Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

KO SOYAYA, ADU'A ITACE MAKAMIN MUMUNI!*"

Daga haka HINDU ta juya tana ficewa a dakin tamkar zata tashi sama ta nufi nata dakin ta bude ta shige a hankali itama ta silale ta saki kukan da ta rike da dukkan karfinta a gaban y'arta, kwarai da gaskiyar yayarta, basuda isashen lokacin da zasu tsaya wasa da NADIRAH, idan suka ce zasu tsaya har ta bada amanarta ta laluba da rarashi da nuna kauna da meye meye meye ko? Sunna ji sunna gani wankin hula zai kaisu dare, itace a kauye, ama ga dukkan alamu ta fi yaya sannin rikicin wasu marikitan!, Shi a tunaninsa zasu je lai tsaye su ga mutumen da shekaran jiya da kansa yace sai a jima ana son ganninsa ba'a samu ba su kai masa wannan magana mai kama da tatsuniya kai tsaye dan shine aljanin sannin abu da hawa kan abu ya yarda ya hukunta bafansa? Idanfa yana tare da wanda koda za'a gile kansa ba zai taba yarda da cewa yana iya masa karya ba ya daurewa bafan nasa? Idan a wajen yin binciken Bafansa ya juyar da komai ya hau kansu fa? Shikenan sun zama mararsa ilimi dan basu je boko suka nitsa ba ko? Lalle zasu nuna masu islamiya itace tushen komai, a cen ake koyar da komai, su kuwa yayan malamai ne ba iya Alkur'ani suka karanta ba, da izinin Allah zasu kai ga ci! Itafa dama a duka kaf rikicin tafiyar y'arta take ji, tunda ta ji yanzun ko? Zasu ci karfinta in sha Allah!

Irin zaman da ta yi a saman gadon bayan fitar innarta dole ta baka tausayi

Kamanin fuskarta kana kallo zaka gane a wani hali take

Fuskarta ta yi jajajir haka idannuwanta sun yi jajajir

A zaunen da take ji take yi tamkar duniyarta ce ta zo karshe a yau

Tana kawo magangannun nan ne sala sala tana bajewa da irin yaren da zata gane

Da ace iya innar birni ce abin ya tsaya da ta tabata da sauki, domin dama innar birni ba fai fushi ba
Sai dai magangannun innarta sun sakata a halin ita ba mutuwa ba, ita ba rayuwa ba

A irin zaman da ta yi Allah ne kadai ya san halin da take ciki

Mahaifinta ya sake zama a gefenta, muryarsa a tausashe sosai ya fuskanceta ya ce" Nadirahna, ki yi hakuri, ki yi hakuri kin ji? Ki yi hakuri sannan ki fadawa Allah, abin nan fa kila wa kala ne, ba lalle bane ya tabata, idan muka fadawa Allah shine zai yi mana zabi, sannan kar ki saka maganar Aminu a ranki, Aminu namiji ne kamar duban sauran maza na duniya, a kanki ba zai kashe kansa ba ko ua bijirewa iyayensa, ki dauka hakan ne alkhairinki, domin koda innarki bata da gaskiya a wani wajen tanada a wani, mahaifiyarsa bata sonki NADIRAH, nima ba zan taba bashi yata ba, domin koda yar Allah bani ce ke ina son abina, kema yar gata ce, kuma ki sani idan auren nan ya tabata ba yana nufin zaki dawama a gidan sarautar bane, na san bakya ra'ayin rayuwar sarauta, idan har Allah ya bayanar da gaskiya Nadirahna zai gode mana sannan ya salameki salim alim kin ji? Ki kwontar da hankalinki dan Allah ki fuskanci abinda yake gabanki, domin yaki ne mai girman gaske, a fada mai tsaurin gaske kin ji?"


