Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iya surutu idan dai har magana da sune zaisa su raina ni har kowa yake k'ok'orin magana kad'an ya dakeni tou na fita sabgarsu danni ina da wata irin zuciya da idan har na gama da abu tou fa tabbas na shafe labarinsa a babin rayuwata, niko nace hada Dikko Sultana ?

Cikin kud'in da Alhaji ya bani na shiga kasuwa na kwankwaso tsadajjiyar sutura, na siyi kaya na kece raina, gyale takalmi jaka turaruka mayuka na shafawa irin ya wayayyun mata, agogo sark"a da "yan kunne "yan hannu zobuna saida na tabbatar nima na zama gogaggiyar mace ta sahun farko a fanni sutura.

Sannan naje nakai dinki wurin telan da nasan shima yasan hannunshi, kuma da naje kai d'inkin na fad'a mishi cewa irin d'inki karuwai nake so yayi min, nace yamin d'inkin dako tuk'i namiji yakeyi idan na wuce saiya dakaya saiya manta da kan sitiyari yake ya tsaya ya kalleni, mukayi tsada dashi na biyashi kud'inshi tare da sharadin idan fa ya lalatamin kayana wallahi saiya biyani, yace kuma yaji ya yadda.

Na gyara d'akina sosai nasa kayan kallo na sake katifa mai kyau na saka ledar tsakar d'aki na saka fanka amma ta k'asa, na kuma k'ara biyan kud'in haya daga lokacin da suka k'are daga lokacin zan siyi gida haka shine tsarina na gaba... Saina sayi gidan zama sannan zan sayi mota kuma duk zakuji ta inda kud'in zasu rik'a fitowa babu b'ata lokaci....

Hankalina kwance banda wata damuwa, banda rashin ci haka kuma babu rashin sha, cikin "yan kwanaki k'alilan na fara sauyawa, k'oshi babu abinda ya bari dan duk daren duniya sai naci nama abinda nake so ci nake ci kuma duk abinda naga dama shi nakeyi babu mai kwab'a kuma babu mai kyahra, jikina kuwa yasha mayuka gani bana jin wahalar wanka dan ko agwagwa bata kaini san ruwa ba, ya jama'a ku tayani hasko kyau ya had'u da gayu, ku tayani ganin gayu ya had'u da wanka, ku tuno wanka ya had'u da k'amshi...... Wuta Sultana lokacina ya fara...... Kalu bale gareku k"azaman mata.....

Kwance nake saman katuwar katifata da tasha shinfid'a da tsaftataccen zani, { bedsheet } iskan fanka sai kad'ani yake ta ko ina, ga wani ni'imtaccen k'amshi dake tashi daga d'akin har jikina, yanzu tunani na bai wuce in addabi Bello ba abokin Babana.....

Dan yanda ya haramta wa Babana wali a cikin garin shi, inda aka haifeshi ya girma a ciki yayi iyali, amma ya gudu ya bar "yan uwa da "ya "ya da matanshi tou shima katsina zata haramta yayi wali a cikinta, idan kuma yayi iskanci saiya d'aure kayanshi yabar birinin katsinar gaba d'aya....

Hannu na, na saka k'ark'ashin katifa na jawo wata "yar k'aramar kwalba dana anso hannu wani d'an daba, ya fad'amin sunan abun amma wallahi kafin inzo gida har na manta, abun fesawa gareshi kamar na turare, kud'i na bashi ya siyomin nace mishi abinda idan na fesawa mutum kawai zai kama bacci babu b'ata lokaci shine ya kawomin shi....

Tashi nayi na rufo d'akina dan ina so in gwada inga ko abun yanayi, saman katifa na kwanta sannan na fesa shi a fuskata..... Luuu wani bak'i na gani ya gittamin daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba saida 11:30am tayi.....

Salati nayi tare da godewa Allah dana farka na ganni a duniya, d'auko kwalbar nayi tare da sunbatar ta, tabbas kece abokiyar tafiyata, amfani biyu zakimin daga Bello sai Dikko daga nan aikinki ya k'are zan yadaki shikenan.....

