , inayin horn aka buɗemin get na shige...

Motoci sunfi goma a harabar gidan , dama nabar wasu a waje ma , cike da ɓacin rai na sauko ko ganin gabana banayi na tun kari palon , ashe ina fitowa mota ya ganni dan haka ya taso da sauri dan ya tareni , a bakin ƙofa ya tsaya ya raba hannunwa shi ya tare ni , kwantar da kanshi saman kafaɗarshi ta dama yace An mata lafiya ?

Cikin ɓacin rai nace ashe kai ɗan iska ne , da sauri ya buɗe bakinshi cikin yanayi mamaki yace me kuma yayi zafi haka ? Nace ban sani ba , ɗan buɗe idanuwanshi yayi sosai yace tou ai kin bani dunƙule bansan abinda nayi miki ba , kince ni ɗan iska ne nace me akayi kuma kince baki sani ba ,

Rufe idanuwana nayi hawaye na zubowa nace ashe danben ranar nan da kake magana iskanci ne , dariya Dikko yayi tare da sauko hannayen shi daga inda ya ɗorasu , jan hannu na yayi muka koma cikin mota ta , bayan mun zauna yace waye ya faɗa miki ? Banyi munafinci ba na kwashe kaf na zayyanawa Dikko labarin da Nana ta bani , dariya yayi sosai yace tou ni bana zuwa kallon danbe ban taɓa zuwa ba , ina da labari dai kuma abinda yasa kikaji nayi maganar danben a waccan rana shi Saminun abokina ne , kuma shine ya kirani yake faɗamin abinda ya faru dashi , kuma nace kizo muje kikace baza ki ba , da wannan abun yasa kika taho ? Da Allah baisa na ganki na tareki ba da haka zaki zo ki ɓara maganar gaban mutane ?

Tou ni ban taɓa kallon danbe kowa ba sai nawa da naki , kuma ina addu'a ubangiji ya tabbatar min dake a matsayin mata ta naci gaba da miki kina alfahari dani , yanzu kin yadda kinajin soyayya ta ko ? Ya ƙarasa maganar yana leƙo fuskata , kauda kaina nayi saboda kunya , Dikko yace kinga kinyi kuka dan kina tunani DK n ki yana zuwa kallon danbe , ki kwantar da hankalinki Dikko naki ne ke ɗaya da izinin ubangiji , ni bana zarginki har abadan duniya anma dan Allah karki sake ki bari zuciya da sharrin shaiɗan yasa aimin wasan danbe dake , ni ɗaya tak na isheki bana gajiya kuma bazan taɓa gajiya dake ba har ƙarshen numfashi na ,

Kwantar da fuska ta nayi saman sitiyari nace to me yasa gwamnati baza ta hana wannan saɓon ba ? Dikko yace tou waye yasan sunayi ? Bayan sun ɓoye babu wanda yasan inda suke sai su kaɗai , muna tare dasu muna cuɗanya bamu sansu ba tunda ba rubutawa akeyi a jikin mutum ba , yanzu dani dake da muka ɓoye mukayi waye ya sani ? Babu wanda ya sani daga ni sai ke sai Allahn daya haliccemu kuma kullum ina neman ya gafarta min kuma ai kin yafemin An mata ko ?

Shiru nayi banyi magana ba , kallon agogon hannunshi yayi yace kizo ki tafi gida dare yayi ya ƙarasa maganar yana ƙoƙarin fita daga motar , nidai bana so ya tafi banƙi mun kwana muna magana ba , dan wallahi maganar Dikko daɗi gareta ga sa natsuwa wani irin harshe yake amfani dashi wurin magana nidai tunda nake ban taɓajin irin yanayin maganarshi ba , amma shi na lura baya san yana daɗewa tare dani , ƙara maido maganar baya nayi cewa ,

