Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

je dakinta ai in dai dubawar da nake tunani ce sai a daka ko?"

Ita dai Matar SHEIK biye take da su, baiwar Allah NADIRAH da kyar take takawa, wajen ne ya karra yin tsami, ga rikicin dake damun kanta mai yawan gaske

Bakun makeken gadonta mai kalar gidan sarauta ta zauna tana sada kanta, Inna ta yi murmushi kasa kasa ta ce da Matar SHEIK " baea na barku, zan zaga bayi cikina ya fara murdawa"

Da ido ta rakata sannan ta maido dubanta Kan NADIRAH

Dan murmushi ta saki ta cire hijabinta da nikaf dinta hakan ya bayanar da nutsatsiyar kamilaliyar fuskarta

Jakar ta bude ta dauko safar hannu ta likitoci tana kallonta ta ce" Bismillah Allah ya karra maki lafia"

NADIRAH ta dago tana kallonta, Bismillah me?

Matar SHEIK ta karasa tana fadin" Baya zaku kwonta sai ki cire wandon ki janye rigar baya na duba da kyau kin ji?"

Ido ta zarro da matsanancin faduwar gaba da tsoro
Bakinta har yana rawa ta ce" Na cire wandona kuma? A kan me za'a wani dubani? Babu abinda ya sameni fa ni"

Ido ta zuba mata itams, karara ta fahimci ko me yake damun Yarinyar

A hankali ta zauna cikin yaren French ta ce" Excusez moi, je ne me suis pas présenté, je suis LUBNA MUHAMMAD, je suis la 4eme femme du Cheikh, et je suis médecin gynécologue je suis enchanté de vous connaître et je serais honoré d'être votre médecin " (Ki yi hakuri, ban gabatar da kaina ba, sunna na LUBNA MUHAMMAD, nice matar SHEIK ta hudu sannan ni docter ce a fannin mata, ina farin cikin sanninki, sannan zan kasance cikin farin cikin zamtowa likitarki)

'kan ubancen kayasa' shine abinda zuciyar NADIRAH ke ayannawa a lokacin da ta kure bakin wannan yar gayun dake yi mata yaren aljannu tana makokwaltu da baki tana hirar da sam bata san me take nufi ba har ta dire maganarta tana sake kallonta

Wannan lamari ya saka LUBNA dan sake karantar Nadirah

Magana ake a kan matar da aka ce ya ce a wajen sarkin Tanut, ba zata taba kawo cewar bata ji yaren da ta yi mata ba, sai dai ko kawai bata yi mata bane

Sake sasauta muryarta ta yi a sanyaye wannan karron da hausa ta ce" Allah ya huci zuciyarki, idan har na bata maki ki yi hakuri dan Allah, idan kuwa wani likitan kike so a kirawo bara na koma na sanar sai a kirawo ko wani likita kike so in sha Allah"

Kasa kasa NADIRAH na rage girman idannuwanta da sansanyar muryarta ta ce" Likita kuma? Ya min me?"

Matar SHEIK ta fuskanceta da duba irin na tsanaki, a hankali ta dan kara matsawa kusa da ita kadan ta ce" ki yi hakuri Hajia, kin san wajen nan waje ne mai matukar hatsari, waje ne da ba'a so a yi wasa da shi, bale ke da iliminki da hankalinki, idan har ya zamto an yi wasa da wajen nan kuma ya raunata akoy katsala, kin ga a wannan fannin ba maganar ka ji kunya, domin ciwo ne, idan ya giga kaine ka shiga uku, idan ya zama gagarare kaine a babar matsala, zai iya gagaraka shiga mutanema bale har ka anfana da shi, yana iya hannaka zaman aure gaba daya, shi yasa nake so ki bada hadin kai a duba ki, a duba wajen dan kowace mace da kika gani ta haka ta girma, wata bata samun matsala kwata kwata, wata kuwa tana samun matsala kadan ne da ruwan zafi kadai ya isa ya warkar da wajen, watan kuwa har tsagewa take yi watau ta damu karuwar da sai an yi mata dinki kin fahimta?"

A tsorace ainun, a matukar tsorace NADIRAH ta sake rage amon muryarta tana sada kai irin bata son hada ido da Lubnar nan ta ce" Hala kin san abinda ya faru da ni?"

Itama LUBNA sai ta samu kanta da kafeta da ido, a zuciyarta kuwa tana ayana wai me yake faruwa ne?,
Turewa ta yi ta fito mata a mutun ta ce" Ba shine sanadiyar kirana ba? Ko ba kin kawo budurcinki bane?"

"Innalilahi wa inna ilaihi rajune, wayo na shiga uku kin ga, ki yiwa huwa rahamanu kar ki sanarwa Innata maganar nan, wayo Allahna bayan cin amanar kuma yamadidi ASADEEK zai yi da ni a duniya? Oh ni jikar mutun hudu na ga rana" NADIRAH ta karashe tana riko hannun LUBNA wace ta kusan zurmawa da gudu da ta ji sunnan da ta kama da kukan da take yi

NADIRAH ta dora da fadin" Amanatul amana maganar nan, kuma abinda kika fada da yaren ko shima dai maganar wannan din dai ne?"

A hankali LUBNA ta shiga tuna kiran da ya samu SHEIK a lokacin da suke zaune shekaran jiya da dare , kasancewar wayarsa ba wani rikaken sirri ne da ita ba, domun sun sha fada masa idan zai yi maganar sirri a cikin mutane ya ringa fita, wayarsa tanada amsa amo mai dan karfin da mutun mai kaifin ji zai iya jiyo hirarsa,
Maganar da ta san ta ji daya ce kafin da hannu SHEIK ya mata alamun ta bashi waje, watau *WACECE SUKA AURA MIN?*

Sake zubawa NADIRAH ido ta yi, a hankali ta koma ta zauna tana tunani da kuma ba kanta amsa
A nutse ta sauke ajiyar zuciya tana sake duban NADIRAH
Bata jin French, bata son a san baban abinda kowace mace zata iya yin tinkaho ace itace ta wayi gari a haka, kuma ta kama sunnan UMUGHLUK ITIBEL

Ajiyar zuciya ta sake saukewa, a nutse ta yakice tunanin nan, tana karra tanatarwa kanta cewa babu ruwanta a wannan lamari, dan haka sai shiga assuring din NADIRAH, cewa babu wanda zai sani, ai sirrin likita da marar lafiya tsakanin patient da docter ne, sannan ta sake bata hankalinta gaba daya tana sake kwatanta mata girma da darajar abinda ta kawo da kuma maganar dubata, a kalla sun dauki awa ana abu guda, daga karshe ta yarda ama sallar da bata yi ba sai da ta yita kusan sha biyun rana tana ayana ba laifinta bane na maci amana ne, sannan ta zauna gaba daya hankalinta ba wani a jikinta ba, jikinta du ba a sake ba da kyar da walahauli ta iya bude jikinta LUBNA ta dubata

Da tausayawa take yi mata bayani kamar Haka" Alhamdulilah baki yi kariwar da sai an maki dinki ba, sai dai kin yi mugun jin jiki ta yadda sai kina shafa maganin da za'a kawo maki sannan kina hadiye na hadiyar, domin wajen daga ciki ya kumburo hakama daga fatar gefe da gefe sannan kin dan karru kadan ba sai an dinke wajen ba, ki samu isashen hutu sannan ku ringa anfani da ruwan dumi kina zama a ciki kin fahimta?"

NADIRAH taa gyada kanta kasa kasa ta ce" Ama dan Allah idan an kawo maganin a yi dabara kar innata ta gane"

Murmushi kawai LUBNA ta yi , sai kuma ta dauki hijabinta da nikaf dinta ta mayar tana gyara kayanta ta ce" Barana na koma da kaina na amso na kawo maki"


Itama ta ji dadin haka , dan haka ta kilacewa LUBNA kayanta a cen cikin adaka ta juyo tana tafiya a hankali sai ga Innarta ta sake faduwa hannunta dauke da kwano yana tururi , watau hanji ne aka rababaka ya samu dahuwa mai daraja yana ta kanshi da tururi

Direwa ta yi a gabanta tana fadim" Yi maza rarabakeshi da zafi zafinsa zai fi warware maki yan hanji, yauwana bayin cen akoy irin bahon bayina na wanka ko? Ko sai na dauko katuwar roba?"

Naman ta dauka, domin yinwa take ji sosai , saima da ta ganshi ta ji yinwar ta sake sheda kanta ta janyo ta yi bismillah ta fara motsa shi tana kallon miyar da tunanin dama ace ta samu nono ne, da ta morw walahi, ama abin nan idan ka ci ai nauyi zai maka a cikinka sosai

Innarta kuwa bata tsaya kulata ba ta shige tana dudubawa

Jim kadan ta fito tana kama haba ta ce" Ke bayinki ta fi tawa girma ko me yasa?"

Nadirah ta dage kafada tana raunar hanta tana kallon Innarta

Wucewa Hindu ta yi ta fice a dakin ya koma kicin dan ruwan zafi ta dora tana gadin ruwan tana dariyar Auntunta, wai daga sanar mata abu sai kawai ta katse kira ta labe🤣🤣🤣, gaba dayama ta ki yarda su yi maganar wai kunya, yo ita yau ai shagali nata walahi, abu ya fara kankama sunna shawara da matar SHEIK? Uhum,

Ruwan na fara tafarfasa ta juye a katon bokici ta kinkima ta koma dakin ta wuce ta yi tsaye tana ta tunanin yadda zata tara ruwa a abin nan kamar yadda matar SHEIK tace

Kai kawai fitowa ta yi ta koma ta dauko katuwar roba ta kai bayin ta zube ruwan ta sirka shi, ama fa da zafinsa walahi sannan ta fito ta yi tsaye kan yar cewar ta taso maza ta je ta shiga ruwa ta tara mata
A wannanma sai da aka yi da gaske, sai da HINDU ta dage sannan Indi ta tafi, haka kuma wajen shiga ruwan da kyar ta iya zama domin ya mata zafi kuma Innarta tace walahi tana sauraronta idan ta karra ruwa zata shigo ta zaunar da ita
Ziciyarta na mata suya, tana cike da tsoron shikenan, kennan Innarta ta sani? A haka ta yi ta gama ta fito da jalabiyar tasa tana kallon rigar da Innarta ta ajiye mata ta dha turare

Hanci kawai take ja ta saka rigar ta haye saman gadon jikinta da zafi zafi tana sauke ajiyar zuciya

Bata jima ba Matar Sheikh ta dawo da maganin innarta kuwa na biye da ita a baya dauke da jarka irin katuwar nan yelow tana murmushi ta ce" Ga nono Indi an turo maki "

Ido NADIRAH ta zubawa nonon, innarta ta ajiye ta fita dan dauko abin zubawa

A hankali Nadirah ta ce" Waye ya bada wannan nonon?"

Lubna dake balo mata maganin ta ce" Daga bangaren UMUGHLUK ITIBEL ne aka kawo"

Baki ta tabe bata ce komai ba, ita kuma ta bata na hadiyar ta sha da kyar sannan ta bara mata na shafawar ta tafi ta shafa da kanta tana sake jin kamar duniyar tai mata zafi ita kam, kamar duniyar gaba daya zata kifun mata ne haka take ji

Dawowar innarta ya sakata barkewa da kuka , tana jin barci na fuzgarta ama ta riga ta faka garin rigima tana kallon Innarta dake zama tana sallalami da tambayar meye kuma ta ce" Inna, walahu ba zan iya karasa aikin nan ba, ba zan iya ba, gida nake so, innata gida nake s............











🧐🧐🧐🧐🧐🧐
8/26/22, 02:01 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





'4️⃣1️⃣




Da sauri innarta ta zauna tana ajiye abinda yake hannunta tana furta" Subahanalah subahanalah subahanalah, Indi gida kuma? Mun gama abinda ya kawo mu ne?"

NADIRAH ta kwontar da kanta saman cinyar innarta tana wani hakin kukan tana fadin" Ba sai mun gama ba, dan girman Allah ki mayar da ni gida Innata, ba sai mun gama komai ba, kawai Allah zai kare shi, mu bamu isa mu yi masa kariyar komai ba!"

Cikin sigar rarashi innarta ta saake tausasa muryarta ta ce" Ama, me ya yi zafi haka da baa wuta ba?, Kyan alkawari fa cikawa, me yasa mun taso mun zo har mun gano wani abu a zamansa da mutanensa zamu zubar mu tafi? Ai hakan ba daidai bane a tunanina, bamu yiwa kanmu adalci ba bale shi mu yi masa, haba kema Indi, me yake damunki ne wani lokacin sai ki rikice kamar ba ke ba?"

NADIRAH ta lumshe idannuwanta domun kanta har sara mata yake yi, muryarta a cinkushe, barcin nan na fuzgarta sosai ta ce" Ban zo gidan nan dan wannan ba, Innata ban zo dan na lasance kazar cikin daki ba, kyan alatun dake zagaye da gidan nan baya cikin tsarin abinda ke iya sakani ni NADIRAH na ji zan iya zubar da komai da na gina na farin cikin rayuwata a nan ba!, Innata bana jin zan iya rayuwa a wajen dake zagaye da munafukai mafi soyuwa a zukatan masoyansu ba, hasalima irin haka ya saka nake guduwata wajenku, domin ban.........ban..........innata Aminnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnunnnnnnnnnnnnnnannnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnn
........" Sadakawar muryarta, daukewar muyarta, da sakuwar jikinta da fitar numfashinta tamkar na dan jariri ya saka innarta lumshe idannuwanta tana sauke ajiyar zuciya da dauke hannunta daga saman kirjinta a hankali tana dan karra kallon Fuskar NADIRAH

A hankali ta shafa gefen fuskar nata sannan ta mike kadan ta gyara mata kwonciya ta luluba mata abin rufa ta fice jiki babu karfi ta koma baban falo

Tana zuwa falo ta tarar da Umma zaune tana amsa waya kafarta daya kan daya cike da gadarar nan

Har ga Allah sai da ta ji gabanta ya yanke ya fadi, jiki babu karfi ta zauna saman kujera ta samu kanta da zubawa Ummar ido tanna kallonta, kallon nan mai kama da kana karantar mutun, kana son gane wanene shi a fasarar badininsa, irin girman waye shi ne a duniyar da ka ajiyeshi

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana cire dubanta ta dora a kasa

Tunda take, bata taba jin tsoro tsoro, firgici firgici, na wannan lamari ba irin na Yau
Aminu? A yanzu da wannan gagarumin abu mai daraja ya wanzu, wanda yake abin a wuni yau ana sukuwa da dawakai a cikin fadar nan dan murna da farin ciki, abindaa take cikin tunanin shin yaya wannan bawan Allah yake cikin farin ciki aa yau? Dama tunda ta ji an fadi maganar nan ta cewa Yayarta walahi ita ta tabata lamari ne na sihiri, ita fa ba zata yarda bama ta tura yarinyarta gidaan sarauta babu tsari, mamakin da take yi, mahaifan HUZNAH a labarin da suke tsinta daidaiku ance shi sarki ya auri yar sarakai ne, yaya aka yi suka miko yarinya gidan sarautha baabu tsari? Rayuwar nan da ta zama abinda ta zama yau ko gidan wani dan karamin mai kudi ne ai ks nemi taimako a wajen bayin Allah wa'inda suka riki ayar Allah kan a karra baka daga hasken addu'a tsari dan yaron ya je ya zauna da nutsuwar zuciya, ba wai ta malake miji ko yin yadda aka so da miji ba, aa wannan fa karya ne, ita babu ruwantama da wannan, lamarin karyar?, Shirme ne gaba da baya bata cikin wannan tafiyar gaskiya, ama a yi gyara, a iya girki, a san tsafta, a iya girki, aa iya kisar gyaran aure da iya yiwa namiji hira, uwa uba talabarsa a fagen da daga ke sai shi ki sakashi ihun jariraima watau wannan na kuryar makogwaro mai kama da kukan tinkinyar nan du abu ne da ta rika da karfi take kuma gannin komai hali irin na namiji da ake kadawa ba zata saki wannan ba domin darajarta ce ta ya mace, namiji kuwa ya kada iya shegen mana, ai kowa da irin rawar da Allah ya bashi ikon takawa, in ba dan tsoron kar a mutu walakiri ya mumuke bawa a cikin duhu ba yan rabiya bama ai da ta bi bayan habu, yanna kada gangar tana ana bakace,

Firgigit ta dago jin muryar Umma na fadin" Hajia lafia kuwa?"

A hankali ta ce " lafiya kalau, na gaa kina waya ne"

Umma ta sake zuba mata ido ta ce" Aa gani na yi ina ta magana shiru kamarma baki san ina yi ba?""

Inna ta kade maganar tana yin dan murmushi da daukar kafarta daya ta dora saman daya tana ji a ranta inama idan ta rufe wannan abar da duka za'a gane yarenta?

Umma ta sake fadin" Cewa na yi, da nace ba zan ringa yawan shigowa ba, dan na fahimci hakan da nake yi yana hadasa mana rashin jituwa, to ama sai na ga yau gaba daya du irin tsayuwar nan da muka yi a kofar mai baban fada bata leko ba, bayan HUZNAH na tsaye tunda safe sai da wancen munafukin ya sanar mana lafiya kalau muka watse, kin san gidan nan ko me kake yi a ido kake, ana binka ne da kallo ana fahimtar me kake yi, ta haka kake shiga ran bayi idan suka ga mu'amalarka da uban gidanka, ta haka manyan barori ke baka daraja har su ji du duniya kaine uwarsu, mu da muke so mu siye kowa ai ba zamu yi wasa da irin damar nan ba, koda nace zan fita a harkar matse mata waje dan na ga yana neman hadasa mana rashin jituwa, ama dole na ringa lekowa idan ta kama dole, domin na ringa sanar mata manyan sirika irin na sarauta wa'inda bakon gidan nan ba zai taba sani ba"

A hankali Inna ta dauke dubanta tana sake tausasa dubanta a kanta ta ce" Hakane, ama sai na ji har kamar hankalina zai tashi da jin wai zaki ja baya dan dan abu ya faru wanda yake abu ne da ko a gida yana yawan faruwa da manyan mutane da ita, jta fa matsalarta kawai kar a shiga gonar iyayenta, idan har ka kiyaye wannan babu mai dadin zama irinta, haba ranki shi dade ina ita ina rasaki a gefe bayan kece uwa kece uba kece makarbiya tata? Kece fa ja gaban tafiyar nan, idan har hakan ya bata maki ki yi hakuri in sha Allah zamu kiyaye, yanzu haka rashin fitarta dan bata sani bane, nan fa muka wuni da ita yanzu barci ya nemi kifata da kas sai ta shige ta kwonta, tana farkawa zan sanar mata fa ga baban sake sai ta je idan lokaci bai kure ba"

Umma ta wani saki murmushi, babu abinda ya fi dadada mata sai jadadawar Hindu cewa itace gaba daya tafiyar nan, uhum tana jin dadin ace itace komai fa a waje, tana matukar kishin ace wani ya kamo kafarta ko zai gogi wajen da take sarauniya ce, take mulki a wajen, ba zata taba manta a lokacin da ran mahaifiyar ASADEEK, idan matar na tafe tana take mata baya sai ta ji kamar ta saka hannu ta maidota baya ita ta shige gaban

A gadarance ta ce" Na yafe mata, ai ba zan jima ina fushi da ita ba, sai dai a yau kar ta fita, zan san hanyar da zan bi na goge tunanin da bayi ke iya farawa da jama'ar babar masarautar, ai sallar BIYANO ke tunkaromu, zan gani abinda ya dace a yi dan ta karra siyan zuciyyoyin WA'INDA suka isa su fada magana ta yi tsauri"

Innarta ta karra gyada kanta ta yi shiru ta koma tunanin abinda zai fisheta har Umma ta gama yatsine yatsinenta ta mike ta tafi

A hankali ta koma dakinta ta zauna ta shiga buga wayar Fadime

Ta yi bugawa ya kai sau uku da kyar aka daga
FADIME na dagawa kasa kasa ta ce" Wai HINDU meye kuma?"

Inna ta yi murmushi tana sauke ajiyar zuciya ta ce" Ba maganar abin dadin bane zan maki, maganar da nake son yi maki Aunty a kan Indi ne, kin ga hankalinta a tashe yake, gaba daya rikici take yi wai mu koma gida, ta tsorata da shi ne inaga, kuma bakinta har yanzu yana ambaton sunnan Aminu wai, bana so kai tsaye ta tona mu fa? Kin san Indi kuma idan hankalinta na tashe komai yi take yi"

Shiru ne ya wanzu na dan lokaci, a hankali Fadime ta ce" A tsorace take sosai ne?"

Hindu ta ce" Gaskiya a tsorace take, domin ban taba gannin cutar da ta kwontar da ita haka ba, kina gani fa ko ciwo take yi tana tsaye a kan kaffafuwanta ne, ama yanzu sai a hankali"

"Shi din, ba cewa aka yi bashi da lafiya ba?, Ko ta ji ciwo ne?" FADIME ta fada da kyar kunya na lumlubeta, dan so take yi ta fahimci damuwar yarinyar

HINDU ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Kamar baki fahimci abinda na fahimta ba, kamar baki zauna a gidan sarautar ba, ba maganar rashin lafiya, kitumurmura ce ai malan ya fada min!"

A hankali Fadime ta sake fadin" HINDU hala banda amsar maganin har wajen boka kika je?"

Shiru Hindu ta yi, sai kuma ta ce" Kashhh, a bar maganar kawai ama ba ni na je ba, Habu na aika gaskiya, kuma ban yarda da maganar ba dai, na dai shirya diyata ne shikenan"

Ajiyar zuciya ta sauke, a hankali ta ce" Kina ji?, Dole zaki sanar mata cewa ko me yake yawo a cikin kanta ya dace ta daidaita tunaninta ta gyara harshenta ta kiyayi kama sunnan wani da auren wanu a kanta, Dole zata bar maganar nan dan kar ta kona kanta garin shirmenta, Dole zata daina tunda tana jin tsoron Allah taba kuma burin gobe kiyama ta samu sakamako mai kyai, aure ibada ne, ba abin wasa bane, du D'a na halak zai kiyaye yin wasa da igiyar aure, ido zaki murje ki fada mata gadkiya, sannan ki sakata a hanya kawai ki yi kamar baki gane komai ba dangane da yarenta, sannan idan da hali kar zama tare da su ya gagareta, ta koma hanyar da aka dorata sannan ta dora daga inda ta tsaya...."

HINDU ta sake sauke ajiyar zuciya, hakan ya saka Fadime a tausashe ta ce" HINDU, na san a gaban matsalar yarki baki da karfi ko dabara, ina so wannan karron ki jajirce kin ji kanwata?"

Kai take gyadawa tamkar yayar tata na gabanta, haka kuma ta ji ta samu kwarin gwuiwar tarban yar tata

Mikewa ta yi ta koma falon tana ci gaba da tsara yadda ya dace ta biyo da Yar tata dan samun kanta, bama baban rikicin watau komawarta dakin mai babar fada


...........................................................
8/26/22, 02:01 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





4️⃣2️⃣




A nutse Sheikh ke yi masa bayani, bayani ne yake yi masa dala dala ta yadda zai fahimta, bayan zamansa a fada da taron da suka gabatar bayan sallar La'asar suka shigo falo,
SHEIK ya dube shi yana fadin" Rabonka da zagaye kauyuka irin su Itar, Timiya, titibe ka jima, akoy dukiyarka a cen na kiwo da noma da ake gadi, ka kuwa san garken rakumanka sun zama arba'in da uku a garin Timiya?, Ya dace ka je ka ga yadda arzikin ya yabanya UMUGHLUK

ASADEEK ya yi dan murmushi bai ce masa komai ba

SHEIK ya sake zuba masa ido a hankali yana kallonsa, a nutse ya ce" Kamae baka jin abinda nake fadi fa?"

ASADEEK ya sake dubansa , a hankali ya ce" Allah ya bamu iko"

SHEIK ya amsa da amen, sannan ya ce" Maganar da na yi maka dangane da rike maganar nan sirri ina fata kana kai?"


Asadeek zai bashi amsa aka sanar da shigowar UMMA

Shigowar Umma dauke da wani gora mai dauke da rubutu ya saka SHEIK yin shiru yana kama kansa hadi da maida dubansa wajen TV yana dan kallo duda ba magana dake fita ta tvn sai hotunan larabawa dake karatu kawai


Zaunawa ta yi cike da isa ta gaishe da Sheikh bayan ta gaishe da ASADEEK tana cire kanta a barin SHEIK din
Kwata kwata a duniyarta ta tsani wannan malamin walahi, mutun ne shi mai shegiyar akida da dan banza iya yi wai shi SHEIK, ta yi kisar, ta bi ta kasan kasar dan ta hadasa masu fitina har ya kore shi ama ya gagara, akoy lokacin da ta so kakaba masa sharin zina karshe ya aure matar ta zama sirri a gareshi, idan ta shigo wajen da yake gaba daya sai ta ji ta tsatsamta da shi, kwata kwata ta tsane shi walahi, wannan fa shine mai yin shahada idan za'a kashe mai aikata laifi irin nata, shine mai jawo masa ayoyi kala kala yana bashi fasara shi kuma yana zartarwa

A dan gagauce ta sanar da adadin kudin da take da muradi saboda kicin , domin kiri kiri HUZNAH ta

Please Login or Register in order to submit comment