Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na godema Allah Mamah, na godema Allah, na kuma tafi da farin cikin gannin lalle Ubangijina shine gagara misali, Mamah, na san Abah babu abinda zai iya yi maku na bacin rai a dangane da abinda ya faru, ku din masu farar zuciya ne, shi kuma ya san talaka da mai Kudi ko mai mulki duka bayi muke a wajen Allah, talaka futuk na iya samun rabauta fiye da sarkin da ya zalinci bayi, shi yasa yake addu'a tun karfinsa tunda sarauta ta zamo masa dole, kar Allah ya dora zalintar bayi a zuciyarsa, Allah ya shiga tsakaninsa da aikata haka......, Mamah yanzu yaya zan yi da farin ciki? Mamah ina son yin waya da .......
Ina son yin waya da ............" Sai kuma ta yi shiru tana lumshe idannuwanta, domin sai ta ji matsananciyar kunyar kiran mijinta mijinta a gaban Maman, sannan bata saba kama sunnansa ba ko kadan

Inna Hindu dake share nata hawayen, muryarta a shake ainun , tana cikin yannayi ne na tashin hankali da kuma farin ciki, ita da kanta bata gane cikin Nadirah ba sai yanzu, emotion biyu sun hade mata, wani irin farin cikin hakan , domin a gidansu zata iya cewa Nadirah ce kawai ta yi dacen daga shiga sai dauka, mamantama sai da shekaru suka ja ta samu cikinta, bale ita gata cikinma bai samu ba, ama ga y'arta nan Allah ya kawo, wannan farin ciki dole ta yi ta ibada tana godewa mai sama, sai kuma tashin hankalin inda yar uwarta da mijinta suke, tabas wannan din shi zai fi disashe komai, sai fatan Allah ya bayana mata su

A sanyaye ta ce" Auta?, Shin wai me yasa mijinki ko a leke ba'a ganninsa? Ba shi babu danginsa? Menene ya sa ya barki ke daya a wajen nan baya zuwa ba kuma ya kira?"

Da farko shiru ne ya gabata a wajen, sai kuma a hankali Auta ta shiga magana kamar haka" To mamah yaya zai yi?, Da farko ya so daukeni mu gudu a lokacin da Umma kadai ce ta yi maganar kar ya kuma kirana ko a waya sai na samu lafia, sai kuma ABAHNA ya shiga maganar, domin Umma ta same shi ta nuna masa cewar dole fa sai an zabi daya, ko a barni tare da shi kulun in ringa kukan ni Abahna zan dawo, ni a kawo ni wajen Abahna, ni meye meye, ko kuma a kawo ni gefen Abahna ya hadani da likitoci a nema min magani , Abahna ya nuan ai bai ga hadin dan ina gannin mijina ko muna waya da shi ya zama matsala ba, mahaifiyarsa kanta ta tako da mahaifinsa kan maganar, a ranar Abahna ya yi tafia, Umma ta bugar da ni , sun ganni a matsayin mahaukaciya tuburan, domin shi mai gidan nawa yace sosai hankalinsu ya tashi, Umma ta hada baki da likita ya nunawa Abana dole sai an nisantani da shi mijin nawa in ba haka ba aiki ne zai ringa komawa baya, domin ba zan daina raba hankalina ba, a dole ya nemi zama da su baki daya ya gabatar masu da damuwar, ya nuna masu cewar ba zai tauye mijin nawa ba, yana iya karra aure ko ya sawaka min, duka dai abinda ba zai takura ba zai yi, shi ya nuna aa ba zai sakeni ba, ama iyayensa sun nuna dole fa sai ya yi aure, Mamah ina ji ina gani Umma ke kawo min komai na rahoton aurensa, aka yi ya tare da matar, shekara biyu ta nemi saki , wai ba zata iya ba tana rayuwa da mutun ama gangar jikinsa ta aura, ko hira take so da shi ta yi tsayi to fa sai idan maganata zata dauko, idan tana son gannin kyautatawa daga gareshi ta kyautata min, gidanta ko'ina kayana ne da hotunana , dakin mijinta hotunana, karshe dai tace ba zata iya ba, daga nan dai mahaifiyarsama ta daina zuwa, ban san dalili ba, a da takan leko lokaci zuwa lokaci, kuma du idan zata zo sai ta sanar hakan ke sakawa Umma ke makar da ni ta tsoratani, du zuwan da zata yi abinda zata tarar ya gyasa wanda ta bari...............sauki sai na Allah, a dole ta yarda na haukace, abin takaicinta danta ya ki rayuwar wani auren da wata........................"

Idannuwan Umma a rintse, cike da takaicin wata rayuwar, a sanyaye ta ce" To ke, me yasa kika zabi zuwa nan ki zauna bayan idan kina tare da mijinki duk rintsi zaki tsalake wata fitinar?"

Jajayan idannuwanta ta dago ta kalli Fuskar inna, hawayen dake diga a fuskarta ya sakata sauke ajiyar zuciya a hankali ta shiga share mata, a sanyaye ta ce" Mamah, a gabana Umma ke zuba magani a madarar Abana, sanadiyar zamana a gefensa kuwa sau bakwai ina zubar da abincin da ta zuba guba a ciki, domin wani lokacin nakan tayar da haukan karya na barar da shi, wani lokacin kuwa nakan yi summar karya ta yadda ba zai iya duban abincin ba, da addu'a da komai Allah ya sa bai ci ba, Mamah, na san ban isa na hanna ba, ama a lokacin gani nake yi ifan na matsa komai tana iya yi, har ta gane da gangan nake hanna masa ci ta tsoratar da ni da maganar mugun aikin nan da take yi, tace na jawa kaina zama a masarautar har na tsufa, kuma ta yi alkawarin idan na yi gigin sanar da maganar zata bugar da ni ta min sharin madigo, Abahna zai jefeni da kansa, shi kuwa ciwon abin ya kashe shi..............."............. Ta idasa tana mai fashewa da matsanancin kuka, kuka na samun sasaucin nauyin dake zuciyarta, tana jin yadda jikin Inna ke rawa na bacin rai, tana kuma gannin yadfa take hanna kanta sakin kukan itama mai karfi

Zuciyarta cike da zafi da kunna a sanyaye ainun ta ce" Allah zai saka maki, Allah zai sakawa Yayanki, ba ku kadai ba Allah zai saka mana muma da ta sako mu a layin ta'adanci, Allah zai sakawa du wani wanda ta cutar, koda ta samu tsiratar da kanta a wannan karron zata hadu da nata gamon , domin tana wasa da hakin da Allah baya yafewa, hakin wani a kanka Allah baya gafarta shi, idan kuwa sakankancewarta ya saka bata gane furfurar kanta da janyewar fatarta da da yanzu ba lalle a kireta mahaukaciya, bata da hankali, ta kuma tabe, wannan mata na ajiye makaman fadana da ita, wannan mata Allah ne zai yi maganinta, wannan mata bama tunanin mutuwama zata zamo mata aya, irinsu su rayu sunna gannin rayuwar ta zame masu ukuba ya fi, irinsu ya dace su jima sunna kallon lamarin ubangiji gannin idannuwansu, wannan mata sai ciwo ya koya mata hankali, wannan mata sai tsufa ya koya mata hankali, Allah ya sa wannan mata ta maimaita shekarun da ta yi a duniya sau biyyar ta yadda zata ringa ihun kiran mutuwa da tunanin shin ita mutuwar ta manta ne?, Ta yadda zata bar duniyar da abinda take cikinta ba tare da ta mutu ba! Tabas wannan matar la'ananiya ce wace bata jin tsoron Allah, munafuka ce ita kuma azaluma ce, ki yi hakuri AUTA, ko me ta yi maki Allah zai warware maki kin ji?"


Sosai Auta ta ji sanyi a zuciyarta, sosai ta ji bakinta ya bude, har zuciyarta ta cika da mamakin dama itama zata iya bude baki ta saki damuwarta haka wani ya saurara?

Kusan a nan suka wuni, abinci da sallah ke tashinsu, kiri kiri NADIRAH kuwa ta labe a daki ta ki fitowa, da farko kuka ta sha da tunane tunanen da ba zasu gyarata ba, daga baya ta rike carbi tana Adu'ar Allah ya bayana mata iyayenta cikin aminci da lafiya, in sha Allah zata zauna da shi idan ya nemeta dan ta ji yaya za'a yi ya barta ta je neman iyayenta, domin ba zata iya zama bata neme su ba fa, sai dai ya yi hakuri idan ta gansu ya yanke hukuncin dake gyara shi a kanta!


A bangarensama, sun cika dare sosai da SHEIK a bangarensa, domin a dawowarsu kusan magariba sai da ya bada damar shigowar UMMA , wace kana kallonta zaka ga bata tare da nutsuwa ko kadan, a yanzu ta saka alkyabar ama gaba daya tamkar an tonota daga cikin rami, domin kana ganninta zaka ga tsantsar tashin hankali da firgici a tatare da ita

Sosai ta gabatar da rainin wayonta, da su koke koken yanzu yaya za'a yi ba'a ga bafansa da gimbiya ba, shima ya nuna mata tsantsar tashin hankali da sheda mata yanzuma daga Tanut din suke an baza dukkan jami'an tsaro ana nemansa, sannan an dora Huzaifa kujera kafin a ganshi
A nan mamaki da tarin tambayoyi suka so zautata, me ya kawo HUZAIFA SOJA saman karagar mulki bayan ga ya'yansa maza manya? Ita fa, haukacewar da ta kusan yi wai jin an sace su, waye ya sace su? Ina suke? Ta zata abin wasa ne kamar yadda suka tsara ne sai ta nemi wayoyinsu ta rasa, karshema baban yaronsa ya sheda mata hankali tashe cewar an fa sace su, kamar ledar piya wata jama'a?, Mutane uku rigis kuma ba'a ga wanda ya dauke su ba? A haka ta koma tana tsantsamce da kowa, domin tana tafe tana waige waige da kame kanta dan kar aje itama a ritsa da itan, wanda ya sace sarki da matarsa da yarsa ta yiwu harda ita a layi, tana shiga bangarenta ta garkame ta kori kowa, sai a lokacin ta yi arba da madarar UMUGHLUK ITIBEL, wace ta yi baki kirin sakamakon maganin gubar da ta sauye baki daya
Hankalinta ne ya sake tashi, ta je garin neman rarumar jug din ta barar da shi ya fadi kasa, ji kake tartsatsa ya fashe gaba daya madarar da maganin suka bare nan kasa
A wajen ta zauna tana hade jikinta tamkar wata karamar yarinta tana yarfe hannayenta bayan ta tuge dan kwalin kanta tana ta wani abu kamar sabin kamu a rikice gaba dayanta ta ce" Na shiga uku, na barar da maganin gana daya, yanzu wa zai samo min wani?, Kai kuma dan Allah ka taimaka ka kirayeni ka ce min kun buyan ne ya sa ake tunanin sace ku aka yi, idan ba haka ba ina zan shiga da faduwar gaba da tsoro a cikin masarauta?, Waye ya sace ku? Me kuka yi masa? Idan ASADEEK ya gane ba ku kuka haifi wancen yar banzar ba yana iya tisoni a gaba fa?, Idan ya tambayeni me zan ce masa bayan ya san na san yarku? Wayo na shiga uku menene wannan tashin hankalin dake nufo ni, komai na kasa ganewa gaba daya komai sai shige min yake yi a cikin junna?, Wayo na shiga uku ..................."


Da wannan suka cika dare shi da SHEIK sunna sake tataunawa a kan hanyoyin da zai bilowa wasu abubuwan
10/10/22, 08:38 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





6️⃣1️⃣


Sai kusan karfe tara da wani abu SHEIK ya tafi, shima ba dan sun gama ba, sai dan su hau kan tsarinsu na gaba, wanda SHEIK din ne zai gabatar da binciken lokacin da zasu iya dauke babbar jakadiyarta a kwana kusa, dan basa so a firgicinta da faduwar gabanta ta samu sasauci ko na second daya

Alwallah ya daura bayan ya yi wanka ya haye salaya, so yake yi zuciyarsa ta yi sanyi, so yake yi ya samu nutsuwa irin wace babu wanda ya isa ya bashi sai ubangijinsa
Sai da ya kai kusan karfe biyun dare yana ibada, sannan ya mike ya karasa wajen kwonciyarsa, ya yi adu'ar barci ya kwonta yana rungume hannayensa a samn kirjinsa, a sanyaye ya lumshe idannuwansa yana jin nutsuwa da sabon tunani a kan matsalolinsa sunna ta shiga kwakwaluwarsa, a cikin tarin dacin da yake ciki sai ya ringa hango sauki , saukin nan kuwa ba komai bane face wani haske da ya shigo kwakwaluwarsa, hakan ya saka shi sakin dan murmushi yana jin abin har cen kasan zuciyarsa, har kamar abin na son ya saka shi jin babu dadi dan baya gefensa, ba komau bane face NADIRAH, zai iya cewa gwadama da suka bashi mace a lokacin da baya tunanin samu....... Zai iya cewa gwadama da suka cenza masa da Soul mai daraja, daya tak da bai hado irinta a kusa ba, idannuwansa ya lumshe a saman lebensa kadan kadan ya ce" TUZURUWAR kauye, ya dace a bar maraya ya huta, tunda ba za'a zo inda nake ba............a bar tunanina ya huta ko?"..................................................... Cike da begen nan a kasan zuciyarsa ya samu barci mai dadi, mai kuma nauyi, dan kuwa sai da kiran sallah kusan karewa ya jiyo a kunnayensa

____________________________________


Washe gari

A ranar wunin da aka yi, an yi shi ne cikin tarin taro na jama'a, ya wuni a fada ne cirrrrrr ba sasautawa, domin baki ya ringa samu ta ko'ina masu tafe da son sannin maganar da ake shelawa ko gaskiya ce?, Da jajantawa, asalima sakonsa na aiken da ya yiwa sarkin yanka sai da yamma suka kadaice ya sanar masa , sannan ya samu ya sake fita ta sirri ya je ya ga bakinsa da ya kilace idan har sun fara gane sun shiga uku ko da saura? Ai kam ya tarar da su ba yadfa suke, madubi ne da shi yana iya ganninsu tar tar, su kuwa basa gannin komai, a lokacin da ya je ya same su Bahija na zaune tana kallon waje daya, fuskarta ta yi jajajir tamkar wace ta sha duka, ita kuma kuka ne ta sha kamar ba gobe, iyayenta kuwa mahaifinta yana tsaye yana ta kallon wutacen dakin, ita kuma mahaifiyarta tana kwonce ta dukunkune cikin alkyabart , ga dukkan alamu ita rashin shayin tuni ya fara kaita makura

Bai ce komai ba ya yi tafiyarsa bayan ya sheda masu kar su rasa abinci ko abin sha, shayi kawai za'a hanna masu

Yana komawa bangarensa ya tarar da tsare tsare irin na mata masu daraja,
Watau aiki irin na mace mai kishin mijinta
An cenza masa su cafet labulaye, komai dai hajia uwar gida ran gida mai girma HUZNAH abincin ruhinsa tana kai kawo sai baza kanshi take yi ta kuma dauki kwaliya daidai gwargwado, duda tana fama da kayan alkyaba, ama kuma tsarin shigarta dake kasa tamatukar kawatar da idannuwansa ta tarbe shi da kula da kauna ta rakashi har dakinsa sannan ta koma falo cike da farin ciki, a zuciyarta tana ayyana ko me take tunani ta fi ta, domin ba zata taba gwada mata kula da mijinta ba, zata ga aikin soyaya ba nata na shirme ba, za kuma ta ga ko tana yar uwarsa ita din ta fita tunda soyaya ce tsakaninsu da aminci, du abinta bakuwa take a cikinsu ta yi biyaya ko ta gaza gane komai, ita dai babu Wanda ya isa ya fit sannin wanene mijinta!



Koda ya sauko cin abinci ya ringa binta ne da kallo mai cike da tausayi da tausasawa

A lokacin da take zuba masa abincin da ta bata lokaci tana daahuwarsa , a tausashe ya dora hannunsa saman nata ya sakar mata da murmushi a hankali ya ce" Ya isa haka HUZNAH ko so kike na gaza barci ciki ya cika sosai?"

Murmushin ta sakar masa itama tana sada kanta, a nutse ta ce" Allah ya taimakeka, idan ka gaza yin barci ai na bani, gwara na bari haka din"

Abincinsu suka ci hankali kwonce, saima da suka kusan gamawa ne , bayan shi ya gama tuni, yana dan shan madara yana dan kallonta ya samu kansa da sakin murmushi, fadansu ita da NADIRAH ba zai taba daina bashi dariya ba, shi kam gaskiya bai san ko aikin shedan ne, ko menene? Sai ya ji fadan nasu ya matukar kayatar da shi, in dai irin fadan nan ne su yi ta yi yana tsakiya yana murmushi abinsa, shima namiji ne kishi ne ake yi a kansa, ya isa ne wai, a hankali ya ce" Bakya yin missing din Auta a diner?"

Abincin da bata gama ci ba ta dan dakata, sai ta samu kanta da tauna maganar a ranta, to ama a kan me zata yi missing din wace bata girmamata, ai Auta bata wani dauketa da daraja ba, gayanan ana yi mata kishiya ta je ta dinke da ita wai harda kwana a bangarenta , ita zata nunawa dangi? Ai dadin abin itama ba daga sama akaa cilota ba, tana da nata dangin , babu wanda zai wulakantata saboda haka

A bayane kuwa sai ta yi murmushi ta ce" Ni raboka da Auta ai yau kwana uku, tana bangarensu"

Dan tsai ya yi, sai kuma ya kawar da maganar daga ransa, domin da farko sai ya ji kamar ba dadi a ransa, Auta ce fa, mai sunnan Maman Aba fa, ko me yasa sam HUZNAH bata damu da kowa nasa ba in ba shi kadai ba, ba ruwanta da kowa nasa sai shi kadai tak, ko mtan Sheik bata zumunci da kowa, ko me yasa? Ita danginta kadai take mu'amala da su, summa basa wani ziyartar junna in ba ta yi dalili ba, ko dan sunna aure da sarakunna ne? To ma shi zumunci ai ba'a ce banda matan manya ko manya ba, du wanda bayaa zumunci ai baima ji dadin rayuwarsa ba sam


Yana kai dubansa kan kujerar Nadirah ya samu kansa da sakin murmushi, rabonsa dai da ita tun jiya daa safe, ko a wulge ba'a leko shi ba, da ace wani abinta ya tsumkota, ko yan nemna rigimarta sun tsumkota da yanzu ka ganta ta yiwu zani daban, riga daban ta zo ta gabatar da neman rigimarta ta karra gaba, wai idan zata gaishe da jama'a sai tace sasanunku, uhum bai taba gannin gidan rikici irin yarinyar ba sam, abinda tun randa ta fara ganninsa bata jin tsoronsa bale yanzu da mata suka ga maza? Ai sai dai a kokarta a ji tsoron Allah kar a raina mazan kawai☹️

Sun dan jima a falon kasa sannan suka haye sama,

A daren ya so fara yi mata sharan shanye, sai dai gaba daya ya ji raunin hakan a zuciyarsa, a dole ya yi shiru da bakinsa ya shiga gabatar da sallah har sai da ya tabatar ta yi barci sannan ya haye sman gadon gefenta ya kwonta yana binta da kallo
Kai in kuwa hakane, gaskiya an cuceta, ga dai mace fa, sai dai an shiga tsakani, an hanna mata jun dadi bale shi
Dole ya ji tausayin HUZNAH, dole kuma ya taimaketa, dole ya tayata neman hanyar da zata bila

*___________*


Ranar biyun kwananta

Kasancewar yanzu itama takan hantse ne a bangaren mijinta, yauma tana zaune saman kujera mai zaman mutun daya, mai laushi tana binsa da kallo, a lokacin da yake dan kawonsa a cikin dakin barcinsu hannunsa daya a bayansa a jimke, dayan kuwa a mike a kusan kunnensa yana amsa kira, da yannayin da ta fahimci kamar an dan sosa ransa, sai dai a nutse yake bayanin da ta kasa gane wani yare yake yi, domin ba larabci bane, ba kuma turanci bane, ba buzanci bane, ba kuma hausa bane, har ya gamaa ya kashe kiran ya dan jefa wayar saman bed dinsa dake gyare da shinfidar da suka kwana sama wace shine ya jaja da hannunsa ya gyara dan HUZNAH kam bata san wannan yaren ba, sanna ya juyo inda ya saka ta zauna dan zai tatauna da ita


A nutse ya janyo kujerar dake gefe ya ajiye face da ita sannan ya hau ya zauna yana mai hade hannayensa ya zubawa fuskarta ido, wace hakan ya sakata sada nata idannuwan dan sun mata kaifi a cikin natan

Dan gyara zamansa ya yi yana kallon agogo, a hankali ya ce" HUZNAH, wata tambaya ce da ni kuwa, ban sani ba ko zaki iya tuna a lokacin da kike amarya, me da me ya faru?"

Kanta ta dago da alamar tambayar bata gane ba

Dan murmushi ya yi ya ce" Oh sorry, ina son sannin a lokacin da aka kawo ki gidan nan, da wa da wa kika mu'amalanta? Wa da ya maki kyauta? Me da me aka baki? Waye mai maki dahuwa?, Wa yake kula da harkar tsaftar bngarenki, komai da komai dai"

Da alamu na ta fara damuwa ta ce" SULTAN, wani abu ke faruwa ne?"

Gefe ya kalla kadan, sai kuam ya sake dubanta, bai ce mata komai ba yana kallonta, watau dai amsa yake so kawai

Zama ta gyara a hankali ta shiga tunani, maganar shekara goma ce fa yake yi mata kai tsayen nan? To ita wasun a lokacin da ko kallonsu bata iya yi dan kunya da bakunta da kuma mutunta su? Abu daya zata iya tunawa tunda aka kawota gidan a matsayin bakuwa

A nutse ta fuskance shi ta ce" Aban AUTA, a lokacin da na zo gidan nan bakunta mun zo da jama'ar fada ne, a kala sun min sati biyu har sai da Abah yace ya isa hakanan maza su dawo gida, abinda nake tune da shi dai a lokacin da nake da bakunta komai nawa a wajen UMMA ne, kama daga abincina, suturuna wa'inda aka ringa nuna min kafin a kawo ni bakunta bangarenka, har zuwa shirye shirye irin na amare da ake kara yi a lokacin, wanda a wannan lokacin ban ga an yiwa BAHIJA ba"

Idannuwansa yake dan kiftawa bayan ta ajiye maganar

A nutse ya sake fuskantarta , da hannunsa na dama yana dan misaltawa ya ce" Ohk, a cikin launikan abincin da ake baki, ko sutura, ba'a baki abinda ya saka kika tsantsamta ba?, Koma menene ba'a baki wani abin da ya saka kika dan yi mamakin abin ba? Ko sutura baki yi anfani da wata wace sam baki yarda da ita ba?"

Fuskarta na nuna alamun damuwa ta ce" Allah ya taimakeka, hankalina ya fara tashi da maganar nan, shin akoy wani abin da yake faruwa ne dan Allah?"

"Kima tune ko bakya tune da komai?" Ya sake fada kai tsaye yana kallonta

Ksa ta sada dubanta, gaba daya kanta ya fara sarawa dan neman abinda ya saka shi yi mata tambaya irin wannan, gaba daya ta nemi amsar da ya dace ta bashi ta rasa tunda ita bata ga dalilin tambayar tasa bamaa kwata kwata
A tunaninta bata hango wani abu da aka bata ta ci, ko ta saka a jikinta ba, wanda zai sakata a wani irin yannayi? Ta rasa gane gabanta bale bayanta, gashi sai magana yake bata a dunkule

A sanyaye ta dago tana kallon kamilaliyar fuskarsa, ba zata ce tana karantar bacin rai a fuskarsa ba, duda ta yi mamakin yadda sam yau bai tashi da muguwar damuwar ya kasa shigarta ba, hasalima bai gwada shigar tata ba, ita dai ya taimakawa ya rikitata har ta samu nutsuwa, ama shi sai ya yi kwonciyarsa yana rungumeta a jikinsa, ta yi tunanin zasu farka daa ciwonsa ne , sai ta ga ya tashi y shige bayi ya samu sallat asubahi, har gashi da ya shigo sun dora hira

Ajiyar zuciya ta sauke a sanyaye ta ce" Ni dai a tunanina, bana tune da wani abin da aka bani wanda ya sakani a wani yannayi, duda ban fahimci wani irin yannayi kake nufi ba,ama sam ni ban ga wani abin da aka bani wanda ya sakani a shaku ko hali na rashin lafiya"


Idannuwansa ya lumshe, a hankali ya kai hannunsa saman llalausan sajensa yana shafawa
Kasa kasaa ya ce" thn, kina iya tafiya "
10/10/22, 08:38 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*







Please Login or Register in order to submit comment