Bata iya bashi amsa ba, ama irin yadda take kallonsa ya san tana jinsa, vai bar dakinta ba sai da ya shinfida mata darduma da carbi da alkur'ani sannan ya tafi ya daura alwallah shima ya fito falo da dardumarda ya fuskanci gabas, domin ya san a yau ba zai iya rintsawa ba ko yaya ya so rintsawar


A bangaren NADIRAH kuwa, a lokacin da ta fuskanci kowa ya fitta daga dakin nan an barta daga ita sai halinta tamkar wace ta rasu aka kawo kabari ta karra saukowa kasa gaba dayanta daga saman gadon tana kallon kasa ta ringa auna komai dala dala, tun daga bayanan mahaufinta,na mahaifiyarta, na innarta, irin gidan da suke ciki, komai da komai sai ta samu kanta tamkar mai hauka sabon kamu

Salayar da mahaifinta ya shinfida mata ba itace a gabanta ba a irin wannan lokacin da ta nutse cikin kogin tunanin shin ta mike ta dadaura wani abu ta shake kanta ta bar duniyar kowama ya huta ko ta mike ta dira ta tagar nan ta gudu idan safiya ta yi a nemeta a rasa?

Ta jima tana kan wannan shawarwari biyu, wa'inda suka karrawaa kukanta karfi ta yadda tta ci kukan da bata taba irinsa a duniya ba, irin kukan nan da zaka iya fasaltashi da kana yi kana fatan dama mutuwa ka yi da irin wannan ranar? Irin kukan nan da shedan ke karra masa siga har ka ringa jijiga kana gannin ka zo duniya a banza ne, kukan kana yinsa ne kana auna rayuwarka tun daga lokacin da ka malaki hankalin kanka kana auna me ka yi da tsauri haka ta sameka,? Kuka ne kana yi kana tunanin aanya mutanen dake zagaye da kai sunna kaunarka kuwa? Irin kukan nan ne wasu kkan kashe kan nasu, wasu kuwa su fada a mugun hannun da zai basu shawarar guduwa............

Tun tana jin muryar kanta har ta dawo tamkar madiriritsi ya danneta tana ihu babu mai jinta

A hankali yinwa ta fara dawo da ita a doron duniya

Tun da sauran sawaye yinwar ta ringa kwakularta

Karfin Adu'ar iyayenta ne? Allah ne ya yi ita din ba zata kashe kan nata ba? Ita dai yinwar nan ta sakata bude ido ta yi tsuru tana jin tashin hankali kamar ana rarakarta

A hankali ta shiga auna yaya mutuwar kennan?
Uwa uba idan ta je a wannan halin yaya zasu kare da walakiri kennan? Wai shinfidar kennan

A hankali ta shiga tunanin iyaye

A duka kaf abinda suka roka a wannan tashin na farko wanda shine na farko a tarihin rayuwarta cikin duban wanda suka yi mata

Yau ko a shegiya suka haifeta sun mata adalci da basu bi da cikin ta magudadar ruwa ba

Uwa uba suka jure shirme nata da sakalci

A hankali ta gangaro kan wace bata yiwa laifi

Idannuwanta ta rintse da zafin gaske da ta tuna kalaman innarta

A hankali ta kawo maganar a namijin kansa

Haannayenta ta watsa tana tunanin wai a cikin wanda suke kira sarkinsu, da wanda take keta rantsuwar tana iya guduwa a kansa wane ya cencenci bijirewa iyayenta a kansa?
Namiji dai sunnansa, zungundumin katon da ba miji yake a wajenta ba bale tace mijinta ne ai maganarsa na kan ta iyayenta

Kennan yaya sunnantama? Zungureriyar yar iska marar rabo?

Aminu baa ciwon yatsa yake yi ba, Aminu angwoncewa zai yi?

Shi kuwa dayan azalumin za'a kai masa ni shima!