Tou baka san Saminu ba , yace An mata ƙungiya ce fa , kuma daga jin irin kuɗaɗen da ake zubawa ai kinsan ba talakawa bane ba , can matsalarsu suyi rayuwarsu muyi namu rayuwar manta da sha'anin wasan danbe kin fara so na yanzu ko ? Shiru nayi , yace tou nidai ina sanki kuma kullum saina faɗa ,

Maganar abokinshi naji yana cewa DK wace "yar yarinya ce ka ƙurmusa a mota ? Fita yayi yana cewa An mata ce zo ku gaisa da ita , a tadai zo ta gaisheni baka faɗa mata ni yayanka bane ? Ya ƙarasa maganar yana zama saman bayan mota , ba tare daya bashi ansa ba ya maidai fuskarshi kamar yadda take wato ya ɗaure tare da rufe murfin motana yana cewa Allah ya tsare hanya ,

Kunna mota ta nayi zan fita , gaba ɗaya mazan dake palon suka fito suna cewa mai gadi karka buɗe yau sai munga "yar matan da yake ɓoyewa , cikin ɓacin rai Dikko yace kai buɗe mata hanya ta wuce , da sauri ya fara ƙoƙarin buɗewa su kuma suna cewa idan ka bari ta fita bamu ganta ba wallahi ubanka zamuci , Dikko yace wai da Allah mi yasa kukeyin abu wani iri ? Koma ce mana kayi mahaukata wallahi sai mun ganta ,

Dikko yace ashe kuwa zakuyi kaffara , kallon mai gadin yayi cikin tsananin fushi yace na rantse da girman Allah ka buɗe get in nan idan kuma baka buɗe ba na rantse da wanda rayuwata ke hannunshi saina taka ka da mota in take ka mutu kamar ɓera kuma babu abinda za'ayi na kashe banza , sanin hali yafi sanin kama , da sauri ya buɗe get in duk zagin da ake mishi ni kuma na fice da da gudu...

Sultana tana fita sukayi kanshi suna zagi dan ubanka ba cewa mukayi karka buɗe mata ba ? Mu da bama bi takanka da mota ko ? Faffala mishi mari kowa yayi sannan suka bi bayan Dikko daya koma palo ya kira Sultana yace karta sake zuwa idan tana san ganinshi zaizo ya sameta ko tana ina , tace insha Allah , bayan ya gama wayar yace hmm An mata ta rainani , bata ganin girmana ko kaɗan , tacemin ɗan iska munafiki hada mari , idanma ban auri yarinyar nan ba ai ta gama dani duk lokacin data ganni tana min kallon sakarai na nasha dakai , duk borinki na waje ne bari dai in lallaɓaki kizo hannu zaki gane ruwa ba sa'ar kwando bane...

Saida na biya ta majalissa akacemin Babana sun tafi wasan caca , raina ya ɓaci naji banji daɗi ba ace daga fara fitowarshi harya fara zuwa caca , ƙaraurawar kaina ta buga dan haka na manta da ɓacin rai nayi gida abina...

Washe gari ranar asabar tunda safe Mamy tazo gidanmu , kuma har yanzu Babana bai dawo ba , da murna na tareta muka shige ɗaki abunmu , bayan mun gaisa ta tambayeni na tuno abinda zan faɗa mata ranar laraba data zo ? Nace mata Eh , wayar na ɗauko na bata nayi mata dukkan bayani amma ban faɗa mata Dikko bane ba ,

Layin kawai ta cire daga cikin wayar ta bani wayar ta saka layin a jaka , nace da Allah Mamy wai da gaske kina da aure ? Tace ina da aure Sultana , nace keko me yaja miki bin mazan waje ? Bayan ga naki a gida ? Naga wasu ma basu samun ƙoshi ɗaya a bayan wasu shekaru { wanda basu da mazaje , basu da masu kwantar musu ko sauke musu sha'awarsu } kuma sunayin haƙuri keko naga kamar kin girtse da yawa...

