Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake juyota ta yada idannuwanta zasu shiga cikin nasa, ya sake riketa ta yadda zata daina zaburar da take kamar sabon kamu, a gajiye ainun da son ganar da ita ya ce" Zuwa yanzu bai dace ace baki gane ba sannin wacece ke ne damuwar ba a wajena, Je te demande une stricte explication !"

Ido take kiftawa tana kallonsa, gaba daya da zai sanar mata ko wani kuda ne ya zo masa da sunnanta da bayanin Aminu da ta rage fargabarta a kansa, gashi yana yaren da bata iya ba kwata kwata, ita kam ina zata shiga da ranta yau?

Muryarta a sanyaye bayan ta saka idannuwanta cikin nasa da suka yi ja a hankali ta ce" ASADEEK, hausar da ka fada kadai na gane, Dan Allah ka ringa yi min hausa dan ba kaunar wani yaren nake yi ba"

Shine ya iya lumshe nasa idannuwan sakamakon abubuwan da zuciyarsa ke ta sasaka masa
Ikon Allah, ashe hargitsi na iya samunsa mai duka zuciya wanda bai shafi talakawansa ba ko hakin Gimbiya? Ashe wata damuwa na iya shiga zuciyarsa wace yake son sani ido rufe fiye da damuwar dake damun Auta?, Ashe zai tsaya kerere da daurin gyauto irin na mata a kugunsa yana jiran yar tatsitsiya ta bashi amsa ama su ringa tarere sunna ja in ja? Ashe zai riski irin ranar nan da yana kallo a ambatar masa wani namijin bayan ya gama gane shima namijin ne, wadataciyar bulalar da Allah ya haliceshi da ita tsaf take iyo ta gigita kowace irin rijiya ce? Ashe zai bude kaya sababi ya saka a matsayin na aro? Wacece ita yarinyar nan ne? Me take tafe da shi matsayin aikin da aka bata ta aikata a kansa? Bakinta ya fada, a cikin firgicinta ta zayane, yanzu da ta dawo hankalinta ta karyata!

"Hum" ya furta daga ciki ciki, sannan ya saki hannunta ya ringa matsota tana matsawa jikin garu har suka dangane da garun tana jin abinda aka gama wanka mata na bin kafarta kamar makeken ruwan fitsari

A hankali ya dake kure fuskarta da kallo
A matsayinsa na alkali, ja gaban talakawa ya lakanci sirrin da mutane da yawa basu lakanta ba, a matsayinsa na Uba wa baba da yaro ya lakanci furuci irin na fuskar bawa, wanda yake da gaskiya da wanda bashi da shi
Idan ya kalli fuskarta a yanzu kwarai yana karantar rashin gaskiya, sai dai ya fi karantar gaskiyarta a kan rashin gaskiyar, hakan sai ya raba masa abin gida biyu, ta yiwu ita din lwarariya ce wajen iya aikinta na mugun nufi ya sa aka turota, ko kuma gaskiyar da Allah ya haliceta da ita ke son hayowa ta bayanar da kanta?
Lebensa ya lashe a hankali yana sake tabatar da abinda zuciyarsa ke wakawa cewa koma mecece ita a haka ya fito dan yakarta, babu abinda ya shafe shi da tarin rikicin dake tare da ita, rikici yau ya fara gani ne? Shi kam a yanzu itace abokiyar gabarsa ita kadai, domin ta hayo ta hanyar da baya tunanin in har zai iya kawar da kai, kau anya kuwa zai iya? Ita wannan ta kama masa wani sunnan daban a gabansa? Aa wannan ba wasan da zai dauka bane!

A nutse ya yi mata daukan jariri, daukan da bata zata shi zai yi mata ba, gaba dayama irin tsayuwar yar Indi ta neman hanyar zabgawa a dubun lamba ce dan ta tsiratar da kanta ta kuma kaima innarta rahoton an samu wani shege mai shegen baki ya kaima ASADEEK bayani dala dala dan haka su shirya cire kai a cikin fada dan a yadda ake maganarsa sam ba adalci a lamarinsa, daga ka dan aikata laifi sai ya sare kanka? Ai ba tausayima kwata kwata a lamarin!

Da suturun dake jikinsu ya tsaya a kasan shower irin ta zamani wace ke zubowa dan kankin kanta dan aljanci irin na nasara

Ta ko'ina ruwan ya ringa sauka a jikinsu, hakan ya sakata tsorata har ta saka hannayanta dake rike da hijabinta wanda ta gama tunanin wannan kuma ba zai yi sallah ba dan ya ga uwawun maza domin da shine ya yi tawul ta hanyar daurawa a kugunsa, ta rukunkume shi sannan ta cusa kanta a cikin kirjinsa muryarta a raunane ta ja sheda tana buda bakinta dan yin numfashi ta bakin

Ita kam ta ga abu, a haka a jikinsa ta ringa jin hannunsa mai laushin balaki yana kamar shafata kamar kuma yana dan wanke mata wani abu, gaba daya sai ta sarewa duniya domin wani abu ya fado mata a rai ita da kawarta Yar dubu, a cen kauyen LABA akoy wata kawarsu da aka yiwa auren dole, a dandali suka ringa jin wani bayani wai mijinta manau makaleta ne, bata da hutu ya mayar da ita kamar sutura wace mutun dai mai hankali ba zai fito babu ba, tsegume tsegumen ke yawo a kauye har ta je da maganar gaban Innarta, a ranar innarta ta bige mata baki sannan ta ringa salalami tana shela gudu bayi da balbalin gida tana tambayar shin ta dan me ake nufi ne? Kai karshe dai a rikicewar innarta ita ta zauna ta zayane mata me ake nufi din sannan ta ringa wasa wuka tana cewa idan ta yarda ta je Aminu ya mata irin haka sai ta yankata sannan ta je lahira walakiri ya fara cin ubanta a kabari kafin ta tarda mai kankatttt din wanda ya haramta, sai gashi itama kamar dai makalematan ne Allah ya kawota wajensa, gaba daya sauraronsa da take yi dan ta gane yarensa ne, nufinsa zai karra ko zai ji tsoron Allah ne ya kyaleta?

Wani irin body contact ne yake gabatarwa a tsakaninsu mai wuyar fasara, cikin salama ya darwaye mata abinda ke jikinta sannan ya sauketa kafafuwanta a saman nasa cikin dabara ya ringa kai hannunsa kasanta a hankali duda tana tarewa tana dan kura masa ido kamar ta kama kwarton nan, har sai da ya gamsu da abinda ya daukarwa kansa niya a cikin zuciyarsa

Sake mayar da ita hannunsa ya yi ya dawo falon nanda jikakiyar rigarta ya shinfideta a saman gadon nan ya zamto sanyin AC ya shiga ratsa dukan kofofin fatar jikinta a dole ta ringa jin wani irin tsigar jikinta na mimikewa sakamakon sanyin, dan haka ya ringa dan son kamo abinda zata rufa cen kasan makoshinta ta furta "Sanyiiiiiiiiiiiiiii"

Kallonta da yake yi ya saka shi gane eh sanyin take ji, irin mimikewar da take yi kuwa ya saka shi gane kwarai ba zata yi masa gardama a yanzu ba, dan haka cikin nutsuwa da dane kokowarta a farkon farawarsa ya samu ya daneta kadan har ya dangana lalausan lebunansa a wajen bayan ya bude kafafuwanta sosai ya shiga gabatar mata da mugun sabo, sabon da ba kowani namiji ke yi ba, sabon da idan ka dandanawa mace shi ko ta bariki ko halalinka da wahala ta iya yin nesa da kai, zaka ji ana cewa me yake bata ta nacewa dan banza yana mata wulakanci☹️, mahaukacin sabo ne da namiji ke yiwa mace mai wuyar fasara, wasu matan saboda rashinsama ya saka basa gane kan abin, wasun kuwa sam basa sonshi😁, da wannan ASADEEK ya yi mata wani irin riko, tun tana zarro ido bata gane me yake faruwa har gaba daya ta rikice ta rukunkume fillo tana neman kurma ihu, a rikice ta saki abinda yake so ya sakin watau ta samu nutsuwa ta wannan hanyar sannan zufa ta tsatsafo mata a gaban goshinta dan rikicewa da bakon al'amarin da bata san shi kuma a wani mataki zata ajiye shi ba,
A hankali ya haye ya janyota jikinsa sannan ya ja masu bargo ya lulube su da shi ta yadda ta shige jikin nasa ta ringa sauke ajiyar zuciya kamar ta yi gudun tseratar da rai,
Hannunta na dama da ta dora a saman damtsen hannunsa ta jimke sannan ta kifa kanta a kirjinsa da irin dokawar da zuciyarta ke yi ya saka shi sauke ajiyar zuciya da yin dan murmushi a saman lebensa ya zagayo hannunsa ya lumshe idannuwansa dan yin barci yana sake jin amon sansanyar muryarta da ta kama sunnansa cirat tana kallonsa hira ce take yi masa kamar na sako da sako............................................................................................. Gishiri gishirin dake saman lebensa yake dan lashewa a hankali yana mai fatan Allah ya bashi ikon gannin ya iya jure wannan aiki, kar aje maimakun ya ci karfinta ya hadasawa kansa da ciwo mai zafi bayan ya rabu da shi.

_________________________________

Faduwar Mancheste din da yake kokarin balawa a hannun rigarsa bayan ya gama shiryawa da nada rawaninsa sasauke ya farkar da ita daga nanauyan barcin da ya kwasheta

Dishi dishi ta ringa gani kafin a hankali idannuwanta su washe ta sauke dubanta a bayansa
Tun daga saman kansa wajen rawaninsa har zuwa kasan wandonsa na shada fara lalausa da kuma farare karkar din kafafuwansa take kallo harda dan sake talabe kanta tana kallonsa a zuwan bai san tana yi ba domin a tunaninta bai san ta farka ba

Cikin nutsuwa ya gama dukkan abinda zai yi ya saka farar safarsa sannan ya juyo, hakan ya sakata rufe idannuwanta ruff tana sauraron takunsa da kunnayenta

Murmushi ya saki ya karasa bakin gadon ya rage tsayinsa ya mana mata kiss a goshinta, cen cikin makoshinsa ya ce" Zan yi tafia, ki min Adu'a idan kin tashi kin ji?, Sannan ki yi wanka fa kar ki mance........."

Idannuwan ta sake rufewa rufff hakan ya bashi nishafi sosai har ya zubawa fuskar tata ido, sannan ya mike ya juya ya saka lalausan takalmansa simple ba na gidan sarauta ba domin abinda zai fitar da shi din bai shafi haka ba lokaci daya ya lalubo wayarsa karama yana rufo mata dakin ya shiga dana msg a takaice ya tura kamar haka" Ki turon adireshin gidanku, yau zan kawo maki ziyara "

Da hanzari yake takawa har ya karasa wajen motar da aka bude masa ya shiga aka rufo sannan ya dubi sarkin gida cike da dakiya da mulkin murya irin ta sarakai ya ce" Boyayiyar fita ce"
Daga haka ya yi shiru ya gyara zamansa yana dan taba zoben azurfar dake hannunsa yana kallon barin da SHEIK yake zaune

Sarkin gida na fitowa da hannunsa ya ringa salamar mutane, hakan ya sa kowa ya juya cikin nutsuwa ya bar wajen domin sun sani idan har fitar sirri ce ZAKIN SARAKAI baya bukatar sanarwa a gari da cikin gida, sannan baya bukatar yan rakiya, harta motar da yake shiga idan fitar sirrin ce bata da number masarautar, su hudu abinsu suke fita, daga shi sai SHEIK, sai Direban dake jansu, sai DAN SAWANIN yaki wanda yake tafiye a saman doki komai nisan wajen sannan shi a nesa kadan yake da su bama zaka dauka tafiyarsu daya ba, hasalima shi din abin tsoro ne wa idannuwan al'uma , haka kuma WA'INDA suka san shi idan suka ganshi a waje sai su shiga neman UMUGHLUK ITIBEL dan sun san tafiyarsu daya ce


A hankali motarsu ta fara tafia, daidai lokacin da UMMA ta fito daga Bangaren Auta tana ta neme neme da tunanin ina yarinyar ta shiga yau?, Idannuwanta suka sauka a bakon lamarin, bakon lamari mana ASADEEK ne zai fita ba da sanninta ba? Ta san motocinsa na sirri baki dayansu, ko a cikin gari zai yi fitar sirri yakan sanar mata ko ta waya ne, ama a yanzu sai bayan motar ta hango tana ratsa jama'ar fada babu mai kaucewa da dukawa dan babu wanda ya san su waye a ciki bale a gane UMUGHLUK ITIBEL NE !

Gabanta sai da ya kwonci kwonci ya fadi dan haka kawai ta ji hankalinta na neman tashi da gannin haka

Da sauri ta juya ta nufi bangaren.................................















😁mun dawo, zamu dora in sha Allah
9/25/22, 16:55 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





4️⃣9️⃣


Da sauri ta juya ta nufi bangarenta dan zuwa ta yi kiran numbarsa, saima ta manta da neman inda Auta ta shiga domin gani take yi wannan rikicin ya fi na neman inda mahaukaciyar y'ar nan take

Tunda ta shige ta zauna ta shiga kira a karamar wayarta gaban munafukan bayinta WA'INDA bata boye masu komai
Kira ta ringa yi har sau uku ama ba'a daga ba, a dole ta dakatar tana hucin dake fitowa daga cen cikin zuciyarta tana kallon waje daya, domin ta sani ba'a masa kira sama da biyuma , idan ka yi daya biyu bai amsa ba ka bari zai taboka da kansa ne

Daya daga cikin bayin ta kara sada kanta tana fadin" Allah ya taimaki sarauniyarmu , sannan uwar UMUGHLUK ITIBEL, Allah ya karawa Gimbiyarmu lafiya da nisan kwana, zamaninki dawamame ne Uwa a wajen zaki, sannan mata daya kwal a wajen ja gaban da muke hari, me yake bata ranku haka ne?"

Cike da hura hanci take dubansu, a kausashe ta ce" A tsakaninku ku uku, akoy wace ta yi sake da aikin da na sakata ne a cikin gidan nan?, Ina nufin akoy wace bata cika aikinta yadda ya dace ne?"

Kusan a tare suke girgiza kawunnansu cike da gaskata mata yadda suka saba yi mata aiki basu cenza ba!

A birkice ta ce" Da mamaki kuwa!, A tarihi a kusa kusan nan ASADEEK bai taba yin fita ba tare da na sani ba!, Rabonsa da irin haka tun yakin sakashi jikina da na yi wanda ni kadai na san irin rayukan da na kawar kafin haka ya samu, dan bama so ya waiga ya ga kowa sai ni kwalin kwal, a yanzu kuma gayacen ya fita ko ina ya nufa?"

Wace ke yi mata leken bangaren UMUGHLUK din ce ta dauki magana tana fadin" Allah ya taimakeki, ta yiwu wani abin ya diro masa kai tsaye, irin mai dirowar nan ba tare da an shiryawa hakan ba, domin ni dai a jiya ina bangaren nan dan kuwa su Kamilu suka yi gadi ya barni na shiga da shigarkin nan, kuma ina nan ta fito da sasafe tana hawayen da ta saba na zo na sanar maki har muka sha dariyar abin, daga shi babu abinda ya faru hasalima sai da na tabatar ya hau salaya na yi anfani da ky din wajenki na fice da taimakon Kamilun, bayanshi sai fitowarnan tasa da kika ce mu dawo mu jirayeki zaki je da kanki Bangaren Auta dan wannan ta ce maki bata kwana a bangarenta ba"

Umma ta sake yin jimmm, sai kuma ta mike ta nufi dakinta ta rufo ta karasa wajen akwatin da ta boye maganin da aka turo dan NADIRAH ta zuba masa a abinci ta dauko tana jujuyawa,
Tunda aka kawo maganin ta so a yi anfani da shi, ama Nadirar ta nuna mata ba yanzu ba, wai ta dakata ta gama abinda take yi, kwata kwata bata san me yasa take sauraron yarinyar ba, abinda ta sani shine har wani shayin yarinyar take yi bata iya hawanta kai tsaye, ko dan tana da bakine? Ko idannuwan nan nara masu lulumshewa dake hadasa mata kasala da jin kamar ta janyota da karfi ta auka mata ne?, Akoy dai wani abu mai karfi a tare da yarinyar, ama kuma ta san ko ba komai yarinyar kamar ta san kanta, dan kuwa a irin yadda ta fara shigewa ASADEEK ta tabata zata gabatar da aikinta a kan tsari, dan hakama zata karra bata lokaci kadan ta gani!

Tino NADIRAH da ta yi da yannayinta ya hadasa mata bukatar aikata aikin da ya fi komai dadada mata ruhi, hikimar ubangiji kuwa ya bige mata tunanin dake ranta na neman auta harma ta ba bayinta dama suka rufe su hudu a dakin suka shiga aikata masha'arsu! ( Subahanalah)


Wani wiki wiki fa ita ta karaso falon bayan ta bude kofar ta shigo ta ja turus tana kallonsu kamar yadda suke kallonta

Auta kam tsam ta yi tana karewa NADIRAH kallo, kasancewar cikin bargo ta yi barci suturarta a jike ya da ba wani bushewa da kayan suka yi ana gannin jikarsu, kai harta irin laushin da gashinta ya yi ya kwonta lambak zaka fahimci wanke kan ta yi, ga hijabin dake hannunta kasancewar milk color ne ana iya gane jikarsa a ido dan kuwa bata saka shi hasalima kunyarsa take ji a ranta ita kam, da shi fa ya rufe abin jama'a!

Innarta kuwa kallon tsaf ta kata sai t dauke kai ta ci gaba da jera girkin fa suka yi ita da Auta ba tare da tace da ita ufan ba, domin alamun yan rikicin sun bayana a tare da y'ar tata, idan kuwa ta biye mata ta tabata zata juye mata borin kunya a kanta ne har ta nada nata duka a banza a wofi,

Kai ta juya wajen agogon dakin ta kalla, a zabure ta dake juyowa tana auna irin awanin da ta dauka a cen kennan? Ita da tace a bar kofa a bude ba inda zata? Kai innalilahi wannan wani irin tarin abin kunya ne haka ke yi mata tarere a cikin jama'a?
Da yannayin bigicewa tana ta taro kafadar rigar da ba faduwa yake yi ba ta ce" Ina kwana Innata"

Innarta ta sake tsareta da ido sai kuma ta dauke kai ta ce" Lafiya, je ki yi wanka ki zo mu ci abinci"

Fuskart ta takwakwaba nan da nan sai ga hawaye yana harhada kansa murya na gargada ta ce" Wanka kuma Innata? Me yasa zan yi wanka ni kuma Allah na tuba?, Babu abunda ya hadani da wanka Innata..........." Ta karashe tana sakin hawayen harda jan hanci fuska kuwa ta yi mata jajajir tana kallon innar tata

Hindu ta ajiye kwanon dake hannunta tana tafa hannu ta ce" Indi idan baki yi aniya da saurin kukan nan ba ina mai tabattar maki idan na kama kifa maki mari ko Habu ba zai amsheki ba bale Aban birni, da kaniya kin yi wanka da safe ne? Yau ga ya yanzu kuma wankan ne zai zama rigima? Wuce malama maza ki je ki yi wanka na sabulu tas ki yi kwaliya ki fito mu debi girkin nan idan kuma kika jima a ciki in bamu cinye kazar ba ki ce min ba Hindun habu ba!"

Ido ta kikifta harda su sauke ajiyar zuciya jin wankan ashe na sabulu innarta ke nufin ta yi

Dakinta ta wuce tana harhada tafia dan har ga Allah ba fa rasss take ba, burinta ta yi wankan nan ta dawo ta sanarwa innarta abinda zai summar da ita, danma kar ta fada yanzu ne innar tace sai sun koma wajensa a haka a ringa mata gani gani?

Auta dake tsaye idannuwanta a kan tafiyar NADIRAH suka sauka har ta shige dakinta tana cicin magani irin karma a wani kawo mata maganar da ba ita ba ta rufo a kan idannuwanta

A hankali ta dora dubanta a kan Inna dake ta dawainiya da kwanuka sai sake goge su take yi tana dan wake wakenta kasa kasa sosai hankali Kwonce

A hankali ta kai zaune saman kujera tana ta fama da tunaninta, har fada take yiwa kanta cewa me kuma ya hadara da irin wannan banzan tunanin? Ai ba huruminta bane sam, sai dai kuma katutun da abinda ta dan ba mai yiwuwa bane ya yi mata a kirjinta ya sakata sada kai ta yi wani iri

Inna dake miko mata ruwan Adu'a ta ga bata amsa ba ta ce" Ke kuwa tunanin me kike haka da yarintarki da komai harda wani motsare lebe kamar kina rike da duniyar nan?"

A hankali ta Kalli inna, zuwa yanzu ta gama gane Inna da yannayinta, shi yasa take biye da ita kamar jelar kare
A sanyaye ta sake kallon hanyar da NADIRAH ta bi muryarta a dan sarke kadan ta yi dan murmushi ta ce" Ko me ya jima auntyna a kafa ne?"

Inna ta juyo ta kalleta, sai kuma ta dauke kai ta ci gaba da hade hadenta a cikin nonon rakumin nan ta miko mata sabuwar tatsa ta ce" Dan kafa kai ki shanye wannan ki bani"

Auta ta amsa tana kallon yadda nonon ya cenza kalla , tana kallon nonon ta ce" Inna menene a ciki?"

Inna ta tabe baki ta ce" Haka fa, ku kam aikin da kuka fi kwarewa a shi kennan, tambaye tambaye baku iya nema ba, sai a riskaku ku ringa yada kai kamar kadagaren da ya sha jifa, Allah na tuba sarauta ko ta makada ana jifa ana shige da fice bale masarautar AGADAZ?, Gashinan ita wancen ai abin inaga a jikinta ne ko? Tunda ai labari dai kasa kasa ana jinsa sai hakuri, ki kafa kai ki shanye ki bani malama maza kuma ki shige ruwan cen da na tara ki yi wankam na zo na maki turare du kin zama wata sangayayiya kina tafe kamar baki da laka a jikinki, ni ba zan yarda da wannan iya shegen ba, ku zagine ku amshi gyara da nemam tsari ba iya kwaliyar da takun kasaitar ba kina raye makashinki a tare da ke, kuma abinda kike tunanin a kan Indi da aban datawa hakane , wai ni za'a yiwa magana a rufe jama'a? Ku dai Allah ya shirye ku baki dayan ku!" ....... Sababi Inna ta ci gaba da yi har ta shige Kicin ta shiga hasa wutar da zata yi masu turare turarenta da tace Habu ta tuta ya amso mata ta bar Auta kamar ta summa a tsaye

Da sauri ta kafa kai ta shanye madarar sannan ta nufi dakin NADIRAH
9/25/22, 16:55 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





5️⃣0️⃣



Nadirah na zaune tana mulka kurkum a jikinta mai hade da madarar gari dan shiga wankan mai gaba daya domin sai da ta kunce kitson da innarta ta mata dan ta wanke kan gaba dayansa ta dago tana janyo hijab dinta a gefe ta yafa a kafadarta tana amsa salamar Auta

Zama auta ta yi tana murmushi ta ce" Sannu aunty, ko na rayaki murzawar?"

NADIRAH ta yi dan tsai tana kallonta, sai kuma ta girgiza kai ta mika mata dilkar ta juya tana fadin" Murza min a bayana to Auta, dan Allah kar ki darza da karfi jikina gaba daya ciwo yake yi, na san dan na yi sharar bangaren cen ne........."

Auta lebenta kawai ta dantse dan gudun dariya kar ta kubce mata, wani irin farin ciki marar misaltuwa take ji yana taso mata, ashe ashe abinda ya faru kennan? Lalle dole yayanta ya zabura da NADIRAH ta fara ihun jinni a hancinta, dole du abinda ta aikata ya ringa binta da ido kamar ya ga bakuwar halita, dole ta siye gaba daya tunaninsa da motsinsa, ya salam wa zata fadawa wannan abin farin cikin? Bata da wanda zata fadawa, sai dai dan godiya ga ubangiji sai ta yi azumi daga gobe in sha Allah, tana gama shafa mata ta yi gaba tana tatare tataren kayan murje murjen ta shige bayi ta rufo bayan ta ce" Kainama sai na wankeshi sai kaikayi yake min"

Ita dai Auta sai da ta ga rufowarta ta sake zamaa tana kyakyata dariyar da a kusa kusan nan bata ga abinda ya sakata yinta ba

Mikewa ta yi ta bude window din dakin ta lumshe idannuwanta iska mai dadi na hurota, a hankali ta furta" Hakurin bawa keda wahala, da ace bawa zai jure da addu'a ya yi ta hakuri da tabas zai kai ga ci, Allah ka nuna min ranar da zamu rike dan jariri malakinmu a gidan nan..............."

Sai kuma hawaye ya bale mata na tarin kauna da tausayin yayanta, harta Huznah sai da ta bata tausayi, shekara nawa tana tare da shi, shekara nawa tana jurewa tana daukan hakuri? Ashe

Please Login or Register in order to submit comment