Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abu ya gagara sawayenmu a likafa zan nado yata mu yi LABA, tunda ai du dadin riga bata yi ya wuyan hannu ba"

Da takaici Fadime ta ce" Dan Allah ki saurara da magana rututun nan haka, ke kinma gane me ake nufi ne?, Haba dan Allah Hindu me zai saka a yanzu da hankalina ke tashe ki karra tayar min har na fara tunanin ko kin haukace ne?"

Hindu ta dubeta ta ce" Ni kuwa nake da hankali, ras nake tunda ni a bayane nake gannin wasan!, Bari ki ji, idan kuka kiya da maganar nan ku tabatar cewa lalle zasu batar da mu din, domin kuwa har Habu da ya auri Hindu kanwar Fadime sai an halaka da makotan Hindu bale wata hindu kayan banza da yar yata da bata taka kara ta karya ba, a cen kauyenma neman inda zan gudu da ita nake yi dan Innar Aminu ta tsaneta Aminu kuwa ya yi mata asiri shege wuya uwa marikin lema!, Na takaice maki ta kife ko ta walare ni inada amsa wa UMUGHLUK ITIFAL, zan rusa na makoki ne na fada masa cewa wuka aka dora a wuyanmu cewa ko mu aminta da auren nan ko a karmu kuma ba za'a daina neman wace zata je ta karshi ba, muka ga mu masoyansa ne gwara mu shigo daga ciki, shi Habu sai a san yadda aka yi a mayar da shi makadain babar masarauta sai a bamu bukarmu mu rabe, a haka sai a raraka kafin Allah ya bamu Sa'a a kansu, domin kin ganni nan sai inda karfina ya karre walahi, numa fa yar gani a kasheni ce a kan Zakin sarakai, aure mun yarda ba sai an kashemu ba!"

Ikon Allah wanda ba'a saka masa rana, kallonta kawai suke yi, yadda take magana da karfinta gaba dayansu gani suke yi bara san irin abinda tske neman saka kanta da ita da yar tata ba

Jiki a sanyaye ya ce" Da ke za'a tafi gidan na yarki?"

Fadime ta yi dan tsaki tana dafe gaban goshinta dan takaicin HINDU ba zai taba kasheta ba walahi!

HINDU ta yi wani murmushi watsar tana kallonsa ta ce" To kai zaka rakata yaya? Ka san dai ba za'a je da kai ba, ka bari idan muka sayi gida sai ka kauro ko?"

"Innalilahi wa inna ilaihi rajune, abanta dan Allah ka tashi ka nemi wanda zaku yi shawara, idan kuwa bari zaka yi sai dare ya yi ka fitar da mu mu samu mu gudu to, ka daina magana da Hindu, hindu fa tunaninta daban da na mutanen kirki!" Fafime ta fada tana neman fashewa da kuka, ita kuwa Hindu ta tabe baki tana gyara zamanta , ita gani take auntun tata ce sam bata gannin me take nufi, ai walahi ko ana ruwan muzuru ba zata yarda a tafi da yar nan ita kadai cikin mayu ba!, Ina, ai tass za'a je da ita, basu sanni bane , basu santa bane walahi, ba zata taba yarda a dauki Nadirah a mikata ita daya ba, koda sun yi haka ita zata je daga baya a matsayin yar shishigin bayi!

A hankali Aban NADIRAH ya dakatar da matarsa dan baya so su fara fada a yanzu da zuciyarsa ke karye, bar ga Allah yana iya yi masu kuka

A sanyaye ya ce" To Hindu yaya zaki yi da yar taki? Ta yaya zaki shawo kanta?, Yaya zaki yi da hakkin Aminu? Shin kunna cin kudin Aminu kuwa?"
Caraf Fadime ta cafe ta ce" Ahaf, cin kudinsa ai sai dai kar a kuma kaima malan walahi da wani zance kake"

"Ki yi shiru mana Fadima menene haka ne?" Aban Nadirah ya fada a sanyaye

Hindu kuwa ta yi tsuru tsuru tamkar zata kifa

A hankali ta ce" Na shiga uku, riginar duka a Indina da Aminu take innalilahi "

