Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nuna masa bana buƙatar hakan ,

Ina shiga gida ɗakina na shige , saida na kwanta sannan naci gaba da tunanin Dikko , inayi ina hawayen baƙin ciki naci gaba kuma da kiran layinshi , har na gaji nayi bacci....

Washe garin ranar kuwa tunda safe Maman Sadiq da Ummu Affan a gidanmu suka bayyana , lokacin ko baccin safe ban tashi ba , dan tunda nayi sallah asuba na koma bacci , zuwansu ya tasheni , saida na fita na wanko fuskata da bakina sannan nazo muka gaisa dasu , bayan gaisuwa Maman Sadiq ta fara cewa dama cewa nayi bari muzo muji yaushe ne taron ?

Shiru nayi tare da tsaresu da idanuwa dukansu , bayan na gama fahimtar wani abu daga garesu nace gaskiya shugaban ƙungiyar munyi magana dashi yacemin in ƙyaleku danshi baya san azo a samu matsala dan basaso a ɓatawa siyasar su suna , matan aure basa iya basu gudumawa yadda ya kamata akwai matsalar mijina yace karna fita , ko kuma ina zan bar yarana ? Ko kuma ni bana zuwa hotel ko kuma inane za'ayi taron ?

Saboda jiya bayan na rabu daku naje wurinshi nayi masa bayani yadda mukayi daku bayan na nemi alfarma dan yaɗan ƙara muku wani abu saboda na lura iyali sunyi muku yawa gashi babu wata sahihiyar sana'a kuma yaran naku duk basu kawo ƙarfi ba , na samu dai yayi muku ƙarin budu goma tunda kune shuwagabannin ƙungiya ,

Sai yace na kawo mishi shugabar ƙungiyar ya gani shine nace ai matar aure ce , kinji faɗa ? Yace mi yasa kika naɗamin shugabar ƙungiya matar aure ? Bayan kinsan meeting na gaggawa zai iya tashi na kirata tacemin bata shirya ba ? Nidai ki mayar min da budurwa ko zawara , dakel dai na bashi haƙuri yace min ai matsalar matar aure wai kina iya zuwa kice aike bakya zama wuri ɗaya da mijin da ba naki ba , bayan dole zaku riƙa ɗan warewa ku tattauna abinda ya shafi ƙungiya ,

Ummu Affan taji zance kuɗi dan haka tace anyi ma aikin kishiya bare na uwar miji ? Daga magana sai mi kuma ? Nace kinsan wayayin maza basa so ayi ta wani dunkumewa a hijabi kinsan "yan boko basa san suga ana sha''ani da hijabi ,

Tacemin ai bansan wurin taron ko za'a nuna a talabijin ba , nace a , a ba'a sakawa a TV , Maman Sadiq tace tou Sultana ai sai mu tafi tare kice nice matemakiyar Ummu Affan , nace kibi sannu duk za'aje da kowa , tace a , a abari ya huce fa shine ke kawo rabon wani , nace aiko bai hucen ba idan rabon wani ya shiga tun yana kan wutar wani zaizo , kinga kuwa ai dole zakuci tare ko ? Tace haka fa , nace tou kudaije ku sake tunani shin zaku iya huɗɗa da maza ? Dan duk zama ɗaya ko wace zata tashi da dubu ishirin idan kuma gwamna yazo ko wace tana da dubu talatin idan kuma kin iya gogayya da maza zama ɗaya ma da hamsin zaki tashi ,

Zasu sake magana wayar Mamy ta shigo , nace tou anyi ma sa'a ga shugaban nan yana kirana ku jira muji me zaice ne ? Ɗaukar wayar nayi bayan mun gaisa da Mamy tacemin in shirya gata nan zata taho , nace tou , sai nace yawwa Alhaji maganar matan auren nan ina dai ƙara baka haƙuri yanzu haka ma muna tare dasu kuma sunyi alƙawari babu wata matsala , shiru nayi bayan wani lokaci nace dubu ɗari da keken ɗinki ? Allah ya ƙara arziƙi wallahi godiya suke , kallon juna sukayi suka ƙyarawa junansu ido , ni kuma na sake shiru bayan wani lokaci kuma nace kai Alhaji dani da ita zamuje har a gaban mai girma gwamna ? Tou muna godiya sai munzo goben , nagode ׳ , yawwa sai anjima na kashe wayata , Mamy kuwa cewa tayi kai wannan yarinya batajin magana ,

Ummu Affan har sauri take wurin cewa wai waye za'a ba keken ɗinkin da dubu ɗari ? Nace shugabar ƙungiya wai cewa yayi idan Allah ya kaimu gobe duk shuwagabanni zamuyi zama da mai girma gwamna shin zaki samu damar zuwa ko kuwa yadai ?

Tace zuwa ma kai zanje , nace tou kidaiyi shiga mai kyau dan kinsan shiga gidan gwamnati bana yara bane , kiyi wanka ki ɗauro kallabi ƙarshen layi kizo muje amma kuyi shiru da bakinku karku sake ku bari wani yaji idan ba haka ba "yan zidaƙuiy zasu zo su anshe ma ɗan tama doki , Ummu Affan tace haba wallahi bama faɗa , nace tou yayi kuje sai mun haɗu goben , Maman Sadiq tace ai wallahi baku bari na wannan ai baƙin ciki ne taya ni na rakaki gidanta kuma a gabana aka haɗa komai sai ku tafi gidan gwamnati ku barni dan baƙin ciki ? Nace kema hada ke za'aje , tace tou yanzu naji magana , murmushi nayi tare da cewa kuje zan shiga wanka ,

Maman Sadiq ce ta fara fita ɗakin dan haka na riƙo hijabin Ummu Affan nace karki faɗa mata ƙarfe biyu na rana zamu tafi , idan ba haka ba keken ɗinkin nan da dubu ɗari tare zaku rabasu , tace bazan faɗa nace tou ku gaida gida ,

Kwando na ɗauka naje nayi wanka , bayan na fito na fara shiri ina saka kaya Mamy ta iso , bayan mun gaisa nake bata labarin yadda mukayi da matan aure , na ƙara da cewa kinga goben idan mukaje sai muyi ta zama ace gwamna yana meeting , ni kuma ina ci gaba da gyara hanya cikin sauran kwana shiddar daya rage har an kaita an baro ta ,

Mamy tace gaskiya ne , nace tou shi mutumin saiki faɗa masa idan munje muka tashi tafiya ya bata dubu hamsin kinsan ita mace da kuɗi ake tafiya da imaninta , Mamy tace haka ne karki samu damuwa nace dama banda ita ,

Bayan na gama shiri na ɗauki jakata da abinda nake shafawa mutane su tafi bacci , saida muka fita ƙofar gida nake tambayar Mamy ko Al ' Ameen ya turo lambar yarinyar ? Tace yace babu waya a hannunta sai dai ta Mamanta take amfani dashi kuma ya turo nace shikenan magana ya ƙare mata tacewa mijinta shege..........





02/10/2019





*JAMILA MUSA....* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 48


Ni naja motar muka tafi Mamy kuma tana gefe na tana waya , dama ta shigo tanayin abunta kuma har yanzu bata gama ba , hanya na iba ɗoɗar saboda ta nunamin hanyar da zanbi da hannunta ta kuma nunamin kawai in tafi miƙe kar in kwanta ,

Munyi tafiya mai nisan gaske sannan Mamy ta gama waya , sawa tayi nayi parking ta anshi tuƙin motar mukaci gaba da tafiya har muka iso inda muka zo Mamy bata sake magana ba ,

Get in gidan buɗe yake dan haka muma muka samu damar antayawa daga ciki , tun kafin Mamy tayi parking Allah ya nunamin Al ' Ameen , haka nan naji gabana ya yanke ya faɗi gaba ɗaya sai guyawuna sukayi sanyi nama kasa fitowa daga cikin motar , ni kaɗai nasan Al 'Ameen Mamy bata sanshi ba , sannan kuma numbershi da ta saka a whatsapp inshi ba shine ba Dikko ne ,

Dogon nazari na shiga to me ya kawo Al ' Ameen wurin nan kuma ?Tunani nayi sosai firata da Mamy ta daren jiya ta dawo min , to duk yadda akayi yarinyar da mukayi faɗa da ita kenan tana da alaƙa da Al ' Ameen ? Na shiga tunani sosai amma na kasa fahimtar ya abun yake ,

Mamy kuma fita tayi daga motar tabar harabar gidan ta koma ƙofar gida , bayan wani lokaci kuma ta dawo ita da wata matashiyar yarinya shekarunta da kamanunta duk bana iya ganewa saboda ta saka niƙaf ta lulluɓe fuskata , ciki suka wuce ta barni zaune a mota kamar mage na dakon tsuntsu ,

Shiru² babu Mamy ba labarinta , ni kuwa sai sassada kai nake ƙasa dan bana so Al ' Ameen ya ganni , gashi ina so na fita nima na shiga amma dole banda yadda zanyi saboda Al ' Ameen zaune yake kuma baida alamar tashi ,

Har su Mamy suka gaji da daɗewarsu suka fito , yarinya bata shigo motarmu ba ficewa tayi Mamy kuma ta shigo mota taja muka tafi , saida mukayi nisa nace mata wai mutumin dake zaune a wurin nan shi kuma waye ? Ko gadi aka sashi ne ? Mamy tace ƙanin matar Baban yarinyar ne , jinjina kaina nayi sannan nace tou wace ce da niƙaf kuma ? Tace "yar uwarki ce da kika ce na farauto ,

Nace Hamida ? Tace ɗiyar ƙanin Babanki ce , dariya nayi sosai nace tsakaninki da Allah tace wallahi kuwa , tou ya akayi kika farauto ta da wuri haka ?

Mamy tace wallahi ina zaune gidana Allah ya kawo minsu ita da ƙanwata , ashe ita ɗiyar ƙanin baban naki aure zatayi ? Mamy ta tambayeni nace mata Eh Safiyya ce zatayi aure , Mamy tace to ai kinsan "yan matan zamani sun saka kansu ƙarya basa haƙuri da abinda iyayensu sukayi musu , basa da gashin wance sai suce dole zasuyi kitso irin nata ,

Ƙanwata tacemin tana naima wa ƙawarta aiki a ƙarƙashi na , na taimaka wannan ƙawarta ce zatayi aure iyayenta basuyi mata wani abun kirki ba na kayan ɗaki , shine ta kawota wurina ko zan taimaka na ɗauketa aiki ita kawai talabinjin in bango da kayan sautin ta take so ta siya sai labulaye masu tsada ta gyara palon ta dan bata so ƙawayenta su raina mata gidan aurenta ,

Saina tambaye su bikin kwana nawa ya rage ? Shine tacemin wata 3 nace tou yarinya banda abinki wata3 taya zaki samu kuɗin da zaki sayi talabinjin in bango da kayan sautinta ? Kona ɗaukeki aiki na baki kuɗi da yawa a wata baifi na baki albashin 3k ba , kinga 3k sau wata3 ya kama 9k ba talabinjin ba ko labule bazai siya miki ba ,

Tacemin haka ne , tou bayan nayi bincike naji daga inda ta fito kuma naga kina nemansu da karuwanci ruwa ajallo yasa nayi mata tayin karuwanci bayan munyi ciniki dashi baban ƙawar faɗan taki akan zai bayar da dubu hamsin , nayi ² ya ƙara wani abu akai umm lusarin a haka ya tsaya , bayan mun gama ciniki dashi ya kafe kai da fata haka zai bayar ,

Kodai yane tunda na samu an farketa shikenan kinga ta tsaya zaman jiran talabinjin dan ubanta saidai kawai taji a salansa tamin hauka akan na bata kuɗi ga vidio na ɗauko ta ƙarasa maganar tana dariya , nima dariyar nayi tare da cewa yaro inya iya ruwa ai bai iya laka ba , dariya Mamy tayi sosai tare da tambayata meye ruwan kuma miye lakar ? Nace zancen sai wanda ya kwana a bakin gabi.... Mamy tace ina ne gabi kuma ? Nace wata matattara ce ta karuwai dake can wajen gari !

Haka dai mukayi ta taɓa fira har muka iso ƙofar gidanmu , bayan Mamy tayi parking ta fara kiran wayar Maman budurwar Dikko da mukayi faɗa da ita wacce bayan an ɗauki wayar naji Mamy tana cewa da Allah Momy ko Mardiyya tana kusa ne ? Eh tana nan Mardiyya kizo anyi miki waya ,

Tazo ta anshi wayar , bayan gaisuwa Mamy tace mata kin gane ɗiyar ɗan caca wacce kukayi faɗa da ita a motar saurayinki akan haryar ku ta zuwa Abuja ? Wacce bayan kunyi faɗan tayi zuciya ta barku a hanya ta samu mota ta dawo katsina kin tuna har kikace mata jahila daƙiƙiya kidahuma jaka kin tunota ? Tace Eh na ganeta ya akayi ne ? Mamy tace yawwa dama cewa tayi ki riƙe wayar Mamanki a hannu ki duba ta whatsapp zata turo miki saƙon ta tashi daga jahila ta koma ma... Da sauri na anshi wayar daga hannun Mamy nace.

Mai ilimi barka da tsakiyar rana , barka dai ta amsa a daƙile , nace suna na *SULTANA ALIYU MUHAMMAD BINNA...* ina miki albishir da mummunan gani , salona ne yin albishir da mummuna ga abokin gaba sai kuma nayi albishiri da kyakkyawa ga masoyina , idan baki manta ba a waccan ranar nace mutuwa kaɗai zaki ki huta da ganin baƙin cikina , tou yanzu muka fara ki fara yininki da wannan anjima ma zan turo miki na kwanciya bacci kisha kallo lafiya...... Gashi nan zuwa , ki gani ke ɗaya idan uwarki ta buƙaci gani itama ki bata ta gani muna da maganin ciwon zuciya na hausa idan kina buƙata kallon Mamy nayi tare dayin dariya nace masu magani kasuwa ta buɗe ....

Ina faɗin haka na kashe wayar , Mamy kuma ta ansa ta tura vidion data ɗauko kuma hada Safiyya a cikin hoton tana ta kwarara ihu saboda azaba yayin da Baban Mardiyya ke kwarara wani irin gurnani kamar kura tayo kamu , na raka vidion da voice note cewa mi yasa ya faɗa ruwa bai iya iyo ba ?

Dariya mukayi dukanmu , saida muka tabbatar an buɗe saƙon kuma ya ɗauki lokacin da ya isa Mardiyya ta gama gani sannan naba Mamy Umarni data goge shi daga wayar mamanta , wato ta saka delete 4 everyone , bayan an goge duka hada voice note in da nayi nasa Mamy ta rubuta cewa ta kawo kuɗi masu yawa sai mu goge idan kuma ba haka ba ta tara a tashar yanar giza gizo.

Bayan mun gama nayi sallama da Mamy na wuce gida akan sai mun haɗu gobe idan Allah ya kaimu , tace Allah ya kaimu lafiya , a gajiye na shiga gida dan haka ruwa na watsa kawai nayi sallar la'asar na kwanta ina hutawa.

A ɓangaren Ummu Affan da Maman Sadiq kuwa fitarsu suka yanke shawara cewa idan na kaisu so ɗaya bazasu sake tafiya dani ba dan abinda suka fahimta zan riƙa ci musu aljihu , ma'ana idan aka basu zan riƙa ragewa ni inci da yawa su abasu kaɗai , ummm kuji ɗan adam butulu ,

Yayin da Maman Sadiq ke bayar da shawara cewa suyi wayau muna zuwa su lallaɓa su anshi lambar shugaban ƙungiyar sai suce masa idan ana taro ko yana nemansu karya kira Sultana ya nemesu kai tsaye , Ummu Affan tace gaskiya haka ne , dan kinga idan aka bamu dubu ɗari zata saka rai a cikin kuɗin ta, ga, tunda itace ta haɗani dashi zata jira na bata wani abu a cikin kuɗin , Maman Sadiq tace haka ne , ai tana nuna mana hanya mun gama da banzar , haka dai suka yanke shawarar su ,

Bayan sun rabu kuma kowa ya yanke shawarar saiya koro abokin tafiyarshi dan kowa yaci shi ɗaya , yayin da Maman Sadiq take tunani idan gwamnati ta bada mai da sabulu da magi da rigunan siyasa da ake rabawa zatayi samayya fiye da tunanin mai tunani ,

Itama a ɓangaren Ummu Affan haka ne dan har ta kasafa dubu ɗari yadda zata kaya mata tun kafin akai inda za'aje har sun yada Sultana a gefe , Ummu Affan ma tana tunanin yadda zata yada Maman Sadiq yayin da itama Maman Sadiq in take tunanin yadda zata kora Ummu Affan taci ita ɗaya ba tare data samu mai tayata ba.

Washe gari kuwa tun 7:22am Ummu Affan ta bayyana a gidanmu , tasha wanka ta ɗauko jagira irin ta zamani sai baɗa ƙamshi takeyi anci jaka da takalmi masu kyau ta ida rufe wankan da wani irin tsadajjen gyale tayi kyau fa abunta ,

Tana zuwa ta ganni ban shirya ba , tacemin da Allah muje kafin wacce mayyar tazo , nace tun yanzu ? Tace Eh na samu na ajiye yaran a maƙota muje mu dawo , nace tou ki bari itama Maman Sadiq in tazo basai mu tafi tare ba ? Tace nidai karmu jirata da Allah ki tashi mu tafi , nace tou yanzu gwamna ma kanshi ai bai tashi bacci ba , tace haba ai da a jiraka gara kai ka jira , dan Allah ki tashi mu tafi , nace kai gaskiya ni ko shara banyi ba , kuma ban wanka ba , tace jeki kiyi wankan ni kuma sai in tattara miki ɗakin kafin ki fito , nace to amma mi yasa bakya so aje da Maman Sadiq , na tambayeta ? Danni dama bana so aje da ita ,

Ummu Affan tace kinsan mutanenmu da baƙin ciki sai kaja mutum inuwa ƙarshe kuma yakai ka rana , nace tou ba aminiyarki bace ba ? Tace wa ni ? Ta nuna kanta sannan taci gaba da cewa ba aminiyata bace ba kawai dai muna gaisawa cikin anguwa , nace tou ina kika cewa mijinki zakije da wannan safiyar ?

Saida tayi murmushi tace tambaya kamar "yar jarida , ce masa nayi ƙawata bata lafiya za'a tafi da ita asibitin zariya zanje na dubata kafin su tafi , nace to misali idan mukaje bamu samu ganin gwamna ba fa sai akace gwamna abubuwa sun mishi yawa mu dawo gobe tou sai muka dawo idan zaki fita goben sai mijinki yace baza ki fita ba tou ya zakayi ?

Tace ina ai dabara ma bazata ƙare ba , idan yace bazan je ba nasan hanyar da zan biyo masa , nace Allah ya taimaka ina faɗin haka nayi waje dan inje inyi wanka , kafin in fito wankan ta share ɗakin tas ta goge shi ta shinfiɗamin zani a katifa , ina fito na shirya a gaggauce ko kalaci banyi ba muka bar gidan kafin Maman Sadiq tazo.

A napep muka je gidan Mamy , a ƙofar gida muka same ta cikin motar wani namiji ga kuma wanda ta nunamin da sunan mijinta yana zaune saman dakali yana kallon ikon Allah , gaisawa mukayi dashi na umarci Ummu Affan da ta shiga ciki na nuna mata gidan tare da cewa shiga muna zuwa ,

Tana shiga ni kuma nayi wurin Mamy muka gaisa na gaishe da baƙon nata , bayan mun gama gaisawa Mamy tacemin in shigo mana , baya na buɗe na shiga bayan na zauna muka ƙara gaisawa ,

Shiru na wani lokaci sannan Mamy tace Sultana ga mutumin ki yaga mutuniyarshi kalli iskanci da yakeyi leƙo ta nan ki gani , murmushi nayi cikin yanayin jin kunya nace ni basai na gani ba , tace dan girman Allah leƙo kiga yadda bironshi ki rubutu babu takarda , dariya nayi sosai nace nidai bana san gani , Mamy tace haba so ɗaya fa zaki gani kawai , nace ba komai idan ya rubuta a takardar zan gani danni bana gane rubutu bisa iska ,

Dariya akayi gaba ɗaya , bayan wani lokaci kuma mukaci gaba da maganganu dai na sakin layi , bayan an gama mutumin ya tambayeni yadda mukayi da sabuwar sheƙar tashi , na goga mishi bayani duk yadda mukayi da su Ummu Affan hada Maman Sadiq duk ban ɓoye masa ba !

Yace babu damuwa ba hamsin za'a bata ba dubu ɗari zan bata yanzu sai ince mata gwamna yaje Abuja sai jibi zai dawo , kinga tana dawowa jibin ke Mamy sai ki bamu aron ɗaki mintuna 30 sun ishemu sau ɗaya kaɗai zan sa mata hannu kuma in bata kuɗi daga nan da kanta zataci gaba da zuwa ana mata singing ,

Shiru nayi sukaci gaba da firansu da Mamy , bayan wani lokaci kuma ya juyo yace Sultana kirata na sallameta tafiya zanyi na ansa da to tare da fita daga motar na nufi cikin gidan babu jimawa muka dawo tare da Ummu Affan bayan sun gaisa yace mata gwamna yaje Abuja wurin shugaban ƙasa amma zai dawo jibi idan Allah yasa muna da rayuwa , tace tou Allah ya dawo mana dashi lafiya...

Ya ansa da amin tare da karkacewa ya fiddo bandir in "yan ɗari biyar² masu zafi ya bawa Ummu Affan da kwalin sabuwar waya yace kuma da akwai layi a ciki , ruɗewa tayi ta duƙe har ƙasa tana zabgaga mishi godiya tare da cewa Alhaji kasa min lambar ka a ciki ? Yace zan kiraki zuwa gobe yadda mukayi da gwamna zan faɗa miki , godiya tayi sosai kamar zata faɗa mishi sai ƙara godewa take godiya irin ta maroƙa ,

Wani irin kallo ya bita dashi yana lashe loɓonshi na ƙasa mai nuni da zan kashe wuta dake , Mamy kuwa fitowa tayi daga mota mukayi mishi sallama bayan muma yayi mana wanka da ruwan naira ya tafi ya barmu da ɗaurewa da ruwan godiya ,

Ai Ummu Affan kuwa cewa tayi bazata koma cikin gida ba lokacin da Mamy tace mu shiga ciki , juyin duniya nayi mu koma ciki tacemin tabar yaranta suna jiranta gida zata tafi , babu ko tayin kuɗin bare ta jira taji munce ko mun ƙoshi , haka ta saɓe abunta tabarmu da kuɗinta da wayarta tai tafiyarta , mu kuma muka koma gidan Mamy , gaba ɗayanmu a palo muka zauna inda Mamy take cemin Al ' Ameen ya kirata ya zageta fess dan Mardiyya ta kirashi ta faɗa mishi babu daɗi yace duk sai yaci uwarmu dagani har ke kuma ya faɗawa mai gida abinda mukayi ma matarshi kuma shi mai gidan yace duk sai an tattaremu an ɗauremu , ni kuma jin haka yasa na kira wannan mutumin na faɗa mishi tunda naga yana cikin gwamnati shima.

Nace to yanzu ya ake ciki ? Mamy tace sai munemi mafita , nace shi Alhajin ya yace miki ? Mamy tace yace mu jira idan anyi ƙararmu zai ɗaukar mana lauya , idanuwa na zaro nace wane irin lauya kuma na shiga 14 nidai gaskiya bana san huɗɗa da koto ƙarshe akai mutum gidan yari ni banda wanda ya tsayamin , kawai saina fashe da kuka , Mamy tace haba Sultana tou miye abun kuka muna fa da bakinmu ki barshi ya yanko sammacin kiga yadda alƙalin zaiyi idan yaga lafiyayun katifu ,



1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment