Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fito sai an turota , wasu takalman yayi masu zafi suma a turo jukkuna gyaluluwa "yan kunne tsarƙa , bawai na siyarwa bane ba , a , a sune dai na zamani su matan idan suka gani zasuje kasuwa su siya ,

Mace kuwa idan tayi lafiyayen girki saita gama tsara abunta kaf a tebirin cin abinci sai ta ɗauko hoto ta turo a group , idan wanka kikayi kika kai ƙarshen adaka zakiyi hoto ki turo matan group in suna zugaki ,

Shin da Allah mace ta dafa lafiyayyen abinci komai yaji banda bala'e kina kallon yadda naman kaji ke wali ga lemuna masu kyau da tsada an jera ki faɗamin ke kinyi ɗan wake da miyar ƙuli ko kinyi zazafen tuwo kin ɗauka ki tura ?

Mace ta share ƙaton fili ga filawowi ta ɗauko hoto tasha kafirarriyar shadda ko wani ƙaton leshi ko super ke kuma mijinki baida halin ɗinka miki super atamfa rober yake da halin ɗinka miki kuma ita gareki shin kin ɗauka hoto ki tura a group in mata masu duniya ?

Banda ko sisi amma ina da style na ɗinkuna a wayata yafi dubu , duk wata jikkar da ake yayi ko atamfa sabuwar fitowa tana cikin wayata , banda sisi mijina baya dashi na manta da hatta yatsun hannuna ba ɗaya suke ba , duk lokacin da wata ta ɗauko hoton palonta ta turo sai ince ya zanyi na maida nawa haka ?

Kafin wani lokaci na fara tadawa mijina hankali cewa duk mazan duniya suna kishin matansu suna musu sutura sun wadatasu da komai amma duk lokacin da nayi maka magana sai kacemin kai babu ,

Idan yayimin nasiha ya bani haƙuri sai kuma in haƙura , kullum dai abu ci gaba yakeyi dan haka na fita daga group in , amma kash ina fita admin in ta biyoni prvt tacemin taga nayi left lafiya ? Ban ɓoye mata komai ba nace gaskiya ina ganin kayane hankalina yana tashi zuciyata tana min wasi² kuma mijina baida kuɗi shi yasa na fita , dan na lura idan aka turo kayan yayi duk wacce ta sawo idan ta ɗinka hoto takeyi ta turo kowa ya gani ,

Tacemin bara in kiraki nace tou , babu ɓata lokaci ta kirani bayan mun gaisa tacemin duk wanda na gani a group in nan matan aure ne , kuma yadda nake tunanin mijina ma baida hali yafi na wasu a cikin group in , kinsan yanzu ana zamanin rayuwar "yanci kina da aurenki amma kina da abokinki a waje , wanda zai ɗauke miki duk wata hidima taki ,

"Yanci shine babban mutunci da zaran kin rasashi taki ta ƙare , cikin mintuna biyar kacal abokinki zaiyi ya miki abinda mijinki da kike aure bazai miki irinshi ba , yanzu an daina duhun kawai rayuwar ƙyaunci ta gushe , ki riƙe babbar waya kici mai kyau kisha mai kyau ki ɗaura mai kyau ki gyara muhallinki babu wanda yaji kuma babu wanda ya gani ,

Nace tou idan kuma mijina yace ina na samu kuɗin da nake wannan hidimar fa ? Tace dama ai kafin ki shiga zaki rufe banza a tulun ƙasa zaki riƙa juya rayuwarshi kamar remote sai yadda kikace dashi babu shi babu magana kuma idan "yan uwanshi sukayi mishi magana tou fa ko uwarshi ce zai iya rabuwa da ita akanki , nace tou abokinki me ake bashi yake bada kuɗi haka kuma a ina zan samu abokin , tace abinda zaki bashi yana nan jikinki samun shi kuma nine zan haɗaki dashi , nace tou zanyi shawara ,