Ta kalli Fadime ta kalli Aban NADIRAH

A hankali ta ce" Walahi ni dai ba zaku aikani fada mata ba in dan wannan nema kuke min rarashi ba zan je ba, yi abinda tace sai ta gudu idan aka hanna mata Aminu? Ai aunty ce kadai zata iya wannan aikin dan walahi abanta kaima kuka zaka mata dan na kula baka hanna kanka kuka yanzun, babu mai hadani da yata walahi" ta karashe tana sharar hawaye na gasken gasken ta dora da fadin" kuma mu bama cin kudin Aminu, Allah na tuba gori ba kyau ni fa na dora masa teburin da Indirah tace a bashi jari, kuma babarsa yanzu haka wannan cirar da kuka ga na mata mun gudo a bakin da baya karya na hi ance babarsa ta kai jaka uku da rabi kudin an gani ana so na yar makotansu, ai ba wani ciwon hannu da yake ihun ba zata masa auren dole bane ya sa na gudo da yata dan na shiryawa kowani dan iska da kyau, ni dai yanzu ta yata nake ba ta rigima ba da kike nemana da fada!"

A hankali Aban NADIRAH ya ce" Ku daina rigimar nan mana dan Allah, innar Indi kina nufin shi Aminun na Indinki ne za'a yiwa aure? Ya Allah "

Hindu zata yi magana muryar jakafiyar cikin gida da muryoyin maza biyu ta karade gidan da salama


A tsorace Fadime ta fara mikewa, hakama mijinta, bale da suka jiyo muryar NADIRAH tana fadin"











🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻
8/13/22, 22:57 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*

*LABARIN UMUGHLUK ITIFAL, BAN DAUKO SHI DAN CIN ZARAFI WA KASATA KO JAMA'AR KASATA BA, SALO NE NA MARUBUCI DAKE BUDE TUDU DA GANGARE DAN HADEWA A MAHADA GUDA, KO KUSA BAN GOGI ADALCI DA KARAMCI IRIN NA SARAKAN KASATA BA, NA KAMANTA RUBUTUNA NE A SAMAN IDEA DINA DAN KAWAI NA ISAR DA SAKONA DA KUMA SALON ALKALAMINA, IDAN HAR A RUBUTUNA NA TABO MASARAUTAR GARINKU KUMA ABINDA YA HAU KANTA BAI MAKU BA , KO YA YI DAIDAI DA HALAYAN DA KUKE FUSKANTA KU SANI BAN JE NA BINCIKA BA, BAN KUMA YI DAN NA CI ZARAFI BA, NA DAUKI ALKALAMINA NE NA KUMA YI AIKI DA DAMATA NA KASANCEWA YAR KASA, VIVE L'INDÉPENDANCE, VIVE LE NIGER, MERCI*



1️⃣5️⃣




A tsorace Fadime ta fara mikewa, hakama mijinta, bale da suka jiyo muryar NADIRAH na fadin" Aa gwara dai ku dakata din innata tace wanda ya wuce na wuce da shi, sirri suke yi"

Da rarafe HINDU ta fito tana lekowa ta ce" Ke zo nan zo" a ranta kuwa tana ayana 'na shiga uku Gimbiya da sara suka, kar ta ja a fasa'

Muryar Jakadiyar ne tana fadin" Ke kauce mana daga hanya ko mu babalaki aikomu aka yi wajen sarkin Dogarai!" Ya saka Abanta saurin fitowa yana dubansu yana kakaro murmushin dole ya ce" Jakadi yarki ce, ta wajena NADIRAH "

Da mamaki ta sake kallon NADIRAH dake tsaye tana sake turo baki

Murmushi ta yi ta furta" Masha Allah, Allah ya raya ya fitar da miji mai takaici"

Hindu kawai ta amsa sannan ta kama hannun NADIRAH suka shige daki suka zauna sunna kallon kallo

Jakadiya ta sake gaisar da su da mutunci, domin su din mutane ne da suka san darajar kansu kuma suke kiyaye dukkan abinda zai iya zubar masu da mutunci,

Bayan sun gama gaisawa ta dube shi ta ce" Mai martaba ne ya turo mu da kansa, yace ace da kai yana wajen sirrin da ka sani, ka je masa da sakon GAGARA yana son gannin idan ya cencenta, yace a ce da kai yana kan bakansa, maganar na nan daram yadda aka yanketa, yace ace da kai yana jira"

Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye ya amsata, yana kallo har suka tafi sannan ya koma yana kallon Fadime dake tsaye ta rungume hannayenta a gaban kirjinta

A sanyaye ta ce" Ana nufin, a tafi da ita bangarensa ya ganta?"

Kai ya gyada ya zauna a nan yana kallonta

Murmushi ya yi ya girgiza kansa ya ce" Anya na yi maku adalci kuwa? Anya ni din uba ne na gari kuwa?, Anya da na zauna a nan ina aikin nan na maku adalci kuwa? Sai nake jin dama dako na je na yi na ciyar da ku, sai nake jin dama buka na samu ko a ina ne na saka ku, na kasance tare da ku, anya ni din nan uba na gari ne kuwa?"

A hankali Fadime ta karaso ta tsuguna tana kallonsa, ta ce" Kai uba na gari ne Abanta, kuma kai miji na gari ne....., Ai inaga da saukima, ko menene inaga an dan rangwonta mana fa, domin da wani karnin ne mu din za'a fara batarwa, kashewa ko badawa a duniyar mahaukata, sannan a dauki y'ar a sakata a mugun aikin!, Abanta ina cike da tsoro, ni bana tsoron sanar mata domin ni nan zan sanar mata, abinda nake tsoro shine kar su rinjayeta, yarinya ce!, Ama in sha Allah, Allah zai kama mana, ni na yi imanin adu'armu ba zata taba faduwa kasa ba, in sha Allah zamu yi ta rakata da Adu'a, ko menene zai zo da sauki, bi'izinillah ba zata aikata abinda suke so ba, .....ka kwontar da hankalinka, a yanzu ka samu ka je da itan, idan kun dawo zan fita da ita, domin bana son abinda zai janyo mana saka ido, zan fuskanceta na fada mata gaskiya, mu da muka rike Allah? In sha Allah shi zai kama mana, shi zai daidaita mana, shi zai kare mana yarmu, kar ka sake sage min gwuiwa bayan na dangana Abanta"

Ajiyar zuciya ya sauke ya gyada kansa ya ce" A saka mata hijabi da nikaf mu tafi"

Ciki Innar birni ta koma ta zakulo lafcecen hijab dinta da nikaf dinta ta ba Nadirah fuska a hafe ta ce" Ke saka maza ki tarda babanki ku je nan ku dawo"

Sakawar ta yi ta fice suka tafi

Sunna tafia innar birni ta zauna ta fuskanci Hindu, a ttausashe ta ce" HINDU, ina so mu yi magana dan Allah, ta fahimta, ina so ki bani duka kaf hankalinki kin ji?"

HINDU ta zauna daga ninke kayan da auntyn tata ta barbazo tana kallonta

Fadime ta ce" HINDU, ina so ne ki fuskanci abin nan da fuskar da ya dace, ina so ki gane cewa a tafiyar nan rikicinta ya fi jin dadinta yawa, kuma ki sani ba za'a taba yinta da ke ba domin uwa ce ke, jinnina ce ke, Gimbiya ba zata taba yarda ki je ba, dan tana iya gannin zaki hannata aiwatar da abinda suka yi niya ne"

HINDU ta kalleta , alamu na hankalinta ya fara tashi da maganar karara ya bayana a tatare da ita
Muryarta a sanyaye ta ce" Ita daya? Ita daya za'a kai babar masarautar da sha yanzu biya yanzu idan aka kamaka da wani laifin? Ita kadai za'a mika wajen da take da kishiya? Yayya kishiyar take? Ita kadai za'a kai wajen da wasu zasunna zuwa sunna azalzalata aikata sabo? Idan fa suka cin mata?, Yaya zamu yi?"

Fadime ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Shi ya da da farko na so mu gudu, ama abinda kika fada din nan ki sani ya yi tasiri a zuciyata, na tabata dalilin wannan har makotanki sai sun shiga uku ba ke ladai ba, da a yi wannan gwara mu zuba ido mu rungumi Adu'a mu barawa Allah zabi,Hindu tabas abin nan ko uwar mata sai wace ta ginnu a kan kafafuwanta zata iya, sai dai kuma yarinyarki tanada adu'o'in neman kariya daga dukkan fitina, haka kuma tarbiyara da muka bbata ba ta kwadayi ko ta alfahari bace, sai mu dangana mu sake dukufa mu ringa fadawa Allah, na tabata wata rana idan da rai zata yi nasara, idan kuwa kadarar NADIRAH ce haka ina fatan kafin su cin mata ta yi kisa ita nata ran ya bar gangar jikinta........." Fadime ta karashe tana lumshe idannuwanta hawaye naa digowa daga ramin idannuwan nata

Itama HINDU, a hankali kuka ya zo mata, kuka mai rauni, mai matukar zafi, domin a da kwata kwata bata hango lamarin nan a haka ba, a yanzu da akai mata irin wannan karatun sai ta ji hankalinta gaba daya ya tashi tana neman ficewa daga hayacinta, tabas ba zasu taba yarda ta bi y'arta ba, a yanzun sai take ji dama basu zo birni ba, da zuwa ta yi ta ba innar Aminu hakuri aka yi auren nan, innalilahi wa inna ilaihi rajune, tabas abin na nemen rikitata, sai dai yayarta ta yi ta tausarta da nuna mata cewa basu da makamin da ya zarce Adu'a, ana karni na yanci kai ne, ama kuma karni na mai kudi shine sarki, bale sarkin da kansa a kan bafadensa? An yi wanda ya fi wannan zafima.


An dauki kusan awa daya da tafiyarsu sai gasu sun dawo, dawowar da suka yi a cikin mota mai sirri, watau mai bakin gilashi, da direba daya kwal su biyu a baya

Bai masu dogon bayani ba, ya taya su kwasar dukkan abinda yake na anfanin gagawa a garesu sannan suka bi shi bisa umarninsa suka shiga motar nan direba ya ja su,
Tafia ta dan lokaci kankanin da bai fi minti talatin ba suka karaso wani gida mai babar kofa da tsari irin na masu hannu da shuni , suka shige bayan ya sauka ya bude masu sannan suka yadda zango a sabon gidan babu mai yiwa dan uwansa magana sunna jiran abinda zai biyo baya, domin ko NADIRAH da ta tambayi innarta cewa nan kuma ina ne? Yaushe zasu tafi wajen bikin? Amsar da ta bata shine ta yi shiru bata son hayaniya yau, hakan ya bata mamaki ya kuma daure mata kai, innarta bata son hayaniya? Lalle akoy abinda yake faruwa, sai dai zata zuba masu ido ta ga koma menene



A gidan sarki kuwa da gadara ya yi kiran Gimbiya, a lokacin matarsa amarya ce ke tare da shi tana zuba masa abinci, a dole ta fita dan zai yi sirri da Gimbiya, zuciyarta cike da daci

Gimbiya na zuwa ta zauna saman kujera fuskarta a cinkushe, yau tunda safen nan da ta dauki mari take bangarenta kamar zata kone dan bacin rai, Dolema ta rikita rayuwar FADIME, ta tabata ta amshi mari daga mijinta ne dan ta mari FADIME ba dan wani laifin daban ba, mari a matsayinta? A gaban bafadensa?, Lalle lalle idan komai ya lafa sai ta yi dalilin da Fadime ta dawo yi mata bauta dan ta wanka mata ninkin ba ninkin din marin da mijinta ya yi mata!


Jus din da ya kai bakinsa ya ajiye bayan ya shanye ya gyara zamansa yana fuskantarta ya ce" Elle est tres belle, mais sauvage, l'a tu remarqué ?" ( Tanada mugun kyau, sai dai batada wayewa, kin kula da haka?)

"Wayewa, abu ne mai saukin koyo, duda jahila ce zai dan bada wahala sosai gashi waje a kure, rayuwar sarauta ce mai wahalar dauka Aban Bahija!" Gimbiya ta fada a tausashe tana sako sunnan Bahija dan ta ga reaction dinsa, domin rabonta da ta sako magana irin haka an jima

Juyowa ya yi daga kunna TVn da ya yi ya dubeta ya ce " Ba jahila bace, saukarta biyu in ji ita"

Baki ta tabe tana dubansa ta ce" Islamiyar kadai ta je, bata da boko"

Kafadunsa ya dage ya ce" Sai a gargadeta da budar baki da yin magana ko a gabansa ne, dan kar hakan ya haifar da matsala, an kai su gidan BAHIJA na yi magana da Lauyana cewa ya mayar sunnan mahaifiyarta a saman takardar"

Da mamaki ta zuba masa ido, a hankali ta ce" Gidan BAHIJA?"

Kallonta ya yi a kausashe ya cire idannuwansa da kansa ya mata alamun kwarai haka yake nufi

Zuciyarta sai da ta yi wani irin tsale ta daki kirjinta dan buguwa da faduwar gaba, sai dia bata yi magana da karfi ba dan ta kula ya fita hawa sama yanzu

A tausashenta ta ce" Ama gidan Bahija fa ka ce Aban Bahija?, Gidan da ka kashe makudan kudi million na gugar million la ginna shi?, Gidan da ka yi masa hawa hawa hawa ka zuba gazon ka yi masa ginnin a zo a gani kace na Bahija ne saboda ita daya ce mace cikin yayanka itace abin tausayi, sauran su nemi nasu maza suke shine zaka saka sunnan wata a sama?"

A kausashe ya ce" A da ba, a da da nake tunanin na isa da ita, a yanzu gaskiya kowa ya yi ta kansa kawai tunda har ni zata duba ta yiwa rashin kunya!"

"Aban Bahija, ka kiyaye, kar son zuciyarka ya fi karfinka wannan karron, domin ka san abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, kar girma ya fadi a kan abinda bai kai darajar haka ba!" Ta fad a dan kausashen itama, domin abin ya fara bata tsoro, gidan Bahijarta? Gidan da take takama da shi a cikin kishiyoyi? Bama a lokacin da ake kan ginninsa basu isa su hadu da ko daya ba sai ta yankawa mutun magana, bale a yanzu da aka gama? Da gadara gadara take dauko maganar gidajen sarki tace kaf ciki gida uku ne ya fi na Bahijarta? Lalle akoy tashin duniya a garin nan!

Zamansa ya gyara da shauki irin na yan duniya ya ce" Kina tunanin da abinda kike tunani ne gidan nan zan malaka mata?"

Kai ta juyar ta sake kallonsa ta ce" To nima shi na gani, me zai hanna ka saka sunnan Uban yarinyar idan ya so idan aka daura aka tafi da yarinyar sai ka maido sunnan Bahija a sama?"

Habarsa ya kama da mamaki ya ce"
8/13/22, 22:57 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*



1️⃣6️⃣


Jinjina da ban girma zuwa a gareku masoya, Allah ya karra lafiya da nisan kwana da rufin asiri amen



Habarsa ya kama da mamaki ya ce" Ke maman Bahija ki ji tsoron Allah, in ba abinki ba yanzu ai ba'a wannan kasadar, mace itace uwar ya'ya, itafa ba zata siyar da gida ba yayanta na ciki, shi yasa fa ake fada maku ku daina makahon so dan idan kuka ringa mika mana kudadenku da yan kadaririnku mun ga damar a kan gardama mu batar da su a dawo a shiga uku, shi yasa na saka sunnan maman yarinyar dan kar a je a dawo mijin ya siyar da gidan, sannan ke in banda abinki in kyautar abinda kike tunani ne ai ba dai wannan gidan ba, dan gaskiya na raina shi wa FATIMA, sai dai wancen gidan na nan gaba kadan , kuma da kuke cewa abu ba zai taba yiwuwa ba lamarin na Ubangiji? Da na zama sarki gadon Ubana ne? Sai ki ga abu ya zo da karar kwana, Sarkin dogarai ya tafi, a cikinku ke ko daya ta tafi, kin ga sai in kawo Fadima malan, mata su ringa tafe maza na rakiya da ido, Allah dai ya sa da sauran karfin yin aikin da ya dace a jikin maza"

Bata taba jin cin fuska da rikaken iskanci irin na yau ba, a matsayinta, da kimarta, da isarta, da kyanta mijinta ya ringa magana irin wannan a gaban idannuwanta? Ashe haka abin yake da ciwo? Idan zata tuna shekarun baya da ta hada matansa da lalurar rashin anfanarsa a saman bed a gaban idannuwansu yake kodata da mata kirarin da sai dai ta ga sun sada kai, ashe haka abin yake?
Mikewa ta yi tana gyara alkyabarta, domin ba zata iya ci gaba da maganar nan a yanzu ba,

Har ta juya ta jiyo muryarsa yana fadin" Ki tabatar WA'INDA zasu bata kula dan gyaran mu'amalarta sun iya kuma sun iya rike bakinsu, gyaran amaryarnan da ake yi ai ita yar nan inaga bama ta bukata, yarinya da ace a gidan hutu ta tashi har an shiga uku da kallonta, ni da kaina saura kirissss nace alfarma aka yi masa yaron cen!"

Zuba masa ido ta yi, gashi dai shekarunma sun ja fa, ama tatacen iya shege a gindin bawan Allahn nan,
Murmushi ta karkaro mai daci a ranta ta ayana' Lalle baka san kaidin mace ba, da ka wulakantani da kula baiwarka ko a dadironka ce gwara na kumsa maka shinkafar bera ka ci ka kumbura ka fashe a dakinka, dan walahi mutuwarma ba zan bari ka yi mai daraja ba tsohon najadu!, Gida kuwa karya kake ka ba wata katuwa yata a raye a zaune ita ta tashi a banzar bazara kennan?"

A bayane kuwa sai ta yi murmushi ta ce" Du ka rikice Aban BAHIJA, bayan baiwa sunnanta baiwa"

Murmushi ya yi yana janyo abincinsa ya ce" Hakane, sai dai wata baiwar cike take da BAIWA, abin saima an dangana da room din ciki"

Da sauri ta yi gaba, ta fahimci yau banda yan wulakancin harda yan iskan ke kansa

Tana zuwa bangarenta ta saka aka mata kiran masu gyaran jiki da lamura na gidan sarauta, bata haye bangarenta ba sai da ta ja masu rikaken warning ta kuma sheda masu aiki tukuru, kar su ringa hutawa sai na cin abinci ko yin sallah idan sunna yi, kar su barta ta huta sai sun gamsu da yannayinta, gyara na waje kadai ba sai sun yi mata na ciki ba domin ba bukata, sannan su iya bakinsu, sai nan da kwana goma za'a dauko su

Tana shiga sama ta bude whatsup dinta ta masa magana a kan matansa da kuma ya'yansa, sosai ta tuna masa me suke son boyewa sannan ta sheda masa cewa ya yi da gaske idanma ba hali kawai ya fitar da su waje, sannan ta kashe ta ringa kai kawo zuciyarta na mata daci, da gaske fa magangannunsa sun mata zafi fiye da tunanin bawa, haka kuma maganar gidan nan ta daga mata hankali, sai dai ba komai zata bi abin yadda ya dace, idan ya yi wasa sai ya wayi gari ya ga wata gagarar ta gagareshi! ( Ku dai kuka sani ku kashe kanku )



________________________


*AGADAZ*

Lulumin da aka wuni da shi jiya har aka kwana da shi wayewar yau ya saka yawancin jama'ar garin hutawa, idan har ba aiki nw da kai a cikin masarauta ba to fa kana hutawa ne, domin sanyin garin ya hadu ya bada wani irin sansanyan ni'ima mai tada tsumin mai mata, ya rikita gwauro

A irin wannan lokacin, a cen cikin dakinsa ya gaji da murmususun tashin hankalin dake jikinsa ya mike cikin nutsuwa ya watsa ruwa sannan ya sha lipton mai zafi ya saka sasaukar sutura ya fito daga dakinsa yana duban agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yana tunanin Anya yau zai samu zaman da yakan yi da Auta kuwa? Ya tabata itama tana cen daki ta labe dan bata son sanyi, gashi irin ranakun nan da baya fira fada, baya amsar korafin kowa yake samun zama da ita su yi hira da wasa da dariya

Karar TV ya saka shi dakawara daga sama ya dubi kasan dan gannin wa yake kallon a falonsa? Ya tabata ba zai wuce cikin mutun ukun nan ba, dan su kadai sukeda wannan damar a masarautar, ta shigowa Falon nan kansu tsaye

Ido ya dan zarro gannin abinda yake hange, watau su ukun ne gaba dayansu a zaune a falon, harda su TV? Ikon Allah

Kasancewar jalabiya ce mai ruwan milk colar a jikinsa sai dan ta karra haska farar fatarsa sabbaj ta lafe a jikinsa kadan har ana iya gannin farar rigar dake ciki da kuma wandon rigar da bai idasa masa har cen idon kafa ba

A nutse ya idasa saukowa, dukkan hankalinsa akansu , a lokaci daya kuma Umma da matarsa suka mike dan girmama shi da yi masa barka fa saukowa, Auta kuwa ta sauke ajiyar zuciya murmushi na wanzuwa a saman fuskarta ta dago daga rubutun da take yi da larabci tana kallonsa

A tausashe

Please Login or Register in order to submit comment