A gaskiya a cikin biyu bata ga daya da zata bijirewa iyayenta saboda shi ba

Manyan azalumen ya dace ta yi yaki da su,

Ita marar gata ko?
Iyayenta bayi?
Abinda ya fi sakata tsanar rayuwar gidan tun tana yarinya idan mahaifiyarta ta tafi sai dare ya ratsa take dawowa, idan ba fitsari ta tashi yi tsakiyar dare ba bata ganninta, idan aka yi wasa sai a yi kwana biyu bata ga umanta ba!

Mahaifinta kuwa yana fama bawon Allah, idan yana tare da ita kowani lokaci ana iya tashinsa dan aikin uban gidansa!, Ashe duka wannan bautar bata isa ta basu daraja ba? A banzan dai suke? Shine za'a tura yarsu yin kisa?
Ita babu ruwanta da wani wai shi ANNEMOKAL ITIFAL!, abinda yake gabanta yaki da azaluman nan, dama ta rayu cikin farin ciki dan su zo tashi daya su wargaza? Lalle sun siya da kudinsu da suka saka Innar birni, Aban birni, da innarta kuka ris ris, ita kuma suka sakata summa! Maganar innarta ne, ba maganar soyaya bace, idan kuma taa gama aikin zai salameta!

Wannan tunani ya kai hankalinta saman dardumar dake shinfide, a lokacin har asuba ta fara sanyo kai domin karfe hudun dare ta yi

Jiki a sanyaye, kwonya cike da tunanin abinda yske kamar film ta shiga gabatar da sallalinta tana fatan wanda ya san inda ciwonta yake ya warkar mata, ...........

Tabas BATA FARA DAN TA DAINA BA!, Aminu kuma yana nan daram a zuciyarta ba wai ya gogu ba, sai dai tana tunanin biyayar da zai yiwa innarsa itama zata kamaanta yiwa nata innar , sai dai shi ya fita cin riba, tunda shi aure zai raya, ita kuma CETON RAI za'a turata!




Yanzu za'a fara 對對對對對對對
8/13/22, 22:58 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS?*

簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alalaminmu ぐancinmu.```
簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*


2儭0儭





Kusan haka suka kwana, kowa na kaiwa Allah kukansa da neman sauki a wajensa

Kamar yadda aka saba daukanta da duku duku hakan ce yauma, sai dai yau abinda ya sakata jin zuciyarta zata tarwatse Abanta kadai ne ke tsaye har aka karasa da ita dakin gyaran, bayan a da innarta na gefe, innar Birni na kai kawo abinta

Kai ta gyadawa Abanta dake yi mata magana kasa kasa cewar ta yi kokari ta samu barci domin idannuwanta sun kumbura hulu hulu, hakama kumatunta

Da ido ta raka shi, sannan ta gyara zamanta jiki a sanyaye tana jira ta ji an fara yi mata abinda aka saba

Abanta na fita ya rasa ina zai nufa, shi kam tunda yake bai taba gannin yayar da kanwar sun yi fushi irin haka ba,

Jiki ba karfi ya nufi ciki da niyar nufar dakin Inmar birni, sai ya tsinkayo maganarsu a kicin

A hankali ya karasa ya dan labe yana sauraronsu, a tunaninsa har yanzu a cikin fushin suke tunda har ya ga babu wace ta damu da lekawa gannin an kai yarsa wajen gyara da sauransu

"Aunty, aa, kar ki cire idon zakaran nan, sakashi walahi" Hindu ta fada da sauri tana tarewa ta saka shi a cikin dahuwar da suke yi

FADIME ta dafe gaban goshi ta kai zaune tana fadin" Kin fi karfina Hindu, wannan dahuwar zaki ba yar taki? Walahi zaki sakata a uku bayan kin san komai"

"Ni babu abinda na sani, hasalima babu abinda muka sani mu dukanmu aunty, ina kankanar mai yusufan? Gaskiya zuwa zan yi na kai mata tun jiya rabona da ita fa" Hindu ta fada tana turo baki

FADIME ta yi yar dariya tana tafa hannu ta ce" Kin manta mun saka jaka goma goma, walahi idan kika je sai kin bani kudina, dan Allah ki barta mu gani ko ta yi hankali mana!, Haba kema, ke kin ce in na je wajen mijina kin ci jika goma, ni kuma in kika je wajen yarki na ci jaka goma, ehe"

Yar dariya ce ta subuce masa har yana kama baki, kai kai kai, matan nan ba zasu taba girma ba idan sunna tare, watau haka aka dora dan a kuntata masa shi da y'arsa ko?
Wani sukuni ya ji a cen kasan zuciyarsa, na ganewa da ya yi ba fushi mai sunna fushi suke yi da su ba, summa sunna ransu

Juyawa ya yi ya nufi ciki zuciyarsa cike da dana sannin ihun da ya yiwa matarsa a kan abinda ta fi shi gaskiya,, ama in sha Allah zai bata hakuri, domin rayuwarsu da suka gina bisa aminci ne ba bisa fin karfi ba da zalunci irin na wasu mazan


Abincin kari HINDU na mikawa masu mata gyara ta juyo ta komo suka ci gaba fa lamuransu ita da y'ar uwarta, hakan ya karra sakawa NADIRAH ciwon kai da zafin jiki mai zafin gaske, har ya zamto a yau gyaran safe kadai suka yi mata suka rakota da nufin ta koma ta huta , domin kana ganninta zaka gane bata yi barci ba , idannuwanta sun nuna

Jiki a sanyaye ta idasa shiga falon da salama a bakinta, a lokacin HINDU na tsintar Zogalen da ta sa aka kawo mata danya sabuwa fill zata yi mata hadin tumaturi da kwai , shima gyara ne na musaman


Muryarta bata fita da kyau ta sake yin salama sannan ta idasa shigowa jikinta ba karfi tana baza idannuwanta dan gannin Innarta ce kadai ko harda Innar birni?

Gannin bata ga innar birni ba ya sakata sakin shagwabar da ta saka innarta zuba mata ido tana kallonta

Raurau ta yi, nan da nan sai ga hawaye kamar an kunna pampo yana zuba ba kakautawa , sannan tana tsaye tana kallon Innarta, watau jira take yi sai ta fara zuwa inda take domin ai a ganninta itace ua dace su lalaba ba a ringa neman kasheta ba ko?

Innarta ta kalli yayarta, ta kuma kallon NADIRAH

Gefe ta matsar da zogalen tana mikewa ta ce" Wayo Allahna jaririyata, zo zo zo nan zo, wayo haka kawai saboda abin duniya na ki nemanki tun safe, zo, aunty zan biyaki kudinki bari mu yi waya da sarki!"

Dariya ce ta kubucewa Fadime ta kirki, dan walahi har fruits din da tale yankawa ta ajiye tana rike ciki
Dama ta san ba zata taba iya wuni bata nemo y'ar ba, ko a yanzu ta cikata da hirar Nadirar, uwa uba wai sarki, in Hindu ta takarkare tana labarin mijinta in bako ne kai sai ka duka ka gaisheta dan zaka yi tunanin sarkin garin gaba daya take nufi, koda yake, sarkin yake, sarki ne a rayuwarya, mutun tsayaye a kan lamarin iyalinsa, rashin karfinsa bai sakashi rayuwa a matse da iyalinsa ba, yana yin iya yinsa dan su rayu cikin farin ciki, ya daure mata kugu ita kuwa sai shagalinta take ita da y'arta

Kuka NADIRAH ta barke da shi tana shigewa kirjin HINDU ta ce" Innata, fushi kike yi da ni? Innata shine ko ki leko ni?"

A hankali ta dagotatana sake taba jikinta ta ce" Indi baki da lafiya ne? Kin ji jikinki kuwa?"

NADIRAH ta mayar da kanta ta dora tana sake rintse idannuwanta ta ce " Innata, ki cema innar birni dan Allah ta yafe min kin ji? Ki ce mata ba zan bijire mata ba, ki ce mata ko me take so zan yi kin ji? Ta daina saurin yin kuka idan na bata mata kar aje na zama yar iska kin ji innata?"


A hankali FADIME ta tsagaita dariyar da dama ba wai tun karfi bane ta daki murya take kyakyatawa tana kallonta

A sanyaye ta dan kawar da kanta, daga garesu kirjinta na wani itin dokawa fat fat fat na tsagwaron kaunar gudan jinninta

Bata shirya ba ta juyo da dubanta sanadiyar jin hannun NADIRAH a saman cinyarta ta rike a hankali ta ce" Innar Abana, ki yi hakuri kin ji? Ki yi hakuri innar Abana, tunda har Innata tace auren nan ba maganar soyaya bace, ceto ne, kuma idan komai ya wuce yana iya sawake min bayan ya gode min, Innata ba sai na zo na samu Aminun ba mu yi abinda ya dace?"

FADIME ta zubawa fuskar Yarinyarta ido, a hankali ta ringa hangen tsagwaron yarinta a tare da yarinyar bayan ta daurari furucinta


A hankali ta janyota jikinta ta rungumeta da runguma mai zafin nan, ya zamto kanta a saman kirjinta tana shafa bayanta kanshin turatenta gaba daya ya gogu a jikinsu kamar sunne suka shafa turaren,

A hankali Innar birni ta ce" Allah ya yi miki albarka, Allah ya baki ikon cin galaba a kan makiya, in sha Allah daga yanzu da kika san komai zamu dawo ne munna gabatar da shirinmu bayan sun gams nasu, kafin nan mu tafi ki kwonta ki yi barci kin ji yar gidan innarta?"

Wata irin ajiyar zuciya take karra saukewa tana jin wani dumi special daga kirjin mahaifiyarta marar cutarwa yana ratsa fuskarta, haka kuma murmushin mahaifiyar tata idan ta dago kai sai ta ji dama ya tsaya haka ta yi ta kallonsa kar ya katse

Ajiyar zuciya, hadi da lalausan murmushi HINDU ta yi tana jin wani irin farin ciki na ratsa mata zuciyarta ta dubi FADIME dake dubanta niyarta ta kai NADIRAH ta kwontar da ita

A hankali ta sakar mata murmushi tana girgiza kanta ta ce" Aunty ni da zan yi wancen, kaita dakinki dan Allah ta huta , na tabata bata yi barci ba, Indin innarta sai kin farka zan baki wani labari mai dadi kin ji?"

NADIRAH ta gyada kai tana biye da mahaifiyarta nesa nesa kadan tana jin banbarakwai , domin bata saba haka ba sam

Sunna shiga ta tsaya tana kallon maman nata dake gyara mata shinfidar

Bayan mamanta ta gama ta juyo tana kallonta

Wani murmushin ta sakar mata mai sanyi ta ce" Indi zo ki kwonta mana?, Cire wannan rufar ki kwonta ama banda safar , bara na gani cikin maganin Abanki ko akoy na zazabi na baki........"

Motsin da ta ji a bayanta, kusa da bayi ya sakata juyowa da sauri

Gannin mijinta ya sakata dan sada kai hadi da murza goshinta kamar wace kunya ta rufe din nan, sai kuma ta ce" Dama, dama innarta tace na shinfideta a wajena, kuma, kuma sai na ji kamar jikinta akoy zafi, shine nace bara na bata magani......"

Murmushi ya saki yana kallonta, shi dama ya san harfa kunyar kar ta ja y'ar a jiki ace tana nunawa yar fari so yake sakata aikata wasu abubuwan

Zagayawa ya yi yana sake dubanta ya ce" To ke da dakinki, magungunnan mijinki, da kuma yar hindunki sai kin fada min, kin ga ni na tafi masalaci a cen kuma zan yi la'asar da magariba, idan zan dawo ina son tuwo tukin Fadimatu Zahra"

Kai ta karra sadawa, NADIRAH kuwa ta saki murmushi domin mahaifinta sai yar dariya yake yi mata sannan ya daga mata hannu ya fice


A hankali ta karasa saman gadon ta hau tana sake bin mahaifiyarta da kallo, wace le boye nata murmushin itama , a ranta ta ayana' Irin rayuwarku na so samu, wace koda baku da yanci a tsakaninku akoy yanci, rayuwa mai cike da barkwonci da soyaya, bama tare da ku na lokaci mai tsayi ama na san a kan daya, daya sai ya bada kansa a sare, ina matukar girmamaku, ina kaunar dadadan amincinku, na so na gabatar da haka da Aminu, domin alamunsa sun nuna shima zai kasance uba, amini, masoyi, yaya a gareni, sai kuma ga bukatarku wace na rantse da wanda raina ke hannunsa koda hakan na nufin rasa numfashina zan aikata, domin ba haramun bane, ama na tabata in da rai da rabo, koda Aminu ya auri wata ni ya fara sanni a soyaya idan na dawo zai dubeni'


Sai da ya narke mamanta ta zuba mata siga sannan ta karaso ta zauna a gefenta ta mika mata tana fadim" Shanye, da innarki ta sakaltaki magani sai an narkar an zuba siga"

Murmushi ta yi mai sanyi, muryarta a sanyaye ta ce" Innar Abana, toh ki baki a bakina mana, innata ita ke bani na shanye kuma ta kama min kaina"


Murmushi innar birni ta yi ta kama mata ta bata da kan nata, tana shanyewa ta bata ruwa, nanma ta sha sannan ta kama mata kanta ta yi mata ADU'A, kuma ta gyara mata kwonciyarta ta zauna a gefenta tana kallonta

A hankali Nadirah ta dago idannuwanta tana kallon innar Birni, Innarta tace a duniya babu mai sonta irin innar birni, wannan magana ta tsaya.mata a zuciya har ta kori tsohon tunanin dake ranta


A hankali ta ce" Innah?"

Fadime ta kalli fuskarta

NADIRAH ta ja numfashi kasa kasa ta ce" Innah, idan na tafi, shikenan ba zan kuma ganninku ba?"

FADIME ta sake zuba mata ido, ta kasa ce mata A

NADIRAH ta ce" Ta yiwu a ranar da aka kaini ya gane ba wace aka bashi bace ya saka a gilen kaina ko?"

Kirjinta sai da ya doka, tana kallonta ta ce " Ki fadi alkhairi mana ko ki yi shiru INDI, sannan an ce bai san BAHIJA ba, ina gannin zuwanki ba damuwa bane tunda bai san wace tale y'ar sarkin ba"


NADIRAH ta gyada kanta, kasa kasa ta ce" Innata, sai nake jin abin wani iri, yaya zan rayu a cikin mutanen da duke baki a wajena?, Yaya zan iya kaucewa kaidin masu kaidin cikinsu?, Yaya zan iya kare mutumen da ban wanene shi ba?"

"Dama wanda ya isa ya kare ki daga dukkan abubuwan nan wanda ya baki aron numfashi ne NADIRAHNA, NADIRAH kowace mace bakuwa ake kaita bakon wajen da zata yi zaman aure, dama kuma rayuwa ta gaji ka zauna ka birge wani, wani ya tsaneka ba tare da ka aikata masa komai ba, halinka shine zai kwaceka NADIRAH................. sai maganar shi , shi Uban gidanki" FADIME ta fada tana shafa gefen fuskar NADIRAH a hankali

NADIRAH ta dago lumsasun dara daran idannuwanta da mamaki ta ce" Uban gidana?"

Mahaifiyarta ta gyada kai yana kallonta

NADIRAH ta ce" Innata, kina nufin ni baiwarsa?"