Kici abincin gidanku kuma kici na gidan wasu , murmushi Mamy tayi tare da cewa aike yarinya ce bakya gane inda aka dosa gashi kuma kwalwarki tana tafiyar ɗimuwar rabin sa'a , murmushi nayi tare da cewa gaskiya ne inajin ƙaraurawar hauka tana bugamin duk bayan wasu "yan mintuka , Mamy tace da yanda idanuwanki da zuciyarki suke ganewa haka kanki ke ja da anyi alfahari dake , kauda kaina nayi gefe nace kwantar da hankalinki ina da ayyuka ne a gabana amma nasan komai zai warware ,

Mamy tace Allah yasa , zatayi magana kiran Hafsa ya shigo wayarta , ɗauka tayi tare da cewa Hafsa ya jiki cikin murna Hafsa tace Aunty ai jiki ya warke matar Dikko ta mutu , shegiya an gaji da ƙwaƙwar duniya an tafi anya mayyar matar nan baza tayowa mutane fatalwa ba ,

Mamy tace innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , ke waye ya faɗa miki ne ? Tace Mom ina taje ganinta safiyar nan tana can ma ta rasu amma tace Dikko yaji mutuwar saboda yana zaune kusa da ita tana bashi labarin abinda ya faru da ita bata gama bashi labarin ba ta zuge gilashi ta kama gabanta ,

Tou Allah ya jiƙanta ubangiji yasa mu cika da imani ya kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo amin , Hafsa tace yanzu tashin hankalina kuma ɗaya kinaji saura sati ɗaya a daura mishi aure , Mamy tace Hafsa bari anjima zamuyi magana , tana faɗin haka ta kashe wayarta ,

Wayoyin mutane ta fara kira tana tambayar da gaske ne matar Dikko ta rasu ? Abunka da masu jaha magana ta karaɗe kaf gari , kowa Mamy ta tambaya sai yace mata Eh ta rasu , kallona Mamy tayi tace kodai maganar mutane ta tabbata ? Nace me mutanen suke cewa ne ? Ƙasa² da murya tace kinsan kuɗin gwamna suna firgita al'ummar , ɗanshi kuma ya taso da ƙarfin dukiyar da ubanshi kanshi abun tsoro yake bashi ,

Anyi itifaƙi kaf gwamnonin nigeria babu mai kuɗinshi , danshi tunin duniya dama yayi kuɗinshi ba'a siyasa ya samesu ba , siyasa daya shiga kawai neman suna yasa ya shigeta amma badai kuɗi ba , to shi kanshi daya haifi Dikkon yana tsoron dukiyar shi , mutane cewa akayi wai ɗan nashi matsafi ne , dama tunda matarshi ta fara rashin lafiya akace ya tsafeta mutuwa zatayi ,

Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji , yayin da zuciyata tace ki rufe idonki ko sau ɗaya ne kiyiwa Dikko adalci Sultana , rufe idona nayi gaba ɗaya a halin Dikko babu ɗaya na zaɓe , Mamy tace da zan baki labari amma gaskiya tashi zanyi na sake dawowa , nace tou , har ƙofar gida nayi mata rakiya saida ta tafi na dawo gida ,

Tunda Mamy ta tafi nake saƙawa nake warware , me yasa Dikko ya zaɓi tsafi ? Me zaiyi da kuɗi dattin duniya da za'a koma ga Allah a barsu a duniya ? Tsikar jikina sai tashi takeyi ,

Har akayi kwana bakwai da mutuwar Sadiya ban daina tunanin maganar nan ba , Dikko kuwa ya kirani har bansan adadin kiran ba amma naƙi ɗaukar waya , daga ƙarshe ma kashe wayar nayi gaba ɗaya ,

Marecen yau kuwa ina ƙofar gida duk abin duniya ya dameni na rasa ina zan saka rayuwata naji sanyi , tunani ya dameni na babu gaira babu dalili , tsayuwar mota a gabana tasa na ɗago kaina da sauri dan a tunani na Baba ne , Dikko ne dan haka na tashi da sauri a daidai lokacin daya sauko daga saman mota , yana fitowa na taga ƙafa ina ƙoƙarin rugawa , a zuciyata nace an cuci sunna gaskiya ga gemu ga tambarin sallah wallahi ka ɓata kyanka ,

Ya kusa isowa inda nake na ruga da gudu ina wayyo Allahna......