Wanka naje nayo tare da d'auro alwalla nazo nayi sallah asuba da ban samu nayi ba, ina gamawa na hau shiri domin yau ba abinda zai dawo dani gida sai nayi ido ido da Bello kuma saina tabbatar da k'udurina akanshi.....

Mai da powder na shafa sai kwalli dana shafawa idona, ban shafa jan baki ba saboda bakina baya buk'atar shafe shafe sai kuma lura da nayi da irin manyan mata mawuyaci kuga sun daddab'awa fuskarsu irin abinda muka shafawa, irinsu jagira aishadow duk basa shafawa shi yasa idan suka shiga wuri suke fita daban, bana buk'atar bilicin koda na kasance ni b'aka ce shima ku lura da kyau bilicin na maciyata ne, d'iyan masu kud'i basa shafe shafe mayuka gaskiya....

Doguwar rigar shadda getzner na saka bak'a, kuma tayi matuk'ar martabani domin dai ta zauna min a jikina ciff na d'aura d'an kwalina coge, na kawo gyale na ida kafe wankan dashi komai dai dana san zai martabo min mutunci na saida na saka a jikina, sannan na yayyafa ruwan turare nayi gaba...

Tun kafin in fito k'amshin turarena yakai tsakar gida, a lokacin dana fito ina rufe k'ofar d'akina kuma gaba d'aya hankalin duk wanda ke gidan saida ya dawo kaina, ina rufe d'aki na saka makulli na a jaka na wuce abuna banma kowa magana ba... Da kallo suka bini domin dai sun gane kura ba sa'ar kare bace ba.....

Tunda na fito gida har nakai bakin titi na zama abin kallo ga jama'a , ban damu dasu ba domin dai duniyar yanzu gaba na bata ba baya ba.....

Napep na tare na fad'a mishi inda zai kaini na shiga muka tafi, cikin "yan mintoci kad'an muka isa, na sauka na bashi hak'k'inshi, majalissar ciki take kamar zata fashe saboda yawan dandazon mazan dake cikinta, ina fitowa napep duk wanda ke wurin idonshi ya dawo kaina...

Banji fargaba ba haka kuma ban daburce ba, banji bazan iya tafiya ba dan ana kallona duk wani bargaba da kunya ko tsoro duk basa tare dani a wannan lokaci, tafiya na farayi zuwa wurinsu na k'addara ma kawai ba maza bane mata ne....

Tsofaffin banza tun daga yanayin kallon da sukemin zaku gane duk sun fad'o rami, kallon tarko suka faramin kamar mage ta ritsa bera. Sallama nayi musu yayin dana isa wurin, kusan gaba d'ayansu saida suka amsa kamar ana biyawa dalibai karatu....

Nima kujera naja na zauna sannan na gaishe su, duka suka amsa cikin sakin fuska, inda Bello yake zaune na kalla tare da cewa Baba wurinka nazo , tou yace amma ban ganiki ba, sadda kaina k'asa nayi sannan na d'an murmusa cikin sigar bariki nace d'iyarka ce ta wurin Aliyu Binna...... Na k'arasa maganar tare da d'ago kaina na kalleshi da kyawawan idanuwa na da suka sha da ado da kwalli nakai karshen maganar tare da d'an sassauta kallo na, sannan na bud'e idanuwan dukansu,

Yashe baki yayi yana dariya kamar yaga wawan zama, sannan yace ahaf tou tou Uwar masu gida ce ? Murmushi nayi tare da cewa Eh, kinyi aure ne ? Ya tambaye ni ? Da kaina na bashi amsa cewa A , a, tou kina ina ne haka ? Ba tare dajin kunyar kowa ba nace ina bariki ne ? Dariya yayi sosai tare da cewa "yar gari kenan yarinya ta gane makoma.....

Nima dariyar duniyanci nayi harsai da kyawawan hak'orana suka bayyana idan dai nayi irin wannan dariya ni kaina nasan tana k'ara min kyau sosai sannan na kalleshi nayi murmushi sai kuma na kama kaina, kallon maita ya bini dashi kamar ya cinyeni a bakin titi sannan yace ina kike zama haka ne ? Ina nan tsohuwar anguwarmu daka sani dai....

Tou taso mana ya fad'a tare da mik'ewa, a raina nace wato tunda na zama karuwa bari a bini a lalace ! Zakaci ubanka domin nima kaina tsoron kaina nakeyi, duk a zuciya ta nayi magana....

'Daukar kujerata nayi muka matsa gaba, zama nayi na d'ora k'afa d'aya saman d'aya sannan nace ya ake ciki Baba ? Am tou aike zan tambaya kinga tunda ga gida ai ba'a kai k'aruwa waje ba....

'Dan gajeren murmushi nayi sannan nace gaskiya kam, amma yanzu kana da mota kuwa ? Eh akwai mota hannuna mana, wace iri ce ? Na tambayeshi yana k'ok'arin fad'amin nace dakata ma barshi kawai kasan ko ka fad'a bazan rik'e ba zan manta ne ,

Duk'owa yayi kusa dani waini zai tambaya yanda muka k'are da Dikko kwanaki, dariya nayi sannan nace ai Dikko ba abinda yayi min kuna tafiya yasa aka dawo dani gida, tsoki Bello yayi tare da cewa kaji sakaran banza wannan tunjumemiyar mace ya bari baisha ruwa ba ?

Murmushin mugunta nayi tare da d'aga girarena nace kila bayajin k'ishirwar ne, tou waike kawai sai kika fara bariki abunki ? Nace sosai ma, tou ya akayi kika zab'i wannan harkar bayan baki san yanda abubuwan suke ba ? Duk zan baka bayani idan kana da wurin saukeni mu tafi kaji komai....

Tou ina zuwa, ya fad'a tare da tafiya wurin abokansu, sallama yayi musu tare da cewa zai dawo da daddare duk zasuji bayani, wani ne daga can yace kayi min register idan ka gama ina layi nima.... D'iyar abokinku maimakon kuyi k'ok'arin d'orani hanya A , a, saidai kuyi k'ok'arin k'ara dilmiyar dani....

A mota ya d'aukeni muka tafi, ko a hanya sai wani kyarma yake yana k'ok'arin kai hannunsa cikin rigata, kallonshi nayi tare da cewa saurin me kakeyi haka ne wai ? Ban bari ya bani amsa ba naci gaba da cewa ko da kayi tunanin yau zaka sameni ? Yace a , a nace tou kasa ma ranka natsuwa har muje inda zamu baje kolin iskancin namu muci karenmu babu babbaka babu wanda yaji kuma babu wanda ya gani...

Kyah kyah kyah ya kyalkyale da dariya tare da cewa gaskiya ne Uwar masu gida, kunji ihu kura ta samu nama, wannan dariya itace yayi shi ya samu Sultanar banza zaije ya gurji banza a tunaninshi, baisan ni nafi shi iya iskanci ba domin dai ni naci uwarshi nasha ruwan kanwa maganin kwarnahin ciki....

Har muka iso ban sake magana ba, horn yayi mai gadi ya yaye mana get muka shige ciki, parking yayi sannan yace muje, kai jama'a kuji rashin kunya don Allah dan kwatawalci d'iyar abokinka, uhum cije lebona na k'asa nayi sannan nace masa rubutamin number wayarka don Allah a takarda, yo baki da waya ne ? Ya tambayeni cikin gatsali, murmushi nayi sannan nace aini ko a cikin kwarin k'arama ce har yanzu da sauranmu kafin mu gama nuna Baba....

Hahaha a haka ma baki nuna ba ? Nace yo dana nuna ka ganni a napep baki da dama yace tare da fara rubutamin number wayarshi, mik'omin yayi bayan ya gama, yana k'ok'arin fita nace ka sallameni kafin mu shiga mana.....

Dubu biyar ya mik'omin , ansa nayi tare da jujjuya kud'in nace ashe gara da bamu shiga ba, yo Baba banda abunka wannan ai ko kud'in fira baka biya ba, zaro ido yayi tare da cewa dubu biyar ? Ke kin raina dubu biyar ? Murmushi nayi tare da cewa tou turaren dana shafa idan akace maka kayi tukwuici ai kasan nafi k'arfin ka bani 5k , koni ai nayi kyautar dubu biyar wallahi, ka bani kud'i masu yawa idan kana bani kaji malam....

Daga gaban motarshi ya jawo wani wuri kud'i na gani kamar in zabgaga ihu saboda yawansu , saida na gani sannan ya maida ya rufe kin gansu nan kud'in da zamuyi caca ne na had'a gobe na k'ara miki ki anshi 5k in mana...

Babu gardama na ansa muka fita daga motar dukanmu muka shiga ciki, saida ya rurrufe ko ina mu kuma mukayi ma junanmu masauki saman gado..

K'ik'iy k'ik'iy ya cire riga ya cire wando, jakata na bud'e na d'auko kwalbata sannan nayo wurinshi cikin karairaya, yana k'ok'arin rungumata nayi ma shege feshin maganin sauro, babu b'ata lokaci ya tafi bacci rik'eshi nayi har yakai k'asa sannan na cire mishi gajeren wandonshi na dauki d'an iska hoto, nayi mishi kuma vidio ko ina saida na d'auka, bayan na gama na janye shi daga saman hanya, saida na lalube aljihunan shi kaf sannan na zauna gefen gado na shigar da numbershi cikin wayata, bayan na gama na ajiyeshi da lamba 2.

Makulin motar na d'auka da jakata na bud'e d'akin na fita, cikin mota na koma saida na kwashe kud'in nan kaff sannan na rufe na maida makullin kusa dashi na ajiye, fitowa nayi na tunkari hanyar fita daga gidan, dubu biyar d'in daya bani itace naba mai gadin gidan kyauta, yana ta godiya na wuce abuna ban tsaya saurarenshi ba na fice daga gidan abuna..........




20/08/2019


*JAMILA MUSA...*

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 14


Saida ma na fita daga gidan nakejin wani irin bak'in ciki ya tokaremin zuciyata, wallahi dana iya mota saina taho da motar Bello, zanje gida na jira zuwan shi domin dai nasan nabar baya da k'ura babu yanda za'ayi ya barni na ci kud'in nan , murmushi nayi sannan nayi magana a bayyane cewa Allah ya kawo ka lafiya Baban kwali Baban tusa.....

Ban tsaya wasa ba haka kuma banyi gigin biyawa gidan kowa ba na yanki santa na fara neman gidan da nake kwana....

Tafiya mai zurfi nayi kafin na fito bakin titi, Allah kuma ya taimakeni ina fitowa na samu abin hawa ban wani b'ata lokaci ba, ko ciniki ban tsaya yi ba na afka nace muje.

Inda zamuje ya tambayeni, ni kuma na fad'a masa yaja muka tafi, raina fes zuciyata dunk'ule da farin ciki na isa gida, ko mai napep 1k na bashi yayi ta zabgaga min godiya tare da jawo addu'o'in samun nasara a rayuwata...

Godiya nayi masa sannan na shiga gida da sallama kamar yanda na saba bawai dan zasu amsa min ba, a , a, inayi ne dan fita hak'k'in musulinci, kai tsaye k'ofar d'akina na tsaya na ciro mukulli na bud'e na shige abuna....

Saida na fara adana kud'ina a ma'adana mai sirri sannan na fara neman abinda zanba baba uban ba'u, { ciki } saida na d'ora girkin abinda zanci sannan na fita nayo alwallah dan ganawa da mahalicci na...

Bayan na fito daga bayi ne naji su Saude suna fira kuma ga dukkan alamu zance Dikko ne sukeyi, da wutsiyar ido na kalli wurin, wata bak'ar cikakkiyar buduwarce na gani tsaye, amma ban tab'a ganinta ba sai yau, kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar tanaji da hutu domin ta huta d'in, duk inda ta fito yarinyar can d'iyar wani attajiri ne...

Fasa alwallar nayi na tashi na koma d'aki na kashe d'an gass d'ina na d'auko asawaki dan inaso inji inda labarin nasu zai tsaya, dawowa nayi na zauna ban kalli inda kowa yake ba kuma banyi ma kowa magana ba na tusa buta a gaba naci gaba da gogo asuwaki a bakina....

A ` i ce ke cewa kai amma gaskiya Hafsat baki da hankali ai da ki nemi d'an mai kud'i da asiri gara ki tafi tsirara kawai ki huta, kina ganin ubanshi banza ne ? Wannan Dikkon da kike gani tun yana ciki an gama dafashi da asiri yanda Babanshi yasha wahala kafin ya samu namiji kina ganin daya sameshi da wahala zai barshi ne yai ta yawo figifigi a duniya ba tare da an bashi dafa'i ba ? Kai wallahi kimayi hak'uri ,

Cikin muryar sakataccin "ya "ya tace no ai da ina kiranshi wani lokaci yana d'aukar wayata amma yanzu ya daina d'auka kwata kwata, da sauri na d'aga kaina na kallesu sai kuma na basar kamar ina kallon wani wuri, wato ita tana ma da number Dikko, tunani na farayi yanda wayarta zata zo hannuna na, ba ansar wayarta zaimin wahala ba yanda zan gano sunan Dikko shine wahala a wurina....

Kawai gaba d'aya tunanina ma har ya tashi daga d'aukar number, kawai harma na hango gani nan na d'auko tsiraicin Dikko na balbad'a a social media, tabbas Dikko saina had'a shagalin partyn wulak'anta mishi rayuwa.... Tunani na ya dawo ne a lokacin da naji Saudatu na cewa aiko ki dage yarinya dan nan da shekara d'aya Dikko baya rik'uwa, tunda shi dama bai dogara da kud'in gidansu ba gaskiya Dikko yana da sa'ar rayuwa idan kika auri shi kin more rayuwa domin dai cikakken namiji ne...

Banyi musu magana ba dai naci gaba da goge hak'ora na, wayau sukayi ma Hafsat suka amshi kud'i masu yawa a hannunta da sunan za'ayiwa Dikko asiri, ci gaba da tattaunawa sukayi amma hankalina baya wurin firarsu ya tafi wurin karatun halayyar Hafsat, tab'e bakina nayi a bayyane nace itama dai "yar mad'igon ce { Lesbian }

Kallona tayi nima na watsa mata mayatattun idanuwana masu sa mutum ya rikice na k'ura mata su sosai domin ina so ta yabani idan har ta shigo hannu na nice zan koya mata barikin da zata kawo min Dikko k'asan k'afaafuwana nima in rama wulak'anci da yayi min dan nayi alk'awari nima sai Dikko ya lashi k'afata kamar yanda yasa na lashi tashi...

Shegiya ta kuwa daskare ta kasa barin kallona, kyakkyawan murmushi nayi mata tare da cewa sannu ko ? Na k'arasa maganar tare da d'an wasa da idanuwana... Murmushi tamin tare da cewa ya kike ? Ban bata amsa ba naci gaba da alwallata...

Ina gamawa ban sake bi ta kansu ba nayi d'aki inajin tana ta magana amma na basar da ita, nadai juya ta ganni maza ma sun gani sun rikice ina ga mata mayun mata kuma ?

Ina shiga na kunna gas ina na kabbara sallah. Bansan yanda suka k'are ba, amma nasan tabbas saita dawo saboda taga ina da irin k'addarar da suke nema...

Bayan na gama sallah na zuba abinda zan dafa a tukunya sannan na zuba ruwa na tafi wanka, lokacin da nayi wanka na dawo har ya dahu, dan haka kashe gas ina nayi sannan na shafa mai da powder, d'aurin gaba nayi sannan na zuba abinci na naci gaba daci....

Bayan na gama duk abinda nake na kunna kallo, sannan na saka kayan bacci na koma saman katifa na kame kamar d'iyar wani shege... Kai gaskiya inajin dad'in wannan rayuwa tawa, saida na kwanta sannan na bud'e data ta, lamba d'aya na gano bayan na ganoshi na tura mishi vidion dana d'auko , tare dayin voice note na tura mishi. Ina turawa na sauka online na kashe wayata gaba d'aya, na kashe kallo na rufe d'akina nayi kwanciyata.......

Tashin hankali shine kalmar da Alhaji ya fad'a a lokacin da yaga vidion dana tura mishi, wata irin gagarumar zufa ta yayyafo mishi a lokacin da ya saurari voice note ina, tashi yayi tsaye cikin tsananin tashin hankali ya rasa gane a wace rayuwar yake rayuwar mutuwa ce ko ta duniya ?

A gefe kuma wayarshi ce take ta kwarara ihu, lambar mai gida Dikko ce keta tsalle babu k'ak'k'autawa amma Alhaji yau kam bata Dikko yake ba, saida kiran ya tsinke sannan Alhaji ya sake kunna maganar Sultana yana sauraro, ga abinda take cewa....

_Ina mai farin cikin sanar dakai wannan mummunan labari, d'abi'a na ne yin albishir da farin ciki yayin fad'ar abu mai munin gaske, kuma nakanyi farin ciki yayin fad'ar abun farin ciki, wannan vidion dai dani dakai ne a ciki kuma kaga irin bad'alancin da muke aikatawa a ciki, nidai banajin komai idan wani ya gani domin ni iyayena tuni sun sallama ma duniya ni, saboda haka ni duniya itace uwata kuma itace ubana, idan na yad'a wannan vidio banajin komai tunda biye nake da mutanen cikinta ina basu, nayi tunanin maidashi faifayin filet na sidi dan in siyar na samu kud'i , sannan kuma in watsashi a yanar giza gizo dan inyi suna, kai kuma kana da dama d'aya tak data rage maka, idan har ka bani naira miliyan d'aya nayi maka alk'awari zan goge shi sai in hak'ura basai nayi suna a duniya ba...... Idan kuma baka dasu in turawa "ya "yanka ko suna da kud'in fansar ka ! Sultana, Sultana ce yarinyar mai dogon zamani, idan kuma kace zakayi gigin sako hukuma a ciki na riga dana turama k'awata nace da taji an kamani firr zakaji su sun watsu a duniya kamar saukar tsuntsaye. Ka huta lafiya habibinah muah_ 💋

Goge zufa Alhaji yayi tare da cewa Allah ka tsinewa yarinyar nan albarka, shegiya tsinanniya ubanta da uwarta basuyi addu'ar kwanciyar aure ba yayin da zasu kwanta Allah ya basu cikin d'ebabbar albarkar yarinyar nan, a daidai wannan lokacin kiran Dikko ya sake shigowa.

Jiki a sanyaye Alhaji ya kalli wayar tare da cewa mai gida kayi hak'uri wannan abun kunya ina za'a dashi na watsu cikin duniya ina zina, abun bak'in ciki da d'iyar da nayi d'iya da ita, garin ciye ciye na har naje na ciwo ma kaina bala'e, kila sai ta k'arar da arzik'ina, kuma tace idan na fad'awa hukuma taba k'awarta vidion zata yad'ashi wannan shine ciwo ya riga ajali zuwa...

Kuka Alhaji yayi tayi tare mitar ya shiga 3 ya bani ya lalace, wannan labarin abun kunyar waye ma zai fad'a mawa bare kuma yasa ran zai samu wata sahihiyar shawara, kai ya bani ya bani ya bani........😰🙆🏻‍♂😭, a daren nan Alhaji baiyi bacci ba kuma baibi kiran Dikko ba, wayar Sultana kuma ya kirata yafi so adadin yawan dutsinan da ake jifar shedan dasu amma maganar dai d'aya ce cewa a kashe.......

Da safe , tunda nayi sallar asuba na koma bacci, can cikin bacci naji ana dukan k'ofar d'akina, addu'ar tashi daga bacci d'auke a bakina bayan na gama nace waye ? Na tambaya cikin muryar bacci tare dakai idona saman agogon dake lik'e a saman bangon d'akina k'arfe 10:36am, cikin muryar murna Nana tace "yan sanda aka d'auko miki Sultana....

Murmushi nayi tare da jawo wayata na kunna sannan nace ma

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment