Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bama, haka kuma yarka ta tsane shi ta yadda bata zuwa garin nan ta sauka a Fada, babu ta yadda za'ayi ya santa, menene dalilin tambayar nan?"

Sarki ya ce" Wannan malamin nasa, wanda ke wakiltar aurensa ne yace min wai Ashe ba sunnanta bahija ba, wai Asadeek ne yace masa Bahija sunnan yarinyar?"


Dan tsai ta yi, sai kuma ta yi murmushi tana fadin" Kai kam ka cika sarau, da bakinmu muka sanar masa sunnan nan, nima da bakina na sanar masa ya kai sau biyu, ina fata baka rikice ka tona kanka ba?"

"Ni dai na ce masa Bahija kiranye ne da Mahaifiyarta ke yi mata, ama duda haka maganin nan da na baki bani shi nanna ajiyeshi a wajena, sai maganar aurensa ta lafa sosai za'a fitar da shi a kai mata, kar a bata shi yau" ya fada yana miko mata hannu


Itama murmushi ta yi, domin a gaskiya idan aka ce daga zuwan yarinyar har ta aikata aikin nan an kamata itama ba zata ji dadi ba, haka kawai take jin bata taba gannin macen da ta dauki hankalinta irin yarinyar nan ba, ciki harda wancen uwar taurin kan da ta zabi hauka a kan hankali,
Maganin ta lalubo a cikin rigarta ta miko masa, tasakashi a ledoji ta masa wani irin dauri,shi kuma ya juya ya kai shi ya boye sannan ya dawo ya tsaya still idannuwansa ba daidai ba ya ce" Idan kuka bata magani me kennan?, Ai zan so ya gwada tashin jarabarsa a kanta,ya ki zuwa inda take da tsoron kar ya je abu ya kwonta, da wannan damar nake so ki saka masa ido, ta yadda zaki turamasa baiwa tsirara, ko waye shi zamu gani ai, idan ya aikata abinda a kansa yake jefe mutun har lahira sai mu gani, jefe shi za'a yi ko gubar macijin nan zai ci?, Ki barni in sha dadin kallonsa a mazinaci mana kema"


Ido ta kankance tana kallonsa kafin ta ce" Bam taba gannin mugu irinka ba, ama wannan tunani ya min , lalle lalle idan haka ya tabata ni nan nice zan tunasar da shi shine fa mai yankewa wani hukunci, yaya kennan?, Uhum ka hango shi a cikin rami kansa a waje, idan na tashi daukan dutsin da zan jefa masa sai na dauko rungumeme na zafta masa ta yadda zai makance kafin ya mutu!"

Wani irin murmushi ya yi yana hangen komai a idannuwansa, a matsayinsa na wanda ya haura shekaru sittin a duniya, yana hango wasu sittin din ne a gabansa? Fa karfinsa? Da hankalinsa? Wai idanma mutuwa bata ratso a lamarin ba, gigita irin na tsufa fa? Wanda ke saka bawa ya dawo tamkar jariri fa? Tsufan da ya zo maka da tsoron Allah da zikirima yaya kake dawowa idan shekarun sunna dauko da yawa? Bale tsufa irin nasa? Allah, kar ka hadamu da makantar zuciya Ya Allah, Allah idan har munada rabon yin makanta cikin biyu gwara mu rasa ganninmu da zuciyarmu ta rufe, domin idan muka rasa ganni irin na hasken musulunci idannuwan namu zasu hasko mana gigitacen ganni a duniya da kiyama!


Agogo ya duba sannan ya kalleta ya ce" Ki je ku fara shiryawa, ki kula da WA'INDA zasu shiga motocinku, da zararan fito daga sallah zaku dauki hanya saboda ku samu shiga da duhu duhu dan kiyaye dokar shiga da Matar sarki da hasken gari"


Kai ta gyada da murmushi ta fito ta sake ratsawa ta nufo bangaren GIMBIYA

Tana zuwa ko Gimbiyar bata kula ba ta nufi dakin BAHIJA wanda aka sauki su NADIRAH da HINDU

Tana kama kofar zata shiga ta ringa jiyo kuskuskus, irin magana ake yi kasa kasa sosai

A hankali ta dan labe sannan ta karra kunnenta, dan gaba daya ita bata wani yarda da marakiyar yarinyar nan ba,

"Kina jina Indin Innarta, ki sani su din sun isa da ke, sarakunan ki ne, da mu baki daya, su muka sani, kuma dole mu masu biyaya kin ji? Ki tabatar kin masu abinda suke so fa?, Idan yau akace ki aikata ki aikata shi, mu mun yarda da su, kuma ko me suka sakamu zamu aikata masu ne dan kauna"

NADIRAH da ta ci kukan jin ana fadar cewa an daura aure an daura aure ta sada kanta , domin bakinta ba zai iya furta komai ba, haka kuma rarashin da Innarta ke yi mata ta jiyar da maganar gannin innuwar mutun ba zata iya amsa ba a yanzu, batada karfin amsa maganar nan gaba daya, shin yaya zata yi da ranta ne? Yau an wayi gari an daura mata aure da wanda batama sanshi ba, shima bai santa ba, bata taba ganninsa ba, Aminunta yana LABA baima sani ba, daga ce masa zata rako innarta biki su dawo, an dora mata alkyaba, an nadeta, an dora mata igiyar da ta fi kowace daraja da nauyi a wuyana, wai a yanzu ita matar wani ce, waninma sarki, ta yiwu tsoho ne takwaf bawan Allah tunda ta ji su ummanta na kiransa baban kowa?, Ta yiwu shiruftar tsufa ta kama shi, ta yiwu kuma wani kasurgumin azalumin boye ne, mutumen da ya saka a kasshe baya ce masa komai? Shikenan an daura aurenta innarta bata saka dinkin da tace zata yi ba, sannan ba'a siya mata gadon karfe mai rumfa ba, shikenan za'a kaita wajen da bata san me zata tarda a cen ba, shikenan za'a yi bikinta babu mahaifanta a gefenta,ko innar birni tana tunata? Ko ta manta da ita? Abanta ko ya dangana ? Ko yana cike da tunaninta?, Haba ta yayama zata iya bada amsar wani wasan kwaikwayo na innarta? Bakinta ba zai iya ba sam!


"Ki daina hawayen mana na ce kin ji yar gidan Indinta?" hHindu ta sake fada tana sake satar kallon kofar

Shigowa Umma ta yi ta mayar da kofar ta rufe ruf ta karaso ciki sosai tana kallonsu daya bayan daya

A nutse ta ce" Kukan me take yi ita kuma?"


HINDU ta ja ajiyar zuciya, irin abin a ranta ta dubeta sannan ta sada kai ta ce" Allah ya karra maki lafiya, dama ita din da saurayinta wanda take so sosai, to da aka daura ne take dan kuka da cin alwashin ta fiku zakuwa ta aikata aikin nan dan ta dawowa saurayinta"

Cike da tsare gida Umma ta ce" Aikin me zata aikata mana?"


HINDU ta dago tana kallonta, irin zata mayse mata lambar nan? Ko ta cire kanta a ciki?, Bata san barikima iyawa bace kennan?

Hindu ta sada kanta, irin ta dan daburce, sai kuma ta dago cike da confidence, watau ta matukar yarda da ita a wannan fannin ta ce" Ina magana ne a kan, aure aka daura mata, dole ta je ta yi biyaya, idan ta dawoma zata tardo saurayinta, ama bawa yake a gareta, domin talaka ne!"

Umma ta sake kurre Hindu da kallon mamaki, lalle wannan din wata biyayiyar muguwa ce, ta ayana a zuciyarta, watau ta ji maganarsu ta bayan kofa, ta zata tare suke ta karra bata magana a jumulce, ta nemi karin haske ta kuma zagayeta

Zaunawa ta yi tana fadin" Wacece ke?, Ina nufin menene tsakaninki da ita?"

HINDU ta dubi NADIRAH, ta dubi UMMA, a hankali ta ce" Ni na raineta"

"Wani irin raino kika bata?" H
umma ta tambaya

HINDU ta lumshe idannuwanta ta ce" Na horeta ne cewa, biyan bukata rai ba a bakin komai yake ba, ta fi yarda da fansa a kan komai, hakan ya sa ta kasance amintaciyar baiwa!"


Wani irin yarda da Hindu ke darsuwa a zuciyar Umma, sai dai sam bata nuna ba, hasalima mikewa ta yi ta karasa wajen akwatin da suka zo da ita ta zauna ta bude ta shiga ciro suturar da ita da kanta sai da ta yi mamaki, domin sakon daga matar UMUGHLUK ITIBEL ne cewa sakon amarya ne kyauta ce daga ita, ita kuma ta dauko bata duba ba dan ta san ba zai wuce kayan da za'a sakawa amarya ba, ta tabata kuma ba zata yi wani abin kirki ba dan bata iya abu irin na fita kunya ba, sai dai a yanzu ta yi dana sannin rashin budewar, da ta rage wasu abubuwan, koma ta cenza su

Sarkar ta zinari ta sake zubawa ido, sai kuma ta tabe baki, ko menene zata dauke daga baya ai

Kayan ta miko ma HINDU tana kallonta a hankali ta ce" Ki shiryata"

Hindu ta amsa ta mike ta ce" Tashi mu shiga ciki"

Umma ta dan dago ta sake raka su da kallo har suka shige

Murmushi ta yi tana karra jin yarinyar na wani irin karra mamaye mata kirji, ita abin har ya farra damunta, anya kuwa zata aikata abinda Gimbiya ke so? Watau idan yarinyar ta kashe sarki a yi yadda za'a gane itace ta kashe shi? Anya zata iya aikata haka? Yarinyar wata irin salihar fuska mai dukkan kirji ne da ita

Sun dan dauki lokaci sannan suka fito

A yanzuma kasa dauke idannuwanta ta yi a kan NADIRAH har HINDU ta zaunar da Madirar a gefe sannan ta sake gyara mata daurin dan kwalinta ta kuma kallon Umma tana jin lalle idan akoy wace ya dace su yi shayi wannan matar ce, dan kuwa gaskiyar NADIRAH tana tare da abin munafurci a tare da ita

Umma ta dauke kanta ta ce" Kina da aure ne?"

HINDU ta sake kallonta a hankali ta ce" To dada, gani nan dai, auren dai gayanan dai, kawai"

"Kina da aure ne?" Umma ta maimaita a dake, domin amsar bata yi mata ba

Hindu ta gyada kai ta ce" Eh "

UMMA ta kawar da kanta ta mike ta dauko alkyabar da za'a lulubawa MADIRAH da safa da kuma baban abin rufa na turkudi mai masifar tsada da za'a lafta mata ta mikowa HINDU sannan ta kama hanyar fita tana fadin " Ki iya bakinki, masoyansa a garin da ba nasa bama sun fi makiyansa yawa, ku kasance cikin shiri koda yaushe muna iya kama hanya"

Tana fita ta daga wayar wa'inda ke tsare da hanyar saboda REBEL ( watau yan fashi da makami) ta tabatar an watsa mutane ta ko'ina da bindigogi dauke da alburusai, domin gari ya dauka ya yi aure, idan akoy masoyansa a daji, akoy makiyansa masu farautar rayuwarsa a bayane!














Ke kuma aboue ko?
8/13/22, 22:58 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*



2️⃣4️⃣



Tana tafia NADIRAH ta dago, muryarta a cen ciki ta ce" Innata, idan kika bi ni Aban kauye fa?"

HINDU ta lumsje idannuwanta sannan ta yi murmushi, a sanyaye ta ce" Ba zasu kwace mana komai ba Indina, zan raka ki har dakinki sannan na dawo in sha Allah, ki min alfarma ki kwontar da hankalinki kin ji?"


Kai ta gyada tana jin sanyi sanyi a ranta, sannan ta karra jimke yar karamar wayar da Abanta ya bata cewar akoy layinsu a ciki, yanzu haka Innarta ta daukota daga ma'adanarta ne dan su yi magana da iyayen nata, sun gama maganarma ama ta kasa mayarwa, da kyar ta ba Innarta ta mayar ta boye sannan suka mike dan gabatar da sallah


Bayan an gama sallar azahar aka shiga fitar da kayan da aka ce nata nw, kayan da su ba'ama nuna masu ba

Lalle an fitar da kaya masu yawan gaske sannan aka fitar da ita

Gimbiya ke rike da ita, irin rikon nan na tana jikinta sosai sannan tana ta shafa kanta tana afkin nuni da rarashi take yi har suka karaso gaban wuleliyar motar da za'a sakata suka shigar da ita sannan suka yi salama aka dauki hanya, domin tafia ce zasu yi a hankali wace zasu dauki lokaci koda sun shiga garin da wuri ba zasu isa gidan da wuri ba sai sawaye sun dauke, dan ba'a zuwa da matar sarki ido na gani


A hankali suke tafe, cikin motocinsu, motocin sojawa sun zagaye su, tafiya wace idan sun doso ake dakatar da masu zuwa sai sun wuce har suka dauki babar hanyar da zata kai su AGADAZ


A hankali Umma ta dan karkata kusa da kunnen NADIRAH ta ce" Kuka kike yi?"

NADIRAH ta dan yi tsam, kafin ta girgiza kanta a hankali"

UMMA ta yi murmushi ta ce" Kina iya kwontawa a cinyana, ko a kafada ki huta kafin mu isa BABAN birni, domin zan so ki bude ido ki ga Baban birni, ko kin taba shigowa?"

NADIRAH ta sake girgiza kanta tana dan gyara zamanta

Umma ta sake yin murmushi ta ce" Garin Agadaz, gari ne dake dauke da al'adu, da kuma yannayin ginni irin na kasa, Mazan garin sunna da kudi , boyayun kudi, mahaukatan kudi, domin wasunsu manya ne na kasa, wasu kuma manyan da suka aikata fashi da makami a da ne, wasun ma'aikatan gwamnati ne, wasu masu cin gashin kansu ne, muna cakule da larabawa, da kuma wasu daidaikun yaren........, Gari ne mai daraja, mai girma, mai dauke da mata buzaye da larabawa masu ji da kansu harma da daidaikun wasu yaren, a Agadaz muna girmama Uban kowa, Shi UMUGHLUK ITIBEL yana zuciyoyin samari da yan mata, datawa da tsofafi.............., Zan iya ce maki kin yi dace kin kuma taka sa'ar da duban yan mata ke hari....kin kafa tarihi koda a yanzu kika mutu"


NADIRAH ta dan dago da idannuwanta ta dan saci kallon Umma, still bata furta mata koda A ba


Umma ta dora da fadin" Abinda ya sa ba'a cika gini irin na bulo da bulo ba sai gidan wa'inda suka gagara, saboda sahara, yankin kasa da kuma tsohon gurbi na Volcan, idan zaka dora ginnin da ba kasa ba ko zana, tabas sai ka girgiza da aljihunka, sai dai idan ka tara hakan ba wani matsala bane kuma sai ka zuba cefa ka zuba ginni, Mijinki ya yi ginnin da harta dakin shn shayinsa Bulo ne.............., Ya tara fa, ke kam kin yi dace"


NADIRAH ta tabe bakinta a ranta tana ayanna' hakane'

Umma ta ce" Zaki sha mamakin darajar da zaki samu, duda ba ainahin ke din bace, ama ke dinma kece, tun daga wajen gari matasa na cen da manyan motoci sun yi niya sai sun yi wasan dauko Amarya duda shi angon ba kece a gabansa ba, ya fita da mahaulaciyar kanwarsa da kuma matarsa shakatawa......, Wannanma ai kamar cin amana ne ko?"


Wani murmushi ne ya kwacewa NADIRAH, a ranta ta ayana' An zo wajen, dama na fadawa Innata kina warin munafukai, da ace ita din ce ta yiwu hakan ya mata ciwo, sai dai kashhhhh ko a kwalar rigata'


Umma ta karra rage muryarta ta ce" kin san manyan ginni na matan gidan hudu ne, daya matarsa na ciki, daya sai ya saka kanwarsa, kema a dayan kike na kusa da na kanwar tasa, na san dayan kuwa rushe shi zai yi dan da wahala wata macen ta shigo a matsayin matarsa ko?"


Lalle A yau a yanzu NADIRAH sai ta rainawa matar nan wayo, kuma ta tabata wannan mata tana fama da jahilci mai tsananin gaske, wanda ba zai iya barinta tunanin fari ko baki ba, sai dai ta aikata abu kanta sake, tabas tana da ayar tambaya a kan matar nan, magangannunta sunna saba kamaninta, sai dai ba zata yi gagawa ba, dan bata san wacece ita a masarautar da wajen baban nasu ba sam,


Sun ja tafiyar iya ja, har sai da duhun magariga ya fara shigowa sannan suka saki tafiyar suka yi mai sauri suka karasa ana gama sallah

A hankali NADIRAH ta samu kanta da dan ba idannuwanta damar kallon hayaniyar da take ji

A hankali ta fara kallon yadda innarta ke washe baki tana daga hannu

Wani murmushi ne ya kwace mata dan tsakanin Innarta da Allah take daga hannayenta bibiyu tana gaishe da masu gaisheta

Da sauri ta damu kanta da karra wara ido tana kallon tarin jere na motoci da dawakai majiya karfi, da manyan babura sun tsara abin gefe da gefe sunna gabatar da wasan a tsare

Karra zubawa abin ido ta yi tana jin wani irin yamyamyam a jikinta, domin wasa ne na kwararun wa'inda suka iya sarafa mota, ko babur, uwa uba DAWAKAn da suka sha ado , ga wata mahaukaciyar busa da manyan makadan kwararu masu gadon abin a jinninsu sunna aiko da busa da kida irin na sarauta sunna karra rike gangar kamar zasu tada wajen

Tabas abin ya kayatar da ita, a hankali kunnenta ya tsinkayo mata muryar Umma tna fadin" Murna suke yi, farin ciki suke yi, burinsu suke gannin har ya cika, Uban gidansu mai tausayin talakawa ya karra aure, ta yiwu a yanzu su samu magaji mai halin datako, sunna farin ciki ne dan burinsu a wayi gari matar UMUGHLUK ITIBEL ta dauki ciki, uwa uba ta haife masu , a yanzu kyauta zaki gabatar masu ta wani abun dake jikinki, ko menene, kina iya basu zoben nan, ba kudinsa zasu auna ba, darajarsa da ya fito daga wajenki zasu duba, idan mun karasa Fada an fito da ke zaki yi kyautar"


Janye idannuwanta ta yi daga kanta, yanzuma bata ce mata komai ba, hakan ya sa Umma karra kallonta, ikon Allah take ta kallo, bata taba gannin yar bayi da saurin daukan abin sarauta a jinni ba irin na yarinyar nan!


Get din gaba daya aka wangale motar dake dauke da ita kadai ta hau baban hanyar su kuwa du suka layu ana ta buda irin ta bugaje ana yi mata oyoyo


Umma ta fara fitowa bayan ta sanar da Innar Kauye cewa ta dakata har a mikata dakinta sai ta shiga, idan ta shiga kar ta zauna a saman kujera ta zauna a kasa har a gama gaishe su a watse

Ita dai NADIRAH tana zaune ta ji Umma ta kamota, a kasan zuciyarta ta rinha addu'ar da Innar birni ta koya mata cewa ta shiga da ita du inda za'a sakata

A hankali ta dan dakata da Adu'ar ta zubawa hannunta dake cikin na umma ido sakamakon jin da ta yi tana dan murza mata hannu

A hankali ta janye hannunta tana mayar da shi kirjinta sannan ta ringa bin sawun Ummar wace ke ta son karra lalubo hannunta

A kofar tamfatsetsen falonta Aka ja aka tsaya da ita

Da wata irin isa da kuma iy sarafa harshe Umma ke yi masu godiya, ta gabatar da NADIRAH a matsayin yar sarkin Tanut sannan mata a wajen Sarkinsu

Sosai wajen ya karra daukan budar farin ciki

A hankali ta juyo wajen NADIRAH kasa kasa ta ce" Ki kwatanta kyautarki wa jarumin matasan garin nan baki daya dan ya isar da sakon wa matasa"


Dan tsai ts sake yi, a hankali ta sake yin yadda zata hangi taron mutanen nan, har jikinta wani irin rawa yake yi idan ta ga wai taronta ne, a gaskiya ta haka ta yarda ko yayane yanada masoya shi baban nasu, domin ba'a yiwa talaka dole, koda an sayi wasu a cikin talakawa wasu ba zasu sayu ba, wandinnan jama'ar kuwa da du fadin masarautar nan ta ki daukansu ta tabata sa kai ne, yan gani a kasheni ne a kan sarkinsu


A hankali ta kai hannunta wuyanta ta bale tafkekiyar sarkar nan ta zinari, ta cire awarwarayen zinarin gaba daya tana murmushi ta fitar da farin hannunta wanda shi an ganshi sanadiyar hasken wajen na fitilu ta mikowa UMMA wace ta yi mutuwar tsaye ta kasa karba har sai da ta budi baki kasa kasa sosai ta ce" Kadan ne, Allah ya sa zasu ji dadin karamawata, na gode"


Wani irkn abu ya sara a gefen kan UMMA, maganarta jakadiyar UMUGHLUK ITIBEL ta ji, nan take ta daga murya ta rangada buda tana sheda kalaman uwar gijiyarta,

A dole Umma ta amshi sakon, tana ji tana gani ta mikawa Hakadiyar sarki sannan ta juya ta budewa NADIRAH kofa tana kallonta har ta gama murmushin tana jin kamar ta cire alkyabar nan ta kwaso shokiiii ta juyo ta shiga falon da take kyautata zaton na sarkin ne ko? Domin tana shiga ta tiles din dake malale ta fara tunanin nan din dakin mai gidan ne gaba daya


Rufewar kofar da muryar Umma kamar cikin fada fada tana fadin" A kan wani dalili zaki dauki zinari irin wannan ki ba wa'inda basu san darajarta ba, ba zasu iya bata darajar da take da ita ba, ko dan kema ba sannin darajar tata kika yi bane?"

Da mamaki ta dan zubawa Umma ido, a hankali ta dake zuba mata wani kallon da ya daka Umma dan sasauta muryarya dan sai take gannin kamar yarinyar na yi mata kakausan kallo ne, gashi bata riga ta san har ina yarinyar ta kai da iya juya nata mumunan halin ba, ba zata so a yanzu wannan ta zame mata matsala ba sam


Dan murmushi NADIRAH ta yi ta ce" Na ji kin ce a karamasu, kuma na ga ku manyan sarakai ne ko?"


Umma ta karra zuba mata ido tana nazartarta

Hakan ya saka NADIRAH dan waskewa tana dafe goshinta ta ce" Baki ji zuciyata ba, Wai dan Allah zinari ne ko menene? Ki ce min karfe ne marar tsada , walahi idan zinari ne zan iya neman wanda zai je ya sato min abina a daren yau!"

Da takaici Umma na sauke boyayiyar ajiyar zuciya na damun nutsuwar tunaninta ta lai zaune ta ce" Ba maganar ki tura a sato maki, ke da muke so ko menene ki zamto a boye ba a bayane ba? , Kawai kin yi n farko gaba sai ki kiyaye, ki cire alkyabar mana ki huta? Sai fama kike gashi da an ganni ana gane tana wahalar da ke"

NADIRAH ta dan yi murmushi tana girgiza kanta ta zauna itama a saman kujera bata ce komai ba, a ranta tana ta karra yin waje tana ajiye Umma


Mikewa Umma ta yi tana fadin" Ohk, ni zan je bangarena na huta, na gaji sosai, sai da safe"

NADIRAH ta yi mata murmushin da ya sakata sake kureta da ido, sannan ta fita a ranta tana ayana a yau dolema ta samu yarinyar da zata dan abinnan, dan gaba daya jikinta har rawa yake idan tana kallon yarinyar cen.....lalle sai ta mayar da son banzanta gefe ta sakarwa yarinyar cen kudi ta yadda zata yi gagawar siyanta, dan ta kula itama mai son banza ce!



Nadirah, kallon Innarta kawia take yi, sai karra bayani take du ta rude na girman gidan nan sannan ta sauke ajiyar zuciya tana kallonta ta ce" Indi, gaba daya na fara tsorata, anya zamu iya kuwa?"

NADIRAH ta sauke ajiyar zuciya ta yaye alkyabar nan hadi da mikewa tana jan zip din watsetsiyar shadar da aka watsa mata a hankali ta ce" Allah zai doramu a kansu in sha Allah"

___________________________________

"Yaushe zamu koma ne Sarkina?,, Kanwata ta tare ba nan, ya dace ace ni na amsheta na tarbeta fa"............... Matarsa ke fada a hankali bayan ta zauna a kusa da shi sosai tana kallonsa

Idannuwansa, masu kashe mata jiki da sakata a yannayi na bege ya zuba mata, sai kuma ya yi dan murmushi ya dauke idannuwan nasa yana tunanin wunin da suka yi yau da Auta, irin hirar da suka sha hankali kwonce, har waya ta yi da mijinta normal, daga baya na da tace masa yaushe zai zo su tafi sula yi fada dan yace yana jira a bashi dama, sarki yace zai tabo shi, sai ta samu lafiya, daga nan ne suka yi fada

Shi abinda yake mashi mamaki da ciwon auta kamar bata son zama a fada, ko tunanin iyayensu ke hadasa mata rikicewar yannayi ne?


A hankali ya kai idannuwansa saman hannun Matarsa, wace ta sakalo da hannun wajen cikinsa a hankali ta shafa cikin nasa, sannan ta kawo kanta wajen wuyansa ta ajiye tana sauke masa numfashi kasa kasa ta ce" Baka ra'ayin, ko shafaka ne na yi, ka samu nutsuwa?, Ta haka kana iya zuba min nutsuwar taka fa, sai ka ga na samu ciki................"


Idannuwansa ya lumshe, kirjinsa ya fara daukan zafi zafi hadi da caji,

A hankali ya dan karra riketa, sai dai yanzu ta masa wani rikon da ya fi na dazu watau gaba dayanta tana neman kanainaye shi ne


Idannuwansa da suka fara zama wasu kala ya bude ya sauke a saman fuskarta, a hankali yake kallon lebenta da lalausar fatarta

Bugawar kirjinsa na karra hauhawa, yannayinsa

Please Login or Register in order to submit comment