29/09/2019




*JAMILA MUSA....* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 45



Tsaye yayi yana kallona , ni kuma da gudu nayi cikin gida har na kusa faɗuwa , a mamakince Dikko yabi Sultana da kallo a ranshi yana cewa ko lafiya ?

Mota ya koma ya gyara parking , yayi zamanshi ciki bai fito ba ranshi ɗauke da tunani daban ² , ga zafin mutuwar matarshi ga ciwon auren da za'a ɗaura mishi wanda rasuwar Sadiya yasa aka ɗageshi , ga iyayenshi sam² sun rufe idanuwansu akan aurenshi da Sultana...

Ya ɗan rame har yayi duhu saboda damuwa da tunani , a gajiye ya fito daga cikin motar ya nufi gidanshi , kafin ya ida shiga Baban Sultana ya faka tashi motar daga can gefe dan kar yayiwa Dikko laifi...

Dikko yana ganinshi ya dawo suka gaisa , bayan gaisuwa yace am dama ina san ganin wannan yarinyar ne , cikin damuwa Baba yace ta sake janka ne ? Fuska dai a murtuke babu fara'a yace a , a zanyi magana da ita ne kawai !

Baba yace tou Allah dai yasa lafiya , a ɗan rashin jin daɗi Dikko yace ba komai fa , shi baya so yayi ta nanata magana kuma anajinsa amma a kasa fahimta ,

Cikin gida Baba ya nufo zuciyarshi cike da damuwa , tunda ya shigo gida yake kwalamin kira kamar ranshi zai fita daga jin yanayin maganarshi babu daɗi a zuciyarshi ,

Da gudu na fito ina tambayar Baba lafiya , cikin faɗa yace me ya sake haɗaki shiga sabgar yaron can mara mutunci kuma ? Ɗan iskan yaro da baya ganin kowa da mutunci , ya raina arziƙin duk wani mai farin gashi dake doron ƙasar nan , fitinanne yaro dako bakin duniya baya tsoro ga rashin mutunci da masifa kamar kishiyar ɓarauniya...

A ruɗe nace ni babu komai , dakamin tsawa Baba yayi yana cewa babu komai inji waye ? Gashi can ya kafe mota ƙofar gida yana ɓacin rai duk abinda nace bana so sai kinyi Mamana kina so dai ki samin ɓacin rai idan na mutu kin huta ,

Hannuwa na duka biyu na ɗaga alamar bada haƙuri nace a , a Babana kayi haƙuri don Allah , dan bana so naga Baba yana fushi akan komai bare kuma ni daya ɗauki soyayyar duniya ya ɗoramin ,

Sassauta murya yayi cikin tausayi yace tou kije ki bashi haƙuri nidai bana so kina jawoshi faɗa uwar masu gida , nace tou Baba , a tsorace na fita ƙofar gida gabana sai faɗuwa yakeyi ,

Dikko yana tsaye ya jingina da mota , da gudu na isa inda yake na riƙe hannayen shi , na irin gani karka kasheni , kallona yayi cikin sigar so da ƙauna yace tou kin kama min hannaye ai gara ki riƙeni gaba ɗayana tunda abin har yakai ga riƙe hannu ,

Sakin hannuwan nashi nayi na ɗaga kaina na kallo cikin kwayar idonshi , wani irin kallo yayi min kwayar idonshi tana motsawa a hankali wanda idan baka iya saka ido ba baka gane motsi takeyi ,

