Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ƙauna Momy tace ba komai yanzu ma zan tafi , zaiyi magana Momy tace ba komai , tana faɗin haka ta fice daga ɗakin da maganinta bata barshi ba , Sadiyya kuma gefe ta koma ta zauna ta rasa inda zata saka ranta dan Dikko ya tsareta da ido....

Tsoki yayi bayan wani lokaci sannan ya gyara kwanciyarshi , idonshi na kallon sama ya rasa abinda ke mishi daɗi , amma yayi alƙawari kamar yanda Sadiya ta nemi ya rufa mata asiri wannan maganar duk duniya babu wanda zaiji kuma babu wanda zai sani , kuma ya zamarshi dole ya zauna da Sadiyya abin family a saketa zuminci zai samu damuwa.....

Saukowa yayi daga saman gadon ya nufi ɗakinshi , Sadiyya kuma abun duniya duk ya dameta , sai yanzu take nadamar da bata da rana.....





13/09/2019



Meelat Musa....💅🏻

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 32


Dikko kuwa yana komawa ɗakinshi wanka yayi , a gaggauce ya shirya bayan ya fito cikin ƙananan kaya , blue in riga da upwhite in wando shima takalmin irin wando ne amma rufaffi ne takalmin , ya naɗe hannun rigar daidai guiwar hannu , turare ya fesa sannan ya ɗauki makullin motarshi ya nufo ɗakin Sadiyya , a bakin ƙofa ya tsaya har yanzu tana nan zaune inda ya barta kamar asara ,

Kamar ba abinda ya faru dashi ɗazu kuma babu wata damuwa a tattare dashi yace zanje in dawo yanzu ! Cikin jin kunya da kama kai tace ina zakaje yanzu ? Naga har 11:05pm shima kallon agogon yayi sannan yace Ey ai na sani juyawa yayi tare cewa saina dawo bai jira yaji abinda zata ce ba...

A wannan dare kai tsaye gidanmu Dikko ya taho ni kuma a lokacin ina zaune saman dakali dani da Alaji muna fira , tun kafin ya fito nasan shine dan tuƙishin yasha banban dana kowa , cikin filinshi yayi parking sannan ya juyo motar ya haskemu da hasken fitila , Alaji dake da matsalar ido ya fara kauce² yana burza idanuwanshi dan gani ke barazanar ƙare mishi...

Fitowa Dikko yayi ya zauna saman mota , Alaji kuma miƙewa yayi ya fara laluben hanya dan gaucewa haske , cikin damuwa na kalli Alaji ina gilashin ka ne ? Ba tare da yayi magana ba ya miƙomin makullin mota , da sauri na ansa na nufi motar dan ɗauko masa gilashi ,

Da sauri na dawo da gilashin a hannuna nace tou saka , bawan Allah hannunshi yana kyarma ya ansa ya saka , ajiyar zuciya ya sauke cewa waye ne ya haska ? Baiga mutane zaune a wurin ba ? Banji daɗi ba gaskiya , haƙuri naba Alaji tare da cewa idan akace kayi hukunci wa mutumin daya haska maka ido me zaka mishi ? Alaji yace wallahi da fitulun motar zan kashe...

Shiru nayi ina nazari dan nasan idan har na faso fitulun motar Dikko na sake tarowa kaina fitina , tou amma ai ba gidan haye muke zaune ba , zuciyata ta ingizani in koma cikin gida kawai in ɗauko taɓarya na rusa fitulun kamar yanda Alaji yake sha'awar gani...

Kallo Dikko nayi dake zaune a saman mota yana kallonmu tas , gaskiya bana iyawa idan ya riƙeni a wurin can jakin duka zaimin babu wanda yaji kuma babu wanda ya gani , ya dakeni ya daki banza , kallon Alaji nayi tare da cewa barshi ya samu daidai dashi muje ka tafi gida ,

Rakiya nayi ma Alaji har wurin mota ya shiga , addu'a nayi masa Allah ya tsare hanya Allah ya fisheshi dare , ina tsaye a wurin harya tafi , buzum² na nufi gida dan anguwar ta ɗinke da duhu sosai gashi babu wasu "yan gayu da zasu kunna gen bare su bamu sadakar fitila ɗaya a cikin anguwa muga haske , yanda baki baya ɓace maka a cikin duhu haka ƙofar gidanmu bata ɓacemin dan haka na tunkari gidanmu cikin sauri...

Ina ƙoƙarin shiga Dikko ya fizgoni tare da cewa yawwa kwanakin baya kince zaki gauraya dani nine abokin wasar ki yarinya ? Ya faɗi maganar cikin neman fitina idan yaji haushi mi yasa tun a lokacin baiyi magana ba ? Sai yanzu ?

Da nayi tunanin babbaka mishi ashariya amma sai zuciyata tace karki biye mishi so yake ya jagula miki lissafi , idan har kika zageshi ko kika faɗa masa baƙar magan akwai wani abu a zuciyarshi , kawai kice masa yayi haƙuri , kinga idan baiba kinsan masifa yakeji...

Cike da rashin kunya nace kayi haƙuri amma hakan baya na nuna inajin tsoronka bane a , a , dan ɗan dambe yaja baya ba yana nuni ya tsorata bane gyaran tako ne , a haka zaki gyara takon kina tarayya da makafi ? Baki ba kwalwarki natsuwa ba zance har 11:49pm a haka kike tunanin zaki gyara tako ? Duk macen da tasan abinda take tana cikin gidansu kamar yanzu amma ke kina nan kina balbaɗewa a santa , kindai ji kunya !

Cikin jin haushi nace kaine kaji kunya ƙato dakai kana faɗa da mace , murmushi yayi tare da cewa kindai gane baki iya gauraya da Dikko kenan ? Tunda dai kinji tsorona kin fanshi kanki a daren nan amma dasai na hanaki baccin dare...

Jana yayi tare da cewa nima muje kimin rakiya , tirjewa na farayi bazan je ba , kallona yayi sannan yace kifa wuce muje idan ba haka ba kinsan Allah ɗaukarki zanyi , tashi nayi na daina tirje² cikin murya mai saukar da kasala yace muje ya faɗi maganar tare da sakin hannuna , gaba nayi yana bina a baya har wurin mota , buɗewa yayi ya shiga ni kuma na juyo da sauri , shima cin taya yayi ya biyoni da sauri tare da cewa An mata zo zo zo banza nayi na shige gida , saida safe ya faɗa , ko inda yake ban sake kallo ba na shige abu na...

12:20am Dikko ya isa gidanshi zuciyarshi na ƙara azabtuwa da soyayyar Sultana , addu'arshi a daren yau itace yanda yakejin kishin Sultana ubangiji ya sanya mata kishinshi a zuciyarta , yanda yakeji soyayyar ta itama Allah ya saka mata soyayyarshi , yasan dama babu ranar da zata ga girman shi tunda ya gama ɓareshi a wurinta , amma yasan idan dai tana mishi soyayya zatasan girmanshi dan darajar wannan son nashi dake zuciyarta....

Da sallama ya shiga ɗakin Sadiyya har yanzu tana nan inda ya barta tasha kuka har ta godewa Allah , cikin tausayawa ya kalleta yace har yanzu baki kwanta ba ? Dakel ta sauke ajiyar zuciya cikin kuka tace ina kaje ? Kusa da ita ya duƙa ya ɗagota cikin sigar lallashi yace meye ? Ki daina kuka kinji ya ƙarasa maganar tare da rumgumeta , cikin shashshekar kuka tace ina kaje ? Shine ka tafi ka barni ,

Shiru Dikko yayi , Sadiyya taci gaba da cewa nasan da ciwo a rayuwarka yau kaji babu daɗi kuma nasan duk lokacin daka kalleni zakaji baka ƙauna na , murmushin ƙarfin hali yayi cewa haba keko waye yace miki haka ? Sadiya tace ka daina ɓoyewa Yaya DK nasan babu daɗi kuma akwai ɗaci kayi haƙuri ka rufemin wannan sirri ko bayan babu ni...

Lallashin ta Dikko yayi saida ya tabbatar ta samu natsuwa har tayi wanka sannan suka kwanta , har Dikko yayi bacci Sadiyya ta kasa bacci baƙin ciki yazo ta taru a zuciyarta sai kukan zuci takeyi tare da nadamar biyewa soyayyar zuciya...

Tunda safe na farajin hayaniyar "yan gidanmu masu abun kuɗi suna ɓoyewa , masu wayoyi na kashewa suna adana abunsu , muryar Naja yayata naji tana cewa wallahi gashi nan yayi parking fa , zai fito , zai fito ya fito , gashi nan zai shigo zai shigo.... Sai kuma naji gidan ya natsu yayi shiru kamar babu masu rayuwa a cikin gidan , tashi nayi na leƙo ta jikin window dan ganin wanda yake shigowa , Babana duniya kenan , kai ina san Babana wallahi dan nafi sanshi fiye da Inna ,

Da sauri na buɗe ƙofa na nufi wurinshi da gudu ina mai farin ciki da ganinshi , cikin soyayyar da ya saba nunamin ya riƙeni tare da cewa bi sannu Uwar masu gida karki faɗi , yayi maganar cikin jin kunyata ya kasa haɗa ido dani tsaɓanin yadda yakemin a baya , rumgume Babana nayi tare da fashewa da kuka nace me yasa ka tafi ka barni Babana ? Kasan ina sanka banajin daɗin rashinka a kusa dani ? Me nayi maka kayi nisa da rayuwata ?

Shiru yayi baice komai ba , naci gaba da cewa idan har akwai sauran wata soyayya bayan wacce nake maka Babana itama na baka ita dan jaddada soyayya da ƙauna a gareka , ina alfahari dakai daka zama uba a gareni , kuma ina addu'a na kasance dakai har numfashin ƙarshena a duniya , kuma ina roƙon Allah yasa kar na wayi gari babu kai a duniyar nan , ɗagowa nayi cikin kuka na kalli cikin idon Babana nace karka sake tafiya ka barni ka kasance dani dan nima na samu duk irin soyayyar da ko wane mai Baba yake samu a duniya Babana...

Baiyi magana ba yaja hannuna muka fita ƙofar gida , motarshi ya buɗe muka shiga muka zauna , cike da soyayya Babana ya kalleni yace Uwar masu gida duk wata soyayya ta duniya wacce Allah ya halitta ta bayan soyayyar shi da manzansa da nake a duniya soyayyarki ke ɗaya tak ta goge soyayyar kowa a faɗin duniyar nan , idanuwana basa kallon kowa haka kuma zuciyata bata nunanin wani a duniyar nan idan bake ba ,tun daga ranar dana sameki ubangiji ya ɗoramin jarabtar soyayyarki a zuciyata , ni Allah bai ɗoramin ciwon son "ya "ya ba , wallahi bansan yanda akejin soyayya ɗiya ba saida Allah ya kawo zamaninki...

Nayi kukan baƙin ciki nayi nadama da har na kasa samar miki farin ciki , tunda nake a duniya ban taɓa nema na rasa ba , haka kuma babu wani abu na rayuwa daya taɓa kubcemin matsawar inajin soyayyarsa a zuciyata , an cuceni an kuma yaudareni da har aka samu nasarar rusamin farin cikin rayuwata , nayi tir da Allah wadai dana zama sokon uban da ya kasa ceto rayuwar "yar sa....

Mamana ki yafemin ni ban cancanci na zama uba a gareki ba , banso kika zo cikin rayuwar wahala ba , banso ba kuma banji daɗin haka ba , da ana canja uba dana zaɓar miki mafi girma da matsayi a duniya ya zama shine mahaifinki domin kiyi rayuwa mai inganci ba rayuwar dana sani ba ,

Uba ɗan caca bashi ne ya dace da rayuwarki ba , ba nine ya dace na zama uba a gareki ba bayan ni na kasance bana cikin mutanen kirki , idona ya rufe da duniya bansan duniya bata da daɗi ba saida na kasa magance duk wata damuwa taki , saboda haka ki daina alfahari dani nasan ke da kanki zaki gogeni daga lissafin rayuwarki matsawar kika gane wane irin mahaifi gareki a duniya...

Girgiza kaina nayi tare da cewa duk rayuwa sunanta rayuwa , jin daɗi ko rayuwar baƙin ciki baya sa a gane mai rabo a duniya , girman zunubi da saɓo baya sa kakai mutun jahanma domin rabon rahama wannan daga Allah ne , ɗan caca da ɓarawo duk matsayin su iri ɗaya ne a idon al'umma amma a wurin ubangiji azabarsu ta rabauta , manta da abinda ya faru baya kawai mu fuskanci rayuwa , amma waye Bello ? Meye tsakaninka dashi ? Me ka mishi wanda har ya zaɓi nice zaka saka a wasan caca.....?

Hawaye ya gangaro daga idanuwan Babana , murmushi nayi tare da riƙe hannunshi ina masa kallo mai tattare da soyayya.....

Cikin soyayya shima ya kalleni sannan yace ki jirani ina dawowa yanzu zan mayar da mutane motarsu , idan na dawo zan faɗa miki asalin waye Aliyu Binna , haɗuwata da Bello abinda ke tsakaninmu saka ki a wasan caca duk zakiji , sakin hannunsa nayi ba tare da nayi magana ba na fice daga motar , shi kuma yaci sitiyari yabar anguwar , cikin gida na koma ban damu da hararar da akemin ba naci gaba da sabgogin gabana....

Har yanzu Sadiyya bata daina kuka ba , kuma Dikko yayi lallashin duniya taƙi ta daina kuka kuma taƙi taci abinci , daga jiya zuwa yau ta rame idanuwanta sun kumbura , Dikko ya gaji yace mata kode shine bata so ? Sadiyya tace duniya da tasan zata zama matarshi kwata² da bata ɓata rayuwarta ba , gajiya yai ya fita sabgarta yaci gaba da huɗɗoɗin gabanshi zai bar gari ana rantsar dashi idan Allah ya kaimu gobe...

Cikin ƙananan kaya ya fito yayi kyau sosai a cikin coppie brown in riga, da wando ash mai haske , rufaffin takalma brown mai haske yayi stocking yafa ɗauku iyakar ɗaukuwa yayi kyau sosai , ɗakin Sadiyya ya nufa yana ɗaura baƙar agogo a tsintsiyar hannunshi yana cin cigom cikin salo mai ɗaukar hankali...

Da sallama ya shiga tana kwance saman gado cikin bargo ƙasa² kakejin sautin kukanta , yaye bargon yayi fuska a haɗe yace waike baza ki daina kukan banzar nan ba ,? Nifa bana san iskanci bana so inyi ta magana abu ɗaya , zan tafi idan kinga dama kiyi shiru idan kinga haggu kiyi ta kuka har masu kuka suzo su sameki....

Murmushi Sadiyya tayi tare da cewa Allah yasa ka sauka lafiya , kuma kayi haƙuri idan har kazo ka samu na mutu to ka yafemin , tsoki Dikko yayi ya fita ba tare daya sake mata magana ba ,

Al ' Ameen shine yaja su , Dikko ne a gaba mutane biyu kuma a bayan mota , su huɗu kenan , kuma saida suka biyo ta anguwarmu amma yau bamu samu haɗuwa da Dikko ba , kuma ya aiko kirana har gidanmu akace masa bana nan , bayan kuma ina nan , amma banji lokacin daya aiko kirana ba.... ,

Dikko yaso ya ganni amma haka ta gagara , dole ya haƙura suka ibi hanyar Abuja.......





14/09/2019




Jamila Musa....💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 33


Tafiyar Dikko babu jimawa Nana ta shigo take faɗamin mai gidan dokuna yazo nema na amma ance bana nan...

Tsoki nayi ban bata ansa ba , tsintsiya ta ɗauka taci gaba da share ɗaki , ni kuma jakata na ɗauko na buɗe ina kallon abinda nake fesawa mutum ya tafi bacci , jijjigashi nayi bayan naji sauran abinda ya rage na mayar a jaka ina mai addu'ar haɗuwa na da iyayen su Hafsa...

Maganar Babana naji a tsakar gida yana cewa duk iya ƙwarewa munafircinku na gano ku baƙaƙen munafikai , wato duk lokacin da kukaji motsina sai ku kashe wayoyi ku ɓoye kar nace ku bani kuɗi kuce babu , idan naji babu zansa wayoyi suci kasuwa , dan ku bani kuɗaɗen , lissafo duk yayuna yayi masu waya cewa kowa ta kawomin wayarta dukanku ancemin har face buk kukeyi , kuma na gani da idona dan babu wacce banga hotonta a cikinku ba...

Cike da damuwa suka fara fitowa Babana yana zaune a saman kujera kowa sai ta bashi ta koma ɗaki cike da ɓacin rai , bayan ya gama tattare wayoyin kaf ya kira babban yayanmu yace maza kasuwar tsaitsaye ka siyar min dasu , da guda² yake bashi wayoyin tare da faɗa masa adadin farashin da yake so a siyar da ko wace waya...

Shima Yayanmu cikin fargaba yace Baba ai duk kuɗin daka faɗa baza'a siya a haka ba , wata irin harara ya zabgaga mishi tare da cewa wannan kuma damuwarka ne , kai tunani ya rage ma yadda zaka siyar danni duk kuɗin dana faɗa su zaka kawomin a ko wace waya na faɗa maka , yana faɗin haka ya miƙe ya nufo ɗakina...

Da sauri Nana ta ajiye tsintsiya saida tayi masa sannu da zuwa ta fice daga ɗakin , bayanta yabi da kallo zuciyarshi tana ƙisima mishi wasu abubuwa , amma bai ansa sannu da ta masa ba...

Gefen katifa ya zauna kusa dani cike da soyayya irinta mahaifa yabini da kallona mai tattare da tsantsayar soyayya , murmushi nayi nima ina kallonshi nace Babana baka da kuɗine ? Murmushi yayi bai bani amsa ba , nima murmushin na sakeyi kamar yanda yayi sannan na jawo jakata ina cewa ni ina da kuɗi bara na baka...

Ansar jakar yayi tare da rufeta yana mai cewa nifa ina da kuɗi Mamana kinsan mage kota ƙoshi sai ta hari ƙwari , ajiye kuɗinki anjima zan ƙaro miki wasu , ajiye jakar yayi a gefena sannan yace Mamana tun kuna ku hamsin da bakwai har yau an wayi gari kun zama ku sittin ciff,

Tsoki yayi tare da kauda kanshi gefe yace tirr , wallahi da za'a tambayeni abinda nake so a musanya min da tulin "ya "yan nan ke kaɗai zan cire a cikinsu sauran a mayar min dasu daga motocin hawa sai ƙayataccin gidaje , ita kuma matar malam bahaushe ita dai burin ta kawai ta tara taron "ya "ya ita dai a mutu kawai taci gado , tou ban ajiye ba kuma bazan ajiye ba duk wacce ta haifi "ya "yanta taji da abunta ni babu ruwana...

Uhum Babana kenan mugunta kamar mai tsaron gidan yari , wato karya nema ya ajiye idan baya duniya a ci gado , hmm halin Babana saishi kallo nabi shi dashi ga wayyen mutum kisan boko ɗan gayu mai buɗewar ido yana da ilimin boko mai zurfi amma saboda tsabar baƙin ciki ko aikin gwamnati bayayi , tunda yaga ana ruguwar haifar mishi "ya "ya ya daina aiki ya koma caca...

Kallona yayi yace ki ɓoye sirrin mahaifinki koda bana faɗin duniyar nan , ki zama maimin addu'a bayan mutuwa ta ɗaukeni daga kusa dake , ki nunamin soyayya irin wacce nake nuna miki Mamana , ina miki soyayyar da duk duniya bana ma kowa irinta , banajin kunyar kowa idan nayi abinda ban kyauta ba amma Allah ya sani inajin kunyarki Mamana , babu wanda ya isa yasa nayi ko na bari amma idan har kika hanani na hanu , labarin waye Binna kuwa zan faɗa miki ne saboda abinda ya faru dake wanda ba'a san raina hakan ta faru ba , kuma ki yafemin na roƙeki ya haɗa hannayensa biyu tare da ci gaba da cewa kuma bazan sake tafiya na barki ba , ya ƙarasa maganar yana mai min kyakyawan murmushi ....

Riƙe hannunshi nayi tare da cewa kayi alƙawari ? Jinjina kai yayi yana murmushi yace nayi miki alƙawari , nima murmushin nayi tare da cewa nima nayi maka alƙawari Babana bazan taɓa tafiya na barka ba , yayi Allah ya albarkaci rayuwarki Uwar masu gida , da amin na ansa tare da gyara zamana , shima gyara zamanshi yayi sannan ya fara....


*ALIYU MUHAMMAD BINNA...*

Shine cikakken sunan da kowa ya sanni dashi , *BINNA* laƙani ne dana sakawa kaina shi bayan na shiga harkar wasan caca , dalilin binna kuwa saboda tsabagen neman asiri irin nawa , *BINNA* a binne kenan , dan da anyi magana kaza bazai yuwu ba , zance a binne shi kawai , tou idan nace a binne sai mutane suka fara ankara da abinda nakeyi dan haka sai nayi waiwayen damisa na zama Binna kawai dan ɓatar da mutane lissafinsu , sunan yana firgita kowa haka kuma yake bawa kowa tsoro duk wanda yaji ance *BINNA....* tou binna abin tsoro ne abun firgici tashin hankali ne ga duk wanda yasan Binna da irin rayuwar da nakeyi...!

Malam Muhammad shine mahaifina , Maryam wacce ƙauye yasa ake kiranta da mero itace mahaifiyata , matan malam 2 mero da sahura , mahaiyarmu itace ƙarama kuma dake ta daɗe bata samu aihuwa ba , ita kuma Sahura dama tuni ta kwankwatso ɗiyanta goma sha shidda , hmmm Babana yayi tare da cije haƙorashin na gefen dama ya karkace leɓunansa sukayi sama , jinjina kai yayi sannan yaci gaba da cewa "ya "ya sha shidda saboda haɗama sai kace wata kaza , dan tun kafin a auro Mero tuni Sahura tayi haihuwarta ta gama...

Mu talakawa ne na abin musali , kaf zuri'armu ba'a taɓa samun mutumin daya mallaki kaza biyar ba , kaf kauyen Ƙarara babu mutane masu talaucinmu , bamu gaji arziƙi ba kuma babu wanda yayi shi , kowa dai yanashan azabar talauci yadda ya kamata ,

Malam kuwa wutar talauci data isheshi ya rasa inda zai saka ransa saiya fara aikin tsubbanci , kuma sai Allah ya tallafa mishi domin idan yayi aiki kamar yankan wuƙa wuyar dai kafin yayi ne kawai , cikin ƙanƙanin lokaci sunansa ya fara ketawa yana zagawa kunnen jama'an duniya , yayin da mutane suka fara kiransa mai gobe da nisa...

Nanfa harka ta buɗe dan Allahn yace masa zama , tun abun bai fita ba har mutane suka fara shigowa daga cikin birni suna zuwa wurinshi , a tsabibincin nasa fa yakai maƙura kuma shekarar arziƙin nasa ya tsaya kalmar zama da Allah ya yaddar masa taci gaba da tabbata akanshi....

Malam fa ya fara tara abun duniya , liƙafa taci uban ta da , dan malam ba mutum bane mai rowa dan haka jama'a suka fara saɗaɗowa zuwa gidanmu cin arziƙi , cin nan 3 a yini tou fa idan mutum yazo zaici ya ɗinke har yayi guziri , shi yasa gidan namu kullum ya koma kamar wani gidan

1 Comments On KWARATA
avatar
muhd-habu

1 year ago

Reply

Nice

Please Login or Register in order to submit comment