Mahaifiyarta ta zuba mata ido tana kallonta,

NADIRAH ta mayar da kanta a hankali saman cinyar mahaifiyarta ta lumshe idannuwanta, muryarta cen ciki ta ce" Ni ba baiwa bace, sannan ni ba yar kaso bace.....Innatah, ba zan rayu a gaban kowa kamar yar kurkuku ba , ciki harfa UMUGHLUK ITIFAL!"


A tsorace mahaifiyarta ta saka hannunta ta......
8/13/22, 22:58 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS?*

簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alalaminmu ぐancinmu.```
簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞簞

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍鳶仍

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*




2儭1儭




A tsorace mahaifiyarta ta dago fuskarta tana kallonta ta ce" Me kike nufi?"


NADIRAH ta tsare fuskar mahaifiyarta da kallo, tsoro, tarin shaka na bayana a saman fuskar mamanta, dan haka sai ta yi murmushi a hankali ta sake komawa tamkar mage ta lafe a jikin mamanta ta yi lamo bata ce komai ba, hakan ya sa mamanta mayar da hankali, ta ci gana da tsoratar da ita wanene UMUGHLUK ITIFAL, da jama'ar dake tare da shi, da tunatar da ita wacece ita, lalle baiwar take tunda yar bayi take

Ita kuma a ranta murmushi kawai take yi, tana ayana abubuwa a ranta kamar haka' Ba zan je ko'ina na rayu kamar baiwa ba Innah, ban ce a aurani a kaini ba, ba kuma zan je a matsayin yar sarki ba, zan je a matsayina na ni NADIRAH, bayanshi bani da matsala da kowani sarki ko hadiminsa!, Ki kwontar da hankalinki, bauta ce ba zan yi ba innata' .................


Wannan shine mafarin shiryawar NADIRAH da iyayenta baki daya, sannan mabudi wata sabuwar rayuwa mai cike da sarkakiya da salo kala kala

A wunin rana ana kula da jikinta ne da gyaran ciki kamar za'a cenzata baki daya

Daga bakin lokacin da zata kasance da iyayenta su kuma nasu salon sunna kokarin karra taurara dukkan wani tsoron da zai sakata aikata aikin da za'a zo mata da shi dan a cutar da mutumen da suke kira Uban kowa ne....., Takan yi murmushi tace banda ita, ita kam ba ubanta bane gaskiya!

Da zarar innar Abanta ta matsa kuwa wani rikitacen yare innarta ke yi mata mai tafe da rikitaciyar tafia mai wuyar fasara a kwakwaluwarta ita NADIRAHn innar kauye

A gaban Innar birni sukan nuna mata Uban kowan nan uba ne ko kallonsa bai dace ta yi a cikin ido ba, innar birni na matsawa fakat Innar kauye ke fadin mace take, Allah ya gama bata komai tunda ya haliceta mace, a matsayinta na mace tana iya mayar da UBAN nan na Kowa dan jaririnta, ba aure ba, Allah ya sa mace dubu ya sani a duniya sannin ragage ne tunda mu'amalarsu ba ta shaar iskar junna bace, ta sunna ce!, Wai innar kauye ta dubeta duba irin na basira tace da ita zata fuskanci kamar bashi da lafiya, wannan rashin lafiyar tasa idan har ya yarda ya shiga harkarta zata yi wasa da ita, da rawa irin ta disko danser kugu a daure kafa a sama?, Ira innar Kauye ke cewa ta karkada kugu kamar zai tsinke fiye da dandali idan UBAN KOWAN cen ya shiga harkarta, to ira maganar gaba daya a duhu take zo mata kuma a dunkule, sai dai ta cira kaita kada kai ta fadawa kanta cewa ba zata dauki hudubar innarta ba, domin a hilacewar Innarta kamar tana son nuna mata zata je zaman aure, kamar yadda

Please Login or Register in order to submit comment