Sati ɗaya ina neman mafita kuma kullum saita kirani ta ƙara bani shawara , ƙarshe dai na haƙura nima na antaya a duniyar kwaratanci , social media tana da amfani tana gyara amma illolin sunfi gyaratanta yawa kusan irin mutanen da kuke huɗɗa dasu , tari tayi sosai cikin yanayin wahaltuwa tace ki riƙe wayata a hannunki akwai wata ƙawata dana haɗa da Bello akwai wasu maganganu da nayi da ita akanki kuma na haɗasu domin ina so duk wani shiri nasa ya lalace ƙarshenshi tazo , naso na kafa rayuwa mai inganci a gareki amma lokaci ya ƙuremin , cikin kakari tace kuma Baban Hafsa da Baban Amisty da Binna ...... Daga nan lumfashin Mamy ɗauke ,

Shikenan Mamy tata , ta ƙare ina da tulin tambayoyi da zan mata amma ta tafi inda bazan sake ganinta har abadan duniya , me mutumin yayi mata ? Ya akayi aka ƙwaƙwale idonta ? Ina ƙawarta data haɗu da ita a sanadin whatsapp ? Ya akayi Babana bai aureta ba ? Cikin abokan Bello waye Yayan Mamy a ciki ? Ina iyayenta suke ? Wayyoni Allahna na shiga 3na , tou wai meye take san faɗamin data kira sunan Babana dasu iyayensu Amisty ? Wai ya rayuwata take tafiya a taltala ? Wani irin juyi kaina yayi na saki wani irin gahurtaccen ihu tare da faɗuwa ƙasa somammiya ,

Ihun Sultana yasa mijin Mamy ya shigo da gudu , da taimakon likitoci aka samu aka farfaɗo da Sultana daga duniyar sumar data tafi , a lokacin dana farko har an fita da gawar Mamy waje an sakata a mota ,

Mijin Mamy ya bani wayoyi duka domin duk firar da mukayi da Mamy yaji komai , yace min kije gida sai Allah ya kaimu gobe za'ayi jana'izar Hajiya , mai napep in da kika zo dashi na sallameshi kije kar a nemeni ,

Yana faɗin haka yayi gaba , kamar wata doluwa haka na riƙa tafiya irinta sakarkari har na fito waje , napep na samu na faɗa masa inda zai kaini , har na iso gida kuka nakeyi haka na sauka daga napep in nayi cikin gida abuna , shima Babana ya sallameshi ya tafi ,

Wanka na farayi har na fito kuka nakeyi , zuwa wannan lokacin kuma labarin mutuwar Mamy ya fara zagawa a cikin gari , har su Amisty sunji labari kowa so yake yaji dalilin da yasa aka ƙwaƙwalewa Mamy idanuwa , bayan na fito wanka ina zaune a gefen katifa na kunno recording in da nayo bana gane komai amma fa ga murya nan lafiya zaw kanajin komai , aje wayar nayi na fita nayo alwalla ina dawowa na saka kayana ban shafa mai ba , hijabi na saka nayi sallah la'asar da ban samu yi ba ina gamawa na maida magrib bayan na sallame na ɗauki alkur'ani naci gaba da karantawa dan har yanzu bana cikin natsuwata ga tsoron da naji daga farko ga kuma mutuwar Mamy da aka zare ranta a gaban idona ....

Tsaye yake gaban madubi yasha ƙananan kaya cikakken namiji kenan tsawonshi ma kanshi abun burgewa ne , sanye yake cikin farar riga da bakin wando rufaffen takalmi baƙi yasha stocking da bakin belt ƙamshin turare mai daɗi da dasa farinci mai jefa mutum yanayi marar gogewa a rayuwa sai tashi yake , murmushi yayi yayin daya fara sharce gemunshi yana cewa , sa'a da kanta take kwankwasa mana ƙofa ga duk nasarar namiji mace ce jigonshi , cingom yasaka a bakinshi saida ya ɗan tattauna yace gani nan zuwa gareki An matana......






05/10/2019




*JAMILA MUSA....* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 50




Cike da farin ciki ya juyo , amma me ? Sai yaga *Jiddah* tsaye ta zarge hannuwan ta , wayoyinshi ya ɗauka sannan ya tunkaro ta dan ta hanyar da zaibi ya wuce ta tsaya , cike da kissa tace haba Yaya daga dawowa kuma ina zakaje haka da daren nan ? Inda raina yake so zanje , haba Yaya gaskiya haka an shiga haƙƙina , kallon raini wayau yayi mata tare da cewa a haba ? Umm gaskiya ina so mu kwanta mu huta duk gajiyar jirgi tana damuna , ta ƙarasa maganar tare da san kwanciya a jikinshi , zamewa yayi da sauri ya karkata ya fice daga ɗakin.

Ni kuma bayan nayi sallah isha'e tunanin duniya yazo ya tokaremin zuciya , ikon Allah wato ita rayuwa haka take , Mamy bata taɓa tunanin mutuwa ba kwata ² a "yan wa'annen lokuta , hawaye ya gangaromin daga cikin idona nace shikenan anyi zamaninta an gama , duk saɓawa ubangiji da tayi saboda samun duniya kuma Allahn ya yaddar mata ta samu kuma ta tara , amma ta tafi ta barshi domin ansa kiran mahaliccin ta ,

Me ake ma haɗama a duniyar ? Bayan babu wanda yazo dashi kuma babu wanda zai tafi da komai , anan aka samu kuma anan za'a tafi a barshi , haba mata meke ruɗarmu a cikin duniya ?

"Yar uwa ko kunyi yar jejeniya da mala'ikan mutuwa ga lokacin da zaizo miki ? To kisani mutuwa bata sallama bata jira sai kin gama sharholiyarki wallahi zata iya riskarki a duk yanayin da kike ciki , ba ruwanta da kina aikata alheri ko akasin haka , ya ubangiji ka karɓi rayuwarmu muna masu aikata alkhairi ka sada mu da aljannar ka dan darajar fiyayyen halitta S. A. W , am3n.

Gadai Mamy nan an tafi neman duniyar amma an haɗu da mala'ekan mutuwa a hanya , kai ubangiji kasa muyi kyakkyawan ƙarshe , ko waye ma ya haɗa Mamy da wannan ibilishin ?

Ƙarar wayata naji a gefena a firgice na juya inda take na miƙa hannuna na ɗauko , lambar Dikko naga ta bayyana a saman screen in wayata , ajiyar zuciya na sauke da sauri na ɗauki wayar tare da miƙewa tsaye na karata a kunnena ,

Sai sauke wani irin wahaltaccen numfashi nakeyi mai nuni da nasha wahala , cikin muryarshi maisa natsuwa yace har kin fara bacci ne ? Kukana ya ƙara kwacewa ban bashi ansar tambayar shi ba nace shine ka tafi ka barni.... ?

Murmushi yayi mai sauti cikin murya mai kashe jiki yace in dawo ne ? Da sauri nace Eh , dariyar mugunta yayi yace An mata taji a jikinta tou fito gani nan ƙofar gida , da gaske ? Na tambayeshi sai kin fito zaki tabbatar da haka , da sauri ya ajiye wayata nayi waje da gudu ,

Dikko yana tsaye ya jingina da mota ya rungume hannayenshi a guje na isa inda yake tsaye da niyar in rungumeshi , a wayance ya matsa daga saitina ni kuma na ɗan sassauta gudu na saboda na iso ina ganin ya kauce nima na basar na rumgumi mota ,

Kauda kanshi yayi gefe tare da cewa ya kike ? Nima juya mishi baya nayi ina wasa da ƙasa da babban ɗan yatsana na ƙafa nace aini dana san kaine ma da ban fito ba , buɗe mota yayi ya shiga yana cewa ai dan nasan dama idan nine baza ki fito ba shi yasa nace miki ga Dikkonki ya dawo , ya ƙarasa maganar a daidai lokacin da yake zama a mota ,

Juyowa nayi dan a tunani na tafiya zaiyi , murmushi yayi yace ba tafiya zanyi ba banajin daɗin tsayuwar ne shigo mu tafi , da sauri na zagaya na buɗe mota na kame a gaba , ina rufe murfin motar ya taka motar muka shiga gidan dawakan shi ,

Kusa da motar daya bani yayi parking , ajiyar zuciya ya sauke tare da riƙe sitiyarin da duka hannayen shi biyu yayi miƙa cikin yanayin gajiya tare dayin hamma yace An mata na gaji wallahi yayi maganar cikin murya mai ladaftar da zuciya ,

Murmushi nayi amma banyi magana ba , dan idan inajin muryar Dikko sai inji tawa wata iri shi yasa ban cika magana a gabanshi ba , wayarshi ke ringing dan haka ya ɗauketa daga gefenshi daya ajiye yana cewa tou fa , karkace kaina nayi ina kallon fuskar shi yayin da hasken wayar ya haskaka fuskarshi dan duba mai kiranshi waya ,

Ɗan kallo yayi mai kyau yayin da idanuwan shi ke duba daga saman wayar zuwa ƙasa , zai ɗauka yace nifa bana san kallo da yawa , ki daina kallona haka nan tunda bakya so na , a dai² lokacin daya ɗauki wayar yana cewa inajin ka ,

Tou haka yace kuma ? A , a gaskiya bana kusa kawai kuje idan na dawo Ashiru zai tattaro minsu , ba komai fa kawai kaje abunka , to yayi kyau , ya kashe wayarshi ,

Bayan ya gama wayar ya juyo ya fuskance ni sosai yace An mata mi yasa kika bar mota tayi datti bakya hawanta ? Nace haka nan , hmm tunda bakyasan Dikko motar da ya baki ma bata burgeki ko ? Nace tana burgeni mana kuma ai nahau ta ma , Dikko yace haba An mata ai da kin hau wannan motar da naji a jikina , zansa a wanketa a daren nan ko baki so na ki hau motar nan don Allah inji daɗi kuma ko bakida inda zakije gobe kiɗan hau ta ,

Nace tou , yace yawwa ngode sosai , bayan wani lokaci kuma ya sake kallona yace An mata wai dan Allah mi yasa kike da kunne ƙashi ? Mi yasa bakyajin magana ? Nace me kuma nayi yanzu ? Bama kisan abinda kikayi ba ko ? Nace Eh , jinjina kanshi yayi yace yanzu ina amfanin irin rayuwar da kika koyama kanki don Allah ? Kullum baki da aiki sai ɗaukar tsiraicin mutane ,

Idan an taroki nan sai ki koma nan kina rayuwa kamar baki da kwalwa a kanki , shiru nayi banyi magana ba , cikin ɓacin rai yace ki kiyayeni ranar da nima zan miki tsirara in miki irin abinda kike ma mutane , bana san ɓacin raina akan ki saboda fushi na baida kyau idan har nace zanyi miki hukunci dai² da irin abinda kike aikatawa lafiyayen duka ɗaya zan miki ki mutu , cike da ɓacin rai nace tou ni yanzu waye kuma nayi ma vidio ,

Ƙanƙance idanuwa yayi yace Baban Mardiyya dama shine baƙin cikin da kike cewa zaki dasa mata a zuciya ? Ki bari bana so , nace tou , sake maimaitawa yayi cewa bana so ׳ idan kuma kuma kika sake zakiji babu daɗi , nace tou ,

Hararata yayi cikin salon so , yace to me kuma akayi miki kikayi kuka naga fuskarki duk sai a hankali , ban bashi ansa ba na canja maganar da tambayarshi wanda ya faɗa mishi nayi ma Baban Mardiyya vidio ? Cikin lallausar murya yace babu ruwanki da wanda ya faɗamin idan nace bana san abu kawai ki bari idan baki so mu ɓata , a ɗan zuciye nace tunda baza ka faɗamin ba bari in tafiyata , hannuna ya riƙo yace yi haƙuri An mata , tou faɗamin , yace ni bana san ɓacin ranki Al 'Ameen ne ya faɗamin , gaskiya An mata Al ' Ameen bai jitu dake ba kullum burinshi ya nemo aibunki ya faɗa a gidanmu duk da kince bakya so na ina so ki zama mai mutunci a idon "yan uwana da kuma iyayena kinga idan aka tashi bada labari cewa za'ayi ƙawar Dikko bata da hali mai kyau ni kuma kinga ai bazanji daɗi ba ko ? A kunyace nace Eh , yace tou da Allah ki baryin abu mara kyau duk ki barbaɗawa "yan baƙin ciki yaji a ido ya ƙarasa maganar yana kashe min ido ɗaya na dama , nace tou ,

Tada motar yayi yana cewa bari in ajiyeki haka nan kar ace kin ɓace , a dai² lokacin daya fara tafiya a hankali , yau da natsuwa yakeyin tuƙi yana ƙara jamin kunne na daina shiga sabgar kowa nayi rayuwata ni ɗaya idan banji bari ba kuma zanji hoho a jikina , a ƙofar gida ya ajiyeni yana cemin idan Allah ya kaimu gobe zai dawo , nace tou Allah ya kaimu ya kuma hutar da gajiya , ya ansa da amin ni kuma nayi cikin gida da gudu , murmushi yayi ya wuce cikin farin ciki ,

Yau zuciyarshi ta ƙara tabbatar mishi da akwai soyayyar shi a zuciyar An mata tunda har tasan idan ya daɗe bai zo ba idan yazo zata zo da gudu ta rumgume shi , kuma yace ko tana so ya dawo tace Eh , babu abinda ya kawo haka idan ba soyayya ba , yau kam yana cikin farin ciki.

Washe gari sai 9:30am na fita daga gida domin zuwa wurin jana'izar Aunty Mamy dan naji ance 10:00am za'ayi mata sallah domin kaita gidanta na gaskiya , doguwar hijabi nasa mai hannu ta saukar min har ƙasa mai ruwan jinin kare , dake ina da haske sosai sai hijabin ta matuƙar martabamin fuskata , babu abinda na shafa domin yau ranar ta jimami ce , makullin mota na ɗauka nayi gaba abuna ,

Ina fita naga su Amisty suma sunsha nasu hijaben cikin mota suna tahowa , ganin zan shiga gidan dokuna yasa Amisty tayi parking dan ganin abinda zanyi , a natse na shiga da jakata a hannuna saboda riƙon wayoyin zaimin yawa a hannu ,

A gidan na iske Dikko da kayan training jikinshi ya cire takalma rufaffi ya jiye a gefenshi ya naɗe kafafuwan wandonshi , silifas ne a ƙafarshi ɗorowo { Yellow } masha Allah shine abinda na furta lokacin da na kalli ƙafarshi , hutu dajin daɗi ya tabbata a gareta har wani hurhurun haske takeyi tsabar tasha madara ta ƙoshi "yar gayun ƙafa da ko mai ba'a shafa mata sabar hutawa , ga wani gargasa ya sauko saman ƙwaurinshi "yan yatsunshi masu kyau dan dani keda ƙafafuwan shi babu abinda zaijamin saka wasu takalmi idan ba irin silifas in daya saka a ƙafarshi ba domin yafa burge ,

Yana gani na ya tashi tsaye ya tare da ɗauko takalman daya ajiye a gefenshi ya tun karo inda nake yana cewa ina zaki tunda asuba haka ? Nace rasuwa akayi , Allahu Akbar Allah Allah ya sawaƙe , nace ba rashin lafiya ba mutuwa , yace Ey ai na sani ina nema ma ahalin gawar sauƙi ne , Allah ya kiyaye hanya nace amin , biyoni yayi bai sake magana ba shima ya nufi wurin motarshi ya buɗe but in mota ya watsa takalman ya rufe ya shiga motarshi nima na shiga wacce ya bani wanda yau itace ranar farko da zan fita da ita ,

Tasha wanki tayi kalar ɗaukar hankali , saida na shiga harna sauko daga inda na ajiyeta shima ya sauko yana cewa mintuna 15 na baki ki dawo , tsayawa nayi nace ya kuma minti 15 sai kace kai ka aikeni ? Ban aikeki ba amma wallahi kika wuce lokacin da nace saina ɓata miki rai za'a faɗamin lokacin da kika dawo ai , haba wai mi yasa kake yin haka ne ? Ki wuce lokacin da nace miki sai kiga dalili , cikin hayani nace aure na kakeyi da zaka tsaramin yadda zanyi rayuwata ne ?

Murmushi yayi ba tare daya kalleni ba yace ai da ina aurenki babu abinda zaisa na barki kije gaisuwar wacce aka kwakwale ma ido tirr ya ɓata baki tare da ficewa ya barni cikin mota kamar sakarai.

Da sauri na kalli agogo naga 10:19am , kenan zan dawo gida 10:34 ? Gashi kuma har naci minti 1 , ina da sauran minti 14 yaushe naje har nayi musu ta'aziyya na dawo ? Tsoki nayi kamar kar naje wata zuciyar tace kije kawai kina ɓata lokaci ,

Da gudu na fito daga gidan kamar zan tashi sama , su Amisty suka rufowa motar baya dan a tunaninsu Dikko ne a ciki , lokacin da suka fito bakin titi tuni na ɓace musu ko ƙurata basa gani , hanyar da motar tabi ta wuce suka gaza gano ta ina motar tabi ta wuce ,

Da nasan haka hawan motar nan zai jawomin tashin hankali wallahi da ban hauta ba , ni kuma na hauta ne kawai dan Dikko yayi farin ciki saboda tayi wata huɗu da "yan kwanaki da bani ita amma ban taɓa hawanta na fita sai yau ,

Ina isa ƙofar soro har an dawo daga kai Mamy dandazon mutane kamar ƙasa gaskiya Mamy tayi jama'a a hankali na shiga mutane suka riƙa darewa suna bani hanya duk wanda ya kauce saiya bi motar da kallo kowa ya ƙagara yaga Dikko ya fito dan nace muku lokacin daya siyo motar anyi ihunta a gari duk garin katsina wannan motar Dikko kaɗai keda ita ,

Daga Qerau zuwa ƙofar soro minti biyu kacal ya kaini shima dan nabi a hankali dan motar tana da tafiya sosai , nabar gida 10:20 , na iso ƙofar soro 10:22 harda parking da nayi , manyan mutane suka fara yayyaɓe motar dan cikawa Dikko sheda ba'a iya gane waye a motar saboda gilashin motar duhu gareshi , wa za'a gani ta fito daga motar ? Ɗiyar ɗan caca ,

Tunda na fito kallo ya koma sama a dai² lokacin dasu Amisty suka iso , banbi takan kowa ba na ɗauki jakata na wuce jama'a suka bini da kallo yayin da surutu ya fara tashi ƙasa² danni taron mutane baya hanani tafiya kuma bai ruɗani bai firgitani haka kuma yawansu basa gigitani kuma banayin tafiya inji kamar zan harɗe na faɗi ,saida nakai gaf da zan shiga gidan Mamy naga Bello , kallona yayi ƙasa da sama yace wai Sultana ce haka bakya ko gane mutane ? Murmushi nayi tare da cewa ya za'ayi lafiya ta kasa gane mai bata damuwa ? Magana ce na faɗa masa ina faɗin haka na shige abuna na barshi da dogon nazari ,

Gidan mutuwar sai koke ² akeyi yayin da tabarmin zamar gaisuwar suka rarraba kashi ² , dangin Mamy da tasu , sai dangin mijinta makota sai kuma wasu lafiyayun karuwai suma sunyi nasu mazauni , ahalinta na farawa ta'aziyya sannan "ya "yanta , sai dangin mijinta , ko inda karuwan suke ban kalla na miƙe zan fita wata mata tacemin nan zaki zauna ke ?

A dai² lokacin dasu Amisty suka shigo gidan , miƙewa nayi banyi mata magana ba , tace ke Sultana take ko wa

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment