Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

6️⃣2️⃣



Kallonsa take yi kamar zata dauke shi da idannuwanta,
Jiki babu karfi ta mike tsaye tana gyara alkyabarta, sai kuma ta sake juyowa tana kallonsa fuskarta na raunana
A sanyaye ta ce" In tafi?, Shikenan ba zaka sanar min wani irin yannayi kake nufi ba?"

Idannuwansa da sam kwanakin nan basa rabo da dan jaja jaja ya sauke a kan fuskarta

Mikewa ya yi tsayen shima, hakan ya sa tsayinsa kere nata sosai

Yana kallonta ta kasan idannuwansa, muryarsa na fita a azance ya ce" Ban san me zan ce ba HUZNAH, ban san wani irin yannayi zan kirayi abin ba, abinda na sani shine damuwar dake damunmu tsayin shekaru goma a jikinki ne take ba a jikina ba"


A rarabe ya ajiye maganar, sannan a lokacin da ya ajiye din kwayar idannuwansa mararsa tsoro sai da suka kauce daga cikin nata dan jin nauyin furucin, hakan ya sakata tsure jayen lebunansa da ido tana son gane me yake nufi bata ko kiftawa

A hankali ta ringa jin faduwar gabanta na dan son ta fi karfinta
Da sauri ta ture tunanin dake cikin zuciiyarta ta hanyar dan yin dan murmushi tana kallonsa a hankali ta ce" Cutar dake damunmu? Wace cuta ce wannan............................"
Sai kuma ta dakatar da furucinta, a hankali ta dago idannuwanta ta saka a cikin nasa domin ya dake juyowa ne yana kallonta
Irin kallon da yake yi mata ya sakata saurin bude bakinta dake dan barbarbar yana rawa kamar mazari , sai kuma ta mayar da shi ta damke shi, ama kuma hannayenta ne suka amshi rawa a hankali a hankali har ta dago su tana kallo,
Shima hannayen nata yake kallo zuciyarsa na neman babalewa dan bai san ta yaya zai iya dogon magana da ita a haka ba

Yanzu fuskarta ba alamun murmushin dazu , ta sake dubansa ido cikin ido , muryarta na crakng ta ce" Husband......., Kan nufin cutar dake damunmu, wace ta hanna mana kasancewa daya, wace muke zaune cikin kunci sanadiyarta......a jikina take? Like a jikina kadai ne kake haduwa da hakan?"


Dara daran idannuwansa ya sake saukewa a kanta, tarin rauni da duba irin na nagarta yake yi mata, hakan ya sakata jin zuciyarta ta yi bugawar da tana da hawan jini ta tabata da a yau sai ta tashi da shanyewar barin jiki

A hankali ta damki damtsen hannunsa sakamakon tareta da ya yi a lokacin da ta ji kamar za'a makata da kas sanadiyyar Juwa
Tun daga kafarsa ta ringa dago dubanta a hankali har ta kawo kan fafadan kirjinsa, zuwa zaratan hannayensa ta sauke a kan ni'imtaciyar fuskarsa mai sakata karra jin du duniya babu macen da ta kaita dacen santalelen gaye a rayuwa
Muryarta cen ciki ta ce" Yaya aka yi ka gane ?"

Bai ce mata komai ba, sai dauketa da ya yi cimak ya nufi bakin bed da ita ya ajiyeta sannan ya tsaya yana harde hannayensa yana kallonta ya ce" Ba wannan ne maganar da ya dace ki tambayeni ba, abinda nake son sani ta yaya hakan ya same ki dan mu nemi magani, HUZNAH mu ba kannanun yara bane da zamu tsaya kan wannan yar maganar mu dagawa junna hankali, inaga a yanzu kin yi girman da ilimin da zaki kaucewa hakan......, Ki dan yi abinda ya fi armashi shine yin nazarin tambayoyina dan na samo mana magani!"

Ta yaya zata iya hanna kanta fashewa da kuka, a dole ta yi kuka, a dole ne ta yi kuka idanma ana yin na jinni a yau ita kam zata yi
Cikin matsanancin kukan da ya sarketa ta zuba masa rinnanun idannuwanta, yanzu mijinta? Abin kaunarta, abin tattalinta, mafarkinta ne wata ta malaka ba ita ba? Har yake nuna karamin abu ne? Ilimin me? Girma? A gingunemiyar uwa yake kallonta kennan? Shi yasa yake iya tsayawa yace da ita ta yi girman da ba zata iya yin kishinsa ba ko me?
Muryarta na fita a hargitse cike da dacin kalmar dake fita a bakinta ta ce" Yaya zaka yi magana da ni a kan abinda ya shafeka ka auna ni a dandaja? Ilimi? Girma? Na yi maka tsufan da kake tunanin zan iya kawar da maganar nan a kiftawa da bismillah?, Innalilahi wa inna ilaihi rajune, a jikina? A ina na hadu da wannan masifar? A ina na hadu da wannan balakin?, Yaushe hakan ta sameni? Na tabata tun kafin ka fara yi min duban mace ce ni da neman samun nutsuwa a jikina na hadu da shi domin a darenmu na farkoma a asibiti ka waye shi dan tarin cutar da ta dunkule maka a mara ka kasa fitarwa, ashe tun lokacin nice rashin lafiyar nake tunanin ina zaune da kai dan soyaya ba zan iya barinka ba koda kuwa baka iya anfanar min abinda kowace mace ke anfanuwa da shi? Wayo Allahna! Na shiga uku, ita ka samu ka shigeta ama ni aa? Ita da ta zo jiya jiya ce ta samu wannan mukami ni kuma aa? A dole ta ringa yi min gani gani, a dole tace min kar na saki na zo idan kun a soyayarku, a dole ka yarda da dukkan furucinta dan ka fi sonta, to ta yayama za'a hada soyayata da tata bayan ita tana iya baka abinda ni ba zan iya baka ba, ta yiwuma itace ta gamani da cutar nan ba kow..........

"h
HUZNAH!" ASADEEK ya fada a kausashe, muryarsa da dan karfi, idannuwansa gaba daya a ware a saman fuskarta cike da mamaki yana kallonta

HUZNAH dake kuka harda majina da hawaye hannayenta bibiyu a saman kanta ta tuje gashin kanta ta bale abin alkyabarta tana jan kasa daga jikinta ta dauko dubanta a raunane ainun ta sauke a saman kansa

A hankali ya miko hannayensa bayan ya sauke raunaniyar ajiyar zuciya yana kallonta, muryarsa a sanyaye ainun ya ce" Haba HUZNAH, maimakun mu yi maganar da zata fishemu,, mu samu mafitar da zata gyara mu, sai ki dauke maganar ki zubata gaba daya kan abu guda daya tak?, Haba HUZNAH................"
Ya dakatar a hankali yana sake kallonta sannan ya ja numfashi kadan ya ce" HUZNAH rayuwar shekara goma fa ba ta kwana goma bace, kuma a yau idan a kaina abin yake zan fi so na sani dan na magance ko dan na nuna bajintata a gabanki ko?, HUZNAH yaya zaki kawo maganar soyaya ta wannan fannin kamar ita kadai ce rayuwar auren? Da ace shi kadai ke iya rike aure da mun jima da raba hannun junna HUZNAH, idan hankali ya tashi ai hankali yake nutsar da shi, kin san tun yaushe nake son na tuntube ki a kan hakan? Kar ki sako magangannun NADIRAH a matsayin wani abin, yarinya ce, kar ki ga laifinta kin ji?, Dan Allah ki sasauta min hankalina a tashe yake fa, kin ga abubuwa sun min yaw yanzu sosai HUZNAH"


Kwarai, idan hankalinka a tashe, komai ganninsa kake yi ba wai, dukkan furucin ASADEEK sai suka ringa zuwar mata a karkace, gaba daya duniyar ta fitar mata a rai a lokacin da zuciyarta ta gama sheda mata hakane mana, dole ne yace damuwa ta masa yawa, a yanzu ai basshi da wata damuwar da ta wuce ta gidan hutunsa, dole yace tata damuwar ta biyo baya tunda yana cikin damuwar an sace iyayen matarsa, yana magana da cewa ko NADIRA ko wace? Wacece Nadirar kuma?, Kwata kwata a yanzu idannuwanta banda bakin kowa ciki harda shi babu abinda take gani

Hannun nasa ta kasa kamawa, da kyar ta iya mikar da kanta, a tsayin shekaru goma da suka yi basu taba samun sabani irin na yau ba, basuma taba samun magana mai ciwo irin ta yau ba, damuwarsu kanta basa zurfafa tunani a kanta dan basu da maganinta kuma basu dora tarayarsu a kanta ba, a yanzu dole ta ji ta rikice, dole ta ji tana neman shiga uku

Tana kallonsa Muryarta na rawa ta ce" Koda baka so, dole na fada, a bayane yake a zuwanta gidan nan na hadu da dukkan damuwar duniya, ni da ita sai dai Allah ya saka min!, Maganar sonta kuwa, ka san ka fi sonta da ni, a bayane yake, takan tsaya ido cikin ido ta yi maka rashin kunya, sai dai ka ringa murmushi , karshe yau ka kirayi lamarin da yarinta, a ina yarintar? Yaan magana sun ce SO hanna gannin laifi ne......., Dan Allah ka bani dama na je Baban gida dan a nema min maganin abinda ban san da shi ba sai da matar so ta zo!"


Idannuwansa ya rintse, soai yake yi mata uzuri domin abu ne da dole ya girgiza zuciiyarta, ama kuma ya yi mamakin saurin gazawarta da saurin yanke hukuncinta, to ita tama rasa a me zata tsaya ne ai, da bakinta tace a washe garin tarewarsuma ya tashi da ciwon, sannan tace ba wanda ya dora mata sai NADIRAH, shi a ganninsa idan aka ce shine a jikinsa zai zauna ne ya yi ta bincikar kansa har ya gano mafita, ama ita ta ki a yi haka, karshema ta bige da abubuwa kamar wata yarinya karama?

Juyawa ya yi ya nufi wajen kayansa ya bude ya zubawa kayan kallo gaba daya ya rasa kayan yake kallo ko kukan da take shekawa ke hanna masa motsin kirki?

Kukanta take yi bilhaki, ta ci gaba da magangannunta, cewa take yi ba zai ce komai ba? Tana jiran amanarsa ne na ta tafi gida, watau gidan iyayenta a nema mata magani, maganin da ta kasa bashi amsar da yake tambaya dan ya sama masu mafita, maganin da a yanzu ya sani yake kuma neman makarin abin, gaba daya ta juyar da maganar ta kasa sauraronsa, cen kasan zuciyarsa sai ya ringa jin muguwar kewa, da son zantawa da wani na jinninsa, sosai kewa irin ta iyaye ta ringa mintsininsa

Yana sauraronta har ta gama ta fice da kukanta cewar ai shikenan tunda yanzu ya samu mace ita kam da take hoto ai sai a kara mayar da ita gefe dan kar ta tsare hanya


Idannuwansa dake lumshe ya bude ya bi kofar da ta fice da kallo, kkasa kasa ya samu kansa da furta" Uhum" a cikin zuciyarsa kuwa yana girmama girma da karfi irin na mace, wanda ba zata daukeka ta makaka da hannayenta a kasa ba, ama Allah ya bata damar da zata iya yi maka sal komai girmanka da jama'a suke gani ta sileka tsaf ba ko kunya da tsoron Allah,

Lalausar shada ya zarro mai ruwan hanta, dinki ne mai gari da yar ciki, kusan du dinkunnansa haka suke dan ba kasafai zai saka dinki simple ba sai irin in zai yi fitar sirri

Bai saka garin ba, rigar da wandon kadai ya saka ya dauko hular kayan da Mancheste ya balla , Hular kuwa ya riketa a hannunsa ya karasa wajen turarukansa ya yiwa jikinsa barin turaren sannan ya koma wajen takalmansa ya sakka , ya karasa wajen comand na AC ya dauka ya kashe su biyun dake dakin ya kuma kashe light din

Bai baro dakin ba sai da ya cire soket din da aka jona na turaran wuta sannan ya janyo kofar ya rufe da Ky dinsa ya fice da shi, sabon abinda ya tsira kennan, a yanzu baya barin Ky dinsa ko dan rashin yardar da aka haifar masa a zuciyarsa


Tafe yake a hankali har ya karaso kofar dakin ta baya ya dakata yana kallo,
Wayarsa ya ciro ya shiga kiran number SHEIK
10/10/22, 08:38 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





6️⃣3️⃣



Wayarsa ya ciro ya shiga kiran Number SHEIK

Bata jima tana ringing ba ya daga
A nutse ya sanar masa cewa yau za'a dauke yarinyar karfe biyu na rana, domin a lokacin take daukan doguwar hanyar dake kaita bangaren da mahaifiyarta take dan amso kule kulensu na munafurci

Ya gamsu da hakan ya katse kiran sannan ya yi anfani da Ky din wajen ya bude ya shiga ta ciki ya rufo ya mayar da shi aljihunsa sai kuma ya ringa tahowa a hankali yana saurarawa dan a sanninsa a wajen nan akoy matar dake iya zama sarakuwarsa, watau INNA HINDU


Dariyar da kunnensa ke jiyowa da kuma hira hankali kwonce ya saka shi sake zuba idannuwansa a kanta, Auta hankalinta kwonce , dariya take yiwa Inna dake tambayar shin abinda ta yi mata kwontacen tuwo ne ko wani tashin hankali ne da galmi galmi a baki da kuma zakin madara, watau FLAN, fama take da Innar kan ta ci abinci , kwata kwata innar kwana biyu sai a hankali, ta cika damuwa a kan halin da yayarta take ciki, dan NADIRAH ba'a zancenta domin ita kiris take jira ta fashe da kuka ba kunyar kowa ta ringa haharba kafa tana fadin innar birni da aban birni

Dan murmushi ya ji yana taso masa daga kasan zuciyarsa, sai kuma ya dan koma kasa kasa ya yi salama ta yadda ya tabata zasu iya jiyo shi

Auta ce ta iya amsawa, inna kuwa ta nemi rikicewa a lokacin da ya bayana a gabansu ama ba wai ya shigo gaba dayansa bane, domin dakatawa ya yi yana kallon Auta da ta nufo shi fuskarta Kwonce da farin cikin ganninsa

A daburce Inna ta nemi dukawa kasa gaba dayanta, ta jimke hannayenta kamar dai yadda ta yi farkon haduwarsu, bakinta na neman hade kalma da kalma ta ce " Barka da warhaka Uban marayu......" Sai kuma ta kai dubanta kan NADIRAH wace tunda suka yi ido hudu da shi gabanta ya yanke ya fadi ta sada kanta tana wasa da yan yatsunta biyu tana jin yadda idannuwanta ke marmarmar sunna kokowar su sai sun kubce sun kalle shi, gangar jikinta kuwa ya kwashi wani irin kaikayin da bata san ko na meye ba, zuciyarta kuwa ta ringa wani irin dokawa har zufa ta nemi tsatsafo mata a gaban goshinta, hakan ya saka ta lumshe ido tana jin wani hawaye mai dumi yana son tarun mata a cikin idannuwanta

Inna kuwa nan da nan ta tuna da abinda suka aikata, su yan ta'ada, hakan ya saka hankalinta ya nemi tashi, kasa kasa sosai ta ce" Ke indi, kar dai hukuncin ne ya tardo mu yau laraba rana ta raba tsakiya gatse gatse za'a karmu ? Ba za'a yi hakuri a kaimu juma'a ba ko samu tsalakewaR tambayar kabari?"

A hankali ya janye idannuwansa daga fuskar Auta dake ta doka masa murmushi ya dan saci kallon Inna, a kalamanta babu abinda bai ji ba domin ba wani kwaramniya a dakin, TVma a kashe take gaba dayanta

Ba zato ya ji dariya na son fitowa daga bakinsa, a dole ya kai dubansa kan Auta ya ringa sakin dan murmushi mai sauti kadan sannan ya dauki wayar tasa ya latsa numbar Aban Birni ya karrta a kunnensa

A tausashe ya amsa salamar da Aban birni ya yi masa, sannan ya ce" Barka da warhaka Abah, ya gida, ya ibada"

Cike da jin kunya da mutunci Aban birni ya shiga gaishe shi, sai dai ASADEEK shima ya kasa amsa gaisuwar dan a ganninsa ta yi yawa, shine ya dace ya gaisar da shi haka, ama Abah ya gaza rage bashi girma har haka

Dan murmushi ya yi ya mikawa Auta wayar yana fadin" ki kai masu wayar"

Auta ba musu ta kawowa inna wayar wace ta yi tsuru tsuru baiwar Allah tana ta maimaita kalmatu shahada dan ta sabarwa harshe da fatan idan abin ya zo a fadeta dai-dai ta karbi wayar tana tambayar Aut waye? Sai dai Autar ta nuna itama bata sani ba, hakan ya sa Inna kara wayar a kunnenta a gajarce ta ce" Halo salama alaikum Hindu ce waye a ta dayan bangaren?"

Yana yar daria ya ce" Ta habu makadi kike uwar Indi ja gabar dukiyar kasan gadon karfe mai komai dozin"

Ido ta zarro, dan kuwa du duniya ta san mutun daya tak cilo yake yi mata irin kirarin nan face Aban birni, tsaye ta mike tana fadin" Ka rantse da Allah salihu ne? Wayo ni ta Habu maman Indi dama kana raye? Ina auntyn take dan girman Allah? Ina kuka shige? Kwai yana nan yana ta fashewa in fada maka Indi dai kafa ta kwasa ta je ta bude zare da abawa a gaban uban datawa, yanzu haka dai mu a hannu muke dumu dumu, ta yiwu a yanke hukunci yau......."
Sai kuma ta shiga rike harshen zani tana fyace majina da hawaye ta ce" Ko a ina kuka buya ka sanarwa Habu ni na yafe masa, ya yiwa Allah ya yafe min yan yawace yawacen da yake hannani nake yi, ina yi ne dan na dan saku da zaman da gida da kuma yiwa maneman Indi da rigima kashedin kar su taba min Ya ka ji SALIHU?"

Auta daria take yi bilhaki, ASADEEK kuwa jingina ya yi da garu ya kawar da kansa ya cije iya cijewa har sai da sansanyar muryarta ta ce" Innata wai Aban birni ne? Ce masa ga Indi bani shi mana "

A hankali ya juyo ya zuba mata lumsasun idannuwansa
Shigarta ba wata rikitaciya bace ba kuma mai kasaita bace, ama sai ta zama wata kasaitaciya a idannuwansa
Tana matukar son atampa, domin sket ne da riga na atampa a jikinta dinkin gaba daya ya bi halitar jikinta ya kawata sai daukan idannuwansa take yi
Hasken fatarta a cikin atampar mai ruwan ja ya matukar haskaka, harma kamar ta fi kulun haske ko dan ya kwana uku cir bai ganta ba?

Dariyar da Inna ke yi tana rike karkadaf da wayar a kunnenta tana sake tambayar wai Fatime ce? Ta rantse da Allah itace , NADIRAH na ja tana ja ya saka shi a hankali ya sauke dubansa a kan Auta
Murmushi ya saki yana kallon yadda Auta ke fara'a da fara'arsu , ta ce" Abahna ka raba rikicin cen fa, ba zata bata wayar nan ba, ka ga Mamah har ta dawo normal bayan kwana biyun nan ko abinci sai na yi da gaske take ci, bale Aunty sam take kin ci bayan yanzu bai dace ta ringa wasa da cikinta ba"

Bai gane manufarta ba, abinda ya fi tsaye masa a rai sunnan da ta kirayi inna da shi, Mamah..................., Sunnan ya fito daga cen kasan zuciyarta ne, kuma a saman lebenta yana bada amo ne kamar idan D'a zai kirayi mahaifiyarsa


Abinda Fatime ke sanar masu ya saka su zarro ido, sai kuma NADIRAH ta ringa tafa hannu ta juyo inda yake tsaye

Sosai magana ke saman lebenta, so ta yi ta ce da ka san inda suke, kaine ka dauke su ama ka kyale ni?, Sai dai tanaa saka idannuwanta a cikin nasa ta samu bakinta da yin nauyi, zuciyarta da bugawa, sai kuma haushin irin yadda yake bambanci da nuna mata yana sin matarsa ya taso mata, hakan ya sa ta turo baki, hadi da galawa bangon da yake jingine Harara kasa kasa ta furta" masu mata ko mema aka zo yi min dakina?"


Tsaf yake kallon lebenta, ta hakan ya gane furucin bakinta
A dole ya idasa sakin murmushinsa ya ringa neman sai sun hada ido, har dai hirar ta Inna ta ki karewa ta shige ciki tana bada bayanin abinda ya faru dala dala , wayaa kuwa kamar tana yiwa na nesa kugi du ta ware murya tana bada labarin gaba daya ta manta wayarma ta waye kuma a gaban wa take, ita dai farin cikinta ya samu da ta ji ahalinta


Shiru ne wajen ya dake dauka
A hankali Auta ta janyo hannun yayanta har falon tana nuna masa wajen zama ta ce" Abah zauna bara na kawo maka juid din da muka yi ni da Aunty"

Tana bada baya ya sake duban NADIRAH, wace ta yi saurin dauke nata idannuwan daga kansa, danma kar a wani ce kallon wani abin ne, kawai dai tana son gane kalar shadar jikinsa ne dan ta mata kyau a jikinsa sosai wollah, kamar majiya karfin filin din indiya

Murmushi ya yi ya miko hannunsa kasa kasa ya ce" Momyn Auta, asalamu alaiki"

Ido ta dan zarro, sai kuma ta dago ta zuba idannuwanta a saman hannun

Da sauri ta kallo hanyar da Auta ta bi, sai kuma ta sake kallonsa, kasa kasa tana dan matsawa kadan ta ce" Ka mayar da hannunka fan Allah kar Auta ta gani ta min wata fasarar, ba kyau gaisawa da kato fa.............."


Tahowar Auta ya saka NADIRAH saurin kara ja baya tana turo baki da kallon dariyar da ya faraa yi yana son dole sai ya bita sun yi musabaha , ita kuma tana neman labewa da sake bata fuska a dole ba zata gaisa da kato ba😌

Murmushi Auta ke yi, zuciyarta fara'a kamar zata fito ta fado daga kirjinta, sai kuma suka raka NADIRAH da kallo gaba dayansu dan a guje ta ruga ta nufi dakin da innarta ta shige tana haki

Dariya Auta ta saka tana ajiye abubuwan da ta jero ta zauna tana fadin" Abah ka korar min Auntyna....."

Shima fuskarsa yalwace da farin ciki ya ce" Ba ta hannaki cewa aunty ba? Momy ce fa?"

Ai kam Auta ta kara saka yar daria tana cewa" Abah, ai idan na ce maka aba ne take kishi, sai tace bafa ta sin bambanci, haka tace Abahna sam bata tunanin idan yana tsoron Allah, wai sai ya kirayi matarsaa a wani sanyaye ita kuma ya ce mata NADIRAH gatsau, abin nan yana bani dariya Aba, wai fa aunty kishi ne mai zafi ke fama da ita......"


A hankali ya tsare Auta da kallo, har sai da ta fahinci kallon ya yi dan yawa ta dan TAKAITA tana kallonsa

A nutse ya ce" Uman Aba, kina nufin ........., auta kina nufin wannan rigimar dan tana kishinaa ne?"

Auta na murmushi ta gyada kanta,

A hankali ya dan gyara zamansa yana dan cakude girairakinsa, kasa kasa ya ce" Ama, ana kishi idan ba'a son mutun?"

Auta ta tsayar da dubanta a saman fuskarsa, sai kuma ta dan girgiza kanta ta ce" Abah, a sanina ba kishi idan ba so"

Fuskarsa ne ya dora alamun dan damuwa, sai kuma ya koma ya zauna da kyau a ransa yana ayana' ni na san bata so na, ita dake nan tana jiran na bata takarda ta jewa Tuzurun kauye?, Ni din kuma ko ta yi yaya da nawa zuciyar.......?', sai kuma ya ringa nanata kalmar nashi zuciyan.....................................

A hankali ya gyara zamansa da kyau yana sake dubam Auta, du a sonsa na ya zanta da ita sosai ko zai ji sanyi sanyi a zuciyarsa, domin dai shima da ya nemi wanda zai nufa dan sanar da damuwatsa ita kadai ya gani a idannuwansa

Dan tabe baki ya yi yana girgiza kai ya ce" Uhum, Auta, wai yanzu HUZNAH ta gama mun fada, harda cewa bana sonta na fi son NADIRAH a kanta, kin ga hali irin na mata ko?"

Da mamaki take kallon yayan nata bayan ta zuba masa dan cake din da suka yi, wanda NADIRAH ta shamaceta ta maka siga , ta ce" Abah, wani abu ya faru ne ama ko?"

Dan dakatawa ya yi da abinda yake yi ya dana kalleta, sai kuma ya yi shiru bai bata amsar nan ba, dan gani yake yi maganar kamar ta fi karfinta , ko yace ba maganar da ya dace ya yi da ita bane

Dan murmushi ta yi, zuciyarta na mintsininta da son sanar masa maganar cikin, tana cikin shakun idan ba cikin bane ba fa? Ama kuma irin yadda Inna ta fada da tabatarwa sai take jin kawai ta sanar masan


"Dama maganin da take baki, kwaya ce ba asalin maganin samun lafiyarki bane?"..................... Ya fada da air na seriuss bayan ya ajiye plate din hannunsa bai dauki Cake din ba yana fuskantar Auta

Gabanta sai da ya fadi, dan magana idan dai ta shafi Umma ko yayane daga mata hankali take yi

Jiki ba karfi ta kalli Abahnta, sai kuma ta sake sada kai
Ko yayane Abahnta ya gano wace Umma tunda har ya kawo wannan matakin a bincikensa

Muryarta a raunane ta ce
10/10/22, 08:38 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu

Please Login or Register in order to submit comment