Hmmm me yasa kika gudu da kika ganni ? Ko na zama dodo ? Bansan abinda yasa bana iya ma Dikko ƙarya ba amma da nauhi wannan kalma mai muni ta fito daga bakina ,

Tou tunda baki da abun faɗa ni zan faɗa nawa , shiru nayi ina saurarenshi , yace zanyi tafiya kuma bana tunanin idan na tafi zan dawo yanzu , bana so na shiga haƙƙinki da yawa dan ina baƙin ciki kiyi damuwa a rayuwa , ina so miki farin ciki bana so kiyi kuka haka kuma bana so ki kasance cikin damuwa ko ƙunci ,

Na baki daga yau zuwa jibi kwana biyu kenan ko ? Ya tambayeni , ina kallonshi banyi magana ba , yace tou kije ki natsu kiyi sharawa da zuciyarki shin kina so na ko bakya so na ?

Cikin yarinta nace ni bama sai nayi shawara ba gaskiya bana sanka , kallona yayi sosai yace karkiyi ƙarya An mata zakiyi nadamar hakan wata rana , nace wai ni ? Na ƙarasa maganar ina masa kallon rainin wayau nace Allah ya sawaƙemin ai baka cikin tsarin mazan da nake so , cikin damuwa yace .

Kina da matsaloli fa daban ² An mata , saurara samar da farin ciki a domin ɓatawa wani ba dai² bane , haka zafin murmushi a yayin da wani yake baƙin ciki da takaici hmm baya da amfani , karki damu kawai cewa zakiyi ina sanka , shi kenan fa babu wani wahala , uhum kana ba kanka wahala kaji , ince ina sanka ? Allah ya sawaƙemin ,

Murmushi Dikko yayi maicin rai yace tou ni kuma na san a cikin kwanaki biyu da wannan taurarin idanuwan naki zaki zamo masoyiyata babu jayayya , zaki zo ki rumgumeni , numfashinki zai shiga kwalwata, zaki kalli idanuwana , ina sanka , idan har baki faɗa kina so na ba , shiru yayi yana kallon fuskata , zuwa wani lokaci yace sai kin faɗa , yana faɗin haka yayi tafiyarshi ya barni a wurin...

Cike da damuwa na koma gida yayin da zuciyata ke shawarta ta ince ina san Dikko wata zuciyar tace karki sake ki faɗa ko zaki mutu ki barshi kawai kuje a haka , kina mace kice kina san namiji haba ai kinci ƙasa ,

Lokacin da kwana biyu ya cika zuciyata ta gama tabbatarmin da bata san Dikko , dan haka kuma na yanke shawarar sanar dashi bana sansa yayi haƙuri ,

Da daddare bayan yazo ya aiko aka kirani dan har yanzu ban kunna wayar ba tunda na kashe ta ban sake buɗewa ba , bayan na fita muka gaisa dashi , bayan gaisuwa yace ina saurarenki , nace gaskiya ansar dana baka tun farko itace har yanzu ,

Shiru Dikko yayi , bayan wani lokaci yace , wannan rana ta kasance min ranar juyayi ne , bana fatan wannan ranar ta sake zomin , ranar ƙarshe kenan banda wani ƙwarin guiwa , An mata ce kaɗai abin alfaharina , umm abinda bana so ya kasance duk lokacin dana runtse idanuwana nakan iya ganin kyakkyawar fuskarki , bansan mace ba sai a kanki idan har na taɓa san wata mace a rayuwata to kece An mata ,

Zan tafi idan har naci gaba da ganinki to zan ɓata miki , kiyi haƙuri bazan sake kiranki ba , haka ma zuwa ba zaki sake ganina ba An mata , kin daɗe kina ƙonani inajin kamar na rasa wani abu , me zanyi ? Bazan iya koda dariyar ƙarya ba , jawoni yayi ya rumgumeni duƙowa yayi ya kwantar da kanshi saman kafaɗa ta , cikin wata irin murya mai tsayawa a zuciya yace sai wata rana , ki yafemin don Allah karki riƙeni zan fita daga rayuwarki dan ina so kiyi farin ciki , zan tafi ki huta koda kuwa ni zan shiga halin damuwa ,

Bayan wani lokaci ya ɗago ya kalleni , cikin kallonshi mai ɗaukar hankali yaɗan ɗauki lokaci yana kallona sannan yazo dai² bakina lumfashin shi yana fitowa saman fuskata , gashin gemunshi yana shafar dai² saitin bakina , lokaci guda jikina ya canja tsikar jikina ta tashi ban taɓa jin irin wannan yanayi ba , bafa haɗa bakinmu yayi ba , daga waje ya sunbace ni wani abu naji ya shiga jikina da gudu saida ya gama zagayawa ya dawo zuciyata ya shiga da ƙarfi , ajiyar zuciya na sauke yanajin nayi ajiyar zuciya ya sakeni da sauri daga jikinshi yaɗan turani baya yace ki tsaya da kyau karki faɗi , zan bada saƙo Umar ya kawo miki kafin in wuce ,

Kasa magana nayi nabi shi da kallo da sauri ya shiga mota ya bar ƙofar gidanmu da gudu , har ya fita daga anguwarmu ina tsaye a wurin daya barni , yana ɓacewa na kyalkyale da dariya , na zabgaga wani irin ihu , daga cikin gidanmu Zainab ta fito da gudu tana tambayata lafiya ?

Sai dire² nakeyi kamar anyi ma doki allura ƙarfi , Zainab tace wai miye yake faruwa haka ? Goge hawaye nayi nace har yanzu na kasa yadda da wannan , Zainab tace miye ne kika kasa yadda dashi ? Nace masoyina ya faɗamin dukkan na kasunsa , shi da yace zan rungumesa sannan na faɗa masa cewa ina sanka DK ,

Zainab tace waye DK murmushi nayi nace baki sansa ba , Zainab tace tou ki faɗa masa kina sansa mana , nace ke jinan ya nunamin yatsansa yayin da yake ƙalubalanta ta cewa a cikin wasu kwanaki zance ina sansa , murmushi nayi tare da rufe idona , nace kamar dai yadda yace naji ina sansa , ƙara ɗaga murya nayi ina sanka mutumi na , ina sanka , Zainab tace to me yasa baki faɗa a gabansa ba ? A , a , a , a , idan na faɗa masa tou zaiyi ta jamin ƙafane har abada , Zainab tace zakiyi duk abinda kike so amma kuma idan kika makara a soyayyarshi fa ? Nace sam ² ki rabu dashi kawai yayi kuka na wannan daren nasan bazaiyi zuciya ba da safe zai sake zuwa , ni kuma yana zuwa zance barka dai DK idan ba tare dakai ba ina ne zanje .....?

Cike da farin ciki na shiga gida , Zainab ta rufomin baya , alwallah nayi na shige cikin ɗakina ina farin ciki ,

Dikko kuwa yana isa gidanshi wanka yayi , bayan ya shirya ya ɗan faffaka abu mai mahimmanci ba kaya ya ɗauka ba , wasu takaddu ne kawai ya tattara , layinshi ya cire ya ajiye , dube² yayi na irin banyi mantuwa ba kuwa ? Sannan ya fita daga cikin ɗakin ,

Wajen da aka tanada dan ajiye motoci ya samu Umar kamar yadda yace su haɗu , Ashiru a gefe sai Al ' Ameen , duk gaisheshi sukayi cikin girmamawa , bai ansa ba , makullin mota ya miƙewa Umar tare da nuna mishi mota yace ka kaima yarinyar nan akwai kuɗi a but in tasha mai , Umar yace mai gida wace yarinya ? Yarinya nawa kasan ina tare da ita ? Haƙuri ya bashi tare da cewa tou ai naji bakace An mata ba , murmushin baƙin
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

6 months ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment