Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi barci? Ni fa du ganni nake yana iya summa, in ba haka ba babu inda zamu je, kin san Asadeek zai iya aurotan kuwa? Wace ta bijirewa iyayenta saboda shi tsaf zata ci mana uwa Aunty"

Ikon Allah Jakadiya ta tsaya kallo dariya na cinta, Auta kuwa kawai dolema ta saka yar dariya tana rungume hannayenta tana kallon tsayuwar da suka yi suka harde hannaye

Sheikh shima dariya ya yi yana girgiza kai, ya bada umarnin a tafi da ita gidan baki, a bata dama t dawo hayacinta sannan ta koma gidansu na familly , domin sarauta ta sauka daga kansu tuni, an dora ainahin dan sarkin mai adalci, jinnin sarauta mai mutunci, da kyar aka cicibeta tana dirari tana ihu tana waigo shi aka fitar da ita, shi kuwa ya sauke ajiyar zuciya yana dawowa wajen mai Damagaram a zuciyarsa ya dauki niyar in sha Allah zai taimaka mata, zai saka a sakata a hanyar da idan ta yiwa kanta adalci zata ji dadin rayuwa ta tubarwa Allah, in kuwa ta ki shikenan, shi dai yanzu kuma gaskiya matan cen biyu da suka juya bayan an tafi da ita baya tunanin zasu bari ya karro wata, to tuzuruwar kauye har ba zata ce a rabu bs? Ta aika tace a rabu ya shiga uku

Sai da komai ya tafi yadda ake so sannan baki kowa ya kama gabansa, matasa kuwa sai da ya yi magana da babar murya cewa babu su babu tarda ahalin asaraki, su barsu su rayu yadfa suke so, du wanda fa ya tada doka koda da sunnansa ne sai doka ta taka shi!, Da wannan ya shige gidansa, bangarensa ya tarda matan rayuwarsa, su uku an yi girki na gani na fada abin mamaki ana zaune ana hira harda wasa da dariya

Yana zama ya saka su a gaba HUZNAH ta duka har kasa tana hawaye ta nemi gafararsa , sosai ya ji dadin haka harma ya saka masu albarka baki daya sannan ya umarci auta maza ta tashi mijinta na jira

Mikewa NADIRAH ta yi tana murmushi ta kama hannun Auta ta ce" Allah ya bamu alkhairi Y'ar gidan momy mu je"

Da mamaki yake kallonta, hakama HUZNAH wace jikinta ya karra yin sanyi

A yanzu ta sani NADIRAH na son ASADEEK tamkar ranta, ama ta fita hankali da wayo ta juya kai ta tafi ta barta a gabansa , lalle zata yiwa kanta karatun ta nutsu kar ta barar da kimarta a idannuwan mijinsu ta hanyar yin koyi da dane zuciyarta a kan kishinsa ta gabatar da kishi tsaftatace ko dan ta karra samun fada a zuciyarsa

Yana kallonsu har suka shigewa ganninsa, sannan ya sauke ajiyar zuciya, bai zaci haka ba, kuma a cen kasan zuciyarsa ya so ya kwana da ita a kirjinsa harma ya ji dumin babynsa, sai dai wannanma dake gabansa matarsa ce kuma mai kaunarsa ce, da wannan ya bata dukkan kulawar da ta dace, itama ta bashi, har aka wayi gari yau HUZNAH ta kawo daki, itama ta zo a mace, Asadeek ya san wacece ita, ta kuma ji menene mazan da take mararin ji har tsoron hakan da neman agajin a barta ta huta ya damketa, dan kuwa ta samu maza a lokacin da suka sake sannin ciwon kansu suka iya haukata mata ta yadda sai sun ji kamar zasu sume dan rikicewa da dadadan lamari kuma zazafa wa bakon shiga........................

Kwonci tashi Asarar mai rai
Yau ya kama wata takwas da aka yankewa mazaluntan wannan ahali hukunci, ya kuma kama watan haihuwat NADIRAH wace ke rainon cikinta cikin kula da tatali na jama'ar dake zagaye da ita, tamkar zasu cinyeta , bama da cikinta ya kai wata bakwai ya zamana idan ta motsa sai dai dan ta yi tafia dan samun lafiyar jikinta da ta abinda yake cikinta, domin gogan ya gama tsare gaba, ya tsare baya, yace aa baya son garaje a bi a hankali zai fi alkhairi, idan ka ga yana garaje yar mutane ya tura saman gado, a nan fa zai ce ne hanya yake so ta budu da kyau dan abinda ke cikinta ya samu fitowa lamun lafiya, ita fai bata da abin cewa sai dai ta jure ta rintse ido, dan kuwa ASADEEK ba abin ya yi ya gama tana barci bane, dole sai ta dadage kar mata da girmansu su ringa ihun a taimake su

Innarta, tunda cikinta ya tsufa ta sake dawowa bangarenta, dan kuwa Habu yakan turota fa kansa ne dan a yanzu sunne manya manyan masu algaitar fadar UMUGHLUK ITIBEL elhazai ne, ganninsu sai da takarda........., Tana nan ta dafa wannan ta bata, ta dafa wancen ta bata dan a samu saukin haihuwa ga ruwan rubutu ba dare ba rana daga aban birni, inda innar birni ke nata rokon ALLAHn ta hanyar hanna kanta barci tana rokon Allah ya raba lafiya

.......................................................

Nishi take yi da dukkan karfinta, a cikin dakinta na barci ne, zufa take tsiyaya kamar babu sanyin ACn da HUZNAH ta kure ta basu waje, ama kan dan ya ki fitowa

Innarta dake tsaye tana matsar hawaye hannunta rike da carbi fadi take" Indi, kamar zaki yi kashi haka zaki nisa, ki yiwa Allah ki yiwa annabi ki nisa dan nan ko y'ar nan su fito hankalinmu ya kwonta, nisa mana"

Ina, Nadirah ba baka sai kunne, idannuwa kawai take zarrowa tamkar zata ciro su ta yarr, azabar ta kai wajen da ba zata iya magana ba yau sai dai nishin da kuma amshi hailalar da Matar Sheikh ke maimaita mata a tausashe tana faman fada mata an kusa ga kai nan ya bado fitowarsa ne dai bai fito ba
Lalle a yau ta yarda cewa idan Kanta da na ASADEEK za'a hada a yi na danta ta shiga uku, jama'a babu wanda nasa kan ba zai amshe langa uku ba tsaf , ina ga shida? Ita kam tata a nan zata kare kuma, shikenan sai dai a ringa fadin ai an yi wata NADIRAH a zamanin da ya shude


A waje kuwa, fifitu HUZNAH ke yi masa, yana zaune hannayensa bibiyu a dafe da kummatunsa ya zubawa SHEIK ido, wanda a dole ya janyo shi ya sako shi dakin nan dan da ya kawo matarsa hannunsa ya riko yace idan baka zo ba in na summa wa zai dauke ni? Gashi dai tun dazu ya yi wani tsuru tsuru yana kallonsa sai kuma ya kalli dakin, sai ya sake kallonsa ga zufa sai sjika maza take kamar shi ke nakudar yana ta yarfe hannu, ita kuma HUZNAH na famar masa fifitu da hannayenta kamar ta haukace dai itama bayan ga AC na kada su

A tausashe Sheikh ya ce" Ka yi addu'a mana ASADEEK, ka san dai ba za'a kaita asibiti ba ko? Ka sani sarai"

Da hannunsa ya nuna cewar yana yi a zuciyarsa sannan ya sake cira kai ya kalli dakin, kai innalilahi wa inna ilaihi rajune, haka haihuwar da take? Kalau fa suka zagaya da ita jiya da yaman nan, ama da asusuba ace masa wai tana gwuiwa? Gasu a gwuiwar har wata asubar zata zo shiru? Lalle a gaishe da mata, wannan ko kashi makayi ne ya rike ka ka kasa fitarwa na awa daya sai ka ji kamar zaka summa bale kan dan mutun? Ga tuzuruwar kauye da katon kai, shi hanyar cema gaba dayanta in yana aunawa sai ya ji gwara dai a je asibitin nan, in ba ikon Allah ba yaya za'a yi hanyar dake komawa ta matse taf kan Da ya fito?

An sha daga, kafin kai yake fitowa, cikin hikima ta idasa zaro jikin wanda ke tafe da uwa,
Yaro ni kosashe jajajir da shi masha Allah ga ni'imat gashi luflufluf a lulube a saman kansa, hannayensa a jimke, ana kuma ciro shi ya calara kukan da ya saka ASADEEK mikewa a haukace yana zarro idannuwansa, sai da SHEIK ya riko shi domin dakin ya nufa da nufin shiga bayan ba zasu so ya shigar masu a irin wannan lokacin da haihuwa ke raunata mata ba

Tarin farin ciki sai da ya saka su zubar da hawaye, cikin sauri Inna ta shiga kimtsa shi yana cacalara kuka kamar zai tsage dakin tana aukin yi masa waka tana juya shi kadan kadan har ta saka masa sutura tana kallo matar SHEIK ta kama NADIRAH ta shige da ita bayi a hankali bayan ta dauke ledar haihuwar ta yi ciki da ita , ita kuma ta nado jaririn dake ta yanyar yanyar ta fito da shi fuskar nan tata kamar ginar auduga ta miko shi wa HUZNAH tana fadin" Wannan miji nawa dai toh, ba dole ya ta ringa zarar ido kamar ta ga mala'ikan mutuwa ba, gayanan yatsa a baki ko me yake nufi kuma? Gaskiya ya kama kansa dan yata barcima zata yi...."

ASADEEK hannunsa na rawa yana kallon jaririn bayan an dora masa shi a hannayensa sai ga Auta ta shigo da gudu dan kuwa tunda abu ya kankama HUZNAH ta sanar mata , ita kuma tace ina ai ba zama sai AGADAZ, sai gata ta shigo ta ci karro da farin ganni

Fadin murna da farin cikin wannan ahalima bata baki ne, kafin kace menene wannan gari ya dauka, murna ta cika ko'ina, hanadallah kawai ake yi, farin ciki kawai ake yi ba baba ba yaro, abu ne da ake jir ake nema ido rufe

Sunna gama gyarata suka fito suka fice baban falonta aka bar ASADEEK shiga ciki da babyn a hannunsa

A hankali ya haura saman gadon da aka cenza shinfida da sabon abin shinfida , dakin sai kanshin turaran ruwa na daki yake dan an zuba shi sosai an gyara ko'ina sai walwali yake karnin nan an dake shi da hypo an ci karfinsa da turaren wuta


Ta yi laushi sosai tana rufe da bargo, idannuwanta kasa kasa take kallonsa har ya idasa hayowa ya rungume babyn a kirjinsa yana kallonta idannuwansa cike da launi na tsantsar soyayarta a cikinsu a hankali ya ce" Allah ya yi maki albarka, Allah ya raya *TUFAINAT*"

Idannuwanta ta lumshe a hankali tana murmushi sannan ta jimke hannunsa a cikin nata , sunnan dda take fada masa tana so ya sakawa yaronta, itama ta ji dadin haka sosai a ranta

A hankali ya saka yaron a tsakiyarsu ya zauna yana ta tofa masu addu'a har barci ya dauke uwar, sannan ya dauke dan ya je ya kaina Inna Hindu dake tsaye kan kaffafuwanta ta yi nan ta yi nan da waya a hannu fadi take itace Hindu ta habu uwar Indi matar UMUGHLUK, yau dai Indin ta haihu ga dan da nan masha Allah da shi a zo biki


Tun daga ranar ya zamto babu hutu babu masala tsinke a fada har ranar sunna ta zagayo aka zanna sunna aka sha wunin biki cikin farin ciki da kwonciyar hankali

Daga wannan lokaci lamari da yawa ya cenza, daraja da kima tata ta sake nin'ninkuwa a idannuwan mijinta da al'umar gari, sosai suke farantawa junna rai sunna kuma kare mutuncin junna da bacin ran junna
A tsakaninta da uwar gidanta kuwa, mu'amala ce ta wayewa da kuma zama da zuciya daya
Ba maganar ba sabawa dan kuwa rayuwa tsakanin harshe da hakorina akan sabawa bale mutun da mutun, sai dai du tsanani ana kokarin sako tsoron Allah da kuma kare hakkin makoci dan a ringa tafiyar da mu'amala lafiya

Sannu a hankali ta zubda wanka, har ta koma bakin aiki, inda baby ya zamo fan yawo abinsa kulun yana bayan inna Hindu ko bangaren HUZNAH, wace a yanzu itama ake yi mata tsatsamin cikin dan kuwa wata ya shige bata ga al'adarta ba, ga kuma yan ciwuka dake sakota a gaba .............

A ranar da ta koma baban daki sai da ta ringa ihun ya kyaleta haka, dan kuwa sai da ya dauki fansar kyaleshi da ta yi na tsayin kwana arba'in wai ita wankan jego, hanyar nan sai da ta ji kamar zai dade mata fata , da kyar ya sarara mata yana lekenta zuciyarsa cike da wani irin mamakin halitarta, itace dai karama, ama kuma a lamarin nan ta dame HUZNAH ta shanye, sai dai ya bar abinsa a ransa burinsa a kulun kwananta ya zagayo ya labe tunda magariba sai sallar asubahi.....to yaya zai yi da ransa, tuzuruwar kauye da ta tashi shigowa rayuwarsa da tumtube ta shigo, tunda ta auko kuma ta kanainaye gurbin adalci kawai ta bari a zuciyarsa.................



____________ranar kai ziyara gidan yari____________


A nutse yake tafia, gefensa Inna Hindu ce cikin zumbulelen hijabinta tana goye da Yarima ko nace daga bayansa dan kuwa a zagaye suke da dogarai da kuma Sarkin yanka sunna ziyartar mutanen gidan yarin har suka zo dakin da Umma ke ciki

Tun daga nesa kadan zaka ringa jin wani irin wari da duhu a daki har ka iso, sunna isowa da sauri ya dauke kansa, domin Umma a shanye take ta baza kafa kuda sai bin jikinta yake wanda ke fitar da wani irin ruwa mai tsami , haka kuma jikinta du ya yi wani irin kuraje luhu luhu, fatar jikinta ta dafe, gashin kanta tamkar na mai cancer du ya zube ya yi furu furu, ta rame sosai sai manyan idannuwa , ita daya ce a dakinta domin wa'inda suke daki daya sun gudu dan idan ciwo ya yi ciwo haka take yagar fatar jikinta tana ihu, an kaita asibitin ya fi a irga, ana bata maganin ama sai a hankali jiki fa ya tabu, wanda a yanzu take rokon a kasheta ta huta, abin ya gagara

Juyawa ya yi yana umartar su koma, a lokacin da ta hangi Hindu ta kuma hango goyon dake bayanta, a lokacin ta saka wani kukan mage mage kare kare tana nuno bayan na Hindu, dan kuwa wani irin abu da ya ringa tukota kennan dai da gaske har haihuwa ASADEEK ya yi? Lalle ita ta zo a banza zata koma a banza....................



Asadeek kuwa, a tausashe yana dan kallon kasa da irin girmama ya ce da Inna" Mamah, a raka ku gida, zamu je kauye mu dawo"

Inna ta amsa ta juya dogarai suka sakata a tsakiya tana taku daidaiya ana gaisheta tana amsawa hakoran nan a fili da hakoran makarta bibiyu sama da kasa suka wuce ciki


A cikin mota sunna tafe Sheikh ya dube shi, a hankali ya ce" ABU TUFAINAT, murmushin me kake yi?"


ASADEEK ya juyo ya kalli Sheik, ya yi murmushi ya ce" Ina yin dariyar sarkin yanka ne, yace wai anya zan kuma.iya yarda da wani dan Adam a kan abinda Umma ta min?"

SHEIK na kallonsa ya ce" Nima na ji tsoron haka sosai"

Asadeek ya koma ya ringesa, cike da iza ya ce" Idan na yi haka kennan ban godewa Allah ba, ai dole za'a iya haduwa da haka, ba kuma haka zai sa mutun ya rufe kansa ba, MUTUN ai rahama ne, Kamar yadda aka samu na banza sosai, haka kuma ake da na kirki sosai, misali GAKA nan, ina alfahari da hakan...ina kuma fatan mutuwa cikin jarabawa, dan kuwa bawan da Allah ke so yake jarabawa........"


SHEIK na murmushi ya ce" Amen ya Allah "







Nima na ce

*ALHAMDULILAH*



*ALHAMDULILAH*






NAN NA KAWO KARSHEN LITAFINA MAI SUNNA UMUGHLUK ITIBEL, INA ROKON ALLAH YA YAFE MIN KURAKURAN CIKI, SANNAN INA ROKON DU WANDA NA BATAWA YA YAFE MIN, INA MIKA GAISUWATA A GAREKU BAKI DAYA, DAN KUNNA DA YAWA WALAHI KUMA KUNA DA MAHIMMANCI SOSAI A RAYUWANA......, INA KUMA FATAN ALLAH YA SA DAGA WANNA LITAFINA NA GABA IN AJIYE RUBUTU HAKANAN, MAI TAKEN *ƊAKIKA ƁIYAR*










Nobel dina na gaba in sha Allah.........



*ƊAKIKA ƁIYAR*




TAKU CE yar mutan NIJAR.........



*Sajida*






Nd

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment